Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels



A DALILIN GATA


Cikin shirin shi na alfarma ya fito falon ya durk'usa har k'asa yana gaida mahaifiyar shi. Kafad'ar shi ta rik'o ta mik'ar dashi ya zauna gab da ita. "Sai ina yanzu son?". "Mum zanje company ne saboda muna da meeting da za muyi da wasu bak'i ne". "Sai ka shiga ku gaisa da Dad d'in ka duk da ina tunanin kamar barci yake yi". "In hakan ne bara kawai in wuce don nasan Dad sai mu wuce 15mnt muna gaisawa, ga shi sauri nake yi". "Kenan kasan halin abinka nan 6angaren, amma d'ayan 6angaren duk yanda nake lurar da kai ba ka gane wa". Da saurin shi ya mik'e cikin murmushi ya doshi hanyar fita "inna dawo ma yi maganar". "Kullum hakan kake ce wa, fatana d'aya Allah yaganar daku baki d'aya". Yana gab da fita ya ji muryar ta tana furta "Brother ni ma ba za'a tsaya mu gaisa ba kenan"?. Cikin saurin ta ta k'araso gab dashi, hugging d'in shi ta yi "Mrng Brother". "Mrng Little Sister, inna dawo za muyi magana". Da sauri ya fice saboda agogon hannun shi daya duba ya ga saura minti biyar, a k'a idar shi bai son African time yayi ko ayi mai. Sai da ya hau kan titin ya k'ara gudu sosai saboda saurin da yake yi. K'eeeeeee kake ji sanadiyyar mugun birkin da yaja wanda saura k'iris ya kad'e mutumen. Cikin isa da k'asaita da kuma 6acin rai kwance a saman fuskar shi ya fito daga motar. Mari biyu k'warara ya yiwa dattijuwar fuskar mutumen wanda baki sake ya bishi da kallo. Hannun shi na dama ya saka ya cire glass d'in shi no respect, yasa d'ayan hannun ya fitar da handkerchief a gaban rigar shi ya goge fuskar shi. Cikin azama ya koma cikin motar ya tada ta, ganin ce wa zai iya bi saman kan shi yawuce yasa cikin sauri yaja jikin shi gefen titi da mamaki fal a ran shi. "Ohhh! duniya ho yanzu wannan yaron zai fito ya faffallamin mari hankalin shi kwance kuma yana k'ok'arin takani ya wuce, duniya ce ta ishi kowa riga da wando".

**

Yau kam tana ganin sun makara ga yanda suke fitowa mazaunin su na masu bara gefen wata ma'aikata. Bayan sun iso gurin ne ta gayar da wa'anda ta tarar sannan suka ne mi guri suka zauna. "Har ga Allah ba na son wannan zaman barar da muke yi, kawai abin ne ya riga yafi k'arfi na, don in mun daina bansan miye mafita a garemu ba". Matar kusa da ita ne ta ta6o ta sanadiyyar wani da ya zo yana raba masu d'ari-d'ari wanda har ya zo kanta bata sani ba nan ta kar6a ta yi godiya. 12:00pm suka fara watsewa da kad'an-kad'an inda ita ma Zajla ta rik'a sandar mahaifin ta suka doshi hanyar gida. Asaman hanyar ne suka had'u da yaran da ke tallar zogale da 6ula had'e da k'uli mai magi da yaji. "Baba ko mu siyi zogale da 6ula?". "Nawa ne muka sa mu yau hala?". Kud'in ta fitar ta irga taga 350 ne, nan take gaya mai ko nawa ne. "Siya mana 6ula na 100, zogale da k'uli na 50". Hakan ta tsayar da yaran ta siya suka wuce gida. Da shigar su gidan ne ta yi masu kwad'o suka ci. Bayan sun gama ne ta ebi ruwa ta je ta yi wanka ta yi shirin islamiya. Wasu kod'add'un uniform kalar blue ta saka sannan ta yiwa Baban ta jagora ta fito dashi k'ofar gida cikin inwar icen mangoro gurin su Malam Inuwa. "Y'ar Baba za'a je makarantar kenan?". Ta bashi amsa ta re da durk'usa wa ta gaida su. "Sai ki biya ki kira Salmat in ta shirya ku wuce". Gidan Malam inuwa ta dosa a k'ofar gida suka ci karo da Salmat, hakan suka sa kai sai makarantar su.
.
Suna shiga islamiyar suka tarar da mutane na alwala sanadiyyar kiraye-kirayen sallar azahar da ake yi ko ina, nan su ma suka yo alwala suka bi jam'i akayi sallah. Bayan sun k'are ne suka wuce ajin su na d'aukar hadda, hakan suka biya da d'ai d'aya inda Ustaz Lukman ke sauraren su had'e da gyara ga duk wanda ya yi kuskure. Da hakan suka k'are har la'asar ta yi suka fito akayi sallah. A k'a idar makarantar duk ranar larba za'a za 6i d'alibai uku cikin Maza uku cikin Mata domin gabatarda abubuwan da ake koya masu a cikin class. Hakan ta kasance yau ga d'aliban da aka za6a sun fito sun gabatar da abubuwan gwanin sha'awa ga ma su saurare. K'arfe shida na yamma aka tashi kowa ya ka ma hanyar zuwa gida. Asaman hanyar ne Salmat da Zajla suke tattaunawa. "Gaskiya Salmat yau sai gaba na ke fad'uwa na zata Ustaz Lukman zai sanya ni a cikin masu karatun satin nan". "Tabbb! Ai kima shirya kinsan satin sama dole za ki shigo a cikin wa'anda za su yi". "Ni fa abinda naso su bar mu muji da karatun haddar mu tunda lokacin musabak'a na k'aratowa".
.
"Lallai ma Zajla kin kai, kawai kije kiyi ta bitar haddar ki sannan ki zauna da shirin fitowa larbar sama karatu gaban ko wa". "Muguwa kawai tunda kin ga kin yi yau hankalin ki ya kwanta ai zaki rik'a kayar min da gaba", tana maganar had'e da kai mata dundu a bayan ta. "Gaskiya kar ki tayar da hankalin ki abin baida wata fargaba kawai dakin fito dakewa za kiyi, kuma kar ki rik'a kallon mutane ki nok'e kan ki kawai". "Shikenan Allah yakai muna rai yasa fargaba ta fice min kamin ranar". "Ameen", ta amsa a gajarce. Da hakan har suka k'araso gida, a tare suka shige gidan su Salmat d'in saboda wannan k'a idar ta ce in sun da wo daga islamiya gidan su Salmat take zama har sai Baban ta sun k'are hira sannan ta fito su shiga gida. ** Cikin 6acin rai ya shiga d'akin meeting d'in wanda sanadiyyar hakan kowa ya sha jinin jikin sa. Hakan akayi meeting d'in rayuwar sa 6ace wanda mataimakin shi ne Imran ya jagoranci komai har aka k'are. Bayan bak'in sun wuce ne wani cikin ma'aikatan ke ba da shawara kan ce wa me zai hana ayi musaya da wa'ancan bak'in a basu fata suko su bada ire-iren takalma, jakunkuna da sauran dangin kayan da ake sarrafawa da fata d'in?. Ya cigaba da ce wa "a tunani na hakan zai fi akan abada fatar su bada kud'i ko ya kuke gani?". Ya k'arashe maganar had'e da kallon mutane cikin nu na bajin ta kan shawarar da ya bayar. Kallon da mutane suka bishi da shi ne na alamar ba kada hankali, wasu kuma na tausayawa gare shi ya sa ya sha jinin jikin shi ya yi tsit. Ko wa ya yi zugum domin jiran me zai biyo bayan maganar da ya furta, saboda duk yanda aka zauna meeting ba bu mahaluk'in da ya isa yace tak ba tare da ya bashi dama ba, barrantana yau da ya shigo rai 6ace wanda ya hana yayi magana har akayi meeting d'in aka k'are. "Duk da ce wa kai bak'o ne a wannan ma'aikatar bazai hana hukunci na yahau kanka ba". Cikin damuwa Imran ya tari numfashin shi had'e da bashi hak'uri amma ina ya gama furta "na sallame ka daga yau". Hakan ya ta shi tamkar guguwa yabar gurin cikin mintunan da basu wuce uku ba. Durk'ushe ya yi gaban mataimakin A.K.A kuma babban aminin shi yana mai bada hak'uri had'e da furta "In har kuka sallame ni bansan ina zan dosa ba, da wannan aikin nake kula da mahaifiya ta da sauran k'anne na marayu". "Sai dai kayi hak'uri aikin gama ya gama duk nan ba wanda ya isa ya janye wannan hukuncin". "An samu matsala ne tun farko ba'a gaya ma tsarin shi ba shiyasa, ko ni nan da nake mataimakin shi kuma babban aminin shi indai a office ne ban isa yayi magana inyi ba har sai ya bani dama". Hakan sauran ma'aikatan suka rik'a bashi hak'uri had'e da fatan alkhairi saboda bakin alk'alami ya bushe, don shine mutum na bakwai da hakan ta kasance dashi tun lokacin da mahaifin shi ya yi ritaya ya bashi kula da company d'in, da hakan kowa ya Kama gaban shi. Mutum biyu ne suke tattaunawa akan matsalolin da ke faruwa a ma'aikatar. "Gaskiya wannan ma'aikatar ba ta nesa da rushewa, kaduba kaga yanda yaron nan ke shuka rashin mutunci son ranshi", cewar tsamurarren. "Tabb to ai abin gado ne haka mahaifinshi yake tsula tsiya lokacin da yana manager, don ni na rasa gane tsakanin d'an da uban wa yafi rashin mutunci", a cewar bak'in mutumen kakkaura. "To Allah yayi masu magani, kuma yaganar dasu". "Ameen". .
.
Hakan ya fad'o gidan ko sallama babu sanadiyyar wani huci da yake yi shi ala dole an 6ata mai rai fuska tur6une tamkar namijin zaki. Da saurin shi ya ta shi ya taryo shi yana bubbuga bayan shi, sanadiyyar ya k'i jinin jure damuwar d'an shi komi k'ank'antar ta. "Wa ya ta6a uba ga Dad kuma d'a ga Dad?, bazan juri ganin ka cikin 6acin rai ba komai k'ank'antar shi". Ruwa ya tsiyaya a cup ya d'ora mashi a baki ya kauda kai yana huci, d'ayan gefen ya mayar da cup d'in sannan ya sha kad'an ya kauda kai tamkar wani jinjiri. "Gayamin Babana meke faruwa, kuma wa ya 6ata ma rai?".
.
Mum baki ta sake tana kallon sarautar ubangiji, abu gwanin haushi. Cikin yanga tamkar wata mace ya kora mai abinda ke faruwa. "Yo banda abinka Son miye laifin wanda ya baka shawara akan cigaban ka?, kuma wai har za ka iya ta da hannu ka fallawa dattijon mutane mari", Mum ce ke wannan maganar cikin 6acin rai da fad'a-fad'a. "To shi dattijon titin uban sa ne da zai zo yana tafiyar yanga akai?", cewar Dad. "Wallahi dai ku bi duniya a sannu daga kai har yaron ka, shin kud'i hauka ne? Su talakawan su sukaso ganin Kansu a hakan? Ku da kuke hakan siya kukayi aka baku gyara?, bai dace ka rik'a nunawa yaran nan gatan da yazarce misali ba". "Mu shiga daga ciki Son, saboda ta fara wa'azin nan na ta da take zama alarammar kan ta taja kuma ta fassara", hannun shi ya rik'a suka haura sama sai bedroom d'in shi. "Mum wannan abin fa ya kusa yawa, miye laifin wanda zai kawo cigaba akan lamurran ka da Brother zai yanke wannan d'anyen hukuncin". "Rufamin baki ai duk halayyar ku iri d'aya ce ku ne masu uba mai kud'i to wallahi ina guje maku ranar nadama saboda wannan abin ba gata ne uban ku ke nuna maku ba", cikin fad'a sosai ta k'arashe maganar. "Kin san dai Mum na d'ara Brother don bazan yi abinda ya aikata yau ba". "Ku dai kuka sani, Allah ya ganarda ku daga ku har uban na ku don wallahi rayuwar ku kanta abar tausayi ce, don mutumen da baisan darajar d'an Adam ba yana cikin matsalar rayuwa, komai za kuyi ya kamata ku rik'a duba cancantar abin". "Kullum game da tarbiyar ku tufka nake yi mahaifin ku na yiman warwara, a tunanin shi wannan gata ne". "Mum tunda munsan girma da darajar ku ai ba muda laifi, dama ca akayi mu girmama iyayen mu". "Sai akace ku taka duk wanda kuke so wannan shine dai-dai a cikin aya da hadisin Dad d'in ku?, wato mu ne mutane saura dabbobi ne a gurin ku". "Mum ba kya ga newa ne, shi fa Dad raini da wulak'anci ne bai d'aukar mana ba shiyasa kike ganin tamkar wulak'anta mutane muke yi, amma ba hakan bane". "Mum fa su mutane ba ka iya masu idan kayi sake sai su ta ka ka son ransu". Mugun kallon da ta bi ta dashi ne yasa ta ja bakin ta ta yi shiru. D'aki Mum ta wuce tabar Saudat zaune a falon, ganin hakan ya sa ta bi sawun su Dad. ** Sanadiyyar yau ta kama alhamis ba islamiya ya sa tun safe tana siyo masu koko suka sha ta hau wankin su ita da Baban ta. Bayan ta gama ne tayi shara ta tsaftace gidan, yau girki ta d'ora masu sanadiyyar tsakin masarar da Mama Inno ta ba su jiya wanda zai kai kwano uku. Waje ta fita ta yi sa'a da yaran da ke tallan zogale dafaffe nan ta siyo ta had'o da d'an magi ta koma gidan. Faten tsakin masara ta yi wanda yaji zogale. Sai da ta samu guri ta saka ma su Mama Inno faten ta kai masu sannan ta dawo gidan. Ruwa ta ebo ta kaiwa Baban ta ya wanke hannun shi ita ma ta wanke sannan suka yi Bismillah suka fara ci. Suna gama wa ruwa ta fara kai mai ya yi wanka sai da ya fito ta taimaka mai ya shirya yana ta sanya mata albarka sannan ta shiga wankan ta fito. Sai bayan la'asar yau suka fita yawon su na bara, daka gansu tsaf dasu sai dai talauci dake barazana dasu. Hakan ta gayar da mutanen gurin sannan suka nemi guri suka zauna, sai gab da magrib suka wuce gida inda ya tsaya gurin su Mal Inuwa itako ta shiga gidan su Salmat. Sallah suka fara gabatarwa bayan sun k'are ne suka rik'awa juna bitar haddar su domin su k'ara daddak'awa. "Salma zo ki lek'a daga waje ki kira Sagiru yakaiwa su Baban ku abincin su". K'ur'anin ta ajiye ta fice bayan ta kira shi ne sannan ta dawo masu da nasu abinci d'akin, nan suka ci suka gama sannan suka gabatar da isha sai k'arfe tara sannan Zajla ta fita ta ja Baban ta suka wuce gida.
.
Zaune suke saman dinning table suna breakfast sai tattaunawa suke yi akan lamarin company. Sai da aka yiwa wayar shi Kira biyu ana ukun sannan ya d'aga wayar ya nufi hanyar d'akin shi, gaisawa suka fara yi sannan ya fara magana fad'a-fad'a had'e da ya mutse fuska. "Kana sane da ce wa duk inda ake taro in har akwai Mata ba na nufar gurin, saboda haka kuci gaba kawai idan kun gama ma had'u, ka isar da sak'on taya murna ta zuwa ga Salis, in ya natsu zan kira shi". Yana kai k'arshen maganar ya dak'ile wayar shi ya bita da wani kallo tamkar ta yimai wani laifi, gado ya fad'a domin ya d'an huta saboda ba mutum ne maison fita ba. ** Kwanci ta shi asarar mai rai, yau ta ka ma Larba wanda Zajla sai gaban ta ke fad'uwa sanadiyyar tunanin da wuya Ustaz Lukman bai fitar da ita cikin masu karatun k'arshen sati ba. Kamar kullum yau ma hakan ce ta kasance, bayan gabatar da sallahr azahar suka shiga class domin bitar haddar su saboda k'aratowar lokacin musabak'ar su. Bayan an gama sallar la'asar ne aka fitar da mimbari da kujeru domin zama tsakiyar makarantar a gabatar da ire-iren abubuwan da ake koya masu. Mutum uku cikin maza suka gabatar da yadda ake taimama da kuma sallar gawa, sai matan biyu da suka gabatar da koyar da alwala a aikace. Zajla ce za ta gabatar da bayanin wankan tsalki da kuma addu'o'i.
.
Bayan ta yi basmala ta gabatar da sunan ta da Zajla Abubakar Zubair sannan ta fara da ce wa'. "Shi dai wankan tsalki ya kasu zuwa kashi-kashi, akwai wankan janaba, akwai wankan haila, akwai wankan d'aukewar jinin bik'i (jego) da sauran su. "Kamar yanda kuka sani su dai wad'annan abubuwan wanka iri d'aya ake yi masu sai dai niyyar su ce data ban-ban ta". "Da farko za'a so mutum ya sa mu ruwan shi tsaftatacce, wa'anda kalar su bata canja ba, d'an-d'anon su bai canja". "Anan abinda ake nufi da kala ko d'an-d'ano shine kar mutum ya d'ebi ruwan Lipton ko ruwan wankin shinkafa ko ruwan da ke da gishiri yace wankan tsalki zai yi dasu". "Da farko mutum zai fara wanke gaban shi, bayan ya wanke zai wanke hannun shi saboda najasar da ya ta6a, zai d'ebo ruwa har sau uku yazuba ma kansa, ya murza kansa har ruwan sukai k'asan kansa, daga nan zai yi alwala shud'i guda-guda sannan ya wanke 6angaren jikin shi na dama daga sama har zuwa k'asa, 6angaren hagu ma haka sannan ya game jikin sa da ruwa ya murza ko ina". "An samu sa6anin wasu maluma da suka ce idan mutum ya wanke gaban shi zai fara gabatar da alwala, wasu kuma sukace sai bayan ya k'are wankan gaba d'aya sannan yayi alwalar. Allah masani". "Addu'ar shiga kewaye (( Allahumma inni A'uzu bika minah khubithi wal khaba'ithi)) "Addu'ar fitowa daga kewaye". ((Gufranak)) "Addu'ar mugun mafalki". ((Allahumma inni A'udhu bika min sharri ma ra'aytu fii manaamee an yadurranee fii deeni wa dunyaay)) "Addu'ar kariya daga azabar k'abari". ((Allahumma innee As'alukar Jannah, wamaa k'arraba ilaiha min k'aulin wa amal, wa A'udhu bika minan naar wama k'arraba ilaiha min K'aulin wa amal, wa A'udhu bika min fitnatil mahya wal mamat wa min fitnatil k'abr wamin fitnatil masihid dajjal wamin Adhabin naari wasu'il maseer)) "Addu'ar neman ya fiyar sa6o. ((Allahumma inni a'uzu bika an ushrika bika wa ana a'alam wa astagfiruka li maala a'alam)) Gyaran muryar da akayi da speaker shi ya nu na mata alamar lokacin ta ya yi, speaker ta ajiye ta koma mazaunin ta. Kabbara ce ta biyo baya had'e da jin-jina mata akan abubuwan da ta gabatar. Nan akayi salati ko wa ya ka ma gaban shi sanadiyyar gabatowar magriba, kowa da maganar (ZAZ) ya fita a bakin shi sanadiyyar add'o'in da ta yi tamkar itama Malama ce ba d'aliba ba.
.
Gaskiya (ZAZ) kin kawo wuta sosai yau, kinji yanda kike rero addu'o'i tamkar Ustaz Yusuf?". "Banson sharri wallahi, kina ji yanda murya ta ke wani rawa-rawa alamar tsorace nake. Ni fa shiyasa kika ga ko wannan musabak'ar da za muyi gabana ke ta fad'uwa saboda na k'i jinin karatu a cikin bainar jama'a". "Tabbb ai wannan shafin mai ne wallahi, kina ganin yanda ake taro sosai idan lokacin musabak'a yayi. Kuma hakan da ake yi duk Larba anaso abin yabi jikin mune har mu saba mu daina jin tsoro", cewar Salmat. "Ranar da duk Ustaz Lukman ya ji kina furta wannan (ZAZ) d'in a bakin ki kya yi bayani, saboda kinsan ya ce adaina kira na da hakan". "Yo ai ba sai kin gaya min kina da mai tare maki ba, duk kauce-kaucen ku za ku fito kuyi bayani ne". "Shin tsaya me kike nufi ne, ban fahimce kiba?". "Kinsan dai ko kin 6oyewa ko wa soyayyar ku da Ustaz Lukman bai dace ni ki 6oyemin ba". Cikin gwalo ido da wani cin birki tamkar mai tuk'in mota ta ja ta tsaya, mamaki kwance fal a fuskar ta. "In har kin yarda kalmar "So" bata ta6a ratsawa tsakanina dashi ba, sai dai mutunci". "Ke ce baki fahimci hakan ba, amma duk wanda ya yi mai duba na natsuwa idan kina gaban shi to zai hango son ki kwance a k'wayar idon shi". "Allah yashirye ki, ke kika san wani abu "So" ni kam da saura na". "Ke ma za ki sani idan lokacin kisani yazo, wa yaga ana soyewa tsakanin Malami da D'alibar shi". "Allah ni ko guntun namiji bai cikin tsari na ko Aure zan yi, na fison dogon namiji wanda zai yi guda da rabi d'ina". Dundu Salmat ta kai mata had'e da furta, "makira kika ce baki san So ba kuma amma ga shi kina wassafa mijin da kike son Aure". "Shi ne sai aka ce maki wassafa ra'ayin ka shi ne So d'in?".. Yanzu bara in tambaye ki
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment