Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanzu nasan sadaki ko nawa ka bayar baka biya ba,zan kara miki Sadakin ki kinji yar Kawu?Ramlat tayi banza dashi bacci ya kara daukesu,Har 3pm basu fito ba ko Leke,sallah kawai sukeyi su sha Fresh milk sai bacci,
Mami ce ta gaji ta kwankasa tare da cewa lafiyarku kuwa?Sardauna yana jikin Ramlat yana ta faman wasa da kirjinta yace gamu nan zamu fito.Ramlat kuka takeyi,Sardauna yace ke nifa ba kari zanyi ba sai dare kiyi ki warke kafin dare kinji sweet Honey,
Wanka sukayi tare Ramlat tana shan gashi wajen Sardauna kamar wata kwai haka yake ji da ita,
Saida suka shirya yace tunda baki da lfy ki kwanta zan kawo miki abinci da komai,
Da ido kawai take binsa da kallo,
Bayan ya fita da 10mnt sai labari yake zubawa Mami na duniya kamar ya zare,yana ta farin ciki,Ramlat ta fito kamar yar kaciya,
Mami tace ke me ya sameki Ramlat tace bigewa nayi a cinya Amma nasha magani,

Ta zauna kusa da Mami tana Hawaye,Mami tace muga wajen?nuna min Mami ta kai hannu zata dakumo cinyar, Sardauna ya rike hannun da Sauri haba Mami ki kyaleta na Sa mata magani fa,Mami tace sai ta gani Ramlat taki yarda,Mami tace ki zauna da ciwonki me ya dameni,Sardauna ne ya mata nuni ta koma daki,dakinta ta shige maimakon Dakin mijin,

Mami ta saki baki tace an ya ciwon nan ba babba bane ka kaita asibiti aga cinyar ko kashinta ya tsage,ko targade,da Sauri Sardauna yace Insha'allah bari na kai mata abinci Mami.


Dafta Jibrila yaga har yau bai samu matar aure ba,kawai sai yace makaranta zai koma,
Suna zaune da yaronsa a chemist yace Saluhu karatu zan tafi kwanan nan Abu Zaria nayi degree na gaji da karamin certificate,
Saluhu yace sai Oga na tayaka murna Allah taimaka,Dafta yace ai mata da kake gani yan iska ne basu da mutunci wlh duk wacce ta rasani tayi asara tayiwa kanta,
Kamata sai garori su takura min,duk zasu ci ubansu na fasa auren ma karatu zan tafi ai yanzu kudi ake so ba mata ba.
Wasu yan matan kauye ne suka zo wucewa sai suka fara gulmar Dafta suna kun ganshi kallon matan tsiya ne dashi kalli yanda yake kare mana kallo,
Karaf ashe Dafta yaji su,kamar abin arziki yace kunga kai yana daga musu hannu wai suzo,yace kuzo kai kuzo,Ai kuwa suka zo gamu,Dafta ya zaro gudan 1k sabuwa kar a aljihunsa tare da budeta ya daga ta sama ta kalli hasken rana,yace kunga abinda ake so yanzu,wannan akansu duniya take yamutsewa,me za a ci daku ai sai farare kalleku yan kauye jahilais daku ku bace min da gani,da gudu suka bar wajen Su na munshiga Uku ashe ya jimu.

Dafta yanzu ya dauki Coper wata Igbo a zaria kullum take masa lesson kan English,Jibrila ya dage da karatu,sai kara kwarewa yakeyi sosai,amma idan yaje kauye sai yace ai Abu yakeyi a zaria,
Yanzu kullum Jibrila hannunsa da littafi ko dictionary Katon gaske,ya koma Sa farin glass yanzu na yan boko,
Babu dama kayi magana hira da Dafta sai labarin karatu yana tsari kan English,
Wani a Kauye Yace Dafta Dafta ya bokon?Kullum yanzu daga karatun Jarida sai dishinare (dictionary) aikinka kenan Gyara zama Dafta yayi tare da gyara glashinsa yana kallon matashin ta ido kuri glass din saman hanci,
Fara bayanin karatu yayi tare da cewa..

Prof yana gida sai masifa yake wa su Chuchu kan cewar Ilmi bai wadacesu ba yafi ganewa Ilmin Ramlat tafi gogewa,
Merry tace har yaushe ta shiga bokon da zata fimu?Prof da masifa yace shut up ta fiku sau dubu bani na haifeta ba amma tazo a banza ta gajeni,yanzu sanda tana gidan nan anfi bin tsarin doka,tunda ta bar gidan nan gaba daya kun canja ba a ganewa sam kamar ba gidan prof ba?,to na gaji wlh da halinku naga Alama kunsa shirme Baza ku taba gadoni ba,ku fito da miji duk na muku aure har yar auta Ichichy a shirye nake na bawa ko waye aurenku banzaye sakarkaru,
Murmushi sukayi domin sun san ma wasa yake musu domin sau nawa yake fadan haka baya cikawa,Prof yace karku dauka da wasa nake yarinyar nan na dawowa zan nemi shawararta yanda zanyi daku.
Ammi tace Lallai prof yanzu nasan karatu ya haukata ka,Prof yace Baza ku san da haka ba sai na aiwatar ya furta tare da Barin gidan fuuuu.

Mami ta gama shiryawa tsab wajen Wani malamin Sunna ya bata ruwan addua kala Uku na Hafsatu da Idrisa, ta buga waya kauyen cewar Lallai Lallai Hafsatu ta zauna da Mijinta tana nan zuwa jibi Insha'allah.Hafsatu taji dadi tayi kuma Murna,yayinda Sardauna yawa Naufal maganar Kanin Ramlat za a sashi schl din Sojoji idan anyi hutu zai zauna dasu,Hannu bibiyu Maman Naufal ta karbi zancen tana murna ta samu yaro dama bata da Yara da yawa.Ramlat bata san da labarin ba.

Sardauna dakin da Ramlat ta shiga ya bita bayan ya tashi daga wajen Mami,tana ciki kuwa ya hangota tana ta faman da jinyar down nata ta matukar bashi tausayi musamman idan ya tuno da irin jinin da ya gani sanda yana Buga harka.matsawa yayi jikinta da niyyar lallashinta,Tun kafin ya karaso ta fara zabga masa uwar harara kamar idonta zai fado,lallashin duniya taki fushi takeyi,a hankali yana kwance kusa da ita yace zaki ci Kaza?Ramlat harda murguda baki tare da cewa Zakara ma yaci ubansa,ta saka kuka yi take ba ji ba gani,
Sardauna shi dariya ma ta bashi,tsokanarta ya kara yi to dan karamin kwanta fa dadi ne dasu?Ramlat tayi banza dashi,me zaki ci to? Ramlat da masifa tace indai abu daga hannunka yazo ko ka bani Bazan ci ba.
Baki da Aldaci Yan mata ko kadan baki da Imani duk hakurin da nayi yanzu ai bai kamata ma kiyi magana ba,eh ai shi yasa naga kaine shugaban masu imani na Kd tunda kasan ni Virgin ce ka min har sau biyu,ina laifin daya ma da dayan kayi ai kasan dai ban sha wahala haka ba yanzu zaka ce min haka haka mana,ai zaka gani Bazan kara yarda ba ko me zakayi,

Murmushi ya saki tare da rike haba yana shafa sajensa yace wannan kuma kinyi karya yarinya ai an nunawa kucciya baka,naga waje gwara ma kiyi shuru karki bata min rai zuwa dare na kara..Sai na fadawa Mami ai,ai kin tona asirinki asirin aure ni ba kunyar Mami nake ji ba yarinya,Ramlat tace ai za'a gani ehe.
Kina yar yarinyarki sai fada,Ramlat tace kai kuma babba ai gashi kana fada dani girma ya fadi,dama tsokanarta yayi yaji ko zata ce masa yaro yanda ta saba da yayi magana zata ce yaro ko sa'anta.

Hannunta ya riko yana murzawa haba yar kawata,mu da muke sa'anni kusan shekarunmu daya,Ramlat ta masa kallon up and down an cuci yaro wlh kato da kai me karfi kamar doki zaka na gwada kanka dani ka daina Cutata wlh,ni ba irin yan Maza bace,

Kefa kikace mu yarane daya muke da me na fiki?ni da ba karfi gareni ba kike kuka a gabana,nima zoki sani kuka kema zaki iya gwada ki gani,tana Hawaye ta kama dariya da ta tuno abinda yake nufi tare da cewa aidai ni ba muguwar bace,ai naga Alama ke baki da mugunta idan mutum ya jefeki da dutse sai ki rama da ruwan zuma,dariya tayi kadan a hankali tace duk da naji zafi da wahala ya kajini? Za aje dani? Tunin ma ai kin wuce kowa baki ji ba kedai bari kawai wani bayanin sai kin warke zan tafi dake garin sweet kema kiji abinda naji.
Shuru yayi tare da kafeta da mayun idanunsa ya dade haka sannan yayi ta gumi yaci gaba da kallonta,kunya ma takeji ita tace lfy? Uhmmmm.....dama haka kike yar yarinya dake sai dandano yarinya kin tsallake rijiya da baya,Ramlat dadi ya rufeta miji ya yabeta tambaya tayi Mark nawa? Malala gashin tinkiya yan mata me zuma kika samu,dariya dadi ta saki.
Kallonta yake yana wani lashe pink lips nasa na kasa,kallonsa tayi ta kau da kai can gefe,yace ko dai a bude ya kara hucewa? a'a barshi haka kawai cewar Ramlat tana tsoro.

Wani dan box na zobe ya dauko tare da riko hannunta yasa mata wani zobe na Gold me shegen kyau,ya mika mata na azurfa wai ta Sa masa tace a'a nima ka bari zan siya da kudina nasa ma shine kyauta ai Amma dan ka bani na Sa ma me akayi ne kenan.
Murmushi ya saki yace u r always updated shi yasa kike birgeni Zumata. murmushi tayi tana kallon zoben da ya sa mata a hannu tana masa godiya.









AsmaBaffa









AsmaBaffa
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€


DUK INDA TA FADI





2pages




191-195. 196-200





Official





By
AsmaBaffa





Wannan page na dukkan masoyana ne wanda na bawa Pages da wacce ban bata Page ba wannan natane,readers masu Sharhi duk ina gani kuma ina jin dadi sosai Allah ya bar kauna,
Duk wacce taga ban mata reply ba to dan Allah ta min Uzuri watarana zan gani ban kula bane,kar ayi fushi.

akwai da yawa fans da suna min sharhi har yau Allah baiyi na basu page ba ko nayi musu godiya cikin Novel dina ba,dan Allah kuyi hakuri ina sonku🀣🀣🀣🀣🀣🀣🀣 me son page ta rada min a kunne irin Sardauna,loves u all.














Abinci Sardauna ya kawowa Ramlat kala kala sai da ta zaba taci ba laifi,bacci ya kwasheta yayin da Mohd yake ta faman nishadi a gidan ya kasa zaune ya kasa tsaye.
Mami ce ta sameshi shi kadai sai murmushi yake faman yi,Mami tabe baki tayi tare da cewa wai lfy kake kuwa yau?Lfy nake mana Mami me kika gani ya furta baki a yaye,Allah ya kawo gyara kasan gobe fa zan tafi garin su Hafsatu kuma zanyi sati guda a kauyen domin sai naga yanda abinda hali yayi zan dawo.Allah ya kaimu Mami gobe,
Ramlat fa ka kaita asibitin?ae mana na kaita dazu kina daki kina bacci ba komai Amma an bata magani,Mami tace da kyau yaron kirki.

Dafta Jibrila ne yaci gaba da tsara abokinsa na kauye da karatun English,yace ku ai mutanan Village u dnt know where world is keeping her front(baku san inda duniya tasa gaba ba)kawai gaku nan dai,You are just In the world, ai ina fada ma Shi English babu languages din da ya kaishi dadi a duniya, musamman Irina da tuntuni ina jin yaren nan,gaskiya ka daure ka iya turanci domin yanzu ni daga nan har Misra ba inda bazanje ba kasan me yasa?abokinsa yace a'a Dafta,da Sauri yace bcause of English,karatu shine gaba duk wata tsiya da za ayi a kasar nan karka sake ace baka da da ko masters ne,Masters shine mafi kankanta a kasar nan ana kallonka a gara da kayi magana a san ka waye yes wise.ita kanta Coper kullum dariyar turacin Dafta takeyi duk yanzu ya dan fara canjawa kadan.
Dafta yayi Sabuwar Budurwa a zaria Hajara,yarinyar kirki ce sosai ba laifi tana da kyanta dai dai ita,Jibrila kaf garinsu babu wanda bai san sunan Hajara ba,ko a garin kana cewa Dafta na Hajara Allah baka Hajara sai ya zaro dari ko dari biyu ya baka,Hajara Dafta yana birgeta sosai har so take yazo tasha dariyar Turanci.
Dafta yana ta faman kashe kudinsa sosai akan Hajara.yauma ya tsara kalamai masu dadi ya tafi wajen Hajara za a sha Love,Hajara ta fito taci wanka tana gwalli.

Saurayin Lantan sayyeed ya sanarwa iyayensa zai auri Lantan,babarsa ita ta tsaya kai da fata tace bai Isa ya auro musu bare can ba,basu san halinta ba tayi masa mata a dangi,haka babansa ma yace,shi Sayyeed tabbas yana son Zabin iyayensa Amma ko Sabo da Basma yarsa yake son auren Sa'a Lantan,amma dole yabi maganar su,takanas ya tako har gidan su Lantan yayiwa iyayen maganar cikin nutsuwa,kuma sun yarda sun amince sun gamsu,Lantan Murna ta koma ciki,
Bakin ciki ya kamata,Sayyeed ya kirata da niyyar lallashinta,Lantan tana fitowa da masifa tace Dalla Malam Adana kalaman ka mayaudari maci Amana,Bazan yafe ba kuma da nasan hakane wlh Bazan ceceka ba tuni zan bari a fille ma kai,zaka ce wani iyayenka ba wani nan kai dai ka shirya abinka kuma ko kabarinka naci da wuta bal bal bazan yafe ba,Ko ni kadai ce za a ce na yafe ma ka shiga Aljanna Bazan yafe ba,

Sayyeed yayi murmushi tare da cewa kiyi hakuri kinji wlh ba a sona ba,kuma na miki bayani da ace niyyar yaudararki nayi da Bazan dawo ba,Harara Lantan ta cilla masa kai dalla gafara ja jiki ni zaka tsara tsaki taja tare da cewa abinda kamin Allah ya maka kuma ka siyo min akuyata da Tinkiya ai iya Rago ka siya ka biyani kudin taimakon dana ma kai da yarka na fasa yi domin Allah a biyani,t a furta tana murguda baki

Kudi ya bawa iyayen Lantan ya bawa Lantan 20k ya tafi yana ayyana rashin hankali irin na Sa'a Lantan.
Lantan kuwa kudin ko kwandala bata ajiye ba tace gidan kanwar babarsu zata koma dake cikin Jigawa dutse ta girmi kauye,
Haka ta shirya da kudinta ta hau mota sannan ta haye mota sai Jigawa domin ta gama tabbatarwa sai ta samu dan birni,wayayye,me kudi,kyakyawa dan haka ta fita nemowa sai ta samu kuma.

Mami ta dira a kauyen su Idrisa ba tare da bata lokaci ba ta fara bawa Hafsatu ruwan addua harda na Idrisa,malamin yace idan Asiri ne zata nuna,idan Aljanune zasu yi magana,idan kuma halinsu ne haka Allah ya ya hallittasu za agansu shuru lfy,Mami tana can kwana daya shuru,biyu,uku,hudu,biyar shuru har yamma ta bawa Hafsatu magani da Idrisa Ai nan take Hafsatu ta dinga kururuwar ihu ana riketa,shima daga baya Idrisa ya fara nasa yana ta birgima a kasa yana ihu,Hafsatu ce tayi magana Amma sam muryar ba tata bace,tace kuyi hakuri haka zaku kashe mu zamu fita,
Kina kona mu. Hafsatu ce ta jawo komai har muka shiga jikinta,Mami da farko ta firgita Amma sai ta dake tace me ta muku?sukace mun dade a jikinta tun kafin tayi aure,sunana Muniba,duk dangina muna jikin Hafsatu mu dari da Uku ne a kanta.
Lokacin da muka shigeta idan tayi wanki ta shanya bata juyawa a dai dai take shanyasu,mu kuma muna Sa kayan tazo tasa muka shige jikinta,sannan a gida tana kwana tsirara cikin daki bata Sa kaya da dare tunaninta ita kadai ce,haka kanina ya kalli jikinta yake sonta,sannan kanta ba dankwali take shiga ban daki bakya hanata,tana zama ba alwala,shi yasa muka samu wajen zama gaba dayanmu a jikinta,Ni Muniba ni ke sata yawo gari gari,Kanina shi ya hanasu zaman Lfy da Mijinta harda yaranta ma,mune muka tarwatsa zamansu,amma yanzu zamu fita,shima Idrisa wata murya ta fara magana zancen Mubinat gaskiyane,halinsa ne shaye shaye amma ko yayi niyyar tuba sai mu hanashi mu muke sashi yasha kayan maye da yawa,masifa ma halinsa ne amma mun kara masa da yawa zamu tafi..zamu tafi.

Su Abu da Sauran dangi sai mamaki sukeyi,suna rike da Hafsatu tare da Idrisa kafin kace me sun fara Atishawa sosai,sai bacci,
Washe gari kuwa Idrisa bai je wajen shaye shaye ba abin mamaki sai neman yaransa da matarsa yakeyi,bayan komai yayi settling sai da Mami ta kara 3days an gama magani kaf kuma Alhmdllh sun warke,
Duk shirmen da sukeyi sun daina,yan Uwa mata a kiyaye ko basu nuna ba zasu iya saka ka dinga aikata munanan halaye a kiyaye tsaraici.

Mami Sabo da murna tun kafin ta dawo ta sanarwa su Ramlat sai ihun murna takeyi dadi kamar zata mutu,Sardauna yace ta taho dasu gaba daya.Mami tace kafata kafarsu ai.

Ranar da Mami ta zo tare dasu, Idrisa harda Kukan murna yana godiya Shaheed ma an taho dashi Sardauna da kansa ya dauko Daddy dake makarantar Sojoji suna ta shan dadi,gaba daya kudin da Sardauna ya tara tare da na hannun Mami ya hada da wani filinsa karami ya siyar yace Kawu a ina kake son zama sai a baka jari?Kawu da murna yace Kanon Dabo, Sardauna yace a siya a Zaria ko dan Makarantar Daddy,
Ai kuwa a Zaria Sardauna ya siya musu gida dan karami madaidaici,me dan kyau na rufin Asiri,Maman Naufal ta zuba musu Furniture,

Suka koma ciki kamar Amare,sannan Mami ta dinka musu kaya sababbi na zamani, Sardauna ya bawa Kawu jari na kasuwanci,
Kawu ya bude Katon kanti a uguwar cikin ikon Allah arziki yaci gaba,har ya kara bude new branch sosai suke zaune cikin farin ciki da nishadi tare da kwanciyar Hankali,
Har Makarantar yaran Kawu ya dau nauyi,Baban Naufal shi ke biyawa Daddy nasa,matsalar su Kawu daya batan Fahat an nemeshi an rasa suna dai ta nemansa ana addua.
Su Abu da Sauran dangi sunzo sunga gidan Kawu da gidan Sardauna dake Kd,yanzu sun san ko ina ana zaune lfy,Alhmdllh su Kawu komai ya daidaita.Saura Fahat kawai.

Ramlat tunda Sardauna ya samu harka sau daya yau kwana goma kenan suna wasan buya dashi,ba wannan ce matsalarsu ba face yanda Daddy Sardauna ya dage sai Sardauna ya bishi tare da Mami sun koma Abuja wajensa,ko kuma yazo yaga yan uwansa dole ma ya bishi can,Sardauna da Mami sunki yarda babu dabara da wayon da bai hada ba amma Sardauna ko Saurarar Sa bayayi,har kyautar companies manya ya bawa Sardauna kudi da mota wanda idan da ace Sardauna ya karba to da shi da talauci har a Bada,amma yaki karba yace baya so,dan wulakanci ma Baza a lallashesu ba sai daΓ­ a nuna musu kudi sune mayun kudi kenan,sabo da bashi da kudi za a yaudaresu dashi shine abinda ya kara Sa Mohd bacin rai.

Bayan Daddy ya gaji ya fadawa Matarsa Bilkisu Momyn Sardauna cewar taje da kanta itama ta gwada,Momy Allah yayita da son kai,rowa,ga tsafta domin ita tsaftarta ta tashi daga tsafta ta koma bala'i,domin iya tsaftarka ba a iya mata,komai tace baiyi ba sai an sake,sanda tazo gidan Mami haka ta dinga takurawa tana yatsina fuska tare da taku dai dai ko a kujera kasa zama tayi wai bata goge ba,
Ramlat tana aikace aikace cikin Ladabi tace Mama a kawo abinci?Mama tace a'a na gode yata,kawai kawo min biscuits da lemon Kwali,kasancewar basa cin kayan zaki a gidan babu wani biscuits Ramlat ta Sa Hijab taje ta siyo mata masu dadi da kanta Sardauna dama yace idan fita ta kama dole ko baya nan taje,Da kanta Bilkisu ta shige kitchen tare da kada kumfar omo ta zuba biscuits ciki ta wanke a ledarsa wai kazamai sun rike da hannu,wanke biscuits cikin leda.

Ramlat tana shara Mama ta tabe baki tare da cewa mopping din nan baiyi ba na hango Kura dawo ki sake,Baba me aiki tana ta faman fesa roomfreshner ai kuwa Mami ta toshe hanci tare da cewa dan Allah kiyi can wani kauri ba dadi kamar wari ma yake wannan,

Sardauna kuwa tunda yaji tazo ya bar gidan gaba daya yaki dawowa har kusan dare.
Mami tace Bilkisu kenan har kin Manta Sanda Kabiru ya auroki fulanin daji Kazama dake dagaje dagaje har kudi ya ratsaki zakizo ki mana iyayi ,yi hakuri Mami cewar Mama.
Mama tace in banda baki da kunya baki da mutunci Bilkisu har ni zakuzo karbar danku wajena,kun manta sanda kuka kawo shi a zanin goyo babu rokon da ban muku ba kuka ki yarda ku gaku wayayyu,da kyar Mohd ya rayu kin san wahalar dana sha kafin ya zama haka?Amma akan burinku na duniya kunzo zaku ci min mutunci,Allah yasa na Haifa bare ku nuna min iyakata,yanzu da ban haihu ba ai da nayi Kukan da ya isheni,karya kukeyi badan Allah kuke neman mu ba,kuma indai ina raye wlh Sardauna bazai biku ba,bazai koma wajenku ba,bazai taba muku biyayya ba Sabo da baku shaku ba,bai sanku ba,baku damu damu ba muma haka,
Maimakon kuzo cikin lumana ayi sasanci mu samu masalaha tunaninku kudinku da isarku ku kuka haifeshi zaiyi tasiri kansa,to mu giyar kudi bata makantar damu mun manta alheri ba,bazan Hanashi biyayya ga iyayensa ba dole ya muku Amma wani kudirinku bazai yarda ba,
Idan kun matsu kuzo a gaisa watarana shima yaje muku amma ni Bazan je inda kuke ba,Butulu wanda basu san mutunci ba,Mami ta fashe da kuka,Mama na Bada hakuri,Ramlat ma haka,sai ga Sardauna ya shugo ko kallon Mamansa baiyi ba wajen Maminsa ya nufa yana lallabata,Mama na kallonsa cikin sha'awa katon namijin gaske kyakyawa,nutsatse duk yafi yaranta nutsuwa,nan take takaici ya rufe Mama tana ganin Mami ta cucesu wai tayiwa dansu asiri baya sonsu baya kaunarsu,wai Mami ta bawa Mohd rubutun Manta Uwa.

Tunanin hakan yasa Mama kuka an rabata da Danta tana dana sanin bawa Mami,
Mami tace Kukan banza kike hawayenki bazai bi Sardauna ya tabe ba domin Allah ya gani ko tsinewa Sardauna kikayi Baza ta bishi ba Sabo da bai ma san wacce shara bace ku,banyi niyyar yi muku hakaba kudi da kuka nuna wai ku kun haifeshi yasa nima sai na nuna muku kudi ba shine komai ba.

Mohd ko gaishe da Mama baiyi ba,Mami ma bata ce ba,
Mama daki ta koma ta kara gyarawa tas ita me tsafta sannan ta kira mijinta Baban Sardauna ta zayyane masa karya da gaskiya tana kuka.

Daddy yace ki bani 3days sai kin taho gida tare da danki harda Mami gaba daya,Sabo da kudi ba abinda basa yi,nasan da me suke gadara dan Mall dinsa da taxi sai wani fili karami da ya siya,badan bana son Mohd zan aikata hakan ba,sabo da ba irin kyautar da ban masa ba yaki karba,yanzu Mall din zansa Gomnati ta rushe har Taxi sai na karbe duk abinda yake dasu har gidan da suke ciki,idan ci da sha ya gagaresu da kansu zasu neme mu har gida ya karbi kyautar shike nan zasu dawo gare mu,sannan nayi masa auren da zan shahara a duniya.

Mama dadi ya rufeta tace Bazan taho ba sai da Dana.
Kwana Uku tsakani,Ramlat ta gano Sardauna baya cikin hayyacinsa tunaninta ko boye masa da takeyi ne yasa,sabo da haka ta dau wanka cikin yar shegiyar rigar baccinta tana kamshi ta wuce dakinsa,still Mama tana gidan kullum lallaba Mami takeyi,

Me zata gani tana shiga ta hango Mohd zaune gefen gado yayi tagumi Hawaye na digo masa,da Sauri Ramlat ta fada jikinsa tana tambaya lfy My King?nice gani wlh ko me kake so gashi,Murmushi Sardauna yayi tare

Please Login or Register in order to submit comment