Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fad'a tana razgar kuka wanda ya sa ta kayar mata da gaba. *** A can 6angaren Alamein kuwa Mum na fitowa daga motar ya je zuwa juya akalar motar shi ya koma gida Mum ta bishi da harara. "In ita gidan za ta wuni sai aka ce ma ni ma nan zan wuni?, wato ka fi k'arfin ka fito mu shiga ka gaisa da mahaifan yarinyar nan ko?, wai kai sai yaushe ne za kayi karatun ta nutsu a rayuwar ka?". Cikin 6acin rai ta kama hanyar shiga gidan ta bar shi, dole ba don yana so ba ya rufe motar ya mara mata baya da handkerchief saman hancin shi yana yatsinar fuska tamkar Wanda ya shigo cikin jeji.
***
Mama Inno ta tallafo ta had'e da jera mata tambayoyin meke faruwa wanda amsa tak'i fitowa sai dai ambaliyar hawaye. Suna hakan ne sai ga Mum ta shigo gidan da sallamar ta had'e da murmushi a fuskar ta, hakan ya sa Zajlah ta fad'a d'aki. Shimfid'a Mama Inno ta yi masu had'e da yi masu kyakkywar tarba cikin fara'a da sakin fuska, Mum ta furta "kin ga y'ar tawa da sangarta muna kawowa k'ofar gida tana fasa kuka, ita da ya kama ta yau ta zamo cikin walwala baki har kunne", cikin zolaya Mum ke furta maganar. "Yo ai kad'an kenan daga aikin Zajlah, ba dai shagwa6a ba har dai in tana gaban Baban ta". D'agowar da Mum za tayi ta ganshi k'erere saman kan ta, muguwar hararar da ta zabga mai ya sa ya janye handkerchief d'in da ya toshe hanci dashi, sannan ya d'osa na gefen ta ya zauna tamkar mai tsoron zama saman allura. "Mu shiga can wurin Mal Abu d'in?". Maganar tace ta dawo dasu hayyacin su su duka biyun. D'aki ta shiga ta d'auko hijab had'e da sako Zajlah gaba suka shiga gidan na su. Nan aka gaggaisa inda suka tarar Baban ta bainan yana gurin Sana'ar shi ta kayan gwari, Mama Inno ce ta fita ta samu yaro don yakiro su Mal Abu. Cikin minti goma sai gashi sun iso, nan dai aka gaisa suka yi mai Allah sanya alkhairi da fatar zuwa lafiya adawo lafiya. Dubu ashirin Mum ta ajiye sannan ta yiwa Alamein alama da ido yaba da nashi, hannu ya saka gaban rigar shi ya kwaso kud'in da shi kanshi baisan nawa ne ba ya ajiye, saboda a matse yake da subar gidan. Shi ya fara ficewa sannan Mum ta kai duban ta ga Mama Asabe tace' "ga y'ata nan ku kulamin da ita zuwa dare Son zai dawo yaje da ita", cikin jin dad'in irin kulawar da Mum ke bata Mama Inno ta furta "za ki samu y'arki lafiya in ma murnar ganin Baban ta baisa ta k'ara k'iba ba". "Ai ko in hakan ta kasance zanfi kowa murna da farin ciki". Da hakan dai suna ta walwala Zajlah ta raka Mum har gurin mota sannan ta dawo gidan. "Zo nan Zajlah inga me ke damun ki, na ga idon ki sun kumbura". Kusa dashi taje ta lafe tana wani zuba shagwa6a. Mama Inno ce ta kar6e da cewa "wacce ta shigo da kuka gidan har ta kayar min da gaba, ashe duk tsabar shagwa6ar zuwa gida ce", nan dai suka ta tsokanar ta ita ko sauraren su kawai take yi. ** *** 6angaren Alamein kuwa har suka kai gida fad'a Mum take mai kan abubuwan da yake yi marar dacewa musamman ga sirikan sa, tun tana fad'an har ta dawo rarrashi tana mai nuna mai irin yanda Zajlah ke mutun ta ta bai dace ya wulak'an ta na ta iyayen ba. Zurum ya yi yana sauraren ta tamkar mai d'aukar darasi, (ni dai Jegal na ce Allah yasa maganar Mum ta shiga kunnen ka Alamein).
.
Lokacin Salmat ta dawo daga islamiya saboda yanzu ta daina zuwa ta marece da safe zuwa la'asar take dawowa gida. Tana shiga gidan ta ci karo da Zajlah je kaga murna tsakanin su tamkar sun dad'e basu had'u ba, d'aki suka fad'a aka bud'e shafin hira. Bayan sun gaisa ne Salmat ke ce mata "ina gadararren mijin ki?, ina fatar kin fara gyara mai zama yanzu?".
.
"Hmm! Bari ke dai Allah ya had'a ni da miji marar tausayi, ai ni wannan auren nan kallon auren k'addara nake yi mai", nan dai ta kwashe yanda zaman su yake da yanda ya yi mata d'azun ta gaya mata. "Tabbb sai kika tsaya kallon shi gashin ki ya zamo linzami agare shi, wai ke wace irin Mace ce?, ni fa in mutum ya siyi mutunci wallahi zan nuna mai nice na raini mutuncin har ya girma, sa6anin ka nuna min rashin mutunci in nuna ma cikin shi nayi na haife shi". "Salmat ya kike so na yi ne?, wallahi ko Mum ban iya gaya wa irin zaman da muke yi dashi, nasan komai yayi farko zaiyi k'arshe watarana sai labari". "Lallai ko yarinya za ki zama goro ko abin saye, tunda kin za6i siyar da farin cikin ki ga wanda bai san darajar d'an Adam ba". "Ko dai ba za ki rama abinda yake maki ba to kiyiwa kanki gatan rashin d'aukar raini, saboda in kince ba za ki motsa to kin zama shara kenan duk abinda ya d'auko zai sauke shi saman kan ki". "Ni fa kinsan ko Mace y'ar uwa ta ban iya sa'insa da ita bare namiji, don haka kawai ki taya ni addu'a ita ce kawai mafita gare ni". "To Allah ya kyauta kuma ya dasawa Alamein bala'in son ki a ranshi". Suna had'a ido ta yi mata gwalo tana dariyar k'eta. Da hakan dai suka rik'a hira wanda Salmat ta so ta lurar da Zajlah muhimmancin k'watar y'ancin ta ga Alamein amma abin ya ci tura. D'inkin da aka ba ta na ashobe ta kwaso kusan turmi goma sha biyu ta jibge ma Zajlah had'e da furta "ga d'inki nan kije dasu kiyi ko za ki rage nisan gadin gida, gobe nake so in ba Sagiru su ya kai maki ki ragen aiki". "Zan dai d'auki goma inje dasu, sauran kuma kya k'arasa tun da ke kika yi had'ama kika kar6i kayan mutane". "Yi hak'uri matar Alamein, uwargida kuma amarya daga ke babu k'ari". Share ta kawai ta yi ta fad'a kitchen domin kama ma Mama Asabe girkin dare, ita ko ta fice gida tana mata dariyar shak'iyan ci. * * * * Babu abinda yake tunawa ran shi yayi mugun 6aci sai tunanin komawa d'auko waccan kucakar yarinyar da Mum ta mak'ala mai. Tabbas ba abinda Mum za ta sa shi ya kasa yi mata, kuma yaji fad'an da tayi mai d'azu sai dai ranshi ke 6aci ko yarinyar ya tuna da ita. Murmushi yayi sosai saboda samun mafitar ba sai ya je d'aukar Zajlah ba kuma abinda zai yi Mum ba za ta ta6a sani ba. * * * Kud'i Zajlah ta fitar dubu goma ta bawa mahaifin ta inda dak'yar ta samu ya kar6i kud'in, a cewar shi na mijin ta da Mum sun isa, duk da hakan sai da ya tambaye ta inda ta samu kud'i. "Baba abokanen shi suka bani dubu ashirin cikin su na ba ka goma na ajiye sauran saika dawo in yima dafuwa". Murmushi ya yi dajin dad'in yanda take kula dashi tun bata kai hakan ba. *** *09:00pm Aka aiko daga waje wai anzo d'aukar Zajlah, kayan ta ta had'a hadda d'unkunan da Salmat ta jona mata, har da guntun hawayen ta na rabuwa da Baban ta. Salmat ce ta d'auko mata kayan ta domin ta taka mata daga nan ta wuce gidan su, da biyu ta yi rakiyar saboda tana so Alamein ya yiwa y'ar uwarta ba dai-dai ba a gaban ta tayi mai tasss, sai dai sa6anin hakan suna fita suka ganshi jingine ga mota da fara'ar shi kamar kullum. "Ustaziya barka da fitowa", Salis kenan yaro mai kamala da ganin mutuncin manya. Nan suka gaisa har yasa Zajlah ta kira mai Baban ta su gaisa, ko da ta dawo hira ta 6arke tsakanin shi da Salmat domin hali ya zo d'aya kowa akun kanshi ne gurin surutu. Har k'asa ya durk'usa ya gaida Baba had'e da yimai fatar alkhairi, shi ma kan shi kud'i ya ba Baban suna ta yimai godiya. Mota ya bud'e mata ta shiga ya kai duban shi ga Salmat "to sai na ganki alhamis d'in banda karya alk'awari". Cikin jin kunya Salmat ta shige gidan, shi ko ya shiga motar ya ja suka fice. Mamaki ne fal a ranta, lallai ta tabbatar da Alamein bai san darajar aure ba, wato ya fi k'arfin yazo d'aukar ta sai dai yaturo abokin shi, irin haka ne shaid'an ke samun kutsawa zuk'atan masu raunin imani sai daga baya azo ana fad'in wane da matar abokin shi yake mu'amala alhali abokin ne ya bashi wannan damar. (Allah ka tsalkake mana zuk'atan mu ka k'ara mana k'arfin imani, kasa mufi k'arfin zuk'atan mu).
.
Har suka kai gida ba wanda yace da wani uffan, kowa da abinda yake sak'a wa a ranshi, fitowa tayi daga motar bayan maigadi ya bud'e masu gate sun shiga godiya ta yi mai sannan ta nufi hanyar shiga falon da kayan ta Salis ya rik'o mata wasu. A falon suka tarar da shi zaune yana kallo yana latsar waya, part d'in ta ta wuce ta kai kayan sannan ta dawo d'aukar na hannun Salis, abinda ta ji ne ya sa ta ja birki ta tsaya. "Yanzu don Allah A.K.A abinda kake yi a tunanin ka ya dace?, don kawai kar kaje d'auko yarinyar nan sai ka kira ni kace inje in d'auko ta wani aiki kake yi kallon ne aiki ko kuma chart da kake yi?". "Salis ya kake so inyi da rayuwa ta ne?, ka duba kaga yanda damuwa tayi min yawa, abubuwa duk sun ja baya, ko company sai ku ne ke kula dashi". "Wallahi in na ga yarinyar nan har wani k'unci ke ziyartar zuciya ta, na rasa ina zan tsoma kaina inji sanyi". "Hak'uri za kayi, muzgunawa yarinyar tamkar rashin bin umurnin Mum ne, kuma ni banga illar Zajlah ba yarinya ce mai hankali da nutsuwa, don Allah ka sassauta mata dame za taji? Auren dole ko rashin bata kulawa da baka yi?". "Ko ma miye ita taja wa kanta, da ace da Mum taje da buk'atar neman auren tace ba taso ai da ta hutar da kan ta, to nasan kwad'ayi ya kawo ta shiyasa". "Ai ko da kaga iyayen ta kasan mutane ne masu wadatar zuci da neman na kansu, kwata-kwata wannan abin bai dace ba wallahi". Ganin cewa baza ta iya jure sauraren maganganun ba yasa ta fad'a falon ta yiwa Salis sai da safe ta kwashi kayan ta ta koma part d'in ta. "To yanzu duba don Allah alama ta nuna ta ji me kake fad'a, kasan dai ba dad'i". "Kai ni fa ko a gaban ta zan furta abinda nayi niya don ba tsoron ta nake ji ba". Ganin in ya yi gabas yayi yamma ne yasa ya yimai sai da safe ya fice daga gidan rai 6ace da halayya irin ta A.K.A.
* * *
6angaren Zajlah kuwa tana shiga d'akin gado ta fad'a tana ta razgar kuka cikin damuwa da tsananin 6acin rai. A rayuwar ta bata ta6a saka ma ranta auren mai kud'i don taci kud'in shi ba, asali ma tafi hangen auren rufin asiri ta samu talaka d'an uwan ta da zai san darajar ta da k'imar ta, saboda yawancin masu kud'i basu cika d'aukar talaka wata tsiya a doron k'asa ba. Hakan ta ci kukan ta har ta gode Allah ba mai rarrashi. Alwala ta yo ta yi sallah had'e da kaiwa Allah kukan ta kan yakawo mafita acikin wannan aure na ta, bayan ta gama ne ta dunk'ula ta kwanta had'e da tunani iri-iri har bacci ya yi awon gaba da ita. * * * WASHE GARI Bayan ta gama sallah ne ta kimtsa d'akin ta, wanka ta yi ta shirya sannan ta nufi kitchen tea ta had'a iya cikin ta sai k'wai biyu data soya, bayan ta karya ne ta koma d'akin ta ta kwashi turamen da tazo dasu ta nufi d'ayan k'aramin d'akin da aka saka mata keken d'inkin ta da sauran komatsan ta, zaune ta yi ta fara yankan d'inkin sai da ta yanka turmi hud'u sannan ta hau keken ta fara. * * * 6angaren Alamein ko yana dosowa falon k'amshin wainar k'wai ta doki hancin shi, sai dai yaja ya yi turus da yaga dinning table d'in wayam sa6anin kullum da yake tarar da girki a gurin. Yau har ga Allah yaso yaci girkin ta kodon fad'an da Mum ta yimai ce wa kar yadawo gidan ta cin abinci in har ba matar shi ce taje mata wuni ba da tasan cewa babu mai bashi abinci ba. (Tabbb ni dai Jegal nace jin dad'in ferfesun kifi ne yasa Alamein zai la6a da fad'an Mum ya kwashi girki, sai ga shi ran Zajlah ya 6aci yau bata ajiye ba, lolx). Zaune ya yi turus a falon yana tunanin mafita, ga shi yana so yaje office cikin lokaci saboda wani meeting da zasu yi da wasu dasu ke da share a company d'in. Ga shi shi ba gwanin girki ba don ko ruwan Lipton bai iya dafawa ba. Kitchen ya fad'a ya yi sa'ar ruwan lipton har sun fara hucewa, hakan ya zuba madara da sugar kad'an ya sha ya fice daga gidan. * * * Zajlah ko na can na fama da d'inkin ta, har wani nishad'i take ji na ganin ta samu abinda zai rage mata damuwa, don har ga Allah ta manta wani 6acin rai data shiga jiya. Jin cikin ta na k'ugi ne ya sa ta ajiye d'inkin ta shiga kitchen macaroni ta yi jallof d'inta da dama ta saka a kula ta d'auki plate da cokali ta koma d'akin. Bayan ta zuba ta ci ne ta tsinkayo kiran azahar, nan ta yi sallah sannan ta hau d'inkin ta.
.
Kwanaki hud'u sun shud'e ba wani cigaba tsakanin zaman Alamein da Zajlah sai ma abinda ya k'arasa kwa6e wa, don yau kusan kwanan su biyu basu had'u da juna ba. Alamein ya fara shiga takura saboda ga shi ba gwanin yawon restaurant ba, asali ma yana iya cewa tun tashin shi bai ta6a cin abincin waje ko na wani aure ba sai dai na gidan su. A hakan yake buge-bugen shi in ya fita office yasha lemo da biskit, sai kuma maltina rabon shi da abincin kirki tun ranar da Zajlah ta wuni gidan Mum. ** ** ** Yau tun safe ta taya Mama Inno aikin gida saboda tana so taje gidan Zajlah, k'arfe 11:00 ta gama kimtsawa ta shiga gidan su Zajlah ta ja Naja'atu domin ta raka ta, saboda tun auren Zajlah ba ta jin dad'in fita ita kad'ai. Naja'atu y'ar k'anen Mama Asabe ce mai kimanin shekara tara a duniya, tun auren Zajlah Mama Asabe ta ji gidan ya yi mata shiru dayawa ta shawarci Mal Abu ta d'auko yarinyar ta dawo hannun ta da zama. Keke napep suka samu suka shiga sai G.R.A, gidan su Alamein ta fara shiga ta gaida Mum saboda karamcin dattijuwar, da murna ta tarye ta kamar ta had'iye ta, nan suka had'u da Yusrah ita ma ta zo ma Mum hutu kwana biyu. Tare suka rangad'a sai gidan Zajlah har Mum na mitar Yusrah ba ta gajiya da zuwa wurin Zajlah, basu had'u da Saudat ba akan tana makaranta.
* * **
Zaune take saman tela ta duk'ufa d'inkin saboda yau take so ta k'arasa ta samu ko d'an mak'ociyar ta ne Shema'u ta aika yakai wa Salmat d'inkin, saboda Salmat ba ta da waya haka ma iyayen mata, su Mal Inuwa ne kawai suke da kuma Baban ta ya wuce saudiya kwana biyu da suka wuce. Jin sun shigo falon ne tsit ya sa direct suka yi part d'in ta, ganin su ba k'aramin farin ciki ya saka ta ba, da gudun ta ta rungume Salmat ta saki ta rungume Yusrah sannan ta saki baki tana kallon su. "Daga ina kuka had'u haka ba sanarwa sai dai ku diro ma mutum ba shiri?", tana maganar ne d'auke da murmushi a fuskar ta. "Allah ne kawai ya had'a mu don mu d'ebe maki kewa yau, Mum na shiga gaidawa na tarar da ita a gidan". "Ai ko gaskiya na ji dad'i sosai da ganin ku", hannun Naja'atu ta rik'o had'e da tambayar ta lafiyar gida, yarinya mai surutu ta yita zubawa har da bata labarin da Baba zai wuce su Mama da Anty Salmat har da kuka suka yi, dariya sosai yarinyar ta basu yanda ta zak'e tana bada labari da kwatan ta yanda su Salmat suka yi. D'inkin Yusrah ta janyo tana dubawa had'e da furta "anya Sis ke kika yi wannan d'inkin?, ko wata ke zuwa tana taya ki?", cikin zolaya take maganar. "Tabbb ka ma kan ki ai wannan oga ce a gurin d'inki, tare fa muka fara koyon d'inkin amma yanzu ko wacce ta koya mana ta wuce ta musamman breast cup tamkar ta auna su". "Kai Salmat ki rage sharri fa, ni dai kawai d'inki ke birge ni shiyasa na mayar da hankali na iya". "Kin manta ana gab da auren ki da muka je gidan Zainab mai d'inki muka tarar ta saka wani style gaba ta zuba tagumi akan ta kasa had'a shi sai da kika kar6a kika had'a?". "Na tuna uwar k'wakk'wafi". Keken ta hau ta k'arasa had'a rigar sannan suka koma d'ayan d'akin a falon ta, lemo da ruwa ta kawo masu sannan aka zauna dasa wata sabuwar hira. "To ku tsaida hirar hakanan kuje kitchen ku ne ma mana abinda za muci, saboda ni dai na gaji bazan iya girki ba". Salmat ce ta bi ta kallo had'e da "furta matar nan dad'i ya maki yawa, mu da muke bak'i mu za mu ne mawa kan mu abinci, to tsaya ma da bamu zo ba waye zai dafa maki?". "Manta kawai barta ta huta, nasan gajiya biyu ce saman kanta ga ta Brother na, ga ta keken d'inki", tana maganar had'e da kashewa Salmat ido d'aya. "Ku dai kunga bone wallahi, tahowa zanyi in gayawa su Baba duk ayi maku aure, saboda na fahimci inda kuka dosa". "Kai rufa mana asiri, mu fa yanzu ake renon mu komai bamu sani ba", cewar Yusrah. "Shi ne naga da rarrafe kuka zo gidan nan k'arewar raino, ku dai yi sauri ku fitar da Maza musha shagalin biki". Salmat ce ta furta "ni kam bazan yi aure ba sai kin haihu hud'u tukuna", "Tunda haihuwar kashi ce, wallahi da kin shiga uku in na haihu hud'u kina gida, Allah sai dai mu bada ke sadaka koda a lima mai ne". Dariya suka yi sosai nan Yusrah ta kama hannun Salmat suka fice zuwa kitchen domin samun abinda suka girka. Ita ko Naja'atu ta janyo tana ta ba ta labari sai dariya take yi, ji take yi tamkar farin cikin ta yad'ore hakan. ®
.
Suna tashi daga office ya ce ma Alamein suje yau gidan shi zai je duba ajiyar shi, jin hakan ya sa Imran yace shima baza'a barshi a baya ba. Hakan ta sa suka d'unguma su duka suka biyo shi, wanda sai fargaba yake yi in ba abinci za suje ci ba, duk da babu abinda basu sani a zaman takewar su ba, sai dai yanzu yana jin nauyin suje gidan ba su da abinda zasu ci. Dabara ce ta fad'o mai na kawai ya nuna masu zai biya gurin Mum yakai mata sak'o, saboda sanin in dai daga office suke direct suka yi gidan to abinci ne na farko da Mum za ta tarye su dashi. Sai dai kash ba yanda bai yi ba Salis ya kafe kan cewa shi fa sai ya je yaga ajiyar shi sannan in zasu wuce su biya su gaida Mum d'in. * * * Abinci suka yi kusan kala uku suka saka a kuloli, saboda cikin su ba wanda yasan cewa ta daina yin girki da Alamein, asali ma Salmat ce ta sa ayi girkin haka a cewar ta gidan Amarya har kullum bai rasa bak'i. Bayan sun k'are girkin ne suka kimtsa gurin sannan suka koma falon ta, abin dariya ko da suka shiga Naja'atu na ta zuba bata lura da Zajlah ma bacci take yi ba. Dariyar su ce ta tayar da ita daga baccin da ya d'auke ta, zama suka yi suna dariyar ta suna furta "neman kud'i da wuya yarinya". "Ai ni ba kud'i ne nake nema ba, rage zango ne nake yi saboda ban aikin komi". "Ashe in aka bada kud'in wannan d'inkin in d'auka kenan", cewar Salmat. Yusrah ta ce' "Sis ni ma zan kawo customers kwanan nan tunda na ga ke expert ce a 6angaren d'inki". Hararar su kawai ta yi ta fad'a toilet ta yi wanka. Bayan ta fito ne ta kimtsa Yusrah ta saka ta gaba da cewa sai ta yi mata kwalliya don tasan yanzu Brother bai nesa da dawowa, hakan ta saka ta gaba ta yi mata make up had'e da wani nad'i tamkar an d'aura gwaggwaro. (Saura k'iris waya ta ta su6uce ta fad'i, sai dai na rik'e ta gam saboda gudun rasa wacce zan kawo maku rahoto, tabarakallah ahsanul khalik'een kawai nake na natawa, lolx). Baki Salmat ta saki tana kallon Zajlah had'e da furta "lallai make up na fitar da 6oyayyen kyau, to ni ma ba za'a barni a baya ba azo a tsantsara min tawa".
* * *
Da dosowar su gidan k'amshin abinci ne yatarye su, mamaki fal a fuskar Alamein sai dai kawai ya dake kuma ya basar. Falon suka shiga sai dai wayam ba kowa sai dariyar su ce ke tashi daga falon Zajlah. Masauki suka yiwa kansu suka zube a falon. Hayaniyar da suka jiyo a falo ce ya sa Yusrah ta lek'o, da d'an sauri saurin ta ta iso falon tana mai fad'in "oyoyo Brother na", cikin sakin fuska ya amsa ta sannan ta gaida su Salis. D'akin ta koma ta gaya masu wanda Zajlah kamar kar ta fito sai dai mutuncin su Imran gare ta sun wuce ta yi masu haka, gyale ta janyo ta yafa sannan ta tunkaro hanyar zuwa falon. Duk zumud'i da zagwad'in ta na saka Salis a idon ta sai gashi wata kunya take ji tana dabai baye ta, jin batajin motsin Salmat bayan taba ya sa har za ta bud'e k'ofar kuma ta juya ta saka ta gaba suka fito falon. Gaisawa suka yi wanda Salmat da Zajlah d'in ko ta kan shi basu bi Ba, shi ko kallo guda ya yi ma Zajlah ya ji wani abu ya tsirga mai take ya mayar da kanshi k'asa yana latsar waya ganin cewa tana tare da y'ar uwar ta mai tsiwa. Kamar kullum falon ta suka koma suka ci na su abinci, bayan sun gama ne suka dawo falon su dukan su. "Ka d'auki ajiyar ka mu wuce, in kuma baka ta shi ba ni in fice", a fad'ar Imran. Salmat

Please Login or Register in order to submit comment