Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta a gidan nan.

Sardauna yasan Ramlat maganar kirki baza ta iya fada musu ba balle har ta kai ga balla wata yama zatayi da wannan jibga jibga haka,a fili yace thts good indai suka miki ki Balla su ki zagi Ubansu ma na tsaya miki,
Ramlat tace zasu ci Ubansu kuwa tunda ka bani go ahead,
Kar ki kyale kowa cikinsu kinji.Ramlat tace hakkun...wannan a zaune take za ayi karamin yaki a gidan nan idan wata ta kawo min maganar banza

Sardauna yace yawwa tawan ki musu kaca kaca tace an gama Ranka Ya Dade Na Mami ikon Allah,yanzu ai ba na Mami bane ni,na Ramlat ne fa ya fada cikin sigar rada, tafiya sukayi har Palo yayiwa Mutan gida Sallama gaba daya matan da Ammi suka rako Sardauna har Mota,Ramlat sauri ma take ta shige gaban mota su kara Sallama Juicy ta sa mata kafa ba tare da kowa ya gani ba sai ganin Ramlat akayi a kasa,ita kanta Ramlat bata San me ya kayar da ita ba ta zata tuntube tayi,Sardauna da Sauri ya dagata yana mata sannu amma me sai ji sukayi
Ramlat tace Allah ya kara min dana fadi,babu wanda Bai dariya ba a wajen har Ammi mutum ya fadi yace Allah ya kara.

Bayan sunyi Sallama yaja mota ya tafi sabo da Bai son ganin Ramlat tana ta faman kuka abin ya isheshi.
Yana barin gidan Ramlat ta tsuguna a wajen tana ta kuka,Juicy tazo ta make mata baki rufe mana baki shegiya gwara ma ki tashi domin yau ke zaki mana girkin rana,
Ichichy me dan ragowar imani tace haba ki kyaleta yau daya dai,Chuchu tace bata isa ba sai tayi annamimiya tare da tallafe mata keya,

Ramlat taji haushi ba kadan ba tace In Allah ya yarda sai kun koma gyada me bawo kuma Allah ya isa ubanku kato me karamin kai ta kwashe da gudun tsiya tayi cikin room dinta, Prof Katon shirgege ne ga tsayi ga kiba Amma kansa dan mitsitsi ne kuma bashi da wuya kansa hade da wuyan Allah me halitta,
kafin Ramlat ta shige Merry ta cafko ta,Ammi tace kyaleta taci darajar Mami amma zata ci ubanta kyaleta.

Ramlat tayi mukus tare da cewa a bani aikin da zanyi to,Ammi tace tafi ki dafa abinda ya dace Sumi Sumi ta shige kitchen tana tsoro,sai da ta gama shirya abinci lafiyayyu ta jere a dining ta koma dakinta tayi wanka tare da fitowa zata ebi abincin Amma su Lilla sukace bata isa ba,Ramlat tace na dafa abin a hanani dan kaina na tsaya na muku girkin nan dan naci naji dadi idan nayi mugunta nasan har kaina zanwa tun cikin arziki Ku bani naci Sabo da kaina na dafa girkin da kaji Sabo da ni ma'abiciyar kaji ce,daga Kaza har kwanta dadi garesu.

Ammi ce ta kwasheta da Mari sai ga Prof ya shigo yana Bala'i dan me za a hana mutum ya fadi ra'ayinsa kamar ba masu ilmi ba bayan Human Right ya ba da dama ka fadi abinda kake so,
Ramlat ganin Prof taje ta ebi abincinta tace wai ni na dafa zasu hanani ci bayan kai kake kawo abincin,kuma tsaro da doka ya ba da dama ko? Prof yace yarinya kinyi gaskiya Ashe kina da Ilmi ko waye ya miki kina da ikon yi masa komai ki fadi komai kina da yanci dokar kasa ta baki Right na ki fada.

Allah kara arziki Papa tayi cikin dakinta,Ammi tace Ku bar shegiya yau sai tayi Aman Abin da taci,
Saida Ramlat taci ta koshi tayi nak sannan tayi sallah ta maida plates kitchen ta dawo tare da ebo littatafai ta fara karatunta amma kuma sai tunanin Sardauna takeyi ta kasa hakuri da rashinsa tayi missing nasa,

Fadeela ta kira a waya suka Sha hira sabo da Fadeela tana kaunar Ramlat sosai haka kawai Allah ya hada jininsu,
Suna gama waya ta kira Sardauna Ring daya ya daga yana picking ko a Bai ce ba Ramlat ta saki kuka wai har ta gaji da karatu ita baza ta iya ba books sunyi yawa bata ganewa.
Sardauna yana driving yace me zan miki yanzu driving nakeyi fa ki Bari zan kiraki idan na je gida, ni bazan yarda ba sai kace wani abu cewar Ramlat,Sardauna yace ok accident kike so nayi na mutu kwana na Bai kareba?ko 27yrs ban kai ba na mutu ai kuma shike nan na rako Maza duniya,ban dandani dadin duniya ba ko auren banji me ake ji ba,

Ramlat taji mutuwa tana turo baki da shagwaba tace to Allah kaika lfy idan kaje ka tabbatar ka kirani,to Mami cewar Sardauna.
Tana kashe wayar ta kira Mami sukayi hira,ta kira Abu yayar Idrisa,Abu ta daga tana magana da karfi kamar tanayi da duniyar nan gaba daya ta cika gidan har waje ana jiyo muryarta ta kashewa Ramlat dodon kannenta da magana da karfi tana

Iyeeeeee....Ramlatu.....na'ammmmm......me kikaceeee.....iyeeeeee......ice ko dai lafiya kuke....Ina mijin naki Ramlatu...kuna zaune lafiya...Ina wajen su kakar taku na'am....Ramlatu....eyeeee....Ramlat tace duk lafiya tana dariyar kauyancin Abu,
Abu taci gaba Idrisa fa ya fado daga saman bishiya ya karye....Ramlat tace yaushe?garin ya?Abu tace shaye shaye yayi ya tafi tare da danewa bishiyar kofar gidansu ya kuwa tiko a kasa ya karye a hannu,an kaishi dori amma da sauki,

Ramlat tace kai Kawu bazai canja ba Allah kiyaye gaba, Ramlat takaicinta ba dama tayi waya da dangin ubanta sai taji wasu mummu nan labarai iri iri shi yasa bata kiransu Sam.
Abu taci gaba Ramlatu....Hafsatu ta hada kayanta tana can wai a Lokoja tana can gidan Abokin Babanku ya bata kudin mota yaci ubanta yace ta taho gida amma sabo da Hafsatu ba yar Albarka bace yanzu tana can wai a Makurdi can kudu gidan kawarta wata bayerabiya,lalacewar Hafsatu tayi yawa,
Ramlat tace Allah kiyaye gaba bari na kira Baba Talatu naji.
Iyeeeeee......eh....ki kirata to Ku gaisa yanzu bari na hadaki da A'i gata nan ma
A'i ta fara da sauri da sauri sabo da tana da Saurin baki Salama'alaikum Ramlatu.....Ramlatu.....kuna lfy..ya mutan gidan...duk Lfy cewar Ramlat, ina me gidan?to a zauna lfy do Allah do Annabi a zauna lfy kinji Ramlatu yi nayi bari na bari...ki zauna a dakinki kinji,abi Allah abi Annabi Muhammadu,Ramlat tace to Baba A'i.
A'i tace to to Alhmdllh mun goda Allah mun yabi Annabi a kula a rike Amana banda Almubazzaranci karki ga mijinki me kudi ne kije kina barna ana zubar da shinkafa kaji suci awaki suci mage da bera ma duk su ci a kiyaye saka yaji a abincin me gida,Abu tace gaya mata domin Ramlatu akwai cin yaji yanda take zankadashi a shinkafa ba a magana,i dan tazo cin abinci wajena sai na kwace yajina karar dashi take gaba daya,

Ramlat ta matsu su gama surutun zasu karar mata da kudin kiran Sardauna su Baza su iya kira ba sai ka kira suyi ta faman hada ka da mutane ana ta surutu da fadan Banza.
A'i tace ga su Ladiyo ma sunce a gaisheki,Ramlat tace ina amsawa sai Anjima,A'i tace dakata Ramlatu ga Alhajiji ya shigo ku gaisa,nan ma Alhajiji yayi ta surutu,zata kashe sai ji tayi wata tace Ramlatu nice Hasifa ...Hasifa ce me Kuli kin ganeni? Nan ma Hasifa tayi nata,tace ga Kululu,aka gama da Kululu,ta bawa Ando me fanke, aka mikawa Ummilolo,Antyyoyo ta amshe itama,Gwadabiya ta karba,Aminan Torotso.Ramlat na gajiya ta kashe wayarta kit.

Su kuwa suka fara Allah Sarki Ramlatu ana can itakam taci gaba wata budurwa me suna Lantan tace Allah samu a danhinta muma mu hige daula ko ma kwahi garabasa.

Ramlat kuwa Talatu ta kira suka gaisa sosai yayin da Talatu (Baba ta birni) ta kawo wani mumman labarin cewar Shaheed Kanin Ramlat Ya dauki wuka yayi wa kansa kaciya ba kowa a gidan yana wasa,Ramlat harda kuka,Talatu tace yanzu Shaheed yana wajenta an kaishi asibiti an karasa masa kaciyar komai ya saitu.
Sannan tace Daddy ma kaninta ya yanke yatsansa da wani karfen langa langa saura kadan yatsansa ya cire yana nan yasha dinki kamar kwarya.

Bayan Ramlat ta gama wayar sai ta kama Kukan tausayin yan uwanta saida taci kuka ta koshi ta kwanta tasha baccinta lfy shar.
Ammi kuwa ta hana a zafafawa Ramlat Sabo da tayi tunani kar ta fadawa Mami da Sardauna su dauketa burinsu bazai cika ba,amma duk da haka zata ci ubanta.









AsmaBaffa
🏀🏀🏀🏀🏀🏀
🏀🏀🏀🏀🏀🏀


DUK INDA TA FADI



121-125



Official







BY
AsmaBaffa






Mardy Bounce
Mum Ifteeee
Wannnan shafin nakune ku kadai na baku shi sai yanda kuka ga dama.🤣







Ramlat kuwa baccinta ta kwasa me dadi sannan ta tashi tayi Sallar La'asar yau ko Islamiyar Sunday wai Baza taje ba zaman makoki takeyi na tafiyar Sardauna gida.
Har dare ko palo bata leko ba tana ta faman kunci da bacin rai ta matsu Sardauna yaje gida suyi waya, Qur'ani ta dauka tana karantawa tare da Yiwa Sardauna addua Allah kai shi gida lfy domin tunda ya ambaci hatsari gabanta ya fadi.

Babu wanda ya nemi Ramlat a gidan kowa harkar gabansa yake sun manta ma da ita,har dare Ramlat an rike charbi ana ta faman ja tare da zabgawa Sardauna addua,
Har bayan Isha yunwa ta dameta ta fito har kitchen,ashe darajar Sardauna take ci domin su Ammi basu damu da girkin dare ba kowa abinda yake so zai dafa yaci yayi gaba,

Ramlat taga ba komai har room din Ammi taje tare da gaisheta cikin Ladabi duk yan matan suna kwance a kusa da Ammi,Lilla ta dakawa Ramlat tsawa lfy? Ramlat tace dama na...na...uhm...na....duba ba abinci,Dalla bace mana da gani mayya cewar Merry,
Chuchu tace sai dai kici hanjin cikinki.
Fitowa Ramlat tayi tare da Zura Katon Hijab kaji matan aure fa,
Waje ta fita ta siyo doya da kwai a wani shago da akeyi da zafinta kusa da gidan Prof,

Tana dawowa fridge ta bude tare da daukan Holandia da ruwa tayi dakinta,ta baje a kasa ta fara ci kenan Sardauna ya kirata a waya,lokacin yayi wanka da komai tare da shirin bacci,

Ramlat ana cin
doya da kwai ga yajinta a gefe tana dangwala bata daga wayar da wuri ba saida ta kusa tsinkewa,Sardauna kuma ya dauka yanga takeyi ko fushi takeyi da shi,
sallama tayi bakinta cike da Doya a ciki kana ji kasan abu take ci,
Ya Sardaunan Mami barka da dare kaje gida lfy? Sardauna a ransa yace yau masu hankalin ne a kanta,a fili can kasa da Murya yace lfy,ya kike?Ba lfy ba,why? Tana so tace masa sabo da baya kusa ne tayi missing dinsa but halin Sardauna ta tuna watarana a kwai rainin hankali shi yasa tace gidan ba dadi fa kawai,
Sai hakuri ai kinji ,me kakeyi yanzu am chilling just
Relaxing Baby ya fada kamar Bature.
Haushi Ramlat taji ya manta ma da ita baiyi missing nata ba, muryarsa ce ta katseta Me kike cine? Ramlat tace au na manta na fada ma na fita waje jikin gidan na siyo Yam and egg ba abinci a gidan wai kowa girki yakeyi da dare ba kullum suke girkin dare ba,shine baza ki fada min ba tun kafin kije sai yanzu?ba sai kije ki dafa ba kema akitchen din.

Marairaicewa tayi kaifa kace kana driving sai kaje gida zaka nemeni sabo da accident kuma yanzu zaka ce ba haka ba.
Ai ya kamata yayi ki fada min first ko? Kace ba Skipping meal kasan ma bazan iya Zama da yunwa ba dole na nemi abinci,idan na bari dare zai yi ban nemi abinci ba,

Kwanciya ya gyara alright it's ok ba matsala, dan Sanmin ko tayi babu?bude bakin na sama kaji kamshinta ko baka ji dadi ba na fada ma daga kazar har kwanta dadi garesu,
Uhmmmmm..... Sardauna yaja numfashi kamar da gaske ya ci tare da cewa gaskiya da akwai dadi wannan me doyar ya iya,Ramlat farin ciki ya kamata tana zuba murmushi bata San sanda tace missed u dear, Sardauna yace missed u much more Baby,muyi video call,dama ya bude mata Skype ta nan ya kirata sai ga Sardauna ya bayyana daga shi sai boxers a saman bed ya kwanta dai dai,
Ramlat da hijab a jikinta cike murna yace a haka kika fita siyo abincin?yea cewar Ramlat tana fari da ido,Sardauna ya daga mata babban yatsa daya tare da kashe mata Ido daya yace da kyau My Precious ana yi ana daraja martarbar auren nan domin rainonsa nakeyi,
Kamar jariri?Ramlat ta tambaya yace sured,
Da hannu ya nuna mata wai ta cire Hijab, kunya fa nakeji,Hararar Wasa ya watsa mata will u pls? a hankali tana sunkuyar da kai ta cire wata yar rigar baccinta Red ta bayyana me hannun bra iya rabin cinya,Sardauna ya wani lashi pink lips dinsa na kasa a hankali tare da dage mata gira daya,
Dariya Ramlat tayi tace kamar micijiji wannan zaro tongue haka

Suna Hira har ta gama cin abarta ta kwashe kayan ta fita palon tare da daga wayar sama tana ta faman yiwa Sardauna murmushi yana Up..up....tana daga wayar tana tafiya tare da cewa kana gani? Yap cewar gogan,Haka Ramlat ta wuce Ammi da matan gidan a Palo suna kallo,hira ta dauke mata hankali bata ma San da mutane a palon ba ta wuce ta dawo wayar a sama tana ta shagwaba ta kara wucesu abinta ta shige daki suna ta video call dinsu,

Tabe baki sukayi Juicy tace yarinyar nan yar iska ce ta gaske a haka in ka ganta baza kace idan an sa mata yatsa zata cija ba,
Ramlat kuwa shiga toilet tayi tare da yin Brush tana fitowa ta kwanta Saman Bed,still Sardauna na kallonta a Skype call, kinyi karatu kuwa? Eh nayi sosai dazu har na Islamiyya ma.ok ki dage kinga da dai abinda ya kaiki ba wasa kar kiyi asarar lokaci da kudin schl kiyi abinda ya kaiki kinji?

A nutse tace Insha'allah, yaushe zaka zo ka ganni?Murmushi Sardauna ya saki yau ya tafi amma tana wai yaushe zai dawo,yasan rigimarta sai kawai yace soon zaki ganni surprise zan miki,
Dadi ya kamata tace ina dan bed dina? Allah sarki dakina nayi missing dinsa,dan mirrow na,ina akwatuna na?dasu yan Sip dina hope dai normal suke? Dariya ta bawa Sardauna sosai yace ai suna nan neat har sunfi da kyau,Ramlat tace wayyo dan gado na har na tuna sanda nake daneshi inyi ta bacci na.
Dariyar Kuruciyar Ramlat yakeyi sosai shi yasa yake missing nata da yawa,

Ramlat tace yau na kira yan uwan Kawu kaji wai Kawu ya fado daga bishiya harda ballewa,Sardauna yayi kalar Sad yace eyya banji dadi ba Allah bashi lfy,Ramlat tace ai an dorashi wai yaji sauki ma,Allah kara Lfy da ina nan sai na kaiki ko? Ramlat tace naji tausayin Kawu Allah Sarki dama shi ba kiba ba .
Shaheed ma wai yayiwa kansa Kaciya, Sardauna yace ban gane ba nan Ramlat ta bashi labarin harda Daddy kaninta da ya kusa cirewa kansa yatsa harda hawayen tausayi,
Shima Sardauna baiji dadi ba,yana matukar tausayawa yaran Amma ko Ya daukosu Idrisa sai ya kwace abinsa bazai bawa kowa ba,babu yanda zasuyi.

Haka ya dinga lallashinta har ta dawo normal,
Sardauna dai zaiyi bacci kuma yana son kallon Boobs din Ramlat yaji dadinsa yasan Baza ta taba nuna masa ba sanda yake kalla ma bata sani ba bacci take kwasa sai ya bude ya gani.
A ransa dai yace bari ya gwada sa'arsa a hankali kamar me Rada yace ki cire rigar nan batayi kyau ba ki canja farar nan,
Ramlat tace ai naga kamar tafi min kyau fa,kuma duk kai ka siyo su da kanka,
No naga tamin kalar kauye yanzu ban san haka take ba da Bazan siyota ba,canja wata,Ni dai ina sonta dan Allah,ke halina dake bakya Jin magana a haka zaki Zama yar wanka?ya furta yana fushi,

Ramlat tace to shike nan bari na cire dan bani 2 mnt kaji, kinji halinki ko ki dauko ki sa a gabana ina kallo,Ramlat tace to ta dauro zaninta ta dauko Riga da niyyar ta sa a saman zanin sai ta zare zaninta shike nan,

Sardauna yace Bana hanaki daura kirji ba?ok bari na daura towel mantawa nayi,har Towel ba a daurawa sai anyi wanka,ki tube Riga ina gani kisa dayar.
Ramlat tace naki haka kawai ka kalleni ba kaya
Tunani Sardauna yayi zata rainashi fa kuma ma ai sai ya kai 27yrs sai yace ke wasa fa nake miki ke wai komai baki San wasa ba,maida rigar tafi kowacce kyau fa,dama gwadaki nayi na gani ko baki San kyau ba,
Ramlat ta saki murmushi har da tana tunanin Sardauna fa dan duniya ne Ashe ba haka yake ba kamili ne gaskiya tayi dace.tana tunanin karyar da yan Company na Citta suka mata

Makaryata yan gidan Citta su Firdausi suke cewa idan akayi aure ana wani abu me Zafi to mene gashi tayi ba ayi komai me Zafi ba sai dadinta ma da take ci.
Sun Dade suna waya da Sardauna sannan bacci ya kwashe su har wayar ta katse da kanta,

Monday Ramlat 9am take da lecture da wuri ta gama shiri yau ma Hijab ta zumbula ita ga me aure,
Tana zuwa kowa yayi mamakin ganinta ita kadai yau harda hijab kuma duk da cewa tana suturta jikinta amma bata sa Hijab Sam,yau gata tazo a napep.

Fadeela tace Hajiya yau kece a matar Liman?,ina bro dinki?Murmushi Ramlat tayi tare da cewa bro ko Husband?bakwa ganewa bro na ne zai zauna yana min haka?
Fadeela cike da mamaki tace miji Ramlat kika auri yaro haka me tashe da ji da kuruciya,me zai miki idan ba shirme ba,basu san darajar mata ba,suna ganinsu yara yanzu suke tasowa mata zasu sosu bare Sardaunan naki yanda yake ji da kansa ga kyau kuma yana da kudinsa.

Ramlat tace kune kuke yiwa maza kudin goro gani kukeyi kowa haka yake ai kowa da halinsa ba lallai bane idan wannan yana da Hali marar kyau kace wannan ma haka yake,
Fadeela tace tab aini wlh bazan iya auren irinsu ba sai manyan maza wanda suka mallaki hankalinsu,suka San mutuncin mace da aure,ni mijina babban mutum ne nice ta biyu a wajensa,gidana daban ya Gina min 3mnths kenan da aure na da shi muna zaman mu lfy,ga hakuri da juriya bazai ma tsaya har kuyi fada ba busy ma kadai ya isheshi kullum sabo da aikinsa da business ba Hutu shi yasa nake shanawata.

Takaici ya rufe Ramlat wato Sardauna ne bai San mutuncin mace da aure ba,kuma Bai da hankali kenan,
Da masifa tacewa Fadeela Malama sauraramin baki ji ba ko a sunan ba daya bane ke F ce ni R ko hanya bamu hada ba,
Mijin nawa zaki fadawa magana ke in kina da mutunci har kin isa ki fadawa Sardauna haka,wato na wani banza naki dukiya kin yabi mijinki kina zagin nawa ko? wai busy ma kadai ya isheshi Ashe shine Bai San darajar aure ba tunda busy yake baya baki kulawa baya nuna miki love kullum ana aiki ke kuma doluwa gani kike shine Jin dadi da shanawa ko,

Kwaikwayar maganar Fadeela ta fara busy ma kadai ya isheshi shanawata nake yanyanyanyan
darajata kika ci har in kika gaisar da Mohd yake amsawa domin baki da yanci da darajar da zai kalleki,kinyi masa dirty wlh,
Ki kalli tsabar Idona ki zagi mijina uban wanda ya mallaki hankalinsa aikin banza aikin wofi,kamar Sardauna baza ki taba samun irinsa ba,dan kin samu ana kulaki,
Banza a banza man kare,me kama da barewa in Allah ya yarda sai kin zama dakikiyar the whole department din mu,sai kin fadi a Course din Malam Salisu,baza ki taba cin test din Malam Isma'il ba,

Fadeela kanta Masifar Ramlat ta bata dariya daga fadar Ra'ayinta akan Maza har ta juya maganar ta zama fada haka, gaskiya Fadeela kinyi laifi domin kin Zagar mata miji karki wayance cewar wata Fa'iza yar class dinsu da take jinsu tana dariya.

Fadeela tace yi hakuri Matar Sardauna ba da fada na fada ba Ra'ayina na fada miki,
Rufe min baki,maida Karuwa yar Iska kinji ko an fada miki banda hankali ki zauna kici min fuska kice ra'ayinki? Kiyi hakuri to dan Allah,Allah ya barku tare da Mijinki kyakyawa cewar Fadeela, Ameen Ameen kuma ki daina yabon mijina ehe a kyaleni na yabi abina Ramlat ta furta tana jijjigar masifa,

Da kyar Fadeela ta shawo kan Ramlat tayi shuru ta hakura Amma tace wlh kamar a kunnen Sardauna kinci dunduniyarsa ashe bakya kaunarsa nan muke zama dake kina shanye mana lemo da ruwa idan na siyo alawar Madarata ko ya kawo min take away na chips mu cinye dake tas amma kinzo kina zaginsa baya nan to sai na fada masa musan irin zaman da zamuyi dake chicken idan zai siyo biyu yake Siyo mana Ashe bakya kaunarsa.

Fadeela dole take danne dariyarta Sabo da ta girmi Ramlat da wurin 5yrs haka ta lallabata dai Amma Ramlat da an danyi mintuna zata kalli Fadeela gaskiya kin ci min mutunci tunda nake a duniya ba a taba min cin fuska mafi muni irin naki ba,idan na kyaleki Fadeela Allah bazai barni ba,
Wani sa'in kuma tace ke sai na kai kararki hukumar makaranta an bi min hakkina na zagin mijina dan Uwana Ranshi ya dade ya Sardaunan Mami bani da kamarsa.

Fadeela tace wai me yake miki kina sonsa da yawa Ramlat,Ramlat tace ba so bane Baza ki gane ba Wato Mohd mtsww karshe ne,ba abinda Bai min ba,haba Fadeela in badan ke bace ai da yau hmmm ni kadai nasan irin abinda zan miki,ki godewa Allah kece kawai amma ki kiyaye harshenki,amma da ace naga dama sai na sace miki tayoyin mota.

Ta Sardauna Dan bani labarinsa naji da Alama ya gama cusa miki sonsa ko?Ramlat tace harma sai ya cusa min sonsa,Sardauna baya bukatar Cusa So

Please Login or Register in order to submit comment