Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gefe, gaban ta ya zo ya gurfana had'e da rok'on ta gafarar abinda ya aika ta mata a baya.

Bata San lokacin da ta rik'o hannuwan shi ba alamar ya tashi sai da ta ji ya fad'o mata ragwaf saman jiki, yunk'urin janyewa ta yi had'e da furta "wash! Hannu na", hakan ta sa ya yi saurin zabura, da saurin ta ta koma saman kujera tana dariya had'e da yi mai gwalo.

Cup d'in ya rik'a sannan ya dawo kusa gare ta ya zauna, baki ya bud'e zai yi magana ta yimai alamar yasha tea d'in sannan su yi magana.
Hakan ya shanye tass ya ajiye sannan ya tattara dukan hankalin shi zuwa gare ta yana wasa da jelar gashin ta, "Zajlah plxxxx kice kina so na", cikin kasalalliyar murya ya furta hakan.

"Ai Kaine baka "So" na, amma ni tun farko ban ta6a jin k'iyayyar ka a rai na ba, sai dai kai da kake ji tamkar ka hasa wuta ka.......".
Bai bari ta k'arasa ba ya dafe mata baki da hannun shi, "ki yarda ni kaina ban ta6a jin k'iyayyar ki ba, sai dai rashin son kula mata da baya gaba na".

"To yanzu gaya min wane irin kalar so kake yi min".

"Ni ba son ki nake yi ba K'aunar kice da ta dabai baye ni take batun mayar dani wani zautacce, saboda K'auna ba ta ta6a canja wa, So kuma wataran zai iya canjawa".

Hira suka shiga sosai kowan nen su na nunawa juna irin yanda yake jin shi a ranshi, wanda ta kai tun suna saman kujera har suka koma saman gado (ni dai Jegal k'ofa na ja masu na fita, su Aunty Sis sunan Ku sorry Zajlah ta lula a duniyar ma'aura ta, kunsan ance tsakanin mata da miji sai Allah, lolx).

............

Kiran sallar magrib ya dawo dasu hayyacin su, inda Zajlah sai wata shagwa6a take mata zuba mai, wanka Alamein ya fad'a sai da ya fito sannan ya had'a mata ruwa ya taimaka mata ta yi wanka, ganin lokacin sallah ya kusa shigewa ya sa ya jasu jam'i suka gabatar da farali suka d'ora da nafila sannan suka jero addu'o'i, basu tashi daga gurin ba sai da suka gabatar da isha sannan Zajlah ta ja jiki ta koma saman gado ta k'udun-dune, gadon shi ma ya hau yana tsokanar ta had'e da saka mata albarka.

Daka kalli fuskar shi za Kasan cewa yana cikin farin ciki, walwala had'e da nishad'i, "ya dace in fita in sawo maki kazar ki ta amarci amma kuma duk kin d'ibge min jiki".

Ido ta gwalo waje alamar mamakin maganar da ya furta, kashe mata ido d'aya ya yi sannan ya furta "ko k'arya nake yi?, ni da ke jinya ko k'arfin jiki bani da".

Kunya ce gaba d'aya ta lallu6e ta dole ta nok'e kan ta had'e da k'udun-dune wa cikin blanket, hakan ya sa ya zira jalabiyar shi ya zari key d'in mota ya fice daga gidan.

Fitar shi ya sa ta yaye bargon da ta lullu6a dashi ta ja jiki sai toilet, jikin ta ta k'ara gasawa sannan ta fad'a kitchen, indomie ce ta dafa masu da ta ji kifin gwangwani, tana juyewa a kula ta ji motsin shigowar shi, a falo suka had'u ta d'auko kular abincin za ta kai dining, shi ko yana rik'e da ledoji a hannun shi, da Sauri ya saki ledojin da ke hannun shi ya taryo ta, kular ya kar6a sannan ya rik'o hannun ta suka k'arasa falon, sai da ya ajiye ta saman kujera sannan ya ajiye kular abincin k'asa, ledojin ya koma ya d'auko ya wuce kitchen ya had'o da plates had'e da spoon.

Sai da ya ajiye kayan sannan ya kai duban shi zuwa gare ta "wa yace kiyi girki yanzu?, in je kawai in dawo ke ce makuku har kin fad'a kitchen", yana maganar ne da murmushi d'auke a fuskar shi tamkar gonar auduga.

"To in banyi girki ba me kake so muci?, ko mu kwana da yunwa kake so?, ni da ma ka maida ma ciki tamkar an yimin yaso".

Suna had'a ido ta nok'e kan ta tana murmushi, "yarinya za kiyi bayani ne".
Daga hakan ya fitar da kaza biyu da fresh milk sai wani take away dake da ferfesun y'an ciki daya siyo B.L.B, baki ta saki tana kallon shi had'e da furta "da mu da wa way'annan kayan?, ka d'auki kaza d'aya ka kaiwa su Mum".

Ido ya gwalo waje yana kallon ta, "wato so kike in bayyana kaina gurin Mum", dariya ta yi sosai sannan ta ware d'ayar ta bashi ya saka a fridge gobe a d'imama akai masu, saboda ita ma tasan baza ta iya zuwa part d'in ba yanzu.

Da hakan suka ci suka k'oshi, sannan suka dasa baben hira da nunawa juna kula wa tamkar sa had'iye junan su, sai k'arfe *11:30pm*sannan suka kwanta.

****

Kwanaki sun shud'e watanni ma haka, inda yau ne Zajlah ke ta shirye-shirye tun safe kan zuwa sunan y'ar da Salmat ta haifa, akwati d'aya suka had'a ita da Alamein na kayan jinjiri da kayan amaryar k'arni, saboda yanzu gwargwado hanyar samu na k'ara bud'ewa Alamein a cikin kasuwancin shi, tun 08:00am ta kammala aikin ta take ta tayar da Alamein kan ya tashi ya sauke ta gida ya k'i sai juyi yake yi saman gado, dabara ta fad'o mata ruwan sanyi ta d'ebo ta yayyafa mai a fuska, yana tashi ya janyo ta saman gadon sai da ta yi ta had'ashi da Allah sannan ya sake ta ya d'auko key suka fice.

Gidan su Salmat cike yake da y'an suna, Yusrah, Saudat, Zajlah sun kammalu gidan inda akayi taron suna aka watse kowa yaci ya k'oshi sai dai fatar Allah ya raya Mus'ab, sai dare sannan kowannen su mijin shi ya zo d'aukar shi suka wuce.

*****

Bayan sati biyu ne da sunan Salmat tana kitchen tana tafashen kayan ciki za ta d'ora girki ta fito aguje wurin toilet d'in su na tsakar gida tana lezaya amai tamkar za ta had'o da hanjin ta, k'arar aman ta ne ya ankarar dashi ya fito da sauri, taimaka mata ya yi ta wanke bakin ta sannan suka koma falon. K'amshin tafashen naman na bugun hancin ta ta k'ara fitowa tana wani aman.

"My Zaz me kika ci hakan yake ta sakaki amai?", a rud'e yake jero mata tambayar, gaya mai ta yi ya kashe risho d'in ya kawo mata gyalen ta za ta shiga gurin Mum, hakan ya kawo mata suka wuce part d'in Mum gaba d'ayan su.

Gaida Mum kawai suka yi ya jefo mata maganar "Mum kinga My Zaz sai amai take ta lezawa har ta kasa zama part d'in mu".
Duban ta ta maida ga Zajlah sannan ta ce' "me ke damun ki halan?", duk da tana zargin shigar ciki ne da ita, amma tana so ta tabbatar da zargin ta.

"Mum tafasar nama ce ba naso shiyasa", murmushi kawai ta yi had'e da yi mata Allah ya sauk'ak'a sannan ta d'ora da cewa "sai ki ajiye girkin har zuwa lokacin da cikin zai yi k'wari, in yaso a rik'a baku anan".

Kunya ce ta kori Zajlah ta yi d'akin Mum ta bar su ita da Alamein, don dama tana zargin cikin saboda watan ta biyu bata ga al'adar ta ba.
Bayan ta d'aga ne Alamein ke ta damun Mum da tambayar abinda ke faruwa, nan ta gaya mai ciki ne da Zajlah d'in. Kan murna bai tsaya ta k'arasa bayanin ta ba ya fad'a d'akin Mum d'in don nuna wa Zajlah tsabar murnar shi.

****

Akwana a tashi ba wuya a gurin ubangiji, saboda Yusrah ita ma ta sauka, sai dai abinda ta haifa bai zo da rai ba, sanadiyyar hakan yasa Imran ya hana ta zuwa gida wankan jego, dole cikin dangin mamar ta aka tura mata wata domin kulawa da ita yanda ya dace.

****

Dak'yar ya barta ta je barkar Ummulkhairi matar Ustaz Lukman, saboda a cewar shi yana kishin ganin ta tare da Ustaz d'in, "banda abinka HUBBY ni da zanje barka me zai had'i na da Ustaz?, wai ma tsaya wa ya gaya ma Ustaz Lukman ya yi "So" na?", da mamaki fal a ranta ta jefo mai tambayar.

Sai da ya k'ara had'e fuska sannan ya yi mata bayani kamar haka, "lokacin ciwon Dad kinsan su ke zuwa yiwa Dad addu'a, to nan ne Ustaz Yusuf ke yimin nasiha kan in rik'e ki da kyau, saboda ke Mace ce mai hankali da nutsuwa kuma nayi dace, inda har yake gaya min da yanzu Ustaz Lukman ne mijinki, ba don ma yana kula da mahaifi na ba gaskiya da na sallame shi wancan lokacin, saboda dana kalle shi wani k'unci nake ji".

"Su kishi manya, to ni dai tashi muje ba dad'ewa zan ba sai ka jira ni mu dawo tare", da hakan suka fice domin zuwa barkar.

A DALILIN GATA Part 31-35 (the end)
.


Zaune suke suna cin abinci da uban tutse-tsen cikin ta wanda haihuwa ko yau ko gobe. " HUBBY ya kama ta kabar ni naje gida wankan jego, kasan fa daga na farko shikenan ba komawa za'a k'ara yi ba".
"Yanzu My Zaz za ki iya tafiya kibar ni cikin tarin kewar ki?, kinsan irin K'aunar da ke tsakanin mu bazan iya jure rashin ki a tare dani ba, ya kama ta ki tausaya min".

Zugum ta yi bata ce komai ba saboda ko ita tasan ba zata iya nisa dashi ba sai dole, ya koya mata k'aunar shi mai zafi yanda bata iya nisanta dashi, "My Zaz in kina ra'ayin zuwa bazan takura ki ba, ko yau zaki je sai ki had'a kayan ki, amma nasan zan takura fiye da tunanin ki".

"Ba komai Hubby na hak'ura, farin cikin ka shine muradi na har kullum, ni ma nafi so kullum ingan ni tare dakai. Yanzu yaushe ne za mu tare sabon gidan mu?".
"Ina ga mubari sai Allah ya sauke ki lafiya kamin suna sai mu tare can ayi suna ko?".

"To Allah yanuna mana lokacin", da hakan suka cigaba da tsara yanda abubuwan zasu kasance.

***

Baban Zajlah Allah ya bud'e hanyar samu har ya sayi wani fili bayan shi ya had'e da gidan shi ya yi gyara gwargwado, saboda a tunanin shi tilon y'ar shi za ta dawo gida wankan jego, baisan sun riga sun kitsa komai ita da mijin ta ba.

***

K'arfe 01:00am ta falka da nak'uda inda tun tana juriya har ta tayar da Alamein daga barci, gigice ya tashi ta gaya mai yakira mata Mum, hakan ya fice ya kira Mum suka zo tare ji yake yi tamkar yad'auke mata ciwon da ke tattare da ita.

Magana yake wa Mum kan suje asibiti, ganin haihuwar ta zo gadan-gadan ya sa tace yad'an tsaya suga yanda za'ayi. Duk addu'ar da tazo bakin Zajlah furtawa take yi saboda ta galabaita iya galabai ta, suna batun zuwa asibiti ta sunkuto y'ar ta sannan namijin ya biyo baya, je kaga murna gurin Alamein da Mum.

Nan dai Mum ta kimtsa yaran ta kaiwa Alamein sannan ta dawo ta kimtsa Zajlah, tea ta had'a mata mai kauri ta bata tasha.
Ko da Mum ta fito falon ya saka yaran gaba yana kallo yana murmushi, "To baban twins aje a kwanta ko?, ba ni yaran inje dasu tunda yanzu 02:30am, kuma nasan da wuya su nemi mamma cikin daren nan".

"Gaskiya Mum sai dai ki kwana nan ko kuma in biyo ki part d'in mu kwana can mu duka", baki ta saki galala tana kallon shi.

"Anya ko Alamein yanda nake murnar na samu jikoki za ka iya bani yaran nan?".

"Ba dai in baki duka ba ko Mum?, ai kyautar d'a sai Allah, zan dai rik'a baki aro koda na awa biyu ne", yana maganar ne had'e da murmushi a fuskar shi da alamar zolaya.

Ita ma Mum murmushi ta yi ta d'ora da cewa "to mara kunya ai yara nawa ne saboda y'a ta ta yi nak'udar su ba kai ba, in yanzu tace ta bani sun zama nawa", ganin cewa tabbas baida niyyar bata yaran ya sa ta fice daga part d'in.

Duk abinda suke yi Zajlah na jiyo su daga d'akin tana murmushi, sai gashi yana k'wala mata kira, hakan ta janyo jiki ta fito falo d'in, "d'auki yaran mu shiga daga ciki, ni ban iya d'aukar jinjirai ba".

Kallon mamaki ta bishi dashi, "amma ko Hubby ka kai, yanzu ma ko yaran baka iya d'auka ba ka hana Mum taje dasu?, to kasan yanda za kayi dasu saboda ni bacci nake ji gaskiya", da hakan ta juya zuwa komawa d'akin.

Lalla6a ta ya yi sannan ta dawo ta d'auki namijin sannan ta runguma mai macen suka koma d'aki suka kwanta.
Sallar asuba kawai ya yi ya dinga kiran mutane a waya yana gaya masu k'aruwar da suka samu, sai da safe aka kaiwa Dad yaran ya yi masu addu'a had'e da sanya masu albarka.

Kamin kace kwabo gida ya cika babu masak'ar tsinke y'an barka, inda Mum ta yi-ta yi dashi akai Zajlah gida ya k'iya, hakan tasa wata k'anwar Mama Inno da Naja'atu suka dawo gidan da zama domin taya ta rainon jinjirai.

****

Ana saura kwana biyu suna ne su Salmat, Yusrah, Saudat da Shema'u suka je kimtsa mata kayan ta a sabon gidan su nan cikin G.R.A d'in bayan gidan su Mum duk da Saudat da Yusrah na fama da nasu cikin.
.
Ranar suna yara sunci sunan Baban Zajlah da kuma Mum, inda ake ma Abubakar inkiya da Ikrama Maryam kuma Ikram.

Ranar gida ya cika mak'il da y'an suna, Zajlah, Saudat, Salmat, Yusrah Naja'atu da Shema'u suka saka kaya iri d'aya wata dakakkar shadda mai ruwan milk.

Fatima, Bahijja, Lateefa da Musirrah suma ba'a barsu a baya ba, don suma sun yima Zajlah kara har da yaran su.

Wata tawaga na hango tafe sunci ado, kowan nen su baki har kunne, sai da suka iso kusa ne sannan naga mai jagorantar tafiyar ba kowa bace sai Aunty Sis, Momma na Mariya girgir (snowhite), Badiyya, mmn Bakir, Ameena Bappa, Feenah umar, mmn Faruk, Humaira Ya'u, Mmn Khairullah, Sofys-closet, Aisha Bello, Maryam yusuf, Hauwa Jidderh, Aunty Baraka suma sun yiwa Zajlah kara, ashe da gaske soyayyar da suke yi mata ba a baki bace kawai.

Ranar twins sun sha d'auka ga mutane saboda pix d'in da ake ta d'auka, sai daga baya ne Alamein ya shige part d'inshi da yaran.
Suna kam ya yi armashi abu gwanin ban sha'awa, kowan ne mutum sai da ya fita da jaka da agogo masu tambarin Ikram da Ikrama.

**

Bayan shekara biyar, yara na hango su uku suna kiciniyar bud'e mota zasu shiga yayin da Alamein ke tara-tara dasu kan su bari inya dawo zai kai su gidajen, yanzu yana sauri ne, rigima suka aza wanda ya rasa ya zaiyi dasu, suna hakan ne sai ga Zajlah ta fito da key d'in mota a hannun ta, nan ta fanshi Alamein ya fice sannan ta loda su a mota suka fita.

Shagunan ta na d'inki ne ta fara kai ziyara inda taga komai na tafiya yanda ya dace, daga nan ta wuce gidan Salmat, Mus'ab da Haydar ne suka shek'o taryar su, nan aka baje ana ta hira.
.
Sunje gidan Saudat da yaran ta biyu, Fa'iz da Muftah, Sai Yusrah ita ko y'ar ta d'aya Zainab, daga nan gidan su ta wuce suka wuni can inda Ikrama yace tunda ba skul nan zai kwana, nan suka barshi suka wuce sai gidan Naja'atu, sai gidan Mum shi da yake kusa da gida.

Ikram ce da little Zajlah suka d'anewa Dad sai tumurmusar shi suke yi, Mum na fad'a kar su karya mata miji, nan dai Zajlah ta bar su ta fice gida, taso ta shiga gidan Shema'u aka ce ta wuce Abuja gurin yiwa oga hutu.

***
Kwance suke yana bata labarin Visa d'inda ya je cuku-cuku an samu ta Mum da Dad sai Baban ta daya biyawa aikin hajji, saboda ita sunje bayan ta yaye su twins, cikin kud'in shagunan ta na d'inki daya bud'a mata ta biyawa Mal Inuwa inda suka yita sanya mata albarka.

"Ina alfahari dake a rayuwa ta domin kin zamo haske a lamurrana, yanzu gashi A DALILIN GATA* da Mum ta yimin na zamo mai kamilallar zuciya da kuma alfaharin samun ki a matsayin uwar Y'ay'a na, ya kama ta yau asamu little Alamein tunda kin raba yara kina buk'atar hutawa da Hubbyn ki".
.
Ganin cewa abin zai fi k'arfin gani na yasa na jama su k'ofa na fice, Asuba ta gari.
.


TAMMAT BI HAMDILLAH


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment