Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tasa wata ta rakata takanas cikin kudin akuyarta ta dauka tayo kitson attach me shegen kyau,
Tasha lalle,cikin kayan da ta samo wajen Matar soja dai dai ita na yan gayu tasa Atamfa riga da skert ta dameta da kyar take motsi ciki,kanwar Babar Lantan ita ba ruwanta da Yiwa Yara fada ko tsawatarwa duk abinda kaga dama kayi haka take,
Tana ji tana gani Lantan tasa dan siririn gyale iya kanta ta fita ta hau Napep,
Sai da ta tabbatar anzo wani hadadden resturant na manyan mutane dama a wajen Saloon tace kai wai bayin Allah a nan jahar ina ne wurin cin abinci na masu kudi da kyawawa suke zuwa?Suka fada mata kuwa ta karbi Adress kala kala har na Hotels,gashi bata iya rubutu ba amma tace don Allah a rubuta mata ko wanne paper daban,ta karbi Biro wani tayi masa Amamar kan Jaki,doki,kaza,wai da haka zata gane.
Da ta hau Napep ma paper daya ta bashi,yace Hajiya kya bani takarda ki min kwatance,Lantan bata só ace kamarta ba ilmin boko,tace Malam bana son surutu da yawa yar madara kaga nayi kalar masu surutu?
Malam dalla ja muje kana Sa bakina yana ciwo ta fada tana yanga,
Ai ko mai Napep yace to ni kam ban iya karatu ba sai daí mu tambaya ko ki hau wani,
Lantan tace Kan Bantan Uba,ni zaka fadawa haka?kasan ni yar gidan wace?
Baka Isa ka bata min lokaci ba na tsaya har wannan lokacin magrib ta kusa zaka ce na hau wani,idan ban kira Babana ya garkameka ba kace shegiya nake,kace yar Zina ce ni,billahillazi sai na Sa anyi maganinka gwara ka kaini.
Me Napep yayi tunanin ko da gaske Lantan yar wani ce,

Wani me Táxi ya tsaida ya bashi Paper ya fada masa wajen dai dai bayan Magrib ya sauke Lantan,tace kudinka?yace dari Uku Hajiya,kacal?Lantan ta tambaya tare da mika masa dari biyar tace karbi na bar maka,mutumin ya dinga godiya ya tafi,

Lantan tana Tafiya tana karairaya ba tsoro ba komai ta shige cikin Resturant yuuuuu Alhazawa suka bi Lantan da kallo,matasa yayan wane sunga yar fulani yar gayu,Lantan ta nemi waje ta zauna tana bata rai,
Masu kawo abinci suka ce Hajiya me za a baki?da turanci ya fada, Gudun kar tayi kauyanci ta dakawa me kawo abinci tsawa kowa yana Jinta tace kai karka raina min Hankali mana kun iya Hausa kuna wahalar da shari'a Bazan bata lokacina wajen yi ma turanci ba kawo min dafadikan Shinkafa,idan babu ka kawo Sakwara da miyar agushi,
Ai ko Lantan ta birge duk mutanen da suke wajen nan,sai dariya akeyi yarinya da abin dariya,wani yace da gani waccen ta goge da duniya ba girman Jigawa bace sai daí Kaduna ko Kano Amma wannan tafi karfin Jigawa.

Me abinci jiki na rawa ya kawowa Lantan abinci tana ci tana yanga sai ga wani Alhaji me kudi dan Duniya yazo ya zauna Table din yace yan mata How far?
Lantan ta kalleshi ido cikin ido tace sannu Baffa,Alhaji ya hangame baki tare da cewa ina matashi na zaki ce min Baffa?Lantan ta sheke da dariya tare da zukar lemonta tace Wlh kafi Baffana tsufa hakan ma kara na maka,ai ko aka kara tintsirewa da dariya a wajen,
Alhaji yace nafi karfinki yanzu yan mata gasu nan ko ina suna tallan kansu duk inda ka zaga sune Resturant,sune Hotels,shopping Mall ma zuwa sukeyi su tsaya a wajen wajen ko a ciki ko suna daukan hoto su dau wankan fitar da sura Sabo da son abun duniya Maza na kallon su a titi macen arziki ta fito 10,11,12 etc na dare tana waje yawo a kwararo a titi suna jiran me kudi ya nemesu,wasu ma sai sun tabbatar da gidan kakarsu ko yar Uwarsu wacce bata kula da tarbiyarsu tasan ko me zatayi babu abinda zai faru sai ta koma gidan da zama ta dinga yawo waje waje Sabo da a samu miji me kudi ko dan wani,ko ta samu fasiki me kudi yana kashe mata kudi,duk gaku nan irinki dan kin samu na kulaki zaki min akuyanci yar akuya.

Tasssssss....kake jin Lantan ta dauke Alhaji da mari,tare da nuna shi da yatsa tace ahir dinka tsoho na wuce ka fada min haka,tunda na shigo kaga na kalli wani da namiji dan ya soni,mazan da kafin a samu na gari cikinku sai an tauna Azzalumai an bar Hajiya a gida da miyar Kuka anzo nan ana cin abinci tana kawowa ace ciki ya cushe,kaje ka nemi mace kayi iskanci da ita kaje gida kace wash na gaji sai bacci kwaaaa harda gwada minsharin Alhaji,jama'a kowa ya gani shi yazo ya zauna wajena Baffa bana neman irinka ko Karuwa ce ni nafi karfin nayi harka da kai komai kudinka ba kalata bace,ba Irina bane,ja jiki dalla Malam,

Alhaji yace kin san ko ni waye?ba kowa bane kai domin da wani ne kai wlh Baza ka tsaya Sa in Sa dani mace karamar yarinya a wajen abinci ba,idan da ka Isa kai wani ne sai daí ka turo min yaronka ko Katinka,baza ma ka min magana a mutane ba isar da ba a Isa ba.

Mutane har komawa akayi bawa Lantan hakuri,wasu sukace ashe tasan me takeyi yarinyar.
Lantan tana fita daga nan ta koma wani wajen Suya na yan gayu,burin Lantan ta auri dan gayu me rufin asiri ko dan kwakwarar Sana'a dan boko.
Tunaninta yawo da matsewa cikin kaya shi zai Sa ta samu miji.
Mata mu kula abinda ke faruwa yanzu kenan mace tsakar dare zaka gansu a wajen Resturant,Hotels,shopping malls etc a gefen titi suna tsaye anci uwar wanka Sabo da son duniya,tunaninsu ta haka za a samu miji me kudi,wasu kuma a samu na fasikanci wanda zai dinga kashe musu kudi.
Idan miji ne ko dan sarkin makkah ne ko kina daki bakya fita Allah ya tsara hanyar da zaku hadu,idan kina raye zaki aureshi komai dadewa mijinki zaizo akwai silar haduwarku indai Allah ya kaddara zaki aure zakiyi sai lokacin da yaso za ayi a daina gaggawa,kowa ya dinga ganin kamar shi yake tsarawa kansa rayuwa,ai mutuwa akeyi gwara koma waye ka samu ka kikara ka shiga,ba so ba komai kinyi kina ta masa hauka karshe ya sakoki,idan Allah yayi baza ki aure ba zaki mutu to ko ansa bikinki kafin lokacin kin rasu,idan zakiyi Allah ya hukunta dole ne,a daina gaggawa ana fadawa halaka.

Akwai yan matan da ake takura musu a dangi ko iyaye dole sai sunyi aure da wuri koma waye ka fitar dashi,ko ayi mata auren dole,ace dole ga wani me kudi shi ya dace,wata kuma ba so a ranta Amma zata iya auren mutum dan kudinsa taya zaki masa biyayya bakya sonsa sai kudinsa,ko an aura miki wanda bakya so dole zaman bazai dade ba,ayi gyara iyaye da yan mata da zawarawa,

Lantan tayi yawo Amma duk mutanen banza ke zuwa mata yan son murji da xxx Lantan taki yarda taci gaba da searching,kullum gidan wasu yan gayu yan mata makwaftansu take shiga suna kara wayar mata da kai akan harkar duniya.

Prof yana ta jiran Ramlat ta dawo shuru,wayar Mami bata shiga Ammi ma ta gwada shuru,haka ya hakura yace dole fa yan mata su fito da miji suyi aure ya gaji,idan ba haka ba zai iya basu ko ma waye.
Dole suka fara neman mafita.

Bayan sati daya Daddyn Sardauna ya koma gidan yaga tabbas da gaske Sardauna ya kwashe su Mami sun bar gidan,amma yasan Talauci zaisa su nemeshi tunda yanzu Mohd bashi da Sana'a.

Yau kimanin Sati guda kenan da zuwan su Ramlat Adamawa,suna zaune lfy cikin jin dadi da kwanciyar Hankali,abu daya ne ya sasu a matsala shine rashin na cefane,suna da kayan abinci na dan kayan miyane babu da wasu abubuwan,
Sardauna kullum a neman aiki yake da takaddunsa,mutumin da ya nemo musu gida shi yake raka Sardauna waje wajen neman aiki Amma ba a samu ba,ya dawo ko Mami ma baya fada mata dan kar ta damu,tunda suka zo sau biyu sukayi girki da nama,abinka da ba me kudi ba duk yan kudin hannunsu sun kare domin Mami tace gwara su rasa komai ko fara da yaji ce su dafa kullum suci shi yasa suka kwashe komai suka siya kayan abinci.

Ramlat wannan lokacin ba me wanki ba injin wanki,ba me aiki ita take musu komai na aikin gida,kafin Sardauna ya dawo daga neman mafita Ramlat ta gama komai na gidan,har wanki tayi ta busar ta goge ba a tara wanki kullum sai tayi har na Mami,
Girki kuma Mami watarana tana dan tayata,Kamar kullum Sardauna yaje neman aiki har companies da private ba a dace ba,ya dawo gida ba tare da ya nuna damuwa ba,Ramlat taci wanka cikin 3qtr da yar riga karama sosai tasha kyau komai ya bayyana,Sallamar Sardauna taji Mami tana daki,Ramlat ta amsa tana me sakar masa murmushi me matukar daukan hankali tare da mikewa tana Tafiya da karairaya ta fitar asiri,ta fada jikin Sardauna kamar yau ta fara ganinsa yanda take murna tana masa oyoyo,shagwaba take masa ta tashin hankali,ashe Ramlat haka take readers?

Sardauna duk bakin cikinsa ji yayi ya yaye gaba daya ya manta da komai,bai san Sanda ya dagata sama ba yana murmushi kamar ya dauki jariri bedroom ya shige da ita tare da fadawa saman gado suka zube,kayan jikinta ya fara cire mata gaba daya ya haukace,Ramlat ta shafo cikinsa My King yunwa fa?ko wanka bakayi ba ka bari sai ka huta am all urs muje ka fara tukun,shagwaba ya fara mata shi fa a'a gaskiya ita yake so,

Da kyar ta lallabashi ta kaishi toilet da kanta ta sallo masa wanka tare da shirya abinta,Sardauna ya zama dan gata ko riga Ramlat bata bari ya cire da kansa ita take masa komai na abubuwa da dama.

Jallabiya fara fitted ta Sa masa da Boxers yace zafi fa kin san gidan nan ba Ac iskar fankar ma ka cika sha Mura zata kama mutum,
Ramlat ta canja masa kaya Wando short da riga armless muje Dining ko?ko ka gaji na kawo nan?yace ae kawo min nan bari na gaisar da Mami,

Mami na saman Sallaya tana Lazimi ya zauna tare da kwantawa a jikinta Mami na dawo fa ya fada da iyayin muryarsa can kasa,

Shafa kansa Mami tayi tare da masa sannu da zuwa tana an dace kuwa? Sardauna yace ba a wani dace ba,kin san kasar nan bare kuma gashi bamu san kowa ba bare ayi mana hanya,Mami tace muna addua Allah zai kawo,Sardauna yace Mami gobe fa da kyar ma idan zan fita?Sabo da ba ko kwandala a ragowar kudin nan na wajen Ramlat,Mami tace nima kaga wlh ba kudin ba abinda zan bayar a siyar komai babu yau ma ragowar Naira dari ce aka siyo kayan miya,yanzu sai daí idan motarka za a siyar,Sardauna yace ai akwai wayoyinmu ni da Ramlat sai na siyar na canja mana kana na ayi amfani da kudin Amma ba yanzu ba kar azo wani Babban abu ya taso mu rasa yanda zamuyi Amma idan suna nan kinga sai a siyar,akan Aikin da bamu samu ba sai asara baza a taba su ba yanzu,

Mami mota ma Baza mu siyarta ba idan na rasa aikin kika sani ko na koma Taxi Driver,Mami Hawaye ya zubo mata dan tasi- tasi fa(Taxi) Sardauna ya goge mata Hawaye yana murmushin karfin hali yace haba Mami ai zaki karya min gwiwa,kawai kiyi addua,

Muhammadu Driban Tassi fa Haba haba kamar mun zagi walliyyai?kaje har turai da degree da masters Amma ka koma Dan Taxi.

To Mami ya kike so ayi mu zauna abincin ya kare ba abinci ba cefane ba sabulun wanka babu na wanki ina namiji da rai na da lfy ta,abin kunya ne dan na nemi na kaina ba da haka ake zama wani ba,bana jin kunyar komai ni kam haka zanyi,da ba motar ma sai na koma saida kayan miya salat da Tattasai,har Dako ma,Mami ta fashe da kuka,ganin ta shiga damuwa yace wasa yake tsokanarta yakeyi,Sai ga Mami tana dariya.

Ramlat ce ta shigo Mami kin rikeshi bai ci komai ba,iyyee kaga masu miji ji nake nan kike ce masa yaro?Ramlat tana dariya tace ai har yanzu yaro ne,
Harara Sardauna ya aika mata da wasa.
Hannunsa ta kamo taso ka biyewa Mami ita ta koshi,
Bedroom ta kaishi suka zauna saman karamin carpet dake jikin bed,ta bude flask daya yaga white Rice,ya bude karamin yaga stew ta jajjage harda kifi,ya bude wani plate me kyau salat ne da tumatir kadai,sai glass cup kuma Zobo ne yasha kayan kamshi,nan ya tuno da dane kaji zai gani Sabo da Ramlat mayyar girki da Kaza ce,
Yace uhmm da gani yayi dadi,Mami tace Naira dari ce a gidan taya naga kifi?Ramlat tace ina duba handbag dina na samo dubu daya wlh a ciki wanda ka bani ajiya rannan tun muna Kd,shine na siya kifin dari da kayan miyar dari,gobe kuwa kaga baka da kudin fita tunda kayan miya ne babu kawai ka rike dari taran gobe,sai ayi shinkafa da wake,ko dan wake, nayi tunanin nayi Alala kai kuma baka cinta ko ka zabi abincin da zaka iya ci ayi haka da yaji da mai,

Sardauna ya rungume Ramlat ashe Matata me hankali ce Allah miki albarka su Kawu sun iya haihuwa,
A cire Naira dari a siyo kayan miya sai kiyi mana ko Faten wake ko Jullop Rice ko dai wani abu da zaiyi dan dadi.
Ramlat tace an gama My King ur wish is My command,

Abincin ta bude tare da daukan spoon zata bashi yace a'a da hannunki zaki bani,Hannunta ta wanke tas sannan ta fara bashi yaci ya koshi yana Santi Sabo da Ramlat ta iya girki domin ta sha gwagwamarya itama.

Bayan sun gama komai ya jawo Ramlat da yamma lis,Ramlat bata hana shi ba Sabo da ita kanta yanzu ta fara sabawa da dadin harkar take ji,
Goge juna suka fara yi da salonsu,Sardauna ya rude yana tsotsar na shanunta,yana lashe mata sassan jikinta,nishin Dadi Ramlat takeyi Sabo da salon da yake mata ya wuce hankali,salo ne wanda ba ko wacce mace bace ta Isa a mata shi ba,wasu mazan ma basu san da kalarsa a duniya ba sai Sardauna wanda ya gama wayewa yasan kan harkar nan ta gaske.
Ramlat ta gama birkicewa kawai sambatu takeyi tana kara canjawa Mohd Sardauna tunani,ta kwance masa notin tunaninsa babu, an rasa wanda ma yafi wani zaucewa cikinsu

Sardauna ai yana tsomawa jirginsu ya bar kasar suka shill a wata duniyar ta Musamman basa ji basa gani.







AsmaBaffa loves u all readers
[10/7, 1:54 PM] 0mmr Farouk: 🏀🏀🏀🏀🏀🏀
🏀🏀🏀🏀🏀🏀


DUK INDA TA FADI





2pages






211-215 216-220





Official





By
AsmaBaffa








Wannan page page nakune
RUKAYYA
HERNEE
MAMAN UMAR

Godiya gareku
Mum Iftee
Flower
Jannat
Diyar katibi
Sameeran Gaya
Jidder Zaria
Zainab Atiku salama
Fatima Abdullahi

Jinjina da jin dadina ga

AsmaBaffa Fans club
Taskar Firdausi sodangi
Hause of Hausa Novels
Kuna matukar birgeni da Sharhi kullum ba fashi na gode kwarai kunfi masu tnx birgeni duk da suma ina ji dasu, kun fisu, taku ba irin tasu bace.

Ayi hakuri da typing error dole da mantuwa.








Ko yaushe su Ramlat jiya i yau,yau fari gobe dai gashi nan Sabo da rashin na cefane da aikin Sardauna.
Sun kwashe wata Uku kenan abincin nasu ma wasu sun kare,sabulan wanka da wanki da abubuwan amfani wanda ya kama dole duk sun kare wasu kuma saura kadan,
Duk da haka baza ka taba cewa suna cikin matsala ba,yanda suke haka suke Sabo da karfin addua da wadatar zuci.
Yau Sardauna bai fita ba kasancewar ba ko kudin Napep bare na man mota,Ramlat ta shiga damuwa basu da wake bare ayi shinkafa da wake da mai da yaji,
Kawai tunowa tayi akwai ragowar kayan miyar jiya da ta rage kadan,kitchen ta shiga tare da dubawa fridge ba komai sai gayyen Alayyahun jiya da yakuwa,
Gyara komai tayi fes ta shirya lafiyayyen Faten shinkafa yayi dadi sosai,zobo take so ta hada ba sugar ba kudin siye
Domin shike nan ragowarsa suka sha shayi lipton kadai,haka ta hakura sai ruwa,da ruwan jarka suke sha,yanzu babu na jarka sai Pure water,shima yanzu kusan ma na pampo Ramlat take Boiling tare da tacewa tasa a fridge su sha,
Gas babu ba kudin zubowa,sun koma risho,Tayi tunanin fara hura itace Sardauna yace sai daí idan ba ransa kerosine suke amfani dashi a resho sai murhun gawayi coal duk tana amfani dashi yanzu sun dade babu Gas.

Tana so ta musu wanki amma ba sabulun yi,ashe Tsabta ma sai da kudi akeyinta,Kayan wanke toilet duk babu,haka ta koma Amfani da toka, Lalle da kuma Normal omo suna kashe kwayoyin cuta da datti ko wari,
tana tsaftace musu komai,
Tana gama girkinta ta zubo suna shan faten shinkafa tare da Sardauna yace Chairwoman?me ya ka mata ayi na sana'a aiki bai samu ba, ki kawo wayarki da tawa a siyar mu samu jari,
Ramlat tace sai dai na saro Alawa da kayan zagi na Yara na dinga siyarwa? Sardauna yace ai Kanti zaki bude a gida irin su Maggi,curry kala kal,wake, sabulai da abubuwa wanda ya Zama dole ayi amfani dasu.

Ramlat tace an gama kai kuma fa? Motar nan za awa paint na Taxi na fara kawai ko ma samu mu tsira da mutuncinmu tun kafin abubuwa su kachame, amma kar a fadawa Mami baza ta bari ka zaman Taxi man ba.

kayi yanda ya dace ta mika masa wayarta tare da zare simcard da Memory ta bashi tana murmushi,
A ranar ya siyar da wayar Ramlat dubu talatin,ya siyo mata karama Tecno ta dubu Shida, tasa kuma dubu dari da biyar, shi bai ma siya wayar ba,mota ya dauka ya mata full tank tare da mata paint na taxi, duk wani kayan abinci ya siyo ba laifi zai kai na 2mnths har Gas risho da coal duk an siyo da yawa,har naman miya yau sunci.

Ramlat kuma duk an siyo mata kalolin su Maggi,curry,wake,da sauran kayayyaki da yawa na amfani zata fara siyarwa da mutan unguwa yan kadan suka siya na bude kasuwa.

Sabo da haka tana gama komai ta shirya sosai ba wanda zai ce tana da aure Sabo da Ramlat ta Hadu ta ko ina, shigar mutunci tayi sosai,
Makwafta ta shiga ta dinga sanar musu abubuwan da suke siyarwa,gidajen unguwarsu duk masu kudi ne most of them,
Wani gidan hamshakin me kudi da kyar ta samu masu gadi suka barta ta shiga a hakan ma Sabo da kyanta,tayi kalar masu kudi suka barta ta shiga,da Sallama ta shiga palon Maza samari matasa da mata tare da Yara rakwacam ne suka amsa mata,mazan sai kallonta sukeyi tunaninsu yar wani me kudi ce hannu bibiyu suka karbi Ramlat,

Dattijuwa da Alama itace Hajiya da taji suna kira cikin shiga ta gaske ta fito suka gaisa tace ban ganeki ba yan mata?
Ramlat zata fara magana kenan sai ga me gidan ya fito Alhaji dashi,
Babban dan nasa ya kalla yace Mustapha a dage da karatu fa,naga wasa kuke,kun san mu karatun Muhammadiyya mukayi bamu san komai a na nasara ba,kuna dai gani ko zo in kasheka da Hausa Bazan iya karantawa ba, ga yan kannenku nan Yan 12,13,11,10,6-7yrs kunga suna da yawa dan Allah a dinga duba aikinsu kunga duk na karshen aji suke dauka Sabo da rashin me tsaya musu,duk cikin Yara na babu me kokari, Allah bai Sa Nayi boko ba amma ya jarrabceni da son dan Boko.
Ku kun iya Amma baza ku nuna musu ba mene amfaninsa?
Wani a Cikin Mazan yace Abba yaran nan mu baza mu iya da kwakwalwarsu ba sam.

Ramlat nan take ta fahimci abubuwa da Sauransu,tazo tallan su Maggi sai ta canja tare da cewa gaskiya dama baku sanni ba wajen Alhaji nazo an Aiko ni magana zamuyi dashi Amma tana bukatar Sirri.

Alhaji yace yarinya ni fita zanyi Kasuwa muje waje na ganki ki fadi matsalarki,
Ramlat tiryan tiryan tabi bayan Alhaji har Compound inda jerin motocinsa suke,sannu Baba ina yini?Alhaji yace lfy lfy Alhmdllh ya akayi? kirrrrr wayar Alhaji tayi kara,Ramlat ya mikawa wayar yarinya dan duba min waye yake kirana kin san ba boko na iya ba,

Ramlat ta karba tare da cewa Bala me Kusa kasuwa,aiko ya karba yana dariya ya daga suka gama waya,yace to ke ya akayi yarinya me basira da hazaka?
Ramlat tace ni makwaftanku ce Baba ni kuma malamar primary schl din yaranka kanana ce,Baba ya kyakyace da dariya yana to to to su Iklima,Maryan,su Abba na,Ameer,gasu nan da yawa a Makarantar ai,Ramlat dadi ya kasheta ta canka dai dai,tace Alhaji ni a America nayi degree da masters,Alhaji Sabo da bashi da ilmin boko komai yarda yakeyi gaskiya ne in dai ya danganci boko, kuma mutum yana cewa yana da Degree to Alhaji zai dinga girmamashi kamar Sarki, yace Allahu Akbar da gani Biri yayi kama da mutum, Ramlat tace a gaskiya Alhaji su Iklima basu da kokari ko kadan na karshen aji suke dauka,ya kamata ka daukar musu malami ko malama me musu lesson a gida Saturday Sunday, ba neman aiki nazo ba amma idan kace na fara koyar dasu weekend zanyi farin ciki su zama masu kokari,

Alhaji yace Alhmdllh inda kikayi tattaki tun daga kasar nan Nigeria kika tafi har America kika yo Ilmi kizo har gida kamar ki kice zaki koyawa yarana karatu ai ko nawa ne zan biya domin ki koyawa yarana dama na rasa yanda zanyi da rashin kokarinsu,zan dinga biyanki 20k a wata,Ramlat tayi murna tare da godiya tace gobe Saturday zan fara zuwa?Alhaji yace me za a fasa mutuwa ko Hisabi?ai kawai kizo ki fara naga yarana suna cin na daya a aji.

Ramlat da farin ciki ta dawo gida tare da fadawa Mami abinda ke faruwa ta samu aiki,Sardauna ma na shigowa da murna ta tareshi tare da danewa jikinsa ta makalkaleshi tana bashi labari yaji dadi sosai tace shike nan baza kayi driving Taxi ba a goge painting kaji.

Murmushi Sardauna ya saki tare da kallonta cikin kauna da shaukin so yace ki nemo mana na nemo mana nima mu dage kawai Amma ina namiji ki fita ni ina gida a'a,
Yanzu ma da akwai yanda zanyi bazan yarda kije ba, dan babu yanda zanyi ne amma indai na fara Driving Taxi ina samu ba inda zaki,abinda na samo Allah musu Albarka,amma yanzu kije goben mu gani.

Washe gari kuwa Ramlat ta shirya har gidan Alhaji,Hajiya

Please Login or Register in order to submit comment