Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

har mutane suka rage sannan suka k'arasa gurin ta, cikin yatsinar fuska Saudat ke kallon su da d'ai d'aya sun sha manyan hijabayyen su har k'asa. "Kyawon zaman takewa ka samu abinda yada ce dakai, amma wasu da ka gansu kasan abin sai maneji". "D'an hakin da ka raina shi ke tsokane ma ido, kuma mutunci siyen shi ake yi ba shi ke kai tallan kanshi ba, mai hikima shi ke tauna magana kamin ya watso ta, wani ko maganar ke neman mak'alewa domin ya suturta ta shiko yana k'ok'arin hankad'o ta". Cikin muzan ta Saudat ta bi Salmat da kallo had'e da mamakin kalaman da ta feso mata tamkar dafin maciji. Yusrah ce ta tsaya suka yi gaisuwar mutunci har suna ta6a hira tsakanin su, daga nan suka fice su kuma suka shiga napep sai gida.
.
Yaune ranar Assabar misalin k'arfe 12:00 dubban jama'a suka shaida auren. AL'AMEIN KABEER AL'AMEIN (A.K.A) DA ZAJLAH ABUBAKAR ZUBAIR (ZAZ) Wanda ya samu halartar manyan bak'i daga gurare da dama duk da ba hakan Dad ya soba, musamman gidan su yarinyar da yake ganin k'ask'anci ne kamar shi yaje wannan k'azamar unguwar kuma ace auren d'an shi ake yi gurin. Dak'yar da lallami k'anen shi Abban Yusrah wato Alh Muttak'a ya shawo kanshi kan zuwa gurin auren. A 6angaren Alamein kuwa shi ma dak'yar da lallami Mum dasu Salis suka ciwo kan shi ya tashi ya yi wanka ya shirya cikin dakakkiyar shaddar shi fara k'al wacce ta k'ara fito da kyawon shi na asali, sai dai daka dubi fuskar shi babu annuri sam a tattare dashi. Bayan gama d'aurin auren ne Imran ke yimai tuni kan gaisuwar da Ango da abokanen shi ke shiga yi gidan su Amarya, tur6une fuska ya yi tamkar wanda aka yiwa wahayi da mutuwa. "Kayi hak'uri A.K.A kakka bijirewa umurnin Mum in kayi hakan ba za taji dad'i ba kuma kasan da za mu fito sai da ta k'ara jaddada mana hakan". Da hakan suka d'an shawo kanshi suka shiga gidan su Zajlah shi da tsirarrun abokanen shi suka gayar da iyayen, sai yak'e yake yi wanda ya fi kuka ciwo had'e da wani tur6une fuska tamkar yad'ora hannu Saman kai yafasa da kuka. Muryar Salis ya ji had'e da wasu friends na su suna tambayar ina Amarya ta fito a gaisa. Zumbur yamik'e tamkar wanda ya zauna akan kunama, hanyar fita daga gidan ya dosa ganin hakan ya sa suka mara mai baya. Can na tsinkayo maganar wata daga cikin dangin Zajlah na giwa tazo na furta. "Gaskiya wannan Angon na da kunya akan wasu mazajen da za kaga sun shigo gaida iyaye an saka Amarya gaba har da su d'aukar hoto". "Gaskiya kam wannan na da sauran kunyar shi", inji wata mata. Da hakan sauran k'awayen Zajlah suka shiga gidan su Salmat suna ta yabon kyawon angon, har wasu na zolayar ta da cewa' "shiyasa ake mana 6oyon Angon ashe ansan mai tsada ne hakan, gaskiya kin more Allah yabada zaman lafiya". Salmat ce ta kar6e da Ameen had'e da cewa ai dole mu 6oye angon mu ga irin ku masu hangen kyawawan Maza. Da hakan dai suka ta zolayar juna wanda Zajlah tayi shiru ita d'ai tasan me take tunani a ranta saboda tana hango abubuwa da dama.
***
10:00pm Aka kai Amarya d'akin ta had'e da y'an rakiyar ta iyaye da abokanai har da dangin ta y'an giwa tazo, a unguwar G.r.a aka kaita gida ne d'an matsakaici mai part uku wanda yasha shuke-shuke na flowers sai k'amshi ke tashi. Nan dai dangi suka yi mata nasiha gwargwado had'e da lurar da ita muhimmancin hak'uri da biyayya, har wata na cewa duk da munsan abinda za mu fad'a duk malaman Ku sun riga mu. Da za su tafi ta ci kuka sosai har ta gode Allah inda take ta tunanin wace rayuwa za ta fad'a yanzu. Har k'arfe goma sha biyu bataji d'uriyar kowa ba, da hakan ta rage kayan jikin ta ta zazzagaya d'akin wanda ta jinjina ma mahaifinta da k'ok'arin da yayi duk da cewa yawanci siyayyar da kud'in da ta samu a musabak'a ne, ta ji dad'in ganin cewa har da keken d'inkin ta aka had'o mata dashi. Da hakan ta shiga ta watsa ruwa had'e da alwala ta yi karatun K'ur'an had'e da addu'o'in ta, ba ita ta kwanta ba sai wurin k'arfe d'ayan dare. ** 6angaren Alamein kuwa ba yanda su Imran basuyi ba kan siyen wani abu da zai shiga dashi gida yak'i, Salis ya nuna zai siya kuma ya hana. Dai-dai da rakiyar da akewa Ango d'akin Amarya cewa yayi ya hutar dasu, hakan ya fice ya bar su nan da mamaki fal a ransu. Da shigar shi gidan ko ta kan Amarya bai bi ba yayi part d'in shi, kayan jikin shi ya rage yayi wanka duk da bak'ar yunwar da yake ji hakan ya dunk'ula ya kwanta don rabon shi da abinci tun goma na safe. ** Kiran asubar farko ta tashi daga baccin, sallah ta fara gabatar wa sannan ta zauna zaman lazimi wanda bata tashi daga gurin ba sai bakwai na safe. Carpet d'in sallar ta ninke sannan ta d'an kimtsa d'akin, k'ullewar da cikin ta yayi ne ta tuna rabon ta da abinci tun la'asar d'in jiya. Bugun k'ofar da ta jine yasa ta saka hijab d'inta ta fito falon, kayan abinci ta gani jere a dinning table d'in. Gate ta nufa inda take jin k'arar ta bud'e k'ofa Sagiru k'anen Salmat ta gani da kula had'e da babban jug. Gayar da ita ya fara yi sannan ya mik'a mata kayan had'e da juyawa zai koma. "Kashigo mana daga ciki". "Aah zan ko ma islamiya ne ko yanzu break muka fito Mama ta aiko ni". "To mu shiga in baka kud'in mashin ko?". "Mama fa ta bani, ga ma mai mashin nan na tsaida waje zai ko ma dani". "Duk dai salon kar ka shigo ne, to ya yi ka gaida su na gode, ka gaya wa Salmat ina dubin ta". Da hakan ya wuce ta rufe k'ofar ta juya zuwan falon, abinda taci karo dashi ne ya saka ta razana wanda saura k'iris jug d'in yafad'i daga hannun ta.
Tana doso falon karaf idon su suka had'e yana mai aika mata da mugun sak'on harara tamkar fararen idon shi su fad'o k'asa. Gaban ta ne ya yi mugun fad'uwa had'e da razana, ba k'aramin k'ok'ari ta yiba gurin rik'e kayan da ke hannun ta har za ta ratsa shi ta wuce part d'in ta komai ta tuna ta durk'usa har k'asa ta gaida shi, ba tare da ta jira zai amsa ba ta wuce kawai. Mamaki ne fal a ranshi sai kuma d'imbin haushi dake cunkushe da zuciyar shi na ganin ce wa ga abinci Mum ta aiko masu tun d'azu amma don rainin hankali ta kira gidan su akawo mata abinci. Wata zuciyar ke yimai tuni kan cewa ka gaya mata an kawo abinci? Ko kuma jiya da ka yi kwanciyar ka ka yi tunanin me za taci?.
.
Hannu ya bud'a alamar ba ruwan shi ko a jikin shi. Abin sai damun shi yake k'ara yi yanda ya ga wannan mitsitsiyar yarinya wai itace matar shi, a tunanin shi ma ko sa'ar Saudat k'anwar shi bata yi ba aiko k'auye an rage wannan bala'in. Hakan dai ya zauna saman dinning table ya d'an tsakuri abincin kad'an saboda tun ranar da maganar ta 6ullo bai k'ara saka wani abincin kirki a bakin shi ba, har wata rama ya yi sai tsawon da manyan ido. ** 6angaren Zajlah kuwa ba k'aramin tashin hankali ta shiga ba na mugun kallon da ya bita dashi, tun jiya take ta nazari ko za ta kamo makamar auren amma kash data had'a zaren zai tsinke. Saboda tun tashin ta ko a tarihi bata ta6a ganin angon da ya shigo gida daren amarcin sa bai waiwayi Amarya ba sai a kanta. Yanzun take d'ora abubuwa akan mizanin awo ko za ta samu wanne zai rinjayi wani, sai dai abin sai k'ok'arin gagarar ta yake yi. Ba komai bane wannan sai zuwan Mum gidan su da kuma zuwan su Imran, sai dai a tunanin ta mizanin awon ta zaifi rinjaye akan zuwan Mum. Ba akan komai ta karkata can ba sai ganin babu tausayi ko kad'an a k'wayar idon angon barrantana shi So ya samu mazauni ko da kad'an ne, kenan hakan na nufin Mum ce mai auren sanadiyyar gajeren taimakon da tayi mata, inko hakan ne wani taimako ya kusa zama masifa domin dai ita wannan bai dad'a ta da komai ba sai tarin k'uncin rayuwa, in ko hakan ne sam babu adalci a cikin wannan lamarin da sake ashe ranar walima k'anwar shi tadinga so ka mata magana, wanda a wancan lokacin har laifin Salmat ta so hangowa na mayar da martani da ta yi. Tabb lallai ko akwai aiki sabo wankan jego da ruwan fridge. K'arar da cikin ta ya yi ne ta dawo daga duniyar da ta lula, kular ta bud'e taga waina da miya ce sai kuma kunun tsamiya cikin jug. Sanin cewa ba ta iya canye ta ya sa ta dake ta fito daga d'akin, kitchen ta nufa ta d'auko plate da cup har ta dawo d'aki bata ganshi ba. Abinci ta ci sai da ta yi k'at sannan ta shiga ta yi wanka ta kimtsa had'e da k'ara kimtsa d'akin na ta. ** 04:30pm Sai hada-hadar shiri ake yi domin y'ar liyafar da Mum ta shirya da za'ayi a gidan ta nan cikin G.r.a d'in wacce za'a yi Mata zalla. Yusrah ta kira ta aike ta takaiwa Zajlah kayan da za ta saka. Duk k'awayen ta da dangi na kusa ko wa ya zo har da iyaye sun hallara gidan Mum. Wata dakakkiyar shadda kalar purple Mum ta aiko mata sai wani k'aton gyale mai kalar ash da takalman ta ash, Salmat ce mai take mata baya har zuwa masaukin da aka yi mata. Mum Faty & Jegal fan's su ne na farko da isowa gurin liyafa, su Bizzy, Yagani, Zainab, Sharubutu, Maryam, Mmn Eman, Hindatu sune kan gaba-gaba, Musha karatu group su ma sun hallara inda Fatima, Aunty Baraka, Maryama, Ummietta wabi, Mrs Zannah ke ta rabon ido, Mumbarin Jabo ma sun iso Innah Habiba da Yasmeeny a sahun gaba. Zauren karatu Serdeeyer, Meenah, Batul A. Go I sune a gaba, sai Zumunci group had'e da Greatest women inda khairat, ummen Alamein, fati salihu, Jamila sahabi suke jagorantar sauransu. Zahra B~B fan's duk ba'a barsu baya ba, Ashnur, Hauwa jidda, Anee fan's Anee, Ayusha, Zayyenab sun hallara su ma, sai kuma y'an Taskar Lubiee. Kallo ne ya ko ma k'ofar shigowa gurin sanadiyyar wasu Mata da suka doso gurin cikin ankon su na materials iri d'aya wato blue sai gwaggwaro da takalman su kalar sky, cikin nutsuwa suke tafiya har suka doso gurin, Stylish, Autar Hjy, Feedoh Deedoh, Munayshat, Miss Hafcy, Queen Miemie sai kuma Miemi Bee, Fulani ced'iya, Hauwa damary, Mrs Umar su ne suka fara ne mawa manyan su gurin zama sannan suka zauna, ba kowa bane wad'annan face Nagarta masu Nagartattar zuciya duk inda suka gilma kallon su ake yi tamkar wasu taurari. Da hakan akaci liyafa cikin farin ciki da walwala abin sai son barka.
.
Bayan an watse daga liyafar ne Mum ta tsaida ta gidan ita da Salmat a ce war ta su bari mutane su watse lokacin an gama gaisawa tasa direba ya maida su, duk da ba wani nisa ne dasu ba. Ad'an zaman da ta yi na awanni ne ta fahimci tsantsar son da Mum ke yi mata da kuma Yusrah wacce ta fahimci d'iyar k'anen Baban shi ce, sa6anin Saudat dake bin su da muguwar harara. Zuwa bayan isha'i ne Dad ya shigo gida, bayan Mum ta yi mai barka da dawowa ne take gaya mai cewa, "na fa tsayar da matar Son don ku gaisa". "Ai da kin bar ta ta wuce ba sai mun gaisa ba, tunda ke da kika k'ulla abin kin ganta kuma ta gan ki. Wai ma kina hankalce da yanda kika lalatamin rayuwar yaro?". "Haba Dadyn Alamein ban fahimce ka ba, me ya ka wo wannan maganar?, me yasa abu baya wuce wa a gurin ka?".
.
"Ba wai baya wuce wa bane, rai na ke 6aci in har na dubi yanda Son ya koma yanzu, walwala, farin ciki, nishad'i duk sun kau a rayuwar shi har wata uban rama ya yi duk ya zabge tamkar wanda ya kwanta ciwo". Murmushi ta yi irin na su na manya had'e da furta "Adalilin gatan da nayiwa Son in har muna raye za kaji dad'in abin, kai dai ka rik'a d'ora shi akan turba ta k'warai had'e da lurar dashi wasu abubuwan". Tana kaiwa k'arshen maganar ta fito zuwa falo ta janyo Zajlah sai falon Dad. Har k'asa ta durk'usa ta gaida shi cikin nutsuwa da girmama wa, har ga Allah yarinyar ta burge shi sosai, sai dai matsalar d'aya ce da Son baya son ta. Saboda shi fa duk abinda zai yi sanadiyyar farin cikin yaran shi yake yin shi, kuma in ba su son abu har ga Allah zai iya yafe abin nan duk son da yake yimai. Mum ce ta ta6o shi alamar yayi magana ya sanya wa auren albarka, hakan ya yi gyaran murya suka k'ara gaisawa ya sanya mata albarka had'e da fatar zaman lafiya. Da za ta wuce dubu goma ya ba ta, sai dai k'in kar6a tayi sai da Mum ta kar6ar mata. Mum kuma turarukka had'e da humra y'ar asali ta Maiduguri ta had'a mata, har za su wuce take tambayar ta ina wayar ta halan? Amsa ta ba ta kan ce wa wayar na cikin kayan lefen ta ko bud'a ta bata yi ba. "In kinje gida ki had'a wayar mana tunda can su Maman Sagiru sun hana kiyi amfani da ita, ko ba kyaso ki gaisa da k'awaye da kuma ni Mum d'in ki?". Murmushi ta yi ta soke kai, karaf Yusrah ta ce' "Mum ta bari gobe zan zo in had'a mata". "To anji sarkin iya yi", cewar Mum. Da hakan direba ya kai ta gida inda ta so Salmat ta shigo ta nuna mata ce wa dare ya yi, kuma ta san unguwar ta su sai a slow, amma za tazo ranar Alhamis ita da k'awayen su na makaranta. Warmers d'in da Mum ta ba ta ta d'auka ta shiga gida had'e da sauran kayan ta ita ko Salmat direba ya wuce da ita gida. ** Bayan Zajlah ta shiga gidan ne ta ajiye kayan abinci a falon, bedroom d'inta ta wuce, saboda tsabar gajiya tu6ewa tayi ta fad'a toilet ta yi wanka. Kayan ta na lefe ta bud'e wanda bata ma san ya suke ba, akwatin k'ana nan kaya ta bud'e ta samu wata night gown mai d'an girma ta saka, hijab k'arami ta d'ora sannan ta fice zuwa falon, plate ta d'auko kitchen ta d'ibi abincin ta koma d'akin ta. Bayan ta gama ne ta je kitchen ta wanke abinda tayi amfani dasu sannan ta koma d'akin ta, alwala ta yo ta shimfid'a carpet ta gabatar da shafa'i da wutri ta yi lazimi sannan ta kwanta. Tabbas ta dad'e tana tsara ma kanta irin rayuwar da za tayi ta farin ciki a gidan auren ta, da kuma kyautata wa duk wanda ta aura saboda samun lada a k'ark'ashin shi, sai dai kash tana ganin da wuya hakan ta kasance a yanda take ganin wannan auren. Gashi a tsarin ta tana son namiji mai tsayi kuma gashi ta samu sai dai a banza don bata gaban shi "ya Allah kakka d'ora min son wannan bawan Allah a zuciya ta". *** 6angaren Alamein kuwa har akaci aka sud'e bai lek'a gidan su ba saboda dama ba mutum ne maison shiga gurin harakar mata ba. Yana shigowa gidan ya ci abinci daya gani a dinning table sannan ya shiga part d'in shi, wanka ya yi ya nemi guri ya kwanta da tunane-tunane fal a ranshi har bacci ya yi awon gaba dashi.
.
WASHE GARI
Bayan ta gabatar da sallah ne da abubuwan da suka dace tayi wanka ta shirya cikin atamfar ta kalar lemon green fitted. Bakin gado ta zauna ta zabga uban tagumi komi ya cunkushe mata, sai tunani take yi dama haka rayuwar auren take ko kuma nata ne yazo a hakan? Duk iya nazarin ta ta rasa gane wane matsayi take dashi a gurin Angon. Jin hayaniyar mutane a falon ne ya sa ta janyo gyalen ta ta yafa ta fita, saboda tana tunanin Yusrah ce kamar yanda ta yi alkawari za tazo jiya. Tana fita karaf idon ta cikin nashi yana dariya k'annen shi sun saka shi tsakiya. Gabanta ne ya yi mugun fad'uwa saboda annurin fuskar shi daya kau cikin second uku. "Laah Brother kace Amarya bata ta shi ba, ga shi har ta tsantsara kwalliya", da saurin Yusrah ta taro ta had'e da zaunar da ita, d'an zamewa ta yi k'asa ta gayar dashi, ya amsa ba yabo ba fallasa saboda k'in amsawar zai sa Yusrah ta dame shi. Breakfast ta had'a mata da kanta tana tarairayar ta sa6anin Saudat dake binta da mugun kallo. Zumbur ya mik'e ya wuce part d'in shi saboda bazai iya kallon kayan haushi ba. Bayan ta gama karyawa ne suka shiga hirar duniya ita da Yusrah har tana tambayar ta matsayin karatun ta. "Gaskiya iya primary school kawai nayi saboda na fi son islamiya akan bokon". "No wonder! Biri ya yi kama da mutum", cewar Saudat. Harara Yusrah ta dinga zabga mata had'e da yi mata alamar gamon ki da Mum, sanin za su iya komawa ta gayawa Mum ya sa ta yi shiru, wayar ta ta fitar tana latse-latse. Hakan ya tuna ma Yusrah maganar had'a ma Zajlah wayar ta, nan ta gaya mata taje ta d'auko wayar ta kawo mata. "Ina fatar kin saka charge". "Eh na saka tun jiya", ta ba ta amsa. Wayar ce ta had'a mata har da layi biyu cikin kwalin wayar da credit, Mtn da Etisalat.
.
Ba number kowa a wayar hakan ya sa Yusrah ta saka mata ta ta number data Mum, ko kad'an batayi gigin saka mata ta Saudat ba sai kuma number Alamein da ta yi mata saving da (HUBBY), lambar ta shiga kira sau biyu tana tsinkewa sai ana ukun kamar bazai d'aga sai kuma ya d'aga. "Brother number Madam kenan". Bata jira me zai ce ba ta tsinke wayar, wayar ya bi da kallo had'e da furta "lallai yarinyar nan ta samu sake, don ma ta samu shekaranjia Mum ta ce nakar6i lambar ta mu rik'a zumunci shi ne za ta wani zak'ewa da baiwa wata lamba ta", za mu had'u ne". Bayan ta nu na mata duk abinda ya kama ta tasani take gaya mata su shiga kitchen suyi girki tunda an kawo komai na amfani a store.
.
Suna cikin girkin ne Alamein ya fito daga part d'in shi ya yi waje sai ga shi ya dawo falon had'e da Imran da Salis, sai wani dake aiki company dayace zai zo taya shi murna. Falon suka zube dukan su inda Saudat ta gayar dasu ta cigaba da latsar wayar ta. A tare suka fito daga kitchen d'in ita da Yusrah, gyalen ta ta k'ara janyowa ta rufe jikin ta saboda wannan shi ne karo na farko da Maza za su ganta ba hijab a jikin ta, har k'asa ta durk'usa ta gaida su had'e da yi masu sannu da zuwa, nan suka amsa cikin sakin fuska da walwala. Part d'in shi Yusrah ta wuce ta kawo masu ruwa da lemu, itako Zajlah ta koma kitchen domin k'arashe aikin. "Tabbb da sallamo wata k'anshin girki yadoki hanci na sannan a kawo min ruwa da lemu, kawai abari in na yi lunch na danne da ruwan", Salis kenan sarkin barkwanci. Hakan suka kwashi dariya duka falon sa6anin Alamein dake wani cin magani. Abincin suka jera ma su Imran a falon bayan sun gama, suka wuce da na su part d'in Zajlah saboda ta gayawa Yusrah ba za ta iya cin abinci gaban Mazan ba saboda bata saba ba. Ba k'aramin dad'i Alamein ya ji ba da suka wuce part d'in ta, saboda a tunanin shi in har zai cigaba da ganin ta falon zuciyar shi za ta iya tashi ya kasa cin abincin, don ko yanzu zai ci ne saboda tabbacin ba ita tayi girkin ba Yusrah ce. Bayan sun gama cin abinci ne har da santin su suka tashi za su wuce, su Zajlah ne suka fito domin suyi sai an jima nan sukayi godiya suka ba ta kud'i wanda ta kasa kar6a saida Yusrah ta kar6a suka yi masu fatan alkhairi da d'orewar zaman lafiya. Saudat ce ta ce su sauke ta gida ita ta gaji da zaman gidan, shi ma Alamein makulin mota ya d'auko domin suje tare tunda sun ce za su biya su gaida Dad. "Ai kai mun yanke ma fita har company sai nan da wata d'aya", inji Imran. "Saboda ga mai laifi an yanke mai hukuncin gidan yari ba", cewar Alamein. Dariya sukayi sosai sannan suka fice daga gidan har Saudat d'in, akabar Yusrah da tace sai marece za ta koma, wanda hakan ba k'aramin dad'i yayiwa Zajlah ba.
,
Hira suka shiga yi sosai ita da Yusrah, saboda gaskiya yarinyar ta yi mata ba tada girman kai irin na masu kud'i, kuma ga alama za ta girme ta kad'an. Tunani take tayi a ranta kan ta tambayi Yusrah asalin ya auren su yake ko kuma ta k'yale ta, saboda gaskiya har ga Allah abin na damun ta sosai. Bayan sun yi sallar La'asar ne suka shiga kitchen domin girkin dare, duk da tana tunanin mawuyacin abu ne yaci abincin ta don tana tunanin k'ila ko d'azun bai ci ba. "Me ya kama ta mu girka abincin dare?". Maganar ce ta dawo da ita daga hayyacin ta, ta kai duban ta zuwa gare ta ta sauke ajiyar zuciya. "Me kike ganin yayan ku ya fi ra'ayi da dare d'in?, duk da ban tunanin in ya shigo zai ci abincin". "Ko da wasa kar kiyi tunanin tunda ba shi yagan ki yace yana So ba za ki rage shi da wani abu na kyautata wa, a tunani na ta hakan ne za ki janyo hankalin shi zuwa gare ki". "Nasan ce wa watarana Brother zai yi alfahari da auren ki ADALILIN GATAN da Mum tayi mai. Saboda har kullum in dai namiji zai jure ya auri Mace ma'abuciyar ilmin addini to tabbas babu shi babu dana sani, yanda tarbiyar yara ke ta6ar6arewa yanzu ka samu mai d'ora yaran ka akan hanya ma abin alfahari ne". "Amma yanzu abinda mutane basu gane wa musamman Maza har kullum burin su shi ne su auri Mace wayayya kuma y'ar boko, basu san ce

Please Login or Register in order to submit comment