Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

waje ba wani babban mutum bane amma ya wuce ace yaro ne,kyakyawa ne ajin karshe,
Ramlat ya kafe da kallo kamar maye,Ramlat ma shi take kallo sabo da kyansa kamar Sardauna sai dai Sardauna ya zartashi kuma da kuruciya,
Murmushi ya sakar mata tare da komawa mota,minti kadan sai ga wani guard yazo wajenta tare da mika mata wani short note a paper,
Tana dubawa taga phone number kuma an rubuta I love u call me if u don't mind,
Ramlat ta zaro Biro tare da rubuta Ina da aure,ta mikawa guard ya kai masa sai gashi ya dawo da amsa

haba yan mata ki kashe aurenki ki dawo ki Mori arziki,ba da komai nake Sonki ba sai da aure kuma da arziki,kizo gareni kiji dadin duniya ga number dina zaki iya nemana idan kinyi shawara.auren talaka Bai kamaceki ba kamar inda kike dalili kuwa farat daya naji ina kaunarki kina kama da zuriya ta,shi yasa nake so na kaiki cikinsu na hadaku.

Tabe baki Ramlat tayi tare da jefa paper da Number ke jiki a jaka tace shike nan,kawai sai taga motocin sun bar wajen sun fasa yin shopping kenan,
Suna tafiya sai ga Sardauna ya fito,yana tambayarta waye suke magana dake?ta dauko paper tare da mika masa tare da cewa
Wani Dattijo ne matashi wlh me kyau kuna kama dashi Sardauna ko Daddyn kane ba a sani ba?, Tsaki Sardauna yaja tare da cewa to sai me idan shine nan ya kwace paper ya yaga paper da Number ke jiki yace muje gida.




Ba time na editing fa akwai error da yawa afwan.tnx



AsmaBaffa
🏀🏀🏀🏀🏀🏀
🏀🏀🏀🏀🏀🏀



DUK INDA TA FADI





146-150




Official




By
AsmaBaffa






House of Hausa Novel
AsmaBaffa fans club
Taskar firddausi so dangi
Wannan page naku ne Sabo da Sharhi kullum ba yankewa tnx.





Prof zaune a palo yana ta faman jira yana jan tsaki an bata mishi lokaci,
Ammi ya kwalawa kira tana fitowa ya fara masifa wannan wanne Nonsense ne African time din yayi yawa,wannan yaron ko waye bai san muhimancin time ba,understand Hajiya ba son each and every single second kayishi ba tare da abu me ma'ana ba,how..how on earth zai zaunar dani ina jiransa yasan ayyukana kuwa yasan amfaninsu,Ammi tace dan Allah Prof ka dinga hakuri a duniya haba zai zo mana,

Tsaki Prof yaja tare da cewa yaro dai kawai kuce bai san ma me yake ba,taya zai karya kundin tsarin doka,Hajiya idan bazai zo ba kuyi masa waya da Allah na wuce important issue na
Chuchu anci wanka ta fito Prof ya balbaleta ya zaki dauko mana kidahumi wanda Bai San darajar lokaci ba,wannan idan kika aure shi nasan common kayan miya kafin ya kawo yunwa ta illata min ke,sabo da Bai San me ake cewa Time ba.

Aure hauka ne ko me cewa akayi dole sai kayi aure zaka rayu,mutane kuna bani mamaki,dan bakayi aure ba ko kaki yi da wuri sai a dinga ganinka wani dan wuta,
Aure hauka ne an an fada miki akan kin matsu da aure sai ki dauko shirme ki kwaso min.

Assalamu'alaikum Sallamar Dafta ta dauke hankalin Ammi da Prof tuni Chuchu an fada daki kaji tsohuwa.
Ammi tana washe baki tace hankali ya kwanta Prof gashi nan

Prof ko amsa Sallama baiyi ba y tari Jibrila da fada,tun anan ka fadi screening,a haka zaka samu aure?Jibrila yana takowa Prof yace work like a sience student ka tsaya kana daudu kamar mace be a man,be strong young boy,
Gumine ya fara ketowa ta ko ina a jikin Jibrila ya gama Tsorata da karaya musamman turancin Prof,
Da kyar ya lallaba tare da gaisar da lo Prof,

Go straight to the point cewar Prof,Jubrila ya gyara zamawa tare da good afternoon sir,Prof ya bude baki tare da furta God ba yanzu muka gaisa ba kuma na mene na kara gaisuwar,jikin Jibrila rawa da gumi yakeyi Prof ya kalleshi tare da tausayinsa yace relax relax young boy,
Jibrila tari ya kasa yi a palon,Prof yace kaine kace kana son yata zaka aura? Yes cewar Dafta,Prof yace good wanne mataki kake a karatu?ya sambado karya ya gama degree da Masters dinsa,Prof yace da kyau amma da ka kara ko phd ne,wanne course?yace medicine,
Wow Doctor ne Ashe na maka murna,
Felicitation

Maganar aiki fa? Dafta I'm Doctoring in my town,tun daga bakin Dafta Prof ya gano karya ce kawai domin turancin ma da ina ina yake yinsa,Prof ya zaro idunawa tare da cewa kai yaro Mind ur tongue harda zaro harshe wai Jibrila ya gane me yake nufi,
Kar ka kawo jokes anan gidan I'm very intelligent I know what am doing young boy ba anan ake mana bagu ba,

Jibrila yayi wuri wuri ya fara Am not doing magu magu to u Sir,this is correct speak(wannan gaskiyar magana ce)
Prof yace u r very stupid am I ur mate? ni za kayiwa karya?
Dafta ya tsure da fadan Papa sai ya manta yace ni...ni...ita tace na fada haka yarka ce makaryaciya amma ni ban saba karya ba.
Jibrila shima ya daina tsoro yace Look Olly (old) Man ni na tsallake jarabawoyi da yawa a rayuwata ban taba faduwa exam ba ko wani Screening ni da kake gani na ka tambayi tarishina(tarihi) hannu biyu yasa a aljihu tare da cewa wato Olly Man ka gane ni yanzu jarabawar Mala'iku kawai nake jira itama nasan insha'allah zan cinyeta gaba daya,

Sardauna ne ya fito hannunsa rike da waya yana latsawa yaci uban wanka kamar Baza a mutu ba,yana zuba kamshi,Jibrila ya kalleshi sosai a ransa yana ina ma nine wannan ga kyau ga kudi ga Ilmi Allah ka bani Ilmi nima a daina wulakantani,
Sardauna kuwa hannu ya mikawa Jibrila suka gaisa Haka ma Papa,Jibrila a ransa yana kaji hannu me laushi sunan wani abu wai shi tissue,
Sardauna shi dariyar shigar Jibrila yakeyi ga dai kaya iya kaya Amma da gani bai iya sawa ba,

Ko kunya Jibrila bai ji ba yace back to our Talk.Sardauna wanda ya juya baya kenan zai bar waje Amma sai da ya juyo tare da kallon Jibrila.
Jibrila yaci gaba
Ina da mutuncina da kudina da aikina bazai yuwu nazo ana min wani Screening ba kasan irin matan da nayi soyayya dasu? Hadadaddu zunduma zunduma kyawawa ni ba a wulakantani ko waye fuuuuuuu Jibrila dama masifar da yayi kawai dan ya nade tabarmar kunya ce ya fece,sannan kuma kowa yasan mutan kauye ko baka musu komai ba basa fuskata kawai ka wulakantasu,

Komai kace ko ayi ai anyi laifi wulakancine dan an gansu na kauye,basa daukan raini,maganar da zaka gayawa na birni ka kwana lfy na kauye baka isa ba sabo da suna da kara da kawaici sosai idan ko ya baka musu kara ba ko ba kawaici to fa ka ci musu mutunci.kuma nasu ne dai dai,domin cikin birni akwai da yawa za a ga magana ko wacce tazo mafi akasari fada akeyi ba taunawa ba tunanin Wannan Babba ne,iyayene,saurayi ko miji akwai maganganun da basu kamata ba wanda tabbas rashin tarbiya ce ido ya bushe.shi dai Jibrila yace an masa wulakanci,kuma ba a masa kara ba a matsayinsa na suruki wanda yaje neman aure,ganinsa ai aure kamar rufawa juna asiri ne zai rufa musu asiri za a masa wasu dakikan tambayoyi bincike ya dace ayi na halayyarsa da iyayensa Addini da sana'arsa anan Jibrila yayi gaskiya shi yasa ma ko ta kan Chuchu Bai bi ba ya fito da niyyar shiga motarsa,

Sardauna yana ta dariya a ransa cike da mamakin kamar wannan matashi zai auri guzuma Chuchu ai gwara ya auri budurwa ta kauye yafi masa,
Sardauna yace tafiya zakayi sai hakuri tsohon haka yake, Jibrila dama kadan yake jira nan ya fara kai kyale gara ni dama asiri akayi min,in ba Asiri ba kamata ace na auri waccen Aljanar tsohuwar ai sai aikin asiri,aka hakan har azo za a raina min hankali aikin banza me suka tara waye Ubansu a Gomnati waye shi a kasar nan,

Sardauna yace ka auri yarinya yar budurwa yafi maka karma ka wahalar da kanka,ga yan mata nan Yara masu nutsuwa,Jibrila yace basu san ko ni waye ba shi yasa,kyalesu Baza su kara ganina ba tare da shigewa motarsa na gode ablkina kai kadai ne me hankali a gidan nan Amma sauran gaba daya basa ja,
Akwai ragowar wata me hankali a ciki tana da aure duk tafi su hankali gata hadaddiya kyakyawa classic ce ta wuce ajinsu mata ta kenan cewar Sardauna wai fa Ramlat yake nufi,

Jibrila yace yanzu kana da aure?yea kwana nan zamu samo Baby boy ma,Jibrila yace kana wuta mutumina gaskiya ka birgeni yau shekarata 34 har yau mata wahalar dani sukeyi,amma zasu ci ubansu duk ranar dana shiga daga ciki billahillazi sai nayi wulakanci

Dariya Sardauna ya saki yana tuno shirmen Ramlat dinsa ga wani irinta.
Sardauna yace ai ni na huta Soyayya muke kwasa dama karatu takeyi a nan A.b.u tana level 2,Jibrila ya jinjina kai tare da cewa NA GODDDDEEEEEEHHH......kaji masu yi domin Allah,kaji manya, Allah ya biya yaro da kai ka iya kula da mace gaskiya I salute u,

Sardauna duk dadin Romancing din jiya ne yake kwasar shi, shi yasa yake ta wani zancen matarsa.
Jibrila ya shige mota tare da yiwa Sardauna Sallama zai wuce,Sardauna ma ya shiga motarsa kenan Ramlat ta fito cikin azababbiyar Doguwar Abaya red kamar Balarabiya,
Tana ta dariya hadi da bude Gaban motar Sardauna ta shige,Jibrila wanda yaga zuwanta yana ta tunani kamar ya San wannan amma ya kasa ganewa sabo da wannan Balarabiya ce

Sardauna yaga ya kuma fitowa daga mota tare da budewa Ramlat kofa ya jawo ta waje yana murmushinsa me tsada,
Jibrila yana kallo ya hango Ramlat zata koma motar Amma Sardauna ya jawota baya tare da Rungumeta yana ta goga fuskarsa a wuyanta,Jibrila ya rumtse idonsa yana kai a birni ana tsiya,
Sardauna ne ya hade bakinsa dana Ramlat ita kuma ta sakalkaleshi ta wuya,Jibrila ya ja dogin numfashi tare da cewa bariki iyawa,

Ramlat ce ta kurawa Sardauna Ido tare da Jan dan gemunsa,Murmushi ya saki da niyyar hugging dinta Bai kai ga yi ba ta zille tare da Fadawa Mota zata rufe ya rike murfin tare da daukota cak kamar Baby ya tafi da ita tana wutsil wutsil har Palo ya kaita ya juwo zai koma mota,da gudu ta wuceshi tare da shiga motar ta rufe,dole ya hakura ya shiga ya jasu suka bar gidan,
Jibrila yana zaune yana Shan kallo sai da ya gaji yace na dau Sharadi shi yasa Harka sai da dan birni kake sani duniya,

Yanzu da ina kauyenmu me zan sani sai dai labarin gona ko gidan wane anyi kaza wance ta fada rijiya,wance zata haihu aikin kenan.

ware gudun motarsa yayi sai Jigawa state kauye
Yana ta masifa gwara ma yaje yayi aikinsa ya samu kudade ya tsaya yana batawa kansa time,
Kauye kuma Patient gasu nan damkan ana jiran Dafta Jibrila likitan likitoci sabo da yau ranar zuwansa ce,yaronsa ne a chemist din sun fi son aikin Dafta Jibrila yasan komai duk tsananin cuta dan ubanta kana ganinsa yayi ma hadinsa yanzu a warke,haihuwa kuwa yanzu me jego da jariri a gansu sumul,idan kuma bazai iya ba zai ce ka tafi asibiti Babba,
Ba a nan Baiwar Jibrila ta tsaya ba har maganin Hausa yake rubutawa mutum ya nemo da kansa a daji ya hada yanda ya fada,ko ka siyo a kasuwa,kuma ba wasu zafaffu ba,irin su Habbatussaudat,Z aitun,gayyen magariya,tsamiya,Hulba,zuma da Sauran ingattatun magani,idan me hawan jini ne ya kara masa da zobo kullum ya tafasa da kaurin Sa yasha,masu Ulcer gayyen magariya zuma da Habba,gasu nan dai idan yaji cewar gayyen Kaza yana maganin Kaza to zaice ka jimancin cin Kaza,Dafta dai kullum a duba Google yake yana dan gano health benefit na kayan ciye ciye da wasu magungunan na Bature,abinda bai gane ba ya hakura.

Idrisa yau yasha ta buga masa kai ya shigo wajen Hafsatu ta masifa har da Marin Salma yar yarinya,daga nan yayi zuciya yace wlh...Hafsatu...zaku rasani kwana nan ....za a nemeni a rasa fa,
Duniya ta min kadan kasar yar kadance nafita girma....bazan iya rayuwa anan ba kawai ya bude karamar Rijiyar gidan tare da tsundumawa ciki,Hafsatu ta fasa ihu tare kiran mutane,da kyar a ka curo Jibrila,duk yabi yaji Raunuka,
Amma yace shi Rijiyar tafi masa dadi sai daure shi akayi a wani daki,ranar ba wanda yayi bacci a layinsu makwafta domin kwana yayi yana kurma ihu kala kala.

Hafsatu ta shirya tsab tare da kwashe masararsu ta siyar da ita ta sai tashar Mota ita da Yarta Salma.
Yaran kuwa yanzu sune cikin kango,bola, makwafta da wurare ba Islamiyya ba boko,duk sun kara lalacewa sun tarwatse yagai yagai dasu abin tausayi.
Idan sun dawo gida ba kowa sai su kadai haka zasu rungume juna su biyu suyi kuka su koshi har ma sun Saba haka kullum sukeyi musamman idan ana ruwan sama.

Mami kusan kullum sai Ramlat ta kirata sun gaisa,
Yanzu ma tana kwance tana bacci Sardauna ya fito daga wanka yaji wayarta na ringing Mami ya gani dagawa yayi suka gaisa yace bacci takeyi to ka gaisheta idan ta tashi,

Yana ajiye wayar kiran Abu ya shigo wayar,yayi picking,muryar Abu ce ta kusa fasa masa kunne da kara ba shiri ya cire wayar daga kunnensa sannan yayi baya baya da wayar yace Hello ina yini barka da dare,Abu tace iyeeeeee....kina jina.... Sardauna murya kasa yace bacci takeyi,Abu bata ji ba tace dan Ubanki kiyi magana mana,Yace bacci takeyi I said,
Iyeeeeee...naam...Ramlatu dan ubanki baza kiyi magana ba A'i ce zata yi magana dake,ga Talatu ma muna tare da ita tattaunawa akeyi akan ubanku,
Ramlatu.....ke Ramlatu,

Sardauna yace bacci fa takeyi ya fada da dan karfi kadan,Tace toooo...me gidan ne?kun San mutan kauye akwai martaba aure da me gida,Sardauna girma kansa ya kara yace Eh nine ina yini kuna lfy?

Wallahi lafiya lau wlh duk kalau muke,Allah ya muku albarka dai,Abu harda Jin kunyar suruki tace dan Allah tasheta ka bata,
Sardauna yace zata kira anjima yanzu idan na tasheta kan ta zai iya ciwo,
Bata mana haka mu iyayenta ne ko baka gane mu bane,

Sardauna ya tashi Ramlat ba shiri,Abu tuni ta kashe wayarta za a cinye mata kudi,Sardauna ya kirata back,yace Hello Mama? Abu tace iyeeeeee....Abu ce Ramlatu,a ransa yaja tsaki,ta cikin wayar Ana Jin Abu na magana da A'i cewar Surukinmu ne A'i gashi Ku gaisa,A'i tace a'a ni ban iya rashin kunya ba,Bazan iya gaisawa dashi ba,haba Abu sai kace yara na gaisa da suruki har Kinsa naji kunya wlh,

Talatu ta karba ita yar Birni ras suka gaisa da Sardauna,A'i tace anyi girman banza,
Abu ta amshe ke Ramlatu Sardauna yana dariya ya mikawa Ramlat ta karba tana Harararsa kana suka gaisa da Abu,tace ke Ramlatu ubanki ya fada a Rijiya fa,Uwarku gaskiya Ku nema mata magani ba kalau take ba,ta kuma tafiya to,
Dan kawai hannunka baya rubewa ka yanke ka yar amma wlh da bamu ba Idrisa,yanzu Ramlatu kin San Abinda Idrisa ya mana cin mutunci,
Ramlat tace me kuma ya faru nan Abu ta bata labari tsab harda kuka,

Haka suka dinga waya dasu Abu da dangi taki karewa,saida Sardauna ya gaji ya kwace wayar tare da kashewa,yace basa gajiya ki dinga takaitawa,kunnenki zaiyi ciwo a jawo min,
Wai kullum kamar a garinku kadai ake da matsala a kasar nan kullum labarin a bun tsiya Bana dadi,Ramlat tace uhm kowa dai ya fada,je kiyi wanka.

Washe gari misalin 5:30 yamma lis Ramlat da Sardauna sunje Shopping Ramlat tana jiransa a waje jikin mota take jingine wata rantsaiyar motoci guda biyar suka tsaya a gabanta, tuni guards suka fito da gudu tare da bude bayan Motar da yafi ko wacce kyau,
Wani Dattijon matashi ne fari tas kalar Naira da gani kudi sun ratsashi ya zuro kafafunsa waje ba wani babban mutum bane amma ya wuce ace yaro ne,kyakyawa ne ajin karshe,
Ramlat ya kafe da kallo kamar maye,Ramlat ma shi take kallo sabo da kyansa kamar Sardauna sai dai Sardauna ya zartashi kuma da kuruciya,
Murmushi ya sakar mata tare da komawa mota,minti kadan sai ga wani guard yazo wajenta tare da mika mata wani short note a paper,
Tana dubawa taga phone number kuma an rubuta I love u call me if u don't mind,
Ramlat ta zaro Biro tare da rubuta Ina da aure,ta mikawa guard ya kai masa sai gashi ya dawo da amsa

haba yan mata ki kashe aurenki ki dawo ki Mori arziki,ba da komai nake Sonki ba sai da aure kuma da arziki,kizo gareni kiji dadin duniya ga number dina zaki iya nemana idan kinyi shawara.auren talaka Bai kamaceki ba kamar inda kike dalili kuwa farat daya naji ina kaunarki kina kama da zuriya ta,shi yasa nake so na kaiki cikinsu na hadaku.

Tabe baki Ramlat tayi tare da jefa paper da Number ke jiki a jaka tace shike nan,kawai sai taga motocin sun bar wajen sun fasa yin shopping kenan,
Suna tafiya sai ga Sardauna ya fito,yana tambayarta waye suke magana dake?ta dauko paper tare da mika masa tare da cewa
Wani Dattijo ne matashi wlh me kyau kuna kama dashi Sardauna ko Daddyn kane ba a sani ba?, Tsaki Sardauna yaja tare da cewa to sai me idan shine nan ya kwace paper ya yaga paper da Number ke jiki yace muje gida.




Ba time na editing fa akwai error da yawa afwan.tnx



AsmaBaffa
🏀🏀🏀🏀🏀🏀
🏀🏀🏀🏀🏀🏀


DUK INDA TA FADI



151-60




Official





By
AsmaBaffa






MUM SAMHA
DJU LUV
JIDDER ZARIA
AYSHA KABEER
TEE TEE EMM
BADIYYA M JABIR
Wannan page naku ne godiya nake.






Suna komawa Sardauna gaba daya Mood dinsa ya canja ko me yasa oho, Ramlat ta kasa gane dalili,sai tsaki yake faman ja,
Aiki ya fara a system dinsa yana ta aikinsa yana shan tea abinsa,Juicy ce ta kwankasa musu kofa tare da shugowa Ramlat ta jingina jikinta a jikin Sardauna tana latsa wayarta tana jin muryar Juicy ta mike tare da dauko blanket da Sauri ta lullube Sardauna luf har kansa kamar wani kayan wanki wai kar Juicy ta ganshi daga shi sai short da singlet,

Mene haka?Sardauna ya tambaya ta cikin Blanket,dan dagawa tayi tare da shigar da iya kanta ciki tace ka zauna haka kai dai ina da hujja,

Sai ya daga zai fito sai ta danne Blanket din,juyowa tayi tare da kallon Juicy tace Anty Juicy zauna mana muyi hira,harara Juicy ta balla mata tare da cewa ke me yasa kullum dakikiyace me zan gani a wannan yaron?
Me kika ji nace?nace shi kika zo kallo?har tayin zama na miki Amma zaki fassara min magana,
To dama shi kika Aaaazo gani?idan ba rami me ya kawo maganar Sa?Ramlat ta furta.

Zama Juicy tayi gefen Bed tana jira Sardauna ya fito daga blanket din tayi maganarta,
Ramlat waya ta jona jikin speakers tare da kure volume din wa'azi yanda me wa'azi yake cin uban mata wanda suka nacewa boko suka ki aure Sabo da duniya,da yanda suke zinace zinace da neman mazan wasu Sabo da duniya.

Juicy sai taji kamar dasu ake Sabo da bata da rabo sai ta tashi tsam ta bar dakin Sabo da basa son gaskiya sam,
Tana fita Sardauna ya fyallar da Blanket wannan wanne shirme ne?yau fada kake ji me ya faru ne Na Mami dan Alhaji Kabiru da....kafin ta karasa Sardauna ya fara masifa karki kara hada ni da wasu can bana kaunar kara jin wannan sunan kusa dani,

Ramlat yanda taga yana masifa kamar ance ga ranar mutuwarsa,ya hakuri to mene abin fushi a nan?ai kece zaki wani ce min dansu ina ruwana dasu,ya furta cor da shagwaba, dariya Ramlat tayi kai My King,Da sauri ya kalleta yaji Ramlat tace masa My King gaskiya ya girma fa,har sunan ma daban.

Muje a kara wanke gashin nan ban yarda dashi ba,ido ta zaro tare da cewa dazu ka kaini Saloon aka kara wankewa,ae Ruwan ne ya min kadan da suka sawa kan wani dan kadan suke sawa ana wani cancana abu,
Towel ya Mika mata ta daura daga shi sai Short hannunta ya rike har cikin Toilet,wata doguwar chair ya bata ta zauna tare da Sa kanta cikin sink ta baya tana a gabansa suna facing din juna,shampoo me kamshi da kyau ya sa ya fara wanke mata,Sai dirje mata kai yake yana yawo kan nata tana kara Kadan,da zafi fa,ko kulata baiyi ba kare mata kallo yakeyi yana ta faman wankewa,Towel din din ya kusa kwancewa rabin na shanunta sun fara bayyana.

Dama kida ka kunna mana kaji,aiko Sardauna ya dauko bluetooth speaker yasa kida yana wanke mata yana takawa kamar ba gobe yana wanke mata gashi watarana har sai tsaya ya taka ya taka sannan yaci gaba,Ramlat kuwa sai dariya take yana birgeta dan ba karamin iya Rawa yayi ba,duk latest idan ta shigo ya iyata harda wacce baka taba gani ba zaka gani wajen Sardauna,

Ramlat kanta duk kumfa ya riko hannunta wai sai tayi tana dariya taki yi,
Sardauna kam yi kawai yake yana I wish Naufal yana wajen nan da kinga yanda ake rawa ya fini iyawa ma ai Naufal shegen gari ne he done Bad finish,
Ramlat kam bata iya ba kuma yace sai tayi masa.

Ramlat da towel ta dan juya kadan yace inye zaki iya gaskiya oya shake it,nan Ramlat ta dan fara haukarta domin tsalle kawai take tana daga kafada.

A toilet suka ruguntsume da rawa kida kamar zasu tashi gidan Prof,Prof wanda karasowar kenan gidan yaji sauti na tashi yayi yawa ba jin kunne,su kansu su Juicy jin

Please Login or Register in order to submit comment