Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanzu zasu tafi."

Miqewa tayi tare da shiga kitchen ta fiffito musu da abin kari ta jera musu kan taburmar shiko Bappa ya bud'e musa sannan ya biqa musu ruwa a qoryar suka wonke Hanna yensu,
tare suka ci abinncin da Bappa yana mai kallon su cikin qauna.

Bayan sun gama sukaje sukayi wonka suka shirya tsab Sani yasa musu kayansu a mota ga kondunan fruits har 3 ga qoren gon zabbi har 2 ga jara kunan man shanu guda 3 tare da jarakunan nono 2 sannan ya had'asu da qoryan zuma yar asali har guda biyu.
sannan suka shiga cikin gida sukawa Inna sai wata rana har zasu fita suka tsaya cak jin muryar wata tsohuwa cikin matsifa tace.

"Kai Bappa wato har zakayi baqi har su gama zaman su,
ni bazaka ce suzo su gaida ni ba,
Ku kuma baqin muna furci ko Baku San darajan manya ba!
ke kuma muna fuka harda kukan gulma toh wlh ki shirya yaune zakiyi kuka mai dalili Yau zaki mai mata kukan da kikayi shekaru 40 da suka wuce!
Ku kuwa baqi yau zaku san kun shigo inda ba'a fita dan kun tari kan bala'i da kukazo nan garin!
ke kuma Bodd'i ko? Yau kyawun naki zai zama ganimar wasu gara dai!."

Cikin mamaki Aliyu da Sani suka juya suna kallon Bappa da inna wacce tuni take zubda qollah murya na rawa take cewa.
"Dan Allah Lari karki cutarmin da Bodd'i,
Lari kibar baqin nan karki sasu cikin mugun furuci !"

Ido suka tsurawa Bappa cikin tuhuma da neman qarin bayani,
shiko Bappa hannun su ya kamo har zuwa bakin motarsu
cikin sanyi yace.
"Aliyu kar ku tsaya neman qarin bayani ba lokaci ku tafi kawai kar masifan bakin Lari ya shafeku ."

Cikin jin haushi ganin gaba d'aya yadda suka rud'e da kalaman matar ya kalli Bappa yace.
"Bappa wacce ita? kuma me had'inku da ita? me kuma zata yi muku?!"

Hannushi ya kuma ja cikin murmushi qarfin hali yace.
"Aliyu kubar wannan yanki Ku hamzarta kar lokaci ya kure muku."

Ganin bazai basu amsa ba yasa suka juya zasu shiga ,
Sosai Aliyu yai mamaki ganin irin kaya da Bappa ya had'a musu ,
Matsoshi yayi cikin sanyi yace.
"Bappa wannan kaya ai sunyi yawa".

kai ya gyada mai tare da cewa .
" a a Ali bayyi yawaba kai dai kuje sai wata rana."

"Toh mun gode" yace tare da juyawa har zai shiga mota sai kuma ya juyo da sauri cikin mamaki jin hayaniyar shanaye da raquma da suke ta shigowa cikin rigar a guje ma kiyayan na binsu a baya tako wacce kusurwa shigowa suke.

Ganin wannan Gainako da ya kawosu rugar ya nufi Bappa a guje yasa shima ya dawo gaban Bappa .
Shi ko Bappa ido kawai ya rumtse tare da cewa.
"Gainako yau kuma rigarmu zasu shigo ko ? yau ma Bodd'i suke son d'aukewa ko?."

Sai hawaye shar a idonshi shiko Gainako sai haki yakeyi cikin d'auki war numshi da haki yace.

"Bappa sunce in muna son kanmu da lafiyar mu a kai musu Bodd'i!
inko muka bari suka shigo wlh zasu kashemu su qona rigarmu kamar yadda sukayiwa rigar Rumoh."

Kafin yayi magana sai ga mutanen rigar duk sun hallara qofar gidan a gaban su wasu dottijai guda 3 suka kalli Bappa cikin tausaya wa sukace.
"Bappa ka samu Ku fita ta qofar baya kaida Bodd'i dan tabbas ita suke hari."

Cikin tsoro wani matashin da ya iso yanzu yace.
"Wlh suna nan a qofar bayan ma sunce nanda azahar a fito musu da ita da kuma dabbobinmu."

Shi kam Aliyu so yake sumai bayani suko sun k'asa sai b'ari suke.

Bappa ko jin haka yasa ya matso jikin Aliyu hannushi ya riqe cikin rawan murya da neman
alfarma yace.
"Aliyu taima konka nake nema zaka taima ka min?."

Cikin kaushin murya yace .
"Bappa ka gaya min meke faruwa?,
ai taima ko shine aikina kodako zan rasa raina sabida nai alqawatin taima ko kafin na fara wannan aiki nawa Bappa aini raina da lafiyata kan taimakon qasata yake ka gaya min suwaye ke son kasheku?."

Kai ya rinqa juyawa cikin sanyi ya koma cikin gida ,
Jim kad'an ya fito riqe da qura'ani mai girma cikin sauri ya miqa mai tare da cewa.
"Aliyu kayi alqawari tsaka ninka da Allah zaka taimaka min zaka kuma riqe amana?."

Ranshi cike da jarum ta yace.
"Nayi alqawari zan taima ka maka kuma zan riqe amana bazan kuma k'asa taima ka maba."

Cikin jin dad'i yayi ajiyar zuciya sannan ya kalli mutanen wurin tare da riqe hannun Sani.
" yace Sani Kaine shaidan Aliyu a garinku in kun koma."
Ya kuma juya ya kalli taron mutanen wurin cikin d'aga murya yace.
"Ku kuwa kune shaida na da alqawarin Aliyu."

Kusan a tare su kace
"Ehh".

Murmushi qarfin hali yayi sannan yace.
" Aliyu na baka auren Amina Bodd'i bisa alqawarin da kayi min!
Kuma yanzu za'a d'aura auren!
yanzu kuma zaku tafi da ita!"

Shi kam Aliyu ido ya zaro woje tare da bud'e baki zayyi magana .

Da Sauri
Sani yace.
"Alqawari kayi oga kuma tsaka ninka da ubangiji kai wannan alqawarin."

Yana rufe baki ya juya ya zaro kud'i masu yawa a cikin moto sannan ya d'auki kondon dibino d'aya cikin sauri ya dawo gaban Aliyu daya murtuqe fuska kamar zayyi ruwan jini.

Kud'in ya miqawa Bappa tare da cewa.
"Ga sadakin ta dubu 50 sannan ga dibino kawai yanzu a d'aura Aure,
shi oga namiji ne ya halatta ya karbawa kanshi Aure." .....

Gaddara ta rigayi fata General Aliyu yanaji yana ganin wata gaddarar rayuwa ta auka mai Wanda dole girman alqawari da bakinshi ya karbawa kanshi Auren Amina.

Ana gama daurin Aureb tare da shaidun mutanen rigar Bappa ya shiga cikin gida,
cikin sanyi da tausayawa kanshi da matarshi da Bodd'i ya kalli Inna ba tare da wani baya niba ya kamo hannun Bodd'i tare cewa Inna.
"Kiyi haquri wannan shine mafita kuma wannan itace sabuwar gaddararmu."

Itako Bodd'i sai binshi tai yana riqe da hannuta.

Gaban Aliyu ya tsaya da ita tare da miqa mishi hannuta cikin sanyi yace.
"Aliyu ga matar ka!
Bodd'i kekuma kibi mijin ki!"

Ita kam bata fahimci komai ba a zancen nasu sai dai ta fahimci tafiya zaiyi da ita shiyasa sai hawaye ke bin fuskar ta.

Shi kuwa kamar makaho Bappa ya jashi har cikin mata Sannan Sani ya shiga suka tafi .

Suna fita cikin rugar ta gefen dutsen Membila sai ga motocinsu da suka bari cikin Membila cikin mamaki Aliyu ya kalli captain Sani da neman qarin bayani duk da dai ya gane Sanin ne ya kira su dan suzo su bawa mutanen rugar kariya.
hakan ko yace mai .
"Oga nina kirasu."

Kai ya gyad'a sannan yace .
"Toh motoci 4 su isa wanda sojoji kusan 28 a cikin sannan yace .
mota d'ayar kuma ta juyo su koma tare.

Haka kuwa Akyi matoci 4 suka nufi cikin rugar,
suko su Aliyu sunka nufi Hanyar Gembu
domain zuwa Yola..

A cikin motar kuwa Bodd'i ta.....

By
Garkuwar Fulani
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*BANDIRAWO* page 6⃣
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

Pure moment of life writers


*Wannan shafi nakune ku kad'ai Sisters In Islam Mmn jhadijah tare da Y'ar mutan wudil sa'a tafi manyan kaya nis@ online writers & Hurairayabo and Feedoh*



Dungu lewa tai wuri d'aya tana mai wani irin kuka mai sanyi da tausayi dan,
gani take shike nan an rabata da tushenta gatan ta ji take kamar an rabata da farin cikin ta,
a ranta take tuna meyasa Bappa baiyi tunanin komai ba ya had'ata da wannan mutumin mai fuskar mugaye,
cikin jin zafin zazzabin da yake shirin rufeta ta d'an bud'e idonta tana mai kallon tsaunu kan da tsirren da suke ketawa yayin da suke bawa rugar tasu baya a take ta saki wani kuka mai cin rai tare da qamqame jikin ta,
ta takure can gefe jikin motar.

Shi kuwa Aliyu ido kawai ya rumtse cikin wani irin zafi da ranshi ke mishi ,
tunani yake shi da yazo neman mafita da samun sauqi sai gashi wani baqin shafi ya shiga cikin littafin qaddarar rayuwar sa,
shin ina zai Ajiye wannan yarinyar da wani matsayi zai nunata ga Mahaifin shi? da yayan mahaifin nashi ?
shin da wace fuska zai nunata ga sauran abokan aikin shi ?,
kai ya kuma juyawa da qara rumtse idon shi tuno Mama da yayi ko me zatace kan wannan batun ! wanne sherri kuma zata bishi dashi !,
shi a wanne yanayin yazo duniya da ya kasance ba mai ji bantan lamuran shi .

Haka yai ta tubka da warwara,
yayin da shiko Sani driving kawai yake,
zuciya yarsa cike da farin ciki ko ba komai yasan insha Allah nan bada jimawa ba Ogan shi zai samu sauyi a rayuwar sa a haka suke tafe kowa da abinda ke ransa, Bodd'i ko tayi kuka har muryarta ta dashe fuska ta kumbura.

A haka har suka bar jihar Taraba suka fara nausawa cikin jihar Adamawa Yola tafiya suke cikin sanyin safiya yayinda Sani ya samu hanya ba cunko son ababen hawa ya rinqa tsula gudu kamar masu firewa yayin da. motar su Garbe ke biye dasu a baya.

10:25 Am Suka isa dai-dai Gurore inda hanyar ta kasu 3 d'aya hanyar da zata sadaka da cikin birnin Adamawa d'ayar kuma wacce zata fiddaka Adamawa zuwa su Gombe Bauchi Jigawa Kano Kaduna Abuja Katsina Sokkoto da dai sauran sashoshin dake gefen,
d'aya hanyar kuma wacce ta kanta suka bullo itace hanyar tafiya Taraba kuma itace ke sada mutun da qasashen kudancin Nigeria kama su Calaba Onitsha Binuye da dai sauran su.

Suna zuwa dai-dai wurin Sani ya juyo cikin neman izini yace.
"Oga cikin Yola zamuyi ne ?"

Ba tare daya bud'e ido ba ya bud'e baki cikin bada umurni yace.
"Miqewa zakayi kawai muyi tafiyar mota dan bazan tsaya jiran ✈ bare ma wannan bororiyar bata da komai bare muyi tafiyar da jirgin."

Toh yace tare da juya hancin motar suka kama hanyar Gombe,
Allah sarki,
Badd'i bata taba zaton rayuwar ta zata juya mata haka ba yau gashi tabar rugarta tabar jihar ta gashi har tana qetare sauran jihohin da suke maqobtaka da jihar su, zuwa yanzu tabar jin ko yanayin sanyin jihar ta bare qamshin furannin rugarsu,
kuka ne tayi shi har qarfin ta ya qare gashi dama ba abinda taci.


Tafiya ma bud'in ilimi Mahmud Yau yai nisa,
yauko Amina ce tai nisa inda tabar sunan Bodd'i a rugarsu ta d'auko sunanta. Amina daga Gombe ko taji wani sabon suna a bakin Sani .

1:00 pm suna cikin birnin Gombawa diban fari ba'a kwana damuba a tashi.

Kai tsaye Shagalin ku Restaurant suka wuce,.Suna isa bayan Sani yayi parking kafin ya fitoh mah su Garba sun fito daga tasu motar a guje suka bud'ewa General Aliyu mota tare da sara mai kab suka qame har saida ya fito,
Sannan suka bishi a baya har ciki yayin da ma aikatan wurin suka fara yi musu hidima cikin karra mawa suka isar da Aliyu can cikin wurin na musamman su kuwa suka koma baya gun sauran mutane gaba d'aya aka shirya musu abinci da nasha suka fara ci domain sauri suke Yau suke son zarcewa Kaduna.

Shi kuwa General zama yayi cikin nitsuwa sannan ya lumshe idonsa tare da shaqan qamshin wurin wanda ya had'e da sanyin A,C a hankali ya rinqa sauqe ajiyar zuciya har zuwa wani d'an lokaci sannan ya bud'e idon shi cikin furza numfashi ya d'an juya kenan ya haggo Captain Sani ta cikin glass din wurin wanda yake kib da area park daga duk kan alamu magana yakeyi amman bai jin abinda yake fad'in ganin haka yasa ya zaro phone enshi ya kirashi ,
bugu d'aya ya d'aga cikin tsuke fuska yace .
"Kai Sani me ka tsaya yi ka dai san akwai sauran tafiya a gaban mu kai sauri ka shigo kuci abinci muyi sallah sai mu tafi."

Cikin kula yace.
" Oga Meenal taqi ta fito tazo taci abinci kuma sai kuka takeyi."


Baki ya tab'e cikin tsawa yace.
"Toh sai me cikin ka ko cikin ta ? ai in taji yunwa zama taci wani bai saniba kar taci mana kai me naka a ciki,
kawai dai inma baza taci abinci ba toh ta fito tayi sallah tun kafin su Garba su fito su ganta aikin banza kawai."

Ido ta tsurawa Sani cikin zubda qollah dan kab taji abinda yake fad'in ga uban tsawan d'aya buga wanda ya firgitata,
cikin zubda qollah ta zuro qafafun ta cikin dishewar murya tace.

"Bandirawo a ina zan samu wurin sallan?."

Gefen wurin ya nufa da ita sannan ya kaita gun masalacin dake wurin Wanda ga fomfunan da keta zubda ruwa a nan tai al'walah sannan tai sallah duk Captain Sani na tsaye yana mata gadi tana idar da sallah ta komai cikin mota,
shiko ya shiga ciki ya d'an ci abinci a gaggauce sannan ya musu Othern abinci yaje ya aje cikin mota sannan suna fitowa sukayi sallah 1:35 pm dai-dai suka bar garin Gombe.

Kafin 2 ma sun isa Darazau Dara birnin bauchi daga nan suka harba jigawa dutsen kafin 6 sai gasu a Kano ta sabo tumbin giwa .

A nan suka tsaya suka ci abinci sukayi Sallan maggari ba sannan suka jira har zuwa isha bayan sunyi ishan ne suka fara shirin tafiya bayan sun dudduba lafiyar motocin nasu sannan suka kama hanyar Kaduna.

Allah Sarki ita kam Meenal gani take tunda take a rayuwar ta bata taba irin wannan tafiya mai nisan ba tun a Yola ta fara tsinkewa da cewa shike nan an rabata da iyaye ta bare yanzu da taga bayan kanon ma gaba zasu qara kawai sai ta ringa tsiyayar da qollah tare da jan wani irin numfashi ta duqqule wurin d'aya.


A ganin su Captain Sani wanda ya taso Taraba 2 Kaduna in yazo Kano ai ya iso gida.

Dan haka yanzu tafiyar suke a tsanake ,
9:00 pm Suna cikin birnin Kaduna kai tsaye agguwar Sarki suka nufa cikin tafiyar shaidawa mutanen gari General Aliyu na gari.

Jiniyar su ce ta shaidawa mutanen gidan nasu Aliyu ya dawo,
Sani na gama parking ya fito su Garba ma duk suka firfito sauran sojojin dake biye dasu ma duk suka fito kab suka zo gaban General din nasu suna Sara mai tare da yimai sannu da zuwa.

Cikin murtuqe fuska ya d'aga musu hannu tare da murza yatsun sa yana kad'asu alamar su tafi kawai ganin haka yasa cikin bin umurni suka juya suka tafi kab d'insu sai Captain Sani daya ke binshi a baya.

Cikin gida kuwa
Kab suna tare a harabar babban parlon Aysha matar Ya Amir ce zaune a gefen Mama da keta surfa mata masifa sai Abdul d'an goyon bayanta da yake gefen ta yana cillawah Aysha harara cikin izzah yake cewa.
"Mama ai ita bata san zafin haihuwa bane shiyasa take mana iskancin da taga dama tunda tasan ni bancin tuwo ai sai ta dafa min abin da zanci."

Nafeesat ce ta kalleshi cikin tsoro tace .
"Ayyah Yaya Abdul Anty Aysha bata da lafiya fa."

Cikin yatsuna fuska yace.
"Ke kuma muna fuka waya kasa dake?."

Maman ne ta kai mata mari cikin fad'a tace.
"Ba nace ki dena as mana baki ba in muna maganar mu."

Shiru tayi tana kallon yadda Aysha ke zubda qollah shima ya Amir sai sunkuyar da kai yayi cikin tausayawa matar tasa.

Ga masu aiki ya kawo amman dole an maida matar sa y'ar aiki sam baza'a barsu su sake ba.

Suna cikin haka
General Aliyu Haiydar ya shigo cikin murtuqe fuska da manna baqin glass a fuskar sa dan ya tabbata Mama zata tare shi da baqar magana sanin haka yasa cikin cije lips enshi ya zaro bindi garshi ya d'aga sama ya danna kuna mar ya rinqa sakin harbi ba qaqqautawa gaba d'aya ya cika gidan da qara Captain Sani ma dake bayan shi sai hannu yasa ya kama kanshi tare da to she kunneshi.

Su kuwa su Mama gaba d'aya suka waste a guje parlon ya zama ba kowa ganin haka yasa cikin sauri da takun cikar zati ya komai farfajiyar gidan kai tsaye motar ya bud'e sannan ya rarumo hannun Bodd'i ya fizgota woje sannan ya jata sukayi cikin gidan,
shi kam captain sai sake baki yayi tare da binshi da ido.

Kai tsaye part enshi ya wuce da ita yana janta da qarfi suna shiga ya jata har cikin bedroom kan gado ya cillah ta sannan ya juyo da qarfin ya rufe qofar sai ya kuma dawo kan.........



By
*Garkuwar Fulani*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*BANDIRAWO* page 8⃣
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

Pure moment of life writers

*Dedicated 2 Aishat A Muhammad & Ummyn Yusrah and Ummu yahya musa sisin mama & Sadnaf and Husna Abubakar Bauchi*

An kama hannu shi cikin tsoro ya zaro ido woje ganin Aliyu ne tsaye cikin murtuqe fuska ga woni irin cabke mai hannu da yayi ya riqe cikin matsar qashin hannun nashi lokaci d'aya yaji wani irin azaba na ratsa shi cikin in ina baki na rawa yace.
"Hamma Aliyu zaka karya min hannu fa ni ka sake ni ."

Bai kulashi ba sai qara damqe hannun yayi tare da soka yatsar sa tsakanin jijiyoyin hannun shi d'in.

Cikin jin zafi Abdul ya saki qara mai qarfi tare da sunku yawa yana cije hagoran sa a wahal ce yace.
"Wayyo Mama Hamma Ali zai karya min hannu Mama zai tsinka min jijiyar hannun."

Matsoshi tayi cikin isa ta d'ago hannu ta yarfa mai mari tare da cewa.
"D'an iska kawai a gabana zaka karya min hannun d'an nawa dan kai baka san dad'in d'aba sannan baka san yadda uwa ke son d'anta ba,
ai ko mutuwa tana jin kunyar uwa bare kai Aliyu."

Ihu Abdul ya kuma saki da qarfi har kamar zaiyi fitsari a jikin shi.

Jin qaran da ya kuma yine Maman ta leqa fuskar Aliyu da yayi jawur dan takaici bawai dan zafin marin da tayi maiba gaba d'aya idonshi sukayi jazir leben bakinshi sai rawa yake dan fushi hakan yasa ya had'e hannun shi da qarfi wanda har saida hannun Abdul yayi qaran targad'e .

Yana tabbatar da ya targa d'ashi ya yarfar da hannun shi cikin fuzgar magana yace.
"Next time in kayi gigin bud'e qofar nan karya ka zanyi."

Yana kaiwa nan ya bud'e qofar sannan ya shiga tare da cewa Captain Sani ya shigo.

Itako Mama kamar ta bishi ta cinye shi d'anye takeji bala'i take kamar ba gobe fad'a take ko numfashi bata ja .

Shi kuwa Abdul kan kujera ya koma ya zauna tare da tallabe hannun da hannun shi mai lafiyan yana maida numfashin wahala.

Su kuwa su Aliyu suna shiga a parlour ya zauna kan 3 str ya koma ya jingina kanshi tare da lumshe ido yana mai jin zafin kalaman Mama a kanshi ko yaushe bata binshi da kalma mai kyau sai baqin alkaba'i,
gefen shi Sani ya zauna riqe da goran Faro mai sanyi cikin fargaba ya miqa mai murya can qasa yace.
"Ser ga ruwan sanyi ko zaka Sha?."

Baiyi magana ba kuma bai bud'e idon shiba sai kad'a qafa da yakeyi .

Ganin haka yasa Sani yayi shiru sai shiga kitchen da yayi ya kunna gas ya d'an d'aura musu ruwan tea.

Har yanzu idon shi a lumshe yake a hankali ya farajin zuciyar sa tana d'an sanyi dan addu'a da yake tayi,
lokaci d'aya kuma ya fara jin sautin a hankali yaji sautin kukan ta na tashi daga cikin bedroom en sai shesheqa takeyi cikin rawan murya take ta kukan ido ya d'an bud'e sannan ya zurawa qofar d'akin ido zuciyar sa na tafasa.

A ranshi yake tuna cewa ,
Itace qarin matsalar sa ko ya zaiyi ne ma shi bai saniba .

A fili yace.
"Ni bansan ya ake kula da wani ba dan ban taba samun kulan ba nike kula da kaina sai gashi an had'ani da wata jarabar tsiya."

Shiru yayi yana sauraron ta,
har Sani ya fito da y'an cup guda biyu da ruwan tea mai kauri a ciki sai qamshin citta da kanamfari yake,
yana zuwa ya jawo Stol ya ajiye mai a gaban shi tare da cewa.
"Ga tea ."

Shiru baiyi magana ba har zuwa woni lokacin,
shi kam Sani bai kuma magana ba dan ya ga ogan nashi a sama yake .

Can dai ya miqe tare da cup d'in tea d'in a hankali yake takawa har zuwa cikin bedroom en ,
kan gado ya ganta konce rufda ciki tasa hannu biyu ta riqe cikin ta tana kuka murya can ciki tare da yin magana cikin kukan.

"Wayyo cikina wayyo Allah na wayyo Bappa na zan mutu yunwa zata kashe ni qirjina ciwo kaina ciwo."

Duk tana maganar ne cikin fillanci shi kuwa tsayuwa yayi dab da ita sannan ya d'aga kanshi sama tare da kawar da idon shi daga kanta murya a daqile yace.

"Ke ya isheni haka banson sakarcin banza ya zaki zauna kina mana ihun yunwa."

A take ta had'iye kukan nata sannan ta yunqura cikin rawan jiki ta zauna tana bari kar-kar.

Ba tare daya kalleta ba ya miqa mata cup din cikin bada umurni yace.
"Shanye ki ban cup d'in."

A yadda take jin yunwa kamar zata kasheta wai a bata abu a d'an cup d'in nan .

Tana cikin tunanin da qoqarin matsowa ya juyo kanta cikin wani irin cilla mata mugun kallo da yana yin zaki karba ko yaya.

Jiki na rawa ta karba sannan ta kafa kai ta rinqa zugan shi a hankali shiko sai zuba mata ido da yayi har ta shanye.

A take sai ga zufa ta keto mata tako ina lokaci d'aya kuma ta fara damqe cikin ta.

Ganin haka yasa ya fito da kofin kai tsaye kitchen ya nufa yana zuwa ya sake had'a mata tea mai kauri sannan ya dawo ya same ta sai riqe cikin take tana murqususu
cup d'in ya kuma miqa mata,
a wahal ce ta rinqa juya kai hawaye na bin fuskar ta cikin wahala tace.
"Cikina zan mutu."

Bai kula taba sai murtuqe fuska daya kuma yi dole ta karb'i cup d'in ta k'afa kai tana sha tana kallon yadda ya tsuke fuska kamar d'an zai mareta dole sai data shanye sannan ta ajiye .

aiko sai zufa take ta karyo mata dole ta zaune tana yiwa kanta fifita da hannun ta duk da A.C dake fesa sanyi.

Ido ya tsura mata tare da tab'e fuska murya a daqile yace.
"Ke ba'a wonka a garin kune?."

Murya na rawa tace .
"Anayi."

"Qazan tace ta hanaki yi ?."

"Nayi ."

"Toh wanna buhun zanin naki kuma na gadone ko?."

Zuwa yanzu hawaye ya jiqa mata gaban riga cikin tsoron yadda yake mata mgnan murya na rawa tace.
"Banida wani kayan."

Mitsss yaja d'an gajeren tsaki sannan ya juya gun y'ar madaidai ciyar durowar ya bud'e cikin durowar ya tsura ido har zuwa wani lokaci sannan ya zaroh wani 3qtr enshi wanda kuma kamar skin teit ne sannan ya zaro riga mai dogon hannu rigar farace qal wondon kuma read ne mai ratsin fari-fari,
gaban ta ya dawo cikin tsuke fuska ya miqa mata,
ita kuwa hannu tasa ta karba tana mamaki ya zatayi tasa wannan kayan ,
ganin ya tsare ta da ido yasa ta shiga toilet ta zare kayan jikin ta tasa wanda ya batan sannan ta fitoh tana ta d'aga hannu tana gyara hannun rigar don ya mata tsawo har yatsun ta hanna yen suka rufe sai fama take da rigar ga wuyan rigar ma ya mata yawa wondon ne dai ta samu yayi kib da qugun ta,
yana ganin ta fito shima ya fice kai tsaye masallaci suka wuce shida Sani dan maggariba tayi.

banya sunyi harda ishah Sani ya wuce Restaurant ya samo musu abinci sannan ya dawo,
a parlon suka ci tare da d'an yin kallo har zuwa 8:15 Pm Captain Sani ya kalli ogan nashi cikin sanyi yace,
" Oga bari inje in kwana a d'akin Abdul,
tunda yanzu nan kam ba fili."

bai kulashi ba har ya fita sannan shi kuma ya miqe cikin gajiya ya d'auki ledan abinci ya nufi cikin d'akin ,
a gaban ta ya dire mata ledan sannan ya juya yaje ya rufe qofar parlour ya dawo cikin d'akin kai tsaye ya nufi.......

By
Garkuwar Fulani
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*BANDIRAWO* page 7⃣
Na
*Aysha Ali Garkuwa* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


Pure moment of life writers


*Na saudau kar da wannan shafi a gareku Salmab Fadeela Fashuna biebie deee Fadeela Lamid'o Firdaus ina al'fahari daku*


Tsayawa yayi a kanta cikin d'aure fuska ba fara'a ko kad'an ya kuma tab'e baki cikin fad'a da bada umurni yace.

"Ke kina jina ko."
Shiru tayi bata kula shiba sai kanta da ta sunkuyar tare da fidda numfashin tsoro da far gaba,
shurun nata ya

Please Login or Register in order to submit comment