Join Our WhatsApp Group

A DALILIN GATA Complete Hausa Novel Document by A DALILIN GATA


A DALILIN GATA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 45327



A DALILIN GATA

Reading Time: 3 Hours

Added On: 03, Apr 2024

Author: Unknown ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 228.44 kb

File Type: txt

Views: 112+

Download: 91+

Last download: 3 hours ago

Description/Story: 

A DALILIN GATA


Cikin shirin shi na alfarma ya fito falon ya durk'usa har k'asa yana gaida mahaifiyar shi. Kafad'ar shi ta rik'o ta mik'ar dashi ya zauna gab da ita. "Sai ina yanzu son?". "Mum zanje company ne saboda muna da meeting da za muyi da wasu bak'i ne". "Sai ka shiga ku gaisa da Dad d'in ka duk da ina tunanin kamar barci yake yi". "In hakan ne bara kawai in wuce don nasan Dad sai mu wuce 15mnt muna gaisawa, ga shi sauri nake yi". "Kenan kasan halin abinka nan 6angaren, amma d'ayan 6angaren duk yanda nake lurar da kai ba ka gane wa". Da saurin shi ya mik'e cikin murmushi ya doshi hanyar fita "inna dawo ma yi maganar". "Kullum hakan kake ce wa, fatana d'aya Allah yaganar daku baki d'aya". Yana gab da fita ya ji muryar ta tana furta "Brother ni ma ba za'a tsaya mu gaisa ba kenan"?. Cikin saurin ta ta k'araso gab dashi, hugging d'in shi ta yi "Mrng Brother". "Mrng Little Sister, inna dawo za muyi magana". Da sauri ya fice saboda agogon hannun shi daya duba ya ga saura minti biyar, a k'a idar shi bai son African time yayi ko ayi mai. Sai da ya hau kan titin ya k'ara gudu sosai saboda saurin da yake yi. K'eeeeeee kake ji sanadiyyar mugun birkin da yaja wanda saura k'iris ya kad'e mutumen. Cikin isa da k'asaita da kuma 6acin rai kwance a saman fuskar shi ya fito daga motar. Mari biyu k'warara ya yiwa dattijuwar fuskar mutumen wanda baki sake ya bishi da kallo. Hannun shi na dama ya saka ya cire glass d'in shi no respect, yasa d'ayan hannun ya fitar da handkerchief a gaban rigar shi ya goge fuskar shi. Cikin azama ya koma cikin motar ya tada ta, ganin ce wa zai iya bi saman kan shi yawuce yasa cikin sauri yaja jikin shi gefen titi da mamaki fal a ran shi. "Ohhh! duniya ho yanzu wannan yaron zai fito ya faffallamin mari hankalin shi kwance kuma yana k'ok'arin takani ya wuce, duniya ce ta ishi kowa riga da wando".

**

Yau kam tana ganin sun makara ga yanda suke fitowa mazaunin su na masu bara gefen wata ma'aikata. Bayan sun iso gurin ne ta gayar da wa'anda ta tarar sannan suka ne mi guri suka zauna. "Har ga Allah ba na son wannan zaman barar da muke yi, kawai abin ne ya riga yafi k'arfi na, don in mun daina bansan miye mafita a garemu ba". Matar kusa da ita ne ta ta6o ta sanadiyyar wani da ya zo yana raba masu d'ari-d'ari wanda har ya zo kanta bata sani ba nan ta kar6a ta yi godiya. 12:00pm suka fara watsewa da kad'an-kad'an inda ita ma Zajla ta rik'a sandar mahaifin ta suka doshi hanyar gida. Asaman hanyar ne suka had'u da yaran da ke tallar zogale da 6ula had'e da k'uli mai magi da yaji. "Baba ko mu siyi zogale da 6ula?". "Nawa ne muka sa mu yau hala?". Kud'in ta fitar ta irga taga 350 ne, nan take gaya mai ko nawa ne. "Siya mana 6ula na 100, zogale da k'uli na 50". Hakan ta tsayar da yaran ta siya suka wuce gida. Da shigar su gidan ne ta yi masu kwad'o suka ci. Bayan sun gama ne ta ebi ruwa ta je ta yi wanka ta yi shirin islamiya. Wasu kod'add'un uniform kalar blue ta saka sannan ta yiwa Baban ta jagora ta fito dashi k'ofar gida cikin inwar icen mangoro gurin su Malam Inuwa. "Y'ar Baba za'a je makarantar kenan?". Ta bashi amsa ta re da durk'usa wa ta gaida su. "Sai ki biya ki kira Salmat in ta shirya ku wuce". Gidan Malam inuwa ta dosa a k'ofar gida suka ci karo da Salmat, hakan suka sa kai sai makarantar su.
.
Suna shiga islamiyar suka tarar da mutane na alwala sanadiyyar kiraye-kirayen sallar azahar da ake yi ko ina, nan su ma suka yo alwala suka bi jam'i akayi sallah. Bayan sun k'are ne suka wuce ajin su na d'aukar hadda, hakan suka biya da d'ai d'aya inda Ustaz Lukman ke sauraren su had'e da gyara ga duk wanda ya yi kuskure. Da hakan suka k'are har la'asar ta yi suka fito akayi sallah. A k'a idar makarantar duk ranar larba za'a za 6i d'alibai uku cikin Maza uku cikin Mata domin gabatarda abubuwan da ake koya masu a cikin class. Hakan ta kasance yau ga d'aliban da aka za6a sun fito sun gabatar da abubuwan gwanin sha'awa ga ma su saurare. K'arfe shida na yamma aka tashi kowa ya ka ma hanyar zuwa gida. Asaman hanyar ne Salmat da Zajla suke tattaunawa. "Gaskiya Salmat yau sai gaba na ke fad'uwa na zata Ustaz Lukman zai sanya ni a cikin masu karatun satin nan". "Tabbb! Ai kima shirya kinsan satin sama dole za ki shigo a cikin wa'anda za su yi". "Ni fa abinda naso su bar mu muji da karatun haddar mu tunda lokacin musabak'a na k'aratowa".
.
"Lallai ma Zajla kin kai, kawai kije kiyi ta bitar haddar ki sannan ki zauna da shirin fitowa larbar sama karatu gaban ko wa". "Muguwa kawai tunda kin ga kin yi yau hankalin ki ya kwanta ai zaki rik'a kayar min da gaba", tana maganar had'e da kai mata dundu a bayan ta. "Gaskiya kar ki tayar da hankalin ki abin baida wata fargaba kawai dakin fito dakewa za kiyi, kuma kar ki rik'a kallon mutane ki nok'e kan ki kawai". "Shikenan Allah yakai muna rai yasa fargaba ta fice min kamin ranar". "Ameen", ta amsa a gajarce. Da hakan har suka k'araso gida, a tare suka shige gidan su Salmat d'in saboda wannan k'a idar ta ce in sun da wo daga islamiya gidan su Salmat take zama har sai Baban ta sun k'are hira sannan ta fito su shiga gida. ** Cikin 6acin rai ya shiga d'akin meeting d'in wanda sanadiyyar hakan kowa ya sha jinin jikin sa. Hakan akayi meeting d'in rayuwar sa 6ace wanda mataimakin shi ne Imran ya jagoranci komai har aka k'are. Bayan bak'in sun wuce ne wani cikin ma'aikatan ke ba da shawara kan ce wa me zai hana ayi musaya da wa'ancan bak'in a basu fata suko su bada ire-iren takalma, jakunkuna da sauran dangin kayan da ake sarrafawa da fata d'in?. Ya cigaba da ce wa "a tunani na hakan zai fi akan abada fatar su bada kud'i ko ya kuke gani?". Ya k'arashe maganar had'e da kallon mutane cikin nu na bajin ta kan shawarar da ya bayar. Kallon da mutane suka bishi da shi ne na alamar ba kada hankali, wasu kuma na tausayawa gare shi ya sa ya sha jinin jikin shi ya yi tsit. Ko wa ya yi zugum domin jiran me zai biyo bayan maganar da ya furta, saboda duk yanda aka zauna meeting ba bu mahaluk'in da ya isa yace tak ba tare da ya bashi dama ba, barrantana yau da ya shigo rai 6ace wanda ya hana yayi magana har akayi meeting d'in aka k'are. "Duk da ce wa kai bak'o ne a wannan ma'aikatar bazai hana hukunci na yahau kanka ba". Cikin damuwa Imran ya tari numfashin shi had'e da bashi hak'uri amma ina ya gama furta "na sallame ka daga yau". Hakan ya ta shi tamkar guguwa yabar gurin cikin mintunan da basu wuce uku ba. Durk'ushe ya yi gaban mataimakin A.K.A kuma babban aminin shi yana mai bada hak'uri had'e da furta "In har kuka sallame ni bansan ina zan dosa ba, da wannan aikin nake kula da mahaifiya ta da sauran k'anne na marayu". "Sai dai kayi hak'uri aikin gama ya gama duk nan ba wanda ya isa ya janye wannan hukuncin". "An samu matsala ne tun farko ba'a gaya ma tsarin shi ba shiyasa, ko ni nan da nake mataimakin shi kuma babban aminin shi indai a office ne ban isa yayi magana inyi ba har sai ya bani dama". Hakan sauran ma'aikatan suka rik'a bashi hak'uri had'e da fatan alkhairi saboda bakin alk'alami ya bushe, don shine mutum na bakwai da hakan ta kasance dashi tun lokacin da mahaifin shi ya yi ritaya ya bashi kula da company d'in, da hakan kowa ya Kama gaban shi. Mutum biyu ne suke tattaunawa akan matsalolin da ke faruwa a ma'aikatar. "Gaskiya wannan ma'aikatar ba ta nesa da rushewa, kaduba kaga yanda yaron nan ke shuka rashin mutunci son ranshi", cewar tsamurarren. "Tabb to ai abin gado ne haka mahaifinshi yake tsula tsiya lokacin da yana manager, don ni na rasa gane tsakanin d'an da uban wa yafi rashin mutunci", a cewar bak'in mutumen kakkaura. "To Allah yayi masu magani, kuma yaganar dasu". "Ameen". .
.
Hakan ya fad'o gidan ko sallama babu sanadiyyar wani huci da yake yi shi ala dole an 6ata mai rai fuska tur6une tamkar namijin zaki. Da saurin shi ya ta shi ya taryo shi yana bubbuga bayan shi, sanadiyyar ya k'i jinin jure damuwar d'an shi komi k'ank'antar ta. "Wa ya ta6a uba ga Dad kuma d'a ga Dad?, bazan juri ganin ka cikin 6acin rai ba komai k'ank'antar shi". Ruwa ya tsiyaya a cup ya d'ora mashi a baki ya kauda kai yana huci, d'ayan gefen ya mayar da cup d'in sannan ya sha kad'an ya kauda kai tamkar wani jinjiri. "Gayamin Babana meke faruwa, kuma wa ya 6ata ma rai?".
.
Mum baki ta sake tana kallon sarautar ubangiji, abu gwanin haushi. Cikin yanga tamkar wata mace ya kora mai abinda ke faruwa. "Yo banda abinka Son miye laifin wanda ya baka shawara akan cigaban ka?, kuma wai har za ka iya ta da hannu ka fallawa dattijon mutane mari", Mum ce ke wannan maganar cikin 6acin rai da fad'a-fad'a. "To shi dattijon titin uban sa ne da zai zo yana tafiyar yanga akai?", cewar Dad. "Wallahi dai ku bi duniya a sannu daga kai har yaron ka, shin kud'i hauka ne? Su talakawan su sukaso ganin Kansu a hakan? Ku da kuke hakan siya kukayi aka baku gyara?, bai dace ka rik'a nunawa yaran nan gatan da yazarce misali ba". "Mu shiga daga ciki Son, saboda ta fara wa'azin nan na ta da take zama alarammar kan ta taja kuma ta fassara", hannun shi ya rik'a suka haura sama sai bedroom d'in shi. "Mum wannan abin fa ya kusa yawa, miye laifin wanda zai kawo cigaba akan lamurran ka da Brother zai yanke wannan d'anyen hukuncin". "Rufamin baki ai duk halayyar ku iri d'aya ce ku ne masu uba mai kud'i to wallahi ina guje maku ranar nadama saboda wannan abin ba gata ne uban ku ke nuna maku ba", cikin fad'a sosai ta k'arashe maganar. "Kin san dai Mum na d'ara Brother don bazan yi abinda ya aikata yau ba". "Ku dai kuka sani, Allah ya ganarda ku daga ku har uban na ku don wallahi rayuwar ku kanta abar tausayi ce, don mutumen da baisan darajar d'an Adam ba yana cikin matsalar rayuwa, komai za kuyi ya kamata ku rik'a duba cancantar abin". "Kullum game da tarbiyar ku tufka nake yi mahaifin ku na yiman warwara, a tunanin shi wannan gata ne". "Mum tunda munsan girma da darajar ku ai ba muda laifi, dama ca akayi mu girmama iyayen mu". "Sai akace ku taka duk wanda kuke so wannan shine dai-dai a cikin aya da hadisin Dad d'in ku?, wato mu ne mutane saura dabbobi ne a gurin ku". "Mum ba kya ga newa ne, shi fa Dad raini da wulak'anci ne bai d'aukar mana ba shiyasa kike ganin tamkar wulak'anta mutane muke yi, amma ba hakan bane". "Mum fa su mutane ba ka iya masu idan kayi sake sai su ta ka ka son ransu". Mugun kallon da ta bi ta dashi ne yasa ta ja bakin ta ta yi shiru. D'aki Mum ta wuce tabar Saudat zaune a falon, ganin hakan ya sa ta bi sawun su Dad. ** Sanadiyyar yau ta kama alhamis ba islamiya ya sa tun safe tana siyo masu koko suka sha ta hau wankin su ita da Baban ta. Bayan ta gama ne tayi shara ta tsaftace gidan, yau girki ta d'ora masu sanadiyyar tsakin masarar da Mama Inno ta ba su jiya wanda zai kai kwano uku. Waje ta fita ta yi sa'a da yaran da ke tallan zogale dafaffe nan ta siyo ta had'o da d'an magi ta koma gidan. Faten tsakin masara ta yi wanda yaji zogale. Sai da ta samu guri ta saka ma su Mama Inno faten ta kai masu sannan ta dawo gidan. Ruwa ta ebo ta kaiwa Baban ta ya wanke hannun shi ita ma ta wanke sannan suka yi Bismillah suka fara ci. Suna gama wa ruwa ta fara kai mai ya yi wanka sai da ya fito ta taimaka mai ya shirya yana ta sanya mata albarka sannan ta shiga wankan ta fito. Sai bayan la'asar yau suka fita yawon su na bara, daka gansu tsaf dasu sai dai talauci dake barazana dasu. Hakan ta gayar da mutanen gurin sannan suka nemi guri suka zauna, sai gab da magrib suka wuce gida inda ya tsaya gurin su Mal Inuwa itako ta shiga gidan su Salmat. Sallah suka fara gabatarwa bayan sun k'are ne suka rik'awa juna bitar haddar su domin su k'ara daddak'awa. "Salma zo ki lek'a daga waje ki kira Sagiru yakaiwa su Baban ku abincin su". K'ur'anin ta ajiye ta fice bayan ta kira shi ne sannan ta dawo masu da nasu abinci d'akin, nan suka ci suka gama sannan suka gabatar da isha sai k'arfe tara sannan Zajla...


Read / Download A DALILIN GATA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album