Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

ο»ΏCompiled By Umar Dalha Funtua.


πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€


DUK INDA TA FADI




1,2,3



Official




By
AsmaBaffa




BISMILLAH





Alhmdllh,Alhmdllh,Alhmdllh. Ina matukar farin ciki da godiya ga Allah da ya sake bani dama da ikon kara sake rubuta wani sabon Novel dina DUK INDA TA FADI.
da fatan wannan ma zai fadakar,ya nishadantar da sauransu.
Readers mu writers bamu cika son godiya ba,kawai a dinga sharhi domin shike kara mana mu writers kwarin gwiwa sosai.
Pls duk wacce bata karanta daga farko ba kar tazo ta kawo min korafi,sabo da wasu basa karantawa daga farko,wasu kuma suna skipping pages,wasu kuma basa tsayawa su fahimci me ake nufi ko me ake son a isar sunfi kuma kowa korafi,
Ayi hakuri da typing error ba time na editing,banda gaggawa domin wasu nasan akwai gaggawa su dai ayi sauri a gama.
Mu writers munfiku gajiya da typing,sannan idan nayi posting me so ta dinga tambaya a groups din da take,sabo da ana cika mu da tambaya mu tura ga typing,ga posting a gp sannan ga korafi kana karba,ga sharhi da kuma masu kira ta waya,da masu jinjina ta text,abun yana yawa,shi yasa nace idan kina nema ki nema a gp, nima idan kinzo idan ina free zan baki sai dai idan bana free ni kuma banso mutanena suji haushi suga kamar ka wulakantasu shi yasa a tallafa mana masu karatu kar asa nayi fushi na koma AMANA na fara naushinku.


SUBBY page din farko dake zan bude,ANTY SUMEE kema haka,MAMAN MINAT Allah ya kara kauna.

ASMABAFFA FANS CLUB KUNE MASU PAGE DIN FARKO KUNJI YAN KAWAYENA,SAI GIDA YA KOSHI AKE KAIWA DAWA,KUNE AMARA KIRJIN BIKI.LIVE U ALL.







Riya riya wasu yan mata suka rankayo su ukku da ganinsu kasan talauci ya musu shigar gaske,babu wata me sassauci a cikinsu,ko kallonsu kayi sai sun Baka tausayi domin wannan tana wane wannan a talauci,babu me ran gwame,wani company naga sun shiga da sanyin safiya domin ana fitowa daga Sallah suka fito domin zuwa wannan company, daya daga cikin yan matan tace Ramlat muyi sauri kin San mun makara nasan yanzu wasu tuni sun fara aiki,ke dama Uwar nauyi komai bakyayi da jikinki,Murmushi kawai Ramlat ta saki wanda dimple dinta ya lotsa fararen jerarrun hakoranta suka bayyana,

Sannan ta kalli kawar tata tace haba Habiba duk saurin da mukeyi bakya gani,Firdausi tace kyaleta Ramlat iya rabonmu shi zamu samu dai, Firdausi tace iyye to Ku hade min kai yan iska ke Firdausi da kuke hade min kai karki manta Ramlat ita tana da gata a company citta domin kowa Sonta yakeyi har turawa karewa,kalli dai Boss duk girman tumbinsa bashi da buri sai son Ramlat,kowa Ramlat yake so cewar Habiba,
Firdausi tace hmm ke dai bari ai ke Ramlat ki godewa Allah ya baki farin jini,duk inda kika shiga sai an soki,da ganinki gaskiya ruwa biyu ce ba yar Asalin Nigeria bace,kina samun Hutu za ayi kallon baiwa sosai.

Ramlat dai bata ce komai ba binsu da kallo takeyi tana takunta dai dai cikin birgewa da iya tafiya,
Firdausi ta kara magana Habiba bani da Ramlat ba rainin hankali ga isa da takama magana sai taga dama,haka duk mazan dake sonta amma bata taba Kula kowa ba ni anya kuwa baki da Aljanu Ramlat,kiyi aure mana ki huta da wannan wahalar duk fatarki ta dafe,da ace mune da samarinki da tuni munyi aure wlh,mu samu me kudi ko me rufin asiri mu aura duk da karancin shekarunmu kuwa ko dan mu huta da wahalar rayuwa da gararanba a duniya.

Har ciki suka shiga suna hirarsu abun mamaki mutane damkam maza da mata Ma'aikata a cikin wannan company,tarin Citta wato Ginger trailers da yawa gasu nan ana juyewa,matan suna zabar Ginger me kyau suna cika buhuna,ga wasu turawa a gefe suna duba aikin,duk wacce tayi buhu daya a bata Dari biyu,haka wasu sai suyi buhu Goma rana daya,wasu buhun Goma sha,babu me kasa da Buhu Goma sai Ramlat kadai,domin Ramlat tsabar lalacinta kullum buhu biyu zuwa uku takeyi watarana ma buhu daya,Mazan
kuma suna dinke buhun Citta suna sawa a cikin trailer, company dai na Turawa ne,haka wannan yan mata ma suna shiga suka kwashi buhu suka fara aiki ka in da na in,ba ji ba gani.kafin kace me sunyi furu furu gashin idonsu kamar hazo akayi me yawan gaske,

Lokacin Sallah nayi Ramlat ke fara zuwa tayi Alwala sabo da haka suke ce mata agogo domin kowa yana ganin Ramlat ta tafi Alwala yasan time din Sallah yayi,basai sun duba ba kawai zasu kama Alwala maza da mata a hada jam'in sallah ayi,

Idan Azahar idan la'asar ma tayi haka,
Kowa ya samu kudin aiki zaka ga ana ta siyen abinci ana ci amma banda Ramlat,gashi tana Jin uwar yunwa sai dai tasha ruwan pampo tayi tagumi a gefe tana nazarin duniya.

Yauma tana gefe kamar ko yaushe,Firdausi tace Ramlat kiwa kanki fada ki kara dagewa ko buhu Biyar ki dingayi a rana saboda yawan kudinki su Karu ko kya samu ki dinga cin abinci,da ranki da lafiyarki sai banzan lalaci, komai na duniya baza kiyi da jikinki ba,kalli duk mazan gidan nan har turawa masu company sai sun sai miki abinci ayi ta turuwar kawo miki a abinci amma kiki karban na kowa kice baza kici ba,muma mun kawo miki bakya karba,tunda hakane ki kara dagewa da kanki ki samu nacin abinci tun kafin Ulcer tayi miki mummunan Kamu,

Haka akayo caaaa kan Ramlat kowa yana tofa albarkacin bakinsa,
Boss ne ya shigo Company da katuwar motarsa ya fito da cikinsa kato,ledojin abinci ne a hannunsa na wani restaurant,Ramlat ya mikawa Leda biyu,ta bishi da kallo tana Murmushi amma bata karba ba,

Wato tsohuwa tukuf Binto tace ke yar nan keko ko aljana ce ne yarinya kamar jaraba yanzu da kinso Boss dinnan da tuni bamu washe ba,ke ba yar gidan uban kowa ba sai Mulki da jiji da kai,ke ba yar makaranta ba ba kowan kowa ba amma dan kin samu ana kulaki sai feleke kikeyi,
Boss dai baijin hausa,da kyar Ramlat ta karbi abincin tace wa Boss tnx Boss,

Murmushi yayi mata ya wuce Office,Binto tsohuwa tace heeeee rai fes ko kefa yarinya inama ni Boss yake so da wlh aurarshi zanyi,can Tsohuwar ta kuma cewa inama ni yayar Boss ce ko yar uwarsa da me zai kawoni aiki gidan Citta,
Dariya kowa ya sheke da ita,tsohuwa Binto ta dauko zogalenta da kuli harda tumatur da albasa ta hada abinta taci ta koshi ta Mike taci gaba da aikinta suna ta hira ana kwasar dariya Har Ramlat tana cin dariya.

Wata tsohuwa ma ana ce mata Dandubu ta fara magana ke yarinya me farin jini ki auri Boss mana tunda shi musulmi ne,Ramlat ta tabe baki a hankali cikin muryarta siririya me zaki ta furta Allah kiyaye me zanci dashi duk katon ciki,
Dandubu ta rike baki dan Ubanki cikin za kici?bafa cikin zaki ci ba,yanzu da kin aure shi
Ai da munci gaba,nanma aka sheke da Dariya.
Binto tace dan nasan tana aurenshi zai bani Manager,dariya akayi Wasu yan mata suma suka ce Binto ai sai me ilmi ake bawa.

Binto dai zazzabi ne ya kamata amma tsabar son kudi taki ta huta,anyi anyi ta huta taki yarda,sai makyarkyata take tana aikinta,
Boss ya fito duba aiki yaga Binto tana karkarwa,driver dinsa bakar fata ya kira yana fada masa da turanci shi kuma ya fada musu da Hausa,idan sun fada ya fadawa Boss da turanci.

Boss yace Binto ta tafi asibiti a dubata,Binto tace yaro kace bazanje ba zan warke sai na kara ko buhu Biyar ne,Boss yace no idan ba lafiya taya zata iya musu aiki ayi ta aiki da yawa haka ba a hutawa,Binto tace ita baza ta tafi ba,Boss ya mika mata kudin aikin yau da tayi sannan ya bata Dubu daya taje asibiti,Binto ta karbe kudi tace ai taje asibitin ba kowa,Boss yace ya za ayi ace Hospital ba kowa,Binto ta kalli Boss tace kai yaro ubanka me Jan kunne na fishi Sanin duniya,Driver ya fassarawa Boss,kowa dariya yayi harda Boss,yace a fadawa Tsohuwa ko kudin ne zai kara mata Amma taje asibiti,Binto tace a kara min,aka kara mata ta fita waje kamar gaske ta labe a jikin gate minti kadan ta dawo ciki tace taje anyi mata allura taci gaba da aikinta,Boss yace taje gida ta kwanta ta huta Amma Binto tace baza taje ba ta rigada ta rantse yau sai tayi Buhu 20 dole aka kyaleta haka.

Ramlat sai kici kici takeyi tun safe har yamma amma har yau buhu daya da rabi tayi,ta gama jigata,Boss yana zuwa ya bata kudin buhu Uku yace ta tafi gida,

Tana Jin dadi ta karba tayi Sallama tace zata tafi sai gobe,Firdausi da Habiba sukace ke kam kwai banza ya baki Dari shidda a uban matsalarki nawa suke ki tsaya ki kara buhu biyu sai mu tayaki mu tafi tare,Ramlat ta cuno baki cike da shagwaba kamar zatayi kuka tace tab ni wlh bazan iya ba na gaji hakan ma Allah sa musu albarka na godewa Allah,

Yanzu ma kalli jikina Zafi da kaikayi hade da radadi yake min,kinsan skin dina ina farawa kuraje suke fito min ina da Allergic da Citta,Habiba tace uhm ke kam kullum ai haka kike sai tattalin fata kamar kinfi kowa,ke kika san mene wani Allergic cewar Firdausi,Ramlat tace eh mijina nake adanawa kayarsa.
Heeeee matan gaba daya suka dau shewa da dariyar Ramlat.

Ramlat tana fita ta dinga sauri a hanya ta siyi sabulun wanka,klin Omo,da sabulun wanki,ta siyi shinkafa cofi biyu,taliya daya,manjan Arba'in da mangyada na 50, sai yaji da sauran yan abubuwa na girki dan kadan kadan ta siya ta tafi gida.

Har ta karasa gida wani wancakalallan gida mafi muni da rashin kyau ta shiga,tana Sallama wasu yan mata su wajen Hudu suka fara zabga mata harara,suna ga su uwar Iyayi an dawo,

Daya daga cikin yan matan tace tambadaddiya maza zo ki mana wanki,ki share gidan nan tas sannan ki wanke bayi,
Ramlat bata ce komaiba ko Zama batayi ba ta fara aikin da suka sata,tana Gamawa wata kojalalliyar mata ta fito daga daki cikin tsumma ta makawa Ramlat Harara tace ki gama kizo na aikeki can karshen layi ki siyo min kayan miya,Ramlat na gamawa ta karbi kudin kayan miya ta fita ta siyo ta dawo ta Sha wahala sabo da wajen akwai Nisan gaske,

Tana shiga ta duba kayan da ta siyo dazu,taga har sun kwashe mata maggi da gishiri da manjanta,kamar tayi kuka haka babu bakin magana ta kwashe kayan ta shiga wani rubabben daki wanda daf yake da ruftowa,babu komai ciki sai tabarma da shirgin tarkace da ake zubawa a dakin,da gani dakin dai na zuba tarkacen da ba aso ne sai kayan wanki a ciki da sauransu.

Canjin da suka rage mata ta dauka ta kara fita ta siyo maggi da manja saboda taga dare yayi,dan wani kwano ta dauko baki kirin kamar tukunya ta wanke tas da Omonta ta zuba ruwa ta kunna wuta a dan wani murhun gawayi Sam Ramlat bata son wahala bata son Kura da hayaki,shi yasa ta siyi murhun karfe na gawayi ba ruwanta da hayaki,gawayi take hurawa tayi girkinta,wani gari ta dakko a Leda ta Eba kadan ta zo ta dama kuninta me kyau,domin kunun alkama,gero da waken suya,su take hadawa takai nika da yawa ta boye abinta kullum dashi take karyawa sannan da dare ma ta kara Sha,sabo da yunwar da take fama da ita idan Babu wannan to tabbas ramewa zatayi ta kwanjale,sannan skin dinta ta lalace ita kuma bata so ta koma haka,shi yasa duk inda taji hadin kunu me gyara fata da murnjewa da kawo rashin rama to fa sai inda karfinta ya kare,shi yasa kullum kamar me cin abin dadi da yar kibarta kadan ba ramammiya ba kamar bata Shan wahalar rayuwa.s hinkafa fara da mai da yaji ta dafa iya cikinta taci ta koshi sannan tayi wanka ta gabatar da Sallar Isha ta fara karatun Qurani ta gama ta kwanta bacci,
Washe gari ma haka suka tafi gidan Cittarsu, tana dawowa wata a cikin yan matan ta Mika mata waya gashi ubanki ya kira yace ki masa flashing,karbar wayar tayi zuciyarta cike da kunci domin tasan babu Alkhairi a wayarta da Mahaifinta,tana flashing ya kira yana zazzaga bala'i sai hakuri take bashi tace gobe zan taho Kawu kayi hakuri.

Tana gamawa ta fara Kuka wiwi tasan idan taje can ta shiga Uku a hannun iyayenta,
Matarce ta fito taji Tausayin Ramlat sosai tace to kinji gwara gobe ki shirya ki tafi kauyenku tun kafin wannan dan iskan uban naki yazo yayi mana tijara a gida,me za ayi da hali irin na Idrisa,Allah wadai da halinsa wlh,jarabar Duniya asara wanda bai san mutunci ba,H arni Idrisa zai zaga ina yayarsa,in rike masa ke kullum ina wahala,yaje duniya ce,sauran Yan matan kuwa murna sukeyi dama Ramlat ta ishesu a gidan mayya.
Matar da kanta ta karawa Ramlat kudin Mota ta kaita tasha tare da sata a mota,Ramlat sai kuka takeyi kamar ranta zai bar jikinta.

Taxi ce ta tsaya a wani gida dan madaidaici me kyau gidan dai irin na marar Shan wahala kuma ba mai kudi ba,dan me kyau dashi yasha tiles ko ina amma dai da gani babu kudi a gidan,gidan me rufin asirine,
Wata tsohuwa ce ta fito da sauri cikin kayanta masu dan kyau fes fes da ita farace sosai kyakyawa wannan tsohuwar tana washe baki tana Oyoyo dan jikalle na,barka da dawowa jikina nan ta fashe da Kukandadi.
Wani dan matashi ne ya fito daga taxi yasha wanka kamar wani dan shugaban kasa haka yake takawa cike da isa da takama,yana wani yarfe hannu,yanawa Unguwar kallon Tara Saura kwata,
Yana sham kamshi hadi da basarwa,.karasawa yayi jikin Tsohuwar ya rungumeta yana murmushi me matukar kayatarwa da birgewa,

Mamina I missed u Badly ina ta tunaninki Mami ta,
Tsohuwa daya kira da Mami tace nayi Kewarka dan nan,Muhammadu na fito da kayan mu tafi ciki Kaci abinci ka Huta,wata trolley ta yan gayu guda Hudu manya manya
Ya fito dasu yana yarfe hannu tare da sakin kara,Mami hannuna Zafi bazan iya dauka ba,Driver tunda ya dauko wannan matashin yaron yake Shan mamakin Iyayi da sanabe hade da ragwanci irin na yaron nan danyen jini,

Mami tace Sannu Muhammadu,kamar zaiyi kuka yana kasa da murya can ciki yace Mami pls Mohd fa ko Sardauna pls mene wani Muhammadu.
Mami tace to SARRRDAUNA shike nan? Shagwaba ya farayi mata Haba Mami Sarrrdauna fa kike cewa haka zakice min SArDAUNA,R din Silent ce ba a fito da ita Ohhhh God Mami ya fadi Sardauna cikin wani mugun iyayi da Salo wanda Mami take fada na kauye ne wai.

Mami tabe baki tayi tace lallai Muhammadu baka canjawa kullum haka kake wato kasar ma da kaje naga kara sangarcewa kayi tare da karo Iyayi,
Driver dai ya fito yace dan Allah yaro dauki kayanka ka sallameni na gaji ni,Sardauna ya kalleshi yayi dariya me kayatarwa yace ni ka daina ce min yaro ba yaro bane ni tunda ko aure sai na rike,
Driver yayi dariya yace iyye lallai ka girma,
Sardauna yace tun yaushe ma ya furta cikin iyayi can kasan makoshi,wani Almajiri ya kirawo shi bazai iya daukan kayanba,Ai kuwa Almajiri ya dauka ya dinga kaiwa har cikin Room din Sardauna ya kai masa tsabar lalacin Mohd shi bazai dauki kaya ba ai yawane kamarshi ya wani kinkimi akwatuna,

Driver ya kalla da iyayi yana sarrafa lips dinsa a hankali yace pls Man kayi a hankali ka nutsu bana sauri ni,shi kam Driver abin ya koma bashi dariya da kallon kuruciya irin ta wannan yaron da bazai wuce 19yrs ba,

Dollers ya Ciro a aljihunsa yace kaga ba canji ban canja ba a airport dana sauka nasan sunfi kudinka ka canja ka rike du,
Driver da sauri ya karba yana godiya,Sardauna yana iyayinsa yace hey chil Man ba yawa na gode.Driver dai ya wuce yana ta faman dariyar Mohd da ake cewa Sardauna.

Mohd dai sanye yake cikin Katon takalminsa canvas na yan gayu kamar mawakin turawa,
Wandonsa Jean Brown pencil sosai daga kasa,sama kuma ya zazzago dashi yayi ass down rabin Boxers dinsa a waje yake yanayi yana gyarawa irin na nigogi,
Sarkar Azurfa ce siririya karama a wuyansa,da rigarsa fara kalar takalminsa,gashinsa kuwa ya kwashe gefe da gefe baki,tsakiya kuma gashi me uban yawan gaske ya konashi ya koma Orange sosai,sai kamshi yake uban zubawa kamar me yana kalallabewa.

Suna shiga ya kalli gidan yasha gyara ko ina kal sai kamshi,wanka yayi ya fito dagashi sai Boxers da singlet,Mami ta kawo masa abinci wajen kala Uku,dasu fruits,cin abincin kansa yanda yakeyin yanga yana tsince tsince a ciki,yana kare masa kallo,haka ya danci ya koshi yasha fruits,Mami na gefe tana kallon ikon Allah.





AsmaBaffa
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€



DUK INDA TA FADI




4.5.6




Official





By
AsmaBaffa





KUNA SHARHI MU NA JIN DADI READERS.




Har ya gama cin abincin sannan ya jawo wayarsa iPhone latest da computer laptop dinsa ya dan dannan ya maida su gefe,ya koma jikin Mami ya lafe a cinyarta ya fara bacci cikin Nutsuwa,Mami na kare masa kallo tana shafa gashin kansa,tare da jinjina girma da tsayin kafa da Mohd yayi,baccin ma a yangance yake yinsa,Mami tana mamaki irin gayu da iyayin Sardauna,saida yayi baccinsa ya koshi sannan ya Mike ya fada toilet ya fesa sabon wanka ya canja jallabiya fara yace Mami na tafi masallaci,
Mami tana Jin dadi tace Sannu dan albarka,
Duk inda Mohd ya ratsa sai an kalleshi sabo da yanda yake tafiya gashi namiji na gaske sai iyayin jaraba,kamar bazai taka kasa ba,sai isa da takama yakeyi,jallabiyar nan fitted sai ya koma kamar Balarabe,gashin kansa kawai ake ta kallo ko ina,bayan sun idar da Sallah harda karatun Qurani a masallaci,kowa sai da yayi mamaki domin sun zata balaren bayahude ne yaron,ko irin Bai San Addini ba.
Liman da kansa ya matso wajen Sardauna sukayi musabiha,liman yace yaro dan Allah zan danyi wani shishigi,Sardauna yace ina jinka Dad wai bazai ce Baba ba na yan kauye ne sai Dad,

Tun daga maganar Mohd liman ya bude baki domin salon da yace Dad ma dabance kamar baturen amurka yanda yake sarrafa magana,hausarsa ma ka rantse Bature ne yazo Nigeria ya koya yanda ya ke maidata kamar turanci turanci da wani salo,
Liman yace Yaro idan baza ka damu ba da ka aske wannan gashin naka yayi yawa gashi ka konashi hakan baiyi suffa Ga rayuwar musulmi ba.

Kallonsa Sardauna yayi da ladabi yana Murmushi yace pls Dad mufa musulmai mune yan gayu ka dinga ganewa Annabinmu dan gayu ne sosai,amma turawa suka karbe mana,kawai dan na kona kaina wani dan zamani ne ya ratso shine ake wankan haka,ku Mallams din Nigeria bakwa ganewa gaba daya tunanin bahaushe shi kadai ne musulmin kwarai,babu wani me musulunci sai Ku,ku dinga ganewa,kunfi so kullum a zauna a dirty ana sa burma burman kaya hannun Riga kamar Bujen su Kaks (kakanni).

Liman yayi murmushi domin yanda Sardauna ke magana abin kallo ne sai ka kasa kunne zaka ji me yake fada,hausar kamar turanci,Murya can can kasa,
Liman yace Yaro mun San haka da Sumar kawai ka Tara ka aske wannan konannen gashin,Sardauna ya Mike tare da zura hannu a aljihu yana shafa gemunsa da ya fara dan fitowa kadan,yace Dad kaga gashin nan misali ina bacci wani ya aske min shi to babu makawa dole sai nayi Shari'a dashi a kotu sai ya biya Tara me yawa,kuma yaci dukan gaske,kaga dan gemunan da wajen nan

Please Login or Register in order to submit comment