Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya nuna da yatsa "kaga ajiya ta nan", kallo aka bita dashi wanda ya yi silar k'ara jin kunyar ta tamkar ta nitse. Zajlah kanta ta yi mamakin faruwar hakan, inda Alamein ke dubin me Salis ya hango a wannan fitsararriyar. Da hakan dai suka ke6e suka k'ara tattaunawa tsakanin su, inda soyayya mai k'arfi ta d'inke tsakanin su. Sai da suka yi girkin dare suka ci sannan kowa ya kama gaban shi. Alamein ko anci darajar Yusrah don ita ke saka mai abinci wanda Zajlah bata nuna mata cewa ita kad'ai ke girkin taba, kuma tasan ganin mutane ya sa shi kan shi yaci abincin.
.
Awanni sun shud'e, kwanaki ma haka, wanda yanzu auren Zajlah da Alamein ke cikin wata na biyu amma ba wani canji tsakanin su kowa sabgar gaban shi yake yi, inda Zajlah d'inkin ta kawai ta saka ma gaba don tana samun customers da dama ta gurin Salmat, Yusrah da kuma Shema'u. * * 6angaren Salmat kuwa magana ta yi nisa tsakanin ta da Salis inda manya suka shiga gida har an saka ranar auren su. Aikin ta ta gama cikin lokaci saboda za taje gida wurin ganin Baban ta daya dawo daga saudiya jiya. Ba tada niyyar gaya mai komi saboda dama yanzu kusan kwana biyu sai taje gidan Mum, wani lokaci ta shiga gidan mak'ociyar ta Shema'u, ko yanzu a waya ta kira Mum ta shaida mata za taje wuni gida, hakan ya sa tace taje kawai ita ma za tazo daga baya. Bayan ta kimtsa ne ta fita sai da takai saman titi sannan ta samu keke napep ta shiga sai gidan su, da murna ta fad'a gidan ta gaisa da Mama Asabe, gurin Baban na ta taje ta lafe tamkar wata mage, bayan sun gaisa ne yake ta ba ta labarin Makkah yana saka mata albarka har da guntun hawayen shi. "Haba Baba miye na kuka a ciki?, ai wannan abin farin ciki ne a gare mu duka". "Dad'i ne yayi man yawa Zajlah yanda na tai Makkah ta sanadiyyar ki, lallai tabbas y'ay'a mata rahama ne, gashi Allah bai bani d'a namiji ba amma kin zame min tamkar d'a dubu".
.
"Ba komai Baba, adai yi ta saka mu a addu'a, Allah yasa anyi hajji kar6a66e", "Ameen" ya furta a tak'aice. Ferfesun kifin da ta yi mai ne had'e da alalen dankalin turawa sai so6o da jinja data had'o mai ta zube gaban shi. "Zajlah Duke ina zan kai way'annan kayan? ai sun yi yawa", yana maganar farin ciki fal ranshi. "Baba ba komai kaci sai ka k'oshi, nasan ka yi kewar abincin Nigeria". Naja'atu ce ta zo tana furta "Baba in baza ka iya canyewa ba ni zan taya ka, kaga ma yau komai banci ba". Dariya ta basu sosai. Kayan aka d'iba akace ta kaiwa Mama Inno ta dawo sannan ta fice. Sai zuwa bayan la'asar ne Mum ta iso ita da sarkin jin kai wato Saudat, sai wani sha k'amshi take yi tana yatsinar fuska tamkar anyiwa zawo yayyafi, saura k'iris Zajlah ta kwashe da dariya ganin yanda take yiwa fuska. Kaji ne dak'wa-dak'wa Mum ta soyo ta zo ma Mal Abu dasu, ba k'aramin dad'i Zajlah ke ji ba ganin yanda Mum ke tarairaya da ita da kuma mahaifan ta, godiya suka zuba sosai wanda har suka sa Mum na jin nauyin hakan da suke yi mata. Basu wani dad'e ba suka fice daga gidan. D'aki suka wuce bayan wuce war Mum suna hira, inda magana d'aya ga ta biyu Salmat ta ce Salis kaza. "Ke tsaya! Wai ke nan nuna min za kiyi kinsan soyayya kenan?, sai wani zak'ewa kike yi ba kida hira sai ta Salis". "Habawa yarinya sunan ki sorry, gaskiya har tausayi kike ban da baki san dad'in "So" ba, yarinya da kin more rayuwarki". "Rashin sanin gard'in So wani lokaci ya fi sanin So d'in kwanciyar hankali, ni kinga yanzu hankali na kwance, ke ko kullum la66an ki basu huta da furta Salis kaza ba". Dariya Salmat ta yi sosai, inda a 6angare d'aya take tausaya wa rayuwar auren Zajlah da take ganin an tauye ta dayawa, saboda wannan auren sunan shi farin cikin uwar miji k'uncin surukar ta. ** ** ** Bayan sati biyu ne dubban mutane suka shaida auren SALIS YUSUF & SALMAT INUWA Wanda aka gabatar da biki cikin farin ciki da walwala tsakanin ango da amarya duk da ita ma ba wasu events akayi ba. Kullum Zajlah na saman hanyar gida tun ranar da aka saka Salmat a lalle har yau da za'a kai ta gidan mijin ta unguwar ni'ima. Mum, Yusrah da Saudat sun yiwa Zajlah kara sun zo auren, duk da auren ya zamo tamkar 6angare biyu a gurin su saboda amintakar Alamein, Imran da Salis d'in sun taso tare ne tun primary skul d'in su, inda abotar tasu har ga iyaye ta kai. Hakan aka dunk'ula Amarya aka kai ta d'akin mijin ta, sai dai fatar Allah yabada zaman lafiya da zuri'a d'ayyaba. Sai da kowa ya watse ne daga ita sai Salmat d'in ta duk'ar da kanta dai-dai kunnen Salmat d'in ta furta "to uwar soyayya kamin nan da wata goma muna jiran muga d'an soyayya". Kasa magana ta yi sai hawaye dake yi mata zuba na kewar gida da iyaye, suna hakan ne Imran ya rako ango nan suka yi raha da zolayar juna sannan Zajlah ta bi Imran ya sauke ta gida.
* *
Bayan kwana biyu Mum na zaune suna hira da Dad take gaya mai tana ganin fa kamar har yanzu babu wani cigaba tsakanin Alamein da Zajlah. "Koma miye Haj Hasana laifin ki ne, saboda kin tauyewa yaron nan rayuwar jin dad'i sosai, don haka gobe zan kira shi yasauwak'e ma yarinyar wannan auren". Bud'ar bakin ta ke da wuya za tayi magana ya yi mata alama da bai son jin komai daga gare ta, da hakan suka je suka kwanta kowa da abinda yake sak'awa a ran shi. K'arfe 02:00am wayar shi ta d'auki k'ara kamar kar yad'aga saboda baisan lambar ba kuma da fargabar waye zai kira shi da wannan tsakiyar daren. D'agawar shi dai-dai take da furta "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un", wanda ya yi dai-dai da zaburar Mum daga baccin da take yi, wayar ce ta ku6uce mai inda ya tafi luuu ya fad'i k'asa a sume.
.
Jijjiga shi Mum ta yi had'e da salati a bakin ta inda ko motsi baya yi, waya ta janyo ta kira Alamein sannan ta fito harabar gidan da kukan ta domin kiran direba da maigadi, har part d'in Dad suka shiga a rud'e, duk iya dabarar da za suyi sun yi amma ko motsawa baiyi ba, kukan Mum dana Saudat kawai kake jiyowa wanda gida duk ya hargitse ya koma tamkar safiya.
* * *
Gigice ya lalabo makullin motar shi ya sauko ya bud'e falon ya fice, inda ya tayar da maigadin shi don yabud'e mai k'ofa, hankali tashe yake yimai bayanin abinda Mum ta gaya mai. Motsin da ta ji ya yi yawa ne har an bud'e falon an fice ya sa ta yaye labulen window d'in ta, cikin tashin hankali ta hango yana yiwa maigadi bayani. Hijab d'inta ta zaro daga cikin wardrobe ta saka ta fito, tana kawowa gate d'in yana ficewa da motar. Baba maigadi ta tambaya abinda ke faruwa, nan ya yi mata bayani kamar yanda Alamein ya gaya mai. "Baba don Allah ka kula da gidan bara in k'arasa a k'afa". "Haba y'ar nan ki duba fa kiga dare ne, kuma ke Mace ce kiyi hak'uri ki koma zuwa safe muji yanda abin ya kasance". "Baba wallahi bazan iya zama ba har sai na ga wanne yanayi Dad yake ciki, da ganin yanda Alamein ya fita kasan abin sai a hankali". Ganin da gaske ta kama hanyar zuwa gidan ne ya sa ya rufe gate d'in ya mara mata baya. Suna kawowa motar direban Dad na kunno kai a guje, inda ta Alamein ke daga waje ko rufe ta bai yi ba. Mum ce da Saudat suka fito a rud'e inda idon kowa cikin su har sun kumbura, maigadin su ta ba umurnin ya shiga motar Alamein yakai ta asibiti saboda ba za ta iya zama ba, don direban su da Alamein suka wuce da Dad. Nan Zajlah da Saudat suka fad'a motar aka fice dasu sai asibitin Aisha Buhari, wanda ko da suka isa har an shiga A&E dashi sai direba ne da Alamein ke kai kawo a wurin, wanda duk iya nazarin shi ya kasa gano miye silar wannan abin. Juyawa ya yi zuwa ga direba had'e da je fo mai tambayar silar wannan abin.
.
"Wallahi Yalla6ai yanda ka ganshi hakan Haj ta kira mu muka tarar dashi, bamu San takamemen meke faruwa ba, sai dai ka jira k'arasowar Haj kaji, Allah dai yata shi kafad'ar Alh", yana maganar yana shartar majina. Da hanzari Mum ta fito had'e da tambayar su abinda ake ciki, Alamein ya bata amsa cikin k'arfin hali cewa tun shiga dashi ba wanda yafito har yanzu. "Mum wai miye silar wannan tashin hankalin?, saboda ni dai a sani na Dad ko hawan jini bashi da barranta na inyi tsammanin shi ne ya ta shi". Nan ta kwashe abinda tasani ta gaya mai. Wayar ce ya buk'aci gani inda aka yi sa'a Mum ta fito da ita, kar6a yayi ya binciko last call d'in wayar ya kira, kawai Mum ganin shi ta yi zaune da6as a k'asa sai hawaye ke biyar idon shi. Mutum mutumi ya koma saboda magana kan ta bai iya ta sai dai kaga la66an shi na motsi sai ido da yake saki tamkar sabuwar gawa, hawayen da bakin dake motsawa kawai zai tabbatar ma yana raye ba don hakan ba sai dai kace a sume yake. Cikin tashin hankali Mum ta dafa kafad'ar shi had'e da jero mai tambayoyi cikin rud'u da firgici, wanda shi ko bin ta kawai yake yi da ido. Cikin tashin hankali Zajlah ta samo ruwa a cup gurin masu jinya ta zo gab dashi tana jijjiga kafad'ar shi, addu'a ta yi sosai a ruwan ta bashi ya sha kuma ta dinga Shafa mai su a fuska tana mai k'ara karanto wasu addu'o'i tana tofa mai, inda gaba d'aya fuskar ta duk ta jik'e da hawaye kan tausaya wa yanayin da suke ciki. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un kawai Mum ke furta wa wanda ta fara jin nutsuwa na sauko mata. Sa6anin Saudat dake wata irin gunza tana fisgar gashin kanta tamkar wata sabuwar kamun hauka. Ajiyar zuciya Alamein ke sauke wa kad'an kad'an saboda wani sanyi da yake ji yana sauko wa tun daga saman kanshi har zuwa yatsan shi. Hannun ta ya janyo da take rik'e da kanshi tana tofa mai addu'a ya d'ora saman k'irjin shi dake dukan tara-tara, ruwan ta kuma d'ora mai a baki ya sha sannan ya sauke ajiyar zuciya ya zube a jikin ta tamkar gawa. K'arar da ta saki ne ta janyo hankalin mutane da dama suka yo gurin, wasu nurse ne guda biyu suka tallafe shi aka shiga d'ayan d'akin dashi na kusa da Dad. (Wayyo ni Jegal meke faruwa haka?, zuciya ta duk ta cunkushe saboda rashin sanin takame-men me ke faruwa da d'a da uba)
.
Babban tashin hankalin su rashin sanin takamemen abinda ke faruwa, suna hakan ne Dr ya fito daga d'akin da aka shiga da Dad, cikin rud'ani suka tare shi kan cewa ya ake ciki? "Ina son ganin wani daga 6angaren marar lafiyar amma kuma namiji ba Mace ba", daga hakan ya shige office ya bar su tsaye tamkar gumaka a chochi.
.
"Mum me zai hana a kira Abban Yusrah a gaya mai abinda ke faruwa, tunda ga Alamein shi ma akwance". Wayar Dad dake hannun ta ta mik'a mata alamar ta kira. Alh Muttak'a ta gani rubuce nan ta kira kusan sau uku sai ana hud'u aka d'aga, bayan ta gaida shi cikin nutsuwa ta kora mai bayanin abinda ke faruwa, nan yace gaya nan zuwa. Suna hakan ne direba ya kawo wayar Alamein da ake kira dake cikin mota, Zajlah ce ta d'aga wayar suka gaisa take kora ma Salis abinda ke faruwa, nan ya ce mata shi ma gayanan zuwa . Kusan tare suka iso asibitin, Imran, Salis da kuma Abban Yusrah, ga alama Imran da Salis sun san me ke faruwa amma ganin tsananin tashin hankalin da ake ciki ya hana masu furta komai. Office d'in likitan suka shiga nan yake ce masu "sanadiyyar abinda ya samu Alh wanda ko mu bamu san miye ba ya yi silar mutuwar 6arin jikin shi had'e kuma da hawan jini na farat d'aya wanda ke barazana da rayuwar shi". Su duka ukun "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" suke furtawa, cikin tsananin tashin hankali Abban Yusrah ke furta "wannan wane irin tashin hankali ne dake neman rayuwar d'an uwa na?, ya Allah ka tada kafad'ar Yaya". Imran ne ya yi gyaran murya had'e da ce ma Abban Yusrah "Abba wannan abin yana da nasaba ne da k'onewar ma'aikatar Dad gaba d'aya wacce ba'a san miye silar hakan ba, yanzu hakan daga can muke wanda har yanzu wutar ke ci". "Shi ne ma kiran da muka yiwa Alamein domin yasan yanda zai gayawa Dad maganar cikin kwanciyar hankali, ashe an samu wanda ya gaya mai har ya yi silar jefa wad'annan iyalai cikin tashin hankali". "Innalillah" Abban Yusrah ke ta nanata wa wanda shi ma ga alama ita ce tayi tasirin samun nutsuwar shi da yanzu shi ma ya zube a sume. "To yanzu likita me ake ciki akan ciwon na shi?". "Za ku jira nan da awa hud'u domin samun farfad'owar shi sannan a hau mataki na gaba". Hakan yasa suka fito jiki a mace tamkar wa'anda k'wai ya fashewa a ciki, cikin k'arfin hali Mum ta tunkare su domin jin me ke faruwa. Ganin cewa 6oye mata bai da wata fa'ida ya sa cikin nutsuwa da lallami had'e da nasiha suka gaya mata me ke faruwa. Ba k'aramar bajin ta ta yi ba gurin aro juriya ta yafa ba, bayan "innalillahi wa inna ilaihi raji'un" sai "Hasbunallah wa ni'imal wakeel" kawai take nanatawa. Zajlah kanta ba k'aramar gigita ta shiga ba na jin k'addarar da ta sauko ma wa'annan iyalin ba, k'arfin hali ta yi sosai sannan ta tunkari Saudat domin rarrashin ta ganin irin yanayin da ta shiga. Likita ne ya fito daga d'akin da aka shiga da Alamein, cikin sauri suka tunkare shi had'e da jero mai tambayoyi na jin wanne yanayi yake ciki.
.
"Za ku iya shiga ku duba shi, amma plxxx banda hayaniya saboda yana buk'atar hutu". Haka suka rik'a rigen-gen shiga d'akin. Kwance yake kanshi yana kallon ceiling wanda kallon ne kawai yake yi amma bai da takamemen abinda yake kallo, saboda tunane-tunane da suka dask'are zuciyar shi wanda yake jin tamkar ma ta dai na aiki. Sannun da suke jero mai ya d'an dawo dashi hayyacin shi wanda ba bakin sai ido kawai da yake bin su dasu, sai kai da yake kad'awa alamar amsawa. "Mum kinji me ya samu Dad? Mum Dad ya mutu ko? Shike nan yanzu ba mu da komai? Mum kisa a kashe wutar da takama a company". Sambatu yarik'a yi tamkar wani zautacce, hakan yasaka Mum ta fasa wani irin kuka mai cin rai. Da saurin ta ta zo ta toshe mai baki had'e da girgiza mai kai alamar yayi shiru inda ita ma sai hawaye ke sauka akan budurwar fuskar ta, ruwa ta kuma bashi tana dafe da k'irjin shi tana tofa mai addu'a, Zajlah kenan yarinya mai zuciyar tausayi. Wayar Imran aka kira had'e da gaya mai cewa an samu nasarar kashe wutar amma fa ta lashe komai na ma'aikatar wanda ko fallen takarda ba'a fita dashi ba, hakan ya yi dai-dai da kiran sallar asuba. (Hakan ya sa ni ma dole na dakata domin gabatar da farali).

A DALILIN GATA Page 21-25
.


Kiran sallar ne ya sa suka ta shi dukan su domin gana wa da ubangiji, matan kuwa gurin Mata y'an uwan su majinya ta suka nufa, nan aka ara masu kayan buk'ata suka sauke farali. Zajlah ta dad'e tana kwarara ma mijin ta da kuma surukin ta addu'ar samun sauk'i da kuma cin wannan jarabawar daga ubangiji, saboda ba k'aramin tausayi suka ba ta ba, asara ta farat d'aya akwai tashin hankali ba k'arami ba. Bayan mazan sun dawo ne Abban Yusrah ya umurce su dasu koma gida tunda su mazan suna nan, sai dai kash cikin su ba wanda ya ji zai iya d'aga wa nan da can ba tare da ya ga halin da Dad yake ciki ba. Mum ce ta yi k'arfin halin furta' "Zajlah kuje gida ku d'an huta, in Dad d'in ku ya farfad'o za mu iso". "Mum gaskiya bazan iya tafiya ba, kuyi hak'uri Abba har muga ya yanayin jikin Dad, amma yanzu zanje gida in samo mana abinda za'a ci". Direba ya kai ta gidan, gaggauce ta dafa ruwan Lipton sannan ta soya k'wai da dankali sai ferfesun kifi da ta yiwa Dad. Wanka ta shiga ta yo wanda ko mai bata shafa ma jikin ta ba ta zura wata doguwar riga y'ar kanti ta d'auki wasu kayan buk'ata ta fice. Ko da ta isa asibitin kowa ya yi jugum ana sauraren farfad'owar Dad, bayan ta gaida su ne ta zube kayan da ta zo dasu, kowa sai sannu yake mata sa6anin Alamein da bakin magana ya mutu sai dai binta da yake yi da ido had'e da jin tausayin ta can k'asan zuciyar shi. Dak'yar ta samu Mum ta sha tea kad'an sannan ta had'a wa Saudat ta rarrashe ta ita ma tasha kad'an, sa6anin mazan da suka nuna ba za su ci komai ba, tana so ta had'awa Alamein yasha ko kad'an ne amma nauyin Abba take ji. Fahimtar hakan ya sa ya furta' "su Mum ne ake rarrashi su karya ba za'a had'awa yaro na ba?". Cikin zolaya yake furta maganar. Kai ta soke tana wasa da yatsun hannun ta, ganin cewa tabbas ita Abba ke jira ya sa ta had'a tea d'in ta kawo mai, zurum kawai ya yi yana kallon ta sannan ya kauda kai, hakan ya sa ta girgiza mai kai alamar kar yace bai sha, nan ya kar6a ya sha kad'an ya bata cup d'in. **** 09:00am likita ya fito daga d'akin da aka kwantar da Dad, su duka suka tunkare shi domin jin ya jikin nashi, nan ya gaya masu cewa ya farfad'o za su iya shiga su ganshi amma kar su cika shi da hayaniya. Cikin murna suka fad'a d'akin dukan su, sai lokacin Alamein ya san meke faruwa da Dad, saboda ko da Abba ya yi bayani yana nashi d'akin. Kowan nen su sai da ya zubarwa Dad da hawaye akan yanda ya koma cikin awa bakwai abin gwanin ban tausayi, lallai tabbas rayuwa ba a bakin komai take ba, rayuwa da lafiya ciwo da mutuwa duk ga hannun ubangiji suke, lokacin da ya d'oro ma d'aya ba wanda ya isa ya yaye ma sai Allah, an dai samu ya farfad'o amma ba uhm ba uhm-uhm sai dai ido, ga kuma 6angaren jikin shi da bai motsawa ko kad'an. Kukan da ya zo ma Mum ne ya sa ta fita daga d'akin ta jingina ga k'ofa tana rasgar kuka tamkar wata k'aramar yarinya, saboda hango tarin matsaloli masu tsabagen yawa a rayuwar su. Tunkarar Dad ya yi yana kuka zai fad'a saman jikin shi su Salis suka tare shi, Abba ne ya bada umurnin duk su fita daga d'akin, bayan sun fice ne ya je gab da d'an uwan shi yana magana ko zai kar6a mai sai dai babu nasarar ko da motsawar la66an shi, duk da k'arfin halin da yake yi sai da hawaye suka wanke dattijuwar fuskar sa. Fitowa ya yi daga d'akin yana mai shawartar su kan a wuce da Dad f.m.c Bk. Kowa ya yi na'am da maganar shi hakan suka yita rarrashin Alamein har suka fice su duka domin duba yanayin wutar da ta ci ma'aikatar, iya bincike anyi amma ba'a gano musabbabin wutar ba. *** Su Mum kuwa gida suka fice domin yin shiri zuwa Bk. "Mum in shirya muje ko?", cewar Zajlah. "A'ah kuyi zaman ku ke da Saudat har muga yanda abin zai kasance, ke Saudat kishirya kayan ki ki koma can gidan su har mu dawo". "Mum kibari ni zan d'ebo kaya na in dawo nan har zuwa dawowar ku, Allah ya tashi kafad'ar Dad yasa ayi farar jinya". Hakan yasa Mum ta yita saka mata albarka. Da hakan ta fice ta d'auko kayan da za ta buk'ata ta rufe gidan ta dawo, Baban ta ta kira ta gaya masu abinda ke faruwa da sauran y'an uwa daya dace su san da faruwar abin. Bayan Mum ta kimtsa ne suka raka ta asibitin, acan ne suka had'u da Salmat, da Yusrah, sai kuma iyaye daga 6angarori da dama da suka cika asibitin tamkar ad'auke wa Dad ciwon da ke damun shi. Ba abinda ni kai na yak'ara firgitani tamkar yanda aka d'auko Dad za'a saka a mota kai kace gawa ce, nan matan masu raunin zuciya suka rik'a kuka. Bayan an wuce dashi ne da Abban Yusrah sai Imran, Alamein, Salis da wasu abokanen Dad biyu. Nan su Mama Asabe suka wuce jiki a sanyaye, Mamar Yusrah da Salmat da Yusrah duk gidan su Mum suka wuce.
.
Kwanci tashi yau Dad satin shi biyu a asibiti ana yi mai gashin jiki wanda ga alama sauk'i ke shiga kad'an-kad'an, wanda har yanzu bakin shi bai koma dai-dai ba abin ya zamo tamkar mai kariyar halshe. ** ** ** 6angaren su Zajlah kuwa ita da Saudat da Yusrah suke kula gidan, saboda tun lokacin da ta biyo su daga asibitin take gidan, sun je ganin Dad kusan sau biyar, haka ma su Mal Inuwa sun je sau biyu duba jikin na shi sai dai fatar Allah yakawo sauk'i. * * * Yau ne aka sallamo Dad daga asibiti ba wai don ya murmure duka ba sai don ganin irin tsabagen kud'in da ake ci na jinya kuma ciwon sai dai hamdala ya sa Mum ta yi shawara da Abban Yusrah kan su nemi sallama aje gida a had'a da addu'o'i.

.
Ba hakan likitoci suka so ba, sai dai ba yanda za suyi hakan suka bashi sallama d'in tare da shawarwari na kula da yanayin jikin na shi. Hakan suka d'ungumo suka dawo gida wanda da murnar su Zajlah suka fito taryar su, sai gashi sunyi turus saboda sun zata za su ga Dad ko da da sanda ne ko kuma yana d'ingishi sa6anin ganin da suka yi an tallafo shi daga mota, dukan su sai da suka zubar da hawaye. Godiya Mum ta yiwa su Imran sosai na ganin irin yanda suke ba da kulawa ga ciwon Dad,

Please Login or Register in order to submit comment