Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Amma wannan miji kwai anace duk mutanen nan?
Ramlat dai wanka tayi taci uban wanka kamar yanzu za a tafi Wedding Dinner din nasu domin ita za a fara yi ta Sardauna kenan Ba Jaririya a ciki domin A'i tace baza taje ba tana gida ita da Baby,Allah kiyasheta da gwamutsa da Maza a jefata a wuta.
Ramlat tana kiran Sardauna yace ta fito su tafi Nononta ta matsa a feeder da yawa ta saka a Cikin flask na tea kar ya huce ta mikawa A'i a bawa jaririya idan ta bukata.
Tana fita Sardauna ya kafeta ido har ta shiga motarsa gaba tace Ranka ya dade muje mana,Sardauna yace kai ayi a gama jegon nan,Ramlat ta bata rai dan kar ya bata matsala ma tasan halinsa da rashin hakuri.

Mene na fushi?ai kaine Baby sai ka dinga magana haka kasan baza ka samu ba kuma kayi min alkawari zaka jure sai nayi 40days Amma tun ba a je ko ina ba.
Shuru ya mata ya figi mota baice mata komai ba har ya kaita gidan yace anjima 6pm ina Sallah zan zo na kaiki MakeUp. Kallonsa tayi to naga kamar kayi fushi ne dani?fushi kuma?ni ba fushi nayi ba sai na dawo ya juya motarsa ya barta nan.
Ramlat tace toooo kamar fa yayi fushi,Ramlat ta shiga cikin bakinsu da Hadiza Mukhtar ta fara cin karo ta wuce ta palo da dinkuna a hannunta,Flower ta fito tare da karbe wani Material nata kar a kalle mata dinki tun bata Sa ba, Auta ce ta shige wanka tana dagawa Ramlat hannu,
Zainab Atiku Salama kam bata magana kayan makeup take ta faman ebowa,Jidder Zaria kuwa har ta fara shafa Lotion ma tare da dauko wani arnen swiss nata,Sameeran gaya tace ina yar Babyn fa?Yan mata da matasan mata masu aure gasu nan ko ina su Jannat,sunyi yawa sunansu bai faduwa ma ko wacce wanka take sha,Mum Suhail da Maman shureim,Maman Waleeda,Queen Mermu,Queen kk,dasu Anfa marubuciya duk suna tare ana shiri,Nabeela da kawayenta suna gefe suma etc, sai manyan mata yan Uwa da abokan arziki kowa da abinda yakeyi basa ma ta Ramlat Sam shiri akeyi,Bangaren Mazan ma hakan take Naufal dasu Zikk duk sunzo gidan suma,Hafsatu da Ramlat Uwa da yarta kayanta daban Sardauna ya dinkawa Umma da Kawu nasu color daya,Lace nata da shaddarsa Suma farare kalar na bikin da za a Sa.

Lantan tana can Saddiq ya kawo mata kayan da zata Sa Driver ya kaita,taje Saloon,tayi lalle da komai kamar Amarya, gidan Saddiq ta tafi direct tana rangaji kamar zata fadi haka ta shiga sai ganinta yayi tana kuka sosai,ya dauka gaskene abin,ya rude yace mene?tace ba...ba...ba..Abba bane yace bai yarda Driver ya kaini bikin ba sai daí idan kaine zaka kaini ka jira a tashi ka maidoni gida bai yarda ba Sabo da da samarin zamani,kuma ni nace masa ya barni ma ina da saurayina a can zai kula dani shima zaije,
Bakin ciki da kishi ya mamaye zuciyar Saddiq hankalinsa ya tashi ya gigice,Idonsa nan take ya canja harda dafe gefen zuciya.Lantan dadi ya kamata tarkonta ya kama,tace Amma karka damu sai na masa waya yazo ya daukeni ya kaini shi Saurayin nawa Amma dan Allah ka rufa mun asiri kace kaine ka kaini kaji Yaya Saddiq dina?
A tsawace ya fara magana kamar zai tashi gidan wanne matsiyacin kike kulawa ban sani ba?har yaushe kika sanshi? Bin Lantan yake zai damkota tana matsawa har taje jikin Bango ta tsorata sosai tunaninta duka zata sha,wata uwar tsawa da ya buga mata dake nake fa am asking u?bata san sanda ta fara kukan gaske ba kamar zata shide ta tsorata soja guda.

Sassauta murya yayi yana maida numfashi yace Ok ..Ok calm down..relax and talk to me wlh sai kin fada min waye ko na harbeki,u r very stupid ance miki zan tsaya ina kulaki haka kawai ne?Baki da hankali bakya gane halin da nake ciki,kin san yanda nake kwana nake tashi da tunanin....Oh God tsaki yaja ya koma kujera tare da zama,Sa'adat tana Kuka an tsorata da kyar ta share hawayenta zata fita daga gidan,muryarsa taji yace dan iskan zaki kira?a'a gida zanje,Karfe nawa ne Event din? 9pm da dare na manyan Yara ne,baki ya tabe ke dai kice zakije wajen dan iskan Saurayin naki,to zan kaiki 9pm zanzo,tace ai zanje wajen Makeup yanzu sai daí ka min waya sai ka daukeni a can,ok jeki kina gamawa ki kirani a waya.Sa"adat da murna tace to tare da ficewa tana ta dariyar jin dadi.
Saddiq kuwa tunanin yanda zai konawa Saurayin Lantan zuciya yakeyi,sai yayi maganinsa da kansa zai janye.

Motar Sardauna ce ta tsaya a wajen gidan Ramlat ta kara wanka tare da dauko kayan da zata Sa ta fito ta shiga suka wuce wajen kwalliya,
Sardauna yana kaita ya wuce wajen aski akayi new stile na ubansu kamar me yanda yayi kyau,an kara fito da da Sajen kadan da gemu,ga shegen aski me kyan gaske kana gani kasan na manyan Yara ne kamar turawa yan ball.
Gida ya koma ya fesa wanka ya fara shiri bayan anyi Sallar Isha,8: 30pm an fara kwasar matan ana kaisu,m otocine iya kallonka ko ina na gaske, Naufal tunda yaga Nabeela me kama da Sardauna ya makale mata,yaki Yiwa Sardauna komai sai abinda Nabeela tace yakeyi shi yake zirga zirga dasu da kawayenta har can ya kaisu,
Saida Sardauna ya zageshi sosai sannan ya dawo wajensa,Zikk kuwa iyaye suka kai da Sauran wasu,komai na cikin wajen da ake Dinner din White and pink docoration ne,wajen kansa abin kallo ne yasha kyau ba na Yara bane,
Kowa ya hallara a wannan waje wasu kuma da motarsu suka wuce kawai direct can,kai haduwa ta kai haduwa,kowa ka gani wanka ya haushi iya wanka na nunawa a duniya duk ba baya a wannan wajen,Lantan ake jira ta shigo Nabeela ma ta matsu Amma sai tace gasu nan shuru,Kida ne ke tashi a wajen,
Ana jiran Sardauna da Ramlat suzo 9pm za a fara ba African time.
Kwalleliyar motar Saddiq ce ta tsaya a wajen,Wohoho takalmin Sa'adat ma kawai abin kallo ne,shigar farare sukayi kar kar color na wajen,suma kusan duk kowa da yake wajen Shigar farare sukayi sai masu arsh light color kusan Farin suma dai manya da Yara,saida masu tsarawa suka tsara komai,ko kinzo ba irin color din to za baki kyauta Mommyn Sardauna ce ta shirya wannan da kudinta ba ruwan wani,tace bazai yuwu ayi colors barkatai ba za a bata show,duk wanda aka gayyata an fada masa wanda baixo dasu ba babu takura Mommy ta dau Nauyi kuma Size din mutum tailors dinta ke aikin a gidan da aka sauki bakin ta kawosu sunfi su goma aiki kawai sukeyi,wasu ma a ranar aka hada musu
Wasu ma sunzo da nasu Amma saida suka karbe na Mommy.
Mommy itace taje ta kara tsara wajen Sardauna ma sai labari masu wajen suka bashi ai tazo ta gama komai.
Lantan da Saddiq kamshi da walwali sukeyi suka shiga rike da hannun juna,ai nan suka ga wanka iya wanka kowa walwali yakeyi kuma ba mutane aka tara da yawan gaske ba a'a ta turawa akayi dai,abin mamaki sai ga su Chuchu, Ammi,harda Prof Family guda suma suna sheki,
Prof yasha Suit harda rike wata Sandar girma ta karfe fari, Hajara budurwar Dafta ma ashe tasan Fadeela da Fa'iza yan Zaria frnds ga Ramlat sai gata cikinsu tare da da Dafta yasha wanka baza kuce Jibrila ne ba mata har kallonsa sukeyi ana yabawa bai san taron tsohuwar budurwarsa bane tab..

Firdausi,Habiba da Sauran yan citta harda Bature Boss da kannensa da suka zo daga can turai ya ebo su sunzo wannan shagalin Amma su a Hotel suke zama,Frnds din Sardauna harda turawa da kuma wasu kasashen África,da na diff state na Nigeria duk gasu nan,kannen Ramlat da iyaye ba a magana,Salma kanwar Ramlat tasha kyau fa dukka Ramlat tawa kannenta dinki,
Fahat an girma sai kallon yan mata yakeyi,Ma'aikatan sai zagayawa sukeyi mata da Maza suma sunsha wanka kamar dasu ake Dinner,Lantan fa Jidder Zaria ce ta fara kwaso gaisuwa wajen Saddiq,Pharteemarh taje domin cusa kanta Lantan ta dalla mata Uwar harara sai kawai ta wuce tabi ta can layin baya ta koma wajen Su Chuchu ta zauna kusa da Prof shima dai Prof bai bi ta kanta ba.

Sabuwar motar da Daddyn Sardauna ya siya masa tafi million 30 itace Driver ya dauko Sardauna a bayanta,yabi ta can wajen Makeup Ramlat ta fito Sardauna harda kara murza Ido kamar ba Ramlat bace ko balarabiyace ko Baturiya oho.tana shigowa wani bala'in kamshi ya dakeshi,itama Ramlat kallon mijin nata takeyi kamar wani dan Sarkin Amurka,wani wanka da yasha me lankwasa ai abin ya wuce sanin mutum a kasar nan.
Motar ma fara ce ta gaske wacce tafi ta kowa a wajen kyau da tsada ta tsaya,Sardauna ya fito tare da budewa Sarauniya Ramlat wohoho ai duk sai miji da matar suka ce ku matsa gefe baku iya ba,

Shigarsu Ramlat da Sardauna pink color ce da fari kadan, Su kuma alummar ciki white,cikin wajen kuma pink and white docoration ,kunga in an hada dai pink and white ne, Sardauna suit yasha kamar a jikinsa aka dinka dama size dinsa aka dinka masa abinka da gayu,wandon pencil pink,top din pink ta ciki fara me dogon hannu,neckt kuma kuma pink,Takalminsa Fari yasa dan gaske,
Ramlat Wedding Gown ce pink gaba daya itama cif cif da ita,da abin sawa saman kai irin na turawa,ta baya kuma rigar me tsayin gaske tana jan kasa sosai,takalminta me shegen tsini fari da pose fara

,Salma kanwar Ramlat da Yar Iklas Gomnati ta haifi mace ta biyu dama ai tana da ciki,to yar ta kai 4yrs itace da Salma kyawawan gaske su aka Sa suka rike kasan rigar Ramlat Sardauna kuma ya rike hannun Ramlat suna tafiya a nutse masu Camera ana ta wal wal da haske,ba ji ba gani,Mc ya Bada sanarwa Ango da Amarya zasu shugo hhh karku manta wedding party ne fa na yau,wani wakar love aka Sa musu ta zamani ta turanci ana watsa musu Golden Buzzer har suka zauna a Sit dinsu,Ramlat ta hango Rahma da Ahmad dinta Maraicin Rahma yaransu suna gida su Biyu suka zo,
Gomnati ikon Allah Iklas me gayya me aiki me hadarin Love da abin dariya tare da Omar dinta da yarsu daya suka zo me rike rigar Ramlat Ma'aikaciyar Gomnati Kunji dai ta haihu ta biyu,Yarta Raudat.

An fara gabatar da shagali sai ga mutan lagos Alim da Amana Ciranin Amana yanzu kam suna yawan zama a Abuja kusa da gidan su Mommy sune Gayyar Nabeela ne domin tana zuwa gidan ko dan kallon love suma su Biyu ne ba yaro, an gabatar da komai aka fara kiran dangin Ango su fito Haka suka cika fili ana fyalli da kudi, shigowar Mubaraka Lilla da Suhail, Gaskiyace shi ya tafi da imanin mutane tare da yaransu biyu,
Defence Abdullah da Shukrah, Ni'imar Allah suna gefe wannan miskilan kansu ne har yau su class dinsu daban ne suna gefe suna shan love, Ade Rufaida da Fauzan Ade Yar Baffa etc ma ba a Barsu a bayaba dukkansu a gayyar wasu suka zo basu san su Ramlat ba amma suna da hadi mai karfi da wanda suka sansu,domin Gomnati ma Jannat ta saleem ce tace dole tazo,Rahma da Ahmad Naufal ne frnd din Kanin Ahmad Ammar gasu nan da yawa a wannan waje.

Gomnati na jin yan kira Ango gaskiya sun birgeta tace Babyna zo mu Bada show,Omar ya daure fuska ki bari ni kayi min rawata a Bedroom so kike a kalle min ke,Gomnati ta fara masa shagwaba sai sunje to ko liki tayi tunda mijinta me kudi ne,Dole yaje suka fara Yiwa Sardauna da Ramlat liki kida na tashi,babu wanda ya Isa yace Ramlat ta haihu in dai ba sani kayi ba,Amana taji ance ai Amarya ta haihu ma,abin ya bata mamaki to mene abin biki kuma sai kace auren ba musulmi ba sune wanda da yawa sai sun haihu ko da ciki za ayi shagalin biki,Alim ta kalla tare da cewa abin haushi kamar na make yan iska wlh yaran nan to ni ai bamuyi bikin ba hakura mukayi amm su baza su hakura ba,da Badriyya na nan sai ta fada musu gaskiya duk da cewar sun hadu dan kawai kudi ya musu yawa mace da yarta sai a kama biki ayi suna mana,nan Amana ta dinga masifa Nabeela bata Fada musu gaskiya ba,Alim yace to sarkin zafin zuciya ina ruwanki rayuwarmu daban tasu daban,Amana ta mike tace muje kayi min liki kuma ni zakayiwa duk da bana rawa ni kadai zaka Yiwa ,Alim ya mike hannunta cikin nasa,Amana ba dai shape ba ta shiga itama kusa da Gomanti,Gomnati ta Galla mata harara za a kallar mata miji,Iklas ga tsokana ba Karfi,Amana da zuciya masifa da karfi,kallon tara saura qutr Amana tayiwa Iklas tare da jawo Alim jikinta,suka juya can Barin,Gomanti anfi kowa tsageranci da tantiranci domin yar tallace da can a tasha da kan danja,tayi hugging din Omar dinta suka koma wajen zamansu dama tsoron Amana taji da gani ba mutunci zata yi ba,ita kuma akwai tsoro danma Omar na kusa,Defence da tasa sai jarabar hade rai a junansu kadai suke hira basa kula kowa,Lilla itama yarinyace Sai shagalinta takeyi da mutane,Suhail ba takura.
Rahma kuwa Tasan Ahmad ma Shi ya riketa a hannunsa ya bata raino shima dai dai gwargwado bata Isa ba ina sai abinda yace sai yace ayi za ayi.

Mutane dai ana ta ciye ciye da shaye shaye ana chashewa ana gwangwajewa a wannan waje,Serve ur self ake ta faman yi,kida na canja Salo,Naufal da Nabeela sun cashe,Dangin Amarya,dangin Ango,frnds da abokan arziki kowa ya Bada nasa kalar,Sa'adat Lantan Saddiq ya hadu da wasu frnds nasa bai sani ba kungiyar su Jidder Zaria suka janye Lantan suka shige filin rawa kowa da kalar tasa,Sardauna da Ramlat sun musu liki sosai,Ramlat tayi mamaki wai Lantan ce ta dawo haka,nan ta fesawa Sardauna ai sai da ya kalleta tare da cewa Allah me iko ke nan,kowa da yanda ya tsara masa,
Dafta tunda Ramlat ta shigo ya tabbatar itace don har tambaya ya kara yi aka tabbatar masa kuma ga Kawu ya gani,Ya kusa suma,tsohon so ya motsa,amma ya danne Sabo da Hajara na kusa,
Prof kuwa har wajensu Ramlat ta sakko rike da hannun Mohd suka gaisa da Sauran manyan nata,d a iyaye kamar larabawa.
Anyi pics sai ga AsmaBaffa ta fito me rabon kaji kowa yaci guda ta Amarci ce aka bawa kowa tasa akace aci uban Kaza ayi Brush da ita,masu Tafiya da katuwar jaka harda leda kwadayayyu duk sun jefo tasu a leda shi yasa dama Mommy tace a sata ayi wrapping na ko wacce a bawa mutum kowa ya tafi da ita gida,harda masu samun biyu Uku hudu,Mommy ta fito ta raba atampofi masu kyau yan dubu 8 ko wacce kalar tata daban.
Wannan rana ba wanda yaso a tashi daga wannan Dinner sai wajen 3am aka fara wucewa gida ana kwashe wanda za a maida masaukinsu,Ramlat da Sardauna ma sune karshen Tafiya,part din Sardauna ta wuce sukayi wanka ya gasa ta sosai tuni an shirya Jaririya tana bacci ma aka kawo mata abarsu suka kwanta sai bacci,jaririya na gaban Sardauna ya koma shine ma me jegon,

Da Safe da wuri aka rada suna a masallaci Taci Sunan Fatima Mami kuma Little Mami za a na ce mata,mami sai murna takeyi an mata takwara,
An yanka Sa da raguna ba a barshi a gidan ba yana can gidan masaukin baki su Abu sun ware part guda suna ta Suya,
Da yamma Liss
Gidan Sardauna ya dau docoration kamar a
India an kawo gasassun Raguna da kayan sha da su tea lemuka,coffee,abinci iri iri gasu nan ansha wani kalar wankan Ramlat Lace tasha da Little Mami tasha kwalliya cikin kayan Yara masu tsada da kyau ana ta Waleema me wa'azi tana yi a gefe,ana ci ana sha,Sardauna ya faso da frnds aka sha hotuna,
Karfe 5pm aka fara 9pm suka gama ansha hotuna Sardauna wata shadda yasa color daya da Lace din Ramlat peach kenan.

Washe gari again Party na Daddy ne 6pm to 12am,wohoho wannan Rana ma da jaririya aka je Ramlat da Sardauna ansha kyau Material tasa Gown me mugun tsada da kyan dinki kamar a turai,Sardauna kuwa yau kamar wani Yarima dan Sarki wani Yadi yasa me Laushi ruwan toka da Golden haka Ramlat ma nata color yau ma ansha buduri anci ansha anyi rawa an gaji,Mami daga baya little Mami ta karbe ta goyata aka tafi da ita gida wai ta gaji cewar Sardauna Kida zai kashewa Yarsa kunne,
Anyi watsi da Naira a wannan waje.

Washe gari ma babu bata lokaci aka tafi iya na samari da yan mata sai matasan masu aure da mazajensu,ba Yara ba tsofaffi,wannan shirin Naufal kenan,Yau yan mata sunyi iya shegen rawa,shi ma kanshi Sardauna kuruciya ta motsa saida ya cashe a gaban Ramlat dinsa ya mata rawa tana tsaye ai kuwa ansha ruwan Naira anci dariya kuma anyi nishadi,
Flower,Asycool gaba daya basa jin magana,Auta saida kowa yasha mamakin irin rawar da ta cashe a wannan waje,Hafah,Hafsycy ana ta juya baiwa a wannan fili basa magana,yau kowa yafi rakashewa a wannan waje,mutanen da suke wannan fili ma Baza su fadu ba suna da yawa Bazan iya kawo sunayensu ba domin za su cike mana shafi.a dunkule duk Masoya wannan novel masu Sharhi da karantawa suna wannan waje sun halacci fili,Lantan guda biyu Saddiq ya kawota dana Sardauna first event da kuma Na Naufal last kenan,sauran kuma duk ita takai kanta. Ansha shagali lfy an gama kowa ya koma masauki.

Washe gari kuwa dukkan bakin da suka zo na nesa ko wacce an bata 10k a envelope Daddy ya musu Booking flight suka koma gida lfy lau shar cike da murna domin wasu kudin da suka samo washe gari sai Tafiya kasuwa aka dan rage zafi na siyan inner wear wasu kuma abinda sukayi daban.

Kwana biyu da gama biki An gama gyara ko ina kace ba ayi wani shagali ba,dama harkar a nutse akayita ba hargitsa waje baza kace ma anyi wani taron Jama'a ba to kowa dan gayu ne.

Naufal ne kadai bai tafi ba yana nan a part din Sardauna sai ya dade a Abj Sabo da Nabeela,kwana Uku da gama suna kowa ya daidaita yayin da Ramlat da Mohd suka kira bakinsu aka musu anje gida lfy, Mami ta tsaya yanzu sosai take gyara Ramlat,Itama Ramlat har gidan Gyaran Amarya take zuwa ana mata gyaran jiki kusan kullum sai Sardauna ya kaita ya daukota,watarana kuma Nabeela,Nabeel,ko Fahat duk suna tuka mota suke kaita su maidota.

Sardauna ya dawo daga aiki Naufal ya iske a Palonsa yasha wanka yana kallon foot Ball,jikan Mami Baban Mami na Ramlat ka dawo kenan Cewar Naufal,Mohd yace kai nifa ka isheni ka dinga zama a side din dana baka a part din nan incase Queen ta shugo fa?Sai kallar mana sirrin dakuna kakeyi nifa ba gwauro bane ka sani da iyalina,Naufal dariya ya saki banza muma zamu shigo ne har yaushe ka zama mutum zaka mana iyayi,matarka ina ruwana da ita wlh dazu ma naje wajen Mami tana can kuma mun dade muna hira,je kayi wanka ka dauko min Daughter dinmu na ganta wlh kun iya haihuwa wannan zukekiya haka,Dariya Sardauna yayi suka tafa irin na abokai yace 'yata dai ba tamu ba,insha dadina na haifi abata kazo kana taku,Ka daure kayi taka kaima,na kosa ma naje naganta,banma san irin son da nakewa yata da wife dina ba wlh kamar na hadiyesu,Wai kai dan Iska da jegon ma tare kuke kwana?Naufal ya tambaya,Hehe ranar da ta haihu ma yaro ni na mata wankan jego kuma muka sha baccin mu kai har yau ni ke mata,Naufal yace tab wlh Bazan iya ba,kai ni fa ko me Period inaga zanyi kyankyaminta,kasan dai na fika tsafta da kyankyami ko?cewar Sardauna to kawai ka daina cewa komai Malam baka san so ba,bakasan ma dadin aure ba,baka san me ake ji ba a wajen mata kayi shuru kawai ban son iyayi,

Naufal yana dariya yace kaji dan Iska ni zaka fadawa haka,karfa ka manta sanda muna England ni nasha murje mata Sex ne kadai banyi ba,kaine ma baka san komai ba lokacin kana iyayi wai kai me tsafta to bari kaji nasan kalar dadi na sex ne kadai sai nayi aure,
Tabe baki Sardauna yayi to yanzu ribar uban me kaci?da me ka fini,ai gashi nayi aurena da kudina na kaina,sannan da yata,yafi min kule kulen matan iska masu watsa kansu a titi,Ai kanwarka zaka bani yanzu wlh kuna kama kuma na tuba ma ai na daina ko rike hannun mata in dai za a bani Nabeela,tabe baki Sardauna yayi yace ni ba ruwana ba wani sanin yaran nan nayi ba in sun baka ina murna Amma ni ka daina sani cikinsu.

Kai fa dan Iska ne in dai ba Mami da Ramlat ta kauyen Jigawa akace ba baka ganewa,bata rai Mohd yayi ka daina kira min Sunan matar sunna,kuma wlh zamuyi fada matukar zaka ce mata yar kauye aikin banza.

Knocking suka ji anyi,Sardauna ya bude Ramlat ta bayyana sanin Naufal na nan Hijab tasa a saman kwalliyar da tasha dama ita ba kwalliya ta cika da yawa ba,powder,jambaki,sai kwalli yawancin kenan sai ka ganta shar ba wani shirme a fuskarta,sardauna ma bai son wannan yawan cika kwalliya a face,Little Mami ce a hannunta tasha wanka suna ta kamshi na fitar asiri,murmushi Ramlat tayi tare da cewa naji ka dawo ban ganka ba tun tuni muna zuba ido shuru,Mohd cikin salon kallonsa yace ga yaron da ya rikeni da surutu ko wanka banyi ba,Naufal yace Amarya kawo min yata,Ramlat ta kai mishi yar baby, tana ce masa yanzu Nabeela ta shigo tana wajen Mami,Naufal yace sai na baki tukwicin albishir kafin na bar garin nan,Dariya sukayi gaba dayansu,Mohd ya jawo Ramlat jikinsa muje ki mun wanka,Kai ku karbi yarku wlh baku Isa ba zance zan tafi nima,
Dole ka jira mu cewar Sardauna,Ramlat ta janye mijinta har toilet dinsa ta alfarma wanka ta masa tare da shiryashi fes kamar wani Ango yanda yasha Shadda kai kace daurin aure zaije,wai duk kwalliyar Ramlat ce akayi mata tata daban itama ta dinga gani,

Suna fitowa Sardauna ya amshe yarsa ya zauna,Naufal ya mike ya bar palon sai part din Mami wajen Nabeela,
Yana Tafiya Sardauna ya jawo Ramlat dinsa ta kwanta shame shame a jikinsa,Hijab ya zare mata matsattun kayan dake jikinta suka bayyana dukiyar fulaninta rabi a waje farare dasu luwai luwai,Sardauna ya kwantar da Little Mami gefe can ya makale a jikin Ramlat dinsa,yana sakin ajiyar zuciya a hankali ya fara kissing dinta,Ramlat tana kwace jikinta kar ayi wani cikin,Sardauna yace kwantar da hankalinki ba abinda zan miki zafi zan rage,Ramlat tayi kicin kucin tace bata yarda ba ai ya mata alkawari sai sunyi 40days dinsu,yaufa 3days da yin

Please Login or Register in order to submit comment