Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abin ya faru kuwa, muna kwance ciwon ciki ya taso ma Alh D'anjimma inda ya tada ni yake gayamin, hakan ya yi silar fita ta domin in sawo mai tea, don na ga koda ya kwanta bai ci komai ba, bayan na siyo mai tea ne na nufo hanyar dawowa kawai naga gidan ya kama da wuta sosai, wanda tsabar rud'ewa tasa na koma titin ban shirya ba, banyi aune ba kawai mota tayi watsi dani gefen hanya, nan mutumen ya fito yana neman agaji kan a taimaka mai amma ina hankalin mutane ya yi gurin ceton rayukan mutane da wuta ke ci, hakan mutumen ya cicci6e ni ya saka a mota daga hakan bansan me ya faru ba saboda loosing memory na da nayi, ina tare da wannan mutumen daya zamo ubangida a gare ni a cikin garin Abuja wanda na yi nema tare dashi har Allah yasa na samu d'an abin hannu na".

"Bayan y'an shekaru ne ya aura min d'iyar shi Binta wacce miji ya rasu ya bari da d'iya biyu tagwaye har sun girma, bayan auren mune muka samu k'aruwar yara uku wanda har lokacin bana tuna komai a rayuwa ta ta baya".

Daga baya ne ubangida na kuma siriki na Alh Usman ya aike ni Lagos gurin wasu harakoki na shi a hanyar dawo wa tane na samu hatsari wanda bayan farfad'owa ta na dawo hayyaci na, lokacin Husain da siriki na na gefe na ina masu kallon rashin sani, bayan an sallamo ni ne yake min bayanin abinda ya same ni".

"Bayan sati d'aya da hatsari na ne nake yawan mugun mafalkai wanda na rasa gane masu, sai dai suna tsorata ni sosai kuma abin yana da nasaba da abinda ya faru sama da shekaru Arba'in da suka wuce, sai yanzu nake hango illar abinda na aikata wanda son kai da rud'in shaid'an ya kai ni da aika ta hakan, sanadiyyar hakan yasa tunanin komawa gida ya dawo kai na, da hakan na gayawa suriki na zan je gida in dawo, daga nan na zarce asalin garin mu sokoto na yita bincike har na gano dangi na na asali, inda na nemi yafiyar gagarumin laifin da na aika ta zuwa gare su had'e da alk'awarin gyara akan( BABBAN KUSKUREN DA NA TAFKA, SIS RASH KARDAM)".

"A gurin kasuwanci muka had'u da Alh Taheer inda naji Jega rad'am a bakin shi, nan hira ta 6arke tsakanin mu har nake tambayar shi ko yasan ka, yake gayamin kai abokin shi ne, da hakan na kar6i lambar ka wanda gashi Allah ya yi had'uwar mu yanzu".
Kowa falon ya jinjina wannan labarin na Alh Ibrahim, sannan Mum ta bashi nasu labarin bayan tafiyar shi, da hakan ya jajanta masu k'addarar da ta hau kan su, wanda har ya fara zargin kan shi da yana da nasaba da abinda ya samu Dad.

Cikin nadama k'arara a fuskar shi yakai duba zuwa gare su yana mai cewa "ina mai baku hak'uri da abinda ya faru, saboda bazai rasa nasaba da abinda na aika tane ya shafe ku ba".
Cikin rud'ani da tashin hankali suka sako mai ido caaaa, wanda ya kasa had'a ido dasu ya nok'e kan shi k'asa.

.........
Cikin rawar murya da fargaba Alamein ke jero mai tambayoyi, wanda bayan ido da Dad ke saki bai da wani abu da zai iya furtawa akan mutuwar jiki, inda dama tun shigowar Alh Ibrahim kawo yanzu kalma guda bai samu furtawa ba.

Nan Alh ya cigaba da bada labari kamar haka, "kamar yanda na gaya maku ni d'an sokoto ne to haka abin yake, asalin zamana nan Jega da kuma dukiyar da na barma na k'ara gaba to ba tawa bace hakk'in marayu ce".

"Kamar yaya, bangane ba", wannan karon Dad ne ya yi k'arfin halin jero mai wannan tambayar cikin tsananin tashin hankali.

"Mahaifin mu ya kasance mutum ne mai dukiya a wancan lokacin, matan shi uku da yaran shi goma sha biyu, na kasance ni kad'ai gurin mahaifiya ta kuma ita ce ta farko a gare shi, ta biyu keda yara bakwai ta k'arshe kuma yara hud'u. Allah ya yiwa mahaifiya ta rasuwa tun ina da shekara bakwai a duniya sanadiyyar hakan na tashi wulak'ance a gidan wanda dai-dai da abinci sai mak'wabta sun bani ko kuma gidan abokai, da hakan na tashi har na girma ba wani canji na zamantakewa ta a gidan, ana hakan ne ciwon ajali ya kama mahaifin mu sanadiyyar hakan yaga cewa nine babba a cikin yaran shi yasa ya damk'amin duka kaf dukiyar shi a zuwan in rai ya yi halin shi in nemi malamai a raba mana gado, lokacin haukar k'urciya yasa na gudo da kud'in kaf saboda tunani na ta hakan ne zan d'ebe takaicin k'iyayyar da matan mahaifi na da y'an uwa na ke nuna min".

"Haka kawai raina ya bani in gudo Jega da zama, da hakan na shigo garin ina y'an sana'o'i na har Allah ya rik'amin wanda daga baya ne muka had'u dakai har mutunci mai k'arfi ya k'ullu, lokacin da abubuwa suka faru har na d'auki dukiya ta duka na baka nabar gari, wani k'anen mahaifi na ne yaji inda nake har ya aiko sau biyu yana nema na, hakan yasa na had'a komai na baka na yanke hukuncin zuwa gari mai nisa don ma kar aji labarin inda nake".

"Daga bayan nan ne nake ta mafalkai kan mahaifin mu na takure cikin k'abari yana rok'o na kan in d'auke mai wani k'aton dutse dake saman kanshi, ko in ganshi yana cemin wannan ce amanar da na baka. Da hakan hankali na ya yi mugun tashi kuma naji ina so in je gida sannan in dawo nan in kar6i hakk'in marayi in kai masu".

"Abinda yasa na furta ina da sila da abinda ya shafe ku kuwa shine, hakk'in marayu bazai ciyu kuma a zauna lafiya ba, saboda dukiyar kaf banda ko kwabo cikin ta in ba an raba gado bane an bani hakk'i na, saboda haka ina mai baka hak'uri da abubuwan da suka faru".

Nan kowannen su ya nisa had'e da jimamin wannan tarihi na Alh Ibrahim, nan aka yi lisafi kan abinda ya bada sai gashi kaf har kud'in gidan Alamein sun shige ciki kuma ana neman k'ari, sanadiyyar kud'in can baya sun fi na yanzun daraja sosai, hak'uri suka bawa Alh Ibrahim kan cewa yabari gobe yadawo za'a had'a kud'in, da hakan ya fice daga gidan.

****

Ba k'aramin tausaya masu yayi ba kan k'addarar da ta hau Kansu ba, har ga Allah yana so yataimaka masu, amma yafi so ya raba su da lalura in yaso daga baya ya taimaka masu, saboda tabbas dukiyar maraya cin ta lalura ce, shi kanshi baiji dad'in abinda ya aikata ba, don da ya mutu hakan baisan da wanne ido zai tsayu gaban ubangiji ba, da hakan ya yi alk'awari a ranshi cewa da an raba gado an bashi nashi kaso zai dawo yakawo ma Dad saboda sun yimai halacci a zaman takewa musamman Baban Maryam wato Mum inda ya zamo tamkar mahaifin shi sanadiyyar amintakar shi da Dad.

***

6angaren su Mum kuwa sabon nazari aka shiga ta neman mafita, "gaskiya Dad mutumen nan bai yi halacci ba, yanzu duk zaman takewar da kuka yi bazai iya yafe sauran kud'in da babu ciko ba?". Alamein ke wannan maganar cikin kumfar baki.

Murmushi Dad ya yi had'e da girgiza kai sannan ya furta "Son ko da yace ya barmin bazan yarda naci ta ba, musamman yanzu dana san cewa hakk'in marayu ce, yanzu abinda nake so dakai gobe kaje kasa ka motoci na biyu kasuwa, nasan za suyi saurin shiga tunda sabon shiga ne, kabar min d'ayar ta ishe ni lalurar yau da gobe".

Baki ya bud'e da niyyar yin magana hannun Dad ya dakatar dashi, "kayi yanda nace kawai", yana maganar yana murmushi, da hakan ya tashi ya koma d'akin shi ya bar su jugum a falon.

..........
Washe gari Alamein ya samo mai siyen motocin Dad saboda suna sabon yayi don kaf garin Jega su biyu ke da irin motocin, da hakan aka kammala ma Alh Ibrahim kud'in marayi aka bashi ya wuce da alk'awarin sai sun ganshi.

Iya damuwa Mum da Alamein sun shiga wanda ya zamo Dad Allah ya sako mai tawakkalin da basu yi tsammani ba don shi ya zamo mai rarrashi a gare su, (ohhh! Duniya juyi-juyi kwad'o ya fad'a ruwan zafi, abin da mamaki wai liman ya auri karuwa).

A cikin ran shi gaba d'aya ji yake yi ya tsani dukiyar shi duk da ya biya hakk'in marayi, sai yana ganin d'an abinda ya yi saura hannun shi tamkar wata k'addarar za ta iya fad'a mai nan gaba. Da hakan dai ya kwantar masu da hankali kowa ya kama gaban shi had'e da tunane-tunanen miye mafita.

*****

Bayan kwana uku ne da faruwar wannan lamarin Zajlah na d'aki tana wasu d'inkuna da Shema'u ta kawo mata Alamein ya shigo d'akin wanda ko sallamar shi bata ji ba ganin shi kawai ta yi gaban ta, d'an zabura ta yi alamar razana.

"Lallai na tabbatar in kina d'inki ba ki jin motsin mutum, sau uku ina sallama shiru".

Gaida shi ta fara yi sannan ta d'ora da cewa "wallahi banji bane", hakan ya samu gefen katifar ta ya zauna ya yi shiru, ganin hakan ita ko ta basar ta cigaba da d'inkin ta.
Ido ya zuba mata yana kallon yanda take sarrafa keken d'inkin sannan ya furta "ah ashe k'afa ta yi sauk'i tinda har ana iya d'inki da ita", "eh ai tin ranar ta yi sauk'i".

Daga hakan kowannen su ya yi shiru saboda rasa takamemen me za'a fad'a, d'azu ne Salis ya kira yake gaya mai Salmat jiki ya yi tsanani kullum cikin amai da k'arin ruwa take, nan yake jajanta mai had'e da gaya mai za su shigo duba jikin na ta, to shine yanzu yake son gaya mata ta shirya suje amma ya rasa ta ina zai kamo zancen, shine yake ta kame-kame.

"In kin k'arasa aikin zuwa bayan azzahar kishirya muje duba jikin Salmat, d'azu Imran ke gayamin bata ji dad'i ba kwana biyu".

"To" ta amsa a gajarce ta cigaba da d'inkin ta, hakan ya sa ya ja jiki sum-sum ya fice daga d'akin kamar wani munafuki.
Ranar da za suje yiwa Baban ta bankwana kawai ta yi mata sak a rai, "ai ko giyar wake nasha bazan k'ara siyo ma kaina wulak'anci ba, hanyar mota daban ta jirgi daban", hakan ta furta a fili sannan ta yi wani gajeren murmushi na tunawa da message d'in da ya yi mata bata San ya za ta bud'e ba har yaci zalin ta ranar, saboda in har bata manta ba ranar da Salmat da Yusrah suka zo gurin ta har soyayya ta k'ullu tsakanin Salis da Salmat to ranar ne Yusrah ta koya mata yanda ake text message, don ba wai wasik'ar ce bata iya ba a'ah kan wayar ce bata sani ba, wanda sai ranar ta bud'e message d'in da ya turo mata.

***

Tana gama girkin tane ta d'iba ta kaiwa Mum, saboda dambun shinkafa tayi Wanda ya ji kayan had'i da zogale, dama in tayi girkin marmari tana kaiwa su Mum, nan take gaya mata za taje ganin Salmat bata jin dad'i hakan ya sa Saudat tace tana zuwa suka fice tare, saman titi suka samu napep suka wuce.

***

6angaren Alamein kuwa har ya dawo daga masallaci ya yi wanka ya kimtsa bai ji motsin Zajlah ba, hakan ta sa ya je d'akin ta, amma ga mamakin shi yana murd'a k'ofar ya jita rufe. Part d'in Mum ya wuce bayan sun gaisa yake ce mata ina Saudat halan?, amsa ta bashi da cewa ta raka Zajlah gidan Salmat, hakan ya ja motar shi ya wuce mamaki fal ranshi, amma kuma yasan wani 6angare tana shakkar fita dashi ne saboda gudun wasu abubuwan, amma duk zille-zillen ta bazai bari ta dawo a napep ba.

****

Shigar su gidan kenan ana cire mata k'arin ruwan da aka saka mata, nan suka mata sannu suka zube a falon, wanka ta shiga ta fito duk ta jeme kan laulayi, dambun da Zajlah ta zo mata dashi ne ta saka mata, kad'an ta ci taji zuciyar ta na tashi ta ajiye, duk tsiyar da Zajlah ta so yi mata ta rushe saboda ta tausaya mata ganin yanda ciki ya mayar da ita gwanin tausayi.

Suna zaune suka ji shigowar Salis da Alamein, a falon suka zube duka, "lahhhh Brother za ka ma zo baka gaya mana mu jira kaba?", fad'ar Saudat.
Ido ya bi Zajlah dashi suna had'awa ta nok'e kai. Alamein ne ya yiwa Salmat ya jiki had'e da mamakin yanda bakin ta na tsiwa ya mutu. Sai bayan la'asar ne Imran ya kawo Yusrah, nan suka baje ana ta hira inda mazan suka fita.

Bayan isha'i ne suka shigo gidan su uku, abinci suka ci sannan kowa ya yi haramar zuwa gida, inda Alamein ya kasa ya tsare wanda ya sa dole Zajlah ta bishi ita da Saudat suka koma gida ba don taso hakan ba.

.........

Awanni sun wuce kwanaki sun wuce wanda abubuwa da dama sun faru, su Mum an fara shiga rayuwar k'unci komai sai manage, da hakan aka sallami duka y'an aikin gidan saboda zaman su na k'arin wasu abubuwa Mama Talatu kawai aka bari.

***

Yanzu ne take ganin ya dace ta taimaka ma Alamein saboda ko mota babu hannun shi, abincin gidan kanshi ya sauya, saboda ga nasu yanayin kuma ga yanayin k'asa wanda ya shafi kowa, duk inda ka zaga za kaga gidan da aka saba tafiyar da abubuwa 80% yanzu sun dawo 40% saboda yanayin k'asa, abin kawai sai addu'a.

****

Bayan sun karya ne ta Shiga gyara d'akin Alamein kamar kullum, zaune ta isko shi saman kujera ya yi zugum ya saka takardu gaban shi ga alama yana cikin damuwa.

Nan ta gaida shi ta wuce ta fara gyara k'uryar d'akin, ko da ta fito falon yanda ta barshi hakan ta tarar dashi, guri ta samu ta zauna sannan ta tattara dukan nutsuwar ta guri d'aya sannan ta jefo mai magana kamar haka, "meke damun ka haka?, bai dace ka saka ma ranka damuwa ba, kar ka janyo wani ciwo na daban".

Hankalin shi ya maida zuwa gare ta had'e da cewa "ya zanyi da raina kusan sati d'aya ina yawon neman aiki ban samu ba, kuma gashi takardu na sun yi kyau amma abu ya gagara".

"A tunani na me zai hana a ajiye neman aiki gefe d'aya a kama kasuwanci?, kana ganin yanda k'asar ta zama yanzu, way'anda ke saman ma tsige su ake saboda bincike ina aka ga damar d'aukar wasu ma'aikatan?".

Zurum ya yi baice komai ba saboda tuna lokacin da ya kori wani daga ma'aikatar su akan bada shawara kan cigaban su, inda ya tuna lokacin da yake neman yafiya gare shi kan yabar shi ga aikin shi wanda ko sauraren shi bai yi ba ya wuce, hakan ya sa ya ji tausayin kanshi da kan shi kan yanayin da yake ciki sai ga hawaye shaaaaa.

Ba k'aramin rud'ani ta Shiga ba ganin yanda hawaye ke ambaliya a fuskar shi, zumbur ta mik'e ta koma d'akin ta sai gashi ta dawo da wata leda bak'a a hannun ta har lokacin hawaye yake yi, gaban shi ta je ta durk'usa had'e da mik'a mai ledar, handkerchief dake hannun shi ta kar6a tana shafe mai hawayen dake ambaliya a fuskar shi, saboda Zajlah akwai raunin zuciya.

Ledar ya kar6a ya bud'e, abinda ya gani ne ya sa ya tayar da kanshi cikin mamaki yana mai kallon ta, bud'e baki yayi zai yi magana ta yi mai alamar yayi shiru, nan ta d'ora da cewa "kayi shawarar wace Sana'a ce ta dace dakai, na baka su halak malak".
Sakin bakin da Alamein ya yi yana kallon Zajlah ne har ta 6ace ma ganin shi ya sa na lek'a ledar na hango kud'i, wanda duk iya biyar kwakkwafi na na d'aukar rahoto naso insan ko nawa ne don in feso maku amma abin ya gagara.

Ledar ya k'ara lek'awa had'e da murza idon shi don tabbatar da abinda yake gani cikin ta, hawayen idon shine suka k'aru sai kuka yake yi tamkar wani yaro.

Kud'in ya d'auko ya nufi part d'in Mum ya tarar tana d'akin Dad, nan ya shiga da sallamar shi suka amsa sannan ya shiga, kud'in ya ajiye gaban su had'e da yi masu bayanin inda kud'in suka fito, dukan su baki suka sake suna masu tarabbabin yanda matar shi ta zamo mai halarci a gare shi duk da irin cin fuskan da ya rik'a yi mata.

"Je ka kiramin matar taka", cewar Dad.

Mum ce ta mik'e tana mai cewa bara ta kira ta da kanta, da hakan ta fice har part d'insu ta sako Zajlah gaba, wanda har ga Allah bata so yagayawa iyayen shi wannan abin ba, ta so yabar shi tsakanin su. Cikin jin kunya ta shiga falon ta nemi guri ta zauna tana mai gayar da Dad had'e da yimai ya jikin kanta na nok'e k'asa.

Gyaran murya Dad ya yi bayan ya kar6a mata sannan ya furta "na ga alkhairin da kika yiwa Son, muna masu taya shi godiya, amma zan so ki gayamin ta wacce hanya kika samu wad'annan kud'in?".

Nan ta yimai bayani kan cewa kayan d'akin ta ta saida sai kuma na d'inkin da take yi ana biyan ta. "Ai ko bai dace ki sai da kayan d'akin ki ba, da ki bari ak'ara duba abinda ya dace don har ina shawarar saka mota ta kasuwa musan abinyi".

"Dad wallahi babu komai, a dai saka mana albarka a cikin abinda za'a fara dasu", daga hakan ta tashi sum-sum ta koma falon Mum.

Kowan nen su ya yi jugum saboda gaba d'aya ta kashe masu jiki, don basu ta6a tunanin hakan daga yarinyar ba, nan dai suka tattauna abinda ya dace Alamein ya yi da kud'in.

(Ni dai Jegal na yita baza kunne inji ko za su fad'i adadin kud'in da Zajlah ta bawa Alamein amma shiru abin tamkar had'in baki, don na hango su Hindatu shehu da Fati Salihu ana baza kunne, lolx).

.........

Sana'a ya fara gadan-gadan inda ya shawarci Dad kan yayi zaman shi ya huta shi zai tashi da nema yanzu.
Duk inda yake yanzu da tunanin ta had'e da muradin sauraren muryar ta yake, wanda sai ya ganta hankalin shi ke kwanciya, amma ya lura da ita yanzu wani basarwa take yi, bata cika shiga sabgarshi ba, asali ma indai ba d'inki take yi ba to tana part d'in su Mum don wani lokaci daga can za'a saka masu abinci ko da zai shigo gidan har ta rufe d'akin ta ta yi kwanciyar ta, hakan ba k'aramin damun shi abin yake yi ba.

***

Yau gidan su ta shirya za taje saboda ta kwana biyu bata je ba, nan ta dad'e tana hira da mahaifinta har yana k'ara yi mata nasiha kan hak'uri da halin da suke ciki har yana yi mata nuni da kowane bawa bazai kaucewa k'addarar shi ba, kuma ta rik'a mijin ta hannu biyu ta girmama iyayen mijin ta.

Bayan magrib ne aka aiko yaro ana sallama da Malam Abu, ita ko lokacin za ta shiga gurin Mama Inno ta yi mata sallama don tana son wuce wa gida, abin mamaki motar Dad ta gani k'ofar gidan su wanda ta yi mamakin hakan a ranta, sai kawai ta dake ta fad'a gidan su Salmat saboda tunanin ba shi kad'ai ne mai irin motar ba.
Tana zaune suna hira da Mama Inno sai ga Naja'atu ta shigo da gudun ta tana gaya mata Baba yace ta fito ga mijin ta ya zo d'aukar ta, sai da safe ta yiwa Mama ta fice daga gidan tana ta mamakin wai Alamein ne ya zo d'aukar ta yau, mamakin ta bai k'aru ba sai da ta ganshi da Baban ta suna hira cikin girmamawa da mutuntawa, hakan ta shiga gidan su ta yiwa Mama Asabe sallama ta d'auko jakarta ta fito, nan Baban ta ya shige gida.

Gudun ta shiga gaban ta janyo ma kanta ya sa ta je bud'e k'ofar baya amma ta ji ta rufe, gaban ya bud'e mata sannan ta shiga badan ta so ba. Yau ko gaisuwa bai samu daga gare ta ba sai wani cin magani da take yi, saboda bata ma son irin yanda yake bibiyar ta kaita unguwa ko d'auko ta, wayar ta ta fitar had'e da kunna data tana charting.

Warce wayar kawai ta ji ya yi sai ta bishi da kallo kuma ta sadda kanta k'asa, saboda bata iya jurar had'a ido dashi. Wayar ya rik'a bincike ya ga group uku, na make up, mu koma kitchen sai musha karatu, contacts kuma Salmat, Saudat, Yusrah sai Shema'u ya gani.

"Kasan dai bincike ba kyau, kabani waya ta", cikin zumb'uro baki take maganar had'e da mik'o mai hannu.
Wayar ya mik'a mata tana mik'o hannu ya rik'e ya d'ora saman sitarin motar yana murza yatsun ta, abinda ya tsirga masu lokaci guda yasa ya yi saurin sakin hannun na ta sannan ya d'ora mata wayar saman cinyar ta, daga hakan ba wanda yak'ara magana har suka iso gidan.

K'ofar motar ta rik'a za ta bud'e ta ji ta gam, sai da ya fita ya zaga ya bud'e mata k'ofar ya rik'o wayar ta da jakar ta inda har ta ji nauyin Baba maigadi daya bud'e masu gate, (nidai Jegal hab'a na rik'e nace sabon salo kiran sallah da usur, ina ruwan neman gindin zama, lolx).

***

Ya dad'e yana bibiyar ta tun lokacin da ya rasa Zajlah lokacin tana zuwa school of health. Ko da ya yi tafiya ya dawo ne yake tambayar wani friend d'in shi dake aiki B.L.B plaza kan cewa ya dai na ganin yarinyar, nan yake bashi tabbacin sun k'are makarantar, bincike ya yi har ya gano gidan su yarinyar, inda bai son a kuma samun matsala ya rasa yarinyar saboda ya yaba da hankalin ta had'e da nutsuwar ta, sai dai ga alama za ta d'anyi ji da kai irin na masu kud'i.

Hakan dai ya ji ta kwanta mai a rai, da hakan ya gayawa iyayen shi kan yana so aje mai tambayar neman iznin ganawa da yarinyar.
Manyan shi basuyi k'asa a gwiywa ba suka je gidan su yarinyar inda kuma magabatan ta suka bashi damar shigowa ya gana da yarinyar.

****

Tun da aka gaya mata cewa za tayi bak'o ta shirya tsab sai zaman jiran ganin bak'on na ta. Ba'a fi minti goma da shirin ta ba sai gashi an aiko tazo bak'on ta ya iso. Sit room d'in Dad na bak'i aka saukar dashi shi da wani friend d'in shi, hakan ta je suka gaisa, nan ya Isar da sak'on k'ok'on baran shi zuwa gare ta kuma ba laifi ta yi na'am dashi, nan yake ba ta labarin tun lokacin da ya fara son ta da kuma shakkar tunkarar ta kamar bazai yi nasara ba, da hakan hira ta 6arke tsakanin su.

Lokacin da zai wuce ne ya nemi tayi mai iso ga iyayen ta domin ya gaisa dasu, gidan ta shiga ta yi masu bayani sannan ta fito ta yi masu iso, bayan sun shiga falon ne suka gaisa da mahaifin ta, inda ya yaba da hankali da nutsuwar yaran kuma yana ganin y'ar shi ta dace.
D'akin ta doso sanadiyyar y'ar ta data matsa sai ta zo sun gaisa da sirikin nata, suna had'a ido take gaban su ya bada rasssss!.

.,,..........
Cikin azama ya zabura da k'arfi tamkar wanda ya zauna dama saman allura, wannan dattijuwar fuskar ba za ta ta6a 6ace mai ba.

"Koma ka zauna, ina zaka je?".

Nan ya gagara bata amsa saboda irin tsabar rud'ewar da yayi, cikin murmushin ta dake k'arawa kamilallar fuskar ta fara'a ta nemi guri ta zauna, "a cikin Ku waye sirikin nawa?". Farouk ne ya nuna Fadeel da yatsa yana mai Sosa kai.
Shi ko Fadeel ji yake yi tamkar k'asa ta bude yanitse a gurin, tsabar jin nauyi duk da a wancan lokacin ya bata hak'uri.

Kawai ganin shi suka yi durk'ushe gaban ta yana mai k'ara neman yafiyar kuskuren da yakusa tafkawa. Har ga Allah

Please Login or Register in order to submit comment