Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wa da wayewar waje k'ara ta gida ba".
.
"Nasan matsalar Brother mai sauk'i ce, saboda shi kwata-kwata matan ne basu burge shi, asali ma ko taro ake yi muddin akwai Mata gurin bazai halarci taron ba, ni kai na da nake k'anwar shi ta jini sai shekaranjia ne Mum ta matsa mai ya kar6i lamba ta, kin ga ko irin shi bazai yi wuyar shawo kai ba tun da idon shi basu bud'e da soyayyar kowace Mace ba". "Saboda haka ki dage ki janyo hankalin mijin ki, in zama ya yi dad'i za ku dace sosai da Brother, kar ki biyewa zugar k'awaye". Hakan dai ta yi ta tsara mata irin abubuwan da ya dace tayi da way'anda basu dace ba har suka k'are girkin. Zajlah ta kai duban ta zuwa ga Yusrah had'e da furta. "Ni yanzu abu d'aya nake so ki samo min customers na d'inki tunda kin ga ba karatu nake yi ba sai dai zaman gida". "Ba yanzu ba kam sai an gama kula da yaya na sannan, kuma ai ni ban tabbatar kin iya d'inki ba, kar in kwaso atamfofin k'awaye na ki yanka ba dai-dai ba Brother ko ya biya su", tana maganar ne d'auke da murmushi a fuskar ta. "Ke dai ki samo za kiyi mamaki". Da hakan suka kammala ayukkan had'e da kimtsa gida sannan Yusrah ta yi haramar wuce wa, leda ta cika mata da kayan sha fa cikin na lefen ta, kuma ta had'a mata da dubu biyu cikin kud'in da su Salis suka ba ta, dak'yar ta karb'i kayan tayi mata godiya. * * * * Alamein na shigowa gidan ko takan abincin bai bi ya wuce part d'in shi, duk da kamin ya fito daga gidan Mum ta yi mai nasiha dai-dai gwargwado kan kula da hakk'in yarinyar mutane wanda ya nuna mata zai yi insha Allah. Sa6anin yanzu yana doso gidan ya ji gaba d'aya ranshi duk ya 6aci shiyasa ya k'i kula abincin ya wuce kawai. Kuma dama bai saba da cin abincin kowa ba sai na Mum, don ko yanzu sai da ya sa Saudat ta d'ebo mai abinci ya ci sannan ya fito. * * * Tana jin shigowar shi tana part d'in ta wata zuciya ke ce mata ta fita tayi mai barka da dawo wa, wata na ce mata kar kije ya maki wulak'anci. Gaskiya ba k'aramin fad'uwa gaban ta ke yi ba akan irin muguwar hararar da yake zabga mata. Da hakan ta yanke shawarar zaman ta d'akin ta, wanka ta yo had'e da alwala ta gabatar da shafa'i da wutri ta yi addu'o'in ta sannan ta kwanta duk da irin tsoron da take ji. Tunani kawai take yi anya za ta iya biyar shawarar Yusrah kuwa?, saboda a tunanin ta ko kyautata wa mutum na tafiya ne da samun fuska, kawai dai ta yanke ma kanta in har ta ga fuska za taci gaba da kyauta ta mai, da hakan 6arawo bacci ya yi awon gaba da ita.
.
Yau ta kama Alhamis dai-dai da kwanan ta biyar kenan a gidan Alamein, wanda sai ta wuni ta kwana basu had'u dashi ba, kuma har ko yaushe ta yi girki za ta ajiye mai sai dai yanda ta ajiye hakan za ta zo ta d'auke shi sai dai ta bayar sadaka wa almajirai. Tun safe take hada-hadar tarbon k'awayen ta da suka yi mata alk'awarin kawo mata ziyara yau d'in. Tana gama ayyukkan ne ta yi wanka ta shirya cikin wata shadda brown fitted gown, ko minti biyar bata yi da shirin ba sai ga su sun zo su hud'u Salmat ce cikon ta biyar d'in su. Hakan suka baje sai hirar makarantar suke ta zubawa, wanda a ciki ne suke gaya mata Ummulkhairi ce matar Ustaz Yusuf ya yin da Safiya ake maganar ta da Ustaz Lukman. Da la'asar ne suka ta shi wuce wa ta rik'e Salmat kan ce wa sai zuwa marece za ta wuce, da hakan suka fice suka bar ta. Hira suka dasa tsakanin su inda Zajlah ta kwashe yanda maganar auren ta ta kasance ta gaya wa Salmat, hak'urin nan dai da Yusrah ta ba ta shi Salmat ta ba ta had'e da nuna mata muhimmancin biyayya. "Ni yanzu ba ma wannan ke damu na ba irin yanda zan yi in tafiyar Baba saudiya ta yi, saboda ko ganin shi ban yi barranta na in gaya mai zan je gida". "Hakan za ki jure gaskiya, kuma ki rik'a kula da gyara mai part d'in shi in har ya fita tun da ya zama dodon ki, Allah ni wannan in ni ce cikin wata d'aya zan gama dashi". Murmushi kawai Zajlah ta yi, da hakan suka yi girkin dare suka k'are. Ba yanda bata yi ba kan Salmat ta tsaya har a gama magrib sannan ta wuce tak'i, "in ma na tsaya wa kika ajiye da zai kai ni in nayi dare? Ga wannan unguwar ta ku kuwar ka banza, ko misk'ilin mijin ki za ki sa ya mayar dani?". "Ina nagan shi ni kaina barranta na insa ya mayar dake, ke dai ayi ta sha'ani". Suna cikin hakan ne sai ga Alamein ya shigo gidan, saboda falo suke tsaye suna maganar za ta wuce.
.
Ba k'aramin mamaki ya yi ba yanda ya jiyo maganar mutane a falon, saboda yau kwanan shi biyu ko motsin ta bai jiba, abincin da yake gani saman dinning ne ke ba shi tabbacin tana gidan, ba don hakan ba da yace ba mutum a gidan. Ba don suna gab da k'ofa ba da ko sallamar shi ba za su ji ba, saboda iya la66an shi sallamar ta tsaya, gaida shi sukayi ya amsa ba yabo ba fallasa, Direct hanyar part d'in shi yayi, "am ji mana Malam". Muryar ta daki kunnen shi cak ya tsaya ya juyo yana yi mata kallon raini had'e da 6acin rai tattare a fuskar shi na jin haushin Malam data kira shi. "Baban mu zai wuce saudiya zuwa jibi in kai bai da darajar da ko gaisuwar surukai kaje yi mai to y'ar shi na da buk'atar zuwa ta gana da mahaifin ta", cikin isa da gadara Salmat ke gaya mai maganar, don ita ba ta hak'urin wulak'anci. Ba k'aramin k'ok'arin ta Alamein ya gani ba na tsaya ta gaya mai magana a gadaran ce, saboda ita ce Mace ta farko da hakan ta ta6a had'a su har ta dubi k'wayar idon sa ta so ka mai magana. "Kin san ce maki aka yi da aka ta shi d'aura auren a k'afa ta aka d'aure igiyoyin uku akace duk inda zan fita tana manne dani da za ki ce min za taje gida, in ta iya ta biki kuje tare kar ta dawo gidan ba damuwar Alamein bace". "Wannan sunan ga alama kuskure akayi gurin rad'a ma shi, ina ga wanda aka k'udurta daban wannan ya fito a fatar baki daban, saboda kwata-kwata sunan bai dace da mutane irin ku ba". "Amma ina mai baka shawara daka canja takon zamantakewar aure saboda in kai ba'a ta6a ganin ka aka furta ana son ka ba, to Zajlah har masoya sai da ta ture, ba'a kawo ma ita saboda rashin mashin-shi ni ba, darajar iyaye ka ci". Ba ki sake ta barshi ta fizgi hannun Zajlah wacce ta zamo mutum mutumi tana kallon Salmat ta kasa ta6uka komai, falon suka bari don ta taka mata. Sai da suka kai gate sannan ta ja ta tsaya, "yanzu ke har wannan namiji ne za ki tsaya shakkar tunkara don kina son fita?, Allah in ni ce wannan sai dai mu gasa juna wanda ya gasu shi zai yi bayani, kin ji ance in masara ta ji wuta ita ke fad'i". "Allah ran da duk kika jibgu hannun mutane ba ruwa na, kinga haka ranar kika so kawa k'anwar shi magana". "Tabbb su jibga manya, ke ni fa zan iya d'aukar rainin hankali daga talaka d'an uwa na ban d'auka ga mai kud'i ba wallahi, saboda abin sai yayi yawa in kayi sake, don mutum bai ga uba na yawon maula gurin shi ba barranta na ya wulak'anta ni". "Kuma yanzu kin ji da kunnen ki abinda ya furta, saura kar ki shirya kije ma Baba ban kwana, ni wallahi da ni ce to ya bud'e shafin yawo sai inda mai ya k'are". Sosai Zajlah ke mamakin rayuwar Salmat don kwata-kwata bata yo halayyar Mama Inno ba, don tun suna yara ba ta d'aukar raini. Hakan ta sa kai ta fice daga gidan had'e da jadda da mata ce wa sai sun gan ta kamin wu cewar Baba. ** ** *** Fadeel ya shiga damuwa sosai saboda tabbatar da ya rasa yarinyar har abada, domin akan idon shi aka d'aura auren ta da wani, ya san ba k'aramar asara yayi ba saboda samun nutsuwa irin ta ta ga y'an matan yanzu abu ne mai wuya, da hakan ya hak'ura sai dai har kullum yana fatar samun Mace natsattsiya tamkar ta, Fadeel kenan da Zajlah ta yiwa nasiha da zai mari Mum. Ustaz Lukman ma hakan ya yakice Zajlah daga zuciyar shi har ya furta wa Safiya k'awar Zajlah yana son ta saboda gudun yakuma nauyin baki.
.
Yau dai abinda ta k'udurta data gama girkin breakfast gidan Mum za ta je tayi mata wuni, hakan ya sa ta gama girkin ta cikin lokaci ko ta kan Alamein bata bi ba ta fice saboda sanin cewa yana company. Da shigar ta gidan Mum ke ta tarairayar ta, bata san ina za ta d'ora taba kan murna ita dai yarinyar ta yi mata har ga Allah don tana ganin mutuncin ta sosai. Ganin cewa Mum ta shiga kitchen ne ya sa ta bi ta domin taya ta girki, "ai da kin koma falo kawai, saboda ba girki ne zan yi ba Daddyn ku ne kawai zan yiwa ferfesun kifi".
.
"Ba komai Mum kawo in d'ora". Hakan ta ba ta girkin saboda matsa mata da tayi kan ta ba ta, suna hira da mai aikin Mum ita ko tana aikin har ta kammala. "Ni fa har yawu na sun tsinke da wannan girkin naki, duk gida ya d'auki k'amshi haka", cewar Mama Talatu. "Kai Mama ai ban ma iya girki sosai ba saboda ko da na tashi gidan mu ban san mahaifiya ta ba sai mahaifi na, Mama Inno kuma bata cika ba mu girki sosai ba duk da mu ma ba zama muke yi sosai ba kullum muna islamiya". "Duk da hakan na san zai yi dad'i gaskiya, don kin fi waccan sangartacciya da ko ruwan Lipton bata iya dafa wa ba sai d'an banzar girman kai da raina mutane". A rayuwar ta ta k'i jinin cin naman musulmi d'an uwan ta, saboda sanin illar hakan, duk laifin ka gare ta ba za ta iya zaman zagin ka a bayan idon ka ba. "Allah ya kyauta Mama, a yita hak'uri. Wai ma ina Saudat d'in tun shigowa ta banji motsin ta ba?". "Yanzu za ki gan ta tun da azahar ta yi, dama tana zuwa health makaranta, auren nan ne ya sa ta kwana biyu bata je ba". Da hakan har ta kammala girkin ta fito falo, har k'asa ta durk'usa ta yiwa Mum sannu da hutawa, hannun ta ta rik'o ta zaunar da ita gab da ita. "Haba Zajlah har yaushe wai za ki daina jin nauyi na? Na gaya maki ki saki jikin ki tamkar kina gaban Mama Inno, ko Mama Asabe zance ne?", tana maganar ne d'auke da murmushi a fuskar ta. Da hakan dai ta samu tana jan ta da hira har ta d'an saki jikin ta, nan Zajlah ke gaya mata tana so gobe taje gida yiwa Baban ta bankwana zai wuce saudiya jibi. "Ba matsala Zajlah zan shirya gobe muje tare in ya so in baro ki can ki wuni ko, ina fatar kin gaya wa Son batun tafiyar Baban na ki?". Tunawa da cewa jiya Salmat ta furta mai maganar ya sa tace' "eh Mum yasan da maganar". Tana shigowa falon ta yi turus ta tsaya tana wani shan k'amshi, da murnar ta ta taryo ta duk da tsorace take saboda gudun hantara, hannu ta mik'a ta kar6i litattafan da ta rungume had'e da furta "sannu da zuwa, ya makarantar?". Yauwa ta furta a tak'aice, duk da taso yi mata wulak'anci ganin Mum ya sa ta yi shiru, don ta san ko ta sha giyar wake ba za ta fara ba. Littafan ta kar6a ta wuce d'akin ta, (ni dai Jegal da ido na bi ta saboda mamakin ko mahaifiyar ta bata gaida ba). "Wai Zajlah ki na da ra'ayin makarantar boko ne ko ya ya?", "a ah Mum an ce boko da wuya kuma ni iya primary kawai na tsaya, sai dai ba laifi ina gane k'ananun abubuwa".
.
"Kuma Mum ni yanzu d'inki kawai na sa gaba, in dai ina sa mu ba laifi nasan zan rage kewar wasu abubuwan". "Au kice da mad'inkiya nake zaune, da fatar kin iya kar ki 6ata kayan mutane a tarar da Mum ranko", tana dariya take wannan maganar. Yanzu ta fahimci Mum na da dad'in zama ga kuma raha da take da, tabbas albasa bata yi halin ruwa ba. "Mum hala Dad bai shigo ba?, yau yunwa nake ji sosai wallahi, ko break ban yi ba a skul". "Kira shi kiji in ba yanzu zai shigo ba sai kici na ki, kin san yau ko yayan ki nan zai ci abinci tunda ga matar shi nan gidan". Jin cewa Brother zai zo gidan ya sa ta hak'ura har sai da suka dawo. A tare suka shigo gidan wanda ya sa ya yi turus ya bi ta da kallon mamaki, sai kuma ya basar ya k'araso cikin falon, don dama ko ta kan gidan shi bai bi ba ya yo gidan saboda ya samu abinda ya ci. Durk'usawa ta yi ta gaida Dad sannan ta yiwa Alamein sannu da zuwa, Dad ya kar6a ba yabo ba fallasa sa6anin Alamein dake yak'e wanda ya fi kuka ciwo. Falon Dad suka wuce saboda nan ne gurin cin abincin su, sa6anin Mum data tsaya suje tare da Zajlah aci abincin, inda ta nuna ma Mum ak'oshe take duk da yunwar da take ji tasan da nauyi taje cin abinci da surikin ta, duk da ta hango su a gurin su ba komai bane, kuma ita ma da tana gida tare da Baban ta take cin abinci. Tsinkayo muryar Mum tayi tana ba Talatu umurnin ta had'a abinci ta kai mata falon ta. Hannun ta ta rik'a ta kaita falon ta, sai da Talatu ta kawo komai sannan ta ba ta umurnin taci abinci kamin ta dawo, da hakan ta fice zuwa falon Dad.

A DALILIN GATA Pape 16-20
.


Falon Dad ta koma ko da ta shiga har sun gaji da jiran ta sun fara cin abincin sai santi suke yi, guri ta samu ta zauna ta saka abincin ta fara ci. "Mum baki ta6a ferfesun kifi da ya kai na yau dad'i ba, ga shi ya ji garlic sai k'amshi ke tashi". "Kawai Son ka fito ka gayan cewa matar ka ta fini iya girki, shiyasa har gaba na kake kasa hak'uri sai ka yabi girkin ta". Cak su duka suka tsayar da cokulan su daga cin abincin, kallo ya koma gurin Mum, Dad ne ya kasa hak'uri ya furta. "Yanzu kina nufin wannan mitsitsiyar yarinyar ce ta yi wannan girkin?, lallai Son kana kwasar ragwada, sai dai har yanzu banga ka fara kaurin wuya ba". Yana maganar yana Shafa wuyan shi alamar tsokana. Shi dai kawai basar da abin ya yi yana dariya yana nok'e kai, sai tunani yake yi ashe kan shi yayi wa da baicin abincin ta. "Gobe ma zanje gidan su yarinyar saboda mahaifin ta zai wuce saudiya, don haka kai ma Son ka shirya don kai za ka kaimu gobe d'in ni da ita". Ji yake yi tamkar yafasa ihu saboda yanda Mum ke son kusancin shi da yarinyar, shi ko har ga Allah ko ganin ta bai son yi, hakan dai ya kar6a ba don ran shi ya so ba. ** ** ** 6angaren Zajlah kuwa abincin ta ci sai da ta k'oshi sannan ta kai kayan abinci kitchen, d'akin ta dawo ta hau gyaran shi duk da ba wani gyara ne a d'akin ba, har toilet ta wanke ta shimfid'a sabon blanket ta feshe d'akin da air fresheners sannan ta dawo falon ta zauna, don jin take yi ba ta da ra'ayin fita falon gidan saboda kar ta had'u da Alamein. Tun daga k'ofar shigowa falon wani dadda d'an k'amshi ya tarye ta, ko da ta shigo falon ta gan ta kwance saman 3sitter barci ya yi awon gaba da ita. D'akin Mum ta za ga ko ina fes dashi sai k'amshi ke ta shi, a ranta take ta saka ma Zajlah albarka had'e da hango alkhairin da ke tattare a cikin auren. Sai la'asar Mum ta ta da ita ta gabatar da sallah ta kuma fad'awa kitchen suka yi girki ita da Mama Talatu, bata wani samu sakin fuska daga Saudat ba shiyasa take mak'ale da Mum ko Talatu. Har k'arfe 09:00pm ba labarin Alamein ba bu alamar shi, kuma wayar shi ma ta k'i shiga dole direba ne ya maida ta duk da ba nisa da gidan sai dai shirun unguwar. Kulolin abincin da ta zo dasu ne ta ajiye a falon ta wuce part d'in ta, saboda ba yunwa take ji ba sai da ta ci gidan sannan ta fito. *** Alamein kuwa da gayya ya k'i ko ma wa gidan, saboda yasan da ya je dole shi zai dawo da ita gidan, sanin cewa Mum za ta iya ne man shi a waya ya sa ya kashe ta duka. Akan idon shi ta shigo gidan ta ajiye abincin sai da ya tabbatar ta shige sannan ya fito ya ci abincin ya ko ma d'akin shi. Kwata-kwata bai son abinda zai janyo alak'ar had'uwar su ko da ta second biyu ce, kwance ya yi yana ta tunanin yanda wai kamar shi za'a yi mai auren dole, don bai ga abin so ga Mace ba. Wasu lokuta in har yana tuna lokacin degree d'in shi yanda friends d'in shi ke rud'ewa in suka ga Mace abin har haushi yake bashi over, don ganin yake yi rashin abinyi ke sa ka 6ata lokacin ka ga Mace. In har bai manta ba akwai lokacin da wata Lubna ta mak'ale mai tana bibiyar shi wanda shi ba ta ko gaban shi, ranar ta tarar da shi zaune dasu Imran kawai ta rungumoshi wait gaisuwa ce, marin da ya kifa mata ne ya dawo da hankalin tsirarun mutane dake gurin nan take aka ta mata dariya tun ranar bata k'ara kula shi ba, da wannan tunanin bacci ya yi awon gaba dashi. (Alamein asuba ta gari inji Jegal, lolx.) * ** ** WASHE GARI Misalin k'arfe 11:00am Mum ta kira Alamein kan cewa ya d'auko Zajlah ya biyo ya d'auke ta su wuce, rasa ina zai saka ran shi ya yi ta yanda zai gaya wa Zajlah ta shirya su wuce d'in, wata dabara ta fad'o mai take ya lalabo lambar ta da Yusrah ta kira shi da ita. Text message ya tura mata kamar haka ( ki fito Mum na jiran mu).
.
Ta dai ji wayar ta ta yi k'ara kuma ta d'auko taga alamar abu a sama amma bata gane miye ba, saboda bayan saving number da call ba abinda Yusrah ta ko ya mata, asali ma bayan Yusrah da Mum ba wanda ya ta6a kiran ta a waya. Ba sarwa tayi kawai ta fad'a wanka. Bayan ta fito ne ta kimtsa tana zaune saman mirror tana taje kanta aka banko k'ofar d'akin da k'arfi wanda sai da ta razana da sauri ta zabura. Gashin kan ta ya kama da k'arfi ya fizgo cikin rinannun ido yake nuna ta da d'ayan yatsan. "Ke wace irin dak'ik'iya ce da zaki banzatar da ni a mota fiye da minti ashirin?, waye bawan ki ko wa kika ajiye?, kinsan ba don darajar Mum ba wallahi baki yi darajar ko da takalmin Alamein su ta ka wannan k'azamiyar unguwa ta ku ba". Hawaye ne kawai ke zuba a idon ta ga shi har lokacin yana rik'e da gashin kanta. Wayar shi da Mum ta k'ara kira a karo na uku ya sa ya sake ta had'e da kai mata muguwar harara. Nan ya d'aga kiran had'e da ce mata ga sunan zuwa, cikin tsawa ya ce mata "fice muje banza kawai dak'ik'iya". Hijab d'in ta ta janyo daga saman gadon ta saka suka fice wanda har lokacin hawayen idon ta basu kafe ba. ®
.
Gaban motar ta je shiga saboda gudun ta zauna baya yace ta mayar dashi direban ta, ashe duk da hakan bata tsira ba harara ya bi ta da ita had'e da furta "baki yi matsayin da zan zauna gaban mota ni da ke ba sai dai ki koma baya, jahilar banza kawai". Sum-sum ta ko ma bayan mota ta takure sai zuciyar ta ce ke mata wani tuk'uk'i. Da hakan har suka iso gidan, Mum ta fito sai dai ta ce dole Zajlah ce za ta shiga gaba ita ko ta zauna baya, akan ta matsa ne ya sa ta fito had'e da durk'usawa ta gaida ita. Tallafo ta ta yi cikin sauri had'e da tallafo ha6ar ta sai ga hawaye shaaa, "me ya same ki Zajlah? Son ne ya 6ata ma ki rai?", duk cikin rud'u take tambayar ta. Kai ta girgiza alamar ba komai, "haba Zajlah yau fa ranar murna ce gare ki za ki je gida kiga iyayen ki, ni da na zata ina fitowa inga bakin ki har kunne kan farin ciki" murmushi ne d'auke a fuskar ta alamar zolaya. Hakan ya saka Zajlah ta d'an murmusa "Mum fa ba komai ina d'auko hijab ne zan saka naji abu ya fad'a man a ido, kuma na duba banga komai ba sai wani zafi da nake ji a cikin idon". Sannu Mum ta mata had'e da saka bakin ta ta bushe mata idon sannan ta rik'a hannun ta ta saka ta gaban motar ta rufe sannan ta shiga baya ta zauna. Unguwar su Zajlah ya nufa wato Birnin yari, ran shi 6ace sai wani cin magani yake yi, har suka isa ba wanda yace uffan har Mum d'in saboda kowa da abinda yake sak'awa a ranshi. Sai dai tunanin Mum har yau babu wani cigaba tsakanin zaman takewar su kawai Zajlah na 6oye mata ne, lallai tabbas yaro man kaza. Da hakan suka iso gidan inda Zajlah bata ko jira su ba ta fad'a gidan su Salmat, Mama Inno ta tarar zaune tsakar gida tana gyaran wake, saman ta ta

Please Login or Register in order to submit comment