Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Matarsa tasan komai ya fada mata,tace sam 20k sunyi yawa a kawai lesson Weekend 2days malaman schl ma ya ake basu bare wani lesson idan zatayi a 7k tayi idan baza tayi a hakan ba ta bar musu gida.

Ramlat tace zata yi hakan,shi kuwa Alhaji yana kaunar Ramlat Sabo da shi bashi da Ilmin boko idan yaga wanda yayi karatun boko sai kawai yaji mutum yana birgeshi.
Bare wai yaji Ramlat har America taje Sabo da boko,masters da Degree.
Mustapha ne ya zuga Hajiyansu kar ta sake Alhaji ya dauki Ramlat aikin lesson zai iya aurenta ya mata kishiya, Mustapha kishi yake kar Alhaji yaso Ramlat saboda bata dace da tsoho ba da shi ta dace,kuma tunaninsa Alhaji fa ya kyasa Ramlat wanda sam zuciyar Alhaji ba haka bane, tunaninsu ma Ramlat bata da aure zata aure musu Uba ko ta dinga cinye musu kudin Sa.

Rana ta biyu Ramlat taje lesson Hajiya ta koreta ba duka ba zagi tace kar ta kara zuwa Alhaji ya fasa ga dubu biyu kudin zuwan yau dana jiya,Alhaji bai san Hajiya tayi hakan ba
Ramlat ta karba cike da takaici ta tafi gida ta fadawa Mami da Sardauna,
Sardauna yace ke kika jawowa kanki Ramlat kiyi zaman ki da wannan siyar dasu Maggi etc yafi mana,kinga yau kwana 2 ina fita harkar Taxi nan,motata me tsada ce kowa gudunta yakeyi idan yaga Taxi wai me kyau haka,kuma duk da an mata paint na Taxi basa yarda su hau tsoro sukeyi za a sace su.

Ramlat tace kuma gashi sun ganka me kyau kalar me kudi ai dole suki yarda su hau motar dan gayu Allah kyauta,zo muje mu siyo Salat cewar Ramlat.
Hijab tasa suka fita tare da Mijinta hannunta cikin nasa abin sha'awa,sai kallonsu akeyi suna birge mutane,
Suka je gaban me kayan miya Sardauna ya siyo Salat na Hamsim da tumatur suka dawo gida suna ta hirarsu cikin nishadi da kaunar juna.
Tare suka shiga kitchen Ramlat ta dafa musu wake da shinkafa mai da yaji, Sardauna yana cikin yanka Salat wukar ta goce tare da yanka masa yatsa kadan,shiiii yaja tare da jefar da wukar,da Sauri Ramlat ta rike yatsansa kamar itace ta yanke haka idonta ya ciko da kwalla ganin jinin Sardauna na diga.

Murmushinsa me tsada ya sakar mata tare da cewa mene abin Kukan to? a tap ta Sa yatsansa ta wanke tare da daure masa da kyalle,tana yi yana kallonta yana murmushi har ta gama,Daukan wukar yayi da niyyar ci gaba,da Sauri Ramlat ta kwace bani zan karasa bana son ka kara yankewa,nama gama aikin muje palo,hannunsa ta rike tashi ta furta tare da turashi Palo ta juya baya tana me ci gaba da aikinta,tsam taji Hannayen Sardauna ya rungumota ta baya yana goga fuskarsa a wuyanta tare da cusa kansa cikin kirjinta yana sinsinar kamshinta Sabo da Ramlat kullum cikin kamshi take duk da ba wasu masu tsada bane bata bari ta zauna ba kamshi ko na Humra ne Sabo da Sardauna me matukar son Tsabta da kamshine shi yasa ta kara dagewa sosai.

Yana jikinta ta gama aikinta kaf tana a jikinsa still ya kwantar da kansa saman kafadarta tare da daukar mata flask daya, ta dauki Bowl din Salat itama suka fito Mami tana palo ko kunyar Mami Sardauna baiji ba,Ramlat can kasa take masa magana Mami na kallonmu fa,
Da karfi yace Mami kinji wai kina kallonmu,ai kai ba kunyata kakeji ba Muhammadu ka rainani cewar Mami, Dariya yayi kuma bai sake Ramlat ba haka suka jera komai Mami ta karaso wajen zata ebi abinci ta zubawa Sardauna Duka a kafada marar kunyar banza,Dariya ya saki tare da hadewa da Mami da Ramlat ya rungumosu duka tare da cewa shike nan ki daina kishi kema na miki.

Mami ta fisge jikinta tana murmushi Muhammadu baka da kunya,matsa ni ku bani waje nan ta ebi abincinta ta koma dakinta ta Barsu nan.

Yau Sardauna shi ya bawa Ramlat abinci da kansa taci ta koshi sannan ya dauketa cak har toilet ya sakar musu shower ta sama wanka yayiwa Ramlat shima tayi masa Amma yaki bari su fito kuma bai kashe Shower ba yatsansa yasa tare da dago habarta ya hade bakinsu a hankali yana tsotsa kamar yaro na shan Alawa, hannayensa bisa boobs dinta yana mata wasu Salo masu haukata duk wacce ake wa,
Ramlat ta fita daga hayyacinta bata San sanda ta rungumeshi ba kam a jikinta tare da goga kirjinta a jikinsa hannayenta na can kan ta cikin Wando tana masa zafafan salonta, daukanta yayi cak tare da kashe Shower din, saman Bed kawai suka fada abubuwa masu zafi kamar zasu cinye juna haka suke aikatawa kansu,
Blanket ya rufa musu nan Sardauna ya fara babban aikinsa Ramlat sai Kukan Dadi takeyi kamar zata mutu Sabo da dadin ya mata yawa.
Mohd kuwa ya fita ma domin Ba kalar Gurnanin da Kukan da bayayi, Surutai da sambatu iri iri yakewa Ramlat wanda ita kanta bata gane me yake cewa Sabo da bata cikin hayyacinta.

Lantan yan Mata Sa'adat ake ce mata yanzu tayi wani gogewa ta kara wayewa,yau kuma Babban Sojan wanda ya dauki Nauyin Karatun Lantan takanas yaje kauyensu a Jigawa zai dauki Lantan zasu koma Abuja ayi mata komai da Komai na makaranta gashi Lantan Sa'adat bata gida an tafi neman miji dan gayu.
Allah yasa Iyayen Sa'adat suna da Number wayar Lantan nan take suka bawa sojan nan ya Kira Sa'adat.
Lokacin Lantan taci kwalliya da yamma ta shiga wani kerarran Hotel na manyan masu kudi,wasu ta saman benen su da suke tsayawa su fito hutawa ta corido masu kudi sai kallon Lantan sukeyi,
Wasu masu shigowa da motoci ma haka,da kuma wanda suke zirga zirga a hotel din jefi jefi.

Sa'adat wata yanga takeyi ta shige cikin Hotel inda ake kama Room alhalin bata da ko sisi sai kudin Napep,
Tana zuwa wasu su hudu duk Maza sunzo suma suna kama daki,mutumin ba bahaushe bane Amma yana jin hausa,da turanci ya tambayi Lantan daki zata kama?
Lantan ta watsa masa harara dalla Malam bama son iyayi azo garinmu a koyi Hausa azo ana mana iyayin turanci idan zakayi Hausa kayi mallam,
Shi kuma ma'aikaci yana son customer yace sorry Madam,Lantan dama a wajen gogaggun kawayenta taji watarana idan suna magana zasu ce is Better for u,Sai da Lantan ta dage ta haddace words,d a kayi magana zata ce Is Better for u duk da tasan ma'anar su ta koya,Lantan Allah ya zuba mata basira,wayo,hazaka da saurin fahimtar abu.

Kallon Ma'aikacin tayi tare da cewa Is Better for u,tana yatsina fuska,Mutanen sunyi tunanin dama Lantan ta iya Turanci gata yar gayu kuma.
Lantan tace nawa ne daki daya?Mutumin yana washe baki yace dubu talatin kwana daya,
tsaki Lantan taja tare da cewa talatin kacal Yaushe Daddyna zai barni a dakin dubu talatin yayi araha da yawa,mutumin yace Hajiya yana da kyau fa sosai,Lantan tace idan kana so na yarda muje naga kalar dakunan,
Ba musu mutumin yasa wani Ma'aikacin ya nuna mata kalar dakunan ba shakka ko yar Gomna ce sai ta zauna ciki.

Upstairs suka kai Lantan tare da bude mata daki daya wani sanyin Ni'ima da kamshi ya bigeta,ciki ta shiga tare da fadawa saman Bed din kamar ta biya,Mutumin ya fara masifa ya bata biya kudi ba zata fada musu bed bayan an gyara komai,mike kafafu Lantan tayi kamar dakin Uwarta,ko ki tashi ko na kira miki security wlh su fitar dake,Ko kallonsa Lantan batayi ba,ma'aikacin ya Tsorata kar ya mata rashin mutunci ko yar wani hamshaki ce gwara ya lallabata,

Cikin lallami ya fara bata baki kan ta fito Amma Lantan saida ta huta na minti 10 sannan tace gaskiya ku canja katifa babu Laushi,ac kuma ba karfi wlh Bazan iya ko yini cikin wannan watsatsen dakin ba,ta fito waje mutumin da Sauri ya gyara bed din ya fito tare da Sa key, wajen da ake kama daki suka dawo,mutumin yace daga cewa ka nuna mata sai ku dade haka,Lantan tace Bazan taba iya kwana a Cikin nan ba malam sai anjima,mutanen da suke wajen haushi Lantan ta basu sai bata musu lokaci takeyi.

Mutumin yace Thank u Madam ta wuce tana yanga,a compound din Hotel din Wani ya dagowa Lantan Hannu ta saman Room dinsa,Lantan ta ganshi wani rusheshe me Katon tumbi,sai ta daga kai sama tace me tumbiiii? Mutumin yayi dariya yana mata nuni ta tsaya,Lantan ta make kafada tare da cewa Allah kiyaye tayi masa gwalo,shi kuwa ya kama dariya yace mata u funny Baby,Lantan bata san me yace ba tunaninta ko zaginta yayi ta murguda masa baki,
Sai tace an bar Hauwa a gida anzo kwana a Hotel,Mutumin sunan matarsa Hauwa dama,sai kawai ya firgita ya zata Lantan tasan Matarsa,
Yace wlh Business ne ya kawoni nima ba komai nayi ba,Lantan tace uhm kaji karya Allah Sarki Hauwa,mutumin ya tsure ta saman benen yace dan Allah kiyi hakuri ki rufa min asiri, Lantan ta sheke da dariya tare da cewa Allah zaka roka Amma watarana Sai matarka Hauwa ta kamaka. Mutumin Ya dafe kai gumi ya fara keto masa yace ke yan mata ni ma wlh tsautsayine dan Allah ki rufe bakinki yaune kadai nazo da wata.

Lantan tana daga kasa tace Allah yana ganinka sai ya sakawa Hauwa ko Laure,ko Amina wa ya sani ko sunanta Sadiya ma.
Ajiyar zuciya mutumin ya saki jin ashe bata san Hauwa matar Sa ba ashe kawai fada tayi,Lantan zatayi magana kenan yar wayar ta tayi kara,bakuwar Number ta gani ta daga,sai taji muryar wani na cewa Lallai gobe tazo gida zata tafi birnin Tarayya Abuja karatu,z ai bar mata kudin mota wajen iyayenta,Soja ne me daukan Nauyin Karatunta.
Lantan Murna sosai zata koma yar birnin gaske,Mutumin dake saman Bene ya kara kiran Lantan Baby?
Sa'adat tace nafi karfinka malam sai mazajen Abuja, ta juya tare da Barin Hotel din sai gida,a ranar ta hada kayanta tas,Magriba tayi Amma tace wlh gida zata tafi kuma sai Kanwar Mamanta ta bata kudin mota,ba yanda ta iya haka ta bata, Lantan ba tsoro tsakanin kauyensu da Cikin Jigawa 30mnt nan da nan sai gata ta sauka a kauyen,
Soja da Securities zasu tafi kenan sai ga Lantan babu bata lokaci tace ina wununku?gani mu tafi, har iyayen Lantan sunyi mamakin ganin har Lantan tazo gida ga wani wayewa da tayi,Babar Lantan tace ko damuwa bakiyi da mu ba ke kawai ki tafi birni?Lantan tace ina sonku mana yo Amma fisabilillahi ga inda duniya take can zan dinga zuwa hutu mun tafi kuyi mana addua.
Kallon Sojan tayi tare da cewa Soja marmari daga nesa Allah taimaki Sojoji Mazaje,Soja dai muzurai yake ba kwayar Rahma a fuskarsu,Lantan tace to ku muje Sojan wata tsawa da ya dakawa Lantan ta kusa suma duk rashin tsoranta,sai da yaga ta nutsu yace shiga mota ko kiyi tsallan kwado yanzu,ba shiri ta shige ciki tayi luf,suka tafi tana dagawa iyayenta hannu,Lantan a gidan Sojoji kuma barikin Sojoji,schls da komai duk a Cikin barikin Sojoji suke.

Idrisa da Hafsatu sun dukufa da Yiwa Ramlat da surukinsu addua sosai tare da neman Fahat.Hafsatu tana girki a kitchen Idrisa yana dauke da Salma yana mata wasa suna ta faman tattaunawa akan matsalar Sardauna da iyayensa,su Idrisa anyi hankali domin yanzu taba kawai yake sha itama sama sama.






AsmaBaffa
[10/7, 1:54 PM] 0mmr Farouk: πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€


DUK INDA TA FADI




2Pages






221-225 226-230






Official




By
AsmaBaffa





Ayi min Afwa na rashin jina kwana biyu da bakuyi ba,lfy lau nake,na dan shiga Busy ne.





Dafta Jibrila na Hajara yanzu kam sai nisa yake wajen Koyon turanci,har ya samu ya zana Jamb abinsa kuma Alhmdllh yaci Jamb, neman makaranta yakeyi cikin ikon Allah ya samu community health yake karantawa a health tecnology Makarfi ta Kaduna State ba nisa da Zaria.
Iyayin Dafta ya karu Amma yana wayewa yana rage karya sosai sai daΓ­ Turanci baya daina yi,
Hajara budurwa Dafta kuwa tun tana ganin Dafta gara dan kauye tunaninta ba sonshi take ba dariya yake bata,sai gashi yanzu ta gano son Dafta Jibrila yayi mata mugun kamu,har tana cewa ya turo manya,murna wajen Jubrila ba a magana,yanzu ya hana a ce masa Jibrila sai Doctor Jibril ba Dafta ba,idan yaje kauyen har tsoho ko tsohuwa basu Isa ba idan baza su ce Doctor ba to suce Jibril.
Tuni kuma ya sanarwa iyayensa cewar a nemo masa auren Hajara ta Zaria sunce a tura.

Chuchu fa sun gama gigicewa tabbas Prof da gaske yake Sadaka zai aurar dasu wajen wasu da basu sansu ba,abin takaicin Mazajen samarin nasu duk sunji zancen aure sun gudu babu wanda ya tsaya..Abin ya ishesu sun hakura sun bawa prof zabi ya aura musu ko waye,
Ammi tace sam Prof bai Isa ya wulakanta mata Yara ba,ya bari zasu samu samarinsu,Prof kuma yayi rantsuwa bazai hakura ba lamarin da ya kawo sabani tsakanin Prof da Ammi,ko magana basa Yiwa juna Ammi gaba takeyi da Prof sosai ba mutunci.

Alhmdllh Ramlat duk kayan da take siyarwa ana zuwa siya har gida sosai take ciniki suna samun na cefane a Cikin ribar har ake tara wasu a asusu kato,
Sardauna kuwa har ya gaji da fita da Taxi dinsa sam baya samu a shiga sai jefi jefi ba riba sai asarar man mota,kamar kullum ya dawo gida rai a bace Sabo da bakin ciki ace kamar shi mace ce zata dinga masa cefane,
Sanye yake cikin 3qurt da t-shirt fara yasha kyau Mohd ba dai gayu ba komai talauci,haka Ramlat tana palo taci kwalliya cikin yar Gown ko gwiwa bata kai ba green tayi kyau kamar wata baturiya tana kulla su citta da kaninfari tare da shirya su Maggi,
Jin Sallamar Sardauna yasa Ramlat ajiye aikinta ta mike tsaye da niyyar tarboshi Amma kamar walkiyya taga ya shige bed room da sauri tabi bayansa saman Bed ta hangonshi ya rufe idonsa da alama tunani yakeyi akwai abinda ya dameshi,

Hankalin Ramlat ya tashi bata taba ganin Sardauna cikin wannan halin ba yakanyi kokarin danne damuwarsa, bed din ta karasa tare da kwanciya itama kusa da shi yanda ya kwanta yana kallon sama itama hakan tayi,juyowa tayi tana kallonsa da damuwa ta kai hannunta tare da shafo tun daga sajensa zuwa gemunsa Amma hakan bai Sa ya bude idonsa ba, hannunta daya saman gemunsa tana shafawa dayan hanun ta sashi cikin nasa tana murzawa a hankali,
Bakinta saitin kunnensa ta furta My King wa ya taba min kai?me ya faru?ni nasan dai mijina baya fushi da Kaddarar da Allah ya Dora mana,
Nasan My Soul namiji ne ba me rauni ba,sannan yasan cewa duk halin daya shiga daga Rabul samawati ne babu wanda ya Isa ya Dora masa,
My love yasan dare daya Allah zai iya canja mu,zai iya azurtamu ta hanyar da bama zato,
Me yasa zanga Namijin duniya,daya tamkar da dubu,wanda baya karaya cikin wannan Halin?why zan ga Ranka ya dade cikin damuwa? Bayan yasan Allah na tare damu,

Hannunta Sardauna ya matse kam cikin nasa yana me murmushin farin ciki,mamaki yakeyi yaushe Ramlat take da hankali haka? Yaushene ma ta tashi daga doluwa marar wayo ko dama haka take wancan lokacin gata da jin dadi ne ya mata yawa?

Juyowa yayi suna fuskantar juna hannunsa yasa yana shafa fuskarta me matukar kyau hancinsu yana Gugan na juna,
Matsowa tayi jikinsa sosai tasa hannu a hankali ta zare masa rigarsa da Wando daga shi sai boxers, baza ma kayi magana ba?shuru ya mata yana murmushi tare da kafeta da idonsa masu kashe mata jiki,
Me zance to bayan kin Sa na daina fushin?muje kiyi min wanka mikewa yayi tare da fisgota ta fado jikinsa Sa,wanka ta masa tare da shirya abinta fes har bedroom ta kawo masa pounded yam miyar egusi, saida ya koshi ya mike tare da yin Brush da aswaki Sabo da sau biyu yake brush da toothpaste Amma ko me yaci sai yayi aswaki da ingantaccen icen aswaki,yana gamawa ya kuskure bakinsa kafin ya fito Ramlat ta gyara wajen tare da kwashe kwanikanta,

Tana shigowa still hango Sardauna tayi gefen bed kamar da Alama tunani yakeyi, saman bed ta jawoshi ya kwanta sosai,itama kwanciya tayi suna facing juna,Gown din dake jikinta ta cire sai wani dan Wando da kadan zai rufe mazaunanta,
Wani light bedsheet ta rufa musu kamar Bedsheet haka yake,Boobs dinta daya ta sawa Sardauna a baki kamar jariri ya wani karbe yana zuka harda cewa yanda kike birgeni ba a koya miki abu komai kin iya,murmushi tayi na jin dadi hannunsa ya daura saman dayan yana wasa dashi yana shan daya,Ramlat kuwa hannunta tasa tana shafa masa gashin kansa tana My King dan Allah ka taimakeni kayi bacci,shagwaba ya fara sai dai ayi babbar Harka shi gaskiya,Ramlat tace nafiso kayi Bacci Dear ka huta da dare sai kayi koma mene kake so,Hura masa kunne ta fara a hankali tana shafa kansa,shi kuwa Shan na shanunta yakeyi yana wasa da dayan nan sai bacci ya kwasheshi ba tare da ya shirya ba,
Ramlat sai tayi yunkurin zare Sardauna daga jikinta sai ya kara manneta tare da ci gaba da tsotsar Dukiyar fulaninta haka Ramlat ta hakura ta kyaleshi yana ta baccinsa itama daga baya baccin ya kwasheta.
Basu farka ba sai bayan anyi Sallar La'asar, wanka da Sallah sukayi shar suka ci kwalliya cikin kayansu masu kyau tunda har yau kayansu masu kyaune Sabo da yawansu kuma suna da yar tsadarsu.
Wajen Mami suka shiga har bedroom dinta tana shirya kayanta da suka hargitse da Sauri Ramlat ta karba tana gyara mata,Ramlat sam bata cika kallon Mami a matsayin kakarta ba tafi daukanta a matsayin Uwar Sardauna surukarta shi yasa ko wasa ne kadan take yarda suyi matsayin Uwa take bata,

Mami ba karamin dadi take ji ba,Mami ce tace to Ramlat yau dai kamata yayi ayi mana tuwon shinkafa miyar danyar kubewa mun dade bakya mana tuwo abunda mijinki ke iya ci shi kike dafa mana,tuwon danyar shinkafa miyar danyar kubewa ai nasan yana ci da wuri zaki yi mana da baya ci nasan baza ki mana ba sai kin kawo wani Uzuri,dariya sukayi gaba dayansu Ramlat tace kai Mami sati daya ne fa kawai banyi tuwo ba a gidan nan,a sati sau daya kike mana shima sai miyar da yake ci kikeyi,daga miyar zogale,sai Kubewa danya,baya cin tuwon gari kin taba yi mana sai na shinkafa.
Mami yau kishin har dani?Sardauna ya tambaya yana dariya.ganin lokaci yana kurewa Sardauna ya riko hannun Ramlat yana muje kitchen yau Mami sai kin gaji da Tuwo,
Ramlat tace tsaya na dauko kudin Kubewa da na kifi,takaici ya rufe Sardauna mace ita zata na musu Cefane,
Tana dawowa Sanye cikin Abaya baka da mayafinta me dan girma suka tafi,hannunta ta tura cikin aljihun Sardauna shima hannunsa na ciki ya rike hannunta suna ta Tafiya duk majalisar da suka wuce sai anyi zancensu tunanin mutane ma basu da aure,

A hankali suke Tafiya har suka zo kusa da wani wajen siyar da wakokin cd kala kala,wajen kida ne yake tashi na hauka me dadin gaske,majalisa ce ta ko ina a wajen, Ramlat tace yi min rawa kaji,Sardauna yace naki ai na girma kuma,cak ta tsaya tace wlh in dai bai mata ba baza ta je ba ta daina kulashi harda bata rai,
Tsayawa yayi tare da cewa wannan abu me sauki, a wajen bainar Jama'ar da suke wajen Sardauna ya fisgota jikinsa suka tafi a haka yana ce mata nafa girma kika sani ko ina da Babyna a Cikin cikin ki ina rawa kuma yanzu ai Dad girma ya fadi,ba wani kai dai kawai kace ka tsufar da kanka shike nan da wuri mijina zai dawo tsoho duk abun matasa ya daina,

Abinka da kuruciya Sardauna ya shiga tunanin lallai fa Ramlat da gaske take cewar Zai jawowa kansa tsufa da wuri,kamata yayi ace ko a gaban dansa ne ya cashe da rawarsa ba wani tsufa,baya son kara'i gwara ya Mori kuruciyarsa,abinka da Da Mohd dama shi ba kunya rawa yake ji ba ko a gaban uban waye cikin mutane ya fara takawa gaban Ramlat cikin birgewa da kwarewa,Ramlat ta tsaya jikin wata bishiya tana ta jin dadi Sardauna ya saki ransa baya damuwa yanzu,
Dariyarta take dannewa da kyar har ya gama rawarsa kadan ya riko hannunta suka karasa wajen masu saida kifi da Kubewa danya,

Mutanen wajen ba wanda baiyi dariya ba ana kallonsu tunaninsu yaya da kanwarsa ne,wasu suna wannan anyi Babban banza,irin marasa kunyar yaran nan ne ko a gaban waye rawa sukeyi,ai da gani wancan kwallon dan duniya ne musamman kalar askinsa da Shigarsa, haka dai mutane suke ta surutunsu.

Daddyn Sardauna zaune yake a katafaren Palonsa dake cikin makeken gidansa cikin Abuja city,tunani yakeyi sosai akan matsalar da ta tunkaroshi ta karyewar companies nasa dama sunyi kasa sosai ba a ci gaba sai ma baya da komai na tattalin arzikinsa keyi a maimakon aci gaba sai baya,Hankalinsa ya tashi sosai karfa a daina lissafashi cikin jerin masu arziki na África, Hajiya Bilkisu Momy itace tazo tare da zama kusa dashi tayi magana ya kai sau biyar Kabiru Fakas bai ji taba,sai da ta taba jikinsa sannan firgit ya juyo cike da damuwa,Bilkisu tace haba Daddyn Yara karfa ka jawo cuta ta shigeka a kan wannan abun,banga abin tashin hankali ba,ka tuna irin tarin dukiya da kadarori da kake dasu ai koma mene nasan har a Bada kafi karfin talauci,bama kai ba Dangina da naka sun wuce Talauci,Har a Bada Alhaji idan ka tuno kudinka baza muyi talauci ba.
Kuskurenmu Alumma sai kaji ana cewa ai Alhaji wane yafi karfin talauci,ai irin kudin da wane ya tara bama shi ba danginsa wlh baza suyi Talauci ba,ana mantawa cewar ko mutum duniya da abin cikinta ya tara komai yawanta Allah yana iya kwacewa dare daya,sai a ga kamar ma mutum wai shi ya bawa kansa,ko yafi karfin Allah ya kwace,wannan kuskure ne Allah sa mu dace.

Kabiru Fakas Hajiya ya kalla yace Kin san inda nake so a duniya nayi suna a san ina cikin jerin masu kudi na duniya?kina gani gaba daya komai nawa ja baya sukeyi dole hankalina ya tashi zuciyata ta dugunzuma,hajiya na shaku da kudi,na shaku da kudi Bazan iya rayuwa ba kudi ba,Bilkisu ta nisa sannan tace muma haka Mijina kaine gatanmu dole muna cikin damuwa Amma ka kara hakuri baza a samu matsala ba na sani komai zai dawo normal ai akwai kadarori ai.

Lantan yau satinta Uku da zuwa gidan Soja barikin Sojoji,a takure take bata fita ko nan da can,tana lekawa

Please Login or Register in order to submit comment