Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

irinku,kai zo na fara dubaka ina da aikin yi city zan tafi zafi ya isheni da sauro.

Nan kanjalallen marar lafiya ya karaso yana numfarfashi Dafta yaji matsalarsa nan take ya masa Allura da Karin ruwa,haka ya kusan yini a chemist daga bisani ya dora yaronsa ciki ya shirya sai Zaria.

Sardauna shuru yayi yana sauraren surutun Ramlat Bai ce komai ba har ta gama sannan ya fara magana cikin muryarsa me dadin sauraro a tunani na yanda muke dake da yanda nake nuna miki Basai na furta da baki ba ya isa ki gane meke zuciya ta,da ace zan gujeki ko na rabu dake wa ya isa ya hanani?amma ni nace naji na gani.
Amma tunda hankalinki yafi kwanciya da hakan ba matsala zan jira har sanda zaki aminta, tunani ya shiga yi na tsawon second sai kuma yace

ke na fasa ma gaba daya ko kince na miki Bazan yi ba sai da kanki kin yarda shike nan?
Ramlat taji tausayinsa amma tace eh na ji tare da sako wata hirar ma.
Sardauna yaga fa Raina masa hankali zatayi sai yace Ramlat Na fasa kawai hakki na nake so a bani abina,

Murmushi ta saki tare da cewa ka fiye tsokana yanzu fa an kashe magana.. ba wasa nake ba karba zanyi ta arziki ko ta tsiya,
Dama ba kayane a jikinsu ba,kici kici suka fara da Ramlat sosai suke dambe kamar wasu zakuna
Sardauna ya kamota yana ni sa'anki ne da har zakiyi kokawa Dani,bari na sauke miki abinda ke kanki ki San ba daya muke ba.

Ramlat tace da nawa ka girmeni ka bari mana ka kara girma tukun amma kana shekarun nan duk kabi ka damu kanka akan dan wannan abun.
Bakin ciki ya lullube Sardauna dama ta Dade tana ce masa yaro baya daukan mataki shi yasa take fada masa,

Flat ya mata ya danne hannyenta da nasa,kafafunsa yasa ya danne da nasa ta yanda da niyya yayi a haka komai zaiwa Ramlat sai ya iya yi mata ko fyade ne tana ji tana gani zata hakura karfinta ya kare gaba daya tayi shuru tana raba idanu, Kallonta yake fuska ba Rahma yace idan kin isa ki maimaita maganarki ta dazu,Ramlat hawaye ta fara tana dan Allah kayi hakuri wlh ni dama bance baka da karfi ba,ban San haka kuke ba yanzu tuni na gane banbancin.
Hmm ai baki gane ba tukun cewar Sardauna,Wlh na gane ya Sardauna tsokanarka kawai nayi ni dama na isa ni din banza ai kune maza,musamman kai da kake kato haka na Dade da ganowa kai me karfi ne babu abinda baza iya ba.

Kyaleta yayi tare da sake mata hannaye sannan yace kyaleki kawai nayi sabo da ba a haka nake so ba amma kinji Allah daya ko da wasa kika kuma ce min yaro wlh duk inda muke komai mutane sai na miki abinda baki zata ba,

Da sauri tace na gode bazan ma kara ba, Allah ya maka Albarka,banza ya mata ta matso jikinsa tare da leka fuskarsa tana murmushi tace to smile,juya mata baya yayi, ta koma gabansa,ya kara juyawa ta koma gabansa again,idonsa ya rufe ruf,ta koma cikin jikinsa tare da mannewa,baiyi motsi ba amma yana Jin wasu tsutsotsi na yawo cikin jinin jikinsa daurewa kawai yakeyi,
Kiss ta dora masa a lips,baiyi ko motsi ba,lips dinsa ta ciza kadan da sauri ya bude idonsa amma ya maida abinsa ya rufe,

Cakulkuli ta fara masa amma dan jaraba ya shanye tsab baiyi dariya ba ba mutunci ance masa yaro wato bazai iya yiwa mace komai ba,
Pls ka min magana,wai baza ka min magana ba,i said am sorry fa bazan kara ba,
Tunda baza ka hakura ba ka rama ko ka min hukunci amma banda wannan pls,Haba na Mami ikon Allah,
Ranka ya dade me girma Sardaunan Ramlat,

Nasan fa kana ji na wlh bazan kara ba,ok tunda hakane am ready ma yanzu tashi kayi zaka iya na sani, da wuri Sardauna ya bude idonsa yana murmushi,Ramlat ba da gaske take ba Sam ganin ya bude Ido yasa gabanta ya fadi kuma ta riga ta fada,
Amma tace wedding party din an fasa ne? Tsaki yaja ya kara rufe idonsa fuska ba Rahma,Ramlat tace na shiga uku tashi dan Allah kayi to wukil ya kara bude idonsa yana kwance lamo kamar jariri,
Hannu ya mika mata hankali yace hakkina za a bani ko ki kwana cikin fushin Allah ni ba ruwa na ba yafewa zanyi ba,
Ramlat ta firgice tace to da mun koma gidan Prof first,a nan nake so idan kuma baza ki bani abina ba ga Allah nan yana kallonki,Ramlat ta fashe da kuka,Sardauna yace wlh yau sai kin bani ko kukan jini zakiyi sai na nuna miki yau ban ban bancinmu,Ramlat tace tun yaushe nasan ba daya muke ba, dan Allah kaji ka dan kara min ko kwana biyu ne,

Shuru ya mata kamar ma Bai San tanayi ba sai da ga baya ya ce kina karawa kanki azaba,idan na kamoki da kaina da Zafi zanyi,Ramlat ta kara karfin Kukanta dama mugunta ka hada min ka kawoni wani ganin gida na Dade da Sanin baka kaunata da nasan hakane bazan zo ba,
Dariya Sardauna yayi yace ai dadin zuma a jita a baki queen bani a bata na Sha na Dade ina tarata kin San tanadin da na mata kuwa?ke da ace kina da Imani ma ai ko musu da baza ki min ba,Har 2yrs na kyaleki fa,yanzu bazan iya ba na yi abinda zanyi,gwara ma ki bani hadin kai kafin nayi yaga yaga dake.

Ramlat tace uhm...to...uhmmmmm.....wayyo...gani to kar kayi da zafin kaji
Daga can nesa ta miko masa hannunta sai ya mika zai jawota sai ta janye da sauri ta ja baya,haka ta dinga masa,sai da ta miko yaki mika hannu ta gama sakankancewa sai ji tayi ya fisgota ai kuwa ta tsala uban ihu kamar ana yankata tun baiyi komai ba,
Nan Hotel ne ba wanda zai kulaki Queen ko mai ihun da zakiyi,fara lallashinta yayi yana ta lallabata yana bata baki,kiyi shuru banga abin kuka anan ba,bafa Zafi karya ake miki duk wasu novels da zakiji suna fada karyane idan mace taki bada hadin kaine yake mata Zafi,bare ke da kin girma shekarunmu daya fa kikace mene abin kuka ai baza kiji komai ba,idan kina kuka bazan iya tursasaki ba,tunda fa mukayi aure zan iya yi kawai ni nake barinki ina ta rainonki, My Queen ko me kike tunani ma ki daina ba dai ni kike tsoro ba kar na juya miki baya ba? To bazan juya miki baya ba idan kina so ma zan iya kama mana gida a Zaria mu zauna tare weekend sai naje Kd ko ayi transfer schl
In dai nine kin mallakeni har Abada amma soon zan nuna miki hakan trust me ya kamata ace kinfi kowa Sanin halina,
Duk abinda kike so a duniya indai baifi karfina ba zan miki ki daina damuwa,

Ramlat tace har kishiya Baza ka min ba? Sardauna yace Allah ne ke tsara rayuwar bawa Amma indai kin iya kula da ni da komai da ya dace mace tawa mijinta duk kinayi to bake ba kishiya, idan kuma Allah ne ya kaddara kece on top ita din banza.

Ramlat tace to ai dai in dai ina maka komai da kake so ba kishiya ko?Yea sured cewar Sardauna,
To har wannan ma idan na yarda shike nan sai ni kadai? Sardauna yace ofcourse shine ma na farko,
Ramlat sai lokacin tayi murmushi tare da cewa ai wuya bata kisa am ready.

Sardauna farin cikin samun nasara ya kamashi,Ramlat ya kankame a jikinsa shi kadai yasan irin farin cikin da yakeyi, yace tashi muyi sallah,

Sallah sukayi da adduoi shima ya kama kanta ya dinga zuba addua,nan ya fara aika mata sakonni ba ji ba gani sun rude gaba dayansu,Malam Sardauna yayi sama da Ramlat zuwa bed,
Ramlat sai Kukan dadi take tana kara tura masa jikinta ta shige masa sosai,Sardauna kuwa ya daina gane komai hanya ya fara nemowa Amma babu alamarta,yayi yayi sam ba hanya,kallonta yayi tare da cewa Queen ina hanya? tace to wai ni ba haka naga ta kulle ba tun rannan dana sha wani maganin Juicy na 1wk shine naga kofar ta kulle,
Sardauna hankalinsa yayi matukar tashi light ya kunna zai bude cinyoyi yaga zahiri,ta ki yarda ni karka kalleni da haske kunya zanji,tsaki yaja ba tare da ya kulata ba ya wangale cinyoyinta ta karfi kamar Doctor ya kara kunna torch din wayarsa ya haska wajen aiko ya hango wanjen saura kadan ma ya karasa shafewa ba kofa ba wani waje babu abinda zai iya shiga ciki sai ko in tsinke ne,

Bakin ciki ya kama Sardauna rufeta da masifa yayi ba ji ba gani ke wai wacce iri ce ke a duniya kina hauka ne da zaki sha maganin baki san ko mene ba,a garin haka kuke jawowa kanku lalura,bamu fara yin komai ba kinje kinsha wani abu iya na Mami da ta baki bai Isa ba,maganin Infection akeyi sai na na',ima ba kawai ki dauki abu kisha ba.
Kin san Allah kin fasa karatun nan tunda haka zaki koma daga nan muje ki kwashi kayanki mu tafi gida na fasa biya miki,dama nasan haka zata faru a gidan yan iskan nan,ko maganin mutuwa suka baki sha zakiyi ko ki dauka ki sha ba tare da kin san na mene ba, dan Allah kayi hakuri Bazan kara ba ka barni wlh yanzu ina son karatuna,Na nunawa Fadeela tace min aswakin mata ne na daka da zuma na dinga shan kadan kullum,ko na hada da kaninfari da Aya sai aswakin matan na zuba a zuma na dan sha,tace yan mata ma suna dan lasa,ni kuma ganin ina da aure kuma gashi da zakin dadi baka ji ba, shine nake zubawa ina shan 2spoon kullum,3wks ban sani ba sai gani nayi na dawo haka,ni ban sani ba wlh kayi hakuri kuma Allah ina son karatu na.

Waya ya Mika mata yana hararta yace kirata kice yaushe zai bude?
Sai da tayi Ringing ta kusa katsewa sannan Fadeela ta daga hello tana ta wani shidewa da Alama dai itama gwangwajewa sukeyi da kyar tace Ramlat lfy da dare haka,na fada miki abun nan ya kulleni fa gam oga ba lfy,Fadeela tayi dariya sannan tace kece da shirme ya zaki dinga sha da yawa,ke dalla bake kika jawo ba,ok to Karki kara sha 2wks zaki dawo normal idan kinyi Sa'a ma 1wk,
Ramlat tace aikin banza kawai kin jawo min salon ki kashe min aure kina can kina wani haukar Kukan banza da tsoho,ban da lokacin ki cewar Fadeela good night.
Ina maganin Ramlat ta bude Jakarta ta mika masa wata farar roba me murfi,magani yasha zuma da kaninfari,Sardauna ya dauki shegen tsumin ya zuba a dustbin,a kwai wani?Sai ga Ramlat ta kara miko wasu tsumin a jarka kala hudu,ya kwace duk ya zuba a dustbin,
Tare da kora mata warning,masu baki Baza su san baki taba komai da Mijinki ba ki kiyaye,ina ruwanki ma da maganin su wata Juicy zaki sha.

da masifa yace sai ki san yanda zakiyi dani,kuma kin daina jin Dadi ko na romancing wlh sai kun bude na karbi Zumata.
haka Ramlat ta zage tasa ya samu nutsuwa sosai ga masifa yana mata, duk da cewa itama tana son Romancing Amma tasan bazai mata ba ta ajiye kwadayinta gefe.

Washe gari da wuri suka gama komai tare da shirin tafiya,Tabayarsa tayi ya kaita gidan Talatu ba musu ya kaita suka gaisar ta da zasu tafi ya bata 5k tayi ta murna da godiya,
Suna mota tace dan Allah kafin mu bar kano kaini company na Ginger,ba tare da ya kalleta ba Sabo da fushi yake ta faman yi tun jiya yace bani Address,ta fada masa sai gasu a Company na Ginger,
Masu aiki suna ta yi dalleliyar motar Sardauna ta shigo ciki,tunaninsu ma ko dan uwan Boss ne bature.
Ramlat ce ta fito cikin rantsatsiyar shigarta domin tafi matar wani me kudin jin dadi da Sa Sutura sabo da Mohd me zuciya ne da karfin hali,baya ajiye kudi duk wanda ya samu za a Shana da kudin ba damuwa.

Har Ramlat ta fito daga mota basu ganeta ba tana taku dai dai da takalmin ta me dan tsini ba da yawa ba, har ta karasa kusa dasu Firdausi basu ganeta ba,sai da tayi sallama tana dariya suka gane Ramlat ce,wajen mata da Maza kallonta sukeyi musamman Boss da fitowarsa kenan zai duba aiki,
Sardauna sai kishi yake taso masa yana cikin mota,

Ramlat Tsofaffin nan suka hada baki wajen fada,Su Habiba suka taho da gudu wajenta jikinsu duk kurar Citta idonsu yayi furu furu,
Gaisawa sukayi sosai suna tambayar bayan rabuwa, Tsohuwa tace Ramlatu ni 'yasu kinga yanda kika dawo baturiya kuwa kunyi kiba kalli fatarki kamar me ciki,iri wannan kyan haka,
Duniya ta samu Ramlatu cewar wani matashi,
Iya tace Wai ina kika shige ne?kin barmu ga Boss har nemanki yake tayi,dan Allah ki aureshi a bani manager ko sakatariya,mutane sai dariya,Ramlat tace Iya nayi aure fa,iyye Ramlatu ko wancan ne me gidan?Ramlat tace eh shine ya kawoni yace nazo mu gaisa daku,gaskiya yana sonki cewar wata dattijuwa,Ramlat ta kara shanye hannu tana yanga tare da yatsina fuska sannan tace Firdausi shine fa Sardauna Mohd dan Uwana da nake fada muku yana sona naki yarda to shine fa.

Habiba ta kwala ihu tare da cewa Allah ya biya tawan kin birgeni,Firdausi tana dariya tace kinga kina cewa bakya sonsa gashi Allah yayi shine mijinki,Ramlat ta saki murmushin yanga tace hmm ya na iya da samarin kakata ai dan Uwana ne ya zanki sonsa,ina mutuwar sonsa,Habiba ta rike baki lallai Ramlat kin faso gari Allah bamu irin naku,kin barmu a baya kinci gaba,kalleki fa tab.
Dama ke ba kalar wahala bace,.

Yanzu dai Sauri mukeyi zamu wuce yaushe zaku zo gidana?Gidana a Kd yake,me yasa bai miki a garinsu Abuja ba?Firdausi ta tambaya,Ni nace nafi son Kd shine yazo ya Gina min hadadden gidana Mami kakarsa ma tace a Kd take so shine muke zaune gani ga Kakata kuma kakar mu daya both ta rainemu fa Amma husband dina shi a hannunta ya girma

Binto tsohuwa ta saki guda a wajen tace ayiriri kice tuwona maina akayi,
Ramlat kanta ya kara fadi taci gaba dan Allah iya kuzo gidana ina gayyatarku watarana bari na karbi Number su Habiba,idan kuma sai na haihu to sai kuzo suna kawai duk da cewa ban san a ina za ayi sunan ba amma zanyi kokari ayi Kd ko dan kuzo min yafi miku kusa fiye da Abuja.

Tsofaffi suka kara sakin shewa tare da cewa wlh zamuzo har Abuja musha kallo,binto tace ai muci kaji da lemo muji dadi kuma idan zamu dawo a cika mana lalita da fararen Abuja.

Wata tsohuwa tace ni Idan nazo in kina so ki birgeni to ki hada min hadadden shayi yasha Madara to yarinya kin gama birgeni ko ba ko sisi ni a bani shayi me Madara.
Ramlat tana dariya tace Iya kin hadu dashi indai shayi ne domin Ba abinda babu a gidana,yanzu yaushe zan iya cin abinci ba kaji,
Habiba ta zaro Harshe tare da sharbe yawu tana lashe lips tace shegiya kin fado mutanena kaji,wata tsohuwa ma tace yarinya ga shawara karki yarda da tsarin iyali ki tsaya ki sankato yaranki zalla zalla gaki da kyau mijin ma masha'ala indai da abinci me kyau da kula ko Yara ashirin kika Haifa dakau kau za a ganki,ki ci ki koshi ki gasa kanki da ruwan zafi yarinya banda gudun wankan jego zaki zama danya hh

Binto tace ga tawa nima karki sake wata ta fiki Maggi yarinya,ki nemi masu karin zaki da dandano,karki nuna masa kina sha,maza iyayi garesu suna gani zasu ce karki sha sunfi sonki haka kina biye musu zasu ji ki ba Maggi su auro wata ta fiki Maggi kiga wulakanci,amma yanzu ko zakiyi kadan zakiyi sai kin haihu zaki nemi dandano har ku yan mata ku dauki darasi ta furta tana kallon su Habiba,

Iya tace angon bazai zo mu gaisa bane?Ramlat tace bari na je na kirashi,

Kafin ta karaso ya taho wajenta
Zuwa yayi wajen suka gaisa da mutane Har Boss dake gefe,Iya tace gaku kamarku daya sannan Allah ya Bada zaman lfy,a kula yaro a kula aure ibada ne ba wasa ba, nan iya ta Dage ta dinga Yiwa Sardauna nasiha akan aure kamar Uwarsa.

Bayan sun musu sallama ya damko hannun Ramlat tare da musu sallama sannan ya bawa matan 5k yace suci abinci,Iya tace wlh Baza a bawa kowa ba sai iya wanda sukai hira da Ramlat yau.

Sai da suka hau kan Zaria road,Sardauna yace kin wani zauna kin dade Maza sai kallonki sukeyi musamman dan iskan baturen nan, oh Boss?ai so na yakeyi da ya dade yana sona,har tausayi yake bani sanda yake nacemin,har abinci yake siyo min,
Kishi da bakinci ya turnuke Sardauna kana yace dama shi yasa kika ce na kawoki,ai da nasan haka ne wlh Bazan kawoki ba,wannan ma a bakin makarantarki muje ki kwaso naki ya naki,

Wlh ni ban taba sonsa ba ma,kawai mutuncin da ya min ne nake ganin mutuncinsa,Haba dan Allah sai ta fara shesheka,Sardauna hararta yayi tare da cewa su kuma sauran mazanfa da na gani suna zuwa kuna gaisawa? Yan kano masu son farar mace mayun Fara ko na mai ne kin wani tsaya ana ta kalleki,

Ramlat tace su kuma yan Kd yan karya masu siyo littafin history na wata kasar ya karanta yazo ya dinga zabga karya suce zuwa kasar sukayi fa,masu bacci da glass a fuska,me gyaran mota yace sai da mota yakeyi,ya aro kaya yace nasa ne yafi kowa wayewa harda murguda baki,

Dariya Sardauna ya saki yace to ai sun waye din ne bayan haka ma ni ba dan Kd bane kin sani bani da hadi da Nigeria,what of u?yar Jigawa yan kauye,Ramlata dukansa tayi kadan da wasa tace uhm Amma ai jini daya muke,a'a wlh da garin Uba ake takama ke fa Dad naki dan Jigawa kauye ma ba city ba,
Ramlat tace ae a haka aka auroni aka gani ana so,kuma arzikin Nigeria kake ci tunda anan kake zaune kake kasuwanci har ka samu kudin aure aka baka scholarship kaje turai in ba tsoro ba ka koma talakar kasarku mana, dariya Sardauna ke yi sosai yace ai harda ke zan koma can kinga kin koma yar can kema,ki godewa Allah baban yaranki dan wata kasar ne yaranki sun Zama yan kasar.

Idan ma kince a haka na gani na auro ni fa taimako nayi nan ya fara kwaikwayar muryarta kayi wani dan Allah ka taimaka min ,
Kukan shagwaba Ramlat ta fara tare da cewa me yasa kayi taimakon ni nace dole ka taimakeni?kawai kaga hadaddiya dama can kana so Ina fada ka wani ce a tsaya kar a daura itama ta kwaikwayesa yanda ya fada da iyayinsa

Dariya ya kara fashewa da ita tare da cewa gwara ni dai ba dan kauye bane yarinya dake,to anji cewar Ramlat tana turo baki.

Ramlat tace amma dai kasan ko sanda ka aureni ba kwalla bace na wuce ace min yarinya,
Sardauna yace yarinya ce mana muguwar kwaila ma a hannuna kika girma lokacin ko Wannan baki dasu yana nuna kirjinta da lips dinsa,
Ramlat tace wlh ina dasu Bana son sharri,ranar dai kika girma ranar kika fara period ni na koya miki sa pad ko ta nan na wuce kice min sa'anki.

Ramlat ta karkada masa Ido tace eh naji,
Sardauna dai ganin motarsa tinted ce ya fara shafa dukiyar fulanin Ramlat yace ah gaskiya kin girma na iya kiwo kinji.

Ramlat mukus tayi batace komai ba domin enjoying takeyi,dama jiya bata samu an mata ba,kwantawa tayi a jikinsa tana langabewa tare da shafa sajensa da gemunsa zuwa wuyansa,ko mu kwana again a kano?na ma tuna kin cuceni kofar Saura kadan ta karasa kullewa,Ramlat muguwar tace dan Allah mu kara kwana,murmushi yayi with time yarinya wlh karkiyi tunanin zanji tausayinki Allah ya kaimu ba inda zan tafi ina Zaria har sai na ganshi abuna.

Ramlat gwalo ta masa yana ta driving cikin nutsuwa har suka isa Zaria gidan Prof yace tayi sauri ta kwaso kayanta zasu wuce,ina zamuje kuma?karatunfa?bayan dazu kace min kana Zaria muna tare? Zakiyi karatunki zo mu tafi gidan Mami Kd zan dawo dake kuma wannan gidan kin gama Zama cikinsa,idan mun dawo da Mami zamu zo ayi musu godiya je ki fito kawai kice Hutu zamu tafi gida.

Haka kuwa akayi Prof harda bawa Ramlat 10k yana ta jimami Bai ji dadi ba wai yana jiran dawowarta ta hada masa laws wanda za a kafe a ko ina na gidan sabo da gudun karya doka.

Yan matan kuwa su Chuchu ko kallon Ramlat basuyi ba takaici ya ishesu,Ammi tace tsinanniyar ta daukeshi zasu tafi Hutu sai da na gama asarar kudina wajen shahararren Malam Ya'u ba kara min kudi na kashe ba akan a samu Ichichy ta samu ta shiga daula nasan Soon Sardauna zai koma wajen Ubansa,gashi yanzu ya tashi a banza,yace min na farke cikin pillow na sa layar a ciki a dinke dayan na sa kasan gadonsu, wani kuma zan bar bada a kofar dakinta ya taka,to yanzu duk na gama aiwatar da komai ina jiran shigowarsu yanzu kalli ko shigowa ma yaron baiyi ba wannan yar iskar ce ta shigo ta kwashi kayanta kaf,
Harda cewa wai yace ayi mana Sallama bazai iya shigowa ba karuwar banza,

Lilla tace ai zasu dawo sai a karbo wani,ke wannan yarinyar ba lallai ta bari su dawo ba,yan kauye idan suka goge sunfi na birni iya shege sabo da rayuwa biyu sukeyi ta birni data kauye sun gama Sanin kan duniya wannan yarinya kwai yar iska cewar Merry,Ammi ta kara da sai da na kashe Dubu Dari da hamsim akan ayi min babban aiki.

Sardauna suna hanya wasu shegun motoci na binsu a baya sun kai goma da Alama su ake bi a baya.






AsmaBaffa
🏀🏀🏀🏀🏀🏀
🏀🏀🏀🏀🏀🏀


DUK INDA TA FADI


2pages

171-175. 176-180





Official





By
AsmaBaffa








Please Login or Register in order to submit comment