Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lokacin d'aya jikin shi ya bar b'ari shiko Ramadan da Bappa suma ,
hamdalan sukayi ,
Inna kuwa sai mik'a mishi zuman tayi zallan farar Zuma wanda tana cikin sak'arta ma tace.
"Karb'i ka rink'a lasa."

Ido ya tsura mata ita da Bappa sannan yasa hannu shi kan mararshi da dazun nan yake da tauri kamar dutse sai gashi yanzu-yanzu wurin yayi normal.

Karb'a yayi yasa yatsarshi tare da laso zuman,
murmushi yayi ciki sanyi yace.
"Ramadan daga Yau kai ba Dr bane,
Bappa ne babban doctor mu kaji wallahi gaba d'aya yanzu ba abinda ke min ciwo Alhamhadullih yau naji sauk'i."

Dariya Ramadan yayi tare da cewa.
"Alhamhadullih B'iyaye na."


Kamar wasa rahanar ubangiji yawane da ita tuni General yaji shi garau,
Inna da Rayhana suka shiga cikin gida suka kawo musu abinci,
Bappa kam tasa Aliyu yayi a gaba kamar yaro sai da ya bashi abinci yaci cikin kulawa shiko General yaji dad'in abincin dan yasha man shanu,
Inna kuwa ruwan Lipton ta had'a mishi ta bashi,
gaba d'aya suna zaune a d'akin Bappan,
cikin tura baki Ramadan yace.
"Wallahi na lura yanzu Hamma Haiydar kawai kuke so ni kun wani shareni."

Dariya sukayi gaba d'ayansu shiko General Murmushi yayi cikin k'aunar d'an uwan nashi cikin murmushi ya d'an bugi kafad'an shi yana.
"Ai kai d'an gatan Ammi ne ni ba masu sona sai Bappa da Inna ."

Haka sukaci abinci suna raha.

Bayan sun nitsu ne a daren Ramadan ya kalli Bappa cikin nitsuwa ya bashi labarin abinda ya faru baki d'aya.

Sannan yaci gaba da cewa.
"Bappa meyasa lokacin da ka had'a auren Bodd'i da Hamma Haiydar ba kayi tunanin wani abu zai iya faruwa ba? Bappa baka ji tsoron Habba Aliyu ba?."



Shiru Bappa yayi tare da komawa ya zauna ya jingina jikin gini
yanata tunani a hankali yace.
" kusan tun bayan tafiyan Bodd'i kullum cikin tunani nake
Harga Allah nayi iya tunani na dazaiyi akan masu son cutar da ita dan na kareta amma babu mafita sai yadda nayin, koda ace nayiwa ALIYU kwatancan mahaifin ta dan ya kaita badole bane yazama inya kaita yakaita lafiya ba dan komi na iya faruwa kasancewar Bodd'i mace ce wacca ta amsa mace, gashi kuma ALIYU namiji kuma shed'an yana iya samishi wani abu tunda shima mutum ne babu Wanda ya wuce jarabawar ubangiji."

Ajiyan zuciya ya sauk'e tare daci gaba da cewa.

"Aura mishi ita danayi itace mafita dan koba komi ina yiwa yaron kyakkyawan zato, hakan yasa komi yazo cikin sauki, aure darajane dashi mai girma wanda insha Allah adalilin auren zata iya gamuwa da mahaifinta,
Sannan kuma ni nasan Bodd'i yarinyace mai biyayya nasan zata yiwa Aliyu biyeyyah zata kuma yi hak'uri zama dashi na kuwa san Bodd'i bata da musu ko gardama,
adalilin haka ina sakaran sake haduwa da ita cikin farin ciki da zuriyya dayyiba,
tun a lokacin kuma na lura da Aliyu yana cikin damuwa a rayuwar sa duk da bai gaya min ba amman na lura yana buk'atar mai shiga rayuwarsa dan tausaya mishi."

Shiru yayi tare da kamo hannu General yaci gaba da cewa.

"Aliyu sana din had'a ka da Bodd'i da nayi ya jazama matsaloli ,
sannan kuma yayi sana d'in had'uwar ka da mahaifiyar ka da k'annen ka,
sai rashin fahimta dake tsananin yayun mahaifiyar ku da mahaifin ku,
Ni kuwa Insha Allah gobe goben nan zamu wuce tare daku da Inna waziri zanje Insha Allah za dai-dai ta tsakanin su Ammin ku zata koma gidan Abban ku."

Shiru Inna tayi tare da cewa .
"Tabbas su Alhaji Ibrahim basu kyauta ba ai ko dan rik'e musu yarsu da kayi da a mana da zusu bar maka ita a matsayin matar ka kuma tunda shi Sani ya gaya musu Bappa ya d'aura muku Aure ko mu bamu isa da ita bane?."



Cikin sanyi Bappa yace.
"Batun auren su kuwa wannan hurumin bana kowa bane tunda aurene akayi a kan Aure kuma wannan matsalar a kawai maslahar ta cikin addinin mu na musulunci dan addininmi bai regemu da duhun komai ba."


Cikin sanyi General yace.

"Bappa me yasa Baku gayawa iyayen Bodd'i aura min ita kumayi ba?."

Kai ya jinji na cikin nadaman abin yace.
"Wannan shine kuskuren da nayi dana yarda nabi shawarar mahaifiyar Bodd'i ita kuwa tace a fad'i hakan ne dan tana ga kar mijin ta yaga banyiwa yarshi adalci ba ko na aurar da ita ga wanda ban sani ba,
amman ni nasan nayi kuskure ka gafar ceni."

Kai ya juya tare da cewa.
"Bappa baka yimin komai ba,
kuma Insha Allah gobe iwar haka muna jihar Kaduna."


Haka suka kwana cikin tsantsar farin ciki, da k'aunar juna.

washe gari da sassafe suka kama hanyar Kaduna,
tafiya kuwa tayi kyau General ke jan motar sai Ramadan a gefen shi Bappa da Inna da Rayhana kuwa suna baya.

11:00 pm dai-dai General ya kutsa hancin motarsu cikin Jaji yayinda gaba d'aya sun cika da gajiya,
bayan sun shiga Ramadan ya jido musu ledodin kayan cima da General ya lodo musu,
ya kawo musu Inna da Rayhana d'aki d'aya suka shiga suna shiga ko ruwan basu shaba suka konta idanun cike da bacci jiki dauke da gajiya.

Ramadan ma tuni ya b'ingire yana bacci Bappa kuwa saida yayi nafilfilinshi sannan ya konta.

Shi kuwa General wonka yaje yayi sannan yazo ya konta tare da k'ura'ani a hannu shi karatu ya rink'a yi cikin sanyin saiti,
jin bacci na fin k'arfinshi yasa yarufe karatun tare ajiye kura'anin,
sannan ya koma ya konta,
cikin hamdala ya matse mararshi tare da cewa.
"Alhamhadullih yau gani lafiya ta lau ba ciwo har na manta na tab'a ciwon ma."

Ido ya rumtse da k'arfi tare da matse cinyoyin sa cikin ranshi yace.
"Allah ka yaye min wannan raunin shawa'an da ke damuna dan tabbas yaji sauk'i amman kuzarin shi da saura.

Haka yayi ta Addu'a.
Washe gari bayan sunyi wonka Rayhana tayi musu girke-girke sukaci suka sha sannan suka nufi cikin kaduna.

Abba kuwa shima da Daddy bayan sun gaba shawarwarin su ,
Captain Sani ya dauke su ya nufi gidan Alhaji Ibrahim dasu.

Shima General kai tsaye gidan Alhaji Ibrahim d'in ya nufa dasu dan a cewarsa lokacin da yaje ya jajubo maganar auren Abban shi bai sanina haka kuwa zai warware abin ba tare da sanin Abba .

Motarsu General nayin Parking sai ga Motarsu.....



By
*Garkuwar Fulani*
πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*BANDIRAWO* page

4⃣9⃣to5⃣0⃣

*Na*
*Aysha Ali Garkuwa*

πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡




*Wannan shafi d'uggu ruggum d'in shi nakine ke kad'ai Khaleesat Haiydar Allah bar zumunci da k'aunah ina al'fahari dake, MI YID'I MASIN KHALEESAT*



Dr Jabeer shima yayi parking,
Ido Aliyu ya tsurawa motar Dr Jabeer d'in cikin takaici,
Meenarl ya haggo zaune a gefen Jabeer daga dukkan alamu tare suka fita kuma yanzu sunka dawo tsaki ya jaa cikin murtuk'e fuska yayi shiru yana matse siteri,
Bappa kuwa da Inna da Rayhana shiru sukayi dan basu san me yasa shi jan tsaki ba kuma ya tsuke fuska ya k'i ya bud'e musu motar,
Shiko Ramadan shima kallon motarsu Meenarl d'in yake tare da son fitowa dan sauri yake yayiwa Meenarl albishir da zuwan su Bappa.

Ita kuwa Meenarl shiru tayi tana kallon Hamma Jabeer d'in nata da ya rik'o hannun ta yana murza yan yatsunta cikin wani salon ya k'ara juyowa gareta suna fuskar tar juna cikin sanyi yace.
"Bodd'i na ina sonki inason kasan cewa tare da ke inason farin cikin ki,
me yasa kike k'untatawa kanki akan Aliyu ai da ya damu dake yadda kika damu dashi da bazai iya korarki ba,
Bodd'i nifa d'an uwan kine na jini ki dawo da zuciyar ki gareni zan soki zan kula dake zan riritaki."


Shiru tayi fuskar ta na cike da k'ollah tace.
"Hamma Jabeer,
Ni ina tausayawa Hamma Haiydar bashi da lafiya kullum dere baya bacci kuma ba mai taimaka mishi sai ni."

Sai hawaye shar-shar a fuskarta tana juya kai.

Shiru Dr Jabeer yayi zuciyar shi cike da k'aunar ta yasa hannu ya tallabe hab'arta k'ara matsota yayi tare dasa hannun shi ya share mata k'ollah.


Shi kuwa General da k'arfi ya rumtse idanun shi cikin k'ara matse siterin yana mai juya kai.

Ganin haka yasa Ramadan dannan pin d'in bud'e motar sannan ya bud'e ya fito tare da bud'e wa su Bappa da Inna suma suka fito,
shima kainshi a sunkuye ya bud'e ya fito cikin tsuke fuska.

Suna fitowa ,
Meenarl ta wore ido cikin tsananin mamaki da farin ciki cikin sauri ta fito tare da yin gudu tana zuwa ta rugume Inna cikin kewar juna Inna ta rugumeta Bappa kam sai murmushi.

Ita kuwa Meenarl sai hawayen farin ciki,
sai ta kuma sake Innar tayi cikin gida da gudu tana.
"Ummi! Ummi ina kike ? Ummi ga Bappa na da Inna ya Ramadan ya kawo minsu."

Su kuwa bin bayan ta sukayi suna dariya a babban parlour suka tarar da mutanen gidan baki d'aya,
cikin farin ciki da k'aunar juna suka gaggaisa.

Shiru Bappa yayi ganin Aliyu bai shigo ba cikin kula ya kalli Ramadan dake gefen Ammin su yace.
"Kai Ramadan ina Aliyu ."

"Yana woje yace shi bazai shigoba tunda masu gidan basa so."

Cikin girma Bappa yace.
"Shima ai nan gidan sune."

Sai kuma ya mik'e ya fita yana zuwa kai hannun shi ya kamo yayi cikin gida dashi suna shiga parlour.

Ammi da ta zubawa k'ofar shigan ido tana ganin shi ta rink'a sauk'e ajiyar zuciya tare da tsura mishi ida wasu hawaye masu zafi suka kwaranyo mata cikin rawan murya tace.
"Haiydar."

Shi kuwa General Kanshi a sunkuye yabi Bappa dake rik'e da hannu shi ,
gaban Ammin yaje ya ajiye shi sannan ya zauna gefen shi cikin kula yace.
"Aliyu ga mahaifiyar ka gata a kusa da kai gata a gaban ka."

Shiru Aliyu yayi tare da tsurawa yatsun k'afafun ta idanu lokacin d'aya yaji wani irin karayan zuciya gaba d'aya sai yaji zuciyar shi ta raunata.

Ita kuwa Ammi hannu tasa ta jawo kanshi ta d'aura kan cinyarta yayinda kan Ramadan yake kan d'aya cinyar Rayhana kuwa ta rakub'e a jikinta,
cikin sanyi ta d'aura hannun ta kan tsakiyar kan Aliyu baki na rawa tace.
"Aliyu Haiydar ina sonka d'ana ina tunako ako wacce rana ban tab'a yin sallah na idar ba tare da nayi maka Addu'a ba Ammin ka tana sonka kaine farin ciki na
Nagode wa Allah daya kare min kai."

Shi kam General manna kanshi yayi da jikin Ammin kamar mai tsoron kar a saceta a hankali yaji hawaye masu zafi irin hawaye da yake ji a duk randa bagen mahaifiyar shi ya dame shi,
ita kam Ammi fad'ar farin cikin ta bazai yiwu ba,
General kuwa zuciyar shi cike da k'aunar mahaifiyar shi a d'aya gefen kuwa har cikin ranshi yake jin zafi da haushin yayun mahaifiyar tashi dan su suka mishi Katanga da ita tun yana k'arami suka mai dashi marayan dole.

Bappa ne ya gyara zama cikin halin girma ya kalli Barrister Lawan da Alhaji Ibrahim sannan ya kalli mahaifi yarsu a hankali yace.

"Wannan shine babban kuskuren da mutanen mu sukayi a wanna zamanin, aiki da zuciya fushi da tunzura a duk inda aka samu saki ya gifta a tsakanin ma'aurata,
mata kin forko da za d'auka shine hak'uri sai kuma a duba darajan Aure sannan a koma a duba makomar yaran dake tsakanin dan gujewa aikin dana sani,
babu wani riba cikin yin fushi dan anyi saki a reba uwa da d'an ta domin ko a shariyance yara suna gefen uwane har sai sun shekara 7 yanzu kai Lawan ribar me ka samu daka reba y'ar uwarka da d'anta kalli hawaye dake bin fuskar ta,
kalli illar rebesun da kukayi yasa Aliyu ya rayuda Bodd'i tsawon lokacin Amman baisan y'ar uwarsa bace itama bata sani ba,
kuna ne manta a can gefen bakusan tana kusa da kuba."

Shiru sukayi baki d'ayansu dan tabbas gaskiya Bappa ke gaya musu,
gaba d'aya zuk'atan su sun cika da nadama,
Barrister kuwa har cikin ranshi yake jin kunyar y'ar uwarshi.

Haka Bappa yayi ta musu nasiha da fad'a da nuna musu illar yin fushi dan an saki y'ar uwarka kace zaka rebata da yaran ta.


Gaba d'aya sun maida hankali kan Bappa shi kuwa cikin girma ya sake gyara zama tare da yin gyaran murya yace.

"Ibrahim wai ka d'aura auren Aminatu da Jabeer."

Cikin sunkuyar da kai Alhaji Ibrahim yace.
"Ehh Bappa na d'aura musu Aure ."

"Yaushe ka d'aura musu auren?."

"Bayan munje Membila lokacin da kukace an saceta toh damuka dawone da wata 1 na d'aura musu auren tunda shi Jabeer yana sonta."

Kai Bappa ya jinjina cikin kafeshi da ido yace.
"A lokacin kana da yak'inin Aminatu tana rayene? a lokacin kana da yak'inin zata dawo ne?
kasan inda take a wanna lokacin ne?.

Ajiyar zuciya Alhaji Ibrahim ya sauk'e tare da jin saurin tabbayoyin Bappa sai kai kawai yake gyad'a wa tare da cewa.
" a a,
bani da sanin wannan Bappa."

Gyaran murya Bappa ya kumayi sannan ya kallesu baki d'ayansu tare da cewa.

"Lawan ana d'aura Aure da babu ne? ana d'aura Aure da wanda ba san inda take ba?."

Cikin goge zufa Barrister yace.
"A a tabbas ba,a d'aura auren da babu matar ,
Amman nima wallahi Ibrahim bai gaya minba sai kawai cemin yayi ya d'aura musu aure."

Cikin ilimi Bappa yaci gaba da cewa.
"A cikin rashin sani kukayi aure a kan Aure! toh cikin wadan nan auraki biyun wanene ya zauna wanda akayi da fari ko na biyu?."

Dr Jabeer kam tuni tabbayoyin Bappa ke tsinke mishi hanjin cikin shi sai ido yake bi Bappa da shi,
shi kuwa Aliyu jinsu kawai yake dan ya gama yanke hukun ci a ranshi shi dai Ammin shine zai tafi da ita.


Cikin sanyi Barrister yace.
"Na farin dai tunda shi na biyun kan na farin aka daura shi ."

Murmushi Bappa yayi tare da cewa.

" toh zab'i yana gun Amina ita zata zab'i wanda take so a cikin su dan haka shariya ta bata dama,
zancen gaskiya kuma Aliyu ni na aura mishi Amina Aure bisa koyarwan addinin mu ga sadakin Amina a hannuna ko sisi ban tab'aba,
kuma ko a wancan lokacin Aliyu bashi yace yana son Amina ba nine na rok'eshi dan sirar da mutun cin ta."

Sai ya kuma juyawa gun Aliyu yace.
"Dan haka Aliyu in baka sonta ka saketa ga sadakin ka sai a maida maka,
inko kana sonta saita zab'a a cikin Ku duk wanda tace bata sonshi sai a maida mishi sadakin shi ."

Gaba d'aya su yarda da maganar Bappa dan gaskiya ce.

Barrister ne ya kalli Meenarl cikin sanyin jiki yace.
"Meenarl wa kike so a cikin su in Aliyu kike so ki fad'i shima d'an uwanki ne."

Ita kam Meenarl sai kawai ta juya kan Dr Jabeer tana kallon shi ido cikin ido fuska cike da k'ollah ta k'asa magana sai kuka an kad'a an rawa tayi magana ta k'asa sai kallon Dr da takeyi tana kuka.

Shi kuwa Aliyu ba k'ara min hatsala yayi ba ganin yadda take kallon Dr Jabeer tana kuka cikin cije lips enshi yace.
"Ni banzan rabata da d'an uwanta ba dan nasan zafi da ciwon dake cin zuciyar wanda aka raba da d'an uwanshi dan haka ni zan barwa Jabeer ita ,
dan shiyafi cancanta da ita kuma shi ya tashi cikin farin ciki dan haka niko banzan zo rana tsaka na rabashi da farin cikin da ya rayu a cikiba ,
niko dama bansan menene farin ciki ko dad'in d'an uwa ba dan haka haka ni zan bar mishi ita."

General yana maganar ne da iya gaskiyar sa dan a can cikin ransa yana jin zafin yadda Minalinshi ke kallon Jabeer tana kuka shi kuma ko inda yake bata kallah ba a d'aya gefen zuciyar sa kuma yana tuna cewa shifa har yanzu lafiyarsa nada rauni.

Shi kuwa Dr Jabeer cikin tsantsar farin ciki da jin k'aunar General d'in yace.
"Nagode d'an uwana Allah ya bar zumunci da k'aunar juna."

Ita kuwa Meenarl zuciyar ta cushewa tayi sai wani irin sautin kuka ta saki cikin tsurawa Jabeer d'in ido.

General kuwa ganin duk sunyi shiru ne ya kara b'ata mishi rai a zuciyar shi yace.
"Ai dama su ba sona suke yiba."

Bappa kuwa ido ya tsurawa General dan ya gano Aliyu yaudaran kanshi yake yi.

Bappa ya bud'e baki zaiyi magana kenan Captain Sani ya shigo parlour cikin sanyi yace.
"Daddy ga Abban su Ramadan yazo tare da d'an uwan shi."

Cikin kula Alhaji Ibrahim yace.
"Maza je ka shigo dasu kace su iso."

"Toh" Captain yace tare da juyawa ya taho da su.

Bappa kuwa haka kawai yake jin wani irin farin ciki mara adadi Inna kuwa da Ummi mahaifiyar Meenarl sai zuk'atan su ke harbawa da sauri-sauri.

Shi kuwa General Captain Sani ya watsawa harara dan ya naga shine yayi shishshigin kawo Abban shi gidan,
Ramadan kuwa sai murmushi yakeyi.


Suna shigowa parlon Captain Sani ne a gaba sai Abba dake binshi a baya.

Inna ce ta mik'e tsaye cikin tsananin mamaki da d'an rud'ewa gaba d'aya jikin ta sai rawa yake yi cikin firgici ta nuna Abban Aliyu baki na rawa tace.
" *WAZIRI* Kaine nake gani ko kamace? Bappa waziri juyo ka gani ga waziri da Usmanu."

Cikin sauri Bappa ya juya tare da sauk'e k'wayan idanun shi kan fuskokin ya ranshi da suka bace masu dere d'aya yau kimanin shekara 38 kenan."

Bappa kam ba abinda yake cewa sai.
"Alhamhadullih ala kulli halin,
Allah na godema da wannan rahawa da kayi min na godewa Allah daya bani aron rai da damar sake sa yarana a k'wayan idanuna."

Abban Aliyu da Daddyn Nafeesat kuwa,
gaba d'aya jikin su rawa yake kamar mazari kai tsaye gaban Bappa suka durk'ushe kamar yara kuka sosai sukayi cikin kewar iyayen sun.

Inna kuwa gani take kamar mafarki takeyi shi yasa ta matsosu tare da rik'e Hanna yensu tana.
"Alhamhadullih Abubakar Usman nagode wa Allah ."

Barrister Lawan ne yayi magana cikin rud'ewa yace.
"Bappa su waye wad'an nan din a gareka ? ka sansu ne?."

Aliyu ma kai ya jinjina cikin zubawa Bappa ido.


Ajiyan zuciya Bappa ya sauk'e tare da nuna Abban Aliyu da Daddyn Nafeesat yace.
"Lawan wadan nan da kake gani yaranane na jinina nine mahaifinmu su
Inna waziri itace uwarsu mahaifiyar su wannan mai kama da Aliyun shine d'anta Wazirin da kukeji ina kiranta dashi ,
wadan nan sune yayun Aysha mahaifiyar Bodd'i ,
yayunta uwa d'aya uba d'aya ,
sun bar rigarmu ne a wani deren munwayi gari babusu ba labarin su munyi nema har muka kareya daga bisani muka fauwalawa Allah tare da saka ran watarana zamu gana,
lokacin da suka bar gida Aysha tana k'arama ,
ashe Aliyu jika nane ban sanina."


Wannan abin al'ajibin ya saka farin ciki a zuk'atan su baki d'ayansu. "

Ummi da Ammi kam sai murmushi sukayi..

Sun zauna sun tattauna sosai sannan daga bisani .
Bappa yace .
"Toh a maida auren Abban Aliyu da Ammi."

Barrister Lawan da Alhaji Ibrahim ne suka kalli juna cikin son nemawa k'anwarsu enci sukace.
"Bappa bamuk'i maganar kaba amman a bari sai gobe in munyi shawara."

Kai Aliyu ya dago tare da zuba musu ido zuciyar shi cike da tsanar su,
ya za'ayi ana son maida auren Ammin shi sukuma suna dojewa.

Cikin hatsala ya mik'e su Aliyun a goshi yace.
"Ni na bar muku y'arku,
Inma nine bakwaso a cikin zuciyar ku,
sannan yadda kuke ganin zaku hana Ammi na komawa gidan Abba na toh,
Shima yana iya d'auke mahaifiyar Meenarl tunda k'anwar sace,
sannan kuma zamu dauke Ramadan da Rayhana tunda yaran shine ,
ni kuwa a karan kaina ni Aliyu zan dauke Ammi na tunda mahaifiya tace,
Ku Kurik'e zuciyar ku muma mu rik'e tamu zuciyar."

Yana kaiwa nan ya fice yana cewa,
"kuyi tunani da kyau."

Yana fita ya figi motarsa yayi gida.

Barrister Lawan kuwa shiru yayi yana tunanin a zahiri fa Aliyu zai iya tsanarsu ya dauki gaba dasu ,
tuno hakan yasa shi yarda a take a wurin aka d'aura auren Ammi da Abba ,
Barrister yayi haka ne dan Samar da fahimta,
sannan batun Meenarl kuwa,
Sukace tunda shida bak'in shi yace ya hakura shike nan.


A ranar Abban Aliyu ya dauki matarshi da iyayenshi da su Ramadan ya koma dasu cikin gidan shi.

Gidan su Aliyu ya cika da farin ciki da wolwola sai dai sam Aliyu baya sake wa da Ammin shi.

Meenarl kuwa tunda General ya fita take ta kuka DR Jabeer yayi iya yinshi tak'i sai cewa take.
"Hamma Haiydar bashi da lafiya wallahi inajin tausayin shi."

Captain Sani ne ya kalli d'an uwanshi cikin sanyi yace.
"Hamma Jabeer wallahi tausayin shine jigon so da zaran tausayin ya zauna toh akwai so maitarin yawa,
inka yarda ka meyarwa Hamma Haiydar matarsa shi take tausayawa ni nasan irin zaman da su kayi."

Washe gari da dare
Wannan magana ta Captain ita tasa Dr Jabeer karaya ganin tun jiya take kuka tak'i ko cin abinci haka ta wuni har zuwa yanzu na d'arfe 9 na dare gaba d'aya ta tsanan ta damuwan ,
hakan yasa Dr ya yankewa kanshi hukunci yanzu zai kaita gun Aliyu shi zai hakura da ita zai bar mishi ita,
ko dan hadisin nan da ya horemu da mu sowa yan uwanmu abin da zamu sowa kanmu.

Haka yasa ya kalleta cikin sanyi yace.
"Muje en kaiki."

Haka kuwa ta biyoshi suka taho gidan su General d'in.


Shi kuwa General a dai-dai lokacin ya sallami Ammin shi ya fito da nufin wucewa cikin Jaji.

A bak'in get ya tsaya ganin motar Dr Jabeer na shigowa,
fitowa yayi ganin Dr Jabeer d'in ya fito rik'e da hannun Meenarl kai tsaye gaban General d'in ya tsaya cikin sanyi ya kamo hannun Meenarl ya had'a dana Aliyu cikin karfin guiwa da zuciya yace.
"D'an uwana ga matar ka ni na bar maka ita har a bada dan na gane cewa a kanka Meenarl tasan so."

Shiru General yayi cikin mutuwan jiki ya k'asa ko magana,
Shi kuwa Dr sai murmushi yayi tare da cewa.
"Fatana zaka bani auren Rayhana."
Shima Aliyu sai murmushi yayi,
tare da cewa "uhummm."

Daga nan shikam Dr Jabeer ya shige cikin gida gun goggonshi Ammi,

Shi kuwa General hannun Meenarl yajawo tare da cewa.
"Minalin Hamma Haiydar zomu tafi Jaji a can zamu kwana."

Sai kuma ya jawota jikin shi tare manna...



By
*Garkuwar Fulani*
πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*BANDIRAWO* page

5⃣3⃣to5⃣4⃣

*Na*
*Aysha Ali Garkuwa*

πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡




*Yebon goni ya zama dole hak'ik'a rigar mutunci kan sanya a zatawa mai sanyashi mutunci kinkai a yebi ki, mu matan arewa muna yebawa da halin ki da shigarki Namecy tawa AISHA LAWAN UMAR jarumar ma aikaci mai mutunci tauraruwar AREWA 24 Garkuwar Fulani ke mik'a sak'on jinjina a gareki🀝😍😘*



Sunku yowa kanta yayi pillow d'in da ta matse a k'irjin ta ya zare a hankali sannan ya d'an durk'usa murya can ciki yace.
"Meenarl a nan zakiyi baccin ai wuyan ki zaiyi ciwo."

Kai ta juya cikin jin dad'i baccin safiyar ga garin yayi lum alamun hadari ga iska mai dad'i ga kasan cewa cikin tsabta ceccen wuri mik'a ta d'an yi a hankali ta kai hannun ta kan,
fuskar shi sajen shi ta shafa a hankali,
Ido ya lumshe tare da sauk'e ajiyan zuciya shima hannun shi ya d'aura a kan goshin ta tare zubawa kirjin ido murya a raunane yace.
"Muje kan gado kiyi baccin anjima zan shiga cikin KD zan dauko miki kayan ki."

Ido a lumshe cikin muryar bacci tace.
"Uhmmm Hamma."

Matsota ya kuma yi a hankali yace.
"Na'am Minali ."

Sai ta kuma lumshe ido tace.
"Bacci nake ji Hamma jikina ya mutu bazan iya tashi ba."

Murmushi yayi tare dasa hannu ya gyara mata wuyan rigar ta dake zamewa sannan ya mik'e a hankali hannu yasa ya tallabo ta tare da manata a jikin shi ,
bedroom ya wuce da ita kai tsaye kan gadon ya direta cikin kula yasa mata pillow sannan ya jawo blanket ya rufe ta ,
sai kuma ya juya tare da d'ago laptop enshi da iPhone nashi juyawa yayi gareta ya ajiye su kan y'ar karamar durowar dake gefen gadon ,
a hankali yace.
"Saura kiyi birgima ki turomin laptop na ki karasi min shi haka jiyama da dare kika rad'a min su da k'asa."

Ita dai baccin ta fara tare da tura mishi baya.

Shi kuwa kai tsaye parlour ya koma ya sassake labulayen sannan ya rufe windows d'in sai kuma ya shige kitchen cikin sauk'i ya had'a musu breakfast mai sauk'i sannan ya kimtsa komai,
tea ya d'an had'a sannan ya dawo parlour tare da kunna TV yana kallin CNN,
tea d'in yake sha yana d'an sauri d'an

Please Login or Register in order to submit comment