Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mai murza yatsun ta,

Shi kuwa hannu yasa a kanta ya jawo d'an kwalinta
sai kuma yayi shiru yana kallon yadda gashin kanta ya zubo kan kafad'un ta,
ita kuwa cikin kalloshi kawai take cikin fidda numfashin da sauri-sauri ,
mik'a mata d'an kwalin yayi tare da cewa.
"Ki bar kukan ki share hawayen ki ."

Shiru tayi bata kulashi ba sai k'ollan dake zuba,
mik'a mata ya kuma yi tare da lumshe idon nashi dan baccin yake ji,
jin shiru bata karb'a ba yasashi mik'a hannushi tare da kamo nata cikin sanyi ya jawo ta kan pillow ya kontar da ita yana mai kallon fuskar ta,
ita kuwa sai janye jikin ta takeyi tana k'ok'arin tashi,
fuska ya tab'e tare da cewa .
"Kinitsu fa."
kukan ta kuma saki tare da cewa.
"Ni zan fita parlour zanje gun Abba."

Tsaki ya ja tare da jawo ta jikinshi ya sata cikin k'irjin shi ya matseta da hannu d'aya murya can k'asa yace.
"Bacci zamuyi dan jiya kema bakiyi bacci sosai ba."

Baki ta tsuke tare da cewa.
"Hamma Haiydar ni bana jin bacci."

Matseta ya kuma yi a jikin shi kamar maiyin rad'a yace.
"Lumshe idon ki,
ki rink'a fidda numfashin ki a hankali kisa kanki cikin k'irjin na,. sabida karki ga haske kiyi haka yanzu baccin zai zo kinji ko."

Bata kulashi ba,
shi kuwa bai kuma mata magana ba sai lumshe idon da yayi tare da jawo blanket ya rufe su.

Shiru kawai tayi tana mai shak'ar k'amshin turaren jikinshi,
cikin shak'ar k'amshin ne ta fara jin kasala jikin ta na sakewa a hankali ta lumshe idon lokaci d'aya bacci safe mai dad'in nan ya kwasheta,
shi kuwa yana jin tayi shiru a jikin shi yasa ya bud'e ido yana kallon ta fuskar ta ya tsurawa ido tare da tsanan ta buga war zuciyar shi,
a lokacin daya tuno yaran da ya had'u dasu a dai-dai k'ofar shiga part d'in Alhaji Ibrahim,
shiru yayi tare da karewa fuskar Meenalin kallo,
cikin sauri ya kuma rumtse idonshi yana tuno kamannin fuskar Rayhana,
a fili yace.
"Wannan wanne irin kama ne ?."
Tsaki yaja tare da cewa.
"Kamar tayi yawa duk da ana cewa ko wanne d'an adam yana da masu kamannin sa har 7,
gaskiya duk da haka kamar tayi yawa."

Yatsarsa yasa yana shafa gashin girarta cikin mamaki ko yanayin gashin girarsu iri d'aya hatta d'an bakin su iri d'aya,
shiru yayi tuno sautin muryar Rayhana tabbas sautin muryar ta sak irin sautin muryar da bazai mantaba duk da tsawon shekaru da yayi baiji muryar a zahiri ba tabbas sautin muryar ta irin ta Ammi ce tunda a koda yaushe yana mafarkin Ammin shi kuma yana jin muryar ta.

Ido ya kuma rumtsewa tuno fuskar Ramadan sai kuma yasa tafin hannushi yana shafa fuskar shi yana mai mamaki a sanyaye ya lumshe ido tare da sauk'e ajiyan zuciya a haka cikin tunanin bacci mai dad'i ya d'ebeshi suna ruggume da juna cikin shak'ar k'amshin juna...


Ita kuwa Mama da gari ya waye bayan sun gama lalalatan su ita da bokan ta ya had'a mata tuggun da take buk'a ya kuma shaida mata aiki ya kammalu daga yau Aliyu ya zamo Aliya bashi ba mace sai dai gani da ido zai zama dashi da logoni basu da babbanci ,
cikin rud'u shaidan da bacewar imani da mancewa Allah na nan ta yarda da maganar bokan nata ta kamo hanyar ta cikin happy ta dawo gida ita da Abdul suka rink'a had'a zalumci yayin da Nafeesat da ya Amir suke binsu da Addu'a da fatan shirya..


Rayuwa ta juya komai ya fara canzawa yayin da kwanaki sunja har ya koma makonni sun ja ,
Ramadan da Rayhana kuwa suna ta k'ok'arin had'uwa da d'an uwansu so sai dai basa son kowa ya sani kuma su a Kansu sun k'asa gano ina yake,
ganin bazai Ganeba gashi wata d'aya zasuyi su koma hakan yasa Ramadan ya yanke shawaran dole su nemi Captain Sani Wanda suke kira Hamma Sani sunyi shawara dashi a kan haka suka yanke shawaran k'iran shi yazo gida sunyi maganar ...


Shi kuwa General Aliyu a hankali rayuwa ta juya mai inda zuwa yanzu ya fara fahimtar akwai abin dake bibiyarsa zuwa yanzu kullum dare Aliyu kwana yake cikin azabben zazzab'i da sanyi da ciwon ciki da kasala mai tarin yawa da tsinke war zuciya da zaran anyi sallan insha wannan yanayin yake zuwa mishi shine bazai samu sa'idaba sai iskar asuba ta fara kad'a daga nan kuma kafin gari ya waye sai ya nemi ciwon ya rasa kab jikin sa sai yayi garau sai dai kuma dole sai yayita yin baccin rana haka yasa gaba d'aya yanzu bai fiye kwana a Jaji ba kuma yamma nayi zai dawo gida haka zasu kwana da Meenarl d'inshi cikin wahala shi baida lafiya ita kuwa tsoron yadda yake wahala da ruggume ta da yakeyi tsam yana rawan jiki shike hanata bacci a hankali ta fara jin tausayi yinshi na ratsata ta yadda take kwana mishi sannu da zubda k'ollah.....

Yau jumma tun da yamma General ya dawo gida a parlour ya zauna jiki a mace dan yaune ya gano wata matsalar dake jikin shi hakan ya sashi cikin rud'ani,
yana kwancen Meenarl ta shigo parlour kai tsaye gaban shi taje ta zauna kan carpet ido suka tsurawa juna cikin kula da tausayi tace.
"Hamma Haiydar yaushe ka dawo?."

Shiru yayi tare da kallon yadda take ma shi maga cikin tausayi yawa da kulawa,
abinda bai tab'a samuba,
ba wanda yasan halin da yake rayuwa a cikin in dare yayi sai ita shiyasa gaba d'aya yanzu tausayawa kanshi yake.

K'ara matsoshi tayi cikin sanyin murya tace.
"Hamma baka da lafiya ko?."

Ido kawai ya tsura mata,
ita kuwa ido tab da k'ollah tasa hannu kan wuyan shi cikin rawan murya tace.
"Hamma yamma tayi ko? har zazzab'i ya fara zuwa?."
Shiru baiyi magana ba sai kanshi yasa ya matse hannun ta a kan wuyan nashi .

Ita kuwa cikin zubda k'ollah tace.
"Hamma Aliyu kamin magana mana."

Ido ya tsura mata cikin tsuke fuska yace.
"Ina kika je? bana hanani fita ba?."

Kai ta lok'k'osa cikin sanyi tace.
"Kayi hak'uri Hamma naje gun Anty Aysha ne."

Shiru yayi sannan ya mik'e ya zauna tare da zaro hankicif d'inshi ya mik'a mata yace.
"Share hawaye ki ni lafiya ta lau,
bari ma inje masallaci,
ki tafasa min tea kafin in dawo."

Toh tace tare da binshi da ido har ya fice sannan itama ta shiga bedroom din nasu tayi sallan..


9:23 pm General ne zaune kan carpet d'in dake gaban gadon nasu sai rawan sanyi yake tare da damk'e cikin shi yana mai jujjuya kai,
ita kuwa durk'ushi take a gabanshi tana zubda k'ollah cikin rawan murya tana.
"Isa Hamma Haiydar sannu ."

Kai ya gyad'a mata cikin dauriya yace .
"Meenarl jeki rufe k'ofar parlour ki kashe wutan da fanka kizo ki konta."

"Toh" tace tare da mik'ewa taje ta rufe k'ofar tare da kashe komai sannan ta shigo ta sameshi ya had'a kanshi da jikin gadon gaba d'aya jikin shi sai rawa yake,
da sauri taje kusa dashi cikin tausayawa tace.
"Hamma Haiydar ni kam bari inje in gayawa Abba inya so sai mu tafi asibiti."

Kai ya juya mata cikin furzar da numfashin yace.
"A a Meenarl barshi kinga yayi bacci kar mu tayarmai da hankali kinga yana da hawan jini."

Hannu tasa ta share hawayen ta tare da jawo blanket zata rufe mishi jiki ganin yadda yake karkarwa,
hannun ta ya rik'e cikin cije lips enshi yace.
"Bari Meenarl ai yau da sauk'i ki hau kan gadon ki kwanta nima yanzu zan hau in kwonta."

Baki ta bud'e a hankali tace.
" toh tashi ka hau."

Murmushi k'arfin hali yayi tare da yunk'ura zai mik'e rik'e da hanna yenta dai-dai lokacin da sunkuyo d'in wani irin.....



*Kuyi hak'uri da wannan sisters ina kuma k'ara Baku hak'uri rashin ganin nolen d'inna da zakuyi gobe zuwa jibi hakan zaifarune sakamakon zanyi tafiya Adamawa Yola 2 Gombe ina Neman Addu'arku fatan Allah ya kaini lafiya ya maidoni lafiya*



By
*Garkuwar Fulani*
πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*BANDIRAWO* page 3⃣6⃣to3⃣7⃣
Na

*Aysha Ali Garkuwa*

πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡



*Moh Allah seini b'uri sembe suno innu adama Jo*




ta zagoyo k'ugunshi tare da turo kanta kan cin yarshi cikin bacci baccin tace.

"Hamma Haiydar Wlh ruwan da sanyi ."

Shiru yayi yana kallon fuskar ta yadda ta d'an tsuke baki sai faman lumshe ido ta keyi,
tana ta shigewa jikin shi,
kai ya jinjina cikin lumshe ido ya sauk'e ajiyar zuciya cikin kula ya shafa fuskar ta kamar maiyin rad'a yace.

"Hmmm ai na kunna ketil d'in toilet d'in yanzu ruwan yayi zafi dai-dai wonkan,
kije kiyi sai kizo kiyi sallah inyaso sai ki koma baccin."

Kai ta kuma turawa jikin shi tare da cewa.
"Toh ni Hamma yau wonkan dole ne?."

Fuska ya tsuke cikin had'e girar sama data k'asa yace.
" Eh dole ne sai kinyi ya ina miki magana kina min taurin kai tunda kinsan baki son sanyi meyasa kikayi ta shigewa jikina d'an fitina ."

Janye jikin ta tayi daga gareshi dan ganin yadda ya tsuke fuska komawa tayi gefe ta zauna ta kifa kanta cikin guiwowin ta.

Mik'e wa yayi tare da juya mata baya cikin muryar fad'a yace.
"Ki tashi kije kiyi wonkan tsarki sannan kizo kiyi sallah,
ai ke ba jahila bace kin sani sarai kin kuwa san niyar wonka da zakiyi."

Cikin tsoron shi ta mik'e ta nufi k'ofar toilet d'in tana tafiya tana juyowa tana kallon shi har ta shige ciki,
sannan shikuma ya juya ya tafi masallaci...



A hankali rayuwa tayi ta juyawa yana yin zaman General da Meenarl ya fara canzawa wani yana suke rayuwa a ciki kullum dare dukan kwana cikin gida d'aya d'aki d'aya gado d'aya blanket d'aya,
sam yanzu General bai yarda da kwana a Jaji dan yana yin ciwon dake damun shi duk daren duniya,
Meenarl kuwa har cikin ranta take tausayawa Hamma Aliyu nata halin da yake ciki,
yayinda shiko General rayuwar sa ta cika da rud'u tunda zuwa yanzu ya gano tabbas bashi da lafiya sannan ya fahimci halin da Meenarl ke shiga kullun in sun kasannce tare ,
yana ganin sha'awarta a fili,
a zahiri shi da kanshi yasan matuk'ar yaci gaba da zama da ita a haka yana cutar da ita tunda ita da lafiyar ta shiko yasan baida lafiya,
abinda yasan da ba haka yake ba tunanin abin na damun shi so amman wazai gayawa tunda shi dai baida wani d'an uwa ko aboki ko amini ko shak'ik'i nashi ba uwa bare ta lura da halin da yake ciki Abban shi ba wani shak'uwa ko sabo a tsaka ninsu tunda basu rayuwa wuri d'aya ba,
shiyasa haka yake kunshe da matsalar sa .

Ita kuwa Meenarl Hamma Aliyu yana bata tausayi sosai tana bashi kula iya kula....


Yau Asabar tunda su General da captain Sani suka shigo cikin Kaduna Captain Sani ya nufi gidan Alhaji Ibrahim d'an yana son ya kwana aca dan Ramadan da Rayhana sunce da safe zasu zo su sameshi a gidan Uncle Ibrahim d'in zasuyi maganar da tasa suka ki rashin.


Tun da Aliyu ya shigo ya samu su Abba da Daddy a babban parlour tare da ya Amir sai Abdul wanda kusan tare suka shigo dan yanzu Abdul ya worke garau tuni yana saka wondonshi yana kuma zuwa ko ina,
gefen Abba yaje ya zauna cikin yana yinshi na rashin wolwolah ya gaida Abban sannan ya juya gun Daddy ya gaida shi,
ya Amir kuma ya bashi hannu suka gaisa,
shi kuwa Abdul sai kallon Aliyun yake cikin yin murmushi mugun ta dan yasan gadar zaren da suka saka mishi ya kuma yi niyar gobe zaiyi abinda zai k'ona zuciyar General wanda harya mutu bazai mance ba d'an ya gama shirin sa sab,
shi kuwa Aliyu wanda yana zaune ne kawai a wurin amman ya fara jin kasalar tana rufeshi ga zazzab'i da tsinke war zuciyar da yake kwana dasu kullum.

9:00 pm. dai-dai ya mik'e cikin sanyi ya kalli Abba baki a mace yace.
"Sai da safe ."
Ido Abban ya tsura mai a ranshi yana jin tausayin d'an nashi tabbas ya fahimci yana cikin matsala toh amman yak'i fad'a ga maraicin rashin uwa da yake gani a k'wayar idon d'an nashi,
hakan tasa gaba d'aya shima yanzu baida nitsuwa baida burin d'aya wuce ya nemowa d'an nashi farin cikin sa,
kallon Abban yayi cikin kula yace .
"Abba kana buk'atan wani abune?."
Kai ya juya cikin sanyi yace.
"A a ba komai Haiydar ka kula da kanka."

"Toh" yace tare da juyawa ya tafi,
yana shiga a parlour nasu ya zauna kan 3 str yana jin yadda gab'b'an jikin shi ke macewa suna sakewa igiyar takalmin k'afafun shi yake son kuncewa da bel d'in k'ugunshi ammam ya kasa duk jikin shi ya mace hatta hannushi ya kasa d'agawa,
yana ji yana ganin abinda yafi k'arfi ya zamo ya kasa aika tawa,
cikin ranshi ya rink'a jin tausayin kanshi da kanshi ya kasa komai sai zuciyar shi dake suya bak'in ciki kamar ya fasa mishi zuciya,
a yaune tunanin Ammin shi ya tsanan ta a ranshi lips enshi ya cije tare da tunanin ya tabbata da Ammin shi nan dole zata lura da cewa baida lafiya ya tabbata da zata riga kowa gane cewa yana cikin matsala ya tabbata ko jikokine dashi da Ammin shi zata tallabeshi ,
baki na rawa ya rink'a magana a hankali yana.
"Ammi na banda lafiya ni kaina bansan meke damuna ba Ammi na na rasa lafiya ta bansan meke faruwa da niba Amina ina jin tsoron kar na mutu ban ganki ba Ammi na jikina duk yana shirin mutuwa."

Sai kuma ya kife kanshi cikin cije lips enshi tare da furta
"Bismillahi"
a hakan ya samu ya mik'e yana bin gini ya shiga cikin bedroom d'in.

Gaban mirror yaje ya tsaya cikin dafe jikin mirror gaba d'aya ya kasa janye hanna yenshi,
Ita kuwa Meenarl tunda tayi sallan ishah ta konta kan sallayar anan bacci ya d'auke ta,
cikin baccin can k'asa-k'asa taji muryar Hamma Haiydar d'in.

Yana tsaye dafe da mirror jikinshi sai b'ari yake murya a cushe yake cewa.

"Meenarl! Meenarl! Meenarl!."

Kiranta yake cikin tausawa kanshi da ita dan yasan duk duniya ba mai tai mako shi sai ita gashi ita kuwa yau ta rigashi bacci shiyasa yake kiranta.

Ita kuwa cikin baccin ta bud'e ido ganin yana tsaye gaba d'aya jikin shi na b'ari yasa ta mik'e cikin tsoro da tausayawa taje gabanshi cikin rud'u tace.
"Hamma Haiydar jinki ko ?."

Shiru baiyi magana ba sai idon ya zuba mata cikin cije lips enshi murya na rawa yace.
"Meenarl Ammi na Meenarl Ammi na ."

Hannushi ta rik'e fuskar cike da k'ollah murya na rawa tace.
"Hamma Ali Ina Ammin me kake son tayi maka?."

Kai ya rink'a murzawa cikin azaba da tarin damuwa yace.
"Meenarl ban san inda Ammi na take ba Meenarl ina buk'atar taima kon mahaifiya ta."

Kuka ta rink'a yi cikin kuka tace.
" Hamma Haiydar gaya min me kake son in yima."

Kai ya rink'a juyawa cikin cushewar numfashi yace.
"Meenarl yau ko bel na na kasa kun cewa ko takalmi na na gaza kuncewa kullum ciwo nan gaba yake yi."

Gabanshi ta kuma matsowa cikin kuka ta durk'usa k'asa sannan tasa hannun ta fara since igiyoyin but din k'afafun nashi ,
tana kun cewa ta kuma d'ago tasa hannu kan k'ugunshi ta fara k'ok'arin b'alle bel d'in tana mai sheshek'an kuka tana kuncewa ta jawo wonddon yinifon d'in nashi tayi k'asa dashi,
mik'ewa ta kuma yi cikin kuka ta rink'a b'alle boturan rigar tasa saida ta b'alle su duka sannan ta kalleshi ido cike da k'ollah tace.
"Hamma Haiydar d'aga k'afafun ka."

Kai ya juya tare da cewa.
"Meenarl "
sai kuma yayi shiru tare da zamewa k'asa kan carpet ya zauna cikin dafe kanshi,
ita kuwa tana ganin haka ta zauna tare da jawo k'afafun shi ta d'aura kan cinyarta sannan ta zare mishi ta kalmi tare da wonddon ta kuma Sa hannun ta zare rigar jikin nashi ta barshi daga shi sai gajeren wonddon da bes,
sannan ta matso gefen shi ta zauna cikin kuka tace.
"Hamma zanje in kira Abba yazo mu tafi asibiti."

Shiru yayi cikin zafin rayuwa sannan ya konto ta kanta kan cin yarta ya d'aura kanshi tare da zagaye k'ugunta da hanna yenshi cikin zafin jikin ya rink'a juya kai yana.
"Ammi na ,
Meenarl Ammi ta tafi ta barni tun bansan kaina ba na resa soyeyyar uwa bani da d'an uwa bare y'ar uwa bani da mai tuna halin da nike ciki."

Magana yake cikin zubda k'ollah tamkar yaro abinda bata tab'a gani ba,
hakan yasa cikin kuka itama tasa hannu ta cikin suman kanshi tare da shafa fuskar sa tana share mai k'ollah dake bin fuskar sa cikin rawan murya tace.

"Hamma Haiydar kana da masoya kuma ni nasan halin da kake ciki ina kuma yi maka Addu'a."

Haka suka kwana cikin damuwa da k'unci sai asubar fari duk ciwon da yake ji ya bari sai sauran kasalan da yake ji cikin k'arfin hali ya kalli Meenal dake zaune tana tallabe da kanshi ,
matsota yayi murya can k'asa yace.
"Meenarl tashi muje kan gado ki konta kiyi ko baccin awa d'aya ne kafin lokacin sallah yayi."

Hannu ta mik'a mai tare da mik'ewa
shi kuwa kamo ta yayi suka nufi kan gadon,
suna konciya ya lumshe idon shi cikin sanyi yaji Meenarl ta matsoshi kamar yadda suka saba kullum da Asuba sai mak'aleshi tai ta shigewa jikin shi dan ya rigada yanzu ta gama sabawa da salon da yake mata,
Shiru yayi cikin tsura mata ido yace.
"Minalin Hamma Haiydar ya akayi ne?."
baki ta d'an tura cikin sanyi tace.
"Hamma nima ban sani ba."

Jawota jikin shi yayi cikin bak'in ciki da tunanin yana tauye mata hak'k'in ta tunda ita dai da lafiyar ta,
ido ya kuma bud'e wa jin yadda ta ruggumo shi tare da manna k'irjin ta a nashi.

Iskan bakinshi ya hura mata a fuskar ta cikin sauk'e ajiyar zuciya yasa yatsa yana zagaye lips d'in ta tare da tsura mata ido,
ita kuwa mik'a tayi cikin yin luu da idanun ta ,
hannu tasa ta kamo yatsar tashi a hankali ta d'aura yatsar kan harshen ta sannan ta rink'a tsotsar yatsar tana lumshe ido,
shi kam Aliyu zuciyar sa ce ke bugawa dan tsabar bak'in ciki yana jin tsoron randa zata gaza hakura yana kuma fargaban randa zata gane shi baida lafiya.

Cikin tunanin yasa hannu cikin rigarta a hankali yake tura hannun har zuwa kan k'irjin ta ,
kallon ta yayi jin tana sauk'e wani irin ajiyan zuciya,
murya a kasalan ce yace.
"Minali na ko in bari ne?."

Ido ta lumshe cikin kunya tace.
"Hamma k'aik'ayin fa nike ji."

Murmushi yayi tare da cewa.
"Toh me kike son in miki?."

Ido ta rufe cikin tsananin kunya ta zaro hannushi sannan tasa hannu ta zuge zib d'in rigar sai ga k'irjin ta a fili ,
ido ya lumshe da ya gane nufin ta kawai sai ya manna bakin shi kan b...
d'in ta ya fara yi mata salon d'aya saba cikin sanyi,
ita kuma sai rumtse ido tayi da sa hannu cikin sumar kanshi..

A haka ya sama mata nitsuwa har saida ta rink'a zubda k'ollah ,
Sannan ya barta ya tafi masallaci ,
ita kuwa yana fita itama taje tayi wonka sannan tazo tayi sallah.


7 dai-dai ya shigo ya sameta zaune gaban mirror tana shafa mai tana ganin shi ta rufe idanun ta cikin sauri sannan tace.
"Ina kwana Hamma ya jikin ?."
Tab'e baki yayi tare da cewa.
"Ni lafiya ta lau."
Shiru tayi dan dama tasan haka zaice.

Shi kuwa wonka yayi cikin sauri-sauri ya shirya tsab sannan ya fito parlour ya sameta ita da Abba suna zaune ,
bayan ya gaida Abban ne ya mik'e tare da cewa.
"Abba bari in wuce Jaji akwai sojojin da zan sallamah zasu tafi borno."

"Toh Haiydar Yau ina Sanin naka?."

"Yana gidan su Abba nima ba dadewa zan yi ba yanzu zan dawo shiyasa ba sai na tafi da shiba."

"Toh" kawai Abban yace,
ita kuwa Meenal mik'ewa tayi rik'e da cup d'in tea da sauri tabi bayan shi cikin kula tace.
"Hamma Haiydar ga tea kasha kafin ka tafi."
Bai kulata ba bai kuma juyo ba,
da sauri tasha gaban shi tare da mik'a mishi cup din tace.
"Ayyah Hamma Haiydar kasha tea nasan inka tafi baza ka nemi abinda zaka Ciba."
Kai ya juya zaiyi magana ,
tayi maza ta manna mai cup d'in a bakin shi.
Ido kawai ya tsura mata ganin yadda ta dago k'afafunta sama tare da d'aga hannu kafin ta samu cup d'in ya isa bakin shi,
a haka ta rink'a bashi yana kurba har ya sha rebin tea d'in,
sannan yasa hannu ya janye hannun ta cikin kallon juna ya manna mata kiss a goshi sannan ya fice da sauri yana jin dad'in yadda take kula dashi..

Yana fita Nafeesat ta shigo Abba ta gaida sannan ta kalli Meenal cikin murmushi tace.
"Meenal yau ne zamuje kitson ko?."

Shiru tayi tana tunanin yau dinma bata gayawa Hamma Aliyu ba kuma ya hanata fita kuma gsky tana son yin kitson,
Jin tayi shirun ne Abba yace.
"Zaku je mama Nafeesatu ai barin kai a tsefen ba dad'i."

Cikin jin dad'i tanaga ta samu madafa ko Hamman ta zaiyi fada zata ce Abba ne ya barta,
tana happy tace.
"Eh zamuje ."

Haka kuwa akayi 11:00 na safe suka gama shirin su tsab suna fitowa suka samu Abdul yana shirin fita a motar shi,
ganin su ya sashi yin murmushi mugunta cikin mugun nufi yayi...



*Sisters wata k'il gob'e bazaku samu ba dan gobe zan koma fatan Allah ya maida in lafiya*


By
*Garkuwar Fulani*
πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*BANDIRAWO* pg 3⃣8⃣to4⃣0⃣
Na

*Aysha Ali Garkuwa*

πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡




*Damoni na damoni! gidd'o mo fina laramo! gaid'o mo fina sukoyo ladde Allah yama d'um! Kinkid'i kakkad'a! ki d'oidi yalete! yoriki tenete! ki b'ibb'e sammete! b'enduki yamete! Mo Allah hoinani wala ko sad'in ta d'um!*




Gunsu kai ya kauda gefe cikin muryar munafurci yace.

"Nafeesat fita zaku yine?."

Kai ta d'an d'ago ta kalleshi tare da gyad'e mai kai alamar .
"Ehh", sannan tace .
"Gidan kitso zamu je."
Ita kuwa Meenarl kai ta kawar gefe cikin rashin son ganin Abdul d'in dan har ga Allah tsoro yake bata.

Kanshi a sunkuye yana k'okarin kunna kid'i cikin motar sa tare da zuge glass d'in motar sama tare da cewa.
"Ku shigo in sauk'e ku tunda nima fitan zanyi."

Shiru Meenarl tayi tare da tuno Hamma Aliyu yama hanata fitan fa kuma sannan ta fita fitanma kuma da Abdul,
itako Nafeesat cikin kula ta kalli Meenarl d'in a hankali ta kamo hannunta cikin yak'ini da karfin zuciya dan ita tanaga har abadan Abdul bazai kuma gigin tab'a Meenarl d'in ba dan ya horu horo iya horo,
ita kam Meenarl kai ta rink'a juyawa cikin sanyi tace.
"Nafeesat ni bazan shiga motar shiba."

kallon ta Nafeesat tayi cikin jinjina kai tace.
"Wallahi Meenarl har abadan Abdul zai kasance mai tsoron ya kuma cutar dake kuma gani gaki insha Allah bazai miki komai ba,
kuma wallahi Abdul yanzu ya canza kinga yana jin tsoron Hamma Aliyu."

Ita dai tsayuwa tayi cikin d'an farga ba,
tana ji Nafeesat ta kamo hannuta suka shiga motar,
suna shiga suka rufe,
shiru tayi cikin jin bugawar k'irji da tsananin firgici da tsoro gaba d'aya zuciyar ta sai duka yake tara-tara.

Shi kuwa Abdul lumshe ido yayi tare da sauk'e ajiyar zuciya yana murmushin mugunta da kanne ido a ranshi yake fad'in.
"Meenarl kinyi gaggancin shiga motata kinyi wautar saurin mance waye Abdul,
Nafeesat kinyi wauta da kike tunanin Abdul zai gani ya k'yale."

A haka ya figi motar a 100 suka fito tare da daukar hanyar tudun wada,
inda ita Nafeesat bata damu ba don tanaga ai hanyar zata b'ulle dasu inda zasuje d'in,
ita ko Meenarl shiru tayi tare da maida hankalin ta kan titi don sam ita bata samu nitsuwa ba kallon titin take da kyau har ta manna fuskarta da jikin glass din ta yadda wanda yake wojema zai ga fuskarta ras,
shiko Abdul a ranshi murna yake a nufinshi zaice bari ya biya gidan abokin shi dasu daga nan zai samu ya aiki Nafeesat bakin titin ta seyo mishi katin woya kafin ta dawo kuwa hak'arsa zata cimma ruwa murmushi yayi cikin mugunta da jin dad'in yana mai yarda da kanshi.


Gudu yake kamar wanda zaiyi doguwar tafiya gudun yake ba tare daya tuna a cikin gari yake bafa.

Gudun yake har ya kamo titin dake bi ta k'ofar gidan gwamnan garin Kadunan ba tare da tuna komai ba ya saki kid'i da gudu kamar mai tashi sama,
a haka har ya isa dai-dai wurin da sojojin dake tsaron kofar gidan ba sassauci ya danno kanshi zai wuce ba tare da tuna ya taka doka ba,
Captain Garba dake kan titin bai kula da motar tasuba har saida yazo gab dashi karar yadda yake gudun ne yaja hankalin Captain Garban cikin murtuk'e fuska da tsarewa irin nasu na sojojin ya d'ago kanshi tare da sa hanccin bindigarshi yana yin k'asa

Please Login or Register in order to submit comment