Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abin kallo,idonsa ba kananu ba, ba kuma manya can ba, kana kallon idon Mohd zaka san ya gama gogewa da duniya,
Idan karanto muku kyau da kyan sura da tsari irin na Sardauna zan cinye lokaci Amma ta ko ina Mohd ya hadu karshe,
Yarone dan 19yrs kacal sai dai yayi tsayin kafa tunda ya fara tara saje da dan gemu daya fito masa,sai ka dauka ya kai 25yrs ma,
Gashi Gomnati ta kaishi kasar waje London yayi karatu sai ya kara wayewa sosai,
Mohd Sardauna tsabar gadara da takamarsa Mami ta sa Masa Sardauna kamar jinin sarauta haka yake,ga mugun iyayi,feleke,hade da sanabe iri iri,duk harkarsa shi dai tsafta da daukan wanka gayu swagg,

Ko a frnds ba kowa yake kulawa ba sai wanda yake dan wanka,komai talaucinka da Muninka indai kai dan gayu da tsafta ne to zaku zama frnds
Mohd baya shan komai,baya neman mata,babu wani abu da yakeyi Mummuna,yasan mutuncin dan Adam,kuma bashi da girman kai,da Mami kadai yake surutu,sai a wajen Mami zaka San yana surutu,best frnd dinsa Naufal tare sukayi secondary tare kuma gvt ta basu scholarship,

Halinsu yazo daya sosai, Sardauna ko fita bai cika yi ba kullum yana gida like da Mamin sa,
Yana da fara'a sosai Amma ba a gaban kowa ba,duk harkar kuruciya yake zuba abinsa na matasan zamani.

Tarihin Ramlat

kunji na wajen Mamanta Hafsatu a wajen Mamin Sardauna,da Sardauna da Ramlat kakanninsu daya,dan wa da yar kanwa suke da Mohd.
Idrisa Mijin Hafsatu Baban Ramlat dan asalin jigawa state ne Roni,tsohon dan Sanda m yayi retire ya koma gadi a wani gida estate dake Kubuwa Abuja,
A boysquatr yake zaune Allah ya hadashi da Hafsatu taje gidan kawarta biki, tace kuwa tana sonsa ba a dade ba ta aureshi Babu yanda su Mami basuyi ba cewar dan shaye shaye ne kuma barawo Amma tace tana so,bayan biki ta tare a Dan akurkin dakinsu na me gadi,katifa siririya guda daya da dan toilet sai tukanen girki da kayan cin abinci,abun ba tsari babu kyan gani,
Watarana ya mata duka idan ya sha kwayarsa,domin Idrisa kwayoyi,wiwi,harda giya yana korawa,ga sata,domin ko wayar mutum ya karba daga cewa mugani to sai dai kaga babu Battery ba memory ya sace,
Sace sace yakeyi sosai da yaga ba idon mutane zai faki ido yayi sata.

Hafsatu tasha wahala a hannunsa domin duka kusan kullum gashi idan ya samu kudinma shaye shaye zaiyi dasu,
Shi yasa Hafsatu kullum a gantalin yaji take,gata doluwa bata da wayo ko kadan,ita matsalarta ba tattali babu adani,komai ta dauka ta siyar kuma abin haushi kudin mota zatayi kawai ta tafi gari me nisa gidan wasu da ta sani ko abokan miji taje ta tona asirin mijinta tayi maula ta dawo gida aikinta kenan,bata wa yayanta fada,babu ruwansu da koma me yaro zaiyi abu yayi tsamari tace bari shike nan,shi kuma Idrisa fadan bazai yi na hankali ba sai duka da zagi.
Hafsatu tana da laifi shima Idrisa hakan,amma shi idan ya samu to yana dan siyo abu kadan na ciyar da iyali sai fadan masifa,

A haka ta haifi Ramlat,komai kankantar yaro to Idrisa zai iya masa mugun duka,idan yaga dama zai iya kwashe suturunsu ya siyar yayi shaye shaye da kudin,idan kuma sune suka siyar ya musu duka,ga masifa da Bala'i kullum aikinsa kenan ba a Zama dashi lfy,sauran Halayen Idrisa zaku ci gaba da jinsa a novel din nan,

Idrisa da ma'aikacin dan Sanda ne,watara yasha kwaya ta buga masa kai ya shirya da kansa ya rubuta retired letter ya bayar ya bar aikin,karshe ya koma me gadi,sun Dade a Abuja, a nan Kubuwa suka haifi Ramlat,sai fahat,sai Omar suna ce masa Daddy, da Shaheed karshe sai yar autar yarinya Ilham ita a kauye aka haifeta.

Bayan Idrisa ya tabka gagarumar sata a Abuja,aka kulleshi ya Dade a prison,bayan ya fito masu gidan suka koreshi daga gadi,suka tattara suka dawo Kano da Zama ya kama haya,nan ma ya addabi yan Unguwa da sata,ga masifa da dukan iyali,nan manyan Unguwa suka kawo masa Hukuma ta koreshi,ya canja unguwa still nan ma bata canja zani ba,dai dai unguwar da Idrisa Bai zauna ba a birnin kano,lokacin su Ramlat ko Hausa basa ji sai turanci sabo da zaman Abuja cikin yare,
Shi yasa komai nasu na yan Birni sukeyi ba yan kauye ba sabo da yanzu suke rayuwa a kauye kawai,

Bayan Idrisa ya kwashi Yayansa sai suka koma Katsina nan ma haka suna ji suna gani zaman Katsina city ya gagaresu,bayan nan Idrisa ya kara samun gadi a Abuja zone 11 nan suka koma rayuwarsu ta city,anan sukayi primary kaf har Ramlat ta kai Jss3 sannan aka kara samun nasarar korar Idrisa daga Aiki,suka koma wata Unguwa wato nyanya,

Dan Uwan Idrisa wato Yayansa Malam Isa dake kauye shi ya kira Idrisa a waya tare da bashi shawara cewar ya kawo masa yaransa kaf zai rikesu da Amana,shi kuma ya dinga zuwa kauye wajensu,su dai Su Ramlat basu ji dadi ba duk da wahalar da suke Sha a hannun iyayensu basa kaunar Kauye,Amma haka aka zubosu a mota aka kawo kauye,

Suna zaune lafiya aka sa su a makarantar gvt abin haushi sabo da jahilci yayiwa kauyen yawa haka aka maida Ramlat Bangaren Arabic,duk da cewa suna islamaniyya ko a Abuja amma me makon ta safe a sata a boko yamma Islamiyya,sai gaba daya both yamma da safe Arabic,

Ramlat lokacin tana yarinya haka suka dingayi,daga nan Idrisa yana yo musu aiken kudi da su sabulai,toothpaste da sauran kayayyaki amma me sai Malam Isa ya kwashe komai nasu Ramlat ya bawa yaransa,

Gashi matarsa Uwa ta hanasu abinci,duk aikin gidan su zasuyi,Ramlat da ta gaji ta nemi Aron waya ta fadawa Idrisa ina da Bala'i.

Tun daga Abuja kafa ba takalmi Idrisa ya tako har kauyen jigawa ba bincike ba tunanin yan Uwa ba komai yaci mutuncin Malam Isa zagi ta Uwa ta uba kuma yana matsayin Yayansa Uwa daya uba daya,Isa yasha Kuka yace Idrisa babu ni ba kai har abada,
Bayan tarzoma ta lafa a kauyen Idrisa ya nemi wani kangon gida ginin kasa ya zuba yaransa tare da Hafsatu ko siminti babu a dakunan,ga yunwa haka suka fige suka lalace suka yi baki,

Har Ramlat ta shiga ss1 sauran kannenta suna primary fahat yana js1,duk schl din kauyen Ramlat ce me kokari,ga turanci sosai dan hausarta bata fita sosai ma.me gidan dake kauyen ne yace su tashi su bar masa gida zai yi aure,
Abu da A'i yayyen Idrisa su suka dauki yaran sannan Idrisa ya koma Abuja ya samo kudi suka bashi filin gadonsa ya Gina gidan kasa,A'i tayi masa rooping da sauransu suka koma gidan Kansu a kauyen,sai dai Idrisa yaje Abuja ya dawo kauyen ya samesu,abin haushi idan ya tafi kafin ya dawo sai ya kwashe shekara amma aiken Dubu daya yake yo musu,Abu da A'i da sauran dangi su suke tallafa musu,

Tun su Ramlat suna kwanciya har suka koma zuwa gona suna yo itace da aikin Gyada ana biyansu kudi, sabo da haka Ramlat ta fara fita zancen dole bata son mutum zata ce tana so dan ta samu kudin sabulu wajen samari.

Mami Babar Hafsatu kakar Sardauna dake zaune a Rijiyar Zaki cikin Kano itace taji tausayinsu tace Ramlat kar ta lalace ta dawo wajenta da Zama cikin kano,daga lokacin Ramlat ta koma Kano ta bar yan Uwanta sai dai tana zuwa ganinsu watarana.kafin kace me Ramlat ta yi kiba ta goge tayi kyau ta Zama yar gayu,lokacin Sardauna yana London karatu.
Idrisa kamar gaske Ramlat nayin shekara daya tal wajen Mami har an sata a schl anyi mata transfer, ya kwashi yan Sanda ya karbo yarsa tare da cin Mutuncin surukarsa,

Daga nan Ya kai Ramlat Zangon Katab gidan Abokinsa ana riketa ko waec da Neco bata zana ba,haka nan Ma ta saba da Zangon Katab ya kara ciwa Abokinsa mutunci wai yarsa zata lalace,

dauko abarsa yayi tare da kara bawa yayarsa Talatu dake zaune a cikin Kano gwammaja,anan Ramlat ta dinga zaman banza har Allah yasa take zuwa Company na Ginger,matsalar gidan Talatu mijinta wani lusari ne har yaranta ciyar da Kansu sukeyi,shi yasa Ramlat ma a gidan girkin takeyi dole babu me ci da ita,amma duk da haka gwara Azabar gidan Talatu da Azabar gidan Idrisa,ga yaran Talatu yan mata sun tsani Ramlat sabo da kyakyawace,komai sai su dinga sace mata ga hantara da zagi.

Shi yasa idan Ramlat ta ji wuya sai kajita a kano,jigawa,katsina da Abuja,zangon Katab,idan taje nan ta Dade sai ta kada can,su kuma kannenta kullum suna yawon gidan makwafta har watarana su kwana a masallaci.

To yanzu Idrisa ya bar Abuja gaba daya sakamakon Zawo daya barke dashi yaki kuma tsayawa,shi yasa ya firgita ya dawo kauye gaba daya yake dan noma kadan.

Idrisa yana da yayye hudu Isa,Abu,talatu,da A'i sai sauran yan Uwa,duk cikinsu talakawa ne sosai,
Zaku ci gaba da Jin labarin sauran nan gaba.



AsmaBaffa
🏀🏀🏀🏀🏀🏀
🏀🏀🏀🏀🏀🏀


DUK INDA TA FADI




11,12,&13



Official



By
AsmaBaffa





Godiya nake readers.



Ramlat fara ce ba kar ba amma tafi chocolate haske,tana da idanu madaidaita,Round face gareta,ga yawan gashi ya wuce kafada da kadan,doguwa ce ba can ba,ba wani kiba ne da ita ba,amma ta wuce a kira siririya dai dai take,tana dauke da manyan cinyoyi da mazaunai,dukiyar fulaninta yan madaidaitane,basu kadan ba kuma basuyi yawa ba, bakinta dan karamine dauke da jerarrun hakora farare kar da yar wushirya siririya a tsakiyar hakoran,ba karamin kyau wushiryar tayi mata ba.

,Ramlat me tsabtace ta iya daukan wanka sai dai Talauci daya sasu a gaba babu abin yi,me rikon Addini ga hakuri da tausayi,sai dai muguwar malalaciya ce,wataran idan tayi wani abun sai ka kusa zaneta sabo da rashin wayo,amma idan kuma tayi wani abun sai kace tofa Ramlat muguwar shu'uma ce ta gasken gaske musamman ta fannin tsara soyayya idan zata cuci mutan kauyen,
Ko da iskanci kaje wajenta baza ta bari ko yatsa ka rike ba kuma sai ta tsare mutum wanda Bai San sanda zai bata kudi ba,kuma baza ta taba rokonka kudi ba,idan ma saurayi ya bata da yawa to sai ta dauki kadan na iya bukatarta ta gobe ta bashi sauran kudinsa,

Baza Kuma ta saki jiki ta nuna ma love ba dan tana tsoro ta yaudari wani,kawai sai dai tace muci gaba da mutunci idan naga halayyarka tamin sai mu fara soyayya na aureka,
Samarin da Kansu suke guduwa idan suka ga Ramlat lallai ba sansu take ba,sun sheka sunga ba kwaya.
Ramlat bata taba son wani ba domin Har tambayar kanta takeyi ko bata da lafiya ne,domin samari babu kalar da batayi ba both birni da kauye amma bata taba Jin digon son wani dan Adam ba ko guda daya.
tana so ma ta samu tayi aure ko ta huta da masifar da suke ciki ,wannan kenan.

Ci gaban Labari

Ramlat ce zaune tana dama musu koko da safe,tsautsayi yasa rabin gasarar ta zube a kasa,Idrisa yana zaune a tarbarma yana dinke slipas dinsa yaga hakan ta faru,
Zagi ya fara aikawa Ramlat yana danna ashar manya manya,Ramlat jikinta sai rawa yakeyi har ta fara kuka tana bashi hakuri,shi kam ko a jikinsa sai ma kara fusata da yayi.

Kanta yaje ya rufeta da duka kina sani yar iska,dabba,akuya dan kudina kenan suka rage na siyo gasarar amma shine kika zubar yar bakin ciki azzaluma,muguwa tassss ya kwade mata kai,da kyar Hafsatu ta fito ta miko Naira Dari tace gashi a siyo wata in dai akan gasara ce gashi na biya kudin da ka kashe a daina dukar min yarinya,

Fisge kudin yayi tare da kaiwa Hafsatu masga Bai sameta ba ta goce ya bugi iska,fuuuu ya fice daga gidan yace Ku kwana da yunwa tunda an biyani kudi na.
Tun safe basu ci komai ba,sai Hafsatu ta dauko wasu kayan sawa kala daya na Ramlat masu dan kyau tace bari na saida wannan na siyo mana abinci,
Ramlat dake Kuka yashe a kasa tace haba Umma yanzu kayana fa sun kare Saura guda Uku kacal ko na zuwa unguwa bani dasu,kullum kayana ake Eba yanzu idan kin siyar da wannan Saura biyu kacal,

Watsa mata kayan Umma tayi tace dan uwarki ga tsiyarki nan,ba ruwana Ku kwana da yunwa,yinin ranar basuci komai ba,sai Ramlat ce ta je gidan Abu da A'i ta samo musu dumamen tuwon dawa miyar kuka,
Suka ci suka koshi abinsu.

Yauma kamar ko yaushe Ramlat ta fita zance tana tare da Amadu me Rake suna ta hira yana ta zuba mata kauyancinsa ya fara magana kamar haka:
Hajiya Ramlatu yan Mata tare da kafe ta Ido kurrrr....Ramlat abin dariya ya bata ma tayi murmushi ta kau da kai,yaci gaba a'a...a'a...kai zaki sa numfahina ya dauke billahillazi zaki kar ni Ramlatu..dariya Ramlat ta kama yanda yake yaye dafaffun hakoransa da dakikantarsa.shi kuma Amadu ya zata birge Ramlat yayi yau zuwansa na farko.

Ya kara karkacewa tare da leka fuskar Ramlat yace Tooo fa Alqur'anin Allah mun gani muna so,domin ni yanzu akanki zan iya yin komai,zan iya saida gonata,ki amince babu abinda bazan miki ba,komai na duniya buruni kawai Aradu naji zaki aureni,
Da kyar Ramlat take rike dariyarta,tace sai dai ka bari muci gaba da mutunci idan naga halinka yayi kana kyautata min zan aureka,
Tsalle ya buga yace Iyyyeeeee Allah dai ya biya tawan,uhmmm kaga ta wajena wannan iya tsara zance filla filla kai wallahiiiiiii....Allah yayi baiwarsa Anan.

Ramlat tace baza ka sani ba sai nan gaba,yace aaaaaa iyye...kice hike nan ni,ai kuwa zaki ga sakamako,kudi ya zaro dari Biyar ya mikawa Ramlat tare da cewa yar makaranta jinin Bature ungo karbi a siyawa Umma goro, munafuka harda kin karba wai kar ya dauka mayyar kudi ce,
Amadu yace karbi mana rabonki ne ai ni kuma Allah ya dora min,ni da kika ganni kyauta ce Dani ga siye siye,kwanan nan zaki dinga cin doya da kwai billahillazi kuwa,
Ramlat taki karba yace ki karba gwara kici sabo da ni indai aka min abin kirki to wallahiiiiiii Allah hankalina baya kwanciya sai na rama,na saka da Alheri nima,

Sadaf Ramlat ta karbe kudi sumi sumi a hijab tace to sai da safe,yace to sai Yauhe ta wajena? Ramlat tace ranar Asabar nan ta shige gida ta barshi yana ta faman murmushi ganinsa ya gama siye zuciyarta.

Washe gari da yamma Ramlat ta tafi ebo ruwa ta hadu da wani Jibrila yazo garin daga wani kauye shima,nan ya gyara hularsa yabi bayanta ya fara rangada Sallama Ramlat ta kara hade fuska dan kar ace bata da class tare da yin Banza da Jibrila.
Jibrila da kyar ya samu ta saurareshi shi dama dan karya ne don haka ya fara zubota:

yan mata ni nan da kike ganina I am a big boy, I am Doctor, my name is Jibrila or Jibril Doctor, nasan kina Jin turanci I am a speak English grammar, I am from Dan Madaho Town,duk da cewar Kauye ne amma Am malaging Doctoring In the Village,treatment the people in the Village, urgent sick like uhm........ ya fara ina... ina.. domin ya manta sunan Amai da gudawa da turanci, can dabara ta fado masa ya sosa kai yace kwalara Kamar Zawo da Amai,sanyin kashi da sanyin jijiya tare da cunkushewar ciki kin gane? Ramlat tace lallai babban likita ne ashe, yace yes duk garinmu ba kamata domin ina Jin turanci,babana shine kansilan garunmu,kuma wallashi tallashi (wai ya waye ba Hi da Hya shine komai sai shi da Sha)ni nan da kike ganina dan gata ne kije kauyenmu ki nemi tarishi na,suna tsaye sai ga Abokinsa wanda suka zo kauyen tare yazo,yace ahhh Dafta Dafta uban karatu yayi gaskiya kayi dace,yan mata ki rike hi Amana wannan da kike gani kaf garin babu Dafta kamarsa,
Jibrila ya kece da dariyar farin ciki yace to kinji dai ko ga abokina Haruna me shayi kaf garin mu babu me iya shayinsa,ai mutumina muna nan muna Shan shirarmu, Haruna yace sai ka aurota zata Hya hayin taji ai mutumina.

Ramlat tasan duk shirme ne amma sai ta nuna ta yarda da zancensu gaskiya ne har biye musu tayi sukayi hira sama sama bata bar wajen ba sai gashi sun bata Dubu daya,
Nan ma saida suka Sha fama kafin ta karba wai ta nuna musu itama bafa kudinsu take so ba,sallama sukayi mata Ramlat tace gaskiya Ku wayayyune kuma kun gama birgeni zaku iya ci gaba da neman soyayyata idan kuma kukayi wasa a kasa Ku.Haruna yace ai baza mu yarda a ture Gomnatinmu ba, Jibrila kuwa ya kara zaro maganin mura Cold time da paracetamol hade da flagyl ya mikawa Ramlat yace ga irin abun sana'ar tamu kema ba a barki haka ba,ba tare da kinsha maganin gajiya ba.

Ramlat tace ai Shan magani haka kawai Illa ne,sai an auna mutum an tabbatar da cutar sannan likita ya rubuta ma magani ka Sha amma haka kawai zan watsa kwaya? Jibrila yace ai kingama ganin babban likita,da ganin ki ai anga marar lafiya malalaciya kina tafiya kamar zaki karye ga fatarki da gani anga kalar shawara...Ramlat tace to na gode ta wuce,tana zuwa gida ta boye maganin tace uban wa zai sha.

Jibrila dai ya fara schl of Hygiene ko shekara baiyi ba aka koreshi daga makarantar sabo da satar Amsa da aka kamashi yana yi ana jarabawa,babu abinda ya sani Bai San komai ba,
Amma yazo kauye yace ya gama karatu ya bude chemist tare da fara siyar da magani,a kwana a tashi sai ga Jibrila ya kware wajen bada magani tun wani yana bayarwa dai dai,wani kuma haukarsa yake hada musu,har ya koyi Allura a jikin alummar kauyen masu karancin Ilmi,yazo ya koyi sa drip,daga nan Ya fara karbar Haihuwa,yanzu haka kaf kauyen babu ungwozoma sama da Jibrila,
Komai sai ace kuje wajen Dafta Shugaban likitocin Nigeria.

Duk wannan samarin da suke zuwa Idrisa yana sane dasu kuma idan yaga dama har duka Ramlat take Sha a wajensa sannan ya kwace kudin zancen ya tafi shaye shaye dasu,shi yasa watarana take boye abinta wajen Abu idan sun shiga matsala ta dauko suyi amfani dasu,
Hafsatu kuwa tana nan bata canja Hali na tafiye tafiyenta ba,

Mohd Sardauna zaune yake a palonsu Mami na gefensa yana aikin business din mall dinsa a system,bayan ya gama kida ya kunna a speakers manya dake palon yana jin kidansa yana bin wakar Chris Brown harda lumshe Ido tare da dora kafa daya kan daya,Mami kawai dariya take Sha tana kallon kuruciyar Jikanta kala kala,
Washe gari 11am Sardauna ya shirya cikin shigarsa ta ko yaushe kana nan kaya,wando Jean black pencil hantsar har wajen kusa da gwiwa ta kawo,rigar me dan tsayi kadan armless blue and white sai top ya dora wata a sama me dogon hannu yasa pcap yayi kyau sosai da sosai takalminsa ma black nan ya shiga fesa turare sosai sannan ya fito tare da yiwa Mami Sallama ya wuce wurin aiki shopping Mall dinsa domin yaga yanda ake aikin,
Harda dan Office din Sardauna a ciki dan madaidaici me matukar kyau,ko Office din ka shiga zaka San na dan gayu ne yanda aka tsarashi neat,
Sardauna ba wani kudi ne dashi ba amma akwai karfin Hali,sai yayi abinda wani me kudin bazai iya ba,ko mutunci sukeyi da mutum to sai ya dinka masa alheri,
Ya iya maida Goma ta koma ashirin da planning shi yasa bashi da wata matsala komai a nutse yake abubuwansa,
Ma'aikatan Mall dinsa dadin aiki suke ji dashi duk da karancin shekarunsa Ogan nasu yasan me yakeyi,amma fa suna ganin feleke a wajensa kuma suna Shan dariya,

Ya dan Dade a office din ya gama abinda zaiyi direct wajen siyen motoci ya wuce,me saida motar saida ya mugun gajiya da Sardauna wajen zaben mota,da kyar aka samu wacce tayi masa marcedes Benz ya Zaba ruwan Toka me duhun gaske,saida ya mata tint,kujerun ma sai da aka sa musu wata rigar yan gayu me laushi,
Akayi mata komai da ake bukata sannan ya tuka abarsa sai gida,dama ya Dade da koyon driving wajen frnds,

Yana zuwa ya fita ya tura dan gate din gidansu ya shiga da motarsa dalleliyar gaske,Mami ta tsorata ta fito da sauri,ta zata wasu bakin masu kudi ne suka zo musu sai ta hango dan jikanta ciki ya ware kida a cikin motar,
Fitowa yayi yana murmushi yace Mami munyi mota muma kin huta zuwa unguwa a ta haya,
Mami tace Muhammadu kaine da wannan uwar motar,yace na fada miki Mami ai sai dai na siyi Babbar mota,wannan da kike gani 5millions kenan,
Mami tace lallai Muhammadu ka gaji Ubanka wajen iya tattali har yaushe ka Tara wannan kudin,
Murmushi Sardauna yayi tare da cewa Mami kinga gidan nan dake jikin gidanmu ko? Mami tace eh lafiya? To yanzu sun tashi sun koma Abuja,ni na siyi gidan zan rushe sai mu hade shi da Namu na sake dankara mana gidanmu ko kuma idan kudin sunfi yanda nake tunani sai na siya mana a wani G.R.A mu Faso gari ko ya kika ce? Idan kuma Bai miki ba ki zabi unguwar da kike so,

Mami murna da farin ciki sosai tace zabi ai sai dan gayu kayi komai da ya dace Mohd, sai addua take sambadawa motar da me motar.
Shagwaba ya fara to Mami get in d car in danaki kiji motar Mana,Mami tayi bismilla ta shiga mota,Sardauna ya figeta ko gate Bai rufe ba gidan a bude ya tafi da Mami yayi ta yawo da ita tare da zagaye Unguwar sannan suka dawo.
Mami gobe ki shirya da yamma muje muyi shopping naga kayan abincinmu sunyi kasa.Allah kaimu dan albarka.

Ramlat da yamma tana gidan Abu wani yaro yayi Sallama wai Ramlat tazo inji Tanimu,Ramlat dai bata San wani Tanimu ba,Tanimu yana tsaye ya dau wanka domin saida ya tsaya a gida suka hadu da Abokinsa suka rubuta kalaman da zaiwa Ramlat sannan ya zauna ya haddacesu kaf a kansa sannan ya taho zance zai saukewa Ramlat su,Duk inda yaga abokansa

Please Login or Register in order to submit comment