Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bata so hakan ba, kuma ba don hakan da ya yi ba to tayi alk'awari baza ta fad'awa kowa abinda yafaru ba, amma sai gashi yana batun bayyana kanshi.

Mamaki ne k'arara a fuskar sauran mutanen da ke falon, kowa alamar tambaya fal a fuskar shi, muryar Mum ce ta daki dodon kunnen su yayin da take furta, "wannan abin ya riga ya wuce a guri na, kuma na d'auki faruwar hakan silar abubuwa da dama, saboda ta nan ne na samu sirika data zamo alkhairi a cikin iyali na, kuma ta hakan ne Allah ya had'ani da siriki na", nan ta k'arashe maganar cikin murmushi.

Fadeel ne ya tayar da kai ya kalle ta, sannan ya kuma nok'e kai, alamar tambaya ta hango fal a fuskar shi. "Wannan yarinyar dai yanzu haka tana gidan nan matsayin matar yaro na".

Daram! Ya ji gaban shi ya buga saboda jin Zajlah na gidan, duk da ya dad'e da cire ta a ran shi saboda hango irin nisan da ta yimai na tabbatar da ta yi aure.
"Ni fa bangane ba sai wata magana kuke yi a dunk'ule wacce mu bamu fahimci ina kuka dosa ba, dama kinsan sirikin na ki ko yaya?", Dad ne ke yiwa Mum wannan tambayar.

Hakan ne ya sa ta kwashe abinda ya faru tsakanin ta da Fadeel ta gaya masu, inda jikin kowa ya yi sanyi musamman Saudat da tasha jinin jikin ta tana jiran ko ta kwana, amma ita gaskiya tunda bai kai da marin mahaifiyar ta ba tana son shi a hakan don ta hango nadama k'arara a fuskar shi, amma dai za ta jira taji daga iyayen ta.

"Kar ka damu kanka akan wannan abin, saboda zan iya cewa wani wa'azi ne na daban ya sauka akan mu duka, don yaro na bai wuce sati da marin wani dattijo ba muka yi karo da kai, kaga ko naka mai sauk'i ne akan na shi".

"Yanzu muna lokacin da y'ay'an masu kud'i basu cika d'aukar talakan mutum da wata k'ima ba, ko kuma sun d'auki cewa dukiyar su za ta sa su taka mutum son ransu kuma su taka banza, suna ganin bashi da wani tsayayye ko kuma a'ah bai da k'imar da za su dube shi da gashi tunda yana talaka".

"Shin shi yayo kan shi talaka? Ko kuma shi ya rok'i Allah yabar shi hakan? Ko kuma wani laifi ya yiwa ubangiji shiyasa ya barshi hakan?, ko d'aya, iko ne da kuma banbancewar ubangiji tsakanin bayin shi".

"Ni dai ina mai shawartar Ku da girmama mutum ko da ko baku San inda ya fito ba ta hakan na Ku iyaye za su yi daraja ko a bayan idon Ku, kuma indai ni na haifi Saudat na baka ita halak malak", tana duban Dad ta furta hakan.
Sannan ta d'ora da cewa "Dadyn Alamein Allah yasa ban yi kaud'i ba", tana maganar tana murmushi.

Jikin kowa sai da ya mutu a falon, saboda yanda Mum bata d'auki lamurran duniya a bakin komai ba, da wata ce tabbas da hakan za ta gilma Katanga tsakanin Saudat da Fadeel.

"Ba komai Mumyn Saudat, Allah ya tabbatar mana da mafi alkhairin sa", fad'ar Dad kenan da shi ma yake magana cikin sanyi jiki had'e da jin dad'in yanda Allah ya bashi mata mai hankali da nutsuwa, lallai tabbas ya yarda da akace in Allah ya baka mata ta gari to ka samu rabin addinin ka sai dai ka cika rabin tsakanin ka da ubangijin ka, kuma sai yanzu yake hango illolin gatan da ya yi nuna wa yaran shi don yasan ba don ita ba da yanzu gidan shi ya rushe gaba d'aya.

"Ku tashi ku koma sit room ku k'arasa zancen ku, siriki na Fadeel a gaida gida". Nan dai suka fahimci Mum Mace ce mai son raha.

Da hakan suka koma sit room suka cigaba da hirar su sai yabon Mum Fadeel da Farouk ke yi, inda ita ko Saudat ke jin dad'in yabon da akewa mahaifiyar ta.

****

Yana falo yana kallo Zajlah ta shigo ta zauna saman d'ayan kujera sannan ta yi mai sannu da hutawa, bai amsa ba kawai ya taso ya zo saman kujerar da take zaune ya zauna.

"Ba ni aron wayar ki zan d'an yi wani abu da ita". Jin ya matse ta har cinyoyin su na gugar juna ya sa ta mik'a mai wayar, a zaton ta ta shi zai yi sai ga shi ya k'ara gyara zama, xender d'in wayar ta ya bud'e ya kamo pix d'in ta da Saudat ta d'auke ta kwana biyu da suka wuce, saboda in bata manta ba ranar ta dame ta da zolayar cewa ta had'u shiyasa ta matsa ta yi mata pix d'in.

Tsam ta zabura daga gurin ta koma d'akin ta falo ta kwanta saman kujera, sai mamaki take yi yanda yake shisshige mata kwanan nan, da kuma son kusancin shi da ita, duk yanda take kauce mai sai ya sako ta a lamurran shi, wanda ita ko ko kad'an bata son hakan.

(Tau fa Alamein sunan ka sorry, ni dai Jegal na tausaya ma daka bari Zajlah ta gano lagon ka).

Alamein sosai yana ganin cigaba a cikin kasuwancin shi, abin kawai sai dai hamdala don yanzu ne yake jin shi mutum kamar kowa kuma yake sanin ya lamurran duniya ke tafiya. Haka kawai ya ji yana sha'awar siyo ma Zajlah wani abu saboda kyautata wa tsakanin su, musamman yanzu da yake ganin cewa da bazar tace yake rawa, in ya tuna cewa tun auren su kawo yanzu bai ta6a siyen wani abu ya bata ba har kunya yake ji, dai-dai da cefanen gidan bai san ya yake tafiya ba, ita ke yi ko Mum bai sani ba, tabbas yanzu yasan cewa ba k'aramin gata Mum ta yi mai ba, gashi duk abinda suke tak'ama dashi sun rasa lokaci d'aya amma gashi ADALILIN GATAN da Mum ta yimai na aura mai nagartattar mata basu shiga k'unci sosai ba, ba abinda yake so irin ya tsokane ta ta dinga fad'a tana cuno baki, wai ita a dole an ta6a ta, yanayin ta da yanayin maganar ta na burge shi, a hakan ya wuce B.L.B plaza ya yi mata siyayya sannan ya hau hanyar gida.

Da sallamar shi ya shiga gidan lokacin tana kitchen tana girkin dare, direct ya risk'e ta kitchen d'in, nan ta yi mai sannu da zuwa sannan ta juya ta cigaba da aikin ta.

"Ga wannan na siyo maki Zajlah", yanda ya furta sunan na ta ne yasa tsigar jikin ta tashi, ji take yi duk duniya ba wanda ya kaishi iya furta sunan ta. Ta so ta share shi kuma zuciyar ta ta kasa juren hakan, wai me yasa kwanan nan kusancin da yake yi da ita yake janyo mata jin wasu abubuwa a tattare da ita?, ko fita ya yi yanzu har matsuwa take yi bai dawo ba, tana so ta gansu guri d'aya yana tsokanar ta hakan na mata dad'i duk da ba wata doguwar hira ke had'a su ba.

Hannun ta ya kama ya damk'a mata ledar da ya shigo da ita, daga hakan bai saurare ta ba ya yi part d'in su Mum. Acan ne Mum take bashi labarin ashe mai neman Saudat ne suka yi karo ranar, nan ta zube mai yanda suka yi daya zo gidan, jikin shi ne ya yi sanyi da hakan had'e da al'ajabin wannan lamari, lallai tabbas Allah mai juya lamurran shi ne yanda ya so, yana nan suna hira da Mum ta k'are girkin ta ta shigo part d'in rik'e da kula data sako ma Dad tuwon semovita da miyar agushi ta ji kifi.

"K'arasa ciki ki kai mai y'ar albarka", cewar Mum kenan, da hakan ta wuce d'akin Dad saboda inda sabo yanzu kam ta saba don har zama take yi su yita hira ita dashi, bayan ta kai mai ne ta dawo falon lokacin Saudat ma ta fito nan suka baje ana ta hirar yanda auren Saudat zai kasance.

Kiran magrib ne ya tada kowa daga gurin domin gabatar da farali, part d'in su suka wuce inda ya yi alwala ya wuce masallaci ita ko ta fad'a na ta d'akin domin sauke farali.

***

Bai shigo gidan ba sai da ya yi sallar isha'i sannan ya wuce ya yiwa Mum sai da safe ya koma part d'in su, abinci ya tarar a dining table kamar kullum amma bai ji motsin taba, hakan ya sa ya fad'a d'akin ta.

Zaune take saman sallaya tana karatun K'ur'an cikin k'ira'ar ta mai sanyi da kuma dad'in saurare inda take karanta suratu Luk'man. Saman katifa ya je ya kwanta yana sauraren ta har ta kai matsaya ta ajiye K'ur'anin sannan ta yi addu'o'in ta ta shafa inda shi ma Alamein ya taya ta shafawa.

Sallayar ta ninke ta ajiye ta had'a K'ur'anin ta da littattafan ta na azkar ta ajiye, sannu da zuwa ta yi mai wanda bai ko samu damar amsawa ba sai fararen idon shi daya bi ta dasu.

Towel ta d'auka ba tare data cire kayan jikin ta ba ta fad'a toilet, jimawa ta yi gurin wankan saboda ba taso ta fito ta tarar dashi a d'akin.

D'aure da towel sanye da hijab d'in ta ta fad'o falon sai kuma ta ja ta yi turus sanadiyyar ganin inda ta barshi bai tashi ba, sai ma wayar ta daya janyo yana latse-latse, basarwa ta yi ta wuce saman kujerar ta da take d'inki ta janyo jakar kayan kwalliyar ta tana shafa mai.

Tausayin ta ya ji ya tsirga mai, ba akan komai ba sai don ganin kowace Mace mai ji da kanta in tayo wanka saman mirror take zama ta yi kwalliya sa6anin ita data zauna saman kujerar keken d'inki.

Jin shi kawai ta yi ya rik'o jakar yana mayar da kayan cikin jaka, sannan ya rik'o hannun ta ya ja ta sai d'akin shi, galala ta saki baki ta bishi tamkar rak'umi da akala, bai tsaya ba sai gaban mirror d'in shi, ita ko ya janyo kujerar ya zaunar da ita, "daga yau ga gurin kwalliyar ki kuma ga d'akin ki", daga hakan ya juya ya koma d'akin ta.

Akwati nan ta ya janyo yayo d'akin shi dasu, baki kawai ta saki tana kallon shi har ya gama kwaso kayan ta kaf ya kawo d'akin nashi, har lokacin bata samu motsawa daga yanda ya ajiye ta ba.

"Bara in maki kwalliyar in ba zaki iya ba", kayan ya fitar na kwalliyar ta ya jera saman mirror d'in, kiciniyar cire hijab d'in ta ya rik'a yi hakan ya sa ta daddafe jikin ta, tana rok'on shi yabari ta kimtsa da kanta.

D'akin ta ya koma domin ya bata guri ta samu sakewa, saman katifar ya kwanta yana kallon videos na d'aurin d'ankwali.

Mamaki ne ya ishe ta na Alamein, tamkar ba shi ne yake hantarar ta yana kira mata dak'ik'iya kuma jahila ba, da mamakin shi fal a ranta ta kimtsa ta saka riga da siket d'in ta na atamfa sannan ta fito domin taci abinci.

Motsin da ya ji falo ne ya tabbatar mai da fitowar ta, hakan ya fito daga d'akin ya ganta zaune falon su ta saka filet d'in abinci tsakiya tana ci. Hannu ya saka suka rik'a cin abincin tare, sai satar kallon ta yake yi yanda yake ganin take tsantsara kwalliya kamar wacce ta shiga makarantar make up, gano cewa neman magana yake so ya sa ta k'yale shi har suka cinye abincin, na shi dake saman dining table ya d'auko ya zuba suka koma ci, da hakan ta tashi ta wanko hannun ta sannan ta fad'a toilet ta yo brush, d'akin shi d'in ta zauna saman kujera bayan ta d'auko wayar ta ta kunna data ta hau whatsap.

Da hakan ya risk'e ta tana charting ya fad'a toilet ya yi wanka, d'aure da towel ya fito inda take satar kallon shi, mutum ne dogo ba sosai ba mai faffad'an k'irji sai dai ba za'a ce mai mai k'iba ba kuma baza'a ce mai siriri ba, fari ne ba sosai ba yana da hanci har baka, sajen fuskar shi ke k'ara fitar da kyawon shi had'e da fararen idon shi tamkar madara, sumar kan shi bak'a ce wulik ta kwanta tamkar ta Fulani, ya fi yanayi da larabawan Sudan.

Firgigit ta dawo hayyacin ta sanadiyyar ruwan kanshi daya sharto mata a fuska, cikin jin nauyi ta nok'e fuskar ta tana latsar wayar ta, "ko in zo ki taya ni Shafa mai ne, na ga hankalin ki ya tafi a kallo na, kinga sankacecen saurayi", yana maganar ne cikin zolaya da kashe mata ido d'aya, still kasa tayar da kan ta ta yi sanadiyyar kama ta da ya yi tana yi mai kallon k'urilla (Zajlah kar ki bada irin su Anty Sis, Hauwa Jidderh, Salmatun Innah, Namcy Sardeeyer, da Wamsyl, masu cewa sun matsu Alamein bai shigo hannun ki ba, toh fa ko reshe ne zai juye da mujiya ke ki shiga tarko?, lolx).

Turare kawai ya fesa ya saka jalabiyar shi mai ruwan anta, ya hau gado ya kwanta, ita ko ta jona wayar ta a charge ta kwanta saman three sitter.

"Wannan ne kuma baki isa ba, saboda haka ki taso ki dawo saman gadon ki kwanta, ba wani abu nace zan maki ba".
Ji rainin hankali, to me tace zai mata, ina ga in na k'yale wannan mutumen rainin zai yi yawa, cikin zuciyar ta take wad'annan maganganun.

Gaban ta kawai ta ganshi yana batun sunkutar ta, da hannu ta yimai alama sannan ta kalle shi sama da k'asa "ina ga ka hutar da kanka da shiga mu'amalar kucaka kuma jahila, saboda gudun kar ta6on ta ya shafe ka".

Daga hakan ta juya ta bashi baya ta yi kwanciyar ta. Tamkar gunki haka ya dask'are a gurin, lallai tabbas magana zarar bunu ce, kuma yana da tabbacin watarana za ta maida mai amsa, wannan ba damuwar shi bace indai za ta hak'ura ta yafe mai laifin shi a gare shi, hakan dai ya ja jiki ya je ya kwanta.

****

Yau ne aka d'aura auren Saudat Kabeer Aminu da Fadeel Ibrahim mai dala, inda aka yiwa Saudat abubuwa cikin tsaka tsaki na masu rufin asiri, sai dai fatar d'orewar zaman lafiya.

Sai ranar da aka kai tane Zajlah tasan Fadeel ne da ya ce yana son ta, tuna abinda ya faru tsakanin shi da Mum ne yasa jikin ta ya k'ara sanyi da lamurran duniya had'e da ikon ubangiji.

.............

Yau ne mummunan labari ya risk'e su cewa Allah ya yiwa Alh Ibrahim rasuwa akan hanyar shi ta zuwa Abuja daga sokoto ya yi hatsari, inda suka jajanta abin had'e da yimai murnar sauke nauyin marayin Allah dake saman kanshi, addu'a suka yi mai inda Mum taso ko Alamein ne yaje, sai dai a labarin shi bai gaya masu takamemen address d'in gidan suba, Allah ya gama rai da gafara, Amein.

***

6angaren Baban Zajlah yana ganin bud'i a kasuwancin shi saboda yanzu shine shugaban masu kayan gwari, don ya daina kasawa a table sai buhu-buhu da yake d'aukowa ana siya gare shi, amincin su sai k'ara k'arfi yake yi tsakanin shi da Malam Inuwa sun zamo tamkar y'an uwa na jini.

***

Cikin Salmat yanzu ya kai wata bakwai, yanzu laulayi ya rage sai d'an banzar kwad'ayi dake taso mata inda Imran ke tarairaya da ita tamkar k'wai.
Yusrah na mak'ale da na tacikin d'an wata biyu wanda ba kowa yasan da zaman cikin ba saboda ba wahala yake bata ba.

***

Alamein ne zaune k'asa dirshan inda Zajlah ke zaune saman kujera tana fuskantar shi sai wani cin magani take yi, ta yi wanka ta ci ado tamkar wacce za ta je bikin aure sai cingum take tauna yana bada k'as-k'as.

"Bazan iya jure wannan garawar da kike min ba, Zajlah nasan ni mai laifi ne a gare ki, amma na yi ta baki hak'uri kin k'i ki hak'ura".
"Tun farko wallahi bansan miye "So" ba ban ta6a tsayawa na yi magana da mace ta minti uku ba, a wancan lokacin na saka ma raina tsanar mace ne ba akan komai ba sai don ganin yanda suke taka rawa a ta6ar6arewar rayuwar d'a namiji cikin shu'uman cin su".

"Bazan manta ba muna farkon shiga university mu hud'u muke tare, Salis, Imran, Salim sai ni Alamein, duk wanda ya san mu tare yake ganin mu, bamu shiga sabgar kowa karatun mu kawai muka saka ma gaba.
Akwana a tashi Salim ya had'u da wata yarinya da ake cema Hafsat inda soyayya ta shiga tsakanin su, ganin rayuwar shi ta fara sauyawa muka nemi raba shi da ita saboda ya kula da karatun shi gashi maraya amma abin ya gagara, saboda y'ar mai kud'i ce yarinyar kuma gwargwado tana sakar mai kud'i, daga hakan ta ja ra'ayin shi suka rik'a holewa har ya zamo tamkar miji a gare ta, hakan ya yi silar muka tsame kan mu daga lamurran shi, wallahi tun daga lokacin na k'ara tsanar Mace a rayuwa ta".

"Tabbas nasan ina da tak'ama da ji da kai, amma ba na saka Mace a tsarin rayuwa ta kwata-kwata, kuma kiyar da dacewa kece first love d'ita kuma last insha Allah, wannan horon da kike yimin ya yi tsanani don Allah ki sassauta min", hakan ya k'arashe maganar yana rik'e da hannun ta har da guntun hawayen shi.

Tabbas ta tausaya mai, amma ita miye na ta ciki na hantara da hwulak'antarwa, tunda ita ma ba ita tace tana son shi ba, kawai daga sama akace an mata miji, me zai hana yayi wa iyayen shi biyayya ko da bai son ta ya shafa mata lafiya kowa tashi ta fisshe shi.

Yatsun hannun tane da yake murza wa ya sa ta fincike hannun ta ta mik'e ta yi d'aki, key ta murd'a ta yi zaman ta d'akin.
Har ga Allah tasan tana son Alamein kuma shine kalar namijin da take so tun bata san miye "So" ba tsayayyen namiji ke burge ta, sajen fuskar shi da dara-daran idon shi ke k'ara d'aukar hankalin ta zuwa gare shi, amma tabbas sai ta nuna mai darasi sannan za ta bada kai bori ya hau.

Tsam ya tashi ya yi part d'in Mum, saman kujera ya zube ya yi kwance hannun shi d'aya ya yi matashi dashi d'ayan kuma ya dafe kanshi inda har jiyojin kanshi sun tashi rad'o-rad'o.
Mum ce ta fito daga d'akin Dad ta risk'e shi hakan, tafi minti uku saman kanshi bai ma san tana nan ba. Tabbas kwanan nan tana lura da takon shi tsakanin shi da Zajlah, tasan ba komai ne ke wahalar da shi ba sai "Son" Zajlah dake d'awainiya dashi, saboda yanda yarinyar ta k'ara fresh yanzu ga wayewa dake shigo mata kad'an-kad'an, inda ko Mace y'ar uwar ta ta ganta cikin kwalliya sai ta k'ara kallon ta barranta na namiji, da hakan ta yi alk'awari ba za ta ta6a nuna mai ta fahimci matsalar shi ba, sai Zajlah ta gama gara shi ta sauko don kanta.

Hannun shi da ya rufe fuskar sa dashi Mum ta janye had'e da furta "waini Son kwanan nan me ke damun ka?, duk sai in ganka tamkar kana cikin damuwa, ko gurin kasuwancin ne?".

Ji ya yi tamkar ya gaya mata me ke faruwa ko za ta taya shi shawo kan Zajlah, sai dai kuma yana tunanin ko ya gayawa Mum ba lallai ne ta bashi had'in kai ba, tana ma iya basarwa da tuna mai baya.

"Ba komai Mum yanayin rayuwa ne kawai, a dai taya mu da addu'a", "toh Allah yashige mana gaba, kaima ka dage da addu'a".

Bayan ya amsa ne ya ji kuma zaman ya gundire shi ya tashi ya yi part d'in su, wanda har lokacin Zajlah na d'aki bata fito ba. D'ayan d'akin ya fad'a ya shiga toilet ya sakarwa kanshi ruwa, sai da ya yi wanka ya fito ba kayan sakawa suna d'akin da Zajlah take, k'ofar yaje yana bugawa had'e da magiyar ta bud'e zai d'auki kayan shi, hakan ya sa ta fito ta bar mai d'akin ta dawo falo.

................

Duk mahaluk'in da ya ga Alamein yasan cewa yana cikin damuwa, saboda har y'ar rama ya yi kuma ya tara wani uban saje a fuskar shi da ya maida shi tamkar wani Sabon shigar hauka.

Ba k'aramin tausaya mai Mum ke yi ba sai dai kuma tana ganin in har tace za ta saka baki a maganar su tamkar ta so kanta dayawa, kuma in za ta duba bata San iya muzguna warda ya yi yiwa ita Zajlan ba har aka kawo yanzu, kuma a 6angare d'aya ta fi so Zajlah ta garashi saboda yasan darajar ta.

Abincin rana ta gama ta kawo ta ajiye, amma ga mamakin ta yanda ta ajiye na safe hakan ta tarar da shi, mamaki ne fal a ranta saboda yanzu suna wasar y'ar 6uya tsakanin su in yana d'ayan d'akin to itako za ta koma d'ayan.
D'akin da yake ta tunkara, har ta rik'a k'ofa za ta murd'a kuma ta fasa, saboda a tunanin ta in tayi hakan ta bada kanta, sai kawai ta dake ta koma d'ayan d'akin ta yi kwanciyar ta, whatsap ta hau amma duk da hakan zuciyar ta tak'i natsuwa guri d'aya, hankalin ta d'ayan na gurin me yasa yau bata ga Alamein ba.

***

A daddafe ta kai la'asar bayan ta yi sallah ta fito domin d'ora girkin dare, still duka abincin ba abinda aka ta6a, cikin rawar jiki ta fad'a d'akin, can k'asa gurin gado ta ganshi zube male-male cikin amai yana dafe da cikin shi, da saurin ta ta kai gurin ta tallafo shi duk jikin shi ya saki.

Toilet ta nufa domin samo ruwa da towel ta gyara mai jikin shi amma ya rik'e ta gam ya hana mata tashi, "Zajlah ki yafe min laifi na zuwa gare ki, inason kisan cewa ko da ta Allah ta kasance a gare ni to na tafi da d'inbin K'aunar ki a zuciya ta, ina sonki kuma bazan daina son ki ba har k'arshen rayuwa ta".
Wani tari ya rik'a yi mai had'e da majina da jini-jini daga hakan ya some a jikin ta. Wata k'ara ta saki ta fito a guje sai part d'in su Mum, koda ta shiga tana zaune falo da remote a hannun ta tana kallon tashar Manara T.V. jin kawai ta yi mutum ya fad'o mata, "wayyo Mum Alamein ya mutu, Mum ki tausayamin kar in rasa shi, Mum ki gaya mai wallahi ina son shi nima".

Sambatu kawai take saki wanda ta kasa yiwa Mum takamemen bayani kan abinda ke faruwa. Remote d'in ta ajiye ta ja hannun ta suka koma part d'in, ko Mum data ganshi a hakan ba k'aramar razana tayi ba, saboda har ga Allah ta zata bashi da rai.
Da saurin ta ta doshi gurin ta tallafo shi, inda Zajlah ke ta shar6ar kuka tana gunza, "yi sauri bani ruwa a cup".

Fridge ta bud'e ta d'auko ruwa ta bawa Mum ta koma gefe ta raku6e sai gaban tane ke dukan uku-uku. Ruwan Mum ta watsa mai a fuska saboda tabbacin yana raye suma ne ya yi, firgigit ya motsa dafe da k'asan marar shi sai hawaye ne ke yi mai zuba.

"Mum kice wa Zajlah ta so ni kamar yanda nake son ta, Mum wallahi na gano kuskure na, zan iya rasa rayu.....".
Mum ce ta rufe mai baki, sannan ta kai duban ta ga Zajlah da ta nok'e kan ta tamkar wata marar gaskiya, "ki kula da mijin ki", hakan kawai ta furta ta bar masu falon, saboda dama tasan duk "So" ne ke d'awainiya dasu amma kowan nen su na basarwa a dole bai son d'ayan ya fahimci hakan.

K'arasowa tayi gurin shi had'e da tattara kayan da ya yiwa amai ta kai toilet ta wanke sannan ta had'a mai ruwan wanka ta fito, taimaka mai ta yi ya shiga wankan, ko da ya fito ta kimtsa d'akin ta fesa turare, sannan ta had'a mai tea mai kauri.

"Sannu ya jikin?".
"Da na mutu ai kin huta tunda ba damuwa kika yi dani ba", cup d'in da ta had'a mai tea ta mik'a mai ya kar6a ya ajiye

Please Login or Register in order to submit comment