Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka rantse turawan London ne sabo da su yan gayune wayayyu,kuma basa daga murya a hankali suke magana musamman Sardauna dan Iyayi da tsirfa,

Naufal yana shigowa suka tafa yace kutmar yaushe ka kayi wannan girman haka Sardauna just 1yr kaganka kuwa ka kara wani mugun kyau,
Tabe baki Sardauna yayi tare da cewa see u ban son Nonsense kai baka ga naka girman ba sai ni,common have a Sit let's talk,zama Naufal yayi yana wow....yayi kyau fa Office din naka,ban son kauyenci wannan har Office ne cewar Sardauna,
Ya akayine ka dawo lfy?Sardauna ya furta,Naufal yace hmm kasan me nifa aure nake so wlh gashi Dad yana kawo wasu magana barkatai,yace schl sai naje London Alhmdllh munje fa munyi har masters,n azo yanzu nace aure Sameera jirana take kawai na tura amma Dad yace wai a'a ba yanzu ba nayi kankanta gashi mun shiga 20yrs fa kuma yanzu wa zai ganmu yace 20yrs muke? Sai dai ace 30yrs.

Ni bazan iya ba ina da karfin sha'awa idan za Amin aure kawai ayi min,
Sardauna bin Naufal yake da kallo kawai yace ...ka bani mamaki kamar ba wise ba,u better change badan shirmenka ba Naufal me zakayi da aure yanzu,ba wai munyi kankanta ba no,kawai nauyi zaka dorawa kanka a banza,duk da nasan kai Dad dinka me kudi ne kuma muna dawowa ya baka babban aiki tunda Company har biyu ya baka ga business na wasu abubuwan ya daura ka akai,but ban san me yasa kake neman jajibo aure ba,ka rasa wacce zaka aura sai Sameera ko degree batayi ba,me ta sani har yaushe ta waye,nasan yanzu ko African kiss baza ta iya yi ma ba bare azo su french hot kiss,

Dariya Mohd yayi yace nama tuno yaushene yarinyar ta daina wanka a tsakar gidansu da kai muke zuwa muna kallonta fa,ka dinga Azumi ka rage cin kayan dadi kawai,amma aure ni da ina zancensa Amma yanzu na gano matsalar,ni kaina ina da abinda zanyi aure matan kasar nan basu waye ba gaba daya yan kasar Koko ne,ina tunanin ma wata kasar zanje a turai na auro baturiya ita ce dai dai da wayewata,nan sardauna ya gama zuga Naufal tsab,Naufal yace gwara da ka tunatar Dani mutumina kyalesu su karaci yawarsu.

Mohd yace ina so kwanan nan zanje wani kauye wajen Kanwar Dad dina zata bani Address dinsa,sannan zan ganta muyi Zumunci Mami tace min tana Shan wahala zan taimaka mata na kuma nuna mata gidan Maminta mu koma Happy family,
Tabe baki Naufal yayi Kauye zakaje? Akan Zumunci?Parent dinka basu damu dakai ba basu nemeka ba amma kace zaka je,ka kyalesu kawai idan sun matsu su Suzo nemanka,Kanwar Dad dinka ai ba wani zumunci bane yanzu iya wanda kuke Uwa daya Uba daya dasu kadai ake zumunci ka daina damun kanka,
Sardauna yace lallai yanzu na tabbata baka je islamiyya ba to bari kaji idan kai baka San muhimmancin Zumunci ba ni na sani,mene amfanin kudin da nake nema sabo da naci na tallafawa yan Uwa da Alummar Annabi,
Ina laifin ma kace na kyale su Dad tunda basu nemeni ba, amma kanwarsa laifin me ta min?

Ok...ok naji Allah bada sa'a ni dai bazan raka ka wani Village ba wlh,Sardauna yace dama kaji na nemeka ne? Haka kace?yea of
course,alright a dawo lfy kuma tunda baka Jin shawarata nima bazan bi taka ba auren Sameera ba fashi,

Banza a banza man kare me zata kareni dashi,yarinyar da ko Nono bata da,kai kanka sai dai manage,nan Sardauna da Naufal sukayi kaca kaca,a karshe Naufal yace kuma insha'allah a kauyen da zaka je za ka samo bagidajiya ka aura Nonsense,Sardauna yace foolish Man wannan kasan karya kake Negative thinker with ur fish brain,
Naufal yace stupid kaine me snail brain with ur big head like coconut,hhhh Sardauna ya fara dariya tare da cewa lallai kai yaro ne Naufal kalli yanda kake Childish,to hell with ur fucking Sameera or what so ever u call her, tsaki Naufal yaja sannan yace yara dai fuuu ya bar Office din,Sardauna ma ya Mike ya shiga motarsa sai gida.

Saida ya tsaya yayi shopping a wani mall sannan ya wuce gida a matukar gajiya,
Palo ya shiga da Sallama yana Mamina,wata Dattijuwar me aikin Mami ce ta fito wato Baba,

Sannu da zuwa barka da dawowa,ina yini dan nan? Sardauna cike da shagwaba yace haba Baba sau nawa zance ki daina gaisheni kin girmeni ni zan dinga gaisheki,kuma ni Bana son doguwar gaisuwa,ina yini,ya aiki,ya gida,ya..ya..ya tayi yawa kawai idan nace kin tashi lfy ko kin yini lfy kawai kice lfy kiyi shuru pls.

An gama Ranka ya Dade cewar Baba,babu abinda Sardauna yake so fiye da a kirashi da Ranka ya Dade,
Ga wani kirari da Baba ke masa kullum kamar yarima dan Sarki,shi yasa Sardauna yake son Baba yar aikinsu.

Ai kuwa Baba ta fara masa Kirari Ranka ya Dade,Allah ja zamaninka,takawarka lfy na Mami,dan Balarabe na Maminsa,farar fata farar zuciya,kaga me kyauta da guminsa,Allah kara lfy da Nisan kwana dan Baturen Mami,Dan gayu me wankan sukari kafin a Sami kamarka mazan sun kare,
Dadi fa ya gama kashe Sardauna,dariya ya kamayi tare da Zama saman kujera ya dora kafa daya kan daya kamar Sarki,
Mami ma wacce ta fito Dariyar Kirarin da Baba kewa jikanta takeyi,Mami tace bakya gajiya Hajara da kirari kullum sai kinyi sabo,
Sardauna ya kwace zancen ai da ace ni sarkine Babace jakadiyata,
Kudi ya irgo Dubu biyar ya mikawa Baba ladan kirarinta.
Baba kuwa Har da juyin murna.

Ramlat bayan ta kwashe watanni biyu a kano shiryawa tayi ta tafi jigawa kauyensu,
Yanzu gari an daina ganin laifin Ramlat da mahaifiyarta data bace laifin Idrisa ake gani,kullum zaginsa akeyi,
Sabo da haka Ramlat na dawowa Samarinta wasu suka dawo ta kara wasu sababbi,cikin wanda Suka dawo kuwa harda Jibrila Dafta me gwalangwajen turanci,
Yau ma yazo wajen Ramlat,tana fitowa ya Fara karyarsa da turanci,Ramlat tace gaskiya kai kyakyawa ne,Jibrila ya shirya Karin maganarsa da turanci wai zai fadawa Ramlat Har kurace zata ce da kare maye,
Sai yace a hyner can not say Dog is a witch.

Ramlat dariya kamar me,shi kuwa yace your love is like tropical Rainforest yanda ya mamaye ko ina,i am inside the local gamman of ur love,
Iam chairman of the Federal ministry of ur Love
Ur love is like Kano state in my heart ya gama hada babban gari gari a zuciyata,

Ramlat dai tana ji tana dariya Har ya bar gidan.

Kwana da kwanaki Ramlat kullum sai ta fita zance,hakan yasa Kawu Idrisa ya kara fusata ya samu wani dattijon liman yace Na baka yata idan tayi maka, sabo da nasan zaka rike ta da Amana,

Liman dai shi baya so saboda yasan Ramlat baza ta taba sanshi ba ta wuce ajinsa,amma haka ya karba yace na gode Allah kaimu ranar daura aure,da liman da Idrisa suka yanke Biki nan da sati Uku,
Zance ya watsu a kauye an bada Ramlat Sadaka,Idrisa tuni ya sanar da danginsa,haka Ramlat ma tasha kuka ba kadan ba har ta gaji ta hakura,

Ana haka kwatsam sai ga Hafsatu Umman su Ramlat ta dawo,Murna wajen Ramlat da kannenta da abokan arzuka har ma da Idrisa ba a magana,
Nan tace ai tana can Lokoja neman kudi,kowa sai da yaji haushinta kamar wata mahaukaciya kuma neman Kudi amma babu abinda tazo dashi sai ma kara ramewa da tayi.haka dai suka hakura akaci gaba da Zama,

Biki yana ta matsowa Ramlat ta fita daga hayyacinta ta tabbata Kawu da gaske yakeyi ba wasa,biki har ya rage Saura kwana daya amma ko katifa Idrisa Bai siyawa Ramlat ba,Hafsatu sai dai kallon ikon Allah takeyi,
Ranar asabar itace Ranar da za a daurawa Ramlat Aure da Liman iya Sadaki kawai Liman zai biya amma Sadaka aka bashi Ramlat,

Mutane sun taru an cika makil yan Uwa da abokan arziki domin shaida daurin auren Ramlat da Liman,
Ramlat ce ta fito da wani uban gudu daga cikin gida tana kuka wiwi,faduwa tayi gaban dibban mutane tana gunjin kuka tare da fadin Wallahi saina canja Uba,saina Canja Uba,sai na Canja Uba....Wallahi sai na Canja Uba,
Ko katifa Bai sai min,a haka za a kaini duk uba na gari komai lalacewarsa yanayi wa yarsa kayan daki,wlh bani da Uba,sai na Canja....sai na Canja Uba..kuka take sosai tana birgima tana faduwa tana tashi,Idrisa yace a fara khudubar daurin aure,ai kuwa aka fara.....wata felleliyar motace ta yanko tare da ketowa ta gaban masu daurin aure,tsabar kyau da haduwar motarce ta sa mutane gaba daya aka tsaya da batun wani aure,kowa ya saki baki da hanci yana kallon wannan motar...

Ramlat dai tana sharbar kuka bata fasa ba,
Da kyar Idrisa ya dawo cikin hayyacinsa daga kallon mota yace a ci gaba da daurin aure,Ramlat ihu ta Kurma daidai lokacin da taga wani hadadden saurayi na bugawa a mujalla ya fito daga wannan uwar motar,da gudu Ramlat ta tafi wajensa itama bata San ko waye ba,amma ta rungume kafafunsa ta hanashi tafiya tana ka Cece ni ka taimaka min sai na Canja Uba,zai min auren dole,zai bani tsoho wanda Bana so,kuma....kuma....ko kayan daki bai min ba,ko cokali Bai sai min ba,dan Allah ka Cece ni........





AsmaBaffa
🏀🏀🏀🏀🏀🏀
🏀🏀🏀🏀🏀🏀



DUK INDA TA FADI


26,27,28,29&30




Official




By
AsmaBaffa




Ina matukar Godiya.


Tausayinta ne ya kama wannan matashi,da sauri ya dago kansa abin Mamaki readers Sardauna ne wannan Saurayin,
Da sauri Sardauna ya dakawa masu daurin aure tsawan da tayi matukar tsoratasu a dakata kar a yarda a daura, ina bukatar ganin Baban wannan yarinya,Idrisa yayi matukar girgiza da karfin Hali irin na wannan dan yaro,rai bace Idrisa yace kai Ku kyale dan iska a daura,ana ci gaba da daurin aure Sardauna yace wlh duk wanda ya daura wannan aure sai na kaishi kara kotu,
Ga bada tsofaffin dake wajen suka firgita sunji ance hukuma,kuma sunga wannan matashi da Alama dan gidan wani me kudinne,

Idrisa yace kai yaro uban me kake nufi to kai zaka aure ta ko ubanka?Sardauna ya rasa bakin magana yayi duf,Idrisa yace aci gaba daurin aure yarinya tace bata uban wani ba,aka ci gaba walliyin liman zaiyi magana Ramlat ta kwalla kara tare da fadawa jikin Sardauna tare da cukunkumeshi dan Allah kayi wani abu gaba daya jikinta rawa yake ta gigice,kayi wani abu dan Allah?
Sardauna da sauri yace a tsaya again ni zan aureta a daura Dani,Idrisa yace dan ubanka kai waye dinta?Sardauna yace na taba yi mata ciki a birni na kaita aka zubar,Sardauna kawai fada yayi ko zaiyi dace a fasa auren,Salati wajen ya dauka,liman yace Idrisa dama yarka abinda tayi kenan kazo zaka cuceni ka lika min tsiya?
Dama Idrisa tunda muka ga yarka kullum a yawon gantali gari gari mun San sai tayi aika aika,kuma yarinya bata da laifi laifinka da mahaifiyarta Hafsatu kune masu laifi,kuma ni na dauki kaddara ko dan na rufa mata asiri ni Liman shehu zan aureta haka,

Takaicine ya kara rufe Ramlat da Sardauna,Idrisa yaji kunya ya tozarta a ransa yace da nasan haka wannan rana zata zo min da muni hade da tozarci da ban Tara wannan daurin Aure ba,amma bari a gama komai sai na kusa kashe Ramlat,

Liman yace a daura auren ai kuwa Sardauna ya jawo Ramlat gabansu tsakiyar masu daurin aure kowa na kallonsu ya mika kansa a hankali kamar zaiyi kissing dinta Amma sai ya fasa ya rungumeta tsam wai duk Sabo da su gani Ango yace ya fasa kaji kuruciya,jama'a fa sai sukayi mutuwar Zaune,suna mamakin rashin kunyar wannan yaron.

Sardauna yace a daura Dani, wlh idan baku daura ba sai na kira muku sojoji,Waya ya zaro ya kama wayar karya yace Sir Burutai a kawo min Motar sojoji biyar Jigawa,bari na turo ma Address,ko wanne jikinsa ya dau rawa,wani tsoho yace Idrisa ka rufa mana asiri a daura dashi mun shiga Uku,yaro kayi hakuri.
Nan take Idrisa yace kawo Sadakinka yaro,Sardauna yace Nawa? Idrisa yace zan kure karyar kudi ai Dubu Dari ne sadakin yata,Sardauna yace tayi min araha da yawa,kowa dake wajen mamaki ya kamashi,Idrisa yace Dubu Dari da Hamsin,Sardauna yace wannan kudin Cow ne dan Adam me daraja ne,tunda kun kasa bari na baku kadan dai dai da kwakwalwarku nan ya bude mota tare da dauko kudin da yazo dasu da niyyar taimakon Hafsatu Kanwar babansa ya mika musu Dubu Dari biyar,kunjifa Sardauna wayayyun yan gayu da karya,

Idrisa jiki na Rawa ya kama dariya ba kunya yace Ramlatu kiyi hakuri kinji Allah miki Albarka fita daga cikin maza ki koma gefe, kuma ni na tabbata bakiyi cikin shege ba,ke ba mazinaciya bace,

Yaro da ace tun wuri Sadakin ka miko da tuni an Dade da daurawa liman bismilla a daura da wannan yaron,ba Sardauna ba kowa dake wajen ya girgiza da halin banza irin na Idrisa,tun a nan Sardauna ya tabbata ba mutumin kirki bane,
An fara addua za a daura aure hankalin Sardauna yayi matukar tashi,hankalinsa ya dawo jikinsa yana mamakin kansa me ya kaishi wannan shirme,gumi ne ya fara keto masa ta ko ina,Liman yace Yaro ya sunanka nine walliyinka,Da kyar Sardauna yace Moh.....Mohd....sai da aka kusa daurawa Sardauna yace wait jama'a wait,can kuma ya hango Ramlat a gefe tana share kwalla,yace sorry a ci gaba,kafin yayi wani tunani sai ji yayi ance Aure ya dauru an daura auren Ramlat Idris da Mohd Kabir, nan take bakin ciki ya lullube Sardauna takaici ya kamashi,daga zuwa kauye sai ya auri yar kauye kazama ba yar gayu ba,bata San komai ba sai hawaye sharrrr a idon Ango na takaicin auren mace ba yar wanka ba hhh.

Ramlat ma kuka takeyi bata sanshi ba an bata shi ko halinsa bata sani ba,nan dai ana ta Cece kuce kowa ya watse,Ramlat ma ta shige gida abinta,Sardauna kuma yace da Idrisa dan Allah kaine Idris mijin Hafsat? Idrisa yana yashe baki yace eh dana nine,yace to ni jikan Mami Babar Hafsatu ne nazo gaisheta na iske wannan Matsalar,
Idrisa ya kece da Dariya yace Ashe danmu ne ma ai,gashi Allah yayi ka auri yar Uwarka Alhmdllh hala dan gidan Alh Kabiru Fakas ne? Sardauna yace eh nine,Allah Sarki Shigo shigo,
Sardauna yana takawa dai dai kamar dan sarki ko ina abinsa akeyi da kallo ana ta gulma Idrisa ya aurawa yarsa Bature sabo da kudi,wasu suce ai balarabene,wasu kuwa sukace tab auren Bature ko Balarabe ai kasada ne guduwa zaiyi ya bar Ramlat,
Wasu suce ai ko ya tafi da ita kasarsu to guduwa zaiyi ya barta,wasu kuwa sukace a'a ai dan Sarkine a nan Nigeria yake ta aura,wasu sukace Kwara ne,babu wanda yake cewa Allah sanya alkhairi a kauyen sai fatan masifa da akewa Ramlat da masu hassada.

Sardauna Nabin Idrisa a baya sai yatsina fuska yake yana yarfe hannu har suka shiga gidan,tab Sardauna kamar ya fashe da kuka kyankyami ya kamashi,ga tausayin Hafsat wai Ashe anan take rayuwa daki ko katifa babu,
Ko a kauyen ga gida nan masu kyau ya gani,amma tunda yake Bai San mutane zasu iya rayuwa a irin wannan gidan ba,bai ma taba jin labarin irin wannan gidan ba,da niyyar kwana biyu yazo amma nan take yaji ko yini ba zai iya yi cikin wannan gidan ba sai dai lalura,yace Allah ya taimakeni nazo da safe yanzu zan gudu daga garin nan..
Hafsatu kuwa tana ganinsa ta gane Mohd ne,murna da farin ciki kamar ta goyashi,kuma kana kallon Hafsatu da yaranta sannan ka kalli Sardauna kasan yan Uwa ne domin suna kama,nusamman Hafsatu da Ramlat,
Da gudu Hafsatu ta fito kafa ba takalmi ta aiki yaro ya siyo mata pure water,
Yan Uwa da makwafta yan biki sun yanyame dakin an Taru akan Ango Sardauna ana ta faman kallonsa,yara sai shigowa sukeyi sun cika gidan ana kallon Bature,
Sardauna gaba daya ji yayi mutanen wari suke gashi duk sun masa cirko cirko a kai,ga sun tare kofa ba shan iska domin wasu ta kofa suke lekensa,dakin ya karewa kallo yana mamakin irin lalacewar dakin duk da cewa Hafsatu me matukar tsafta ce ba kazanta sai zallar lalacewa,
Wata yarinya ce ta zuro hannu ta shafa gashin Sardauna me askin yan gayu,a fusace Sardauna ya dago ya kalli yar yarinyar jikinta butu butu ba Wando duk koko a bakinta ya bushe ga cikinta kato kamar zata haihu,bai san sanda ya saki dariya ba,
Sai ya wayance da fine Baby how far? Yarinya tayi wiki wiki bata san me yace ba,Matan dake dakin da Yara sukace ahe wlh Bature ne baya jin Hausa,wasu sun zata bai jin Hausa suka ce Hegen yaro da iyayi kalli yanda yaki zama a dakin yana ta wani kyankyami yana yarfe hannu,Sardauna bai nuna yaji ba,suka ce kalli yanda yayi askin yan iska duk ya kone kansa,kunji ahe wai a wajen daurin aure tanimu yake fada mana wai ya Rungume Ramlat yana ta lahe mata baki kuji yan Iska,a lahewa mutum baki yo idan ba maye ba na taba jin irin wannan ni Hansatu,
Ko a film ban taba gani Adamu Usha ko Ali Nuhu Sunyi ba.
Wasu suka kara rike baki yau mun higa Uku Kun san Ramlat ma fa idonta a bude yake yar iskarce in badan haka ba yauhe zata tsaya,wata tace Kazanta Allah kiyahe mu da wannan kazanta.

Suna ta gulmarsu har Idrisa ya shigo yace ko wacce ta tafi gidan Ubanta ko mijinta an gama biki,wannan shine mijin Ramlat dashi aka daura kuma duk wacce ta kara zaginsa sai na fasa mata kai, dama danginsa da bakin da sukazo suna gidan Abu can suke girkin bikin,yaci gaba kafin na shiga daki na fito ku tabbatar kun bar min gida wayon a cinye min abinci jaraba gayyar tsiya.

Yara da manya da yan mata sun San halin Idrisa ba mutunci yanzu ya wulakanta mutum,kafin kace me gidan ba kowa tsit daga Hafsatu da ta shigo da ledar Pure water guda da lemon Roba guda daya me sanyi Fanta sai yaranta a gidan,Idrisa na can wajen abokai.

Ramlat kuwa tana daya dakin ita ba kuka ba ita ba dariya ba haka take,
Hafsat ta dinga sawa Sardauna albarkar Zumunci,tace Mohd ina Mami Sardauna yace muna Kaduna yanzu ai,zan dawo na daukeki na kaiki gidan ki gani,Mami tayi fushi dake da Dad shi yasa ta canja unguwa amma kar ki damu zan kaiki next time idan na dawo,dama zuwa nayi na ganki mu gaisa,sai na tarar ana daura aure ashe yarki ce ya karasa da shagwaba ni kuma naje nace a daura dani....farin ciki ya lullube Hafsat tace bakayi kankanta ba Mohd da kai aka Daura?kai ya daga yace yes dani aka Daura,yanzu Ramlat matarka ce? yace eh mana kuma Umma kice tayi min biyayya sai abinda nace,dariya Umma Hafsat tayi tace kusan shekarunku Daya da ita fa Mohd,ko shekara baka bata ba,lokacin da ka kai 7 mnths a duniya lokacin na haifi Ramlat.

Karki fada mata Umma kice 5yrs na bata karta rainani ai kuwa Sardauna bai sani ba Ramlat tana jin komai,a ranta tace dama Shine Mohd Sardauna din dan uwanmu,wanda nake ta zuba karya yace yana Sona,tsaki taja ashe ma yaro ne kai....me zanyi dashi auren yaro ko shirme dan dai yana da kyau ne ma.

Sardauna da Hafsatu sai hira sukeyi sosai,sannan ta kira duka yaranta suka gaisheshi tace me bin Ramlat Fahat ya bata har yau ba a ga shi ba,
Sardauna ya tausaya sosai gashi Hafsat ta kwashe irin zaman da suke da Idrisa ta fadawa Sardauna tana kuka,
Sardauna yayi mamaki da Mami ta bar yarta haka alhalin tasan irin halin da take ciki,yace kar ki damu komai ya kusa zuwa karshe za a san yanda zanyi zan kwatar miki yanci,yanzu ki daina tafiye tafiye ki zauna a nan zan dawo ba dadewa ba zaki ga me za ayi,sannan zan kaiki wajen Mami,amma dan Allah ki daina tafiye tafiye haka ki zauna ki rike yaran Nan,gashi dalilin hakan Fahat ya bace,
Nan Sardauna ya dinga Lallaba Mami,sannan yasa aka shigo da kayan abinci da yawan gaske babu abinda babu,da atamfofi Da laces dasu shadda sannan ya bata kudi dubu hamsim yace ki boye kar ki nunawa mijinki zan bashi nasa,

Yaran sauran ya kamo tare da shilla su sama ko wanne ya bashi dubu daya daya sabuwa dal yace kudin break a schl,sai murna sukeyi suna tsalle,Ilham yar yarinya kuwa su chocolate da yawa ya bata ya mike tare da rubutawa Umma Number sa,ko mene ki kirani Umma karki je ko ina,
Tace insha'allah Mohd zanyi abinda kace Amma dai da matarka zaka tafi ko?saboda ya farantawa Umma rai yayi murmushi yace kafata kafarta Umma,

Cike da farin ciki tace to bari ta shirya ku tafi kar dare yayi,Sardauna yace a kano zamu kwana daya sai mu wuce kd ta shirya a nutse.
Hafsat ce ta kwalawa Ramlat kira wacce ta kasa kunne tana ta jin hirarsu da Mohd,
Fitowa tayi tana tafiya Salo Salo jiki ba kwari Ramlat tace gani Umma,kije ki shirya zaku tafi yanzu da dan uwanki,Ramlat me hakuri tace to Umma cike da kunya,Sardauna kuwa ya tafi duniyar tunanin rungumar da yayi ma Ramlat kafin daura aure mafi dadi a wajensa, yasha rungume mata a London amma ta kauye yajita daban, a hankali yace shege Naufal ya min baki gashi ta tabbata.

Ramlat wanka ta shige abinta ta dade sosai sabo da Ramlat bata komai da sauri akwai Nawa,daya dakin ta shiga ta shafa vaseline sannan tasa wata yar mitsitsiyar Bra dai dai da ita fara me kyau Talatu ce ta kawo mata daga birni jiya ana gobe daurin aure harda panties guda hudu da flat shoe baki me dan araha, sannan matar me Damusa ta katsina ta kawo Mata dogayen riguna baka da brown kala biyu da dankwalinsu masu kyau da yar tsada sama sama harda skin tight short guda biyu,
Sallama dangin Idrisa mata sukayi gaba dayansu a gidan,saiga matar me Damusa,da mutanan zangon katab,da sauran baki mata na kusa dana nesa,mazan kuwa wasu suna dakin Idrisa,dama duk fita sukayi suna can gidan Abu suna girkin yan biki ashe Idrisa ma ya kori yan bikin,

Kyaleshi sukayi tare da kiran Ango Sardauna suka sashi a tsakiya,a

Please Login or Register in order to submit comment