Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a zuciyar mace kawai zaki ji sonsa kawai zuruf ya shigeki,ke kanki nasan fada min gaskiya kar kici Amanata nasan kinji son Mohd a ranki,Fadeela ta saki dariya ita da Fa'iza, tace Haba Ramlat da aure na fa zan so wani, nasan a Rina an saci zanin mahaukaciya cewar Ramlat nawa akayi mace da aurenta tana son wani a waje musamman ke da kike yar gayu nan tsab zaki so mijina ai cin Amana ya zauna a kasar nan.

Tun wuri ki fitar dashi a ranki ko ni ba sonsa nakeyi ba da kike gani kawai halinsa ke birgeni amma Sardauna bashi da abin so,
Me zaki ci dashi yaro dashi,Fadeela tace kikace kina sonsa dazu?Ramlat tace wasa nakeyi Sardauna ba wanda za a so bane,nan Ramlat ta fara kushe Sardauna wai dan kar Fadeela taso shi,tafi so taji Fadeela tace bata sonsa sai taji dadi,
Fadeela ta tsokaneta ke Fa'iza ce ta Dade tana sonshi har hanya tace nayi mata yanzu har ta fara gyaran jiki da Shan tsumi zata yiwa Sardauna tanadi sabo da wuri take so ayi bikinsu,




πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€



126-130





ASY TAWA GA NAKI KEMA





Ramlat jikinta yayi Sanyi tace a wai ina zata ganshi ma? me zai yi da ke Fa'iza ki rufawa kanki asiri domin Sardauna maganar farko mari zaki Sha kina da dirty yaushe zaki birgeshi a haka da kunnenki falo falo kamar kalangu.
Yan matan dake wajen suka kyalkyale da dariya sabo da Kunnen Fa'iza da gaske Fala Fala ne,
Fa'iza tace Fadeela kin gani kin jawo ana cimin mutunci ko,

Suna haka sai ga kiran Sardauna ya shigo wayar Ramlat,Da Sauri tace kuyi shuru kuyi shuru me girma me daraja ya kira,Allah sarki yaji a jikinsa ana ta gulmarsa ana zaginsa Allah ya saka maka.

Fadeela tana dariya tace karki daga da wuri ki kyashe murya,Ramlat da masifa tace mijinki ne?dan ki jawo na bata masa ya min kishiya munafimfim,
Su Fa'iza suka kwashe da dariya tace banza baki da wayo ai haka ake waya da Saurayi ko miji,ana yanga da kashe murya,Ramlat tace to kun isa Ku koya min?nima na iya fa ehe,ni da aka haifemu a Abuja muka girma a can,n a zauna cikin Kano,Katsina city,Zangon Katab,nazo ina aure a Kd har wasu yan Zaria zasu nuna min wayewa,banyi niyyar yi bane.

Fadeela tace kiyi hakan Ramlat hanya muke gyara miki wlh,Ramlat tace ai tun farko sai kuyi min bayani ai da tuni a wuce wajen,amma sai Ku tsaya zaku nuna mun kunfi ni Sanin duniya,aure kuke aure nakeyi nima,abinda ake muku ana min wanda yafi naku yara.

Waya dai tuni ta katse har ya kara kira,
Maimakon suga Ramlat tayi abinda suka ce da ita sai suka ga ta kyararrabe ta koma muguwar shagwababbiya irin yan yara na 3yrs ko 2 ma,
a hankali can kasa kasa ta fara bubbuga kafafuwa tana wa Sardauna magana Tare da turo baki morning hw was ur night? Sardauna maganar nan ta Ramlat har jinin jikinsa yaji ta. Uhmmmmm...ni Wahala am so tired of all ths wahala,
hot sun ya isheni pls uhum..uhm..harda Jan kukan karya kamar yar Baby,Maza da suke wajen kusa dasu suna Jin abinda sukeyi suma dariya sukeyi suna Jin Ramlat, Sardauna yana ta aikin lallashi har tsigar jikinsa tashi takeyi yanda Ramlat take abun ba a magana,
Me kakeyi Na Mami? Ina kwance anjima zanje Office naga nawa aka tara,
Allah yasa an samu da yawa muji dadinmu ko?yeah cewar Mohd,
Wacce shiga kikayi? Black and green Atamfa da hijab shoe,bag du green,
Yar gayu inyee kwalliya fa?cikin siririyar murya tace powder lipgloss,uhmmm sweet har naji kamshin ya wani Shaka kamar gaske,
yanzu zamu koma lecture anjima zan kira,Alright bye missed u cewar Sardauna,mee too uhm....ta kare tana ta faman shagwaba,

Fadeela harda tafa mata,Fa'iza tace green snake dama haka kike?shuru shuru dake Ashe shegiyar kanki ce,
Ramlat tayi wani murmushin gadara tare da cewa an fada muku Ku kadai ne kuka San komai,ta kalli Fadeela hajiyata ki koma kiyi course a dinga yiwa dattijo a gida,shagwaba + kallon so hade da zaman daukan photo,kinsan ko Zama zakiyi to irin na daukan photo zakiyi ki gama zuko kyanki a dai daita baki,ido,komai ya Zama cib kamar kina jira a kyasta ki a pic,sannan ki zuke masa jini da kallo ,kafin ya dawo hayyacinsa ki kara bugeshi da shagwabarki kalamai masu sanyi before u knw hmm Ramlat ta dora hannu a zuciyarta wai so ya sakalkaleshi yarinya.
Karyar banza mu za a koyawa duniya ina ne ban zauna ba idan na fara nuna muku true color na baza Ku iya dauka ba.ai ki karanci mijinki me yafi birgeshi,idan wanka ne ki dinga kasancewa kullum kamar zakije party,nafa sani yara yi ne bazan yi ba,yanzun ma nuna muku nayi kusan na sani ehe.

Fa'iza tace iyye malamar love zamuzo a koya mana,Fadeela tace Allah Ramlat shegiya ce ke, ta kirki ma kuwa cewar Ramlat,
Dama duk kin iya wannan?wata Mardiyya ta tambaya.

Mazan da suke sauraronsu sai dariya sukeyi abinda Ramlat yar yarinyar ke yin iya shege ba kunya take sakalo zance,
Sai lokacin Fadeela tace waccen mazan fa mu suke saurara suna dariya,
Ramlat tace ke kika damu dasu da aurenmu ina ruwanmu dasu garori kawai,

Ni ba so nake suga mutuncina ba sabo da nayi aure babu wanda nake bukata ya yabeni ko ya kyasa ni ko na birgeshi bana neman kowa yaga mutuncina sabo da ba aure nake neman yi ba me nake nema a wajensu,akwai me biya min kwandalarsa? Bana so aga mutuncinna Bana kauna ace ina da halin kwarai sabo da na Riga na siyu wajen me martaba me girma Sardauna Mijin Ramlat Jikan Mami.

Fa'iza ta sheke da dariya Allah ya biya ta Sardauna yau da masifa kika fito fa muje class time yayi,suka koma aji abinsu.
Lokaci Naja Rayuwa na tafiya Ramlat kullum tana zuwa schl kuma tanayin karatu amma watarana idan ta gaji ko taji haushi sai tace baza tayi ba ai ba ita tace a kawota schl ba,
Ko test za suyi ko exams haka zatayi karatunta watarana kuma ko Zero zata ci baza tayi ba,amma haka Allah yasa take ta tsallakewa sai aga tafi kusan masu kokarin ma Mark da yawa take ja,
Kuma da an tabo ta zata ce Allah sa ta fadi tana wa kanta mugun fata.

Kuma sai a ga ta cinye,dama haka ikon Allah yake abinda baka damu dashi ba sai yayi ta tafiya normal,idan ka damu dashi a jarabceka ta hanyarsa,
Gashi wanda suka damu da karatun sai korar su akeyi wasu su samu carry over da yawa,amma Ramlat ko duba exam bata zuwa sai dai a dauki pic a tura mata ta turawa Sardauna ya gani,yana ta murna.

Gidan kuwa Prof haka take wahalar Zama dasu har ma ta saba,Fadeela dasu Fa'iza suna kara koya mata wasu abubuwan da bata sani ba na harkar rayuwa da aure,amma Ramlat tace wlh basu Isa ba ta fisu wayewa ita tashin Abuja ce,su kuwa yan Zaria ne har wani city din kirki ne.

Yanzu ko yaushe zaka gansu tare da Fadeela ko Fa'iza,
Har ziyara suna kai mata gidan Prof,itama tana fadawa Sardauna taje gidajensu kuma baya hanata,
Kudi kuwa Sardauna wannan lokacin an samu riba ko yaushe yana turo mata kudi bata da matsala,Kullum kuma suna waya sau Uku sau hudu watarana ma ba adadi suke waya.

Wasa wasa sai gashi Ramlat har suna shirin gama level 1 zasuyi Hutu,kuma har yau Sardauna Bai dawo wajenta ba,
Yafi so ta saba tayi karatu Bai son ta kashe zuciyarta shi yasa yana so yazo ya ganta amma ya hakura sabo da tafi dagewa tayi Karatu.kuma yana so yayi sauri ya girma ya kara shekaru,idan yana tare da Ramlat sai yaga shekarun basa tafiya.

Ramlat kuwa ta kara wayo ba laifi duk da cewa har yau akwai Saura wani salo ta fito dashi yanzu kuma ganin tana da aure ta kara tsayi da kyau sosai komai ya bayyana sai girman kai takeyi,ko waye Bai isa ba itama yanzu gadara da Mulki take tashen yi gani takeyi babu kamarta tafi uban kowa sabo da tana University degree takeyi,
Komai sai tace degree da anyi magana zata ce ai karatu in ba degree ba kai aikin banza ne,yanzu ta gama Raina Prof har tsayawa takeyi suyi fito na fito ta fada ya fada akan boko,Prof yanzu duk yafi son Ramlat sabo da yaga alama tana bin tsarin doka.

Sardauna ma ya gane matakin da Ramlat take kai yanzu ita wai yar University domin Har Sardauna yi masa takeyi dan dai shi ya take ta a nasa iyayin dole take taka birki,Sardauna karshe ne nasa gayun da iyayin ba fake bane ba kakalowa yayi ba haka yake nature dinsa ne.

Ramlat kuma ta kara fetsewa tare da fitsare kafar ta, ga iya tsari yanzun nan sai ta tsaraka tas
Haka ma tana kiran yan Uwanta da iyayenta tare da abokan arziki suyi zumunci,tana so taje taga Mami da yan Uwanta da iyayenta,Sardauna yace baza taje wajen Mami ba,zai zo ya kaita kauye da sauran wurare su zaga dangin idan sunyi hutu, Idan yaga dama zai kaita wajen Mami,sai murna takeyi.

Sun gama Exams Sardauna next wk zaizo wajenta,tana palo taji Juicy na waya a hada mata maganin mata zata zo ta karba next wk,Ramlat tace af budurwa da maganin mata ai dole kasar nan baza a zauna lfy ba,J Juicy tace zanci uwarki wlh
Budurwa ma tayi bare ni me aure,
Juicy wayar ta bari a saman Sofa ta shiga kitchen tana tsaki.

Lallabawa Ramlat tayi tare da daukan wayar ta duba last call ta saci Number ta ajiye mata wayar ta shige daki abinta tare da kiran me maganin mata a waya,suka gaisa tace nice wacce mukayi waya yanzu Juicy fa, nace next wk zan karba na fasa gobe zanzo na karba idan akwai,
Matar tayi dariya tace Hajiya da alama me gidan zai dawo da wuri?eh yanzu ya fada min bani address kawai zanzo na karba,
Dama Ramlat taji cewar Juicy ta tura kudin ta accnt din matar ta biya komai,Ramlat takanas tayi shiri taje har gidan matar ta karbo kaya Viva Leda guda,sannan ta kara komawa wajen Fadeela tace ta Rakata gidan da ake gyaran Amarya,

Sardauna tasa ya turo mata kudi wai zata yi wani abu ba tare da ya tambaya ba ya tura mata taje suka biya aka fara mirje mata fata ga tsuminta da tayiwa Juicy fashinsa tana ta sha yanda malamar ta karanta mata,amma bata Shan na matsi da na sha'awa,duk me Zafi bata Sha,

Juicy kuwa ta shirya tsab bayan kwana Hudu taje karbar kaya,sai matar tace ai ta karba,watace tazo ta karba me kala kaza fara me tsayi wata kyakyawa nan,nan dai matar ta gama fadar kalar Ramlat,Sai lokacin Juicy ta tuna tabbas Ramlat ce domin tana wajen tayi waya zata zo ta karba kuma har magana ta fada mata Budurwa ma tayi bare matar aure.

Da Bala'i ta dawo gidan tana kwalawa Ramlat kira,Ramlat dawowarta kenan daga wajen gyaran jiki, Ramlat ta fito Simi Simi tace Anty Juicy lfy? Ubanwa ya baki damar zuwa ki karbi magungunan matan dana ce a hada min?Ramlat tayi mukus da kyar tace gani nayi...uhm....ehm...ke budurwa ce zaki hassada alfasha a doron kasa,baki da aure,taya zaki sha irin wannan tsumi ki zauna lfy?dole ki bi mazan wasu,shi yasa naga Bai dace ba na taimakeki naje nayi Sadaka dasu wa matar aure wacce idan ta sha mijinta zai kawo agaji a samu Lada,

Juicy tace uhm lallai to uban wa kika bawa Sadakarsa? Kaina nayiwa Sadaka gida bata koshi ba ai bazan kaiwa dawa ba,ni kinga Mijina zaizo ths wk zaki samu Lada ko?

Juicy bata San Sanda ta shake Ramlat ba ta fara dukanta sosai tana danna mata zagi,Ramlat anji wahala sai hakuri take bata،su Chuchu ma suka taho zasu Hadar mata sai ga Prof ya shigo,

Yana zuwa ya wanke Juicy da Mari tare da daka mata tsawa u are very stupid,wannan wanne stupidity ne haka,whats wrong with u,Juicy tace Papa kasan abinda tamin wlh sai na kasheta,U are very stupid foolish girl,how....how...dear u zaki mareta haka?da duka haka,baki San duka a fuska ba matsala ne,tana da yanci,
Tsarin kasa ya bata dama,human right ya bawa kowa dama tayi abinda yake so sannan ke kizo ki kawo naki tsarin?
According to laws
George dikks and Albert Cinies Williams duk laws dinsu ya tabbatar da wannan ba dai dai bane,jahilan banza illiterate kuje kuyi research Ku karanta kuji me suka ce,kunzo baku San komai ba bakwa karatu zaku shigo da shirme gidana da ilmin naku cikin cokali just common Degree and Masters kuje kuyi kokari Ku Zama Profs,

Ku tsaya kuyi karatu shine gadonku wlh wlh bazan bar muku ko 1 Naira ba a gado karatunku shine gadonku,shine Inheritance dinku,Chuchu ta kalleshi, Papa ma yayi mata kuriii da Ido ta cikin glass yace yes kalleni da kyau I mean it.
Ammi tace Yanzu akanta ka mari yaranka?wlh sai ta gane kurenta zaka fita ne ai,
Ramlat ta kalli Papa tare da cewa Prof Albert chinie Williams laws dama ban ganeshi ba ina ta faman Research dan Allah anjima zaka koya min,Prof ya kyakyace da dariya tare da cewa shi yasa kike birgeni kullum a research kike thts really good,great and Good Idea,
Bari na nutsu nazo kiji sauran Laws sabo da naga kina ganewa ba irin wannan banzan yaran ba,ina ma ke yata ce ni na haifeki ai da kinyi gado na.
Ramlat ta kyalkyale da dariyar haukar Prof tace ai Papa yanzu ma sai na Zama prof nima,Papa yace very good hehehehe Allah nuna min ranar.

Ammi kuwa sun gama shiri tsab na kulunboto ana jiran isowar Sardauna.






AsmaBaffa


Loves u all masu sharhi
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€



DUK INDA TA FADI




131-135




Official





By
AsmaBaffa





Page dinku
AUTA
SAMEERA GAYA
AYEESHA(MUMMYS FRIEND)
FA'IZA M ALMODA
ZAINAB ATIKU SALLAMA.wannan page nakune Ku kadai.


AUTA ina mika godiya ta musamman gareki.




Sati daya Ramlat tayi mugun kyau na fitar hankali ko Sardauna yace suyi video call sai taki yarda dan kar ya gani wai tayi kyau surprise zata masa,sai faman shirye shirye takeyi,
Tana so ma ta shiryawa Sardauna harkar girma takanas taje shopping ita da Fa'iza za ayi harkar manyan yara,
Sardauna dai tuni an shiga 22 yrs yanzu yayi wani mugun girma da kyau na mamaki,
Ya canja wani kalar style again na gyaran gashi wani iri ake mata daga gefe an tsagata iya tsagar an kona wajen yellow line ya fita sosai,an dan rage yawan Sumar kadan,
Nan ma babu wanda zai gani Baice Sardauna Bature bane,sai a dauka Balaraben bature ne,
Yanzu dai sosai yake sa manyan kaya sabo da afi ganin girmansa.

Ramlat fa yau tana can ana ta girke girke a gidan su Fa'iza gidan masu kudi yan gayu,
Sosai aka shirya harkar girma a motar Fa'iza suka kai kayan a manyan food flasks da abubuwa na yan gayu,Sardauna yana hanya yana ta sharara uban gudu a titi cike da nishadi ya kusa karasowa,Ramlat ta rude sosai kar yazo bata je gidan kwalliya ba,Wanka tayi tare da shafa cream dinta me kamshi tasa sabon wata readymade fitted Gown black tasha kwalliya da peach color botin ta baya tayi matukar kyau kamar a saceta,komai cif ita abin birgewa ta cika dam tayi haske tana sheki sumul sumul da ita kalar Hutu,yar Madara.

Da sauri ta fito da cokalelen takalminta peach color da mayafin rolling shima peach harda Pose black,
a Palo Fa'iza na Zaune tare da Prof yana ta karanta mata tsarin harkar boko tare da turanceta,su Merry suna can suma ana shirya last born dinsu Ichichy sabo da tayi kyau Sardauna zai so ta itace yarinya.
Ramlat tace let's go Fa'iza mana kin zauna suka yiwa Prof Sallama suka tafi,

Ramlat ta zauna aka tsantsara mata kwalliya amma tace bata son foundation kwalli za a sa mata da eyeliner a saman Ido sai jambaki maroon,sai kuma a gyara mata gira itama kadan kawai za a tajeta bata son a kara mata komai akan gira,ai kuwa yanda tace haka suka mata tayi mugun kyau babu wani zafafa kwalliya anfi kyau,

Fa'iza tana waje ita da Farooq dinta suna soyewa yazo wajenta,
Ramlat ta gama ta fitowa tare da cewa muje bayan sun gaisa da Farooq,anyi mata Rolling da dan mayafin tayi matukar haduwa,
Fa'iza muje mana kinga kiransa fa maybe ma ya shigo gari, Farooq yace gaskiya ki koyi yanda kawarki takeyi nima na huta idan munyi aure,
Ramlat tace karka damu tunda tana tare da me girma ni an gama,

dariya sukayi gaba daya sannan Fa'iza ta jasu suka tafi Farooq ma ya ja tasa motar suka bar wajen,
Kafin su karasa Sardauna yaje gidan dasu Ichichy yayi arba duk sun ci uwar kwalliya,karku ga Sardauna yanda ya hada saje da gemu yayi shegen kyau cikin Shadda peach color ta alfarma sai kamshi yake zubawa,wani shegen Zama da yayi a kujera kamar wani Gomna kafa daya kan daya yana karkadata,
Harda chewgum a bakinsa baya taunawa kawai tsotsa yakeyi,
Sumar ce abin kallo ma,kayan dinkin ba a magana kamar Wani Boss sabo da rigar kamar babbar riga kuma ba babbar riga ba,kuma tsayinta iya farkon cinyarsa,Hannunta dai irin kamar na babbar riga amma Sam ba babbar riga bace,babu wanda zaice ya taba ganin kalar dinkin mazan nan sai a jikin Sardaunan gayu,

Cikin can kasa da murya ya tambaya ina Ramlat,Ichichy tace ta tafi gantalinta ai bata Zama kullum a yawo take a gidan nan,Sardauna yace muna waya ai na San da fitar.
Ammi ta tabe baki tare da cewa kurici dangin hauka in ba yaro ba wa zai bar matarsa na garari a titi,shi yasa ba a so irinku suyi aure sabo da shirme kukeyi.

Magazine ya dauko yana dubawa ba tare da yace musu komai ba,abinci kam gashi nan a gabansa Ammi tasa Ichichy ta jera masa,
Kallon abinci yayi tare da ci gaba da karanta jaridarsa,
Fa'iza tana ajiye Ramlat a kofar gidan ta juya ta wuce gida itama ganin yamma lis tayi,
Ramlat tana shigowa gate taga wata tsaleliyar farar mota yar gaske ta nunawa a gari,kowa ya kalli motar sai ya kara,duk motocin su Ammi sai suka koma akwariki dasu,
Bata taba ganin irinta ba marcedes Benz ta hadu gaskiya.

Palon ta shigo kwas kwas cikin takunta me kayatarwa dauke da Sallama,wani kamshine ya bugi hancinta wanda bata taba Jin irinsa ba,
Palon ta karewa kallo iyalan Ammi na ta zuba hirarsu,Wani rantsatsen Saurayi ta hango zaune yana duba magazine hannunsa daure da wani shegen Agogo,a ranta tace wow kamar Sardauna kamar ba shi ba,ko dai shine?kai wannan yayi girma da yawa,kafafunsa ta kalla nan ta tabbatar Sardauna ne sabo da yatsunsa masu kyau da ta gane,
Jin anyi Sallama ba a shigo ba yasa Sardauna dagowa Ido biyu sukayi da Ramlat,
Nan take ya sakar mata murmushin da ke susuta mata tare da kureta da kallo yanda gaba daya ta canja ta girma ta kara kyau Sosai,uwa uba ta koma yar gayu,
Muryarta ba irin wacce ya sani bace da,domin wannan ba alamar tsoro ko kunya da Confidence yaji ta duk da cewa siririya ce dama muryarta amma yanzu ta kara zaki da dandanon Saurare,

Murmushi ya kara mata har dimple dinsa ya lotsa abin gwanin sha'awa,itama murmushi tayi yayinda wushiryarta siririya ta bayyana,
A hankali ta karasa wajensa tare da Zama kusa dashi cike da nutsuwa tace sannu da zuwa,hannunta ya rike gam gam yana murzawa ba tare da yace komai ba ya mikar da ita tsaye tare da janta Bed room dinta har ciki suka shige kafin tayi magana ko wani motsi ya rungumeta sosai a jikinsa suna shakar kamshin juna

Dagowa yayi tare da zuba mata idanu yana shafa fuskarta da hannu daya dayan ya rungumeta,idonta ta wani lumshesu, bakinsa ya kai kan nata da niyyar kissing dinta ya tuna sai nan da 4-5yrs fa Kun San an kara cire daya coz da yace 5-6 yanzu 4-5 ne ya kara shekara guda girma yana ta zuwa.

A hankali yace u look so beautiful,Ramlat kunya ta kamata da kyar tace tnx tayi shuru kamar ba ita ba,
Mene kikayi wani shuru?kiyi ma magana yarinya,Ramlat tace nice yarinyar? Yeah da mece?da nawa ka fini ina katotuwa haka dan ka fini tsayi,
Kafeta da Ido yayi yanda take magana a nutse tare da isa tana iyayi magana a hankali ga shagwaba,Sardauna dadi ya gama kasheshi wai yaro dashi ake wa wannan abu haka dan ya kyasa a birgeshi Allah me iko namiji da baiwa yake,gashi su Lilla ma duk girmansu wani cusa Kansu sukeyi wajensa.

Sardauna a ransa yace Allah na godema ma,wai ka bada kudi mutane su taru ayi yan maganganu da addua ace an daura aure kuma a baka mutum me daraja guda sai yanda kaga dama,gashi dai an bani wannan guda ni kadai sai abinda nayi Allah me iko.
Ramlat yaji tace ga abinci ko wanka zaka fara yi?
Kallonta yakeyi shifa mamaki yakeyi wai wannan tasa ce guda gashi har cewa akeyi ga abinci ko wanka zaiyi hmm.
Ramlat ta kara magana lfy wai? Lfy kawai yace mata tare da kashe mata Ido daya,
Yanga da girman kai suka kara baibaye Sardauna yace bani abincin na fara ci naji kin iya ke kikayi?
Kai kawai ta daga masa alamar eh,
Sardauna yace ga kuma kunya wai duk ni ake jiwa uhmmmmm...a ransa ya furta.

Kayan ta dinga jera masa sai da ta cika masa gabansa gaba daya,


Please Login or Register in order to submit comment