Join Our WhatsApp Group

NAGA TA KAINA 2 and 3 Complete Hausa Novel Document by NAGA TA KAINA 2 and 3


NAGA TA KAINA 2 and 3

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 36150



NAGA TA KAINA 2 and 3

Reading Time: 3 Hours

Added On: 29, Sep 2023

Author: Hafsat Sodangi ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 177.89 kb

File Type: txt

Views: 1705+

Download: 718+

Last download: 9 hours ago

Description/Story: 
Na farfado ne daga dogon suman da na yi na jini Jike sharkaf da ruwa da yawun addu'o'in da akc tofa min ina Kwancc jikin Antina wacce tuni idanuwanrta suka yi luhu-luhu saboda haka na kalli baba babba wanda har lokacin bai gaji da karanto addu'o'i yana tofa min ba na yi karfin hali da kyar na iya bude bakina saboda nauyin da ya yi min ga sarawar da kaina yake yi na ce baba cikın sauri ya amsa na'am Badi'atu na ce da gaske ne Muktar ya yi haisarin jirgin sama ko kuwa mafarki nake yi? Ya gyada kai tarc da cewa E Bad 'atu abinda suka sanar damu kenan kuma a halin da ake ciki tuni har an iso da gawarwarkin mutanne biyar daga cikin bakwai dake cikin jirgin na dora hannu biyu na dafe kaina saboda jin shi nake tamkar zai arwatsc na shiga halin kidima da dimauta na rasa abinda zan yi in ji saukin bakin cikin dana tsınci kaina a yau sai kawai na kurma ihu ina cewa wayyo ni Badi'atu wayyo na ga ta kaina wayyo na rasa Muktar na shiga kuka haka kuwa ma tsananı 1arc da tsima zuciya da bada tausayı Antuna da Hajiya Mariya suma tayani kukan suka yi ina kuka ina sambatu me na yiwa Muktar? Me na yi mishi da zai bari su kasheshi bayan ya yi min alkawarin in har na yi mishi alkawarin kame kaina in tsare mnishi mutuncina shi kuwa zai yi duk yanda zai yi ya ga ya dawo gida mun ci gaba da rayuwarmu mu biyu don ya ga ya yiwa suaran maza kwalele a kaina Joda ta dora tafin hannunta a bakina ta rufe da karfi cikin kuka take ce min yi shiru Badi'atu daina yi magana don kar ki yi sabo, ni kam a kidime nake na kasa mallakar komai nawa shi kan shi baba hankalınshi ya kai matuka wajen tashi sai salati yake yi yana karawa Gali da Nai11u suka shigo sun dawo daga inda suka je duba gawarwakin da aka kawo su dukansu biyun tamkar an zare musu laka baba ya bisu da kallo cikin matsanancin soro da racana jikinshi har bari yake yi cikin Rarfin hali ya tambayesu kun ganshi a cikinsu ko? Gali ya ce a'a ba ya cikinsu, baba ya sake tambaya kun duba da kyau kuwa? Ya ce e, baya ciukikafafuwansu muka duba muna nan cikin wani hali da ba zan iya kwantawa ba wajen karie biyar na yamma aka sake aikowa wai ga wata gawar an kawo su Gali da Nafi'u suka ruga suka tafi gani muka shiga jira, jiran da na rinka ganin tamkar na walanni ne saboda kidima jimawa can suka dawo suna zama Nafi'u ya fashe da kuka wiwi gaba daya muka tsare sai Gali ya shiga yi mishi fada me ye haka Nafi'u zaka 1sorata mutane baba ba shi bane Major Balogun ne na zaro ido lare da dora hannu biyu kaina na kurma ihu ina birgima gaba daya dakin kowa kuka yake yi baba yana salati hawaye suna zuba a idonshiGali ne kawai yake durkushc a gaban baba yake aikin báshi hakuri yana cewa har yanzu bamu tabbatar Muktar ya rasu ba, baba ya ce gaba Gali an kawo mutum shida cikin bakwai kuma daga cikin wadanda aka kawo din nan har da Balogun abokin aikinshi na kut da kut, ai kuma shi kenan "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un Allah ban yi kukan rasa dana don butulci a gareka ba sai don zuciyata bata da karfi kan abinda ya shafeshi na yi burin Muktar ya yi min rakiya ta karshe zuwa kushewata ashe ba haka aka shiryo ba Allah mun gode maka da ka bamu shi a lokacin da bamu sani ba ke ni'imtanmu da rayuwarshi ka karbeshi a lokacin da ka yi niyya tsarki ya tabbata a garcka ya Ubangiji wadannan su ne jein kalaman da ke fitowa daga bakin baba ko baka san Muktar ba ganin baba kawai zai.iya sanya dan adam zubar da hawaye kiran sallar isha'i da aka yi shi ya dawo damu cikin nutsuwa kowa ya nufi wurin sallah tsawon dare ran nan Nafi'u da Gali suma officc din G.0.C. suan kokarin wai a taimakesu a sanyasu cikin sojojin da za a sake turawa Libcria saboda an samu labarin har lokacin ba a san inda Muktar yake ba yana da ra ko ya mutu ba a sani ba, wajen hudu na asuba su Nafi'u suka dawo dukanmu kuwa babu wanda ya runtsa muna hallare a lalon Muktar mun yi zugun kowa da abinda zuciyarshi ke raya mish Gali ya cewa Baba bayan sun zauna mun yi sa a baba an amince da tatiyar mutum daya a cikinmu kuma dama akwai karin sojoji mtasu taiiya gobe su yi canjin masu dawowa har da Brigedier Kabir a masu tafiya shi nc ma ya yi mana kokari aka yarda da tafiyar mutum dayan baba ya ce haka matarshi ta gaya mana dazu da zata koma gida cewar in banda tafiyar tashi da anan ta kwana to yanzu ya ya waye mai tafiyar? Gali ya ce ni nc baba na bayar da sunana baba ya zuba mishi ido da baka bar.....cikin sauri Gali ya katseshi a'a baba ni ne nafi kowa cancantar in bi Muktar do haka ni ne zan tafi ya mike ya shiga dakin da yake sauka idan ya zo gidan jimawa kadan ya fito cikin shirin tafiyar kananan kayane a jikin bai rike da komai a hannunshi ya zo ya durkusa a gaban baba ya ce zan bi bayan Muktar baba in har yana raye da izinin Allah zamu dawo tare ka yi hakuri bisa abinda ya samemu cikin sauri baba ya dafa kafadarshi ya ce Allah ya yi maka albarka Gali Allah ya tsareka ya dawo da kai lafiya da haka Gali ya fita ya bar gidan daidai karfe biyar na asubahi abin mamaki gari yana wayewa sai kawai ga abokan Muktar suna ta isowa daga wurare daban-daban har daga Benin Legos da Sakkwato wurare masu nisa amma wai har sunyi mafi yawanci kuwa sukan isone tare da matansu nan da nan gida ya zama babu masaka tsinke wannan yazo wannan ya tafi kwana biyu da faruwar al'amarin ran nan cikin dare muna daki na a kwance duk da dai ba barci muka yi ba misalin daya da rabi na dare Nali'u ya zo ya yi magana kusa da ko far dakina Anti kar ku ji mun fita a mota ku damu zamu kai baba asibitine cikin sauri ni da Anti muka fito muna rige-rigen shiga falon Muktar, mutumin da muke makwabtaka dashi wanda suke matukar zama lafiya da Muktar Major Amadu yana rike da baba yayin da Uzairu yake rike da wata.tasa jini yana zuba ta hancinshi tamkar mai habo sai dai yanda jinin.yake gudu abin ya fi karfin ace mishi habo, ni da Anti zubewa a kasa muka yi muna ta aikin kuka a haka suka fita da baba wanda ya zama tamkar wanda ya dade yana jinya. Suka tafi suka bar mu muka zauna anan ni da Anti muka yi kuka har muka gode Allah Uzairu ya shigo muka bishi da kallo na.neman bayani sai ya ce ni fa dama basu tafi dani ba ina nan a waj ina tsayc Uzairu ya wuce zai shiga dakin baki na sashin Muktar yana cewa Anti hakuri fa kawai zamu yi don kuwa babban al'amarn ya samu zuriyar mu sai dai kawai mu yi ta rokon Allah sauki.
Har wajen tara na safe kafin Nafi'u da Major Amadu suka dawo muka tambayeshi jikin nashi? Sai Nafi'u ya ce mana da sauki amma baba karami ya zo ya tafi dashi Zaria Anti ta ce dama kun gaya musu ne? Naft'u ya ce e sai da na yi mishi waya na gaya mishi nai da yake ciki da asibitin da muke shirin kai shi sannan na yi muku sallama kuma tun shida da rabi ya iso garin nan shi ne ya ce a sallameshi su tafi gida kawai zai fi samun nutsuwa tafiyar baba babba ya sanya zuwan babanlungu don wai ba za a bar gidan babu wani babba ba shi ne wakilin baba babba saboda yanda mutane ke ta zuwa daga wurare daban-daban zuwan baba al'amura suka sanya daga zaman karbar jaje ya koma karbar gaisuwa wai bai kamata a biye min a ki yiwa Muktar abinda ya kamata ba wai ashe su dama a Zaria zaman karbar gaisuwa suke yi tuni na ji na gundura da zuwan nashi muka samu rashin fahimtar juna ni da Antina don so take in yarda takaba nake yi ana gobe Muktar zai cika kwana bakwai da yin hatsari da safe Antina wai tana min bayani tana so in amince da shirin su baba na yi mishi sadakar bakwai.
Na ce ba zai yiwu ba nan gidana ne tunda gidan mujina ne na ce bana son gorin ana yi mishi sadakar bakwai anan aje Zaria inda ak a yi mishi sadakar uku a yi mishi na bakwai din Anti ta zuba min ido cikin bacin rai ta ce rashin kunya zaki kawo mana tana shirin fara yi min lada na yi maza na jawo waya na buga lambobin baba babba na ji maganarshi cikin kuka na fara mishi bayani ina gaya mishi baba da Antina da babanlungu basa mu'amalla dani b1sa kyautatawa, a hankali ya tambayeni me suke miki? Na shiga yi mishi bayaní saida na gama sai na ji ya ce daina kuka ki ji abinda zan gaya miki na sassauta kukan da nake yi sai na ji an ce ki kyalesu su yi abinda suka ga ya yi musu daidai yin hakan ba zai hanashi dawowa ba in har yana raye in kuwa baya raye kinga babu mamaki abinda kike kokarin hanawar ya amfaneshi a halin da Alhaji yake ciki a yanzu bana so ke ko wanı ku yi mishi maganar da ta shafi yaron nan don kuwa bai da lafiya tun safe yau bana zaton Albaji ya san wanda yake tsaye a kanshi cikin sanyin jiki na maida wayar na ajiye sai a lokacin na fahimci da baba karami nake magana na dago ido na kalli Antina tausayınta ya kamani na matsa kusa da ita na kwanta a jikinta ki yi hakuri Anti abinda kawai na iya fada mata kenan na soma kuka muka rungume juna ni da ita muka yi kuka har muka gaji muka yi shiru tunda mu biyu ne a dakın ma kwancea jikınta na.ce mata kenan na soma kuka muka rungume juna ni da ita muka yi kuka har muka gaji muka yi shıru tunda mu biyune a dakin ina kwancea jikinta na ce mata Antı kije gida kije ki smau baba babba ki bashi hakuri a yanzu babu wani wanda zai iya kwantar mishi da hankali in bake bace ta cc to ke fa Badi'atu? Na ce bar ni kawai Anti ki je wajenshi ni da na soma son Muktar a kwanan nan ma na ga musiba kari abinda ya sameshi ballc baba da tun ranar da Muktar ya zo duniya yake son abinshi na shiga wani sabon kukan, Anti ta amsa sallamar da aka yi da ita ta tashi ta fita na bita da kallo katon cikin da take tarawa nake kallo tare da tunanin Ubangiji ya kiyaycta daga fadawa halin da nake cikin tunda ga halin da baba yake ciki yanzu ma kenan ran da aka zo mishi da gawar Muktar ko me zai faru oho? Tunani mai nisa na yi sai kuma na ga to ai ita Antina tata da sauki ko yau aka ce babu ran mijinta dan dakc cikinta na bakwai nc bakin cikinta da sauki baba ya bar baya ni kuwa fa? Su kansu su baba inda nikc tarc da cikin da Anti ke dashi da abin ya fi musu sauki 6acin rai don sau biyu suna sawa Anti tana tambayata wai ko ina da ciki? In cc a'a in na yi wani tunanin sai in ga wata kila ni ce
na hana Muktar barin kwanshi a duniya da na bashi hadin kai kila da yanzu tsohon cikine dani shike nan sai masoyanshi su yi ta zuba idon ganin isowar dan shi zuwa cikin wannan duniyar wacce bata da tabbas, Anti ta dawo tabbas, Anti ta dawo tana kai kawonta a dakin na ce Anti dazu ina kokarin ajiye wayar nan na ji kamar baba karami yana cc min innarsu Wasıla tana kan hanyar zuwa ko zaki shirya ne in sun zo sai kawai ku koma tare? Ta ce mun to bayan sallar Azahar ina zaune gaban inna tana min nasiha ni kam cikin zuciyata magana nake yi ina cewa yau ne zuwanta gidan Muktar na farko sai dai kuma bata zo a dadin rai ba ta gama yi mun nasiha ni kuma na yi mata bayanin a binda ake ciki na matsa min da ake yi wai in an yi bakwai in koma Zaria na gaya mata abinda Muktar ya gaya min cewar duk abinda ya faru bai yarda in je ko ina ba in hakura har sai ya dawo, ta ce to zan yi magana akan hakan tunda ga umarnin da mijinki ya baki da yamma suka tafi bayan ta ce in an yi sadakar bakwai dinni a bar ni in zauna a dakina tafiyar Antina sai na shiga wani hali na karin tsanani don kuma Antina mai sona ne mai tausayına mai tattalina a yanzu ta bami tare da Joda wacce take so ta ga na bi ka'idojin yin takaba ana ta fahimtar muna cikin wannan zaman da ita sai ga baba Sabuwa mahaifiyarsu Gali ta zo da niyyar yi mun kwanaki wai babansu Galin ne ya turota da ya ji Komawar Anti gida ya ce bai kamata a barni daga ni sai Joda da masu aiki ba, ita ce ta ceceni wurin Joda ta ce in yarinyar nan nunda bata son kira mata takabar nana kyaleta kawai babu wani abinda take yi na sabawa shari'a ita ba fita take yi ba, ba surutu ba, kowane lokaci tana kudundune in ba bakine suka zo ba, kowae iokaci a azumin nafila da salloli sanda da jan kafa ahankali da ake cewa mai takaba ta rinka yi wannan camfine babu shi a Musulunci Joda ta ce to ai shi kenanan daga nan kuwa ta fita harkata sai mu'amalar arziki, kullum na Kai azumi baba Sabuwa zata shirya min kayan buda baki in na ki ci sai tace to zaki yi bakin ciki da abinda Ubangyi ya dora miki nc? Kin cin abinci shi kuma ame yake? Wannan abinda ya samemu ba wai Ubangiji yana kinmu bane jarrabawane ya kuma jarrabi manyan bayin Allah ki duba ki ga tarihin shugabanmu Annabi Ayuba ta...


Read / Download NAGA TA KAINA 2 and 3

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

1 Comments On NAGA TA KAINA 2 and 3
avatar
aisha-5-5-1

7 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album