Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko matsi tsakanina dasu duk abinda suke so shi nake so saboda haka babu maganar ki za6ama son abokiyar rayuwa sai ranar da yaganta da kanshi yakawo ta". Suna cikin maganar ne sai ga Alamein da Saudat sun shigo d'akin, bayan sun gaida mahaifan sune suka nemi guri suka zauna. Sai da ta tattara hankalin ta a gare shi sannan ta fara magana cikin hikima da basira. "Alamein matsayi na na mahaifiyar ka data shayarda kai kuma ta raine ka da gudun 6acin ranka in na nemi wata alfarma gurin ka za ka iya yimin ita?". "Haba Mum miye duniya bazan iya yi maki ba? Duk duniya banda tamkar ku ke da Dad sai kuma Lil". "Da kyau Son! Mata na nema ma mai hankali da nutsuwa ga ilmi wanda nake fatar inka amince aure nan da wata d'aya indai har iyayen yarinyar basu yi mata miji ba". Yanda kasan ana kid'a ganguma haka zuciyar Alamein ke bugawa, cikin abinda bai wuce second biyar ba zufa ta wanke mai fuska duk da sanyin A.c da fanka da suka yalwata d'akin. "Aure kuma? Mace? Ni da kaina? Bazai yuyu ba, miye abin so ga Mace d'in? Me zan yi da ita? Tauyewar rayuwa kawai". "Anya zan iya bijirewa buk'atar Mum? Duk k'ask'anci na nasan darajar mahaifa na, in na yi mata hakan banyi biyayya ba", duk a cikin zuciyar shi yake wannan tunanin. Ka aure ta kawai in ya so daga baya ka mak'ala mata wani sharrin ka sake ta kawai. "Bazan so in zamo mai rayuwar auri saki ba shiyasa tun farko Mace ba ta gabana". Duk a zuciyar shi yake ta sak'a wad'annan maganganun da ya rasa samun mafita akai. "Mum ina fatar ba wannan maganar ce silar zuwan mu gidan su wannan kucakar yarinyar ba? Me Brother zai yi da wannan mitsitsiyar yarinya, kuma ma y'ar talakawa haba Mum". Maganar Saudat ta dawo dashi hayyacin shi daga tunanin da ya cunkushe mai zuciya. "Y'ar talakawa fa? Duk yanda naci buri akan auren Son da bak'i daga k'asashen waje a hakan zan tozarta?". "Alamein". Kai ya d'ago ya kai duban shi zuwa ga Mum had'e da saka handkerchief yana sharce zufan da ke karyo mai ga jiki ta ko ina. "Amsar ka nake jira in har ka amince shikenan, in ma baka amince ba ka gayamin bazan tilasta kaba, sai dai ina hango alkhairi tattare a zaman takewar ku". "Mum na amince". Da hakan ya mik'e ya fita daga d'akin zuciyar shi tamkar ta fashe. "Alhamdulillah! Allah na gode ma, yanzu sai ayi haramar zuwa neman aure". "Ke kuma fitsararriya da kike maganar y'ar talakawa ce na gaishe ki y'ar k'aruna, a hakan dai ta fiki mutunta mutane, ta shi ki 6ace min dagani". Cikin 6acin rai Saudat ta mik'e sai da ta kai k'ofar fita ta furta "Allah yasa anmata miji kuma har an saka rana", sannan ta fice da sauri. Murmushi Dad ya yi had'e da ce wa "wannan auren kan ki za ki d'aurawa shi saboda babu mai son shi". "Saboda son kai da rashin hango abinda nake hangawa ba, amma nan gaba za ku gane inda na dosa.
.
Cikin sauri suka gaggauta shiryawa suka hau hanyar makaranta. Suna fita suka ci karo da mutumen kamar kullum sai dai sa6anin kullum yau ya fito ya jingina da motar yana waya idon shi akan su tamkar maye. Hakan suka gilma ta gaban shi suka wuce, sallamar da ya yi ce yasa Salmat ta ja birki ta tsaya had'e da rik'e hannun Zajlah dake neman fincikewa. Amsa sallamar ta yi sannan ta nemi ci gaba da tafiya, ganin ce wa in ya k'yale damar shi ta k'arshe za ta wuce, nan ya furta. "Don Allah ki taimakamin da number k'awar ki ina so zanyi magana da ita, na yi tunanin bai dace in tsayar daku saman hanya ba shiyasa nake neman lambar muyi magana a tsanake". Tana ta yar da kanta karaf idon su suka had'e take hoton abinda ya faru ranar ya dawo mata tangaragan, da sauri ta kauda kanta had'e da furta. "Malam kayi hak'uri banda waya kuma an yimin miji, sai an jima". Hannun Salmat ta fincika da k'arfi suka fice wanda Salmat sai mamakin ta take yi fal a ranta. "Haba (ZAZ) wannan abin dame yayi kama?, ke ce fa a kullum ke yi muna nasiha kan ce wa wulak'anta d'an Adam bai da kyau amma ga shi yanzu kin yi da kan ki".
.
Nan Zajlah ta ba ta hak'uri had'e da ba ta labarin abinda ya faru, sannan ta d'ora da ce was' "a ganin ki wannan ko mijin aure na rasa ya dace da rayuwa ta?". "Duk da hakan ya kama ta ki yi masa uzuri don baki sani ba ko godiya zai yi maki, ko kuma yana tafe da wani abu mai muhimmanci". "Ko ma miye yanzu shi ta sha fa don ba ya gaba na". Da hakan suna tattauna wa har suka kai makaranta. ** "Daddyn Alamein banji kace komai ba har yanzu kan maganar yarinyar, wallahi ina hango alkhairi ne tattare cikin wannan auren in har ta yiyu". "Me kike so ince? Ai magana na hannun ki saboda yanzu ke ce mijin ni ne matar, tun da har kika iya k'udurta neman auren ba da yawu na ba". "Haba abin bai kai haka ba, yanzu ya kamata mukai k'arshen magana kan turawa gidan su yarinyar, in kuma har kana ganin abar maganar ne wallahi ba matsala sai abar ta". "Tu da kin yi magana da Son har ya amince ni me zance? Yanzu ki fara bincika wa kiji in har ba'a yiwa yarinyar miji ba sai kiyi k'ok'arin samun wa'anda za ki tura ayi maganar don bazan sa kai na ba cikin abinda yaro na bai so ba". "Shikenan ba matsala za'a yi yanda ya dace tunda Abban Yusrah na da rayuwar shi, kuma ko da ran ka shi ne waliyyin shi". Da hakan ta fice daga d'akin ta shirya sai gidan su Zajlah. Bayan sun gaisa da Mama Inno ne ta sako mata buk'atar da ke tafe da ita kan tambaya in ba'a tsaidawa Zajlah miji ba kan za su turo manya domin ne mawa yaron su ita. Nan Mama ke tabbatar mata ce wa Zajlah ba tada miji, har suka ajiye kan ce wa za'a turo manya, da hakan Mum ta fice daga gidan. ** Yana batun fice wa ne suci abinci Mama inno ta tsayar da shi take gaya mai abinda ke faruwa. "Kin ga abinda nake gudu, shiyasa nake matsawa Mal Abu kan ce wa yasamu mata yayi aure tunda ya samu lafiya kafin yaran nan su samu mazajen aure, ga shi har an fara zuwa neman su bai da mata, kuma bai dace ayi auren d'aya daga cikin su bai da iyali ba". "Yo in haka ne abar min maganar zan tuntu6i k'awata Asabe in har ta amince sai ayi auren nan da sati d'aya tunda dukan su ba yara bane kuma tana da hankalin ta da nutsuwa, kasan ita ma mijin ta rasuwa yayi". "To shikenan sai munji daga gare ki duk yanda kukayi". Da hakan ya sa kai ya fice zuwa mazaunin su yana mai labarta wa Mal Abu maganar neman auren shi tunda ya k'i nemo wa da kanshi had'e da gaya mai za'a zo neman auren Zajlah. "Ba komai Mal Inuwa Allah ya tabbatar da abinda yafi zama alkhairi, na gode sosai da karamci Allah yabar zumunci". Amein ya furta a tak'aice. Saboda hakan yake jin Mal Abu tamkar d'an uwan shi na jini. ** BAYAN SATI BIYU Anyi auren Mal Abu da Asabe wanda ta tare gidan, suna zaman su na fahimta akan su duka ba yara bane, kuma Asabe Mace ce mai hak'uri da sanin ya kama ta don bata san inda take aza Zajlah ba kan kulawar da take ba ta. Cikin hakan ne Zajlah da Salmat suke zama duk gidan da suke so tsakanin wurin Mama Inno da wurin Mama Asabe. A 6angare d'aya kuwa k'anen Baban Alamein wato Alh Muttak'a Mum ta nema had'e da d'ora mai nauyin maganar auren Alamein, domin halayyar su ba d'aya ba shi da Dad, mutum ne mai karamci da iya zama da mutane. Wanda karamcin shi da sanin halayyar shi ya sa yana tunkarar su Mal Inuwa da magana take nan aka ba shi Zajlah, saboda a tunanin su yaron gurin shi ne ke son ta.
.
Ustaz Yusuf ne da Ustaz Lukman ke tsaye suna tattauna wa akan tafiyar da tsarin makantar su kan musabak'ar da za'ayi nan da next year. A tsayen da suke ne suna tattaunawar d'alibai ke wuce wa ta gurin suna gaida su ciki kuwa har da su Zajlah. "Wai har yanzu baka tunkari yarinyar nan da maganar cewa kana son ta ba?, kasan fa ance abari ya huce shi ke kawo rabon wani, kar wani ya yima shigar sauri". "Bazai ma kawo ba saboda ina nan da shirin tunkarar ta kwanan nan insha Allah, akwai abubuwan da nake jira ne da komai ya kammala zan tunkari mahaifin ta". "To Allah yataimaka yasa kuma rabon kace, da na yima murna sosai saboda hankali da nutsuwar yarinyar". A hakan dai suka k'are tattaunawar suka shiga cikin makarantar domin fara karantar da d'alibai kamar kullum.
**
Tun ranar da aka sanarda shi maganar tsayar da ranar auren shi da wacce bai sani ba ya shiga tashin hankali marar misaltuwa wanda daka kai dubanka zuwa gare shi za kasan ya fice daga hayyacin shi. A kullum tunanin shi da wanne ido zai kalli friends d'in shi da kullum yake cika bakin kan cewa Mace ba ta gaban shi, wanda a kullum maganar shi bata wuce shi aure baya gaban shi. K'arar rufe k'ofa ce ta dawo dashi hayyacin shi wanda kan tsabar tashin hankali idon shi har sunyi ja, guri ta nema ta zauna sannan ta fara magana. "Yanzu Brother kana gani za ka zuba ido a d'aura ma aure da wannan yarinyar? Wallahi talakawa ne sosai kuma da ka ga yarinyar za ka shaida cewa ko boko batayi ba, ko kusa baku dace ba wallahi". "Ya kama ta in ma aure ake so kayi to a baka dama ka zak'ulo yarinya mai class ba kamar waccan kucakar ba". A kasalance ya tashi daga kwancen da yake ya saka filo a bayan shi ya jingina da gado, ido ya sako mata tamkar yayi kuka. "Ni ba ma yarinyar ce ta dame ni ba kamar auren da za'a yimin a dai-dai wannan lokacin da ban shirya ma abin ba, sai dai wani hanzari ba gudu ba bazan iya bijirewa buk'atar Mum ba a gare ni zanyi mata biyayya insha Allah". "To Brother Allah yaba ka iko, kuma yasa auren ya zamo alkhairi a gare ka kamar yanda Mum ke furta wa". A tak'aice ya amsa da Ameen. "Amma ya kama ta ka gayawa su brother Imran saboda fara shirye-shirye, kaga sati biyu ya rage har auren". Wayar shi ya d'auko ya mik'a mata had'e da bata umurnin ta kira Imran da Salis ta gaya masu yana neman su yanzu. Cikin mintunan da basu wuce goma ba suka iso gidan, Mum suka fara biyawa suka gaida sannan suka wuce part d'in shi saboda ba suda shamaki da gidan. Bayan sun shiga d'akin ne suka tarar da Saudat na rarrashin shi kan ko tea ne yasha Wanda duk ya fara jemewa, dak'yar yasha tea d'in kad'an sannan suka gaisa. Nan Saudat ke labarta masu abinda ke faruwa, kowannen su mamaki fal a ran shi. Sai dai jin cewa za6en Mum ne suka ga cewa lallai gata ne aka yimai. Nan dai suka tattauna yanda abubuwan za su kasance, amma ya jajirce kan ba za'a yi komai ba bayan d'aurin aure, a hakan suka biye mai saboda sanin hali. *** 6angaren Zajlah kuwa mamaki ne fal a ranta kan ce wa an tsayar da maganar auren ta da wanda bata sani ba, kuma har yanzu bai zo gidan su ba, to wannan waye shi? Tasan dai ba wanda suka gani a mota bane. Koda jiya ankawo kayan sa Lalle har da lefe duka, anan take jin ana fad'ar cewa mijin bai Nigeria sai ana saura kwana biyu aure zai dawo. "ZAZ mu gayawa Mama ta fitarwa y'an ajin mu da ta su alawar da kuma malamai". "Wannan aikin na kine, ni dai inkin shirya ki fito mu wuce kinga ko jiya mun kusa makara har Ustaz Yusuf na mana fad'an mun fara rashin mayar da hankali yanzu". "Ke kam yanzu da mayar da hankali da rashin mayarwa duk uwar su d'aya ubansu d'aya, saboda dole ki jingine makaranta". Muguwar harara Zajlah ta sakarwa Salmat wanda yasa cikin sauri ta fad'a d'akin Mama Asabe ta d'ebo iya adadin alawar da zasu baiwa y'an ajin su da malamai suka fice. Ustaz Yusuf ne ke rarrashin Ustaz Lukman kan tashin hankalin da ya shiga sanadiyyar alawar da Salmat ta kawo masu had'e da bak'in labari a cewar shi. "Tun ba yau ba nake lurar da kai kan ka gaya mata muradin ka a kanta amma ka tsaya sanya ga abinda ya faru yanzu". Magana kan ta kasa yin ta yake yi saboda sai ya bud'a ba ki ya kasa furta komai. A hakan ya buga mashin d'in shi ya fice daga makarantar da ya ga ta koma mai tamkar
.
Bai gasga ta maganar ta ba har sai da ya tura manyan shi da maganar aure aka tabbatar mai cewa auren ta saura sati biyu. Har ga Allah ya so yasa mu yarinyar a matsayin abokiyar rayuwar shi, har kullum yazo kwanciya muryar tace ke yimai amsa kuwar maganar da ta yi mai, a tunanin shi duk wanda ya sa me ta ba k'aramar sa'ar rayuwa yayi ba. Fadeel kenan yaro ga Alh Ibrahim da Haj Fatima wanda yataso cikin gata da jin dad'in rayuwa har yake tunanin zai iya taka kowa ba tare da antakura shi ba. Sai gashi yanzu ya yi sanyi sosai tamkar ba Fadeel ba sanadiyyar soyayyar da ya d'orawa Zajlah tun ranar da ta rik'e mai hannu had'e da yimai nasiha kan abinda ya kusa aikatawa, sai gashi kuma ashe ba rabon sa bace.
***
Imran ne had'e da Salis suka zo k'ofar gidan su Zajlah, bayan sun gaisa dasu Mal Abu ne suka yi masu bayani kan cewa abokanen Ango ne ya turo su gurin Zajlah ne. Da hakan Mal Inuwa ya shiga gidan shi ya gaya masu su shirya suna da bak'i saboda suna gidan shi. Shimfid'a aka yi masu a zaure ya fito ya gaya masu su shiga daga ciki. Zaman su bai wuce minti biyar ba Zajlah da Salmat suka fito nan suka gaisa duk da basu san su waye ba. Sarkin tsokana ne Salis ya yi gyaran murya had'e da furta. "Amaryar mu ya kike?".
.
Nok'e kan da tayi ne ya bayyana cewa ita ce amaryar, a ranshi yake k'iyasta lallai Mum ba k'aramin gata tayi wa Alamein ba saboda Zajlah ba tada makusa ko kad'an, don ga alama inta sa mu guri za tafi haka fresh. Gyaran murya Imran ya yi ya kai duban shi ga Salmat yana mai tambayar ta abubuwan da za suyi na aure. "Gaskiya babu abinda muka shirya sai walima wacce za'a yi cikin makarantar mu ranar juma'a ana gobe d'aurin aure". Wani dad'i ya ziyar ci zuciyar su Salis duka sanadiyyar jin ra'ayin su d'aya da Alamein. Yanzu sun sa mu hujjar da za su kare kansu ga friends d'in su koda sun dame su da tambayar ya akayi biki babu wasu events, za su basu amsar amaryar ustaziya ce. "Ashe Ustaziya zamu aura bamu sani ba, to Allah sanya alkhairi ya had'a hankulan ku", cewar Imran. Waya Salis ya fitar yana kira tak'i shiga yakai duban shi ga Imran yana mai cewa' "ka ga wayar mutumen ta k'i shiga yana yuyuwa network ne ba kyau, kuma gashi ya ce yana so yaji zazzak'ar muryar amaryar shi". Ido d'aya ya kashewa Imran saboda ganin ce wa bai fahimci inda yadosa ba har yana batun magana ga shi yana gudun ya kwafsa mai. "Tun da ba'a sa mu wayar shi ba sai ki ba da taki number a tura mai ku gaisa kamin yadawo". "Wallahi banda waya, saboda su Baba sun hana mu rik'a waya". Ba k'aramin dad'i yaji ba da amsar da ta bashi, saboda ya san ko number ya kar6a ko kallo bata ishi Alamein ba, asali ma za ta iya zama silar samun sa6ani tsakanin su. Dubu hamsin suka zube masu domin hidimar aure inji Ango a cewar su. Da hakan sukayi sallama dasu suka fice had'e da yaba hankali da nutsuwar yaran. *** Tabbas yau ya tabbatar da cewa a bari ya huce shi ke kawo rabon wani, "gaskiya ba k'aramar asara nayi ba da ban sa mu Zajlah a matsayin mata ba, saboda ban zaci wannan risk'in ba ko kad'an". "Ko da ance wani bai auren matar wani Allah bai k'addar to aure tsakanin mu ba dole inyi hak'uri in fawwala ma Allah lamari na, takan yuyu ba ita ce alkhairi a gare ni ba". Duk a zuciyar shi yake wannan tunanin yana cikin tsananin tashin hankali, a hakan ya tashi ya yi nafila raka'a biyu had'e da addu'o'i ta ke yaji nutsuwa ta sauko mai.
**
Suna koma wa gidan ne Salis ya saka Alamein gaba da surutu har yana ce mai, "Gaskiya friend ka gode ma Allah da wannan gatan da Mum tayi ma, wallahi ta za6o ma Mace mai hankali nutsuwa da ilmin islama, ko fa waya ba'a bari ta rik'a gidan su wallahi hakan ya burge ni sosai". "Saboda waya ga budurwa ba k'aramar illah bace, itace jigo na farko dake fara taka rawa a lalacewar tarbiyyar yara". "Duk wannan kai ta shafa kuma matsalar kace ba tawa ba, ina ruwan k'wai da aski, kuma in ka zo ne kacika min kunne da surutu sai in ta shi in ba ka guri, saboda na ga ka zo da sabon salo kiran sallah da usur". "Wa ne ni in takura Ango, ai sai dai ni in d'aga in ba ka guri". Hakan ya gama zolayar shi suka fice daga gidan. (Ina so inyi kira gare mu iyayen yara akan sake ma yaran mu domin amfani da waya, muna ganin tamkar burgewa ce ko wayewa to gaskiya wannan bai yi ba. Ba'a ce kar ku bari yaran ku suyi amfani da waya ba, sai dai ya kama ta ku saka ido akan kowan ne tako na yaran ku saboda kaucewa fad'awa hatsari. Kar kice ai shiriya ba a hannu na take ba ga Allah take, kulawar ki zai sa Allah yadubi zuciyar ki ya tallafa maki gurin d'ora tarbiyyar yaran ki akan hanya madai-daiciya. Gare ku y'an mata, ina mai kira zuwa gare ku daku tsalkake zuciyar ku akan mu'amala da waya domin sharrinta ya fi alkhairin ta yawa. Ya Allah don darajar sunayen ka tsalkaka, don k'udurarka don iradarka don k'arfin mulkin ka ka shirya mana y'ay'an mu Maza da Mata.)

A DALILIN GATA Part 11-15
.


Sun baro part d'in shi ne suka had'u da Mum har za su fice daga gidan, bayan sun gaisa ne take tambayar su shirye-shiryen da suke yi a game da auren. "Gaskiya Mum babu wani abu da za muyi, saboda yanzu haka daga gurin yarinyar muke ita ma babu wasu events a tsarin ta, walima kawai za su yi a islamiyar su". "Ni ma ranar assabar zan had'a k'aramar liyafa insha Allah. Ku cigaba da lurar da mutumen ku had'e da shawarwarin da suka dace, Allah yak'ara had'a kan ku yabar zumunci". "Ameen Mum, ai tsakanin mu da Alamein sai dai godiya don ya yi mana duk yanda ake yi", cewar Imran. Nan Mum ta wuce bedroom d'in Dad, ta bi shi da ido hankalin shi kwance yana karatun jarida. Gefen shi ta samu ta zauna sannan ta fara magana. "Ya kama ta a fara shirye-shirye, na ga ko I.V baka bugo ba gashi lokaci sai k'aratowa yake yi". "Kisa a buga ko Abban Yusrah yasa a buga don ni na fad'a maku bazan saka baki na a wannan auren ba har sai na ga cewa Son ya sauko yana walwala kamar kowa". "Yo ko yanzun ce ma akayi baya son maganar?, ni fa na rasa gane wane irin mutum ne kai, don Allah kayi hak'uri ka saka ma wannan auren albarka". Dak'yar da lallami ta samu ta shawo kanshi ya sauko har suna tattaunawa kan abubuwan da suka dace ayi na auren.
***
Akwana a tashi wataran jariri ango ne, yau dai ga shi har ansaka Zajlah a lalle duk wani abu da za'a yi na al'ada 6angaren amarya da ango duk anyi, inda a 6angare d'aya Amarya tasha gyara daga wata shuwa dasu Mama Asabe suka d'auko musamman domin wannan rana. Yau ce ranar da za'a yi walimar Amarya a makarantar su, inda ba k'aramin jurewa Ustaz Lukman ya yi ba cikin Maluman da suka gabatarda walimar. Amarya tasha nasihohi sosai ga Malaman ta sai dai fatar d'orewar zaman lafiya ita da angon ta. "Yanzu Yusrah duba kiga wai wannan yarinyar ce Brother zai aure, da ace auren da yake so ne da events da za'a sai mun ture". "Ai ko hakan ba laifi, don ni dai abin ya burge ni sosai har ina tunanin in aure na ya tashi ni ma irin wannan walimar za'a yiman". "Ni kam wallahi ranar aure na sai an gwangwaje bazan yi irin wannan ba, kinga har Mum ta biye wannan abin wai ita ma za tayi liyafa gobe". "Ke inda Dad na son wannan auren ai wallahi da yanzu gari ya d'auka tun ana saura wata d'aya auren, amma duba yanzu wai gobe d'aurin aure amma abu shiru tamkar mutuwar sarkin gari". Dariya sosai Yusrah ta yi tana mamakin wannan ak'idar ta Saudat na k'yamar talaka, ta san da ace Zajlah masu kud'i ne to da duk yanda suka tsara abin ba za ta kushe ba. "Mu wuce gida Yusrah tun da an k'are". Maganar Saudat ce ta dawo da ita hayyacin ta. "Kibari mutane su rage sai mu gaisa da amaryar sannan mu wuce, kin ga yanzu jama'a sun mata yawa". "Don Allah ki wuce muje, ai dai tasan ba za'a rasa zuwa daga dangin Angon ba kuma munzo buk'ata ta biya ai shikenan". "Miye amfanin kiran sallar kurma?", ce war Yusrah. "Ban fa fahimce ki ba, ke sai ki rik'a je fawa mutum magana a dunk'ule". "Ke kuma ga ki ba cikakkar bahausa ba, to ina nufin miye fa'idar mu zo bamu gaisa da Amarya ba mu fice". "To ni dai ba don ta na zo ba, saboda yaya na nazo kuma babu lallai sai na tsaya". "Yo ai duk d'aya an cewa shege marar uba". Maganganun na Yusrah suka ishe ta ya sa taja bakin ta ta tsuke, ba don ta so ba ta tsaya

Please Login or Register in order to submit comment