Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dai baice kala ba ya shanye Marin sa,Mami na ganin haka tazo ta kama hannun Sardaunanta tace mutu ka raba ni da jikana da a Sadaka na sameshi kuma na tabbata yafi duk su Nabeel din da kike takama dasu,Nabeel ya fara magana wlh kuwa Mami ya fimu muma sheda ne akan hakan,Momy dan Allah ki dinga hakuri akan kishiya kiyi ta fada haka,Momy tace dan Uwarka bazanyi ba ko kaima bayansu zaka bi,ku hade min kai Ku kasheni Ku huta nace Ku sa kaina gabas Ku yanka tunda bakwa kaunata,Shuru sukayi suna jinta Ramlat ta shiga damuwa tace dan Allah kiyi hakuri Momy bazai kara faruwa ba hakan,huhum humm dalla rufe min baki bakar munafuka an mallakemin yaro baya kaunata an bashi manta uwa zakizo da kuturin munafunci,ji nake jiya naji ance wai shi ya miki wankan jego?namiji tunda nake aduniya idan ba shirka aka yi masa ba na taba Jin namiji nason kallon kazantar mace jinin biki ma,amma ya zauna ya kalla harda miki wankan jego yo ni a duniya na taba Jin namiji da wankan jego.

Dad ne yaja tsaki yace tafiyarki Ramlatu ki kwanta ki huta Ku kuma Nabeel muje gida,ke kuma karya idan fadan zakiyi sai ki zauna Bismillah,kuje ni zan bi taxi na dawo motarka dai bazan shiga ba Kabiru.
Shashasha amma ai zaki gidana ko?wlh kikayi wasa gidanku zan koraki kwanan nan aje can ayi kwanciyar kai da kafa,Momy tace amma da arzikinmu ka ganni,na Shanu ba wanda ba a ci sai dai su mutu,oho dai kuma wlh ka koreni gida naji zan tafi amma wlh sai an wuce dakai gadon asibiti domin sai na Sumar dakai cikin biyu za ayi daya ni zan tafi gida ka kwanta a asibiti na
yarda,Nabeela tace haba Momy haba Momy dan Allah Daddy ne fa a gabanmu?nayi din shi waye da bazan yi ba,Fahat yace Allah kyauta,karaf Momy tace kai a suwa?harda kaza a cin Danko?Ai Allah?dan karere harda kai?
Kabiru Fakas dai driver ya kwashesu da yaransa suka tafi cike da takaicin Momy,Ita kuma ta fito fuuuuuuu ta hau taxi sai gida,tana zuwa ta wuce Su Nabeel tana waya tana fadawa kawarta guda daya tal abinda ya faru a waya,Wani halin Momy shima bata da Sirri yau zaku hadu sai kasan sirrinta kaf,kuna haduwa ko a gidan biki idan hira ta hadaku to fa sai kasan Sirrinta.
Kuma anayin abu zata zaro waya da wanda ya kamata da wanda Bai kamata ba duk sai sunji labarin.

Mami kuwa tasa Sardauna a dakinta tana ta masa fada sosai daga nan tayi masa nasiha kan hakkin iyaye,kar ya kuma fadan wani abu marar dadi kan iyaye da danginsa koma mene ya barshi a ransa yayi addua.
Mami sabo da Allah me nace?kayi kuruciya Muhammadu dan me zaka ce ayi wa uwarka kishiya idan dadi ne kayiwa Ramlat mana,Baka son fushinta kai baza ma ka iya adalci ba ko ba haka kace ba?in banda Kuruciya daga kawo maka zance sai kace ayi kishiya, Ramlat dake gefen Sardauna ta yi magana kuma kana fadan kai baka damu da ita ba wannan kalma ce dan Allah Mami? Ramlat ta kara da nata fadan hhh,Harara Sardauna ya buga mata,tace ai gaskiyace ana so a samu daidaito kai kuma kana bata abu,kamar ba Sardauna ba wanda komai ya iya Ramlat ta kara fada,akwai maganganu da ka fada basu dace ba gaskiya,tunda mun gane halinta sai ka kyaleta muyi hakuri hakan abinda minti nawa ne ta gama ta tafi gidanta?
Wannan Babyn tamu ce take kawota Allah sarki tazo ta kula da jikarta taga danta amma kana gwasaleta kai baza a fika ba? Harara ya kara ballawa Ramlat dake zaro zance,yanzu ko tazo kawai mu barta tayi abinda zata iya,ko aikin tace a bata a bar mata ai jikinta ne in ta gaji zata bari da kanta,idan kasan halin mutum sai Kaci maganin Zama dashi ko ba gaskiya ba Mami?Mami tace yawwa Ramlat yar gari karbe masa girmansa yar shekara dayan nan ki kwaceta du,murmushi Sardauna yayi yace in ta isa ta kwace ta gani,Ramlat tasan me yake nufi tace ni na isa,Mami tace Ashe da gaskiyarki da kike ce masa yaro yanzu na gani,
Sardauna fushi yayi ya Mike zai bar dakin Mami ta dakatar dashi da cewar na fada ma kar na kara ji ko gani ka nutsu ka kiyaye harshenka,Ramlat tace kuma ka dinga tauna magana.

Mami Allah kice ta daina samun baki a maganata doluwa kawai har yaushe tayi wayon ma?dariya sukayi gaba daya shi kuma ya fice yana fushi Mami ta masa fada gaban Ramlat,itama Ramlat harda sa baki zata sani.

Wajen tsarin party nasu ya tafi yana ta shirye shirye sun gama komai da Naufal tare da wasu frnds nasa ta waya.
Ramlat kuwa tana can dakin Mami tana baccinta ita da jaririya.Sardauna fadan Mami ya shigeshi Fahat ya kira a waya ya bashi Address na gidan iyayensa har can yaje gaskiya gidan ya hadu kamar Aljannar duniya lallai kudi sunyi kuka,Daddy tuni ya fice wajen aiki,Nabeel ma haka Fahat da Nabeela suna gida suka tarbi Sardauna da murna,ya zauna yace ina Momy?sukace tana Bed room sai kuka takeyi wai za a mata kishiya,har dakin suka raka Sardauna suka fito tare da rufe musu kofar.
Har kasa Sardauna ya durkusa duk da zuciyarsa bata so hakan ba haka ya gaisheta yace Momy kiyi hakuri dan Allah nasan ban kyauta ba kuskurene na tongue amma insha'allah Daddy bazai miki kushiya ba Sam yanda kike haka ina zai iya hadaki da wata ai babu kamarki samun kamarki sai an tona,dama Momy kamar Sardauna ya sani Budurwar zuciya gareta bata yarda ba ita bata tsufa komai ba a barinta a baya na zamani,
Nan take farin ciki ya lullube zuciyar Momy ga farin ciki yau Sardauna danta ne har Bedroom dinta,kuma ya durkusa yana bata hakuri da lallashi tare da kalamai masu sanyi,a ranta tana tunanin masifar da tayi ce tasa Sardauna yazo ya bata hakuri,kaji mushen tunani bata San dai wanda take cewa sun asirce danta ba sune dai suka saita mata komai ta dalilinsu yazo tarbiyarta ce wanda ta gaza bawa yayan nata da take ikirarin tafi so,

Momy a fili tace Allah maka albarka yarona da nayi fushi dakai amma yanzu ka wanke min zuciya,ai shi yasa na musu kaca kaca gashi ka gane gaskiya ba kaunarka sukeyi ba ka dawo gaskiya dole,haushi da takaici ya kara lullube Sardauna wannan wanne bahagon tunani ne na Momy?amma haka ya daure yayi murmushi yace ba komai in dai kin hakura shike nan,na hakura dana muje na baka abinci me dadi idan zaka ci,idan kasan baza Kaci ba kar kasa nayi asara domin mu nan ba a rage abinci idan na na zubo sai an cinye,kaji uwar rowa sai an tambaya ko zaka ci hakan ma dan danta ne da ko tararwa yayi ana ci baza ta yi masa tayin ko ruwa ba,
Sardauna dai dan su rabu lfy yace a bashi zaici abincin Momynsa yau,idan kunga abincin sai kunyi dariya wasu Manyan food flasks ta kawo na alfarma amma abincin ciki Bai fi rabin plate ba ko dan yaro tsab zai cinyesu du ya Sha ruwa,
Sardauna ya jinjina a ransa ya dai yi shuru harda zuba masa dan mirit can kasan plate harda cewa na kara ko ya isa haka?Sardauna da murmushi yace ya isheni hakan ma,ya kai hannu zai dauki spoon tace kai a'a tsaya muje a wanke hannu ina ai Ku haka kuke cin abinci ba wanke hannu? Ai sai a dauki cuta,Sardauna yace da spoon fa,a'a tashi muje,sardauna yayi shuru ya bita a baya ta koma tare da kwashe takalman Sardauna ta kaisu toilet ta wanke masa su Allah yasa ba masu daukan ruwa bane,sannan ta wani jinginesu jikin kofar daki wai su bushe ya tako mata kasa,
Ta barshi a toilet yana jiranta tazo tana ta share wajen da ya taka mata,kuma duk shara daya biyu sai ta wanke tsintsiyar ta dawo ta ci gaba,Saida ta gama tazo wajen Sardauna ta bashi soap yana wanke hannu tana ce masa kara wankewa sosai.

Yana fitowa su Nabeela suma suka shigo sunje Islamiyya yau ba schl sun dawo,tun daga waje ta kai musu kayan sawa wankakku Sardauna yana Shan kallo yaga sun cire a kofar palon sun sa wanda ta basu sannan ta kada kumfa a wani bowl ta karbe uniform din ta zuba cikin ruwan kumfa ta shige toilet ta wanke su fes ga injin wanki amma wai hannu takeyi tafi motsa jikinta,ta gama ta fito ta shanya musu fes har na Fahat kato dashi,ta wanke musu takalma ta jinginesu su ba ruwansu sun Saba da Momy komai kafin tace sai yaga sunyi abinsu basu damu ba.
Allah Allah yake ya gama ya bar gidan wannan abin ya isheshi,Momy tana gefensa tana huce gajiya tace ai da zaka kai dare da ka cire kayan na wanke ma,sai ka sa na Nabeel,Sardauna yace yanzu zan tafi zanje aiki ne,
To muje kaga gidan namu mana,nan ta dinga zaga Sardauna ko ina tana bashi labarin kasashen wajen da suka zauna mu a Germany yaushe muke kantama gida haka nan kuwa sai a dinga sace kudin kasa ana rusa manyan gida,A Paris gasu Nonon Rakumi nan ko ina in kana so,nan kuwa ba a samu sai an Sha wahala,sanda muna Madinatul munawwara laban na gaske masu inganci amma na nan kasar taku duk Zawo suke sawa wa yasan da Nonon me sukeyi.
Har dakin Daddy ta kai Mohd,ya zauna jikin wata rigar Daddy jallabiya wacce Momy ta wanke ta goge tare da sakaleta da sauri tace kanka kash matsa kayan Baban Nabeel ne zaka bata masa su,wayyo kai bashi kawai ya zanyi na sake wanke masa anjima,
Muje na rufe masa dakinsa kar Kura ta shigo masa,suna fitowa sai ga Daddy ma ya dawo yasha farin cikin ganin Sardauna haka,da farin ciki suka gaisa suka zauna a Palo suna hira sai ga wasu mata yan uwan Momy suma da gani ba a kauye suke zaune ba,yayarta da kanwarta duk cin birni suke aure,Mami na ganinsu da sauri ta Mike ta zuge Labilen barin Kabiru mijinta,ta rufe Kabiru da labile kar a ganshi a kalli mijinta wanda ba muharraminsu ba,kallon Sardauna tayi tace tashi ka tafi sai nazo ka runtse idonka da kallon matan mutane wanda ba muharraminka ba,Wai dan kar ya kalli matan wasu ta sallameshi,su dama sun San halin yar uwarsu,shima me gidan yasan abarsa,yana jinta ta kwashe matan ta kaisu wani palon can daban karma su hadu da mijinta by mistake.Sardauna kuwa shi takaicin Momy ma yakeyi aransa yana za a dade ba a kara ganina ba a gidan nan,wannan abin na Momy ko dai kwakwalwarta ba kalau take ba?to ni dai bazan iya ko yini a gidansu ba,yana dawowa ya dinga bawa Ramlat da Mami labari,Mami tace kaine baka Santa ba dama can haka take yanzu ne dai abin nata yafi da can,shi yasa kaga babu wanda yake shiga harkarta,ko Ramlat taje kaga dai Yanda Babanka yake da Ramlat to wlh indai ko Ramlat ce taje sai ta zuge mijinta cikin labile kar a kalleshi ko ta rufe kofa da key yana ciki,ko yarta bata so ta kalli mijinta bare matan waje,Sardauna yace aiko muma zasu dade basu ganmu ba,ni Bana fatan abinda zai kara kaina gidan nan Sam.

Sa'adat cikin nishadi ta isa gidan Saddiq yace tazo ta gyara masa gidansa,tun safe take aikin duk da ba wani dirty haka ta gyara ko ina yana kyalli,kitchen ta fada domin ya kusa dawowa baya gidan,key ya bata na gidan,girki ta shirya lafiyayyu abubuwan da tasan yana ci,a dining ta shirya komai tare da gyara kitchen,saida ta zauna taci nata ta koshi sannan tayi sallar la'asar ta fito zata tafi shi kuma ya dawo,murmushinsa me kyau ya sakar mata itama Lantan haka harda shanye idanu a hankali ta karasa jikin motarsa tare da cewa sannu da zuwa ya Saddiq,Baba driver ina yini suka gaisa da Driver ma,ta karbi ledar hannun Saddiq ta bishi a baya har Palo ya hau step din samansa Lantan tana binshi a baya yace jirani a Palo yan mata so kike ki jawo min shedanu su sani abinda banyi niyya ba,Lantan murmushi tayi tare da Zama a kujera tana jiransa,ya dade saida yayi wanka da sallah sannan ya fito,yana fitowa ta Mike tace zan tafi yamma tayi Matar Abba zata bani punishment Itama ta Zama soja, dariya Saddiq yayi kadan bakya jin magana shi yasa ai,yaushe zakije kauyen naku Hutu?Sa'adat tace sai naje Sunan Ramlat a Asokoro sai na wuce daga can, Saddiq ya tabe baki tare da cewa banga abin so a suna ba har kika damu kullum baki da zance sai na Suna,ai na dauka kaine zaka kaini tunda ba nisa tsakaninmu Abuja suma suke,Allah kiyaye sai dai Driver ya kaiki ko Abbanki,
Can kauyen kuma dasu wa zaki bi?iyayena tunda zasu zo suma har gidanmu,ok Allah kaimu Saura kwana nawa? 5days kacal,leda ya mika mata gashi tafi gida kicewa Baba driver ya kaiki gida.murmushi tayi ta karba tare da cewa na gode Allah kara budi,ta bude ledar kwalin katuwar waya ta gani da kayan ciye ciye dangin zaki,daya ledar kuma agogo ne kala biyu masu kyau da tsada,Sai takalma designers da jakankanuna kala Hudu hudu,dayar kuma cosmetic iri iri.
Da murna ta masa Sallama tabi Driver ya ajiyeta a gida,Karima matar Abba Abdullah ta nunawa kayan,Karima tace an gode masa amma dai kin masa godiya ko?Lantan bata ce gidan taje ba tayi aiki sai tace gidan kawarta taje suka hadu da Saddiq a hanya yace dama wajenki zanje gashi ki gaisar da Maman Arfat,Karima harda dariyar Jin dadi tace ina ruwan Saddiq ai yaron kirki ne,da ace zai soki da wuri zan bashi,Lantan dadi ya kamata tace ga sweets dinnan yace a baki wai nasu Arfat ne a basu suma,Karima tace to fa ai Saddiq baya gajiya Allah dai ya masa albarka ga iya bada tarbiya,sanadiyyarsa kikayi hankali fa Sa'adat, Lantan ta washe baki tace ai yace nan gaba ma idan ya ganni ina yawo Sai ya farfasa min jiki,Karima bata San Lantan
Bata ki a kwana ana mata hirar Saddiq ba,Karima tace to aiko ya kyauta waye a zamanin nan zai kular ma da yaro,nan da 1mnth naji Abban Arfat yace za ayi musu Karin girma kuma harda Saddiq sabo da kwazonsa.

Ni sai naga ma kamar ba aikin yake ba cewar Lantan,Karima ta bude baki tace keeeeeeee na rabaki ai Saddiq in kika ji irin bajinta da yakeyi a kasar nan sai kin rike baki,gashi da yan mata suyi ta sonsa da yake Allah ya masa baiwar kyau da sura,Lantan Dadi fa ya gama kasheta ana yabon gwaninta,harda tabe baki tace nidai MumArfat banga wani kyau ba a nan,Karima tace a sai dai idan baki da Ido,amma gashi kalar skin dinsa ma daban ce,shi ba fari ba shi ba chocolate ba,ga uban kyan diri ga tsabta da iya wanka,Lantan karaf tace ai Fuskarsa tafi komai kyau Antyna hancinsa Allah kamar biro shape Din fuskarsa da dan bakinsa ko nawa Bai kai ba fa,Karima ta kurawa Lantan Ido yanda take tsaro surar Saddiq,to munafuka kika ce bakya ganin kyansa?yanzu da kike fada fa?Dariya Sa'adat Tayi tace ai tunowa nayi,ta Mike tare da Fadawa bedroom dinta ta fada saman Bed tare da jawo pillow ta rungume kam tana murmushi tana tunanin Saddiq sai duk haduwarsu Saddiq Bai kama kafar Sardauna ba.

Kaya Sardauna ya zubewa Ramlat cikin kwalinsu guda Uku duba ki gani nasan zasuyi a party nan su zaki sa,nawa ma suna dakina in kinje zaki gansu,Ramlat tana murna ta bude daya wata gown ce me matukar kyau da birgewa kamar ta Amare kalar kuma ta Larabawa can baya tana Jan kasa fara kar,Dayar kuma itama wata kalarce daban ita kuma irin wedding gown ta turawa harda abun dorawa a kai pink color tayi kyau,
Ta uku kuma lace ne dan gaske ya hadu shima dinkin Amare gown,Ledar takalman da pose ya mika mata komai Shar Shar,nan suka ware na ko wacce rana da zasu sa Mami ma nata dinkunan daban,har na ranar Waleemar Ramlat,Yar jaririya ma haka nata daban kamar yar Sarki.Ramlat sai godiya akewa Sardauna,
Kuma duka Event din Sardauna ke shirya komai a nutse sai dai kawai suyi shawara da Ramlat,
Harda bugo katin gayyata masu kyau ko wanne invitation card shine pass ticket dinka na shiga ko wanne event.
Ba a San ya akayi ba sai ga Sa'adat da invitation har kala Hudu na Sardauna,ashe Nabeela ma kawar Sa'adat ce a saloon suka hadu shi yasa take Sanin labarin komai na Ramlat.

Momy har yau kullum suna zuwa ganin Jaririya amma duk da haka
Ba kullum zata bari a rabu lfy ba sai ta jawo magana wajen Mami tun suna kulata har suke shareta idan tana wasu abubuwan,
Suna ya rage kwana daya tal da Waleemar Ramlat za a fara ranar sunan kuma cikin gida,mutanen jigawa ma sunzo su Abu anga gida an gigice,Hafsatu da yaranta da Kawu Idrisa suma sunzo amma anyi anyi su zauna sunki yarda wai gidan suruki ne sai Mami tace to duk baki masu kwana a kaisu guess house na Daddy a sauki baki a can duk ranar event sai a kaisu can,hakan akayi duk baki can ake kaisu da ma'aikata dama Sardauna shi Bai son ko jikin bango yaga jambaki ko bakin kwalli a gidansa kuma yasan Halin mata,ko wanne da sun kalli Jaririya an gaisa sai a kaita can gidan saukar baki,part na maza da mata,Naufal ne kadai yace ba a isa ba a nan gidan zai zauna kusa da yarsa ya dinga ganinta kullum yana part din Me gida Sardauna,Mamansa da sauran frnds da wasu duk sunce su suna can gidan baki suna ganin yan mata na gilmawa yafi musu,gashi kida sukesha a can ta ko ina Dj na tashi,kaci abinda kake so kasha,ma'aikata na aikinsu na komai basu da matsala komai kace za a kawo maka masu goge goge da share share ma haka,Su Abu kaf dangin Ramlat suna part din Ramlat,Su Habiba Firdausi dasu iya yan gidan Citta,yayan Talatu,na Katsina da sauransu sunce ai suna can gidan da yan mata suke anan ake shagalin,kana shigowa za kaga wasu na cashewa ana ciye ciye,kayi kallon yan mata da kwalliya iri iri,ga abin dariya sabo da duk inda za a hada akwai yan mata da samari ai dole a Sha kallo,Kawu Idrisa ba a barinsa a baya kullum sai yazo wajen Hafsatunsa ta fito wajensa kamar wasu saurayi da budurwa su dade suna hira abinsu.Abu ta cewa Sardauna kai dan gayu a kaimu gidan shagalin nan,Naufal ne ya kaisu ai ko Abu tace baza su dawo ba suma sunga wajen Zama.
A'i ce kawai da Mami sai Sardauna da Naufal suke kwana a gidan,A'i abinda ya daure mata kai Bai wuce yanda take ganin kafin su tashi daga bacci tazo part din Ramlat ta mata wanka sai ta tarar har tayi wanka,kuma Sardauna a dakinta yake kwana tare da ita,
Mami ta tambaya wai ni ba wanda ke kula da Ramlatu ne kam?mijinta a dakinta kuma sai naga tayi wanka in dai ita take wa kanta ai baza ta gasa kanta ba Sam,Mami tace tab mijinta ke mata wlh kuma har fimu iyawa ma,kinga yanda har ta warke da wuri,A'i tace mun shigesu Miji? Ta tafi wajen Ramlat ta sameta ta cakare kamar Amarya A'i tace ke dan Ubanki wannan kwalliyar sai kin jawo yayi miki wani cikin ko?tun ba a je ko ina ba,to wlh ki daina kwana dashi kina kwalliya zaki gayawa mutan garinku,in banda iskanci na taba Jin inda miji yayiwa mace wankan jego,ko kunya bakya ji,

Ramlat ta turo baki Ku wlh kun cika wani tunani,kuma dan yamin abu to mene Bai sani ba nawa,A'i tace daga yau ni zan dinga kwana dake ai Abu bata sani ba tana can awajen yara bari ki gani,kirrrrr ta kira Abu halo Abu kinji yanda Ramlatu ta koma wai miji yayi amata wankan jego yo ni na taba Jin haka,kuma wai Ashe tare suke kwana,Abu tace laaaaaaaa amma wannan kwai yar iskar yarinya ni dai bazan dawo ba ina gidan nan A'i kallo ya barki kizo kiga yan mata da Samari yanda suke cakarewa ammafa cikin shigar yan iska ,A'i tace Abu ni ai a kofar gidan Ramlatu nake yini ina kallon Arna da dangalallan skert bingel bingel,watama ko cinya Bai kai ba kuma kiga sun jero da maza karshen duniya yazo,Talatu kuwa da ita ake rakashewa tana cikin yara cewar Abu,A'i tace ke rabu da Talatu ai ita duk shiririta tana cikinta wai ita yar Birni.Haka dai suka gama wayarsu saiga Momyn su Nabeel tazo tana kyankyami A'i kuwa ba mutunci gareta ba, ba a kawo musu raini....






Mu hadu a next page.








AsmaBaffa
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€


DUK INDA TA FADI





261-265






Official






By
AsmaBaffa







DeeMamy ga page naki tnx for the fireπŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ˜…





Mommy tana kyankyaminta dai haka ta zauna gefen Bed din Ramlat tare da daukan Jaririya ta maida ta saman Dan gadonta tare da cewa Bai dace ta dinga kwanciya a gadon manya ba fatarku da tata ba daya bane ba wahala cuta ta shigesu,Ga girki nayi miki kici farfesun hanta ne,Ramlat da murna ta karba a dan karamin flask wata yar kadan batafi yanka goma ba, tana godiya da Ladabi ta gaisheta,ko mene tana taka tsantsan yinsa gaban Mommy amma duk da haka komai sai tace ba a iya ba,A'i tana kallon ikon Allah abin ya isheta.

Tsaki A'i taja baiwar Allah a wacce kasar aka haifeki ne?ji nake dai a Nigeria ne?ba kece ta kauyen Tudun wada ba kano can dajin shanu?da ba a San Asalin balbela ba da sai ace daga masar take,Ramlat tace kiyi shuru Baba A'i pls,A'i tace yo tazo ta raina mana hankali ita me tsabta,Mommy shuru tayi sai dai daga baya itama ta hayayyako da masifa cewar nifa Hajiya ba me Zafi na fada ba,daga na kawo gyara,ai annazafatu minal Iman,A'i tace mun fiki sani Allah kawo Abu kiyi wannan a gabanta ki gani dan ni kin sameni ruwan sanyi ce hh kaji A'i duk masifar nan.
Da kyar Ramlat ta kiftawa A'i ido tayi shuru,Mami tana can ta tafi gidan da baki suke tana tarbarsu,Sardauna kuwa ya shigo kenan ya tarar Mommy suna cacar baki da A'i shi dariya ma fadan ya bashi dan haka ko a jikinsa dama neman wanda zaiyi maganin Mommy yakeyi tunda shima ta masa hakan.

Direct wajen Ramlat ya wuce tare da sa hannayensa a gefe da gefenta wato tana tsakiyarsa a gabansa daf da juna kamar zai maidata ciki,a hankali tace Mommy dasu Baba fa na kallonka,Gashi yan AsmaBaffa Fans club ma suna ciki,Taskar Firdausi Sodangi,kalli yan House of Hausa Novel ma duk gasu nan dai manyan frnds sunzo ganin Baby nan kafin su wuce waccen gidan suyi shirin tafiya Shagalin nan,ko Saurarar zancen Ramlat Sardauna baiyi ba yace tashi zakiyi ki shirya kije wajen Bakin da suka zo,anjima zamu tafi wajen makeup fa,amma ai sai suga ba a daraja su ba.
To wa zai kaini?Suma sauran fa?suje waje akwai su Naufal duk za a kwashesu,idan kin shirya just give me a ring ok.
Yana fita A'i ta rike baki tace abin yafi karfina dankari

Please Login or Register in order to submit comment