Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tare da cewa am sorry Queen,

Me kike so yau?banza ta masa,Gwiwowinsa ya dire a kasa tare da tallafo hips dinta da hannunsa biyu sannan ya dora kansa a cinyarta yana faman lallashinta yana bata hakuri haba Sweet heart am just kidding you fa kema kin San I don't mean to hurt u,
Kamar bata ji ba haka ta masa,d amunta yayi da magiya sai lokacin tace ni kaji nace ina fushi dakai?,ai gaskiya ka fada mene a ciki? Ok to naji Amma me yasa kike shareni?Kai kake ganin hakan, to me zaki ci yau a kawo? Ramlat tace bana ci ni haka nake so na yini,kuma kince bakya fushi mene amfanin kudin da Queen bata so wlh gwara na rasa sisi yafiye min kwanciyar hankali.
Harara Ramlat ta zuba masa, kansa yana Saman cinyarta har ta gama abinda takeyi ta mike da niyyar Barin wajen,Da Sauri ya rike ta tare da cewa wai mene haka pls baki san wasa ba Ramlat?

Shuru ta masa idonta tab da Hawaye mikewa tsaye yayi tare da rungumo ta jikinsa kamar jira takeyi ta fashe masa da kukan shagwaba yana dan bubbuga bayanta a hankali yana bata hakuri tare da cewa nine?sorry Bazan kara ba baki san wasa ba daga tsokanarki sai fushi,baki ta cuno gaba tare da cewa ba wani wasa ba haka kukeyi ba daga wasa sai ya koma gaske,wacce ta Isa na kalleta bare har na aurota?kafi ni sani ai sai yanzu zaka shiga 25yrs kaga kuwa yanzu kake ji da kuruciya zaka auro yarinya ni dama ai kusan mate muke.

Cewa zakayi na tsufa ka auro wata dai dai kai ta furta tare da ci gaba da Kukanta,Dariya Sardauna yakeyi Ke da kike ce min yaro sa'anki nefa Amma kina kuka daga na miki wasa,ni wacce Mace zan gani ta kaiki,sai dai kawai na kara dan Ra'ayina,Sardauna ya kara furtawa dan yaga kishin Ramlat domin dadi yakeji a ransa matarsa na sonsa,Ramlat kuwa Kuka ta kara fashewa dashi gashi nan ka kara furtawa da kanka zaka auro dan ra'ayinka Allah sai ka sakeni Bazan zauna ba,fuuuu Ramlat ta shige daki kamar wasa sai gata ta fito da katuwar akwati ita gida zata tafi dole,M ami wacce fitowarta kenan dauke da plate din Naman Rago tace ke kuma fa? Ramlat tana shesheka ta fara sanarwa Mami,

Mami kin san me yace kuwa wai na tsufa same age muke dashi sai ya auro kanwarsa yar 16yrs,Harara Mami ta makawa Sardauna sannan tace kyaleshi ai wajena zaki dawo kiyi masa yajin tunda duk gidane,sai ki dawo dakina sai yazo Biko idan munga dama ki koma.
Trolley taja tayi hanyar dakin Mami Sardauna ya rike yana Haba Mami wato yanzu bakya so na ko?ai akan kishiya Bazan Goya maka baya ba Ramlatu ai yar halak ce,Mami da wasa fa nake daga tsokana sai ki yarda wlh wasa nakeyi mata kema kin sani Mami..
Da kyar Mami ta amince tace Ramlat ta koma dakinsu da kayanta.

Lantan ce yau a makaranta wata yarinya ta zageta ta kama yarinyar kamar Allah ya aikota tayi mata jina jina, jini ta hanci ta baki,malaman suna gani basu dauki mataki ba,
Ranar katsam ana tashi sai ga lafiyayyar motar Saddiq da Alama Sa'adat yazo dauka tare da driver dinsa,
Yarinyar da Lantan ta Zane jini duka fuskarta da gudu ta karaso wajen motar Saddiq tana barka kuka,yana budewa ta kwashe karya da gaskiya ta fada masa,yasan Halin Sa'adat sarai zata aikata,hakuri ya bawa yarinyar da kudin magani sannan yasa Driver ya Rakata clinic na schl din,
Kafin Lantan ta karaso tuni labarin ya iso wajenta cewar Saddiq ne yazo daukanta yau kuma wacce ta Zane ta fada masa komai,tun a hanya Hawaye suka fara wanke fuskar Lantan tana yau na shiga uku na Lalace,wata kawarta tace to ke kibi ta dayar hanyar mana sai mu fada masa kin rigada kin wuce gida,Lantan tace ai abinda zai min wlh yafi wannan gwara naje kawai idan yasan na tafi gida har can zaije ya kusa hallakani.
Hankalin Lantan ba a jikinta ba ta dinga Sauri zuwa wajen da take hango motar Saddiq,
Tana zuwa ta fara kame kame tana cukwikwiye Hijab dinta ta rasa me zata ce sai tace Ya Saddiq gobe zan koma kauyenmu wlh na fasa karatun nan iya wannan ya isheni Rayuwar duniya,dan Allah kacewa Abba Abdullah ya maidani gidanmu sai hawaye sharrrrrr harda shesheka,
Yau dai Lantan ta bawa Saddiq tausayi,Hannunta daya ya riko,Lantan taji tsigar jikinta ta tashi wani yirrrrr....zirrrrr shima Saddiq yaji, a hankali yace me yasa kika daketa haka?Kuka taci gaba tana dan Allah kayi hakuri wlh Bazan kara ba tsautsayi ne yau ma,kuma muna rubuta Test ta dinga copying nawa,na mata magana ta zageni, karya Lantan ta kara tace sannan kuma baka ji ba yanda ta dinga zaginka tana dura ma ashar,Saddiq ya gano Lantan tayi kari Amma sai yace dan Allah?Me tace?Sa'adat ta gyara tsaiwa harda kara rike hannun Saddiq irin an samu shiga tace ai tace Saddiq din Banza,shi din wa?Me akayi aka samu wani Saddiq,kina gadara ke me yaya Saddiq,dan yana da kyau aikin banza aikin wofi,kuma sai na aureshi kin koma kanwata na dinga zaneki,Murmushi Saddiq yayi yace lallai bata da kirki,Lantan tace ai shegiyace ta gaske wata maganar ma Bazan iya fada ma ba irin zagin da ta dinga maka ai kare bazai ci ba,to Dan Allah laifina ka gani dan na mata duka,ta zageka na kyaleta ai nayi asara Yaya Saddiq,D ariya Saddiq yake yi yanda Lantan take gwada kalar zagin da akayi masa yasan Karyane kawai ya daure fuska tam yace muje gida,
Hamdala tayi yau bata sha Mari ba,suna zuwa gida yace tayi tsallen kwado har zuwa dare,wata Soja yasa mace tayi masa gadin Lantan.

Babu magiya da Kukan da Lantan batayi masa ba amma yace sai ranar da kika daina Karya,a ranta tace wato ya gano karya nakeyi,cikin Uwar Rana Lantan take ta frog jump har sai da Abba Abdullah ya dawo ya kwaceta hannun Sojar nan,a mma yanzu maimakon taji haushin Saddiq sai taji mugun birgeta yakeyi matuka,kullum bata da aiki yanzu sai tunanin Saddiq mugu,
Sai da Lantan tasan yanda akayi ta gano gidan Saddiq cikin Barak din,sunday ba schl ta shirya taci kwalliya ta tafi gidan a hankali ta danna Door bell, wata Dattijuwa da Alama Maman Saddiq ce ta tsufa ba laifi,Lantan ta washe mata yan kyawawan hakoranta tare da gaisheta har kasa Matar tace shigo mana,
Har kayataccen palonsu ta bi matar tare da Zama cikin daya kujerar me tsadar gaske,yar aiki ce ta cika mata gabanta da kayan ciye ciye,
Lantan ba bata lokaci taci ta koshi,sannan ta kalli matar tare da cewa Umma makwaftanku ce mu gidan yana farkon layin nan sannan ni kawar kawar yaya Saddiq ce shine yaki kawoni mu gaisa ai ko na dinga bincike har na gano nan ne gidan nace ai ko dole na gaisar dake.
Dariya Umma tayi tace amma kin kyauta na gode yar Albarka,Umma harda murnar zuci Allah sa Saddiq dinta yaso wannan yarinyar ya auro taa fili tace nima yau satina biyu da zuwa Amma Kano muke da zama da babansa tare da kannensa su Biyu Maza.
Lantan tayi murmushi harda cewa Allah Sarki,Umma baki da wani aiki na tayaki? Umma tace an gode Amma duk anyi min komai har wanki me Guga kadai nake jira yazo ya goge min.

Da Sauri Lantan tace na iya Guga kawo na miki dan Allah Umma,Umma ta kwasowa Lantan kayan guga da yawan gaske,tayi mata shinfidar guga,ta dauki dutsen guga ta fara me kyau sosai,sai da ta kusa gamawa sannan Saddiq ya shugo dauke da Sallama,
Mamaki ne ya kamashi ganin Sa'adat a gidansa harda yiwa Umma guga,to yaushe ma suka saba?Sa'adat ta kalleshi tana dariya da fuskarta me kyau Saddiq yaji ta wani birgeshi,sannu Da zuwa ya Saddiq,Fuska ya tamke yana muzurai,Lantan tace ka daina mamaki ni sanda kake zuwa gidan mu ai ban yi fushi ba har zuwa kake ka bani punishment Bana fushi sai dan nazo gidanku zaka wani hade rai,Zan mareki taji Saddiq yace murmushinta me kyau tayi tace Umma na kusa na fika yanzu a wajenta,Sama ya hau yayi wanka sannan ya shiga Bedroom wajen Ummansa suka gaisa tace abincinsa na Dining,
Yana cin abinci saman Dining yana kallon Sa'adat tana aiki tare da rera wakarta.

Cikin fushi Ramlat ta shiga Bedroom dinsu,Sardauna ya rufa mata baya yana aikin Lallashi sai da taga kamar zaiyi mata Kuka sannan tace ba komai ya wuce ai ni baka ji nace zan rabu da kai ba amma ni bana son wasan kishiya, murmushinsa me kayatarwa ya saki sannan yace kishinki yayi yawa Babyna,Dariya tayi tare da furta ai gaskiya ne wannan cin fuska ne kake neman yi min gani da Katon cikinka,akan kishiya sai ki rabu dani Queen?ofcourse why not akan nayi sharing naka ai gwara na hadiyi zuciya na wuce.
Daina min zancen Tafiya ki barni ya furta tare da jawota ta zauna saman cinyarsa tana wasa da kirjinsa, My King pls ka dan min rawa mana?Na girma yan matana gashi har na kusa zama Daddy ina rawa ai ba tsari,shagwaba ta fara ita fa sai yayi Amma Sardauna ya ki yi wai ya girma,
Shirya muje yawo ki daina min rigima Queen.

Tana murna ta shirya cikin arnen Lace Fari kar me ratsin green,tayi kyau ka rantse ba mai ciki bace,Sardauna ya kunna mata wakar Ado gwanja wai sai tayiwa Babynsa ta
ciki rawa sannan zai tafi da ita yawon,Ramlat taji yawo harda kara turo cikin ta wani kara yi tare da dan juyawa kadan,
Kamar Jaririya Sardauna ya dauketa cak har mota ya sata a waya ya fadawa Mami sun fita.
Wani hadadden waje na manyan Yara masu kudi Sardauna ya kai Ramlat babu abinda babu na jin dadi da hutawa,kida na tashi sai kallon Su Ramlat akeyi best couple ever.

Yanda Sardauna ke ji da Ramlat yana kula da ita ba a magana abin kallo da birgewa,Icecream tace tana so tana zaune ya kawo mata tare da fara bata a baki tace bata sonshi yanzu chips zata ci,nan ma dandanan ya kawo yana bata,ko kuda bai Isa ya matso jikin Ramlat ba,
Ita kuwa har mamaki takeyi yanda Sardauna ke sonta yana kula da ita,sai yanzu take tuno da kalaman Mata cewar auren yaro bashi da inganci basu san darajar mata ba,sai yau ta gane ko wanne da halinsa wasu ne suke bata wasu yaro idan kayi dace yafi Babba komai,kai tsaye a daina sukan auren yaro mace zatayi aurenta mata su dinga zugata cewar yaro ne bai san darajar aure da mata ba,na Allah bai taba karewa ba,ko wanne da halinsa ga dai Sardauna yafi dan shekara 100 hankali ma da sanin kima da darajar aure da matarsa,ba wani biye biye,a daina yanke hukunci ba lallai a Novels ba akwai Yara da yawa da sunfi manyan komai.

Hammar gajiya da bacci Ramlat ta fara wanda Sardauna ya rigada ya gano hakan tunda 8pm tayi,take away yayiwa Mami suka wuce gida,Ramlat sai shagwaba takeyi harda kuka wai ta gaji gaba daya ta ruda Sardauna Sauri yake suje gida ya mata tausa.
Kallonta yayi tare da cewa ko na tsaya da Driving ki huta a motar? Hannu ta yarfe ayi a kaita gida ita,minti kadan suka Isa gida lfy,Mami ya mikawa kayan ciye ciyenta tana ta Sa Albarka,Ramlat tuni ta mike saman Bed,ruwan zafi ya hada yayi mata wanka shima yayi tare da Sa mata yar rigar baccinta sabuwa me kyau pink,Kwanciya sukayi ya fara mata Tausa me dadin gaske nan take bacci ya kwashe ta,
Sardauna ya tasheta Queen daga tausa sai bacci tashi kiji wata magana,Ramlat tasan maganar da yake nufi tace a bari sai anjima ko da asuba King,ni yanzu nake so pls Dear,
Tana mugun jin bacci haka ta mike tare da watsakewa suka fara murje juna da salonsu,sai da suka jiyar da juna dadi sosai sannan sukayi bacci abinsu.

Chuchu ana gidan mijinsu Prof shiri yayi tsaf tare da Tafiya gidan yaransa mata zai musu nasiha ta gaske a nutse.
Gidan Chuchu ya fara zuwa sanye cikin suite yasha farin glass, sunsha Nasiha da Laws iri iri sannan ya tafi gidan Sauran yayan nasa suma sunsha nasu ba laifi..Gidan Juicy da ya je aka kawo masa farfesu,Prof yace harda Farfesu to karfa ki dauka cewar kullum zaki dinga cin irin wannan,shi aure ba haka yake ba,watarana aji dadi watarana kuma Asha wahala,kar kice kullum sai ya baki wannan kinci,abu na gaba kai kuma Bazan boye ma ba kar kace na zalunceka ka saka ido a kan Amaryarka tun a gida bata da kunya kayi hakuri ka kula sosai,Juicy ta kalli prof tare da cewa haba dan Allah Papa,Prof yace ai gaskiya na fada masa dan uwaki ni bana boye boye na dannewa wani hakkinsa.Juicy haushin Prof taji shike nan miji zai dinga mata gori,an musu auren dole kuma wai gashi yana jawo musu gori.

Ramlat cikinta ya shiga wata tara kenan ta damu kanta ita tayi Sauri ta haihu ma ko taji dadin duniya,Mohd gininsa na Abuja an gama komai da komai kawai jira yake Ramlat ta haihu su koma can,Mami tace tunda haihuwar bata zo ba kawai su tafi ta haihu a can,
Duk kayan da zasu yi amfani dasu iya na sawa su kadai Sardauna yasa a motar Sa aka kai can Abuja sabon gida har motar, gidan Sa kuma da suke ciki ya Bada haya,suna tashi wasu zasu zo su zauna a gidan, washe gari ya musu Booking flight to Abuja,suka tafi tun a jirgi Ramlat ta fara nakuda kusa da Sardauna,Mami dake gefe tana kallon irin cijewa da gumi da Ramlat takeyi.
Kanta tasa saman kafadar Sardauna tana Hawaye kadan sabo da Azabar da takeji,
Sardauna sannu yake mata duk ya rude burinsa kawai su sauka a kaita asibiti karta haihu a jirgi,Alhmdllh Jirgi ya sauka Lfy a garin Abuja da sauri suka fita,Ya dauki Ramlat Bai tsaya ko ina ba sai cikin Taxi da suke airport din,direct Hospital me kyau suka kai Ramlat,Mami tana biye dasu,nan take aka basu room,Da sauri ya biya komai tare da komawa waje yana jira cikin damuwa.
Bilkisu Maman Sardauna ce ta fito daga asibitin cikin shigarta me kyau,ido hudu sukayi da Sardauna wanda ke jiran Matarsa ta haihu,da wuri Sardauna ya dauke kansa yana kallon wani waje daban,
A gigice Bilkisu ta karaso wajen Sardauna har tana tuntube zata fadi,
Ba tare da Bata lokaci ba ta dire gwiwoyinta a kasa tana Kuka wiwi a gaban Sardauna,
Munyi kuskure ka yafe mana Mohd,bamu kyauta ba mun zalunceka,na tabbata bamu cancanci iyaye a wajen ka ba,amma da Allah kayi hakuri wlh ba sai ka dawo wajenmu ba,kayi hakuri ka yafe mana,Babanka yana kwance Rai a hannun Allah Sanadiyyar abinda yayi muku,
Nabeel da Nabeela ne suka tsomo baki pls Bro we are Sorry kayi hakuri ka kalli darajar iyaye,
Ammar kuwa Hannun Sardauna ya rike yana rokonsa ya hakura yaje wajen Daddy,
Mami dake gefe can tana Jin komai farin ciki ya mamayeta Sardauna da alama zai shirya da iyayensa da yan uwansa,
Mohd ya tausaya musu ganin duk sun rame sun koma wasu iri dasu,kallonsu yayi jikinsa yayi Sanyi yace sai abinda Mami tace idan ta yarda sai na duba shi,Yafewa kuma ni bakuyi min komai ba idan ma kun yi min na Dade da yafe muku,Mami ce ta karaso cike da farin ciki tace Alhmdllh jikana Allah yana son me hakuri da yafiya,na yarda kaje ka duba lafiyar dana kar ya rasu baku gana ba,ku kuma su Bilkisu wannan kadai ya isheku ishara,ba a wulakanta kyautar Allah baku San me ya baka ba,ga dai Sardauna kin gani kun kwace masa komai kuma Allah yayi har yafi da kudi,bai taka muku ba Bai zubar muku ba sabo da kwadayin duniya,yanzu ina kudin naku?rannan munji a radio Kabiru ya samu karyewar Tattalin Arziki babu rabin arzikinsa ya kare kinga kanku kuka cuta Alhakin mune ya kamaku,Allah yasa bakin wahalar kenan,Bilkisu tace dan Allah Mami ki yafe mana, tabe baki Mami tayi sannan tace ai yafewa ta Zama dole amma mu baza mu zauna a gidanku ba,gidanmu daban naku daban,Murmushi Bilkisu tayi tare da cewa Mami hakan ma mun gode ai indai kun Amince zamu dinga zumunci.
Mohd yace Mami bazanje yanzu ba sai nasan Halin da Matata take ciki idan ta haihu lfy,Bilkisu tace au Haihuwa zatayi?Mami tace Insha'allah kuwa,Muhammadu kaje kaga mahaifinka,Mami ki koma wajen Ramlat wlh ba inda zanje sai na tabbatar Queen tana lfy,Bilkisu da Mami da Sauri suka fada dakin da Ramlat take kwance cikin nakuda.










AsmaBaffa





Har kullum ina kaunarku masu Sharhi da masu kirana ta waya,afwa za a ci gaba da yi min Sabo da rashin lokacin typing.


Tnx alot.
🏀🏀🏀🏀🏀🏀
🏀🏀🏀🏀🏀🏀


DUK INDA TA FADI





246-250






Official






By
AsmaBaffa











Hangota sukayi tayi Zuru Zuru ta rike jikin karfen Bed kawai kamar ta suma,Sannu suka mata da kyar ta iya dago kanta tare da kallon Mami sai Hawaye sharrrr da shesheka yi take ba ji ba gani,ita dai bata ce komai ba,Tausayinta Nabeela kanwar Sardauna taji da Sauri ta kirawo Sardauna wai yazo tana kuka,ba a hana Sardauna shiga ba ya shige da Sauri,cike da rauni Ramlat ta dago kai suka hada Ido fuskarta jage jage da hawaye,amma duk da haka ganin Sardauna yana shirin Kuka shima sai da Ramlat tayi murmushi kadan tana girgiza masa kai kar yayi kuka,Mami tace iyye ah da sauki wlh tunda har kika San me kikeyi a gaban miji.

Hararar Mami Sardauna yayi wai tana yiwa Ramlat dinsa masifa,Mami tace zaka bar dakin nan yanzu marar kunya Ku Masoya ko?
Ramlat bata ganewa Hawaye ne ke zuba wani na bin wani ratatatatata,S ardauna ma kwalla ta cika masa Ido ya karasa jikin Bed din ya kara gyarawa Ramlat kwanciya tare da wale mata cinyoyi kamar shine likita,harda nade hannun Riga tare da rufa mata bedsheet ya tura kansa ciki yana kici kicin kwaye mata zani,duka yaji Mami ta zabga masa a baya Bilkisu da sha'awa take binsu da kallo tana dariya tare da cewa wannan jikokin naki basa ji Mami,Sai lokacin Sardauna ya kalli Mum dinsa Jin muryarta ta yan gayu irin tasa,a ransa yace me yasa to tun farko banji kalar Voice dinta ba sai yau?a ransa still yace itama yar gayu ce zan dinga kulata tunda dai muna kama da ita kadan.Bilkisu ma kallonsa take ta faman yi tana murmushi domin Sardauna wankansa kadai ya isa ya birge duk wanda yayi tozali dashi.
Bilkisu ce tayi magana ina kayan haihuwar?ko baka dakko ba?Sardauna a hankali yace yana wajen Mami,Mami tace gasu can,Nurses ne suka shigo sai lokacin Sardauna ya fita direct dakin da aka kwantar da Daddynsa ya shiga,shi kadai ne a kwance sai idanunsa da suke motsi,a hankali ya matsa kusa dashi tare da sa hannunsa cikin na Daddy ya fara magana,Dad Mohd ne gani nazo ni baka min komai ba na yafe koma mene,a matsayinka na mahaifi ai baka laifi,ko ba komai kune silar zuwana duniya,ko wajen dana ke aiki da ka karba dama Allah ya tsara hakan ko ba ta dalilinka ba,gashi yanzu naje wani garin har na linka da kudi Alhmdllh,Allah baka lfy Dad.
Firgit Kabiru ya bude idonsa tare da da mikewa zaune kamar ba shine kwance ba,kankame Hannun Sardauna ya kara yi tare da cewa da gaske ne ko mafarki nakeyi?da gaske ne Dad cewar Nabeel dake shigowa yanzu shi da Nabeela, Ammar na binsu a baya,
Nan take ya jawo Mohd ya kankame shi tare da sauran yaransa,Nabeela ma ta fado da gudu tace baza a barni a baya ba,
Dad harda Hawayen dadi,Sardauna dai kallonsu yakeyi dan Bai saba da su ba ba wannan shakuwar tsakaninsu da dai Mami da Ramlat ne to nan yafi sani,
Amma haka ya daure ya dinga hira dasu yana yake musu baki,su kuwa duk dama sun shaku da junansu sosai,Dad yace Mohd ba sai ka dawo gidana ba amma ina rokon da Ku hadu kuci gaba da juya sauran dukiyata kai da yan uwanka,Murmushi Sardauna ya saki me kayatarwa sannan yace ina da nawa Dad sai dai na koya musu na taya su Nabeel suci gaba da kula da harkokinka amma ni Allah ya bani nawa sun isheni,hakan ma yayi Mohd jikan Mami cewar Dad yana dariya.
Sardauna ma Zama ya gyara yana murmushi Nabeela sai faman kallonsa takeyi,Nabeel yace Nabeela wannan kallon fa?tace hmm kai dai bari ya Nabeel yafi mu kyau wlh da ace ba dan Uwa na bane ai da dole yayi ta biyu Dani amma Blood daya hhhhh suka kwashe da dariya gaba daya Sardauna yace da kin mutu kuwa bakiyi aure ba domin wife dina ban iya hadata da kowa wlh, kuma thnk God Blood daya muke sai ki adana kwadayinki,
Fahat ne ya shigo dawowarsa kenan daga schl ya wuto Hospital wajen Dad,mamaki ya kamashi ganin Sardauna domin bazai manta ba ya taba ganinsu shi da Ramlat Antynsa a Jigawa state yana tuka Napep,Sardauna ma ya ganeshi yace amma wannan koma ta yane kanin Queen ne ko?wife dina wanda muka gani a Jigawa,Fahat cewar Dad nan ya bawa Sardauna labarin komai har haduwarsu dashi,Murna kamar me wajen Sardauna Ramlat zata ji dadi,

Ina Anty Ramlat? Sardauna ya watsa masa harara sai yanzu ka San da ita mun ganka a Jigawa tana ta faman kiranka kaki kula mu sai yanzu,Dariya Fahat yayi tare da cewa lokacin ina cikin fushin su Kawu wlh,amma yanzu na huce next wk ma zamuje da Nabeel can wajensu naji ance mijin Anty ya sai musu gida,Sardauna yace to waye mijin Antyn idan bani ba?banzan yaro kasa wife dina Kuka rannan.

Dariya sukayi gaba daya har Bilkisu dake shigowa ba karamin farin ciki takeyi ba gani family guda sun hade Kansu,
Mami ma ta shigo da Sallama Kabiru jiki na Rawa ya sauko ya durkusa yana bata hakuri,Mami tace tashi mun yafe mu Allah Baka lfy,
Ganin Mami yasa Sardauna mikewa ya koma wajenta yana tambayarta ya jikin matarsa,Jan hannun Mami yayi tare da barin dakin suka kebe,Mami ya jikin nata?har yau bata haihu ba?Mami da jimami tace ai sunce ba yanzu ba da Saura,

Tsaki yaja tare da zagin Doctors Na Nigeria tare da cewa Allah da nasan haka ne kasar waje zamu tafi ta haihu a can,Mami bari naje na kara dubata,ya shige dakin da kansa lokacin Ramlat ta Mike tsaye ance ta zaga dakin,bata iya komai sai hawaye Sardauna ya risketa a hakan,Tana ganinsa ta fara yarfe hannu,Addua ya rada mata yace ki dinga maimaitawa,Ramlat cikin kuka da masifa kamar zata cinyeshi tace ni wlh bazan iya ba malam, matsa ka dameni ka kyaleni naji da kaina, to fa Queen wannan masifa haka,ka daina fada min wata Queen ka nemeta can gidan sarakai ba ni ba,

To am so sorry muje ki

Please Login or Register in order to submit comment