Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ramlat kayanta sannan ta kaiwa Sardauna nasa kayan shima,
Mami tace yan mata wannan rigar taki fa kamar ta Maza?Sardauna yayi maraf Mami sun baci tana period bata sani ba shine na bata nawa,Mami tace kai na tambaya?Allah muku albarka sukace Ameen.

Je kiyi wanka ki huta kizo kuci abinci,dakin da Baba ta kai mata kaya ta shiga,
Sardauna ya miko ya kwaso jallabiyoyinsa kala Uku,da t-shirt Uku,boxers tight Uku ya kaiwa Ramlat dakinta ta fito daga wanka ta ganshi yace gashi nan su zaki dinga sawa Sabo da yau Bazan iya fita siyo miki kaya ba gobe ma haka sai jibi,kiyi manage da nawa,Mami nata Baza suyi miki dai dai ba kinga tsohuwa ce kuma tana da kiba sosai.

Tnx tace ya bar mata dakin ya koma wajen Mami ya sanar mata tace ba matsala ai dama kayana Baza suyi mata ba sam,
Mami akwai fa magana babba sai gobe idan na huta zan fada miki komai,to Allah kaimu Muhammadu.




AsmaBaffa





AsmaBaffa
[9/19, 11:40 PM] ‪+234 903 434 4926‬: 🏀🏀🏀🏀🏀🏀
🏀🏀🏀🏀🏀🏀


DUK INDA TA FADI



61-70



Official



By
AsmaBaffa





Hause of Hausa Novel ina godiya da sharhi tare da sauran groups.




Tana gama wanka ta wanke kayanta tas ta shanya su a toilet din, canja jallabiya brown tayi tsayin ne kadai ke mata yawa Amma fadin bai mata yawa ba.
Dafaffiyar gyadar da Data hade da carrot sai kilishi ta kawowa Mami har Bedroom,Mami sai murna takeyi tace bari na wanke su a shirya a fridge gyada kuwa yanzu zamuci mu barta,
Palo suka dawo suna ta ci harda Baba,
Mami kallon Ramlat tayi tare da cewa abincinfa? Ramlat tace ai mu duk a koshe muke tunda muka taho muke ciye ciye,
Dariya Mami tayi tace aikin Mohd ne ko? nasan halinsa idan tafiya ta hadaku to komai kika nuna sai ya siyo maka,yayi ta faman cika maka ciki,
Dariya sukayi gaba daya,Sardauna shima ya fito cikin 3 qutr da t-shirt arsh color yayi kyau sai kamshi yakeyi.
Jikin Mami ya kwanta saman cinyarta sai shagwaba yake zuba mata,
Ramlat mamaki ya kamata ta bude baki tana kallonsa.sun dade suna hira sannan kowanne ya tafi makwancinsa.

Kauyen jigawa matasa samarin Ramlat sunji labarin ai Ramlat balarabe ta aura me kudi,ranar yazo ya aureta,sadakinta kusan milliyan daya,haushi suka ji tare da hada meeting zasuyiwa Idrisa zanga zanga sai an biyasu kudin zancensu, Dafta Jibrila shine team leader,sunkai wajen su Hamsim suka hada kungiyar zanga zanga suka jera suka tafi gidan Idrisa suna sai anbamu kudin zancenmu sai an bamu,an cucemu an cucemu,a bamu kudin mu a bamu.....har gidan Idrisa suna ta da Kura ga Yara na binsu.

Idrisa ya fito da sauri cikin hargowa yace lafiya???? Team leader yace an zaluncemu,an tozarta mu,an ci mana mutunci yarka ta nuna mana bamu san me mukeyi ba,bamu waye ba,to bari kaji nayi maka da hausa dole a biya mu duk abinda muka kashewa yarka,
Idrisa ya kallesu sama da kasa tare da cewa idan kuma ba a biya bafa? Wlh sai mun daki kudinmu cewar Saminu,
Idrisa ya saki dariya yace to sai nima ku tsiro min zancen yata da tayi daku a tsinke,ma'ana duk zance ko dariya da tayi daku ko wanne ya tsiro min shi a tsinken tsire ya kawo min ni kuma zan biya ku kudinmku,

Amma ruwa zafi sanyi sauro duk ya cije min ya Sabo da ku jahilan kauye ne zaku ce a baku kudin ku,rokarku akayi?wa yace ku bata?ku bakuji kunya ba? Soyayya ta cinye kudinku kuma wlh idan na sake ganin wani a gidana sai na sumar dashi,

Team leader Jubrila yafi kowa rashin kunya yace kai tsohon banza dan wiwi barawo, sai ya fara hado turancinsa I study world ( ya karanci ),you will not open our eyes, ( baza ka bude mana ido ba),we are big people, manyane ,(mu mun san me mukeyi),a hyaner can not say a dog is a witch,(har kurace zata ce da kare maye)?
Sauran mutane suka tafawa Jubrila yana ta turancinsa,

Idrisa kuwa dariya yayi yace kauyawa shirme yakeyi kuna tunanin turanci yakeyi,gida Idrisa ya shiga tare da dauko katuwar tabarya,ga wani Katon dutse a hannunsa,suna ganinsa ya fado cikinsu ya kai duka Allah ya kiyaye bai samu wani ba suka kwashe da gudu suka bar kofar gidan sunga fa Idrisa ba hankali da gaske yake.

Washe gari da Safe da wuri Ramlat tayi wanka ta shirya cikin jallabiyar Sardauna milk color me hula a baya ba tare da ta daura dankwali ba kawai ta gyara gashinta jelar na yawo a kafadarta ta fito palo ta duba ko ina ba kowa sai Baba a kitchen,gaisheta tayi tare da tayata suka gama abincin,sannan suka gyara gidan ko ina banda dakin Mami da Sardauna.
Me gadi Baba ta kaiwa abinci,Almajirinsu ma yazo ya karba ya tafi,
Ramlat sarkin ci Zama tayi tare da shan tea da chips sai farfesun naman rago,
Ta gama ta bar Dining din ta shige dakin Mami,Mami tana Sa kayanta Ramlat ta gaisheta har kasa,Cike da fara'a Mami ta amsa mata sannan tace Mami nayi breakfast ni,bari na gyara miki dakinki mun gyara ko ina da Baba saura nan da dakin Mohd dinki.
Murmushi Mami tayi tare da cewa Baza ki bari ki huta ba ko Ramlat,Mami ai ba wani aiki bane,to shike nan gyara bari naje na karya.
Tana fita Ramlat ta gyara room din da toilet ko ina yana sheki da kamshi ta fito tana Mami jikanki bai tashi ba bare a gyara nasa,
Mami tace Sardauna ai sai wurin 2pm zaki ganshi ya fito indai bazai je aiki ba to baya tashi da wuri,aikin ma idan zai je da kyar nake iya tashinsa akwai nauyin bacci.
Zama tayi tana ta kallon tashar larabawa,saida ta kai 12pm tana faman kallo sannan ta koma room dinta tare da cire jallabiyar tasa t-shirt da short wandonsa ta kwan ta sai bacci,
Ba ita ta tashi ba sai 2pm,a gurguje tayi wanka hade da Sallah sannan ta shirya tare da maida jallabiyarta ta dazu ta fesa bodyspray dinta ta fito palo,
Mami ta gani tayi shirin fita,tace Ramlat zanje makwafta yinin biki ga abinci can a dining ki eba ki ci,to Mami a dawo lfy cewar Ramlat,

Tana zama a dining Sardauna ya fito cikin dogon Wando pencil sosai na Maza Jean dark Brown sai singlet yasa sarkar Azufarsa karama yayi kyau sosai sai kyalli yakeyi da kamshi,
Dining ya zauna shima,ko kallon Ramlat baiyi ba yayi serving kansa ya fara cin abinci,Ramlat tace lallai dan wulakanci kamar ma bai sanni ba,
Ya Sardaunan Mami good afternoon, ba tare da ya kalleta ba yace How u? tace am Good.
Babu wanda ya kara magana,Baba ce ta fito daga kitchen tana faman Yiwa Sardauna kirarinta na yau da kullum,sai ga Sardauna yana fara'a sosai,
Ramlat a ranta tace ikon Allah kuruciya kenan.
Baba tace Ranka ya dade bari a gyara ma dakinka,no Baba ki barshi ki huta kinga wacce zata dingayi kullum da room dina dana Mami Sabo da aikin ya miki yawo,
Baba tace godiya nake Ranka ya dade na Mami.

Ramlat kuwa baki ta tabe tare da mikewa ta karbi kayan share share da goge goge ta wuce dakin Sardauna me matukar kyau,kamshi da tsafta baya bukatar gyara sam Amma haka ta kara gyarawa sosai,ta fada toilet kamar dan Adam baya shiga ciki Sabo da tsafta,.
Wankewa tayi sosai tasa turarukan da Baba ta nuna mata na daki harda su turaren wuta Amma me ruwa na fesawa.

Kulle komai tayi tare da karo karfin Ac,zata fito Sardauna ya shigo yana magana zauna ki min Hira da Kirari ko ki karanta min English Novel din nan,
To bari na maida wannan abun sharar,
Bayan ta dawo ta zauna saman Sit din madubi,wanne zakiyi a ciki? Tace kawo na karanta ma Novel din,karba tayi ta bude first page zata fara Mami tayi sallama tare da shigowa dakin,fuska Mami ta tamke lfy na ganku a nan dakin?ni fa bana so ku dinga kebewa Sabo da gudun shedan,ku ba muharramai bane aure ya hallata tsakaninku bana son zama one room,
Murmushi Sardauna ya saki tare da cewa Mami kin makara dama maganar da nake muyi dake kenan zauna pls kiji komai,

Zama Mami tayi gefen bed tare da cewa ina jinka,Mami dana je kauyen Su Ramlat ya kwashe abinda ya faru kaf ya fadawa Mami,

mamaki ya kama Mami tace Muhammadu nasan baka karya Amma Bazan gama yarda da zancenku ba sai naji daga bakin yan uwan Idrisa da shi kansa Idrisa kuma a hada ni da Hafsatu,
Amma dan shirme me yasa baka kirani a waya Ba kawai dan kuruciya sai a daura ba dangin ubanka,Mohd yace to nima ai ba sonta nakeyi ba kawai taimako nayi zaki ta min fada kuma dangin Dad bake kika ce kar na neme su ba Sabo da dalilinki,ai ga Umman su Ramlat ne itama danginsa ce,
Haka kawai ki barni na nemi yan Uwa da iyaye kika wani ki yarda Sabo da ke dama ba wani zumunci kikeyi ba,Mami baki bude tace to dan ubanka Muhammadu kai ba sai kayi ba,
Ramlat tace Mami kyaleshi baki ga yanda ya dinga jin tausayin Ummammu ba,wai harda kawunmu ya karar da kudinsa a kansu tunaninsa zasu canja hali,
Wlh Umma Baza ta canja hali ba sai ikon Allah yanzu da za a je maybe ta bar su Shaheed ta bar kauyen,wani halin Umma idan tanayi ai har gwara Kawu,Kawun ma duk kanwar ja ce babu na zabe.

Mami tace kyaleshi yayi ta yi idan ya gaji zai daina,bai san su bane sai sun kusa sashi hawan jini,kekam Ramlatu Allah ya hada ki da miji anan,Amma kuma nayi matukar murna sosai da wannan lamari,

Kira min yan Uwan kawunku naji daga bakinsu Mami ta furta baki har kunne Sabo da farin ciki,
Number Abu Ramlat ta bawa Sardauna ya kira ring daya ta dauka ya mikawa Mami wayar ai kuwa Mami taji gaskiya Sardauna ya fada,bayan Abu ta kira A'i taji iri daya,ta kira Idrisa shima ya tabbatar da zancen har ya hadata da Hafsatu,harda Kukan murna Sabo da tayi waya da Maminta,Allah sarki da da mahaifi...saida suka sha hira ma sosai sannan sukayi Sallama ta hada ta da Ramlat suka yi hira Sama sama sukayi Sallama ta mikawa Mohd wayarsa.

Mami tace an kwace min miji ashe kishiya ka rangado min ban sani ba,ka shirya zuwa zumunci sai ka dawo da aure.
Shuru sukayi duk kansu Ramlat sai kunya takeji ba shiri ta bar dakin,
Hadasu Mami tayi ta musu nasiha sosai,ta kara Yiwa Sardauna daban nauyi yanzu ya hau kansa.

Mami na barin dakinsa ya kira Naufal ya sanar masa komai ai kuwa ya dinga masa tsiya da dariya,yace dole ayi dinner, Sardauna yace ai dama so nake mu shirya komai,duk da ba auren so bane tayi dirty yarinyar bana so frnds suce boyeta nakeyi kar a ganta Sabo da yar kauye ce bata hadu ba.
Naufal yace haba ai dole mu gigita guys a wajen nan Party za ayi iya party na gaske na bugawa a jarida kawai mu fara shirye shirye nan da next mnth sai ayi party na kece raini,Sardauna yace ai dole su san mun Faso gari,amma fa zasu sha mamakiinka wa ya zaci Sardauna zaiyi aure yanzu,tunaninmu duk sai mun rigaka,kalli ikon Allah dama shi aure zuwa ne idan Allah ya kawo babu makawa sai anyi ko kana so ko baka so cewar Naufal,
Sardauna yace kamar a film frnd ni kaina mamaki nakeyi,za a sha mamaki wajen mutane,kawai ka sanar musu suyi hakuri ba shiri akayi auren basu samu katin gayyata ba Amma akwai dinner next mnth.

Naufal yace yanzu Amaryar tana ina shegen gari? Tana nan yanzu ta bar room dina cewar Mohd,Naufal yana dariya yace yaya to mutumina ko ka fara rage zafi ne? In ma na rage sai na fada maka ance ma yaro ne ni,ba abinda nayi to kawai Novel din nan zata karanta min wanda muka siya,au ta iya karatun turanci?ashe to ba a kauye take ba cewar Naufal,Sardauna yace ta iya sosai a Abuja fa ta taso kawai dai daga baya suka koma kauyen,ok yanzu naji zance,
Kai dai ka dage kayi auren kaima ka auri Sameeranka tunda kana sonta haka duk da nasan ba wani haduwa tayi ba wankanta ni bai min ba,
Naufal yace duk wankan Sameera zaka ce bata waye ba? ni to haka nake sonta zan aureta tunda auren wuri za ayi mata dai dai ni ce,gashi nan ai duk tsirfa da iyayinka ka kare a kauye wa yasan kalarta ma ko mummunan ce,maganinka kenan kuma dole frnds susha news,

Dan Uwarka ka dade baka basu labari ba sai me yar uwata tace sai me kuzo ku ganta mana munafikin banza Allah sa Sameeran tace bata sonka.
Dariya Naufal yayi yace kwantar da hankalinka ba fada musu zanyi ba zance kawai kayi aure ai Bazan tona ba ka sani,ka tona mana matsalarka ce tare da kashe wayarsa.

Bayan Sallar isha Duk kansu suna dining suna cin abinci, Mami da Ramlat ke hira Amma Mohd baya magana ma waya kawai yake dannawa tare da cin abinci.

Wanka Ramlat tayi tare da shirin bacci sanye da boxers da t-shirt din Sardauna nafeela tayi sannan ta kwanta tana tunani kala kala,
Mami ce ta shigo da Sallama tace ya na ganki anan Ramlat? Mami ban gane ba,hm Yara kenan ai tun farko da nasan an daura muku aure bazan ware miki daki ba,sai ki dinga zuwa dakin mijinki kina kwana can,
Ma.... Mami... Dan Allah ki barni anan taimaka min kawai fa yayi dan kar a daura da tsohon nan,amma ai wasa akeyi fa Sabo da Kawu shine ya daura auren Amma mu ai bama so bayan haka ma Sabo da mu kubuta akayi hakan,
Dariya Mami tayi tare da cewa idan baki da Ilmi Ramlat Sardauna yana dashi ya sani,dole na saki a Islamiyya ya za ayi aure da williyai da shedu da komai kuzo kina shirme,
Mijin naki yaro ne fa idan yaga wata fa gobe? Mami sai ya kara aura su zauna ni kuma dama ai ba da gaske nakeyi ba,
Bana son shashanci Mohd dina nutsatse ne nasan kuruciyarsa me kyau ce baya muamula da mata karki ki jawo ya fara dalilinki,idan da ya hakura bashi da aure yanzu zaiga ya girma ya Isa harka da mata tunda yasan har aure ne dashi dole wannan tunanin zai darsu a ransa,
Baki ta zumburo kedai Mami kawai kice kinfi son Sardaunanki a kaina tunda ke kika raineshi,yau naji yar banzar yarinya Kishi kikeyi Aiko dole ki dinga kwana wajensa domin ya zama babba tunda ya aureki,ke yanzu kinyi dai dai kenan?duk halaccin da yayi miki baki gani ba?
Mami Sonfa kaine wannan dan kawai ke kika raini Mohd shi yasa kike kareshi,ae naji muje na rakaki,yanzu Mami ko gyaran Amarya babu ba biki ba komai ni gaskiya ba a sona wlh,

Zan mareki Ramlat ina wasa dake wuce muje,Sardauna da kike gani ya fiki sanin wayewa da harkar gyara ki bari ki gani sai yasa anyi miki,gata nake miki Sabo da ki mallaki zuciyar mijinki da wuri kar ya hango wata,
Ke yanzu baki da hankali Baza ki gane nufina ba sai nan gaba,

Muje nan gidan mijinki ne ba gidana bane,shi ya Gina abinsa nasa ne babu wani Gini da zai miki daban bare kice za a kai Amarya nan ne gidanki,ki dauka ni kuke rikewa da ciyarwa bani keyi ba,domin shine yake min komai na rayuwa,Sardauna yafiye min Kabiru da Hafsatu dana Haifa a cikina,nafi sonsa dasu tashi muje Baza ki samin jika a wani Hali ba,da ran Muhammadu ya baci gwara ran Mutanen Nigeria ya baci gaba daya,muje karki yarda naji yace kiyi masa wani abu kinki yi kome yake so kiyi wanda baya so kar kiyi shi,idan kina so mu zauna lfy kibi mijinki,sosai Mami take mata fada har room din Mohd,
Ramlat tace Mami yanzu kinfi sonsa? Mami tace bata bakinki kikeyi Ramlat,Muhammad ya soki shi zaisa na soki son da nakewa Mohd shi zai shafeki duk da cewa kema jini nace ina kaunarki sosai Amma Mohd yasha kan kowa tsakani da Allah nake fada miki ko Yayana na ciki na Mohd yafi su a wajena,indai Mohd yana son abu to nima ina so,sabo da haka Muhammadu ya Soki nima na soki ki dage ki kular min da abina,tsoka daya a miya,daya tamkar da dubu,

Mohd yana jinsu yana latsa waya yasan dama Mami ta fada masa dole tare zasu dinga kwana shi yasa bai yi mamaki ba,kuma Mami ta fada Masa tafi Son Ramlat dashi ma,yaso Ramlat ta kara Sonsa sosai .
Taya zai iya Sonta shi kuwa?Ya kasa nemo amsa,
Mami ce ta katse masa tunani kaji dai me na fada maka ko?yace eh Mami naji to ka kiyaye gata nan saida Safe.
Yace Allah tashe mu lfy.

Ita kuwa Ramlat haushi take ji Mami Sardauna kadai take so banda su,







AsmaBaffa
[9/19, 11:44 PM] ‪+234 903 434 4926‬: 🏀🏀🏀🏀🏀🏀
🏀🏀🏀🏀🏀🏀


DUK INDA TA FADI



71-80



Official




By
AsmaBaffa






Mami fita tayi tare da rufe musu kofa a ranta tana wa yace Ku yarda a daura zaku kawo maganar banza.
tunda Ramlat ta shiga takaici na Cinta ta hau saman Bed tayi kwanciyarta ba tare da tace komai ba,Sardauna yace sauko min daga Bed sai dai ki kwanta a kujerar can ko kiyi shimfida a kasa bazan iya bacci dake ba,
Bana iya bacci da mutum a Bed dina sabo da kadan yake min.

Mami tace da sassafe zata shugo tagani a kasa na kwana ko a ina kuma fada zata min tace kai kadai take so a duniya ya kake so nayi to,
Ai ko bakin ciki zai kasheki akan kishi Dani wajen Mami,ki ganni da abata kizo sama ta kai kice zamu Zama matsayi daya kema kin San bazai yuwu ba.

To ba sai tayi ta Sonka ba mana ni ina ruwa ko ciki zata maida ka ta kara haifoka,
How dear u talk to me like that, am i ur mate mate? U better mind business cewar Sardauna cike da masifa,
Saukowa tayi kasa wai tayi zuciya tayi kwanciyarta a kasa Bama a carpet Din dake gaban gadon ba,kasan tiles ta kwanta koma me zai faru ya faru.
Kin taimakawa kanki cewar Sardauna,
Kwan kwan Mami tayi knocking,ai da gudu Ramlat ta fada saman Bed din tare da shigewa blanket,Shigo Mami cewar Sardauna, a'a ba shigowa zanyi ba leko ka karbi sakonka.

Budewa yayi kafin yayi Magana Mami ta mika masa Leda katuwa Baka ta juya abinta.
Rufe kofar yayi tare da bude ledar kaza katuwa gashashiya da fuits Apple da inibi suma ledarsu daban sai yogourt da lafiyayyar fura me sanyi,ruwa da juice,murmushi ya saki yace Mami na kenan Na gode Allah biyaki.
Fakat Ramlat tace me ta baka mu gani?ta furta kamar yarinya
Bude mata yayi ta gani harda shakar kamshin tace uhmmmmm daga gani akwai dadi lallai Mami tana Sonka,

Sardauna yace ai baki ga komai ba,sakkowa tayi kasa tare da Zama gaban sa,tace to ni da wuri zanci nawa zuba min a wannan ledar,
Kallonta Mohd yayi sosai yace ke kinfi kowa kwadayi a kasar nan,kinma San ma'anar kazarne da Mami ta kawo lallai yarinya,
Ni ba sai na San wani ma'anarta ba dan Allah muci karta huce,
Dariya ma ta bawa Sardauna yanda take mika wuya cikin ledar tare da lashe lips dinta.

Furar ciki ya dauke yace ga shi nan kici ko mene kinga nawa ni,
Dubawa tayi taga fura roba dayace tal a hannunsa daga yogourt sai fruits da kazar da kuma ruwa hade da juice,kallonsa Ramlat tayi ni me yasa ake min haka ne? Ina favorite dina nima?yace me?tace fura mana,
Ai ke kaza ce taki ko du ki cinye ta baki da matsala.oh naji to Dan Allah ka sanmin taka na sanmaka tawa kaji,
a'a bazan iya ba kowa yaci nasa dazu wacce rashin kunya ce baki min ba? bafa rashin kunya nayi ba kusan fa shekarunmu daya fa 7mnths ka bani don na dan tsokaneka kai baka San wasa ba? Wasa fa nake maka.

Musha furarmu kaji Na Maminsa,Dan Sardaunan Mami Allah maka albarka dai kullum addua nake maka me taimakon Alumma,kyakyawan Mami dan gayu,
Eh yanzu kya fadi haka mana tunda abu kike nema dazu mene baki ce min ba,ai na daina to yi hakuri,zan baki kisha Amma sai da sharadi,eh naji zanbi,sai kinyi alkawari Baza ki kara Cemin Sardauna direct ba ko Mohd gatsal,sai dai yaya Sardauna ko Ya Mohd,nayi Alkawari Amma nima duk abinda nake so zaka min? Har waec zan biya miki na kaiki University,

Murna ta lullube Ramlat nan take tace nabi an gama Ya Sardaunan Mami ,Ya Mohd din Mami yaya Sardauna.

Yawwa to kinwa kanki gata kuma Bana son ki dinga jayayya Dani abinda nace shi zakiyi,da Sauri tace yi nayi bari na bari an gama Ya Mohd na Mami ikon Allah.
Murmushi yayi tare da cewa to da wanne za a fara? tace da fura sabo da kar cikin mu ya cika mu fasa Sha,
budewa yayi tare da mika mata spoon suna ta Sha kafin ya kai 2 spoon Ramlat tayi biyar.

Suka ci kazarsu yasha Ruwa sannan yasha fruits ya shiga Toilet wanka da Brush yayi sannan yasa riga armless ta bacci da wani guntun short irinsu daya da rigar.
Ya gama shafa turarukansa,har yau Ramlat tana ta ciye ciye sai da taji ta daf sannan ta kwashe komai ta kai kitchen tare da gyara wajen tasan halin Mohd da tsafta,
komawa tayi room dinta tayi Brush tare da wanke hannunta

Please Login or Register in order to submit comment