Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gode Kakus gaskiya kina Sona Mami,gafara can ba ke nake so ba dan jikana nake so yazo duniya kato dashi,Daga Sardauna har Ramlat dariya sukewa Mami wai wasa takeyi babu wani ciki.
Da Ido Sardauna ya yiwa Ramlat magana tazo suje Bedroom,Fruits Salat da dambun naman kaza ta kawo masa,kafin ya huta ta cika masa gabansa da girke girke na zamani masu matukar dadi da kyan kallo,saida ta cika masa tumbi tana jifansa da kallon dake rikitashi da kyar ya daure ya kara yin wanka yace tazo ta bashi abinda yake bukata Ramlat tace taki sai ya dawo da dare,ba yanda baiyi ba tace sai dare zasu kwana sunayi,Sardauna yace to shima ya fasa fita wajen aiki sai gobe tunda baza ta bashi zuma ba,d a wayo dole Ramlat ta bashi abinda yake bukata.

Washe gari kuwa 12pm Lokacin Sardauna Bai dade da fita wajen aiki ba Ramlat ta gama komai ta fesa sabon wanka tana kwance tana kallon wani film cikin sabuwar katuwar wayarta da Sardauna ya siya mata kwana nan Turawan Ne suka fara Romancing juna sosai,Ramlat taji ba wanda take bukata irin Sardaunanta yanzu,sha'awarta ta motsa ba ta wasa ba,
Number Sardauna ta kira bugu daya ya kirata back,Sweetheart ya kk?naji muryarki wani iri? Sardauna ya tambaya,Ramlat a hankali cike da kasalalliyar murya tace My king?naam Sardauna ya amsa yana lfy?can kasa tace King tana shgwaba me ta da hankalin masoyi,Sardauna tsigar jikinsa ta tashi yarrrrrr ajiyar zuciya ya saki sannan yace me kike so Babyna?murya a dishe Ramlat tace You My Love,I need u Badly,ni ka dawo gida yanzu pls a bar aikin yau,Murmushi Sardauna ya saki na Jin dadi yayinda son Ramlat ya kara sukansa Sam bata boye masa idan tana bukatarsa ba kamar wasu matan ba sai dai namiji yayi ta nema ko tana so baza ta nema ba wai kar ya rainata,hakan na sa namiji ya gaji shima kuma bazai dinga Jin dadi ba sai yaga kamar shi bakya sonsa baki damu dashi ba ko abinda yake miki bakya Jin dadinsa sai ya rage masa kwarin gwiwa shima ya ja baya yana tunanin ko dai yana da matsala ba kya Jin dadinsa.

Yaran Sardauna kaf sun San yanda yake tsananin son matarsa ko me yakeyi idan Ramlat tace a bari ko yazo to ba makawa sai yayi abinda tace sai abinda tace basusan itama Ramlat Sai abinda Sardauna yace takeyi ba.
15mnt sai ga Sardauna ya dawo cikin dakakkiyar milk yadinsa sharashara fitted dinki na maza,stile din gashin yanzu ma kalarsa daban,M aminsu na kitchen tana girki yau ta hana Ramlat tace ta huta, Ramlat najin shigowar Sardauna ta fara boye fuska wai kunya,Sardauna kuwa wanka ma zai shiga tayi Sauri ta rikeshi tare da rada masa ni bazan iya jira kayi wani wanka ba,
Lfy kike yau kuwa Queen?Ramlat tace au dan na nemi mijina shine bani da lfy?amma ai kasan dama ni akanka ba hakuri gareni ba,Dariyar Jin dadi Sardauna ya sakar mata,to ya zakiyi Babyna idan na tafi Abuja kin san nan da 2days zanje wani aiki zamu hadu da Naufal ma,Ramlat tace zan iya hakura tunda baka kusa Amma dan Allah ka tafi dani kaji?
Indai zakije ai ni nafi son hakan Bazan iya yin komai ba idan bakya kusa dani,Ramlat tace kyale maganar sai anjima ayita yanzu kayi abinda na kiraka.
Ba tare da bata lokaci ba Mohd yace ni dama haka nake so ki koma kullum kinga da sai nafi haka jin dadi kullum ki zama cikin sha'awata da na gama jin dadin duniya tunda ni kinsan bana gajiya dake.Ramlat dai
anyi shuru ana karbar sakon dadi cikin jikinta sambatu takeyi iri iri ita da gogan nata.








Dan Allah Readers ayi min Afwa zaku dinga gani bana muku posting ko yaushe ina yin wani aiki ne bani da time da kyar nake daurewa ina muku Sabo da bana so Novel din ya samu matsala na bata labarin shi yasa bana yi kullum..



AsmaBaffa
🏀🏀🏀🏀🏀🏀
🏀🏀🏀🏀🏀🏀

🏀🏀🏀🏀🏀🏀
🏀🏀🏀🏀🏀🏀


DUK INDA TA FADI





236-240





Official





By
AsmaBaffa







Kuna da matukar yawa Readers fans wanda nake burin bawa page Amma kash aiki ya min yawa,duk inda kuke ina matukar godiya da jinjina.Masu Sharhi ko wacce ina gani ina kuma jin dadi Allah ya bar kauna.Wanda suke kirana a waya ban daga ba ayi min hakuri bana kusa da wayar ne.







Dafta Jibrila Karatu da neman aure yayi nisa duk ajin su Dafta babu me ba da dariya kamar Sa,idan Dafta bai zo ba gaba daya basa jin dadi,game da practical idan suka zo to ko malaman sai dai su shafa Fatiha wajen Dafta domin yafi malaman sanin aiki da magunguna,Allura dasu karin ruwa da Sauran abubuwa sai dai kaga dalibai na tururuwa wajen Dafta ya koya musu,Malam kansu wani abun a wajensa suke kara sani,Allah kenan Ba yanda baya iyawa kuje da turancinku wani ya fika basirar aiki,
Ana Yiwa Dafta dariya da kallon dan kauye ne sai gashi Dafta ashe yafi su sanin aikin asibitin komai ya iya ya sani,
Turanci kuwa Almhdllh ana samun ci gaba,ya kara wayewa da gogewa ba wanda zaice Dafta ne yanda yake daukan wanka yanzu yayinda Hajara budurwarsa ta kara mannewa Dafta,a schl ma wasu matan son Dafta suke Sabo da kokarinsa da jan aji tare da wulakanta yan mata duk kyanki da surarki Dafta yace Hajara ta fiki.
Komai dadin sunanki idan ba Hajara ne sunan ba babu dadi wajen Dafta.
Dafta ya canja motar shiga sabuwa me kyau abinsa ga tsafta kamar me.k amar kullum sun fito daga Lecture Dafta bai saurari kowa ba yace Wajen Hajara zaije ya kaita shopping ana ta dariya Dafta yace kanku akeji ya wuce abinsa.

Daddyn Sardauna Tafiya ta kamashi Jigawa state yana cikin garin unguwar da zaije bai ma san unguwar ba gashi a flight yaje mota daya ce ta daukeshi Driver Sa,napep suka tare domin ya musu jagora zuwa inda suka nufa,haka Me Napep ya kaisu har inda suka bukata,Daddy yayi yayi yaron ya fito ya karbi kudi Amma yace kyauta yayi bazai karba ba,
Katinsa Daddyn Sardauna ya mika masa yana ta faman kallon yaron yanda suke matukar kama da Hafsatu kanwarsa,da Ramlat,haka Sardaunansa ma,t ambayarsa yayi yaro ya sunanka?yaron yace Fahat,Mamanka fa da Babanka?shuru yayi bai ce komai ba,Daddyn Sardauna rokonsa yayi kan dan Allah ya bishi Abuja gidansa zai bashi Babban aiki.
Da kyar Fahat ya amince da zaije,
Bayan kwana Uku Kabiru Fakas ya gama abinda ya kaishi Jigawa ya dauki Fahat irganman namiji suka wuce Abuja gidansa.
Suna zuwa Bilkisu tace wlh wannan bazai wuce dangin Hafsatu ba,kannen Sardauna yan wulakanci da kyar suka masa magana,shima da yake Fahat ya goge da duniya ko kallonsu bai yi ba,Sai Daddy yake ganinsa kamar Sardaunansu
Shi dai Fahat bai fadi sunan iyayensa ba sam,haka Daddy ya kaishi wani Company nasa da ya fara mutuwa sannan ya sashi a makaranta da me masa Lesson sosai Fahat yake jin dadi yana Yiwa Daddy Addua banda Bilkisu sarkin Tsabta da kyankyaminsa,
Ko side dinta bata bari ya shiga ba sai in Alhaji yana kusa to zaiwa Bilkisu da yaranta fada dole suke Dagawa Fahat kafa sai abinda yake so.

Lantan Sa'adat anci kwalliya za a je party na wata kawarta da kyar ta samu Abdullah ya barta a motar Amare zasu tafi party itama yar wani Babban Soja ce,Sa'adat kamar itace Amaryar Sabo da yanda ta dau wanka.cikin motocin Amare suka jera har kayataccen wajen da za ayi event din yan mata da samari tare da matan Sojoji suna ta shiga kowa ji yake da kansa,
Sa'adat ana yanga kamar itace Amaryar zata shiga ciki kenan taci karo da Saddiq shi da wani frnd nasa,da kyar Saddiq ya ganeta Sabo da kyan da tayi ba a magana,
Harara Saddiq ya watsa mata yana muzurai Amma Sa'adat Kidan da ke tashi ya gama Tafiya da ita
Ko kallon Saddiq bata yi ba ta wuce jikinta na rawa kamar ita aka kira,Ta samu waje gaba gaba ta zauna tana shan kallo har party yayi nisa ana ta harkoki,Sababbin kudi yan Dari dari taga an miko mata kallon mutumin tayi sai taga Saddiq ne jiki na bari ta karba tana godiya dan kar taki karba ya zaneta wai.
Lantan da ta shiga cikin wajen rawa kadan ta lika ta boye kudinta zata sha shagalinta da su,
Tana fitowa anzo daukansu za a maida su gida Saddiq ya tareta a hanya tare da kwace Jakarta ya zuge ya kwashe kudin da ta boye kaf ya mika mata Jakarta tare da cewa nan gaba abinda na baki kiyi da kudi shi kadai zakiyi ba kashewa nace kiyi ba,me zakiyi da kudi yarinya dake?Maza shiga mota mu tafi ko ki kwana kina tsallen kwado a nan wajen.sum sum ta shige motar Mugun nata suka wuce ko ta kan motar Amare bata bi ba,Saddiq satar kallonta yakeyi tayi masa kyau yau musamman da ta hade rai wai a dole an bata mata rai.

Sardauna ya dallo sabuwar Motar hawa yar gaske ta million biyu murna wajen Ramlat ba a magana haka Mami ma murna harda rungume Sardaunanta tana Sa masa Albarka,Ramlat tace Ya kamata ka kaimu yawo ni da Mami,Sardauna yace Mami zan fara kaiwa ke kuma sai gobe zamuje mu soye a hanya abinmu murmushi Ramlat tayi tare da sakalo hannunta ta wuyan Sardauna da kafadarsa kamar wasu manyan abokai,Harara Mohd ya watsa mata cikin sigar wasa tare da cewa ni sa'anki ne?dariya tayi tace da nawa ka fini ji min yaro,Murmushi ne ya subuce masa ba tare da ya shirya ba,fakar idon Mami yayi ya manna mata kiss a goshi yana gyara mata fuskarta da yatsansa,Me zaki ci yau Queen?fari tayi da ido tana wani mulmule lips cikin jan hankali tace tattabara yar shila da chips kuma ni Bazan yi da kaina ba take away nake so idan nayi da kaina Bazan iya ci ba,
Kallo yake kare mata sannan yace Babyna ko dai ciki ne da ke bamu sani ba? kalli ma fa cikinki ya dago sama ke da baki da tumbi,Ramlat tace haka ake cikin? banji komai ba kawai cin abinci da yawa ne ya jawo min nake ta cikowa,Ni dai ban yarda ba zan fara yarda da zancen Mami muje asibiti karfa ko ciki ne muzo kici wani abun ya zube cewar Mohf, dariya Ramlat tayi kaini Allah banda ciki wai haka ake yin cikin lafiya ta lau fa,kin manta rannan fa amai kika dinga yi bakya cin abubuwa da yawa,zazzabin malaria ne fa kawai Darling dina ta fada tana shagwaba,bari mu koma Bedroom yan mata sai kimin a ciki nafi yabawa,kitchen zan shiga yau kwana biyu Mami ce ke min komai na abinci ya kamata ta huta,Mami yanzu naga Alama tafi sonki kin kwace min abuta,

Hmm fada kawai kakeyi ai Mami kai kadai tafi so nima albarkacinka nake ci,muje kitchen din to muyi girkin cewar Sardauna,yau baza ka bini kitchen ba kaje ka huta yanzu fa ka dawo,amma kin san La'asar ta wuce ba kyau bacci me kike so nayi ina kwanciya kin san dole bacci zai kwashe ni ai.oya muje to kaga Mami ma ta shiga makwafta ta'aziyya goyani muje,dukawa yayi ta dane bayan Sa har kitchen taki sauka ya kaita jikin fridge ta ebo abinda zata yi amfani dasu ya kaita jikin wurin sink sannan ta sauka suka fara aikin a tare,ta fara girkin kenan zuciyarta ta fara tashi Amai ya kamata,Mohd duk ya rude yana tambayarta lfy bata iya magana ba sai bedroom da ta fada tayi cikin toilet sai Amai tayi kadan Mami wacce shigowarta kenan ta fada dakin itama tana rike da ita ta gama,ta wanke jikinta suka fito Sardauna yana ta lallabata,Mami tace Muhammadu je ka siyo mata abubuwan da take iya ci,bari nayi abincin ni,itama rigimarta ce nace ta daina girki zan dinga yi bata jin magana,
Da Sauri Mohd ya figi sabuwar motarsa dalleliya nan da nan ya siyo mata duk abinda yasan tana so da yawan gaske,Ramlat sarkin kokari kafin kace me har ta feso wanka tare da gyara gidan kaf ko ina sai kamshi ke tashi,Mami tana kitchen tana girke girke,
Sardauna a Palo ya samu Ramlat tana ta waya da frnds nata su Fadeela,Fa'iza da yan gidan Citta su Habiba,sai nishadi takeyi abinta,Ramlat Sam bata da lango akwai karfin Hali sabanin wasu ko ya cuta ta samu sai kaga sun fice daga hayyacinsu sun ragwargwaje,ko wanka basa yi bare gyaran gida,duk da rashin lfy ce a dinga daurewa mata ana dan karfafa jiki idan da dama.

Kusa da ita Sardauna ya zauna tare da kwantar da kansa a cinyarta yana shakar kamshinta waya na a kunnen Ramlat ta nutsa yatsunta cikin sumar Sardauna tana sosa masa gashinsa tace Fadeela sai anjima mijina ya shigo zamuyi magana later,Fadeela tace oh Ramlat har yau kina nan yanda na sanki da son miji,idan ban soshi ba wa zan so ina da wanda yafi shi ne ta fada tana walwala Ido ganin Sardauna ya kafeta da mayun idanunsa shine ta aika masa da sako kamar bata San yana ganinta ba,Apple kawai zan iya Sha cewar Ramlat kafin ta rufe baki Mami ta shigo da Apples cikin bowl da alama wanke mata su tayi,

Kabiru Fakas duniya kullum kara Zafi take masa tattalin arzikinsa ya karye fiye da zaton me karatu,babu abinda yake tunani Sama da Sardauna da Mami abinda ya aikata musu,duk wanda ya tambaya Bai da labarin wacce duniya suke abinda ya kara tayar masa hankali kenan ya rasa Jin dadin duniyar,kullum a neman inda zaiga Mami da Mohd yake abin ya gagara,yayi nadama da dana Sanin abinda ya aikata,Bilkisu ganin mijinta shima Bai da sukuni itama haka ta rasa ya zatayi da Daddyn su Sardauna sabo da Hawan jini ya kamashi sosai.
Ita kanta Bilkisu ta koma addua Allah ya nuna musu su Mami ko za su samu nutsuwar Kabiru.

Washe gari Sardauna dole ya dauki Ramlat zuwa asibiti private me matukar kyau,gwaje gwaje akayi mata nan take suka tabbatar da Ramlat na da ciki har na tsawon Wata hudu da kwanaki,mamaki ya kama Ramlat tana kallon Sardauna bakinta yaki rufawa tace aikin Banza kash dama haka ake cikin ba wata rashin lfy ta azo a gani amma mata suke damun mutane da zancen laulayi Ashe duk iyayi ne,musamman idan suka zo haihuwa ayi ta faman ihu da kuka ana fadar wai kamar za a mutu,ai kawai lango ne,kallonta Doctor din yayi shima Sardauna haka tare da cewa kema Allah ne ya baki me sauki kawai ki Bari ki tsallake nakuda,kafin ya rufe baki Ramlat tace af kai yi shuru kaji surutun mata ne. doctor dariya kawai yayi tare da jinjina kai.

Da murna suka shigo gida Sardauna ko Zama baiyi ba ya hau kwalawa Mami kira tana fitowa ya bata labari,Ramlat kuma na rufe fuska tana kyalkyalar dariyar farin ciki,Mami tace ni dama banyi mamaki ba tuni nasan Ramlt cikine da ita kune dai kuke shirmenku,
Sardauna murna kamar me ranar ba a magana,washe gari a wajen aikinsa yaransa sun Sha kyauta gaba daya ya sanar musu idan Mace ce sunan Mami zata ci kuma little Mami za a ce mata,idan Namiji ne kuwa to ya koma Baban Ahmad sunansa zai sawa dansa amma shi Ahmad za a kirashi,I dan Twins ne mace da namiji to Mohd da Ramlat mutanen wajen suka kwashe da dariya,wani yace Oga ai da Mama da Babanka kasa kawai,Sardauna yace ai mutane uku duk duniya zan iya maida sunansu,Mami,Ramlat,sai ni amma sauran wife dina tasa abinda taga dama zabinta.

Yau Sardauna kasa Zama yayi da wuri ya koma gida da kayan ciye ciye iri iri,harda kayan Baby kala kala na yan gayu wanda mace ko Namiji zai iya sawa,
Mami fada ta dingayi a bari ta sauka lfy mana,Sardauna yace ina Sam shi bazai jira ba,Ramlat kuwa Bedroom take shigewa tayi ta yiwa Babyn cikinta magana ita kadai, Yau ma tana cikin daki gaban dressing mirror tana ta faman magana tana shafa cikinta tare da aunawa da tape,Yaya kike yar gidan Sardaunan Mami? kinci abinci kuwa?Apple da naci kema kika ci ko? to ki dinga Shan ruwa da yawa kinji,zan na cin kayan dadi kiyi kiba ki fito katuwa kinji? Allah sa dai kanki b kato bane?dariya Ramlat tayi taci gaba kin San dalilin tambayar?kar ki lalatawa Dad dinki wajensa da katon kanki,ki fito cikin Salama da ikon Allah,dan Allah banda kukan dare,Sardauna yana jikin kofa yana jin Ramlat yanda take zuba shirme,shima ba a barshi a baya ba ya sadado hannunsa saman cikin tare da rafka Sallama,Assalamunalaiki ya Daughter Muhammad Sardauna,nafi Mum Sonki,Ramlat kamar zatayi kuka ta damke cikinta wlh karki yarda nafi Sonki,gaki nan a cikin cikina abinda nake ci shi kike Ci sweet Angel,Sardauna yace ai dai ni nake siyo kayan har take ci tana San miki da ban siyo ba baza kuci ba,Oh kinji Gori ma yake miki kin San kuwa baya Sonki,a kunne ya rada mata amma dai kinsan ni nayi cikin?idan kin isa kiyiwa kanki mana,na dinga juye miki komai na jikina kizo kina wani cewa kece a gaba,
Itama Ramlat wai dan kar yarinyar cikinta taji iyaye na rashin kunya ta radawa Sardauna shima ai dai ni na yarda kayi ko da ban yarda ba fa?
Rigarta yaja tare da rufe cikin rufe min yata kar taji Sanyin duniya tun yanzu,Ramlat ta hangame baki au dama suna Jin abinda ke duniya? Mohd yace sosai ma,da Sauri Ramlat ta dauko rigar Sanyi ta jibga a jikinta,banda Dariya ba abinda Sardauna keyi na shirmen Ramlat domin wasu abubuwan yana sani yake biye mata suyi ta faman yi ita kuma bilhakki yarda takeyi.

Wanka ma da Ramlat zata duk da cewa ana Zafi sai tace dole da ruwan Zafi zatayi kar Baby taji sanyi,
Cikin Ramlat ya shiga wata 5 da yan kwanaki amma baza kace akwai ciki ba Sam,suna zuwa Asibiti sosai kula sukeyi da cikin gaba dayansu an rasa wanda yafi wani son cikin,Mami,Sardauna da Ramlat.
Babyn ciki kuwa ya fara yiwa Ramlat motsi,ranar tana Palo ana wani film an kwalla kara a ciki sai Babyn ya zunguri Ramlat da karfi tana jikin Sardauna ta juya tare da Fadawa jikinsa ta makalkaleshi tana kurma ihu sai da Mami ta fito ta tambayeta shine take fada mata,Dariya Mami tayi tare da cewa ai dan cikin ki ne yake sanar miki lafiya lau yake,
Ai Ramlat sai murna nan take ta kwaye rigarta tare da tambayar cikin lafiya kake?to Alhmdllh naji kana lfy nima Allah kara ma Lafiya da Nisan kwana,Mami da Sardauna dariya suka dinga yi ba ji ba gani,
Tunda Ramlat ta gano cewar ko kara ko buga kwano yana sa danta dake ciki ya firgita sai taji yayi motsi yana zungurinta, ai sai ta samu abin yi idan ta ji shuru baiyi motsi ba sai ta kunna TV ta kure Vol har sai dan yayi motsi zata rage,ko kuma ta samu ta buga Faranti a kasa sai firgit taji yayi motsi to shike nan burinta ya cika,shi kuma Oga Sardauna duk lokacin da yake gida cikin Ramlat yake budewa ya kafeshi da Ido yana kallon Numfashi kala biyu sai Ramlat ta ja nata sai yaga cikin Ramlat ana yin wani Numfashin daban shi kuma burinsa kenan,bashi da aikin da ya wuce wannan idan yana gida,Mami sai dai ta kallesu tayi ta dariyar shirmen da suke zubawa.

Sa'adat da Soja Saddiq har yau basa shiri ya gama sawa Lantan tayi laushi,duk tsokanar da takeyi ta daina idan kaji tana fada to an tabo ta,Saddiq ya gama takurawa Rayuwar Lantan ya hanata sakewa mutumin da bashi ya daukota ba ganinta kawai yayi amma dalilin Lantan Matar Abdullah soja Da shi kanshi wani girmama Saddiq sukeyi yanda yasa Lantan ta nutsu,ko Laifi Lantan tayi ana cewa za a fadawa Uncle Saddiq zata fara kuka tana magiya tasan indai aka kirashi bazai mata ta dadi ba.
Har yan makarantarsu da yawa sun gano hakan shi yasa ko wani ta tsokana duk ranar da Saddiq ya kawota schl da kansa zasu taru suje su kai masa karar Lantan.
Shi yasa yanzu bata tsokanar kowa ma sai da dalili,kullum kokarinta karuwa yakeyi a schl.

Daddyn Sardauna ya bada bincike Lallai sai an nemo masa Sardauna da Mami,sosai cuta ta kamashi kullum yana asibiti ganin likita,Yayin da Sardauna kullum arzikinsa kara bunkasa yakeyi domin yanzu yafi karfin shaguna sai shopping mall kala kala, burin komawa Abuja da zama yakeyi gaba daya Amma baya son Su Mami su sani sai nan gaba,ya mallaki Kadarori da dama har yau su Ramlat basu sani ba so yake ya basu mamaki.







AsmaBaffa
DUK INDA TA FADI





241-245






Official






By
AsmaBaffa








Tunda Kabiru Fakas ya samu labarin ba a samu inda su Mami suke ba Hawan Jininsa ya tashi ya kaishi harda kwanciya a asibiti ranga ranga,Bilkisu kuka wiwi takeyi abin ba a magana,Kannen Sardauna Nabeel da Nabeela harda Auta Ammar gaba daya basu da kwanciyar hankali,suma da kansu neman inda zasu ga Sardauna da Mami suke amma ba labari kullum asibiti wajen Daddynsu cikin Kuka,
Bilkisu ta rame sosai kudin ma da suke gadara dashi duk babu sun tarwatse a hankali ba tare da sun san inda kudin sukayi ba,sai Kadara da ake ta faman siyarwa.
Cutar Daddy itama tana cin nata rabon kasa kasa suke kaishi Amma ba sauki an ma kasa gane wacce cuta ce.

Sardauna kuwa Yanzu Sunansa ya fara karade Adamawa Sabo da yanda ya taso da kudi ya fara tashe,Hannun jari ya zuba cikin manyan kunguyoyin Kwallon kafa na Nigeria,ya gina manyan stadium na kwallon kafa masu matukar kyau ana haya ayi Ball ciki ta ko ina kudi shugo masa sukeyi, Amma har yau ba a gama gininsa na Abuja ba yafi so Ramlat tana haihuwa su tafi kawai,Cikin Ramlat ya shiga wata 7 yanzu kam ana ganinsa ba da yawa ba,sai wani kiba da kyau da take tashen yi,Sardauna duk inda kake neman hadadden guy to ya kai karshe,kyalli da kyau yake zubawa,uwa Uba wanka ba a magana musamman yanzu da duniya take gara masa akwai kudin,Ramlat kullum kishi takeyi bata so yana yawan fita kar ana kalle mata miji,shi yasa sau da dama a mota yake sata suna tafiya duk inda zaije tare da ita kafarsa kafarta,
Ramlat ana cin uwar Sutura yanzu masu tsadar gaske suke sawa, zaune take saman kujera tana gyara farcenta yau me gidan yana nan bai fita ba sanye ya fito cikin arniyar shadda light blue yana takunsa cikin Isa da gadara kamar dan Sarki,
Zama yayi kusa da matarsa jikinsa na Gugan nata kamshinsu ya hadu ya Bada wani kamshi me matukar dadin shaka,dauke kai Ramlat tayi ba tare da ta kulashi ba tana cika tana batsewa, Ido ya zuba mata amma ko kallo Bai ishe taba,hannunta ya riko tare da cewa kawo na yanke miki,Wani kallo da ta masa yasa ba shiri ya saki hannun nata

Please Login or Register in order to submit comment