Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

KASAITAR SO Complete Hausa Novel Document by KASAITAR SO


KASAITAR SO

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 36653



KASAITAR SO

Reading Time: 3 Hours

Added On: 07, Jul 2024

Author: Nana Halima ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 09030398006

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 187.56 kb

File Type: txt

Views: 1099+

Download: 1363+

Last download: 3 hours ago

Description/Story: *ƘASAITAR SO!*

©️ *Nana Haleema*

*_Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, godiya ta tabbata ga Allah subahanahu wata'ala da ya bani ikon fara wannan littafi cikin k'oshin lafiya da kwanciyar hankali, yadda na fara lafiya Allah ya bani ikon kammala shi lafiya amin, wannan labarin k'irk'irar sa akayi in yayi kama da naki ko naka ayi hak'uri rashin sani ne._*

_Ban aminta a canja min labari zuwa wata siga daban ba tare da izini ba!_




*1*

*KANO STATE*
*K'OFAR NASSARAWA.*

Kasancewar yanayin damuna da ake ciki lokaci d'aya hadari ya had'o garin yayi bak'i yayi duhu sai iska me k'arfin gaske da take kad'awa, samari ne guda hud'u d'aya yana zaune a saman mota sauran ukun kuma suna tsaye a kusa dashi, kallo d'aya zakayi musu ka gano zallar rashin tarbiyya a tare dasu duba da yanayin shigar su da irin askin da yake kansu, wad'an suke k'asa a tsaye iska ta dame su sai rufe ido suke suna kare fuska da hannayen su suka kalli wanda yake kan motar yana danna waya kamar shi iskar bata dame shi ba.

"Mai gida iska tayi yawa fa gwara mu bar wajan nan kafin ruwa ya sakko" d'aya daga cikin wanda suke tsaye ya fad'a yana kallan wanda yake kan motar, bai d'ago ya kalle shi ba balle ya saka ran zai amsa masa sai ma cigaba da danna wayar sa da yayi yana d'an murmushi alamun abinda yake yi yana bashi nishad'i.

Ganin baiyi magana ba ya saka wani a cikin su ma zai masa magana d'ayan yayi saurin zaro masa ido yana girgiza masa kai alamun kada ya ce masa komai, dole suka kama bakin su sukayi shiru badan sun so ba dan sanin halin mai gidan nasu.

Bai d'ago ba bai kuma yi magana ba sai da ya gaji dan kansa sannan ya d'ago kai yana shak'ar iskar take kad'awa, saurayi ne matashi wanda bazai gaza shekara talatin zuwa talatin da biyu a duniya ba, kyakykyawa ne wanda ake kira kyau ajin farko, fari ne irin tas d'in nan me d'auke da doguwar fuska wacce take su6ul babu d'igon kurji ko tabo a jikin ta, manyan ido gare shi masu girman gaske da d'aukar hankali masu saka mutum ya shiga taitayin sa ko baiyi niya ba gasu farare tass, yana da hanci amma ba sosai ba dan baiyi wani tsaho can ba kuma bai bud'e sosai ba, bakin sa me kyau da d'aukar hankali kwantattcen gashin sa ya zagaye bakin nasa sai ya k'ara masa kyau da kwarjini.

Gashin kansa bak'i sosai duk da an aske ta anyi masa askin da ake kira low cut ita sumar ba'a aske ta duka ba kuma ba'a bar gashin ta, sai wata star guda uku da aka zana a kan nasa ta fito tarr kasancewar sa farin mutum, bud'e idon sa masu kyau yayi ya sauke su a kan wad'an da suke tsaye a kusa dashi fuskar sa babu alamun annuri ko kad'an yace, "Bana san yawan magana kun sani ku kyale ni." ya fad'a cikin kakkausar muryar sa me firgita mutum.

Dole suka ja bakin su suka tsuke badan su so ba dan harga Allah iskar wajan ta dame su.

Sauri-sauri y'an matan suke yi duba da hadarin dake garin dole ya saka suke sauri kamar zasu tashi sama ko wacce burin ta taje gida lafiya, d'aliban makarantar yusuf mai tama sule dake unguwar k'ofar nassarawa dake garin Kano kenan da suka fito daga lecture a lokacin, y'an mata ne guda biyu da jakar goyo a bayan su suna ta sauri sunayi suna kallan sama.

Sunzo gab da wad'an nan samarin d'aya daga cikin samarin ya kalli y'an matan yace, "Kai kaga wata cika had'ad'dar gaske" ya fad'a yana kallan ta gefen haggu wacce tafi d'ayar sauri, yarinya ce dan baza ta gaza shekara sha takwas ba, sanye take da doguwar riga tayi rolling kanta da mayafin rigar, fara ce ita sosai doguwa siririyar gaske, dai-dai lokacin suka k'araso wajan motar wanda yake kallan ta yasha gaban ta yana k'are mata kallo.

Ja baya tayi sauri tana dafe k'irji dan harga Allah ta tsorata tace, "Malam lafiya?". K'are mata kallo yake tun daga sama har k'asa yana yi mata wani irin kallo yace, "Lafiyar kenan malama." Dirowar Zaid daga kan motar ya saka Gaye ya juyo yana kallan sa, k'arasowa yayi inda yarinyar take yana k'are mata kallo tun daga sama har k'asa, tab'e baki yayi ganin ta y'ar cili da ita kamar taliya shi bai san meyasa sam siririyar mace bata burge sa ba, yarinyar da ta gama tsorata da Gaye da Zaid ta zaro idon ta waje tana girgiza kai ganin Gaye yana nufo ta.

Juyawa tayi ganin wacce take son gani ta tawo da sauri ya saka ta da sauri ta k'arasa wajan ta tana fad'in, "Anty Ibteey kin ganshi yau ma suna biyo ni" ta fad'a a tsorace tana nuna mata Gaye da yake wani irin munafukin murmushi, wacce aka kira da IBTEESAM ta mayar da yarinyar bayan ta ta kalli Gaye tace, "Malam Lafiya?" Ta fad'a fuskar ta a tamke tana bin sa da wani irin banzan kallo.

D'ago kai da Zaid zaiyi suka had'a ido da Ibteey kafin ya d'auke kansa yana can tsaki, da confidence dinta ta nufo shi tana zuwa ta kalle shi tun daga sama har k'asa kamar yadda shima yayi mata, "mtsww meye dalilin ku na tare min k'anwa?" Ta tambaya tana binsu da kallo. Wizzy ya kalli Zaid tare da sauran abokan su kana suka dawo da kallan su ga Ibteey Gaye yace, "An tare ta d'in ko akwai uwar abinda zakiyi?" Ya tamabaya cikin muryar marasa d'a'a.

"Wallahi akuyar ku ta kiyayi rama ta in kuma tare sauran yara ku zauna lafiya wallahi baku isa ku tab'a min k'anwa ku zauna lafiya ba" ta fad'a tana nuna su da yatsa gabad'ayan su. Dukkanin su tsoro ya bayyana a fuskar su ganin tana nuna Zaid da yatsa har tana hararar sa tare da tsaki, "Ke! Dan uwar ki kin san su waye mu!?" Wanda yake amsa sunan Mugu ya fad'a yana zaro mata jajayen idon sa.

"Su waye ku banda y'an iska y'an shaye-shaye? Su waye ku banda y'an zaman banza masu tare yaran mutane kuna lalata musu rayuwa? Su waye ku in ba abinda na lissafa ba?". A fusace Zaid ya zaro manyan idon sa masu kama da madara yace, "Kee!! Su waye y'an iskan?." "Suku, kaine ma babban d'an iskan ma dan na lura kaine shugaban cikin su, to ba shugaba ba ko jagaba ne kai baka isa ba balle su, ku fita hanyar k'anwa ta ba yau ne na farko da waccan yake tare mata hanya ba na rantse da Allah aka sake sai na nuna muki baku da wayo, banzaye y'an iska y'an shaye-shaye, masu lalata yaran mutane" tana gama fad'ar taja wani dogon tsaki tana bin su da wani kallo taja hannun Jidda suka bar wajan.

Wizzy ne ya yunk'ura zai bita Zaid yayi saurin d'aga masa hannu alamun kar yaje, "Mai gida kana ji tana jifan ka da wad'an nan kalamai kace a kyale ta? Ka barmu da ita mu canja mata kamanni dan Allah". Dai-dai lokacin aka fara ruwan sama a lokacin Ibteey da Jidda suka shiga keke napep bayan ta juyo ta sake sakar musu harara.

Da hannu yayi musu alama da su shiga mota, ba musu suka shiga Wizzy ya ja motar suka bar wajan, _banzaye, y'an iska, y'an shaye-shaye masu lalata yaran mutane_ kalmomin da suke yiwa Zaid amsa kuwa a cikin kunnen sa kenan, tunda Allah ya kawo shi duniya ya tsani a kira shi da d'an iska baya so ba kuma ya k'auna koda wasa, ko waye kai ka kira shi da wannan suna zai ya ci mutuncin ka sabida sunan yana k'ona masa zuciya.

"A nemo min address d'in ta da sunan ta daga nan zuwa gobe, duk wannan yayi k'okarin samowa a cikin ku yana da 200 thousands" Zaid ya fad'a muryar sa a d'an shak'e sabida b'acin ran da yake ciki, dukkan su suka amsa da an gama me gida a dai-dai lokacin da suka iso titin race course, ba wanda ya sake magana a cikin su har suka k'arasa gate d'in wani gida me bala'in kyau tun daga waje, horn Wizzy me gadin ya bud'e suka shiga cikin gidan.

Tun daga wajen zaka san mallakin gidan ba k'aramin hamshakin me kud'i bane ba duba da girman gidan da kuma motocin da suke zube a parking space d'in gidan kamar wajan saida motoci, neman waje Wizzy yayi ya faka ya kashe motar Wizzy yana niyar bud'e motar Zaid yace, "Noo kuje da ita kawai we will communicated" ya fad'a yana b'alle murfin motar yana ficewa
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download KASAITAR SO

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album