Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da suke yi yasa ya tayar da kai ya dube ta. "Kar kayi mamaki kuma kar ka zargi Zajlah da abinda ba haka bane, don tun auren ku wata magana data shafe ka bata tab'a had'a ni da ita ba". "Na dad'e da fahimtar hakan tun ranar da muka je gidan su yiwa mahaifin ta sallama, kuma ko kukan da take yi nasan da biyu take yin shi saboda akwai abinda kayi mata". "Yanzu dai dabara ta rage gare ka ta yanda zaka shawo kan matar ka ku zauna lafiya, don yanzu ka tabbatar da ita ba k'ashin yarwa bace". ** ** Ko da ta shiga d'akin Saudat bacci take yi, hakan ya sa ta nemi guri ta zauna ta bud'e datar wayar ta ta hau whatsap, yanda taji ana comments kan wani novel ( *AL'ADUN WASU, BATUL MAMMAN) ya sa ta yi ta tambayar farkon buk d'in, nan take aka tura mata saboda musha karatu akwai kula juna. Datar ta rufe sannan ta hau karatun littafin, sosai buk d'in ke saka ta nishad'i da walwala, dariyar tace ta tayar da Saudat daga baccin da take yi, had'a ido da suka yi yasa tasha jinini jikin ta saboda jiran saukar rashin mutunci kwando-kwando. Kafad'ar ta ta dafa had'e da furta "matar Brother me ya saka ki nishad'i haka kike ta dariya?". Cikin sanyin jiki ta gaya mata har da nuna mata buk d'in, "kai an baro ki baya ai ni yanzu kullum cikin zuba ido nake in matsu ba'a turo cigaban ba, saboda novel d'in yayi gaskiya ga dariya cikin shi sosai". "Aiko da zan iya dana ajiye karatun har tagama duka, saboda banson jira gaskiya matsuwa nake yi". "Ni ko nafi so ana yi ina biya kodon y'an comments dasu ke baka labari kuma ban iya karatu in yayi yawa". "Tabbb ai ina ga babu group d'in da suka kai musha karatu comments, kuma gasu da kula juna gaskiya, oh! kinga na manta, ya jikin ki?". "Ai naji sauk'i sosai don kan ya daina ciwo", hakan suka zauna suna ta hira wanda ni kai na Jegal nake mamakin hakan.

** ***

Zaune yake jugum yana sauraren maganganun Mum had'e da nazari kan su duk jikin shi ya yi sanyi. "Abu na gaba shine ka dai ga yanda Allah ya sako mana jarabawa farat d'aya wanda bamu yi zato ba kuma bamu yi tsammani ba to ya kama ta ace ka natsu kasan me duniya take ciki, a wancan lokacin in har ina lurar da kai wasu abubuwan sai dai ka rik'a biyar zugar mahaifin ku na rud'in dukiya, yanzu gashi duk tak'amar ku da ji da kan ku da izzar ku ta rushe lokaci guda wanda baku da wata dabara sai yanda wanda ya baku ya yi daku". "A zamantakewar rayuwa ana so mutum yasan k'ima da darajar d'an Adam, ba akan komai ba sai don gama wa da duniya lafiya, wanda ka gani talaka haka Allah ya so ganin shi, ba don ba ya son shi ya yi shi hakan ba, sai dai ban-ban cewa tsakanin rayuwa da kuma hankalta". "Yanzu ka duba kagani yanda Allah ke baiwa kafiri kud'i ya hana wa musulmi, kuma fa ba don ya fi son kafiri d'in akan musulmin ba, a'ah don ya gwada k'arfin ikon shi ne da kuma tsara abubuwan shi yanda yaso. Da wuya kaga kafiri yana fama da talauci tamkar musulmi, ko yaushe za ka ganshi cikin jin dad'in rayuwa, to wannan jin dad'in na duniya shine ribar su gaba d'aya saboda lahira jahannama ce mazaunin su". "Sannan kayi nazarin wacce Sana'a ta dace ka fara, saboda yanzu zama haka kawai ba naka bane, don kaga kaine Babba kuma kaga yanda mahaifinku yake, ko babu ciwo akwai yanayin girma daya kamata kad'auke wa mahaifinka wasu abubuwan". "Ba matsala Mum bari zan binciki Imran da Salis gobe muyi shawara, daga nan asamu mai sayen gidan, in an kammala kud'in sai muga abinda yayi saura sannan asan Sana'ar da za'a kama". "To Allah yasa a fara a sa'a, Ameen ya furta a taka'aice had'e da dogon nazari na rayuwar shi. Duk wad'annan abubuwan da Mum ke jerowa har ga Allah yasan hakane, amma me yasa a wancan lokaci bai yi duba zuwa gare su ba? "Giyar kud'i", hakan wata zuciya ta bashi amsa. Lallai tabbas ya yarda da hakan, saboda yasan in can inda aka fito ne bazai tsaya ya saurari Mum ba har maganar ta tayi tasiri akan shi ba kamar yanzu. Bayan sun gama tattauna wa ne ya k'arasa gurin Dad suka gaisa ya yi mai ya jiki, sannan suka d'an ta6a hira, duk da ba magana mai tsawo yake iya yi ba sosai.
.
WASHE GARI
Wata shawara ce ta yanke a ranta bayan ta kira Salmat ta gaya mata abinda ke faruwa, inda ita ma ta tausaya masu sosai had'e da k'ara k'arfafa mata gwuywa kan abinda za tayi. Bayan ta gama breakfast ne ta jera a dining table sannan ta fad'a wanka ta fito ta kimtsa, sanin cewa yanzu yana gurin Dad ya sa ta shiga ta kimtsa d'akin na shi kamar kullum sannan ta fito ta ci abinci. 11:00am Ta fita zuwa gidan Shema'u mak'ociyar ta, "yau wace rana Zajlah a gidan nan?", cewar Shema'u. "Kai Anty shaidar da za kiyi min kenan, yanzu fa zuwa na na uku kenan gidan nan, ai gara ni kefa zuwan ki biyu". Da hakan dai suka gama zolayar juna sannan suka gaisa, jugum ta yi kamar kar ta furta abinda ya kawo ta, sai kuma take tunanin duk duniya bayan Salmat babu wanda za ta iya gayawa halin da take ciki bayan Shema'u d'in, saboda ta yaba da hankali da nutsuwa irin tata, kuma ba mace ce mai yawan surutu ba ga alama za tayi rik'on sirri kuma gashi za ta girme ta da kusan shekara shida ko bakwai, sai da ta gama nazarin ta Shema'u na gurin kawo mata ruwa da d'an lemo ta dawo kenan take furta mata abinda ke tafe da ita kan ta yi mata magana da masu sayen kayan d'aki. "Ke ko Zajlah me zai kai ki siyar da kayan d'akin ki?, duka fa aure ko wata hud'u bai yi ba za ki siyar da kayan d'aki". Nan ta kora mata bayanin abubuwan da ke faruwa, sannan ta bata tabbacin za ta sa a nemo masu siya. "Kinga ko banyi mutunci ba wallahi ban shiga yiwa Mum Allah ya tsare gaba ba da abinda ya faru, Baban su Taheer d'ai yaje dubiya sau biyu". "Yanzu ko daga nan can zan shiga", "ina ga bara in d'auko hijab d'ina muje tare in dawo". Hakan suka fice zuwa gidan su Alamein, Shema'u ta yi jaje da Allah tsare gaba ta koma gida. ***** Su Imran suka samo masu sayen gida aka yi ciniki suka sai da inda Alamein ya nemi su bashi kwana biyu ya kwashe kayan shi daga gidan, da hakan suka fice zuwa gidan su shi da su Salis. Kamar yanda Shema'u ta yi alk'awari hakan ya sa ta nemo masu siyen kayan d'aki aka dace da masu siyen su cikin daraja Zajlah ta sai da, kayan kitchen sai kayan falo da keken d'inki kawai ta bari.

**

6angaren Alamein kuwa yaje gida gurin Mum sun tattauna yanda abubuwan suka kasance, sannan ya d'ora da gayawa Mum tasa a gyara masu d'ayan part d'in gobe da safe zai samu way'anda zasu kwaso masu kayan su, da hakan ya wuce gidan shi. Motsi ya ji a kitchen alamar Zajlah na ciki, yana son yashiga ya gaya mata ta kimtsa kayan ta zuwa gobe za su koma gidan Mum kuma yana jin nauyin yanda zai yi mata magana, saboda tun zamantakewar su maganar arzik'i bata ta6a had'a su ba, hakan ya sa ya tunkari kitchen d'in gaban shi na dukan tara-tara. Alamar mutum ta ji a bayan ta ta juyo ta ganshi tsaye ya jingina da k'ofa ya sako mata ido, "sannu da zuwa", cikin sark'ewar murya da in ina ta furta hakan. Da sakewar fuska ya amsa mata sannan ya d'ora da cewa "kar kiyi girkin dare saboda yau za mu yi parking kayan mu gobe a kaisu can, don an sayar da gidan kamar yanda kika buk'ata". "Ba matsala Allah ya kai mu lokacin", da hakan ya wuce d'akin shi. Bayan ta gama girkin ne ta ajiye mai nashi ta d'ibi nata ta ci, sai ta yi zugum tana so taje d'akin shi ta had'a mai kayan shi guri d'aya amma bata son abinda zai had'a ta dashi guri d'aya kuma tasan yanzu yana d'akin bai fita ba. Hakan dai ta daure ta nufi d'akin shi, ta fi minti biyar bakin k'ofa tana sak'a yanda za ta Shiga d'akin, jin motsin zai fito yasa ta k'wank'wasa k'ofar. Mamaki ya hana shi bud'e k'ofar ya yi zurum, sai da ta buga a na ukun sannan ya murd'a k'ofar ya ra6e gefe d'aya. Tsaye ta yi tana wasa da yatsun hannun ta sannan ta furta, "kayan kane zan had'a ma". Hanya ya bata alamar ta shiga d'akin, k'ofar ya rufe ya dawo ciki shi ma, ganin hakan ya sa gaban ta ya bada daram!, saboda ta zata fita zai yi don da shirin shi ta ganshi. "Hala kin kammala na ki kayan guri d'aya?", tambayar ce ta doki dodon kunnen ta. "Eh" ta furta a gajarce. "To bara in kama maki aikin saboda suna da yawa". "Ah da ka wuce kawai ai zan iya tunda ba girkin dare zanyi ba", ta furta hakan ne saboda ta fi so ya fita ya bata guri tayi aikin ta za tafi Samun sakewa, amma tasan zaman shi zai takura ta. Shi ma 6angaren Alamein gidan su ya yi niyyar zuwa ya turo Saudat a zuwan za ta kama ma Zajlah had'a kayan, to yasan in har ta zo to Zajlah za ta kama suyi aikin tare ne, amma da ta nuna za tayi ne ya sa ya fasa fitar. Nan dai suka zauna jigum ba mai magana, shi ya yi k'arfin halin bud'e wardrobe yana jido kayan shi yana d'orawa saman gado, sannan ya bata umurnin ta d'auko akwati na ta jera kayan a ciki, ba k'aramin mamaki ta yi ba ganin yawan suturar shi kama daga manyan kaya zuwa k'anana. 6angaren turarukan shi suka koma ana jibga su guri d'aya, ta d'auko wani turare za ta ba shi yasaka a wata jaka karaf hannun su ya had'u guri d'aya, wani shocked da suka ji ne ya sa cikin sauri dukan su suka janye hannun su kowane a tsammanin shi d'ayan ya rik'a, hakan yasa kwalbar ta sauka k'asan tiles ji kake yi tarassss, da sauri ta ja baya sai ga k'afar ta saman kwalbar da ta fashe ta watsu a gurin. K'ara ta saki da k'arfi ta rik'e k'afar tana yarfe hannu, da saurin shi ya zo gurin ta ya bata umurnin ta zauna bakin gado, dak'yar ya samu ta tsaya ya cire mata guntun kwalbar inda jini ke ta zuba, nan ya samu ya yi mata dressing gurin had'e da duban ta irin yanda take ta zubar hawaye tana cije le6e had'e da runtse ido. Nan ya barta ya je ya kwashe kwalbar ya k'arasa had'a kayan, sai murmushi yake yi shi kad'ai ganin yanda ta yi kuka had'e da shagwa6a tamkar wata k'aramar yarinya, hakan ya sa ya ji ta burge shi.

washe gari

Jakar ta ta hannu kawai ta d'auka ta fice daga gidan tunda ya gaya mata zai samu way'anda za su kwashe kayan duka akai gidan su, ko da ta fita ko ruwan Lipton bata sha ba saboda ya gaya mata kar ta kunna komai na amfanin girki, kuma Mum ta kira ta gaya mata cewa za ta yi girkin safe dasu. Karfe 10:00am ta shiga gidan, bayan ta gaida Mum ta yi mata jagora ta k'ara duba jikin Dad had'e da gaida shi sannan suka dawo falo suka zauna. "Meke damun ki naga kina Jan k'afa?", Cewar Mum. Nan ta labarta mata abinda ya same ta da suna gyaran d'aki, jajanta mata tayi ganin abin da d'an sauk'i. "Ina Saudat halan? Banji motsin ta ba". "Ta ji sauk'i yau ta wuce skul, kinsan tun ciwon Dad bata koma skul ba, to suna ta shirye-shiryen exam ta k'arewa shiyasa yau ta je", "ok Allah ya taimaka". "Amein", ta furta sannan ta had'awa Zajlah kayan kari ta kai mata falon ta saboda tasan ba za taci tare da su ba. ***" 6angaren Alamein kuwa ba k'aramin mamaki ne ya cika mai ciki ba da ya shiga d'akin ta da sunan fitar da na ta kayan ba, saboda wayam ya gani ba komai kuma ya san dai ko da aka kawo ta da kayan d'akin ta, asali ma gaban shi aka had'a su saboda ranar Mum ta takura shi dole sai ya tsaya gidan har a k'are aikin sannan in fita zai yi ya fita. D'akin ya gani da alamar an d'auke kaya a gurin, to ko ta kai kayan ta ne wani gurin? Ko kuma ta sa ankai mata can gidan? Ganin bai samu amsa bane ya sallami masu kwashe kayan daga d'akin ta, saboda akwatunan tufafin ta tun safe ta saka almajirai suka kai mata, kujeru kuma da sauran tarkace dama ya sa an fita dasu. Ba'a gama ba sai kusan k'arfe d'aya na rana, saboda wasu na kwashe wa suna kai gidan su can kuma da masu had'awa. Dama part d'in da aka basu babban falo ne mai d'auke da d'aki biyu da suke fuskantar juna kowannen su ciki da falo sai toilet a cikin su, kamin a Shiga falon akwai kitchen da store, sai kuma 6angare d'aya toilet d'in tsakar gida. D'aki d'aya aka saka mata na ta kayan a falo sai katifa uwar d'aka, shi ma aka saka mai na shi kayan d'ayan d'akin. Da hakan aka kammala komai na gyara gurin. Zajlah da Saudat suka taya Mum girkin dare sai da suka gama ne sannan ta shiga part d'in su ta yi wanka akan tsabar gajiyar da take ji, abinci ta ci sannan ta je ta kwanta saboda dama Mum ta sako masu nasu wanda dashi ta shigo ta d'ibi na ta ta ajiye mai sauran. Bata fi minti goma da kwanciya ba bacci ya yi awon gaba da ita. Ko da ya shigo bai ji motsin ta ba hakan ya sa ya ci abinci ya yi wanka, jin ya yi yana son yaduba ya yanayin k'afarta yake, da hakan ya doshi d'akin ko da ya shiga tana kwance uwar d'aka saman katifa daga ita sai wata night gown mai d'an sharara sai dogon wando gashin kan ta ya bazu saman filon da ta yi matashi dashi, kallo d'aya ya yi mata ya kauda kai saboda wani abu daya ji ya tsirga mai, kuma bai ta6a ganin mace a irin yanayin da ya ganta ba, bakin katifar ya dawo ya zauna ya kai duban shi ga k'afarta yaga gurin har ya soma haushi kad'an, hannu ya kai zai ta6a gurin kuma ya fasa daga hakan ya zabura ya fice daga d'akin tamkar wanda aka tsikara.

***

Tana tashi da asuba ta gabatar da sallah had'e da azkar d'inta sannan ta koma saman katifa ta zauna saboda ba aiki za tayi ba don Mum ta gaya mata da safe za'a kawo masu breakfast, tana so ta shiga part d'in su ta taya Mum aiki kuma tana ganin ta yi sauko dayawa, don tasan saurin karyawar su gidan k'arfe 10:00am. Kud'in ta ta jawo ta irga ta koma maidawa ta ajiye a tunanin ta lokacin buk'atar su bata yi ba. Bugun k'ofa ta ji ya sa ta zabura ta fito ta bud'e, Mama talatu ce ta kawo masu kayan breakfast bayan ta kar6a ne ta gaida ta ta koma daga ciki, abinci ta ci sannan ta shiga wanka bayan ta kimtsa ne ta shiga gurin su Mum. **** Bayan azzahar ne Salmat ta kawo mata ziyara, bayan ta gaisa da Mum ne take tambayar jikin Dad inda Mum ta gaya mata ya samu sauk'i sosai. Part d'in Zajlah suka koma aka baje sai hira ake ta zabgawa had'e da shawarwarin abubuwan da suka shafe su.
.
Akwana a tashi yau satin su biyu kenan a gidan su Alamein, wanda har yanzu babu labarin Alh Ibrahim sai dai a ko yaushe suna masu sauraren zuwan shi, jikin Dad kuma ya yi sauk'i sosai sai dai bai iya doguwar tafiya haka kuma bai cika son doguwar magana ba don in ta yi tsawo ji yake yi tamkar numfashin shi ya d'auke. Kusancin su ya sa abubuwa sunyi sauk'i sosai a zamantakewar su, saboda Alamein na ba ta kulawa gwargwado, kuma wani lokaci sukan had'u part d'in su Mum a baje ana ta hira, amma fa baza su iya hira tsakanin su ba saboda kowa tsorace yake da wani. *** 6angaren Zajlah an samu k'aruwar wayewa a gare ta ta hanyar Anty Shema'u da kuma group-group na whatsap musamman na kwalliya da ake turo videos na kalar kwalliya iri-iri, wasu ma in an turo bata gane ba to gidan Shema za taje tayi mata bayani in ma ta kama ta zauna tayi mata to za ta yi mata da kanta. Tun lokacin da aka yi mata aure Mama Asabe da Mama Inno basu zo gidan taba sai kwana biyu da suka wuce, koshi don ta dame su ne kan basu tahowa kuma Mum tasa baki shiyasa suka zo, inda taji dad'in zuwan su sosai. ** Yau saura kwana biyu auren Yusrah da Imran, su Zajlah babu zama musamman da Mum ta mayarda Yusrah gidan kacokan, a cewar ta ita za ta shirya abar ta, duk wani kayan had'in gyara na jiki ko na Mata a tare Mum ke had'a masu shi wato Yusrah da Zajlah, inda Zajlah ta fito real amarya sai wani k'amshi suke zabgawa ita da Yusrah. Kamar yanda Yusrah ta k'udurta ma ranta tun auren Zajlah haka ta gaya wa Mum cewa makarantar su Zajlah za'a yi mata walima saboda bata son bidi'o'in nan na raya Al'adu, ba k'aramin dad'i suka ji ba na za su ziyarci makarantar su, ko banza sun San cewa tsarin Malaman su da d'aliban na burge mutane da dama.
,
A gurin walimar ne suke jin labarin auren Ustaz Yusuf da kuma Ustaz Lukman sati biyu da suka wuce, inda matar Ustaz Yusuf ke basu tabbacin har mazan su sun zo auren kuma tare da gudummuwa, nan suka yi masu fatar alkhairi aka k'are walima kowa ya kama gaban shi. Washe gari bayan d'aurin aure ba'a gabatar da komai ba sai dare amarya ta tare a gidan ta dake ni'ima inda basu da wani nisa sosai da Salmat, Zajlah ne da Saudat suka tashi za su fice ta dafa kan Yusrah had'e da furta "muna jiran baby nan da wata goma, saboda ke ga su wance anji hud'uba ta sai wani tartsin yawu ake mana", tana maganar ne had'e da kallon Salmat tana murmushi. Sanin cewa tsokanar ta ne take yi ya sa ta yi shiru ta k'yale ta sanadiyyar yanzu baki ya mutu ko dogon surutu bata so. Da hakan suka watse suka bar Yusrah had'e da yi mata fatan alkhairi. *** Bayan kwana uku ne da auren Yusrah Alh Ibrahim ya diro garin Jega, direct wayar Dad ya kira kuma akayi sa'a da babu kowa a tare dashi, kuma gashi su Mum basu yi mai bayanin komai ba. Wayar ya d'aga suka gaisa ba tare da yasan waye ba, daga baya Dad ke tambayar shi waye halan saboda bai gane mai magana ba, amsa ya bashi da cewa wani tsohon aminin shi zai kawo mai ziyara, ba tare da tunanin komai ba ya gaya mai address d'in gidan shi. Suna gama waya Mum na doso d'akin na shi, nan yake gaya mata zai yi bak'o duk da bai san waye ba, ya dai ce mai tsohon aminin shi, take nan gaban Mum ya bada rass, saboda jikin ta na bata Alh Ibrahim ne, ganin jikin ta ya yi sanyi ya sa yake tambayar ta ko lafiya, cikin yak'e take bashi amsa da ba komai, "bara inje ad'an tanadi d'an abin motsa baki wa bak'on", da hakan ta fice daga d'akin ba tare data jira me zai ce ba. Wayar Alamein ta kira had'e da gaya mai duk inda yake yayi sauri yak'araso gida. Lokacin yana tare dasu Imran suna process d'in wane business ya kama ta su fara, nan ya yi masu bayani da sauri ya wuce gida. A gate suka had'u da juna dai-dai yana waya da Dad yana gaya mai gashi ya iso gidan, nan Alamein ya tsaya suka gaisa Alh na ta mamakin girman shi, da hakan ya yi mai jagora cikin fargaba suka doshi hanyar shiga falon. Sai yanzu Mum ke nadamar rashin gaya mai da basu yi ba, ba akan komai ba sai akan matsalar ciwon da yakan iya tashi farat d'aya wata babbar matsala ta samu, saboda ko dawowar su Alamein gidan bata gaya mai ansayar da gidan su bane, kawai ta ce mai wani gyara ake yi gidan in an gama za su koma, wanda ga wancan lokacin take hango hakan a zuwan mafita sai yanzu take nadamar aikata hakan.

A DALILIN GATA Page 26-30
.



Alamein gaba Alh yana biye dashi suka shigo falon, karaf idon su suka had'e guri d'aya inda Dad ya yi mutuwar zaune, idon shi ya fara murzawa domin tabbatar da ba mafalki yake yi ba, bud'ar bakin shi kenan zai kira sunan shi wani irin tari ya taso mai, yi yake yi ba k'akk'auta wa, da saurin Alamein ya taso ya dafe mai gaba had'e da jero mai sannu ba adadi, Mum ce ta mik'o kofin ruwa Alamein ya bashi.

"Dad ka kwantar da hankalin ka duk abinda ake ciki munsani kuma insha Allah komai zai zo normal", Alamein kenan dake son kwantar wa Dad da hankali, saboda tsorace yake kar ciwon shi ya tashi. Cikin ikon ubangiji ba wani abu na tashin hankali daya samu Dad, sai dai daka ganshi kasan juriyar da ke tare dashi ba tashi bace shi kad'ai sai da ya aro wata. Mum kanta hankalin ta tashe yake, hakan dai ta jure ta baje ma Alh Ibrahim kayan motsa baki da abinci, bayan gaishe-gaishe ne na yaushe rabo Dad ya kai duban shi ga Alh Ibrahim had'e da furta "muna zaune kawai sai ga sak'on rasuwar ka ta risk'e mu, wanda bamu yarda da hakan ba sai da na garzaya da kai na kurmi sannan aka tabbatar min da hakan, sai kuma yanzu gashi ka dawo, meke faruwa halan?".
Gyaran murya ya yi sannan ya fara basu labari kamar haka, "lokacin da wutar ta tashi gidan gaskiya bana ciki na fita siyen tea bakin titi, saboda akwai wani da Allah ya had'a jinin mu dashi wato Alh D'anjimma wanda kusan tare muke lamurran mu dashi, duk wasu abubuwa tare muke yi".

"Daren da wannan

Please Login or Register in order to submit comment