Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwananan ya fito rainonsa nakeyi kamar kwai yana fada yana shafawa yace to ko shi aka aske min kotu ce zata rabani da mutum.

Liman yace Allah me iko,yaro ko babankane? Sardauna ya dan lashi jajayen lips dinsa yace shi yafi komai sauki ma kenan.
To yaro Allah kara lafiyar wanka,Mohd yace Amen Dad goodnight ya bar masallacin.

Liman yaron yana birgeshi Iyayinsa da tsirfa ce kadai matsalarsa saboda yaga yaron kuruciyar tasa me kyau ce baya raina manyan mutane,bai da girman kai amma da gani wannan yaron jinin Mulki ko kudi ne duk da cewa yasan gidansu amma gaskiya da Alamar tambaya.

Sardauna yana komawa gida Mami tace dan Albarka ko zaka siyo min ashana kaga Ashe ta kare ina so daura mana abinci, haba Mami kamata naje siyo Ashana kato dani haka wai ashana kawo dai na bawa Almajiri,Mami tace tab lallai Sardauna ka bunkasa,to mene idan ka siyo,kamar zaiyi kuka yana shagwaba oh Mami nifa ba wai girman kai ba ko nafi karfi ba kawai Mami duk wankan nan ana ganin mutunci na a unguwa a ganni da ashana duk kayana zasu yamutse idan naje kin San kuma mutane wani da palm oil wani da peanut etc duk gasu nan zasu bata ni da dirty ya karashe yana yatsina fuska tare da dage gira,
Mami tace to rufe min baki karbi ka bawa almajirin,
Karba yayi ya kaiwa Almajiri ya siyo,yace kai student kullum ka dinga zuwa ana aikenka kana karbar abinci kuma zan dinga biyanka some cash a wata karfa ka dauka da yawa domin aike kawai zaka yi.Almajiri da murna ya amsa ya tafi.

Mami dai tana kallonsa batace komai ba a ranta tace a haka yaron nan yana haka ina ga yasan waye Ubansa a kasar nan.
Sardauna yace Mami kiyi hakuri kinji,murmushi tayi tace ina ni ina fushi da dan jikana tsoka daya a miya,dariyayi tare da lafewa a jikinta kamar zai koma cikinta.
A hankali ya furta Mami kin san na girma zaki fada min inda Dad dina da Mum suke ko? Mami ta kada kai alamar eh,yace to Mami ai na girma yanzu ki fada min,
Mami tace zan fada ma Mohd,amma babanka ya bata min rai matuka musamman Uwarka data biye masa,
Mami kawai ki fada min pls nasan inda na fito.
Gyara Zama Mami tayi cike da jimami ta fara bashi labari...

Jigawa state mota ta sauke Ramlat ta kara hawa wata dagargajajjiyar mota r kauyensu,cikin karamar hukumar Roni.
Can wani kauye ta sauka a kasuwa gida je tsalli tsalli da gani fulanine usul a kauyen domin ko ina Shanu da masu kwaryar Nono ke zagawa da sintiri a kauyen.

Machine ta hau suka kara kutsawa cikin kauyen har wani gidan kasa katangar ta gama zaizayewa, ta kare domin idan ka Mike za a hangoka a tsaye,ko bandaki ka shiga ana kallon kanka ta waje idan ka Mike kiri kiri zaka hada Ido da mutane,domin watarana ta bayin suke gaisawa da mutanen da suka zo wucewa idan sun sansu ka Mike zaka sa kaya,
Tana shiga ta hango Babanta wani yamutsatse dashi ga tsayi kamar rakumi,gashi siriri,idonsa kwala kwala jajur dasu,shi kanshi abin tsoro ne yanda ya watsa kansa,
Da Sallama ta shiga yana ganinta ya Mike a fusace Ramlatu ki kiyayeni,zan miki Illa Ramlatu,dan kundun ubanki ni zaki kawowa iskanci ji kake tas ya sharara mata maruka biyu,kafin ta huce ya dauki sanda da nufin kwala mata a kanta,hannu tasa da niyar karawa
Tana bashi hakuri ai kuwa ya buga mata a hannu,baras hannunta ya balle ta durkushe a wajen tana kuka da ihun tare da neman a gaji,haka ya bita ya jibgeta sosai,Kannenta ne suka shigo dukansu suna Anty....Anty...suma duka dattijo ya kai musu suka fice daga gidan da gudun tsiya,Umman su ce ta fito tana kuka da yar yarinya kimanin shekara daya a hannunta,tace Haba Idrisa haba kafin ta rufe baki ya kai mata mugun duka itama ya mata duka,da kyar Umma ta Mike ta shiga daki tare da hada kayanta,
Yar yarinyar sai kuka take itama tana rarrafe ta barko kashi a kusa da Kawunsu ai kuwa ba wata wata kawu cike da rashin Imani ya fesawa yar yarinya mari har biyu saida ta kife a kasa tana cin kasa da bakinta duk jini,kafin kace me fuskar yar jaririya ta kumbura suntum,Umma kuwa katifarta ta daga ta kaita makwafta aka siya ta Goya Yarta ta bar gidan tana kuka mota ta hau sai Abuja ta tafi neman dan Uwanta da taki yarda da hukuncinsa ta bijire masa akan yaranta.

Makwafta da yayar Idrisa su suka taimaka suka kai Ramlat wajen dori,sannan suka kaita asibiti,tana Jin sauki ta tattara nata ya nata tace Duk inda ta fadi Sha ne,ta koma tasha ta shiga mota sai Katsina state.
Yaran yan kanana kannen Ramlat duk sun bazama a cikin kauyen ko wanne da gidan da ya Zaba ya shiga suna rokon a taimaka musu gasu yan yara kanana.
An bar Kawu Bala'i shi kadai a gidan sai zirga zirga yake,ya shiga ya fita ta shiga ya fita,ya tafi gabas ya koma arewa,
Dakinsa ya shiga yaga ba kowa kawai sai ya dora hannu aka tare da kurma uban ihu,ya tsuguna a wajen yana ta gunjin Kuka,
Yana haka yayarsa Abu Babba ta shigo gidan tace kayi Asara Idrisa Baka ji dadin halinka ba,albasa batayi halin ruwa ba,ba haka iyayenmu suka rike mu ba,Amana fa Allah ya baka Idrisa kasan mene hakkin yaya kuwa da mata?kaji tsoron duniya,
Kallonta Idrisa yayi yace Abu me nayi?Abu tace ubanka da Uwarka kayi kana wano min Ido kana kwalo min Ido da Ido kamar na kururu,
Sai ka zauna kai kadai kuma wlh duk cikinmu babu me rike ma yara,mun zare hannunmu tunda baka San arziki ba dan Iska,dan kwaya,dan bariki,giyarka da kwayarka ta gaya maka karya Abu ta gama zagin Idrisa tas ta bar gidan,
Kwana daya danginsa suka tafi office din yan Hisba dake Roni suka kai karar Idrisa abinda yake yiwa iyalinsa,sosai suka kamashi suka dinga masa fada da Wa'azi kamar gaske ya bada hakuri yace a nemo masa iyalansa su dawo gida,
Umman su Ramlat kuwa haka ta Kari garari a Abuja dan Uwan nata da iyalensa sun canja state,babu labarin garin,unguwar da suka taba Zama a Kubuwa Abuja ta je,christain din da suka Santa sune suka bata kudin Mota ta koma Kano neman gidan mahaifiyarta,cikin rashin sa'a bata nan itama sun bar state din. gidan mijinta Idrisa ta koma.

haka aka dinga neman Inda Ramlat ta kada an rasa,da kyar wani yace sun hadu a tasha ta hau motar Katsina,nan Idrisa ya tabbatar gidan Abokinsa me Damusa ta tafi,nan take ya kira abokinsa,ai kuwa yace gata nan zan kawota gida gobe,amma Idrisa ba ka kyautawa kalli yanda ka karya yarka budurwa mace kamar wannan,nan Me Damusa yayiwa Idrisa tatas,washe gari Ramlat na kuka ya kawota har kauyensu,Ummansu ta gani da kannenta duk sun dawo gida suma,

Idrisa harda siyo danyen kifi me yawa asha farfesu,Idrisa Dubu biyu ya zaro a aljihunsa yace Hafsatu ga jarin Awara Ku fara ta siyarwa, Hafsatu cike da Jin dadi ta dinga murna,Idrisa yace ke Ramlat bana Son kiyi talla ban yarda da tallan mace ba,su Fahat sa dingayi,

Wasu kaya ya dauko cikin buhu yace gashi gwanjina ne na sawa ko wanne da nasa ya Zaba,Ramlat harda sababbin panties guda hudu da sauran gwanjo masu kyau,su Vaseline manya,su toothpaste manya wajen biyar,sabulai komai dai ras,

Harda yan kayan abinci na talaka,sai murna sukeyi,nan Idrisa ya fara musu fada da nasihar rayuwa data karatu,nasihar har ta ishesu sun gaji da ji,dan shi in ya fara abu ba tsayawa har sai ya koma bala'i

Kamar gaske Umma Hafsatu ta fara rangada Awara tare da taimakon su Abu,abu dai ras anci gaba sosai,har kayan abinci da komai nasu ya kare kaf,Idrisa ba kudi,Abu ke aiko musu da Abinci yaran wasu su shiga makwafta suci da yaransu,

Tsabar shirme da dolanci irin na Hafsatu ta samu Abu tace a bata kudin jarin Awara da sukeyi da ribar duka,Abu ta fara mata fada,sai kace dabba Hafsatu,baki da hankali? Hafsatu ta hayayyako itama da masifa Dame zanji,ni hanuna babu kudi,bani da kudi ya zan zauna ba kudi,Abu haushi ya kamata ta watso mata kudin domin Abu ke boye musu kudin

,Hafsatu ta kwasa ta tafi gida,tana zuwa ta kame kaji da zakarun Fahat da yake kiwo ta siyar ta hada kudinta kaf washe gari da safe ta Goya Yarta tace Ramlat na tafi unguwa,zanje Lokoja,Ramlat tace me zaki a Lokoja?bamu da kowa acan ai gwara mu siyi abinci da kudin,

Rufe min baki ke zaki tsara min yanda zanyi, zanje gidan Abdullahi abokin babanku neman kudi,Ramlat tace Umma shima fa talaka ne kawai kinfi so Ku dinga samu a wani Hali ke da kawu,Hafsatu tace yunwa ta kasheku ga ubanku nan na tafi,
Uban kaya ta loda a Ghana must go ta hau mota ta tafi,Idrisa sai da ya dawo Ramlat ta fada masa,abin ya masa ciwo ya kama bala'i har ya gaji,
Ramlat basu da komai na ci ga yunwa duk ta rame tayi duhu,ga kannenta suna bata tausayi,dan ma Abu na taimaka musu kadan,dabarace ta fado mata,a gidan me Damusa kafin ta taho ta samu kwancen kaya kala Biyar,a Leda ta zuba su masu kyau taje ta siyar a wani gida a kauyen,itama Ramlat dake yarinya ce sai kawai ta dinga dagar gazar musu dadi kwana biyu ita da kannenta suna cin dadi harda Kawu,kudi suka kare,
Kawu Bai San ina ta samo kudi ba yaga dai suna girki shima yaci,watarana yunwa ta ishesu kamar zasu mutu,tsohon takalmin Kawu ta dauke wanda ya taba aikin dan sanda,doka ce aga takalmin wani yasa,Bai sani ba Ramlat ta dauke taje gidan ta kara siyarwa suka kwashi girki harda Kawu,saida aka dauki sati guda Kawu yaje inda suke shaye shayensu yaji ance anga tsohon takalminsa na yaikin dan Sanda wani na sawa a gari,yace shima a wajen yarka Ramlat ya siya.

Kawu yaje Har gidan yaron ya tambaya aka tabbatar masa,harda cewa ai kayanta ma duk ta siyar,Kawu yana dawowa ba zato Ramlat taji ruwan duka saida ya farfasa mata jiki ko tashi bata iyayi,ba Imani ya kara janta ya buga kanta da bango,yana sai na kasheki yau,nine ajalinki,yara sai kuka da kuka,Kawu ya daka tsalle ya fisgo bishiya tare da basgo katon sanda ya fafaki sauran yaran ya bisu da duka har waje,
Ramlat makwafta suka ceceta da kyar ya kira su Abu da sauran yan Uwansa yana huci ya hada zufa yace saina kashe Ramlat Ku sheda,
Abu tace humhum shashasha sakarai Dabba banza wofi,jaki a jakinma iceko Idrisa kai Aura ki ne,
Kowa ya hau Idrisa da zagi,Idrisa yace kalli takalmin da ta siyar kamar ni,ta sai da kayan sawarta?tana so ta gaji Uwarta,da kyar na nemi aron kudi na fanso kala biyu a kayanta,
Kowa dake wajen akayi caaaa kan Ramlat wacce ta farfado tana numfarfashi,ana kece da laifi kema kinyi Kuruciya baki kyauta ba,kaima Idrisa mene abun duka yarinya yunwace ta ishesu,Abu ce ta dauki Ramlat ta tafi da ita gidanta,ta gasa mata jiki ta bata abinci ta koshi,

Bayan komai ya lafa yau wajen wata guda da tafiyar Hafsatu sannan ta dawo,Idrisa dai saida ya kafeta da mari uku sannan suka shirya,
Ana zaune yau yunwa gobe babu,Ramlat tana ta fita zance a kauyen sabo da ta samo kudin zance sa rage Zafi,
Idan Ramlat ta samo kudin zance Dari biyar Dubu daya,sai ta samu jikin matsematsen Katanga da kwanon rufi ta boye kudinta a nan,ko ta samu cikin ginin bulon siminti na gidan Abu ta tura ciki ta danne da dutse,
Rannan dai tana so ta dauki kudi ta lallaba cikin duhu garin dauko kudi suka zurma cikin ramin bulo,tayi tayi ta dauko ya gagara,ta kira Abu Baba kinga kudina na sa anan sun fada ko zaki Ciro min,

Aka lallaba aka Ciro kudi tare da tallafin matan gidan kishiyoyin Abu,ana irga kudi sai aka Ciro Dubu uku,Abu ta hangame baki tana Salati Ramlat ina kika samo kudi,
Ina....Ina...Ramlat ta fara tana susar jiki,Abu tace zaki fada ko sai na kirawo ubanki,da sauri ta zayyanewa Abu cewar kudin Mota take Tarawa Idan gari yayi Zafi ta samu na tafiya,idan ta nunawa Babanta da Umma karbewa zasuyi,Kawu zaiyi shaye shaye Umma kuma kin San kudin Mota zatayi ta bar garin,
Abu tace to badan haukarki ba Ramlat ki dinga kawo min ina boye miki,Ramlat ta yarda da Abu bata ci musu Amana ta bata kudin,Abu dai ta zaunar da ita tayi ta yi mata fada da kuma gargadinta na ta kikayi samarin Zamani,kuma kin San sarai babanku ya hanaki zance da daddare tace eh to ki kiyaye.,
Amma mutan gida sun Sha dariyar Ramlat ta boye kudi sun fada ramin bulo asiri ya tonu.wace ce Ramlat?






AsmaBaffa
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€



DUK INDA TA FADI



7,8,9 & 10




Official




By
AsmaBaffa





Mamice ta fara bawa Sardauna labari: Yara biyu na Haifa a duniya sauran duk mutuwa suka dinga yi suna yara,
Ni Fatima asalinmu fulanin chardi ne,dangina da dama duk sun kare,Allah ne ya hadani da kakanka kafin ya rasu wato mijina Malam Usman shima dan chardi ne, sana'arsa kasuwanci wanda shine dalilin dawowarmu Nigeria, sauran duk suna chardi yanzu kasan ba zumunci,munje munje har mun gaji basu taba neman inda muke ba,har muka gaji muma muka daina zuwa,
Nasha haihuwa amma duk mutuwa suka dingayi Kabiru babanka da Hafsatu sune kadai suka rayu,Kabiru mun bashi tarbiya da Ilmi Addini dana zamani kanwarsa Hafsatu iyakacinta jss3 akayi mata aure, Kakanku ya dora Kabiru akan kasuwancin gwala gwalai,

Kafin wani lokaci arziki ya cikamu,Ana haka ya Nemo Babarka Bilkisu,Bilkisu yar Asalin Kano ce,cikin karamar hukumar Tudun wada,fulanice Usul itama
Borno state a nan muke gaba dayanmu katsam,Kabiru yace zasu koma Kwara state kasar yarabawa sabo da business dinsa yafi yawa a can,
Sun barmu suka koma shida Amaryarsa Bilkisu,tana dauke da cikinka Allah ya dauki ran mijina Malam Usman,

a kano ya siya min gidan na zauna tsawan shekaru Ukku da suka bata min rai na siyar da gidan na siyi wannan sabon gidan da muke ciki a Kaduna state unguwar Rimi.

Kudin Kabiru ya bunkasa, ga siyasa yanayi,gashi an bashi babbar Sarauta a kasar Kwara, ya rike mukamai da dama,kasuwanci ya Zama hamshakin attajiri wanda kaf Africa an San dashi,da kasashen ketare,kudi ya ratsasu da Mulki Alhaji Kabiru
Fakas kenan shine Ubanka Mohd dana ne na cikina,Mohd yace ai ina ganinsa a news, Abinda sukayi ya bata min rai shine Bilkisu Uwarka tana haifarka da Wata Ukku suka daukoka kana jariri suka kawo min kai wai na rike sun bani,ita baza ta iya shayawarwa ba saboda kar Nononta ya zube,Kabiru Fakas yace shi Sam Bai shirya haihuwa yanzu ba ya za ayi basu ci Amarci ba a samu ciki harda da,
Babu yanda banyi ba kan Bilkisu ta shayar dakai taki yarda makudan kudi suka bani wai na siya ma madara sukayi tafiyarsu kasashen ketare.
Nasha wahala kamar zaka mutu da kyar ka samu lafiya ka rayu,tunda suka tafi basu kara nemana ba ko a waya har shekara Biyar,shine takaici ya kamani gashi ina kallonsu a TV kawai na siyar da gidan na kano muka dawo nan,da kudin da suka bani dashi na biya maka schl da abincinmu,har Allah yayi ka girma,na siyar da komai nawa na tattara da kudin wajena na Bude maka shopping mall dan madaidaici,na zuba yara shine nake turaka domin ka nemi na kanka,gashi har Allah yasa ka samu scholarship gwamnati ta dau nauyin karatunka zuwa London kaje kayi Degree da masters ka dawo,Babanka da ace yayi niyyar nemana ni mahaifiyarsa da tuni ya nemoni amma duniya ta rufe masa ido,abinda yasa na karbeka nasan tsab zasu iya bawa wata ko wani ya rike dan basa kaunar haihuwa ko dan a lokacin.

Mohd cike da tausayin Maminsa yace to ita kuma Hafsat fa? Mami ta nisa tare da cewa kash,Hafsatu ai tana can cikin wahala a jigawa state karamar hukumar Roni can wani kauyen Fulani,
Babu yanda Babanka da ni namuyi ba don ganin Hafsatu bata auri Idrisa ba amma taki ji,sabo da Idrisa ba mutumin kirki bane Sam,shaye shaye ne aikinsa da wasu munanan dabiu,
Bayan ta aureshi ta haifi yara 5 dashi Uku Maza biyu Mata,
Duka da hauka babu kamar Idrisa,ba ci ba Sha bare sutura,Kullum Kabiru ke dawainiya dasu amma Idrisa dake Butulu ne har Gida yaje ya ciwa Babanka mutunci,lokacin Ramlat Yarta na karama shekara daya tal ka girmeta, na karbeta ina riketa tare da kai,Babanta yazo har gida ya kare min zagi harda yan Sanda na bashi yarsa, haka na bashi ita,

Hafsatu kullum a kawo kara take,nace a raba aure amma tace wlh babu wanda ya isa sabo da yaranta,sukayi kaca kaca da Kabiru babanka yace karta kara zuwa gidansa,
Nima nace taje kar ta neme ni,sanda Ina Kano tana yawan zuwa kana yaro,dana canja state ko fada mata banyi ba saboda bacin rai,yanzu bata San inda nake ba,bakin cikinsu ya isheni haka,

Ci gaban labari

Sardauna ya kara kankame Mami sannan Mami taji ya wani kyalkyale da dariya,Da mamaki tace Sardauna Lfy? Sardauna yace yanzu akan dan wannan abun kike ta fushi haka,ni na zata wata gagarumar matsalace،
Ashe Mum and Dad yan gayu ne sun San wanka da love,gaskiya sun mugun birgeni da soyayyarsu, yayi gaskiya wlh wannan ai ba dai dai bane ace daga Aure sai ciki,ko Amarci ba ai ba,Mum kuwa ta birgeni wlh da bata bari Breast dinta sun zube ba ta adanawa Dad abinta, duka Mami ta danawa Sardauna tace kaga Illar da basu shaku da kai ba yanzu ai da Baza ka fada musu haka ba marar kunya,Mami yace to ke kalli naki kamar Slipas kamar Gugan danko,gaba daya kinyi expired,murmushi Mami tayi tace oh Muhammadu Allah shirya min kai,ai da shi zan baka ka sha,fuska ya yatsina gwara da baki bani ba,ashe ni dan Madara ne tunda na ganni nasan ni dan Madara ne.

Abu daya ne bai dace ba rashin nemanki da basuyi ba kuma ni ina dansu basu damu su ganni ba,Amma gaskiya harkar wankan yayi,
Sun waye haka ake so,Allah sarki Poor Hafsatu na tausaya mata,amma ba komai zanje na ganta muyi zumunci itama ai Mum dina ce.

Amma Mami ni da kin fada min tuni da na nemo su Mum,Mami tace yanzu ban san a wacce duniya suke ba,kaje gidan Hafsatu nasan ita zata san inda suke tunda baka da zuciya basu nemeka ba kai ka tafi nemansu.

Murmushi yayi tare da cewa Mami ni wlh sam ban damu dasu ba,bazan ma iya daukansu a iyaye ba,kawai dai zan nemosu Sabo da watarana idan zanyi aure,
Mami tace kai Muhammadu ka kiyayeni kana 19yrs din zan maka aure so kake ka saki matar da shirmenka,

Shagwaba ya kama kai Mami ni ki daina Cemin yaro na girma,kuma idan nayi auren zaki ga yanda zan riketa har ta haifo min Yara,oh Muhammadu ba kunya,Allah nuna mana,
Zansha kallo naga wacce yar gayun za a auro min,dariya Sardauna ya fara harda boye fuskarsa jikin Mami yace Allah Mami zaki sha mamaki muguwar yar gayu zan auro,wacce take daukan wanka,yar wanka ta gaske me tsaftar Bala'i,Dariya Mami tayi sosai tace zamu sha biki,yace bikin yan gayu ma kuwa bikin na yan daukan wanka

To naji tashi kaje ka kwanta gobe da wuri ai zaka je wajen shopping Mall din naka kaga yanda ma'aikatan ke aikin? Mami na je yau fa acan na yini na gama komai kuma ana samun ci gaba sosai,burina kawai na samu na dallo motar hawa,dan guy kamata ba mota wannan fuck up ne,
Allah ya hore Sardauna,Ameen Mami.
Ina da kudi a accnt dina dana ajiye na scholarship din da suka rage wurin 2millions ga ribar Mall dina,kamata yayi mu sake ginin gidan nan yafi haka haduwa,sai na siyi mota,ni bana son siyan mota karama nafi son ta yan wanka,wanda ana gani na an san yes nima nine,tabe Baki Mami tayi tare da cewa kai baka da zance sai na wanka wannan wankan uban mene wai?Kullum sau wajen Uku ko hudu kake wanka fa Amma har yau hankalinka bai kwanta ba,
Dariya ya kamayi swagg fa Mami ke bakya ganewa,dagani shashasha,

to bari muyi wata hirar Mami tattalin Arzikin Russia ya sauka kasa last wk,Tabe baki Mami tayi tace uhm,yace Brazil tattalin arzikinsu yahau da wajen point 5,Mami ta matsar da kanta gefe,nan Sardauna ya dinga lissafa mata kasashe da tattalin arzikinsu ya karu,da wanda suka ragu,Mami tace a canja hira ,Mami ke baza ki waye ba bakya kallon News baki san inda duniya tasa gaba ba,
Mami tace eh naji,nan ya canja hirar yan Ball,Mami Messi kin san nawa yake dauka duk sati?Mami tace mene kuma Massi?Messi ake cewa,Ronaldo fa ya bar Madrid,ga Harri kane ya daga Golden Booth,kin san Lingard me yace a satin nan,Mami tace kai daga min cinya kai ka sansu,
To na daina zauna na baki labarin wata dana gani yau,Mami kinga yanda ta dau wanka? Gata me kyau gaskiya chick din tayi ta San harkar swagg,kuma Mami bafa matse jikinta tayi ba tsabar iya wanka ne,

Mami tace sai da safe kai baka da labari sai na wanka,da yan ball saina kasashen turawa,da kudi aikinka kenan,Mami ta shige daki,shi kam ya tabe baki a ransa yace Mami Baza ta waye ba,ya fara research a system dinsa da phone,
Kida yasa tare da jibga uban headphone a kunne yana ta faman bin wakar raps.

Halayen Mohd Wato matashi Sardauna.

Mohd dai fari ne Amma ya sirka da ja,kamar balarabe don babu wanda zaice ba ruwa biyu bane, domin da yawa dauka suke kwara ne,dogo ne Amma ba can ba dan dai dai yake,siriri Amma kuma ba siriri ba domin da yar kibarsa jikinsa mul mul yake ba kasusuwa,hancinsa siriri me tsayi Amma ba can ba,gashinsa bakine wuluk me santsi Amma
irin na yan fulani ba na ba indiye bane ba kuma na Balarabe bane,domin a gashinsa zaka ce dan fulanine,gashi ya tara suma sosai,kalar askin

Please Login or Register in order to submit comment