Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shima rufin asiri ne sai karfin hali da zuciyar yin Abun.

Fitowa sukayi gaba dayansu abin sha'awa Salma na kafadar Mohd,Hafsatu da Idrisa suna gaba Shaheed da Daddy suna tsakiyarsu while Ramlat da Mohd suna bayansu ,Mohd sai munafuncin su Hafsatu yakewa Ramlat yana kalli Umma wlh fari takewa Kawu ko dama ita kika gado?
Ramlat tace na fada ma fa ba wani shiryuwa sukayi ba haka sukeyi watarana zaka gani kuma dama mu mun san haka suke ai bari ka gani zai wahala gobe basuyi fada ba

Motar Sardauna suka shiga Ramlat da Mohd a gaba tare da Salma,Idrisa da Hafsatu tare da su Shaheed suna baya.
Jan mota yayi sai cikin Jigawa city
Wuraren shakatawa ya kaisu iri iri suna shan Ice cream da Sauran kayan ciye ciye,kudi ya dauko sunkai dubu dari a Cikin evelope mikawa Ramlat yayi tare da cewa rike wannan duk abinda zamu siya kawai ki biya kudin
Hannu biyu Ramlat tasa tare da cewa Auzubillahi minalshaidanirrajim Bismillahirrahmanurrahim sannan ta karbi kudin kamar ta dauki Jariri

Harara Idrisa ya gasa mata tare da cewa Har yau shirmen naki yana nan ko? ai baza ta daina sokonci ba indai Ramlat ce cewar Hafsatu.
Ranar har kusan dare suna can shakatawa basu dawo ba,Idrisa yau ba shaye shaye amma ya damu sabo da ko wiwi Bai dan zuka ba, kallonsu yayi tare da cewa Ina zuwa da sauri ya zaga bayan Building din dake park din tare da Zaro wiwi a aljihu ya kyasta Ashana ya fara zuka,sai da yasha kara Uku sannan ya dawo wajensu, Hafsatu da Ramlat tuni sun San shaye shaye ya tafi,lokacin da ya dawo sai kaurin Wiwi yakeyi yana shan tom tom sweet.
Suna gamawa suka dauko hanyar dawowa cike da nishadi Yara suna murna sunsha yawo da kallo.

Hafsatu uwar son yawo sai farin ciki takeyi Idrisa a mota ya kalleta tare da cewa ai duniya tayi mana daurin Alewa ta kulle daga sama har kasa da tuni bama wannan kauyen,Hafsatu tace ai birni ta kimu bata kaunar mu idan muka je maimakon ci gaba sai baya,Tsaki Idrisa yaja tare da cewa ke dai bari na gama tsara rayuwata nayi planning Amma baya tafiya dai dai.

Tabe baki Hafsatu tayi tare da cewa a hakan?wanne planning gareka da kana da shi zamu zauna haka?da ka rage abinda kakeyi wlh ai dole Baza ka taba ci gaba ba,Kana tauye mun hakki,ai Idrisa Baza ka taba yin gaba ba kayi kokari dai ka nemi lahira ka gyara halinka,Idrisa da masifa yace uban me nakeyi?ke baki ga abinda kikeyi ba sai ni? gantalalliya ni da aka cuceni aka rufeni sannan na aureki da nasan hakane ai da wata tsaleliya zan nema,

Hafsatu tace ai wlh ni aka cuta kowa ya kalleni yasan ba kalarka ba ce nafi karfinka,jinin larabawa duk yarana ni suka ebo da kai suka ebo ai da sai da Suratul Yusuf zasu shiga,
In banda hakuri da zaman yaya me nakeyi dan kauye jinin kauyawa.kowa yayi shuru a motar yana jin fadan su Kawu Idrisa girma ya fadi,kayi kai kadai ni a gaban surikina nake Bazan kula ka ba Hafsatu ta kara fada.
Idrisa yaja tsaki da kwafa yace za a je gidane zakiyi bayani.
Hafsatu tace ai ni ba zama zanyi ba wlh tuni zan bar ma gidan naka ehe.

Ramlat ta juyo tare da cewa dan Allah Umma wai mene haka?Ubanki wato ubanki kike so ko to wlh Baza a hanani magana ba indai ya min sai na masa,ni bakya kaunata dama na sani ai.
Sardauna dai yana driving a ransa yana lallai su Umma yan Koko ne na gaske basu waye ba,kai Baza su waye ba ai yanzu ba a fada tunda Baza su waye ba kuma ba yan gayu bane bazai kara daukansu yawo a motarsa ba dama Sabo da Ramlat yayi don taji dadi,

Sardauna karku manta baya mu'amula da wanda ba wayayye dan gayu da wanka ba duk Sabo da Ramlat yayi hakan sai kuma albarkacin Umman su Ramlat jininsu ce sai yaran da yake tausayi Amma idan ta Idrisa ne ko motar haya bazai zauna kusa dashi ba.

Bayan sun dawo Sardauna duk a takure yake ya matsu ya bar garin,Ramlat ma ta gano hakan suna zaune tsakar gida Saman tabarma yayi shuru,kamar daga Sama suka ji amfara Shela a kauyen kan Hafsatu.

Yeeeee.....kuwaaaaa...Jama'a....mai..gari...ya....aikoni....Ya....Ba...da....sanarwar....gaggawa.....cewar ..duk....wanda....yaga.....Hafsatu Matar....Idrisa.....za...a....ganta....Wata....doguwa....me....kama....da....Aljana......kar...kowa....Ya...tallafa...mata...da...abinci...ko...kanzo...kuma...ko...Naira...daya...kar...a...bata....kyauta..ko..rance...idan...ta...kawo..kayan... mijinta....abinci....ko..kayanta...kar...wanda....Ya..siya.
Hafsatu har jari an bata tace baza tayi Sana'a ba kuma ba fasa yawo zatayi ba,shi yasa suka mata haka don dole ta daina yawo ta kula da yaranta.


Haka duk garin aka dinga sanarwa lungu da sako,Ramlat tasha mamaki Amma bata ce komai ba,Daddy dan yaron yace Alhmdllh gwara haka zamuga da me Umma zata tafi yawo ta hau mota ta barmu mu kadai,Ramlat ta make masa baki,ashe Hafsatu ta ji me Daddy yace ta fito a fusace ta dinga dukansa da kyar Sardauna ya karbeshi.

Washe gari da rana Sardauna da Ramlat sun shiga cikin garin Jigawa katsam wani Napep ya sha gabansu tare da gangarewa kasa da alama Passenger zai sauke,

Sardauna yazo dai dai Jufatu yayi parking sun fito kawai Sai ga wani dan matashi da bazai wuce 18yrs ba da gashinsa yayi masa shegen askin yan iska kida na duka a Napep dinsa,

fitowa yayi yana duba Napep din juyowa yayi suna magana da wani kawai suka Hada Ido da Ramlat,
Ihu Ramlat ta saki tare da kwalawa da karfi Fahat....Fahat nunawa yayi bai ma santa ba sam da Sauri ya shige Napep dinsa yaja yayi tafiyarsa.

Sardauna ya karaso wajenta yana girgizata ke lfy kuwa? Fahat wallahi Fahat ne na gani shine a Napep din can yana tukawa.
Tunda kikaga bai kulaki ba maybe ba shi bane kama ce,wlh wlh Fahat ne waccen,to naji karki fadawa kowa Sabo da kar su Umma su shiga damuwa nan gaba zai nemesu da kansa.

Da kyar ya lallaba ta tayi shuru da zancen,suka siyi abinda zasu siya sannan suka wuce wani Suya sport da ake zama ana ci a wajen,
Kaji iya kaji Gasu nan gaban Ramlat Sardauna yace sauri kici mu wuce tafiya zamuyi yau din nan na gaji da falavar kauyen nan kullum abinda zai dameka daban kala kala har zazzabi jiya nayi akan matsalar su Kawu zaman nan nasu sai su.
Ramlat tace yanzu ya zamuyi da Daddy tunda Shaheed ya samu masu rikeshi kafin nan gaba idan kayi kudi?
Tunanin da nakeyi kenan wlh kuma Daddy yafi Shaheed rashin ji zai iya lalacewa ko yaushe,tunanin da nakeyi tunda Kawu bazai barshi hannun Mami ba ko mu kaishi gidan Su Naufal kinga gidansu sojojine ko ina baza su bari ya shiga ba bare ya karbo shi,Sai a kaishi Makarantar sojoji ta Kd idan sunyi hutu ya tafi gidan su Naufal kafin muga yanda Hali zaiyi,ita kuma Salma a kyaleta dole sai nan gaba.

Hannu ta Mika masa suka tafa yace yarinya ki jira nayi arziki zakiji dadi komai sai an miki,Makkah da Dubai duk sati ,Manyan motoci na Alfarma,kaya kuwa room guda na sawarki,sai kin koma Sarauniya,ganinki sai an cike form,mune London mune Germany,mune France,ke kiyi addua maybe ma a Canada zakiyi masters,kuma sai anyi wedding party namu a london.
Ramlat sai dariya take tana washe baki kamar kudin sunzo,
Harda cewa Motar milyan Hamsim za ka siya min ko dari ta yarona ko ta yarinyar da zan Haifa me zuwa nan gaba ma masu tsadar gaske wow ya ka ganni Ramlat ta wani yi yanga tana yarfa hannu kamar kudin sun samu,mutanen dake wajen suna jinsu sai tsara rayuwata jin dadi da kudi sukeyi,sai dariya akeyi a wajen wani yace Allah sarki kuruciya basu da matsala.

Sardauna yace taya yar tawa zata hau motar kinki yarda ki haifo ta ko shi sun gaji da jira a haifosu,nan ma mutane suka kece da dariya,sabo da wajen dan karami ne ko kayii kasa da murya sai an samu wasu sunji me kace.
Allah kuma kaga hakane na haifo ta kawai kar kudin nan suzo bamu da yaran nan,

Sardauna farin ciki ya lullubeshi ya rada mata a kunne ki daure ayi abin nan ko dan kiji dadinsa, daga ganin kalata sharp Shooter ne ni duka daya dauka ne,

Ramlat na dariya ta rada masa shima kasa kasa ba wanda zaiji tace ai ni ba wani sauri nake na haihu ba Nafi so dai na dinga cancana dadina ina jinsa kadan kadan a nutse,
Idan zaka sha giya kasha ta dubu hajiyata cewar Sardauna.

Mutanen wajen duk sun gama sun tafi daga Ramlat sai Mohd a wajen Ramlat tace tsaya na murkushe Kajin nan first nan Ramlat ta fara lashe kaji sannan tace wai da Kajin gidan gona da na turawa da na Hausa wanne suka fi dadi?na kasa tantancewa,
Sardauna yace ah na turawa sunfi dadi,tace ina bazai yuwu ba domin na gida natural ne ba chemical,
Kara Yago tsoka tayi a hankali tace ina fada ma wato ita Kaza tayi a rayuwa,Sardauna bai ci ba yana kallonta yace haba Rago ya fita tace kai ina kauce gefe Ai ko miyar kaji ce kaci sai kaji kamar ka tsinke yatsanka,

Karfa kace Santi ne gaskiya nake fada,kuma masu gashin nan sun iya kaji wani Maggi Amma da gani sai an tsuma kazar nan a kayan hadi ko?Sardauna dai dariya kawai yakeyi Ramlat taci koshi tace Alhmdllh Allah ya kara arziki da budi nan gaba muci ta kullum kullum tafi haka duk da cewa kullum sai naci to Allah sa naci ta kasar Moroco ma haka ko ta Jafan,Allah mun gode maka da kayo mana kaji ka halattamana cinsu, dariya Sardauna yakeyi sosai yace inama kwadi ne Kajin,Ramlat tace ai indai sunansu kaji ba kwadi ba to cinyesu zanyi.

Mikewa sukayi tsaye ga mutane alhazawa wasu sun shigo wajen suma kowa yana cin nasa da wasu yan mata da samari Amma Sardauna a gaban mutanen ya riko kan Ramlat a hankali tare da manna mata kiss a lips,sannan suka wuce a kudin da yabata a jiya na envelope ta zaro ta biya kudin tana gadara da yanga ita ga me miji yana sonta duk kudinsa ma ahannunta suke sai dai idan an siyi abu kawai ta zaro ta biya yana tsaye,mijin Hajiya tana juya mijinta,

Suna komawa gida sai ga Lantan yar Uwar su Ramlat itama budurwa ce tunda taga Sardauna take kaunarsa shi yasa kullum ta makale gidan su Ramlat dan kawai ta dinga kallon Sardauna,
Sai tazo jikin Ramlat kullum ta zauna suna hira tana kalle mata Sardauna,Ramlat bata gane ba Sam,
Yau da suka dawo Lantan tazo gidan tana ta faman kallon Sardauna idan suka hada ido da Sardauna sai ta kashe masa ido daya watarana kuma ta murguda masa baki,
Sardauna shi bai ma san tanayi ba ya zata tabin kwakwalwa ne da ita takeyin haka ko nakasashiya ce,Yau ma yana zaune jikin wata bishiya saman kujera tsakar gidan yana latsa waya,dagowar da zaiyi sai suka hada ido da Lantan ai kuwa ta Dage masa gira tare da murguda masa baki tana gatsine,wani muni da tayi ba shiri Sardauna ya dauke kansa gefe,
Tace kai... kai..tana daga masa hannu, bata san sunansa ba sai kai take cewa,Sardauna ya juyo tare da kallonta,ai Lantan ta kusa suma Sabo da kyan da yayi mata,Fari tayi masa da ido tare zaro masa Harshe tana masa gwalo wai ita a dole love take nuna masa,

Sardauna takaici ya lullubeshi ya dauke kansa yana tsaki,amma Lantan bata hakura ba a ranta tace Allah sai de ka hadamu da Ramlatu yar uwata muyi kishi na gani ina so.

Mikewa Lantan tayi tare da matsawa kusa da Mohd tana leka wayarsa tana hangame baki,Sardauna da Sauri ya mike yana matsawa baya ta matso tana ka tsaya kai ka daina tsoro nice Lantan wallahi na gani ina so,

Sardauna ya gasa mata Harara Lantan ta sheke da dariya tare da cewa yo ai ni na fika iya kallon nan harda haka kaga kai ta masa murgude murgude da kumatun ta luhu luhu,

Zata matso wajensa Sardauna ya kwalla Ihu yana kwalawa Ramlat kira Queen....Queen of beauty....Baby....Sardauna ya furta cikin muryarsa ta yan gayu,

Ramlat ce ta fito cikin shirinta me kyau tare da cewa Lfy My King kaji fa Masoya ga Queen da King,
Lantan ya nuna mata yana wannan Aljanar ce take wani abu ni dai a fitar da ita daga nan gidan,
Lantan me kikayi masa?Ramlat ta tambaya tana kallonta,Harara Lantan ta watsa mata cike da kishi tace ina ruwanki ta murguda baki tare da cewa gani nayi ina so sai me,mijin mace hudu ne ko ke kadai aka haifowa shi.
Ramlat tasan Sarai Lantan karfi ne da ita idan ta kulata duka zatayi mata domin tasha zaneta,
Shike nan zaki ga abinda zai faru tunda kike son mijina.
Dakin Hafsatu ta shiga,Lantan tasan Idrisa Ramlat zata fadawa kuma Idrisa ba hankali karyata zaiyi Sabo da ba a taba masa Yara a kwana lfy Amma shi zai iya musu duk abinda yaga dama.

Guduwa Lantan tayi daga gidan tana cewa kai ina jiranka idan ka shirya
Ramlat dan Gulma da kuka ta shiga Dakin Ummansu ta samu Idrisa yana hutawa Umma na gefe,kawu zumbur ya mike yana lfy?me akayi miki?uban wa ya miki wani abu? Ramlat tana shesheka tace Lantan ce taje ta rungumi Mohd sannan tace tana sonsa sai ya aureta,na mata magana ta mareni sannan tace wai takama nakeyi da kai har kai baka isheta kallo ba wlh sai ku daki juna har kai na fada maka in ka Isa kaje ka sameta ta tafi gida yanzu kuma sai da ta mari Daddy ma.

Da Sauri Idrisa ya mike yace kut kan uban nan,Lantan din ?tace itafa,yace zata cu Kundun Ubanta sai na karyata na girmi ubanta na haifi kamarta ta Isa ta tace zata so mijinki Sabo da rashin mutunci,ba a ja da jini na

Ke kuma banza lusara kina tsaye ta mareki Albasa batayi halin ruwa ba baku gajeni ba,kunyi asarar gado me kyau,sau nawa nake fada muku kar ku bari a nuna muku yatsa ko uban waye ku rama ni na saku.

Muje gidan naci ubanta daga ita har iyayenta a gabanki,Ramlat tace ai Mohd bazai barni ba,to zauna ni bari naje,Fuuuuu Idrisa kafa ba takalmi ya fita,aiko a jikin bishiya ya hango Lantan tana cin gyada ba zato taji fas an masge mata keya,

Sai da ta daina gani na dan wani lokaci sannan ta juyo da masifa,ruf ta rufe bakinta ganin Idrisa ne,Mari ya zabga mata sai da taga wuta yana zaginta yana rankwashinta har gidansu ya samu Baban Lantan yayi musu tatas kuma yace kar ya kara ganin Lantan a gidansa zumuncin ba dole baya so ya daina zumunci dasu ya ciresu daga danginsa.

Ramlat tasan abinda Idrisa zaiyi dama ta huta da Lantan.ita Kuwa Lantan tace wlh baza ta hakura ba sai dai a kasheta akan haka ma sai ta bi Sardauna birni ta nemoshi duk inda yake ya aureta.

Sardauna sun gama shiri tsab sannan ya fadawa Daddy kar yaje ko ina za a zo a daukeshi za a kaishi makarantar sojoji,Daddy sai murna,Shaheed harda Kuka shi banda shi,da kyar ya lallashe cewar shima nan gaba za a kaishi.
Kudin cefane ya bawa Idrisa suka musu Sallama suka tafi mutan kauye sun basu tsarabar su gyada,kukar miya etc.

Daddy yana ta murna ya nutsu yana sauraren azo a daukeshi.
a Kano yace su kwana a wani Hotel,
Da dare sun gama komai sunyi shirin bacci Babu yanda Sardauna baiyi ba Ramlat ta yarda ayi babbar harka taji dadi Amma taki yarda ita ba yanzu ba sai a gidansu na aure,

Zuciya Sardauna yayi wannan lokacin yace ko Romancing din ma baya so,haka suka kwanta ko wanne karshen bed ya juya baya,cikin dare Ramlat batayi bacci ba Sabo da ta saba da Abinda sukeyi Da Sardauna kullum.
Yar rigar baccin nata ta cire tik tare da wullota kasa ta koma jikin Sardauna ta manne,
Sardauna shima ba bacci yake ba ashe duk zuciyar da yayi sai yaji ta gudu,baya fushi ko kadan saima juyowa da yayi suna facing din juna.

Kirjinsa ta shafa da yatsanta sai da ya shide tare da rike hannunta da hannu daya dayan Hannun kuma yana shafa fuskarta sannan yace kiyi hakuri na shareki ko? me kike so?shuru tayi tana jin kunya gashi shi yana son abu ta hanashi,
Ya ganeta kawai sai ya share tare da sakin Murshinsa me tsada yana kare mata kallo a hankali Ramlatu ta dinga matsowa da fuskarta tare da manne bakinsu wuri daya,
Nan suka fara Aikawa juna hot kisses,suna sakin numfashi.
Mohd yana kare mata kallo yanda idonta ya canja gaba daya shima wajensa hakan take,
Ramlat rigarsa ta zare masa tare da kwanciya a saman sa,nan fa ta gama kunno engine Sardauna,
Fara kasheta yayi da salonsa itama Ramlat ba a barta a baya ba wajen nuna masa cewar itama fa za a je da ita domin wajen nan Ramlat bata da kunya ko kwaya.
Yau abinda Sardauna yake mata ya zarta na kullum Sabo da taji dadi da yawa har ta yarda suyi Babbar Harka,
Ramlat ta gama fita daga hayyacinta shima haka,
Ko magana kasawa yayi da kyar murya na rawa yace ayi miki? Amma taurin kanta tace a'a ni dai banda shi,Sardauna yace wannan shine last da zan kara miki zancen abin nan,turo baki tayi tana shagwaba to kai sai ka nuna benefit dina ne ni kadai ai sai ka nuna kai kadai kake so zai maka amfani sannan na yarda Amma komai kace wani Xxx nake bukata wato kai baka bukata sai ni mayya,ko tambaya zakayi sai kace wani a samu Yara wato Sabo da Yara zaka yi badan so ba,
Nunawa kakeyi kai zaka rayu ko ba shi baka damu ba kawai sai na yarda nima ban damu ba ehe.

Murmushi ya saki lallai Ramlat tana da wayo watarana tabbas baya requesting cewar shi yake so sai dai yace kina so?,ayi miki?pls ayi zaki ji dadi,ko Baza kiyi ciwon maraba shi Mahaifa take bukata duk baya cewa kansa sai ita.
Kuma ita Ramlat ta fi so sai a gidansu na aure,tsoro ma takeji Sabo da Yara matasa irin su Sardauna kar ya samu wani abu ya hango wata ya rabu da ita,dama gasu yan duniya ita kam ba yanzu ba bare ma da take schl ba a tare suke ba sai ta yarda da yana sonta yanzu kokari zatayi tukun ta tabbatar bazai iya rayuwa ba ita ba first.

Dafta Jibrila ne zaune a cikin Chemist dinsa ginin kasa gefe guda katon dakin kara ne da manyan benchi sunfi goma a nan ake kwantar da patient ana musu Karin ruwa da sauransu.
Wata ce Lami yar budurwa ta shigo Chemist din ta Dade tana son Dafta amma Dafta yace yar kauye ce yafi karfinta,yau ma zuwa tayi suyi hira ko zata dace,Dafta yayi mata kallon Banza tare da Kebe baki yana yatsina fuska,turancinsa ya fara feso mata cewar....


Mu hadu next page reders








AsmaBaffa
🏀🏀🏀🏀🏀🏀
🏀🏀🏀🏀🏀🏀


DUK INDA TA FADI





166-170





Official





By
AsmaBaffa







HBD my Flower, Sardauna yana miki adduar Karin year da kikayi ban dashi,yace shine ya dace ya kara shekara ba ke ba,shi da ya matsu ya girma kin masa wayo wai.


Maman Aliyu ta ina gaisuwa,Jamila Sule yar Amana ina Hajiya Jamila ta buya ne? Jannat ina murnar dawiwarki.

Godiya fans.

wanda ban muku page ba masu sharhi a hankali kafin na gama Novel din nan Insha'allah zaku ji ku a ciki.





Dafta Jibrila yana magana cikin turancinsa I will do not Love you yarinya kazama Village girl because of u raina min wayo zaki zo wiz leg like mosquito,i pass u wiz everything,Look young woman,look at me, am Doctor wiz original certificate,zagaya budurwar yayi tare da cewa look my big Chemist like Sahad store in kano city,Wallashi I pass ur power(nafi karfinki)my faza he is a mai gari of zis town,iam a rich,look at you ur kwankwaso is like muciya wiz atamfa Zani.
Yarinya taji Jibrila yana ta turanci yana yatsina fuska sai tsoro take ji,tace na higesu dan Allah Dafta wlh ban iya turanci ba ka fada min da hausa,Dafta yaja tsaki u are jahilai in zis village,u have never knw anything empty head Ram Brain,budurwa ta fashe da kuka tana bashi hakuri,
Dafta yace u r not crying u are laughing (ba kuka kike ba dariya kike yarinya hhh).

Ze Middle of me and u(tsakanin ni da ke) is to coming and give u a injection like quinine,gentamacin,arthemeter,and also paracetamol injection but wiz love no..no.no never ever wallashi,dont carry ur self like Lady no u are nothing but kwaila.tsaki yaja yana tabe baki ga mutane damkam a chemist ana ta sauraron turancin Dafta suna sha'awa ina ma sune,Dafta ganin ya birgesu yaci gaba da cin uban wannan Budurwa Lami,
Go to ze Zaria city and look yan mata da yawa jibgas jibgas zey are following me like tauraron dan Adam,go to ze Zaria and see my frnd very beautiful and wise,iam a Wise wiz money,waje ya nuna mata look my Car Honda accord,
Mutane dai sai birgesu yakeyi Jibrila yace pls dont me open my eyes and see u inside my chemist my business place my life my tattalin arziki.

Lami ta fashe da kuka tana dan kaga Bana Jin turanci shine ka zaki iyayena ka tsine min albarka ba komai duniya ce ta isheka amma bazan daina Sonka ba,Jibrila yace u don't have class u are not going to ze work shi yasa,(baki da aji bakya zuwa aiki baki da aikin yi) amma ni I pass ur power, (na fi karfinki)tana tafiya yaja tsaki tare da cewa banza Wiz head snake,

Mutanen dake wajen suka kyakyace da dariya kamar sunji me yace tare da cewa Dafta me jama'a Dafta me Jama'a gaskiya matan sunyi yawa ina ma nine suke kawo Kansu wajenmu amma jibi Lami fa duk inda Lami take ji da kanta kuturun uba lallai Dafta duk garin nan ba kamar ka. Dafta ya kara doro yana yanga yace ai Lami sai Ku yan jagwal

Please Login or Register in order to submit comment