Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kai 27 sannan za a yi bikinsa tare da Gina sabon gida.
Ramlat bata da wata matsala domin har waec da Neco ya biya mata ta zana.

Mami har gidan su Hafsatu taje na kano Amma babu kowa a gidan,Idrisa an tafi shaye shaye,yaran suna makwafta yawon kwadayi da bara,Hafsatu ta bankada yawonta da ta saba,haka Mami ta dawo ba labari sai na bacin rai.

Wasa wasa sai ga Ramlat ta shafe wata 5 biyar da zuwa gidan su Mami,zamansu sukeyi Lfy,Sardauna ya zama busy da neman kudi baya zama kullum sai dare yake dawowa yana zuwa yaci abinci sai bacci,da sassafe ya fita Ramlat sai tayi sati bata ganshi ba,tunanin Sardauna fa ya daina kula Ramlat sai ya kai 27yrs sannan zai karbi aurensa shi yasa ma ya Zama Busy wai kar ma ta ganshi ta rainashi, yanzu Sabo da karma ya lalace ya daina shiga harkar Ramlat kwata kwata gaisuwa kawai ke hada su,ko hira basayi idan ma ta kawo zance bazai taba saurara ba cewarsa zai iya biyeta ta rinjayeshi ya lalace haka kawai akan yayi aure,shi bai shirya sanin mace ba.amma duk time din da take period ya gama haddacewa yayi ta Sa mata ido, bazai ce mata komai ba amma sai yayi ta cewa kije kiyi sallah mana wai dan tace ai bata yi sai kawai yaji dadi Yana tunani wajen,
Sai kuma ya dameta taje ta canja pad zata yi staining,mnth nayi za a ganshi da pad guda biyu,bazai taba siyowa da yawa ba dan kar da dinsa ya kare sai month yayi yake kawowa cike da nishadi,ranar ko Bai ganta ba zata ganshi yana ta zuwa room dinta ziyara har susha hira. Suna a haka har 1yrs ta wuce Sardauna ya kai 21yrs Ramlat na 19yrs,ta dan kara hankali kadan amma da akwai dai rashin wayo har yau,
Sardauna kuwa sai abinda ya Karu ma a harkar wanka da tsirfa tare da shiriritarsa ta kuruciya,

Yanzu kusan ko yaushe Ramlat ce ke dafa musu abincin Gidan. Sardauna takanas yaje wajen Dad din Naufal ya nemowa Ramlat makaranta A.B.U zaria ta samu sociology,saboda Sardauna yaro ne yanzu bashi da hanyar samo University a kasar nan, sam bata yi murna da samun wani degree ba tafi son tayi NCE ko Diploma a Schl of health tecnology,Ko irinsu su Nursing college Amma Sardauna yace shi sai degree dole zatayi kuma abin haushi har Zaria zata zauna a hostel.sai rokonsa takeyi wai ita Diploma take so ba degree ba,idan da hali ma certificate kadai take so kar ya kai Diploma hhh kaji rashin wayon Ramlat.

Ramlat harda kuka an sata a schl ta kwana,tunanin Ramlat zata koma ciyar da kanta babu me kula da ita,yanzu ta saba hankalinta kwance Su Mami ke mata komai na rayuwa yanzu za tafi zama Hostel,kuma har 4yrs lallai ramewa ma zatayi ta lalace.
haka Sardauna ya dawo gidan ya hangota ta tasa Mami gaba tana kuka sai dai a kaita tayi Diploma ko certificate domin degree yayi mata yawa tana yarinyarta ace har tana Degree guda yaushe ma zata iya wannan karatu me yawa haka,Mami dariya kawai takeyi na shirmen Ramlat.

Dariya Sardauna ya fara sosai tare da cewa ban taba sanin rashin wayonki ya kai haka ba sai yau,wasu fa nema sukeyi idonsu rufe amma ke kin samu ba kya so,ni to ko free nursery banyi ba,kuma primary 2 aka sani,jumping Dad din su Naufal yayi mana sosai tun daga primary har secondary jumping aka yi mana,muna shiga ss1 yace mu zana waec yanzu karatu ba a jira sauri akeyi,muna yan Yara mun gama secondary muka tafi degree domin Course mafi sauki wanda ake degree 3yrs yace mu zaba,sannan masters 1yr,
Har yanzu wasu a frnds dinmu basu ma fara degree ba wasu kuma level 1to 2 suke kuma suke duk da hakan an musu jumping suma.

Fuska cike da hawaye Ramlat ta dago kai tare da cewa ni ina ruwana da naku,kowa kansa ya sani kuma ni Allah ina ma banci Jamb din ba,Allah sa ko na shiga na fadi a koreni daga makarantar,
Sakin baki Mohd yayi yana kallon ikon Allah,
Taci gaba da yiwa kanta mugun fata in Allah ya yarda bazan taba cin jarabawa ba,dole sai dai nayi NCE ko Diploma,kuma ko naje wasana zan tayi nayi ta haukata ina gwalangwaje na a littafin,ko exam muka zo Bazan rubuta ko a ba sai an gaji an koroni gida,Sardauna ya kyalkyale da dariya yana kallon haukar Ramlat,tace ba dariya kake ba kuka kake yi Insha'allah sai na koma dakikiyar ajinmu zaka gani,kai din me ka sani mutumin da aka dinga masa tsallaken aji,baka san komai ba kaje kayi abu sharp sharp ka dawo mene amfaninsa shine ni ka turani nayi me yawa dan ka cuceni sabo da mugunta,ta Allah ba taka ba kuma sai Allah ya saka min,kawai dan kana so kaga bayana Ubangiji bazai baka sa'a ba, sabo da ka tsaneni sai ka hada min mugunta dan na bar muku gidanku Allah sai ya bi min hakkina

Sardauna yace to fa abin kirki ya Zama tsiya Ramlat wato ke kinfi ganewa su Dafta Jibrila ko? Murmushi tayi domin ita ta bawa Mami da Sardauna labarin Jibrila da sauran Samarinta na kauye.makaranta dai dole ki tafi next wk ki Zama ready,hawaye ya kara zubo mata sharr...ba sai ka kasheni ka huta ba kawai, Allah yasa a kore ni ko shekara bazanyi ba,bige mata baki Mami tayi tare da rufeta da fada Sakaryar banza,Ramlat yaushene zaki wayo wai tunda na sanki haka kike ba kya canjawa kika sake zaki cuci kanki kije Allah ya amsa adduarki kiyiwa Mutane Asarar kudi,
Ramlat tace Allah ameen ni dama iya Secondary nake so nayi a duniya Bana son ci gaba.ai kuwa karya kike tunda an Riga anyi komai sai tafiya,Sardauna gobe Ku fara siyayyar kayan tafiyarta.

Washe gari Sardauna bashi da kudi duk ya karar da dan abinda yake samu sabo da komai baya yinsa na kudi kadan,in dai yana da kudi to sai yaga bayansu,ga tafiyar Ramlat,yama rasa da me zai siya mata abubuwan tafiyar tata,gashi Sam Bai iya cin bashi ba kuma babu kudi a kasa a mall dinsa sai wanda za a siya kaya dasu,

Saida ya cinye kwana 4 yana tunanin inda zai samu kudin yasan Mami ma bata da shi sabo da shi ke mata komai,kuma kayan abinci ma sun kusa karewa na gidan,
A kwai wata Taxi daya siya ya bayar da haya ana kawo masa balance duk sati,mutumin da ya bawa motar a karkashinsa yake idan ya karbi motar ya siyar ya toshe masa hanyar cin abinci,kuma yana da iyali dattijo ne na kirki.dole ya hakura ya fasa siyar da ita sabo da mutumin,idan ya taba kudin shopping mall dinsa jarinsa ya karye,Naufal ya kira a waya yace yana bukatar Dubu Dari da Hamsin kafin wani lokaci,Naufal dan danan ya karbo wajen Abbansu ya bawa Sardauna sabo da shima Naufal kudin iyaye ne bashi da na kansa a yanzu Bai tara ba.

Sardauna komai ya siyowa Ramlat ya gama mata komai na schl registration da sauransu,abubuwan da zata tafine dama babu,har abincin gidan ya karo amma bada wani yawa ba sabo da ba kudi,
Abin haushi yana kawowa Ramlat bata San ta yanda ya samo kudin ba kawai ta fatalar da kayan akan bata son degree ita,
Mami ma taji haushin abinda tayi saida tayi mata fada sosai sannan tace wa Sardauna idan bata so a kyaleta kawai ta zauna haka,yarinya Sumi Sumi kamar doluwa amma sai iya shege,.

Sardauna kuma yace shi wlh matarsa sai me degree dole sai tayi ko tana so ko bata so shi dole ta waye ta goge ta koyi daukan wanka sannan ta kara wayo da hankali idan tana shiga mutane zata fi Sanin rayuwa.
Ramlat tace rayuwa ni wacce ce ban sani ba,kuma na goge tuni ko kai kadai ai ka isa ka wayar Dani,
Takaici dai ya cika Sardauna amma yace dole fa taje.

Mami tasa ta a gaba dole ta hakura zata je amma baza tayi kokari ba kuma idan aka koreta wlh ba ruwanta,duk da haka kullum tana ganin Sardauna zata fara kuka ita a fasa wahala zata Sha baza ta iya ba,ko kulata bayayi.







AsmaBaffa loves u all readers masu sharhi.





AsmaBaffa
[9/23, 12:55 PM] ‪+234 808 968 1079‬: 🏀🏀🏀🏀🏀🏀🏀🏀🏀🏀🏀🏀


DUK INDA TA FADI



101-105




Official





By
AsmaBaffa








DIYAR KATIBI,KHADY CAFE,QUEEN MERMU
TASKAR FIRDAUSI SODANGI
ASMABAFFA FANS CLUB
HAUSE OF HAUSA NOVEL
SAKAMAKO FANS
SURAYYARMS FANS
LITTAFINMU NA HAUSA
SAURAN GROUPS
READERS MASU SHARHI MASOYA
JINJINA DA GODIYA GAREKU ME TARIN YAWA.




Yauce ranar da Sardauna zai kai Ramlat schl ya gama mata komai,sai kumbura takeyi tana hawaye,ko tsinke tace baza ta dauka ba bare ta sa a mota,shi ya dauki komai ya kai mata ciki,dama kayan ma Mami ce ta hada mata komai
Mami fada tayi mata sosai sannan tana shesheka tace Mami nasan ma wahala zan Sha kawai shike nan ni kuma tawa ta kare,da kyar Mami ta lallasheta tare da Rakata har Mota,
Sardauna kuwa ansha wani yadi baki da milk shara shara me matukar kyau yayi kyau sosai domin ya aske jar sumarsa tas baka ta fito sosai tayi uban yawa ya sake sabon stile din aski shima an kwashe gefe da gefe ya barshi a tsakiya yayi yawa gefe da gefe kuma an rage ta sosai,daga gaba kuma an dan yafito wata kadan ta kwanto kamar baturen England haka ya koma ba kara min kyau yayi ba kamar dan kwallon kafa.

Ba tare da yace mata komai ba yaja mota suka bar gidan,yau Sardauna ba kida aka sa ba karatun Qurani yasa a motar,
Malama Ramlat tana ta faman hawaye ana gogewa da tissue kafin kace me ta karar da tissue din da ke motar Sardauna a kwalinta tsabar iskanci ta zubar dasu a kasa ta cika kasan kazarta da tissue,
Bai ce mata komai ba sai ma da yazo danja ya siyo mata wata tare da mika mata daya,fisgewa tayi ta goge idonta da hancinta ta jefar,kafin ta dago ya kara zaro wata ya miko mata,kawai karba takeyi tana dirje idonta wanda yayi jajir ya Kode fatar Idon kanta da hancinta ya koma red sabo da gogewa.
Take away ya mata na kaza da fura,duk da kukan da take saida tayi murmushi taga kaza,
Luf kakeji ta daina kukan harda cewa iceko dai ka siyo pad da yawa sabo da tsaro kasan ko duba kayan banyi ba,ta yagi cinyar kazarta tare da lumshe Ido,tace ita kaza tafi komai dadi kenan ko?

Bai ce mata komai ba sai dariya da yayi kadan,ta kara magana yanzu wa zai dinga sai min kaza kullum ina ci ai dole naki son makarantar nan Na Mami Ku laifina kuke gani,kallonta yayi kadan tare da amaida hankalinsa ga tukinsa,ka siyo min Madara da bounvita?cornflakes da indomie? Sardauna yace harda Dambun Nama Mami tayi miki yana nan ciki zaki gani...Ashe nan ma zan dinga cin dadina ko? Sosai ma indai kinyi kokari to kudin kaji zan na turo miki ko yaushe a accnt din da na kaiki kika bude rannan, rau rau tayi zatayi kuka tare da cewa ni bazanyi kokari ba,Jakar aji ce ni,
Tsaki Sardauna yaja ba tare da yace mata komai ba, kazarta taci ta koshi tare da rage ta anjima,idan ta huta sai ta bude yar ledar tare da yago kazarta ta tura a baki tare da rumurmushe kashin tana Santi duk sanda taci kazar sai tayi surutu,a hakan ma tasa ya siya mata dafaffiyar gyada,Aya,data,dabino da coconut wai duk in ta sauka zata ci abinta,Coconut sai ya siya mata kwallo uku wacce ba a fasa ba, lallai yanzu na fara Jin zan iya Zama a makarantar nan inci Aya ta da kwakwa nayi dan girki na.
Sardauna yace har kudin cefane zan baki,dadi ya kashe Ramlat tace ai na zata ni zan nemo na cefane da kaina,
Harara ya watsa mata Jin shirmenta tare da cewa wai kin dauka Almajiranta aka kawoki ko me,
Kuma Saura kice baki da aure ko waye ko wace kice ke kina da aure,kinji dai fadan da Mami ta miki,banda kawaye kwashe kwashe,maza banda kulasu,karatu kawai zakiyi kuma karki na Zama da yunwa kullum ba skipping meal daga sau uku sai zuwa sama kinji ni ko,
Kuka ta fara an takura mata kawaye ma baza tayi ba sai karatu an cuceta,yace sannan bafa iya boko zakiyi ba shi yasa baza ki zauna a hostel ba sabo da Saturday Sunday zaki je wata Islamiyya kina daukan karatu makarantar matan aure ce.
Ai kuka ta kara sosai tace ni ina da na sallah ya isheni zaman duniya,nasan na sallah da wasu abubuwan sun isheni rayuwa,Sardauna yace sai kiyi kuma na rigada na biya komai kuma dole kije,to wai a ina zan zauna?Mami bata fada miki ba? gidan kawarta ce sosai Zaria take auren wani lecturer yaranta 5 duka mata ne kuma duk sun girmeki guda biyu ne basu gama degree ba,amma uku suna da Masters ma,
Ramlat ta hangame baki kace gidan yan iska ne kawai harda Masters ba aure,kina musu rashin kunya zaneki zasuyi kuma gidansu kika je dole kiyi biyayya,
Fari tayi da Ido tana murguda baki Allah kiyaye wlh basu isa ba sai dai mu daki juna,Dariya ma ta bawa Sardauna yanda take ta faman wulwula idanu ita wai ga yan mata.

Wani katon gidana me kyau ba laifi dai da gani ba a talauci a gidan,gidan basu da nisa da Makarantar su Ramlat,Islamiyyar kuwa a jikin gidan da aka kawo Ramlat take.
Katon gate aka wangale suka shiga ciki yan mata su biyar masu matsagaicin kyau lukuta lukuta suka hango a tsakar gidan ko wacce ba dankwali a kanta suna zaune saman Katuwar tabarma ko wacce da laptop a gabanta suna latsawa,ga wayoyi maka maka a gefen kowacce,wata a ciki harda glass fari irin boko ya ratsata,
Juice ne a gabansu cikin glass cups suna korawa,gefe chips ne a plate.
Motar Sardauna suka bi da kallo wacce ta tsaya yanzu,

Ramlat kuwa kallon matan kawai takeyi kamar iyayen mata rufda rufda dasu,dariya ce ta kamata da kyar ta danne Sabo da kuncin wata a ciki kamar bread,

Fitowa Sardauna aayayi abin mamaki matan nan suna ganin Sa suka saki ihu da hayaniya Sardauna dan duniya,dama kana gari?Wata a ciki tace yaron nan ka girma wlh yanzu Kaine haka,daya a ciki tace Amma fa ka kara kyau sosai,sai tsokanarsa sukeyi tare da binsa da mayen kallo kamar zasu cinyeshi,yar wacce bata cika kiba ba a cikinsu ce tayi hugging din Sardauna ba zato ba tsammani tana ta manne masa a jiki tare da tambayarsa Mami,

Basu san Sardauna bai son ace masa yaro ba har aure ne dashi za a ce masa yaro bakin ciki ya lullubeshi nan take Mood dinsa ya canja musamman banzar da ta wani rungumeshi kucaka tayi dirty da yawa cewar Sardauna a ransa,a fili kuma ya danyi dariyar yake kadan yana basarwa cike da isa da gadara yace ya kuke ina Ammi?
Tana ciki cewar babbar ciki,Ramlat ya budewa Kofa tare da cewa fito yan mata,
Tana fitowa suka zuba mata ido,Ramlat kuwa a doluwarta ta fito tana tafiya Salo Salo kamar kwai ya fashe mata a ciki,ta rike hannun Sardauna kam ido cike da kwalla taga mata iya mata a gidan ga girma ga kiba gasu sun wani hade sosai yan gayu dasu.
Sai ta raina kanta tana kallon ta waye sai ta ganta wata ajawo da ita,a ranta tace da gaskiyar Mohd Ashe ni kidahuma ce.

Ido suka zubawa Ramlat suna kama da Sardauna amma su basu San yana da kanwa ko yar Uwa ba,yan mata fa su dukkansu suna sha'awar Sardauna sosai,inama da ace Saurayin su ne ko romancing sunyi dashi duk da cewar sun fishi shekaru.
Musamman da suka ga ya girma sosai kamar dan 26yrs,ko wacce cikinsu kwadayinsa takeyi, wani banzan kallo suka watsawa Ramlat tana gaishesu amma babu wacce ta kulata a ciki,shi kansa Sardauna yaji haushi,

Kallonsa Ramlat tayi hawaye suka sulalo mata,ta bashi tausayi,kawai sai ya tsuguna a kasa yace hau baya kinji yar autar Mami, aiko ta dane masa baya tare da sakalo hannayenta ta wuyansa ta kwantar da kanta a bayansa tana goge hawaye, yan mata suna kallon ikon Allah ko wacce tana Jin ina ma ita Handsome Sardauna ya goya a bayansa haka,
Haushin Ramlat suka ji sosai suna gani ya shige cikin palonsu da Ramlat a bayansa,
Ammi tana Palo da bakuwarta Sardauna yayi Sallama dauke da Ramlat,Ammi cike da fara'a ta amsa masa tare da tambayar Allah yasa lafiya Ramlat take taga ya goyata,
Yace Ammi rigima take ji da kyar fa tazo garin nan,
Murmushi tayi tare da cewa lallai Sardauna an tauye maka hakki an zalunci rayuwarka,kamarka ace an aura ma wannan da shekara daya ka girmeta fa,ai tsufa zatayi ta barka,karon farko kenan da Ramlat taji zafin magana akan aurenta da Sardauna ance zata tsufa ta barshi da kadan ya girmeta,
Sardauna ma baiji dadi ba amma yace kai Ammi ni ba aura min akayi ba da kaina na zabi a bata kuma ni ko yar 40yrs ce indai ina sonta zan aureta mene a ciki.

Share zancen Ammi tayi tare da cewa Mami tace ai bata son karatun ma,Sardauna yace ai dan bata saba bane tana sabawa zata so,tabe baki aaAmmi tayi tare da kallon Ramlat gwara ki tsaya kiyi karatu yanzu an waye nan ba kauye bane,haka Mamanki Hafsatu taki yin karatu karshe ko mijin kirki bata samu ba,ai a zamanin nan indai bakayi karatu mai zurfi ba to ko mijin kirki baza ki samu ba,yanzu maza sai mai ilmi suke aure,
Sardauna yace tab ni kam wlh kawai dai ina so tayi ne amma ko batayi primary ba indai ina so aurenta zanyi mene a bokon.kuma miji da matar kowa a rubuce suke ko da ilmi ko ba ilmi sai ka aureshi kuma sai kiga kafi son marar ilmin ma matukar tana dana addini,

Sai wacce batayi ko primary ba ta auri shugaban kasa ko sarkin Saudiyya.
Ai kai yaro ne Baza ka gane illar ba sai nan gaba anyway sannu da hanya.ina Mami,cike da labadi Ramlat ta gaishe da Ammi ta amsa da sakin fuska ba laifi Sabo da jinin Mami ce shi yasa.

Kayan Ramlat Sardauna da kansa ya kai mata dakin da Ammi ta bata,Ramlat ce kadai a kasa amm dukkansu yan gidan a sama suke kuma da rooms empty a saman Amma ta bawa Ramlat a kasa jikin na yar aikinsu.
Ammi tasan Baban Ramlat talakane futuk shi yasa,amma tana son Sardauna Sabo da tasan Babansa kusa ne a kasar nan,sannan abinda yasa take kawance da Mami saboda Baban Sardauna Danta ne ko banza ace kawar babar Alhaji Kabiru Fakas ce.
Tuni take damun Mami ta kaita gidan danta su nemo inda yake a kasar nan Sabo da ta dinga zuwa tana dangwalar arziki.
Hafsatu kuwa tasan ba wani karatu tayi ba,tana kauye ga auren talaka me zatayi da zuriarta,
Dalilin da yasa ta ce a kawo Ramlat ta zauna a wajenta kar ta zauna a hostel kenan Sabo da tana so ta kara Kusanci da Mami tare da Sardauna,burinta ma bai wuce a cikin yayanta daya ta auri Sardauna suci dukiya tunda suna Sa rai watarana dole zai koma wajen ubansa,
Ko banza yanzu zasu dinga ganin Sardauna yanda zasu samu daya a ciki ta cusa kanta wajensa ko da sun girmeshi ya auri daya.
Ammi mayyar kudi ce da karya ita burinta ace gata yarta na auren wani,ko dan wani kusa,ko ta Zama kawar matar wani me Naira,ko ma dai ta yaya ta kulla alaka da mai Naira,shi yasa duk kawayenta da na yaranta da duk wanda suke muamula dasu to masu kudin gaske ne.kunji fa Hajiya Hadiza Ammi.

Mijinta kuwa Professor Hafizu Isa( Papa) shi kawai ayi boko in dai kana so kuyi hira ko ya zauna dakai to kawai ayi harkar boko da boko,idan baka da Masters bazai baka yarsa aure ba,kuma ya Zamo kana da babban aiki,shi dai kawai ayi zancen boko,ina kaje boko ina ka dawo boko,kuma baya kunyar maganar banza a gaban yaransa ko wacce tazo bakinsa fada zaiyi ai wayewace kar kaji kunyar kowa ko me kayi niyyar fada ko a gaban ubanwa kawai ka fada shine ya nuna kai ka waye kayi ilmi kana ganewa,
Amma idan yaga kana kunya kana kasa magana a gaban wasu sai yace ya kamata kaje asibiti a duba ka cutar kunya da tsoro ce ta kamaka,kaje likita ya baka shawarwari ya aunaka idan da magani a baka,ko hadisi ko Aya idan ka kawo masa to shi kuma sai ya kawo maka law na wani kasurgumin bature,su Charles laws,su Marvel's etc haka zai ta kawo laws bazai saurari Hadisi ko Aya ba.
Su kuma yaran su biyar, Nafeesa chuchu,Zara juicy,Muhibbat Baby lilla,Maryam merry,sai Zulaihat Ichichy.gaba daya sunayensu na gaskiya ba a sansu dashi ba sai nickname,
Tunda suka taso a kangare suke basu da tarbiyya ko kadan Islamiyya ma basuyi ta kirki ba suka ce sun girma sun daina yawa ce,
Mami Sam bata san yanda suka lalace ba sabo da danta me kudine ko sunje mata ko taje cikin mutunci suke mata komai sabo da kudi kamar zasu goyata,shi yasa ta yarda Ramlat ta zauna dasu,
Iyayensu basa son suyi aure sai da Masters gasu dama ba tarbiyya,karatu ba Illa bane amma an fassarashi daban kowa da yanda ya daukeshi,wasu dalili aka dora akai marasa amfani.

Su dai su Chuchu manufar karatunsu daban,kuma sabo da kudi sun lalace gaba daya,Ichichy itace karamarsu kuma ta dan fisu sauki da dan hankali kadan duk cewa itama hakan take amma bata cika wulakanta mutane ba,kuma ita bata kaisu tsayi da kiba ba.

Kafin kace Me Ammi ta cikawa Sardauna gabansa da kayan Alatu tana rawar jiki sabo da kudi,
Sardauna ya dade rabonsa da gidan tun kafin ya tafi London karatu,sai yanzu ya gane ba gidan Zama bane gidan dole watarana ya dauke Ramlat idan har ya tabbatar bata Jin dadi ko zata lalace.

Ramlat anga kayan dadi fa,gashi bata ga fuskar ci ba,bakuwar Ammi matar wani dan majalisa ce sai ji da kai takeyi haka ta tashi driver ta ya dauketa ta tafi.


Please Login or Register in order to submit comment