Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwanta kafin nurses suzo,banza ta masa ta wuce ta zauna zumbur minti daya kacal ta kara mikewa tana rike mara,yunkurin Amai ta fara sai kwaaaaa ta dinga Amai kamar zata yo waje da hanjin cikinta,lokacin Nurses suka shugo tana jikin Sardauna,masu gyara wajen suna tayi,

Sardauna suka ce ya fita zasuyi aiki,
Fitar Mohd da 1hr Ramlat ta haifi yarta mace zukekiya me kama da ita,tasha wahala sosai,Mami da Bilkisu Mum suna wajenta sai da suka gyara Ramlat fes da Jaririya taci abinci sannan tasha Allurai sai bacci,Sardauna Mami ta kira tare da mika masa jaririya murna kamar me wajen Mohd sai kallon Baby girl dinsa yake yana mamaki wai shine da ya guda,yanzu yana da yarsa,
Mami ya kalla tare da washe hakora yace Mami wannan tawace ko,dakuwa Mami ta masa uwaka Sardauna marar kunya, Ramlat ya duba tana ta baccinta cikin nutsuwa,Addua ya dinga zubawa Jaririya a kunne har sai Bilkisu ta kwaceta tare da kwantar da ita,
Dawowa jikin Bed yayi tare da makalewa kusa da Ramlat da yar Jaririyarsa.

Hafsatu dai ana zaune ita da Idrisa abinsu lfy basa fada sai watarana ana dan tabawa dama zaman tare dole a samu hakan,amma sabo da masifaffe ne Idrisa duk ranar da suke Fada to fa ba mutunci dama tun asali yana da zafin Zuciya. Hafsatu dama itama ba baya bace wajen iya fada idan an bata mata,kamar kullum yau Idrisa da fushi ya tashi yana ta faman cin magani,Hafsatu ko magana ta masa sai ya hayayyako da masifa,Hafsatu tace bamu da shinkafar tuwo ta kare a siyo wata,Da masifa yace ke dai kawai kice Almubazzaranci kike min da abinci,Hafsatu ma zuciyarta ta baci tace ae ai gadon gidanmu ne,kar dai ki zageni cewar Idrisa wlh domin kin San halina,Hafsatu tayi tsalle ta dire harda rike kugu me jiya tayi bare yau? bazan taba zaginka ba amma in dai ka zageni to kasan dole na rama iyaye basu fi iyaye ba ehe,
Idrisa yace ban san ma ya akayi na auroki ba,ni ya dace na fadi haka tunda kaf dangina sai da suka hana na aureka nice nace naji na gani,ba dole ki like min ba kaf samarinki kina da kamata a lokacin?,ni na rufa miki asiri zakiyi min iyayi,
Hafsatu tace kut kaine dai manniru kaska dubeka fa Ido kamar na Kururu,kunne Fala Fala kamar ganyen tumfafiya,murmushi Idrisa ya saki tare da cewa a cikin Farillai da shika shikan kyau kin taba ji ance wane yana da kyau me idanu kanana?ai sai dai ace me Ido Dara Dara,kefa da Ido kamar na Kuma kamar da Reza aka dan tsaga,kuma kin San in banda ta duniya ai wlh ni fari ne kar, ni kuma sai akace ma baka ce kalleni ka dubeka me idon Kwadi wa ya sani ma ko Aljanine dan ruwa,Hafsatu ki kiyayeni na fada miki zanyi kasa kasa dake a gidan nan.
Hafsatu tayi shuru cike da tsoro tasan Idrisa ba mutunci da Imani gareshi ba.Shaheed wanda dawowarsa kenan daga schl Daddy ma yazo Hutu gida daga gidan su Naufal suna Jin fadan Iyayensu su dariya ma abin ya basu kamar fadan yara sai gori sukewa juna.

Sa'adat Tayi shirin makaranta da sassafe gidan su Saddiq ta nufa sabo da yanzu tayi mugun sabawa da Umman Saddiq ba inda bata shiga a gidan,
Da gudu gudu ta karasa sai Haki takeyi yau Umman Saddiq zata koma Kano tana so suyi Sallama,door bell ta danna bugu biyu Saddiq ya bayyana daga shi sai dogon wandon sojoji a jikinsa,Lantan tayi sauri ta rufe ido sannan tace ina kwana? Allah yasa dai Umma bata tafi ba,kallonta Saddiq yakeyi ba kifta Ido yana jiyo kamshinta cikin Uniform,kafafunta masu kyau yake ta faman kallo sai da ta gaji ta bude idonta da sauri ya dauke kai tare da cewa ta tafi tun dazu kin makara shigo ki karbi sako tace a baki,
Binsa tayi har Palo ta zauna, muryarsa taji me dadi yace Hada min tea ina zuwa,kitchen ta shiga,shi kuma ya shiga bedroom zuciyarsa na bugawa,duk sanda yayi tozali da Lantan sai gabansa ya fadi,
Kafin ya fito ta hada masa komai,iyayin Lantan itama saida ta hadawa kanta tare da soya kwai kamar gidanta,sai ganinta yayi tana ta faman cin kwai da Bread ga tea me kauri a gefe,

Birgeshi tayi sai kallonta yake yi tana ta cin abinta hankalinta kwance ba wani tsoro,zama yayi shima ta tura masa kwan gabansa yasha yaci komai sannan yace muje nayi dropping naki a schl,idan kin dawo daga schl sai na baki abinda Umma tace a baki.
Ni dai da ka bani yanzu nasan ma kayan dadi ne sai naci a schl,murmushi yayi tare da cewa kwadayayya kawai let's go, dama ya rage tea dan kadan a cup nasa Bai gama shanyewa ba Lantan ta Mike tsaye tare da kara dauke cup din ta kafa kai ta zuke ragowar tea din nasa tace uhmm naka yafi dadi ta lashe lips bari a wanke cups ko nayi late sai ka musu magana kar a zaneni ko? kusa da ita ya matsa sosai tana Jin kamshinsa jikinta ya mutu murus bangaren Saddiq ma haka tissue ya dauka tare da goge mata lips da ta shafa masa madara yana kare masa kallo ji yake kamar ya tsotsi lips din amma ba dama,ita kuwa Sa'adat ta wani lumshe Ido tare da langabe kai.

Kanta ya buga da hannunsa tare da cewa muje idan mun dawo zan wanke komai,zumbur ta bude Ido tare da Dafe kanta tana kallon Saddiq a hankali ta turo dan bakinta tace da Zafi fa,tsigar jikinsa ta tashi yarrrrrr sakamakon shagwabar da Sa'adat Tayi masa ji yake kamar ya rungumeta ya huta,da sauri yayi waje tare da daure fuska yace zo muje mana u r waisting my time,
Tasan masifar sa da Sauri ta shiga gaban wata Hadaddiyar motarsa wacce bata San yana da ita ba sai yau.
Tunda suka fara tafiya ta cika motar da wake waken schl dinsu na turanci iri iri,ta koma national anthem taken Nigeria,harda nannada takarda ta mayar da ita kamar speaker wai ta rike,
Saddiq ta cunawa a baki wai yar jarida ce ita zata masa tambayoyi.

Assalamu'alaikum masu kallonmu yau muna tare da babban bakon mu shahararren Sojan nan da kuke ta Jin labarin jarumtarsa da taimakon talakawa wato Captain Saddiq Umma Hashim, abin nata dariya ya bawa Saddiq Amma ya daure,tace masu kallonmu nasan zaku so jin takaitaccen tarihin wannan Irganman soja naku,Captain Saddiq bismillah,kamar bazaiyi magana ba yana driving ya fara magana jikin speaker ta paper nata,kamar yanda kuka sani Saddiq Umma Hashim nake by name,34yrs nake an haifeni a Maiduguri muka dawo kano nan iyayena suke zama,ina da kanne Uku Hussain,Hassan da Rayyan,Sa'adat ta cika da mamakinsa ashe dai shi gaske yake biye mata yakeyi,
Tace to Alhmdllh masu Kallo kunji,bari mu fara daga wayoyin Jama'a masu Kallo,hello....hello....nice Auta daga Niger muna Yiwa Babban bako barka da zuwa,sannan dan Allah ko Saddiq yana da aure? Lantan dai ita kadai take kidanta tayi rawarta,
Ta kara sawa Saddiq speaker,ya fara magana yana dariya yace to a gaskiya bani da aure ban taba aure ba amma Insha'allah kwanan nan zanyi,To Auta kinji abinda Sojan namu yace,bari mu karanta masu turo mana sakonni,Assalam wace budurwar Saddiq muna so mu san sunanta Sako daga Flower,Asycool,Zainab atiku Salama,Diyar Katibi,Sameera Gaya da kuma Maman waleeda.

Saddiq yace sai nan gaba zaku san ko wace Insha'allah,Dariya Sa'adat tayi,ta kara cewa hello waye akan layi?Queenmermu ce ina Yiwa Babban bako fatan Alkhairi.
Dariya Saddiq da Lantan sukeyi sosai kamar gaske,hannu ya mika mata suka tafa,dai dai lokacin da ya kawota schl,
Har kudin break ya kara mata ya wuce yana ta murmushi tare da tunanin halayen Sa'adat.

Dafta ansa bikinsa da Hajara Saura 4mnths lokacin kuma ya gama schl dinsa,sosai yake sake Gina sabon gidansa me kyau cikin garin Zaria,soyayya kuwa suna zuba ta shi da sahibarsa sai abinda tace,
Yauma yana wajenta suna soyewa,wani kallo Dafta ya watsawa Hajara har wani zaiba zaiba da kibiyoyi take hangowa cikin idon Dafta,bata taba ganin ana murmushi da ido ba sai a kan Daftan ta,domin Dafta ya kware wajen sarrafa idanuwansa wajen kallon so,
Dafta searching yanda ake love na yan zamani yakeyi ko da yaushe kuma ya aikata kan Hajara,kafin kace me Dafta ya kara Tafiya da Imanin Hajaransa,
Ga wanka da yakeyi yanzu na samarin zamani,har tuno wankan Sardauna yakeyi ranar da ya taba ganinsa ina ma zai kara ganinsa da ya kara daukan darasi ko dan ya nemi suna wajen Hajara ya kara birgeta.

Su Juicy kuwa tunaninsu auren manyan mutane shine dai dai Sabo da ana cewa manya sunfi sanin darajar aure duk abinda kayi basa magana kayi abinda kaga dama basa damuwa neman kudi kadai ma ya ishesu busy basu da time,shi yasa ko da akayi musu auren dole da manyan mazaje basu damu ba,amma yanzu abin ya damesu sosai ganin duk Mazajen nasu kullum cikin busy suke na aiki basa dawowa gida da wuri sai can dare,daren ma kuma sai su zauna gaban computer ko su ebo takardu suci gaba da aiki,koma me zakiyi kiyi basu da time,Juicy uwar sha'awa mijinta sai Sha daya na dare yake dawowa kuma ko abincin gidansa baya ci yana dawowa zaice cikinsa bashi da lfy,Computer zai bude tare da kirawo manyan yaransa mata guda Uku su zauna gefensa suna tayashi aikin ita kuma wacce yake dakinta tana kwance saman bed,Juicy tayi fadan tayi nasiha har ta gaji,iya hakuri tanayi abinda yake bata mamaki yaro kamar Sardauna jibi yanda yakewa Ramlat,shi bashi da kudin ma da aikin da zai hanashi sakewa,yara matasa idan kayi dace sune masu time,sabo da koma yayane sai ya bawa matarsa lokaci musamman ace yana sonta komai aiki sai ya bata time,duk da cewa su ma manyan akwai masu kamantawa,yaro kafin ace yayi kudin da zai zama busy bashi da time lokacin kunci duniyarku da tsinke,

Ichichy kuwa nata dattijon yana kamantawa ba laifi komai aiki yana basu hakkinsu ko yayane,Lilla kuwa tsohon nata bai damu ba ko ina zataje ma tayi ta gantalinta ba Sa ido bare kula da matansa,ko me zakiyi bazai magana ba amma zai dan kamanta baki hakkinki,ko abu Lilla tayi masa sai daí yayi dariya yace kuruciyace kamar yar cikinsa yake ganinta,ko fada zai mata irin yanda zaiwa yarsa yake mata, Merry kuwa tana bata masa zai kwadeta da Mari bai ma cika zama a kasar ba yau Dubai gobe China,Chuchu yana da mata har hudu Amma yana bin wasu a waje tsofai tsofai dashi,kuma ko da waye zaki iya kebewa bai damu ba,kuma ki zagi ubansa ma ko sauraronki bazaiyi ba bare ya dau mataki sai abinda kika ga dama,sannan yafi son uwar gidansa sai abinda tace,sauran kuwa basu Isa ba.Ichichy ce kadai tayi dacen dattijo na kirki.
Dama haka yawancin manya suke basu da lokacinki bare har kuyi fada ko wani abu,suna da hakuri akan halin mata Sabo da sun saba,matasa kuwa in dai caring ne ba kamarsu indai kinyi dacen na gari yana sonki,haka manyan ma akwai na gari ciki,kayi da kyau kaga da kyau sai daí ko jarabta ta Allah,a daina saurin yanke hukunci cewar Yara basa rike aure,ko manya Kaza Kaza kowa akwai amfaninsa da rashinsa Allah Sa mu dace Ameen.

Ramlat sai da suka kwana a asibiti sannan aka sallamesu,Bilkisu tace a kai Ramlat gidansu tayi jego a can , Sardauna yace munki wayon,Mami wayo zasuyi mana mu zauna a gidansu,hakane Muhammadu gidan mu zamu tafi ku kudinga zuwa kuna dubamu,
Dad Kabiru yace ba matsala zamu dinga zuwa,Sardauna ya dauke Jaririyarsa yana jijjigata,Ramlat kunya takeji sai a sace take kallonta,da taga ba kowa a wajen sai ta kalla tana washe baki,da taji motsi sai ta dauke kai tayi gefe dashi wai irin bata damu ba.

Dad ma ya samu sauki harda shi aka bawa sallama,direct katafaran gidan da Sardauna ya Gina suka nufa dake Asokoro Abuja.
Zo kuga gidan Sardauna na mamaki wanda Banga irinsa ba ko a Abuja.wani labarin gidan sai a next page.










AsmaBaffa.
🏀🏀🏀🏀🏀🏀
🏀🏀🏀🏀🏀🏀


DUK INDA TA FADI





251-255






Official















By
AsmaBaffa







Gidaje suke ta wuce masu kyau duk tunanin Mami a cikinsu za a shiga daya daga ciki,Su dai kallon ikon Allah sukeyi har motar ta tsaya dai dai wani katafaren gida na Alfarma,gidane na gasken gaske wanda ya wuce tunanin me tunani,Mami ta firgita tare da cewa amma ba nan bane gidan Muhammadu ko? Sardauna dake gaban mota dauke da Jaririya a hannunsa ya wani basar irin za a Sha mamaki ba a ga komai ba ma.
Ramlat da su Bilkisu sai Zare Ido sukeyi suna Shan kallo,
Tun daga gate suka ga yana jin hucin mota ya wangale kansa sun kutsa ciki a nan kallon yake katon gida na gaske gate Uku ne a cikin gidan yasha Flowers,garden ma daban harda wajen tsuntsaye,swimming pool na gaske,can gefe motocine lafiyayyu masu tsada guda Hudu na Alfarma,ga part dinsu masu aiki a gefe Amma ba kowa ciki.

Cikin palon suka shiga a nan kallon yake ashe,bene hawa Uku ne part din farko na Sardauna,na tsakiya na Ramlat gaba dayansa duk Bedrooms din da komai,hawa na karshe shima na yaran da zasu haifa ne,nufin Sardauna duk abinda ma zai faru ya fara samunsa kafin matarsa da yaran sa shine dai na farko,harda lifter kamar a turai.
Furniture da suke gidan kuwa kamar a gidan Larabawa masu kudin gaske,komai na alfarma kana ganin gidan zaka San an kashe kudi gida gidan yan gayu komai na yan gayu ba karya,Sardauna akwai karfin Hali,dama burinsa ya mallaki gida na gaske da motoci ga matarsa da yaransa sannan yana Business din sa kuma Allah ya cika masa burinsa.

Su Ramlat daula ta samu bata San Sanda ta rungume Sardauna ba,Mami tace dan nan kaine kayi wannan gida ina ka samu kudin,nan Sardauna ya zauna ya Fayyace musu irin ribar da yake samu da kadarorinsa sai kuma wasu abubuwa da ya bude a kusan ko wacce state ta Nigeria,
Sunsha Mamaki gaba daya har su Dad da Momy tare da kannen Sardauna sai Santin gidan sukeyi,Nabeela ta fara daukan Selfie tana cewa nan zan dawo da Zama ya Sardauna,da Sauri Sardauna yace baki isa ba yarinya baza ki zo ki sa mana Ido ba..Mami tace a'a mene idan tazo nan din? kafada ya make kamar dan yaro shi Bai yarda ba,Momy dariya takeyi duk da yanda gidan yake a goge komai yana kyalli da kamshi amma Momy tace Sam masu Mopping basu iya ba,da kanta ta fara sake sabon Mopping kamar me Aljanun Tsabta,

Sardauna ya hade rai shi fa abinda Bai so kenan ana shigar musu rayuwa,in hakane ma ai yafi Momy tsafta zata na raina musu hankali,don wannan raini ne idan wasu ne ya tabbata baza tayi musu haka ba,mutum da gidansa sanda ya Gina sun sani ne sai wani Mopping..shi fa baza su shirya da Momy ba in dai zata dinga zuwa tana nuna musu basu San me sukeyi ba musamman kar tazo ta dinga damun Ramlat da yar Jaririyarsa.

Mami ce ta dakatar da Momy domin ta fuskanci Sardauna ransa ya baci,tace sau nawa zan fada miki Bilkisu ki dinga iko a gidanki,ki daina shiga abinda ba ruwanki,har yaushe muka yafe muku zaki zo ki kara bata lamari,akan wannan wlh baza mu shirya ba kije gidanku kiyi haukar tsabtarki uwar iyayi,

Dad yayi dariya tare da cewa ai ni kaina Mami ina Jin Aljanar Tsabtace a jikin Bilkisu,abin nata ya wuce Sanin mutum.
Dariya su Nabeela sukayi tare da cewa wlh kuwa.ita kuwa Ramlat sun Kebe da Fahat dinsu suna ta zuba hirar yaushe rabo,cikin nishadi har Momy bata hakura ba tace ke taso kije ayi miki wankan jego,wannan Asibiti da muka zauna ai kayan jikinmu ma sai dai mu zubar dasu a shara.

Sardauna dai Bai ce komai ba,Mami tana ta masa signa yayi shuru,Muje nayi miki Momy ta kara fada karo na biyu,Sardauna yace ni dai baza ki taba min mata ba sai dai Mami tayi mata,kina Surakarta ya dace ki kalle ta?Mami tace bazan ma bari ba Dan nan kwantar da hankalinka,Nabeel,Nabeela da Ammar haushin Sardauna ya kamasu kamar ba uwarsa ta jini ba sai wani disgata yakeyi idan Bai San darajarta ba ai su sun sani,tsaki suka ja tare da ficewa abinsu daga gidan,Dad yana kallonsu yasan Bilkisu ce bata da gaskiya kuma Sardauna Bai mata komai ba,gaskiya ce ya fada,
Momy ma bata ji haushi ba sabo da ita indai akan tsabta ne to ko zaginta kayi baza ta damu ba,sai ta kalleka a kazanta ce tayi ma yawa shi yasa.
Sabo da tsabta ko unguwa gidan mutane bata zuwa,idan ma taje gyalenta idan ta cire yana hannunta,tana dawowa kuma zata wanke kayan tas ta shanyasu,idan ko tsautsayi yasa wani ya mata Amai ko fitsari to har Abada baza ta kara sa kayan ba,kuma baza ta bawa mabukaci ba sabo da rowa gwara ta zubar a dustbin,
In kaje gidanta ko yini baza ka iya ba yanda zata bi ta tsangwameka,komai kazanta,komai baka iya ba sai ita,
Hattana girki ita ba a isa ka koya mata ba,ko bata iya ba sai tace ta iya ta fika iyawa ma,turmi da tabarya ma kullum sai ta wankesu ta sasu a cikin katuwar ledar buhun sugar,
Idan taje kauyensu kuwa har murhun dutse sai ta wanke musu shi,idan taga bayan tukunya da baki a jiki ko me ka dafa da tukunyar baza taci ba.

Sai Kaci kwalliya kana kamshi kana zuwa kusa da ita sai tace wari takeji,sam turaren me wari ne,amma nata ko wanne kala ne to shine me kyau me kamshi etc,
Komai da an zauna hira to zancen kasar waje zata fara maka,ai mu a kasarmu kasa kaza bama cin kaza,yaushe za ayi kaza,ai mu a kasar mu ta Kaza Kaza muke ci aikinta kenan,
Yau idan tasha tea sai tace Ulcer ta tashi,gobe taci farfesu tace ta sata zawo ta zubar a shara,har kudi chanji idan aka kawo mata sai ta wanke,magani paracetamol ko wani idan zata sha sai ta wankeshi a kwalinsa,
Babu yanda za ayi ka gamsar da Momy nan gaba zaku ji halayen Momyn su Sardauna wanda bata da ko kawaye duk sun gujeta ba wanda yake saurararta Sabo da halinta musamman rowarta abinci kaje gidanta ba karamin kudi ne da kai ba zata baka kaci,sai yaranta da Mijinta,ma'aikatan gidan ma dan ba yanda zata yi ne su suke dafa ma kansu,duk da haka yan aiki basu cika zama ba halinta zai Sa su gudu.

Ramlat ce ta mike tabi bayan Mami suka dinga zaga gidan gaba dayansu subhanallah beds dinma da suke gidan abin kallo ne,komai na gidan fari da pink ne abin sha'awa kamar wani aljannar duniya,tsayawa fada muku yanda akayi ginin sai Pages su kare ba a gama ba domin gidane na haskawa a labaran duniya,kamata yayi ace BBC ta haska gidan nan a news kowa yasha kallo a duniya🤣.
Mami ce ta kai komai nasu part dinta domin ita nata hade yake dana Sardaunanta su biyu,abin mamaki komai na amfani har Sutura komai Sabo gasu nan iri iri an shirya komai,Ramlat ma ta haye bangarenta tab kaya na alfarma ba abinda babu a gidan,ba abinda mutum zai siya komai akwai,kayan Ramlat kuwa akwatuna ta gani guda 20 yan gaske,gefe kuma ga wasu guda uku na yaro,Mohd ne ya shigo yana kallonta,Ramlat tace wannan kayan sawar fa harda su Cosmetics da saura su? Sardauna yace Lefenki ne da ban miki ba,dariyar jin dadi Ramlat tayi harda lefe King duk abubuwan da kayi min?yeah mene to waccan kuma na Baby girl dina ne,Ramlat ta kara jin dadi sai addua takewa mijinta ta fice da Sauri tare da kirawo su Mami,Momy,Dad wai suzo susha kallo,aifa kowa ya wanke idonsa da kallon kayan gayu masu tsada da birgewa iri iri,Mami ma tace azo a kalli nata,itama gasu nan komai akwai,Sardauna kuwa nasa ma ba a magana ka rantse dan Adam bazai iya gama sakasu a duniya ba.
Waya ya yiwa Maman Naufal ina masu aikin da yace yana nema mace Dattijuwa me jini a jika da namiji shima me jini a jika Amma Babban mutum,Mami tace bari nayi wa Baba me aiki waya wacce mukayi zaman mutunci itama tazo taci gaba da aikinta tunda yanzu Allah ya hore ko,Ramlat tace Good Idea,Sardauna ya kalleta tare da sakin dariya ya tuno da Prof, sai yace no Good decision zakice,
Momy da Dad sun zama yan kallo,daga nan sukace su zasu wuce Dad zai huta sai gobe kuma,Har mota suka rakasu Driver ya jasu suka tafi,su Nabeel dama tuni sun janye Fahat sun tafi gida Sardauna ya basu haushi.

kar kuyi tunanin Sardauna dukiya ya tara me uban yawa no kawai zuciyar yi ce baya ajiye kudi duk abinda ya dace zaiyi to idan ya tattara kudin haka zai yi,idan ma wani zai taimakawa ba ruwansa da kudinsa kadan ne kawai zai kundige yayi abun bajinta,haka yakeyi ba za ka taba zama da Mohd ace baka moreshi ba,zaiyi planning komai zaiyi a tsari amma. Fa shi baya tara kudade zai dai bar wanda zai isheshi ko mene zaiyi dai dai gwargwado,gashi duk gidan da yaji ance akwai marayu sai ya basu wani tallafi ko yayane dai dai karfinsa,haka yasha biyawa marayu kudin schl tun suna Kd har Adamawa,mata wanda basu da miji an bar musu Yara,da sauran mutane marasa karfi ko dari biyar ce sai ya baka,ba wani batun ayi ta tara kudi ana jibge kadara ga Alumma cikin talauci.

Mami ta gama hada ruwan zafi me mugun yawa yana tafarfasa Sardauna yaga ta cika Bahon wanka dashi zaiyi bucket uku,yace Mami wannan ruwan za a zuba mata? Ramlat wacce ta fara kukan Ruwan,Tace ae King da shi akeyi kuma wlh zuba min zatayi skin dina zata koma baka,na kone,Sardauna yayi tsalle ya dire yace baza ayi mata ba,Mami tace zan mareka mu duk ba haka akayi mana ba,ayi mata na towel mana ko a rage masa zafi ta shiga ciki ta zauna,Mami tace ai danya ce yanzu baza taji komai ba duk zafin nan musamman da nake so nayi mata na ganyen runhu,
Sardauna ya hangame baki irin wanda ake Zane mutum ga duka ga ruwan zafi ni dai Allah baza ayi mata ba,in hakane ni a barni nayi mata ai na iya.

Dariya Mami tayi tace ke wuce muje,Ramlat ta makale a bayan Sardauna,Idan nayi fushi Allah sai dai mijinki ya miki komai na jegon nan,Ramlat tace ae ni zai min,Mami tace to kuje kuma har Jaririya sai ya mata,Sardauna yana dariya yace Allah barmana ke Mami abu me sauki ma kenan Yiwa Baby wanka,Zauna ki huta.

Mami tana kallon kuruciyarsu suka shige toilet din Ramlat na Bed room dinta,Ruwan ya bari ya dan huce dai dai wanda mutum zai iya zama ciki,amma fa da zafi rau rau,harda zuba gishiri,yasa garin Gayyen magariya ruwan sai kumfar magariya da yaukinta yakeyi kadan ga zafi,
Ramlat

Please Login or Register in order to submit comment