Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

DUK INDA TA FADI Complete Hausa Novel Document by DUK INDA TA FADI


DUK INDA TA FADI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 145142



DUK INDA TA FADI

Reading Time: 12 Hours

Added On: 13, Aug 2024

Author: Asma Baffa ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : +234 8061929616, 08033933642, 09032409668, +227 90795939

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 763.15 kb

File Type: txt

Views: 923+

Download: 3225+

Last download: 18 hours ago

Description/Story: ο»ΏCompiled By Umar Dalha Funtua.


πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€


DUK INDA TA FADI




1,2,3



Official




By
AsmaBaffa




BISMILLAH





Alhmdllh,Alhmdllh,Alhmdllh. Ina matukar farin ciki da godiya ga Allah da ya sake bani dama da ikon kara sake rubuta wani sabon Novel dina DUK INDA TA FADI.
da fatan wannan ma zai fadakar,ya nishadantar da sauransu.
Readers mu writers bamu cika son godiya ba,kawai a dinga sharhi domin shike kara mana mu writers kwarin gwiwa sosai.
Pls duk wacce bata karanta daga farko ba kar tazo ta kawo min korafi,sabo da wasu basa karantawa daga farko,wasu kuma suna skipping pages,wasu kuma basa tsayawa su fahimci me ake nufi ko me ake son a isar sunfi kuma kowa korafi,
Ayi hakuri da typing error ba time na editing,banda gaggawa domin wasu nasan akwai gaggawa su dai ayi sauri a gama.
Mu writers munfiku gajiya da typing,sannan idan nayi posting me so ta dinga tambaya a groups din da take,sabo da ana cika mu da tambaya mu tura ga typing,ga posting a gp sannan ga korafi kana karba,ga sharhi da kuma masu kira ta waya,da masu jinjina ta text,abun yana yawa,shi yasa nace idan kina nema ki nema a gp, nima idan kinzo idan ina free zan baki sai dai idan bana free ni kuma banso mutanena suji haushi suga kamar ka wulakantasu shi yasa a tallafa mana masu karatu kar asa nayi fushi na koma AMANA na fara naushinku.


SUBBY page din farko dake zan bude,ANTY SUMEE kema haka,MAMAN MINAT Allah ya kara kauna.

ASMABAFFA FANS CLUB KUNE MASU PAGE DIN FARKO KUNJI YAN KAWAYENA,SAI GIDA YA KOSHI AKE KAIWA DAWA,KUNE AMARA KIRJIN BIKI.LIVE U ALL.







Riya riya wasu yan mata suka rankayo su ukku da ganinsu kasan talauci ya musu shigar gaske,babu wata me sassauci a cikinsu,ko kallonsu kayi sai sun Baka tausayi domin wannan tana wane wannan a talauci,babu me ran gwame,wani company naga sun shiga da sanyin safiya domin ana fitowa daga Sallah suka fito domin zuwa wannan company, daya daga cikin yan matan tace Ramlat muyi sauri kin San mun makara nasan yanzu wasu tuni sun fara aiki,ke dama Uwar nauyi komai bakyayi da jikinki,Murmushi kawai Ramlat ta saki wanda dimple dinta ya lotsa fararen jerarrun hakoranta suka bayyana,

Sannan ta kalli kawar tata tace haba Habiba duk saurin da mukeyi bakya gani,Firdausi tace kyaleta Ramlat iya rabonmu shi zamu samu dai, Firdausi tace iyye to Ku hade min kai yan iska ke Firdausi da kuke hade min kai karki manta Ramlat ita tana da gata a company citta domin kowa Sonta yakeyi har turawa karewa,kalli dai Boss duk girman tumbinsa bashi da buri sai son Ramlat,kowa Ramlat yake so cewar Habiba,
Firdausi tace hmm ke dai bari ai ke Ramlat ki godewa Allah ya baki farin jini,duk inda kika shiga sai an soki,da ganinki gaskiya ruwa biyu ce ba yar Asalin Nigeria bace,kina samun Hutu za ayi kallon baiwa sosai.

Ramlat dai bata ce komai ba binsu da kallo takeyi tana takunta dai dai cikin birgewa da iya tafiya,
Firdausi ta kara magana Habiba bani da Ramlat ba rainin hankali ga isa da takama magana sai taga dama,haka duk mazan dake sonta amma bata taba Kula kowa ba ni anya kuwa baki da Aljanu Ramlat,kiyi aure mana ki huta da wannan wahalar duk fatarki ta dafe,da ace mune da samarinki da tuni munyi aure wlh,mu samu me kudi ko me rufin asiri mu aura duk da karancin shekarunmu kuwa ko dan mu huta da wahalar rayuwa da gararanba a duniya.

Har ciki suka shiga suna hirarsu abun mamaki mutane damkam maza da mata Ma'aikata a cikin wannan company,tarin Citta wato Ginger trailers da yawa gasu nan ana juyewa,matan suna zabar Ginger me kyau suna cika buhuna,ga wasu turawa a gefe suna duba aikin,duk wacce tayi buhu daya a bata Dari biyu,haka wasu sai suyi buhu Goma rana daya,wasu buhun Goma sha,babu me kasa da Buhu Goma sai Ramlat kadai,domin Ramlat tsabar lalacinta kullum buhu biyu zuwa uku takeyi watarana ma buhu daya,Mazan
kuma suna dinke buhun Citta suna sawa a cikin trailer, company dai na Turawa ne,haka wannan yan mata ma suna shiga suka kwashi buhu suka fara aiki ka in da na in,ba ji ba gani.kafin kace me sunyi furu furu gashin idonsu kamar hazo akayi me yawan gaske,

Lokacin Sallah nayi Ramlat ke fara zuwa tayi Alwala sabo da haka suke ce mata agogo domin kowa yana ganin Ramlat ta tafi Alwala yasan time din Sallah yayi,basai sun duba ba kawai zasu kama Alwala maza da mata a hada jam'in sallah ayi,

Idan Azahar idan la'asar ma tayi haka,
Kowa ya samu kudin aiki zaka ga ana ta siyen abinci ana ci amma banda Ramlat,gashi tana Jin uwar yunwa sai dai tasha ruwan pampo tayi tagumi a gefe tana nazarin duniya.

Yauma tana gefe kamar ko yaushe,Firdausi tace Ramlat kiwa kanki fada ki kara dagewa ko buhu Biyar ki dingayi a rana saboda yawan kudinki su Karu ko kya samu ki dinga cin abinci,da ranki da lafiyarki sai banzan lalaci, komai na duniya baza kiyi da jikinki ba,kalli duk mazan gidan nan har turawa masu company sai sun sai miki abinci ayi ta turuwar kawo miki a abinci amma kiki karban na kowa kice baza kici ba,muma mun kawo miki bakya karba,tunda hakane ki kara dagewa da kanki ki samu nacin abinci tun kafin Ulcer tayi miki mummunan Kamu,

Haka akayo caaaa kan Ramlat kowa yana tofa albarkacin bakinsa,
Boss ne ya shigo Company da katuwar motarsa ya fito da cikinsa kato,ledojin abinci ne a hannunsa na wani restaurant,Ramlat ya mikawa Leda biyu,ta bishi da kallo tana Murmushi amma bata karba ba,

Wato tsohuwa tukuf Binto tace ke yar nan keko ko aljana ce ne yarinya kamar jaraba yanzu da kinso Boss dinnan da tuni bamu washe ba,ke ba yar gidan uban kowa ba sai Mulki da jiji da kai,ke ba yar makaranta ba ba kowan kowa ba amma dan kin samu ana kulaki sai feleke kikeyi,
Boss dai baijin hausa,da kyar Ramlat ta karbi abincin tace wa Boss tnx Boss,

Murmushi yayi mata ya wuce Office,Binto tsohuwa tace heeeee rai fes ko kefa yarinya inama ni Boss yake so da wlh aurarshi zanyi,can Tsohuwar ta kuma cewa inama ni yayar Boss ce ko yar uwarsa da me zai kawoni aiki gidan Citta,
Dariya kowa ya sheke da ita,tsohuwa Binto ta dauko zogalenta da kuli harda tumatur da albasa ta hada abinta taci ta koshi ta Mike taci gaba da aikinta suna ta hira ana kwasar dariya Har Ramlat tana cin dariya.

Wata tsohuwa ma ana ce mata Dandubu ta fara magana ke yarinya me farin jini ki auri Boss mana tunda shi musulmi ne,Ramlat ta tabe baki a hankali cikin muryarta siririya me zaki ta furta Allah kiyaye me zanci dashi duk katon ciki,
Dandubu ta rike baki dan Ubanki cikin za kici?bafa cikin zaki ci ba,yanzu da kin aure shi
Ai da munci gaba,nanma aka sheke da Dariya.
Binto tace dan nasan tana aurenshi zai bani Manager,dariya akayi Wasu yan mata suma suka ce Binto ai sai me ilmi ake bawa.

Binto dai zazzabi ne ya kamata amma tsabar son kudi taki ta huta,anyi anyi ta huta taki yarda,sai makyarkyata take tana aikinta,
Boss ya fito duba aiki yaga Binto tana karkarwa,driver dinsa bakar fata ya kira yana fada masa da turanci shi kuma ya fada musu da Hausa,idan sun fada ya fadawa Boss da turanci.

Boss yace Binto ta tafi asibiti a dubata,Binto tace yaro kace bazanje ba zan warke sai na kara ko buhu Biyar ne,Boss yace no idan ba lafiya taya zata iya musu aiki ayi ta aiki da yawa haka ba a hutawa,Binto tace ita baza ta tafi ba,Boss ya mika mata kudin aikin yau da tayi sannan ya bata Dubu daya taje asibiti,Binto ta karbe kudi tace ai taje asibitin ba kowa,Boss yace ya za ayi
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download DUK INDA TA FADI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album