Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma basu zauna ba tun faruwar abin kullum suna asibiti. "Lallai kun zama abokanen arzik'i, samun irin ku a wannan zamanin sai an tona, Allah ya yi maku albarka yasa ka maku da khairan", tana maganar tana hawaye. "Amen Mum, amma kakki damu wannan ba komai bane yi wa kaine, kuma Dad tamkar uba yake gare mu duk abinda muka yi mai ba fad'uwa ce a gare mu ba, fatar mu kawai a gare shi addu'ar samun sauk'i". Da hakan suka fice daga gidan suna masu tausaya wa zuwa ga Dad. Zajlah ta so ta kwana gidan amma Mum ta nuna mata tunda sun dawo ta tashi ta koma gidan ta had'e da yi mata godiyar d'awainiya da kuma kulawa da ta basuwa akan ciwon Dad, hakan dai ta had'a kayan ta ta wuce don ba hakan taso ba musamman da taga Yusrah ta dawo gidan da zama gaba d'ai. Hakan dai ta kakka6e y'ar k'urar da gidan ya yi sannan ta yi wanka ta kwanta, wata zuciya ke ce mata biki kyauta ba Zajlah ke fa sai da kika gyara inda za ki kwanciya sannan kika kwanta ya kama ta ki gyara wa bawan Allah na shi gurin, wata ke ce mata sassaucin da fa kika samu rashin lafiyar Dad ce amma yanzu in kika shiga sabgar shi zai iya wulak'anta ki, wannan shawarar ta fi duba wa ya sa ta yi kwanciyar ta. * * * "Son ka ga har 10:00pm ta yi kuma Dad ya samu bacci ka tashi kaje gida ka kwanta". "Mum kibar ni na kwana anan, ko na je gidan ba bacci zan samu yi ba". "Bazai yuyu ba Son ko matar ka d'azu na kora ta gida saboda haka kai ma ka fice gobe ka dawo". Ba don ran shi ya so ba ya fice daga gidan wanda ko sai da safe bai yiwa Mum ba, shi ala dole an 6ata mai rai. Ko da ya shiga gidan tsab komai ta gyara sa6anin d'akin shi dake fama da k'ura birjit, ganin cewa bazai iya kwana d'akin ba haka kuma bazai iya ta6a k'urar ba ya sa ya d'auko blanket ya dawo falo ya yi shimfid'a ya kwanta, da tunane-tunane fal a ranshi 6arawo ya yi gaba dashi. ** ** Washe gari Kiran sallar farko ya tayar da ita daga baccin duk da bata cikin tsalki, wannan sabo ne duk baccin da take yi da ankira sallah za ta tashi, alwala ta yi ta d'auko littafin ta na azkar tana karanta wa, sai wurin k'arfe 07:00am ta fito domin samun abinda za ta dafa taci. Turus ta yi a falon ganin shimfid'ar shi alamar nan ya kwana, ji ta yi ba dad'i a ranta ko ba komai ya ci ta kyautata mai matsayin shi na mijin ta kodon gudun fad'awa fushin ubangiji, saboda tasan hakk'ok'in miji akan matar shi kuma tasan na mata akan mijin ta. A fili ta furta "insha Allah Alamein daga yau zan kula da hakk'in ka a kaina ko da ba zaka kula da nawa ba". Kitchen ta fasa shiga ta yi d'akin shi duk da gaban ta dake dukan uku-uku, ga mamakin ta tana tura k'ofar ta ji ta a bud'e turus ta yi ganin yanda d'akin ya yi uwar k'ura. Ita da na ta ta kasa kwana cikin shi ina ta ga na shi da tun auren su bai ga gyara ba, karfa ta mayar da mijin ta KAZAMIN MIJI (SIS JABO), duk tsaftar namiji ba kowa ne daga cikin maza zai iya gyaran d'akin shi ba saboda haka za ta tashi tsaye a wannan 6angaren. Gyaran d'akin ta shiga yi sosai, sannan ta fad'a toilet kayan shi k'anana ta saka a wash machine ta wanke sannan ta wanke toilet d'in, kayan wanki ta had'a ta fito dasu ta kaiwa Baba maigadi akan cewa don Allah yasamu mai wanki da guga yaba shi ya wanke, "aiko yaro na sana'ar shi ce zan kai mai ya wanke". Godiya ta yi mai sannan ta koma gidan ta d'auki turarukan d'aki ta je d'akin shi ta fesa, kitchen ta wuce ta yi masu girki ta saka mai a kuloli ta kai dinning table, Baba maigadi ta kaiwa sannan ta ci na ta ta fad'a wanka. ** ** 6angaren Alamein kuwa daga masallaci ya rok'i liman a saka Baban shi a addu'a sannan ya fitar da kud'i ya bada a raba sadaka, daga nan gidan su ya wuce domin duba jikin Dad. ** ** K'arfe 11:00am ta kammala duka ayukkan gidan sannan ta fice zuwa gidan su Alamein, a gate suka had'u tana rik'e da kula a hannu kamar ta wuce komai ta tuna ta tsaya ta gaida shi, nan ya amsa ba yabo ba fallasa ta shige gidan shi ko ya fice zuwa gida.
.
Yana komawa gidan ya nufi dining table ya ci abinci kad'an duk da yana ganin yau ya ci dayawa akan tun fara ciwon Dad bai ta6a cin abinci irin yau ba, d'akin shi ya nufa domin ya yi wanka ya koma gidan su, yana tunkarar hanya k'amshi na tarbon shi har ya sadu da k'ofar, yana turawa ya yi turus yana kallon d'akin saboda yanda komai ya fito tsaf sai k'amshi dake tashi d'akin, saman gadon ya je ya kwanta yana ta tunane-tunane har bacci ya yi awon gaba dashi. ** ** Tana shiga gidan ta gaisa dasu ta bawa Mum Kular abincin da ta zo wa Dad dashi, "dama kenan jira kike yi gari ya waye ki fito tamkar wacce ke zaune saman k'aya", cewar Mum. Murmushi kawai ta yi saboda tana son zaman gidan musamman yanzu da Yusrah ke gidan saboda Allah ya had'a jinin su sosai. "D'auko kular muje kiga Dad jiki ya yi sauk'i akan jiya", masha Allah Mum Allah yak'ara sauk'i". Da hakan suka shiga d'akin ta ganshi ta yi mai ya jiki duk da ba iya kar6awa yake yi ba sai dai yayi alamar amsawa da kai. "Mum akwai zam-zam a gidan nan?". "Eh akwai Zajlah har galan d'aya da rabi". "Mum kawo rabin galan d'in muga". Bayan ta kawo ne Zajlah ta karanta (falak', Nas, Ikhlas) kowaccen su k'afa uku-uku sannan ta had'a da (Ayatul kursiyyu) had'e da wasu addu'o'i na yayewar lalura ta tofa. "Mum gasu nan ki rik'a bashi yana sha kuma ki rik'a shafe mai jikin shi dasu, insha Allah zansa a gayawa Ustaz Yusuf ko Ustaz Lukman su rik'a zuwa suna yimai addu'a, ba abinda addu'a ba za ta yaye ba sai in ba'a kai kuka gurin ubangiji ba, ubangiji Allah ya tashi kafad'un shi ya yaye lalura". Mum har da hawayen ta na jin dad'in kasancewar Zajlah a cikin zuri'ar ta, "tun farkon had'uwa ta dake jiki na ke bani ke alkhairi ce a gare mu". "Mum ba komai mudai dage da addu'a", da hakan ta fice daga d'akin ta koma falo gurin su Yusrah. * * * * Sai kiran azzahar sannan Alamein ya tashi daga bacci wanka ya fad'a ya kimtsa ya yi masallaci saga can ya wuce gidan su. Bayan an gaisa ne Mum take gaya mai abinda Zajlah ta yi da kuma shawarar da ta basuwa na kiran d'aya daga cikin Malaman su don yiwa Dad addu'a. Baiyi k'asa a gwuywa ba ya yi makarantar tasu Zajlah, da Ustaz Yusuf ya ci karo suka yi magana ya bashi tabbacin zai rik'a zuwa da safe Ustaz Lukman ko bayan isha'i. Godiya ya yi sosai had'e da d'auko kud'i ya bashi, nan ya nuna mai bazai kar6a ba sai dai gobe d'in in ya zo. ** ** Yau sati biyu kenan ana kula da yiwa Dad addu'a had'e da mayar da ruwan zam-zam da Zajlah ta yi mai addu'a ruwan sha da kuma shafe mai jiki, jiki kam Alhmdulillah don yana magana yanzu kuma har yana iya takowa da k'afa daga d'akin shi zuwa gate abin sai son barka. ** * ** D'an zaman da suka yi da Yusrah ya sa ta k'ara sanin kan waya sosai don har whatsap ta bud'e mata kuma ta saka ta group na gyaran jiki dana kwalliya, sai kuma group d'in musha karatu saboda gwada karatun littattafan soyayya, inda take samun littafai har ta rasa na za6a ta karanta. Tana bud'e data ta shiga whatsap ganin cewa ba'a turo AL'ADUN WASU (SIS BATUL) ba ya sa ta rufe data ta hau d'inkin ta da Yusrah ta kawo kusan turmi takwas. * * * Soyayya mai tsafta da kulawar juna ake bugawa tsakanin Salmat da Salis tamkar su had'e juna saboda tarairaya.

* *

Inda kuma 6angaren Yusrah da Imran soyayya ta k'ullu sanadiyyar zaman da ta yi a gidan Mum shiko Imran yana saman hanyar duba jikin Dad kusan kullum. * * * 6angaren Zajlah kuwa kullum sai ta gyarawa Alamein d'akin shi sannan in ta yi girki za ta ajiye kowanne kuma yana ci, kamar yanda inta gaida shi yake amsa mata cikin sakin fuska sai dai bayan hakan babu wata alak'a tsakanin su. Kamar kullum yau ma ta gama had'a breakfast ta d'auko ta kawo dining ta tarar dashi zaune ya had'a kai da gwuywa, ga alama yana cikin damuwa, bayan ta ajiye ne ta koma kitchen ta d'auki na ta kayan abincin ta yi falon ta. Kasa cin abincin ta yi sai juya cokali da take yi a plate duk jinta take yi ba dad'i, waya ta janyo ta kira Salmat suka gaisa sannan ta kora mata abinda ke damun ta. "Yanzu ne ya dace ki nutsi ku ajiye duk wani shirme da kuka yi a baya saboda mijin ki na cikin tsananin neman taimako da mai bashi shawarwari, saboda haka don Allah ki rik'a bashi kulawa ki ajiye komai a gefe". "Tabbbb Salmat yau ke da kan ki ke furta hakan?, ke fa kika ce in gyara mai zama amma yanzu ke ce mai yi mai yak'i". "Alamein d'in ne ya zamo abin tausayi shi da ubanshi, har dai yanayin da suke fuskanta yanzu dole a tausaya masu, amma kar kiyi saurin bada gari daga shawarwari ki zurma, don nasan ki da raunin zuciya sai anja aji", cikin dariya da zolaya take maganar. "Ke dai kika sani, Allah ya shirye ki", daga hakan ta kashe wayar ta bita da kallo tana nazarin kalaman Salmat. "Lallai ni shaida ce ciwon Dad ya sa Alamein ya sauya, saboda daga ranar da abin ya faru kawo yanzu babu hantara ko kallon raini, ko don yana ta lafiyar ubanshi ce bansani ba". A fili take ta maganganun ta ita kad'ai inda dai ta d'an ci abincin kad'an ta tashi ta mayar da kayan kitchen, turus ta yi a falo ganin yanda ta barshi hakan ta dawo ta tarar da shi tamkar ko yatsan shi bai motsa ba, kayan ta je ta ajiye sannan ta dawo kanshi ta yi tsaye saboda rashin takamemen ta ina za ta fara, don gaskiya har yanzu tsorace take ga kutsa kanta cikin lamurran shi. A duniya tak'i jinin ganin babban mutum cikin damuwa duk sai taji ta kasa nutsuwa a ranta abin yai ta damun ta, hannu ta kai za ta ta6o shi ko me ta tuna ta fasa oho, zaune ta yi nesa dashi kad'an saman kujerar da yake zaune, gyaran murya ta yi amma kuma a banza ko motsi bai yi ba. Tsoro ta ji sosai na ko ya suma ne a hakan, cikin sauri ta kai hannun ta saman kafad'ar shi ta girgiza shi kad'an ya zabura cikin razana, yana tayar da kan shi idon su suka had'e guri d'aya nan take bugun zuciyar su ya halba lokaci d'aya.
.
Ganin ya k'i d'auke idon shi akan tane ya sa ta yi saurin kauda na ta idon, saboda ba zata iya jurar kallon fararen idon shi da suka rine suka koma ja ba kan tsananin damuwa tamkar wanda ya ci kuka ya k'oshi, yatsun ta ta dinga wasa dasu kanta na nok'e k'asa. Hannu ya kai ya tallafo hab'ar ta had'e da yi mata alama da d'ayan hannun na me aka yi?. "Na ga tun d'azu baka ci abinci bane shiyasa", "Ayyah kar ki damu zanci yanzu, nagode da kulawa". Wata zuciya ke ce mai me zai hana ka gaya mata damuwar ka tunda ita ta kasa jure taka damuwar har tazo ta yi ma magana, d'ayar ke ce mai kakka tsaya gaya mata komai, me za ta iya yi akai? Salon ka ja ma kanka raini daga gurin ta tunda wuri haka. Tamkar guguwa haka ya ta shi ya nufi d'akin shi ya barta nan zaune sake da baki, "tabbas mai hali ba ya canja halin shi, irin hakan nake gudu shiyasa ba nason sa kaina cikin lamurran shi, ko ma miye Allah ya yaye", a fili take maganar ta ita kad'ai, da hakan ta wuce na ta d'akin. * * * Zuwa la'asar ne ta gama ayukkan ta ta ji tana ra'ayin shiga tak'ara duba jikin Dad, har ta kimtsa ta fito ko motsin Alamein bata ji ba hakan ya sa ta ficewar ta. Tana isa gidan ta gayar da Mum haka ma Dad don jiki ya yi kyau sosai yana magana kuma yana d'an fita sai dai tafiya ba mai nisa ba. Abu d'aya ya yi mata tsaye a rai ganin yanda kwana ukun da bata zo gidan ba Mum ta kod'e ta jeme duk ta fita hayyacin ta tamkar wacce ta yi jinya. "Mum hala ciwo kika yi bansani ba?". "Wallahi a'ah Zajlah jarabobin rayuwa ce kawai da suka yi yawa". "Mum indai ciwon Dad ne ai Alhamdulillah don jiki ya yi dama sosai, sai dai a k'ara dagewa da Addu'a". "Tabbas a rayuwa anason bawa ya yawaita addu'ar Allah ya kare shi da miyagun k'addarori, to su ne suka hau kan Daddyn ku". "Tun lokacin da yafara wannan ciwon abubuwa ke ta kunno kai, wanda masu bashi da way'anda k'addara ta rutsa da dukiyar su suke ta kunnowa neman abar su". "To amma wannan ta su mai sauk'i ce akan wacce ta kunno kwana biyun nan, a rayuwa ana so mutum komai dukiyar shi yarik'a sayen kadara yana ajiyewa saboda ranar da lalura ta taso zai iya fitarwa ya saida yayi lalurar shi ba tare da wani ya ji shi ba". Zajlah dai zurum ta yi tana sauraren Mum, saboda har yanzu bata fahimci ina ta saka ma gaba ba, a tunanin ta irin dukiya ta Dad bazai ma yuyu ba ace cikin kashi d'ari an ta6a ashirin ba, amma dai bari ta saurare ta har takai k'arshe.

* * *
ASALIN MU "Mu haifaffin garin Jega ne, ni da Dad d'in ku auren zumunci aka yi mana sanadiyyar mahaifin shi da mahaifi na uwa d'aya uba d'aya, inda tun muna yara iyayen su suka yi hatsarin mota suka rasu, hakan ya yi silar dawowar su gidan mu da zama shi da k'anen shi Muttak'a wato Abban Yusrah". "Hakan Baba na ya rik'a su amana had'e da basu tarbiya gwargwado duk da ba wani hali ne dashi sosai ba, ko da suka dawo gidan da zama dama mahaifiya ta ta rasu tun gurin haihuwa ta sai wata mata da Baba ya auro". "Daga baya soyayya ta k'ullu tsakani na da Kabiru wato Daddyn ku har muka yi aure, shekarar mu kusan bakwai da aure Allah bai bamu haihuwa ba sai daga baya aka samu cikin Son wanda haihuwar shi ta sa Kabiru ya d'auki son duniya ya d'ora mai kuma nan yaci sunan mahaifin shi wato Aminu. Haihuwar shi da wata bakwai ne Allah ya yiwa mahaifina Baba Sani rasuwa inda matar shi Aisha ta gama wanka ta k'ara gaba sanadiyyar bata haihu dashi ba, shi ko Muttak'a ya auro Balkisu mamar su Yusrah". "Hakan zama ya kasance tsakanin mu iya mu saboda bamu da wasu dangi na kusa, Son na da shekara biyar na haifi Saudat lokacin ne Allah ya k'ara bud'awa Dad hanyar samu yana bawa yaran shi kulawa da kuma soyayya wacce ko ni kaina na ta6a su to zan had'u da fushin shi ranar". Lokacin ne kuma arzik'in shi ya k'aru ta hanyar wani babban aminin shi mai kud'i wato Alh Ibrahim wanda yake shahararren mai kud'i sosai, kusan lokaci guda akayi auren mu da nashi, Allah cikin ikon shi matar shi ta samu ciki gurin haihuwa ta rasu ita da abinda ta haifa bak'in cikin hakan ya sa kaf ya had'a dukiyar shi ya ba Dad ajiya, saboda gaskiya babu wanda yasan dangin shi Sana'a ce kawai ta had'a su ko ga hira bai ta6a cewa ga dangin shi ba, don ko neman auren gidan mu aka shige mai gaba, wancan lokacin kurmi ya yi shirin tafiya da zai wuce ne Dad d'inku ke ce mai yaushe zai dawo? Gaya mai ya yi babu rana, sannan ya ce mai in Allah ya yi mai rasuwa ya bashi dukiyar shi kaf. Daga hakan Mum ta yi shiru hawaye na mata zuba cikin k'unar rai.
.
Zajlah ce ta ni sa had'e da rarrashin Mum ta d'auko mata ruwa tasha sannan ta cigaba kamar haka. "Da hakan ya wuce kurmi wanda bayan kud'in abinci da suturar jikin shi bai fita da komai ba dai-dai da gidan shi sai da ya saida sannan ya bar garin nan. Dad ya so ta6a kasuwanci da kud'in da Alh Ibrahim ya bashi ajiya na nuna mai hakan bai dace ba sannan yabar kud'in ma'ajiyar su ya cigaba da juya nashi gwargwado Allah ya bud'a mai hanyar samu ba laifi. Bayan shekara hud'u da tafiyar shi ne mummunan sak'o ya risk'e mu cewa Allah ya yi mai rasuwa sanadiyyar gobara data tashi gidan da suke zaune, wanda wancan lokacin Dad yaso share maganar sai da na takura shi kan cewa yashiga mota yaje kurmi don tabbatar da zancen, hakan ya sa ya shirya ya je wanda bai dawo ba sai da tabbacin duk wanda ke gidan bai fita ba sanadiyyar wutar dare data tashi ba zato ba tsammani. Bayan rasuwar shi da wata uku ne Dad ke maganar dukiyar margyayin wanda sai da aka nemi malamai had'e da takarda daya rubuta na tabbacin tunda baida kowa in ya rasu Dad ya d'auki kud'in, hakan ya sa kud'i suka zamo nashi. Da su ne ya bud'e company da sauran abubuwan shi na kasuwanci."

* * *

"Dad ba mutum ne mai son siyen kadarori ba, wanda kullum ina mai bashi shawara kan siyen filaye da kuma shaguna ya bada haya, maganar shi bata wuce yana da dukiyar da ba yaran shi ba har jikokin shi zasu ci su raga wani abu daga ciki". "To yanzu gashi karon farko k'addara ta sauka kan company, kud'in da aka aje account sune ake cirowa ana lalurorin yau da kullum, dai-dai da gida daga wannan da muke ciki sai naku babu ko da filin da za'ayi kiwon kaji a ciki, duk wannan ba shine tashin hankali ba sai tahowar labarin tabbacin Alh Ibrahim yana raye don Alh Taheer abokin Dad da akayi d'awainiyar asibiti dashi shi ya ganshi ra'ayul ayni a Abuja kuma ya bashi tabbacin yana nan tafe kwanan nan". (Ba Zajlah da ake ba labari ba ni kaina Jegal mai d'aukar rahoto ba k'aramar razana nayi ba, don sai da na zaga toilet, lolx). Cikin razana ta tayar da kai ta kalli Mum "yana raye fa? To ya akayi haka? Anya ko inda akace anyi gobarar nan yake?". "Tabbas an ganshi kuma shine, don har lambar Dad ya kar6a don ya kira su gaisa, sai dai ko da yakira ni na d'auka muka gaisa saboda Dad na wanka lokacin, bayani nayi mai kan cewa Dad na asibiti bai da lafiya, ba akan komai ba sai don gudun kar yakira Dad yasan da maganar yayi silar tashin ciwon shi farat d'aya a koma sabuwar jinya, to kinji babbar damuwa ta da kuma tashin hankalin mu ni da Son wanda muke neman mafita kamin abin yazo ga kunnen Dad". "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, hala Mum kud'in za su kai nawa?", cikin tsananin tashin hankali take maganar don jin take yi tamkar ita wannan musibar ta fad'awa. " kud'in wannan lokacin zasu kai million hamsin, kuma Son yace abinda ke cikin account ba zasu biya kud'in mutumen ba, sannan ba muda masaniya akan komai yanzu Zajlah har sai ya shigo garin nan munji daga gare shi". "Mum ina da shawara d'aya akai in har hakan zai yuyu, saboda a kammala kud'in mutumen kamin ya iso". "Zajlah ba muda wata mafita ta kud'i kuma babu wata kadara da zamu saida mu cika mai kud'in shi, shi ne abin dubawa". "Mum ko mu muke da kadara da zamu saka kasuwa a biya komai cikin kwanciyar hankali ba tare da kowa ya ji mu ba". "Ta wacce hanya Zajlah?. "Mum gidan mu za'a saka kasuwa a saida mu ko mu dawo nan gidan mu zauna d'ayan part d'in da ba kowa a ciki". * * * Maganganun ta ne yasa yaja birki ya tsaya don jin me za ta furta, abinda ta fad'a ne ya sa yaja ya yi turus, "me yasa duk iya tunanin mu ni da Mum bamu kawo hakan a zuwan mafita ba?, garin ya ya ta fi mu nazari da hangen nesa? Lallai tabbas ba girma ne hankali ba, ba shekaru ne tunani ba, dame yarinyar nan ke aiki cikin kwanyar ta?". Duk shi kad'ai ke yiwa kanshi wad'an nan tambayoyin sanadiyyar mafita da ya ji Zajlah ta samo wanda iya nazarin su basu kawo hakan ba. Mum ce ta janyo Zajlah ta rungume kan jin dad'i tana hawaye, sai albarka take saka mata wanda take jin tamkar ta maida ta ciki kan irin son da take yi mata da kulawa da dukkan damuwar ta. Suna hakan ne ya yi sallama ya fad'o falon, wanda daka kalleshi zaka hango walwala, farin ciki, annashuwa kwance saman fuskar shi, har k'asa ya durk'usa ya gaida Mum, cikin farin ciki ta amsa fuskar ta sake. "Sannu da zuwa", cikin sanyin muryar ta ta furta hakan sannan ta wuce zuwa d'akin Saudat da Mum ta gaya mata tana fama da zazza6i, kuma tana so ta basu guri su gana da junan su.
.
Bayan ficewar ta ne Mum ta kai duban ta zuwa ga Alamein had'e da furta "ka fara ganin irin alkhairin da nake hango ma a cikin zamantake warka da yarinyar nan? Wallahi na yi imani da Allah da wata ce ko siyar da gidan kace za kayi sai kunsha artabu da ita, in ma bata ce sai ka sake ta ba". "Wannan zamanin da ake ciki mun kawo ga6ar da yawancin y'an Mata basu cika yin aure saboda Allah ba, farko kana zuwa neman yarinya za kaji ana fad'in da wacce mota yazo? Daga hakan sai kaji iyaye na fad'in ai ko ki auri abinki ance yana da hankali da nutsuwa, nan ko nutsuwar kud'i ce ba nutsuwar Allah da Annabi ba". "Ina mai baka shawara daka rik'e yarinyar nan amana domin ta wuce k'ask'anci yanzu daga gare ka, ina sane da har yanzu babu wani cigaba a cikin rayuwar auren ku saboda bak'ar ak'idar da ka saka a zuciyar ka na k'yamatar talaka". Cikin razana da mamakin ina tasan irin zaman

Please Login or Register in order to submit comment