Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai ace Tanimu sai yace ai na tanaji zafafan kalmoni,ko yace na tanaji zafafa...shike nan yanzu ake ce masa Tanimu Zafafa.

Ramlat tana fitowa ta ganshi ya dau wanka yana kamshin wani turare me kauriin hayaki ba dadi, Yana ganin Ramlat tayi masa Kwarjini gaba daya yaji Haddarsa ta goge,Zafafan kalmomin sun gudu,
Ya rasa me zaice sai yace Salama'alaikum....sunana Tanimu....ina da yaya Zilkifilu Okocha,a kofar Kudu aka haifeni....can sai yayi shuru ya rasa kuma mai zaice,ita kuma Ramlat bata ce komai ba,wasu akuyoyine sukayo ayari guda zasu shiga gidan Abu inda Ramlat ta fito kenan,sai kuwa idea ta fado masa ya samu abun magana yace wannan akuyoyin gidanku ne?sai ya cusa hannu a aljihu ya zaro Dari Biyar tare da mikawa Ramlat to ga wannan a sai musu dusa,
Ramlat da kyar ta danne dariyarta ta karbe kudi ta shige gida shima ya tafi,

Kwana biyu wani shima Bai zo ba sai aiken kayan kwalliya da aka ciko Leda dasu aka kawowa Ramlat Inji Hamisu Almajiri wanda yazo daga Maiduguri,
Sai bayan sati da kawo sako Sannan Hamisu yazo zance,daya zo shima dama tsoron mata yake ga Ramlat kyakyawa sai ta masa Kwarjini kawai jikin sa ya kama rawa ko a Bai ce ba,sai da aka Dade itama Ramlat batayi magana ba,
Can....ya nisa yace ammmm.......sai kika ga sako? Ramlat tace eh sai naga sako....ya kara yin shuru sai kara cewa sai kika ga sako......Ramlat tace sai na ga sako....ya kara cewa sai kuma kikaga sako...Ramlat tace sai fa naga sako....sai yayi shuruuuuuuuu....again yace to na tafi na gode saida safe,
Ramlat tace to tayi tafiyarta.

Idrisa ya gaji da turuwar da samari suke wajen yarsa Ramlat,yace to aure zaiyi mata ta fito da miji,Ramlat bata da wanda take so ciki,wasu ma matasan yara ne basu shirya aure ba a cikin samarin nata,
Sauran kuma duk gasu nan dai babu na zabe,kwatsam sai ga abokin Idrisa da suke shaye shaye da sace sace tare yaga Ramlat yace yana so,
Shi kam Idrisa sabo da Abokinsa ne abokin harkarsa yace na baka ita,ka shirya aure nan da sati biyu,Ramlat da Hafsatu da dangin Idrisa kaf babu me kaunar wannan aure,amma basu da bakin magana domin Idrisa duk wanda ya soki wannan aure to ba fashi sai yaci mutuncinsa,Ramlat kuwa yasa mata takunkumi ba fita ba shiga,Abokinsa me sonta Zakari kwaya shi kadai yake zuwa wajen Ramlat zance shi aka bata,
Idan bata je wajensa ba Idrisa ya mata mugun duka,ko kallon Banza tayiwa Zakari Kwaya to ranar Idrisa sai ya zaneta,gaba daya yaran sun tsani Ubansu Idrisa,duk soyayyar da da mahaifi yanzu basa yiwa Idrisa ita,don sunfi so ma yayi tafiya.


AsmaBaffa
🏀🏀🏀🏀🏀🏀
🏀🏀🏀🏀🏀🏀


DUK INDA TA FADI



14-20


Official



By
AsmaBaffa




Sharhinku yafi komai birgeni readers tnx.




Yau Idrisa yayi shirin tafiya Abuja neman kudin auren Ramlat,sai Murna yaransa sukeyi Babansu zaiyi tafiya su huta da Bala'i,
Yana tafiya Hafsatu ta kwashe Dubu biyun da ya bar mata na abinci itama ta cika rigarta da Iska ta shiga motar kano ta tafi gidan kawarta wai..
Ba abinci ga Ramlat bata fita zance,kannenta Maza su Uku duk sun tarwatse ko wanne ya samu gida a makwafta ya labe ya shiga cikin yara ana dan basu ragowar jagwalgwalo suci,Ramlat da su Abu sun nemosu amma suka kara guduwa,sabo da kaf yan Uwan Babansu ko wanne da kalar tasa masifar,

Duk inda suka je ma tsiyarce ko za a basu sai sunsha dunguri da tankade keya ko zagi,har su Abu haka suke hantararsu ganin basu da kowa basu da gata basu da me Kula dasu,
Haka za ayi ta cin zalinsu shi yasa maimakon suje dangin Ubansu sai su tafi wajen alummar Annabi sunfi samun taimako,

Abu da sauran dangi duk yanzu taimakon da sukewa yaran Idrisa sun daina yi ko daya,Ramlat ma bata da gun zuwa yanzu idan taje gidan Abu da sauran zaginta sukeyi su koreta,
Yanzu duk inda ake biki ko suna a kauyen sai kaga Ramlat a gidan nan zata samu taci ta koshi har ta zubo wani a leda,kanzon tuwo ta kankaro ta shanya abinta ya bushe ta dafa taci,itace gona aiki ita ce ebowa mutane ruwa a biyata kudi,
Allah ya taimaketa Wasu sukazo zance ta samu kudin Mota,Talatu yayar Idrisa ta bugawa waya zata zo domin zuwa Company citta tayi aiki ta samu kudi,
Talatu tace gantalallu Ku kenan a titi dan iskan Ubanku,da shashashar uwarku hala sun kada wani wajen? Tace eh su Fahat ma suna makwafta,to sai kinzo kema uwar gantalince ce ai dole kiyi ai gado ne.

Ramlat taji haushi amma bata ce komai ba ta ce to sai na zo,haka ta shirya washe gari ta hau Mota sai kano gidan Talatu tana ajiye kayanta ta wuce aikin Citta,
Sai murna akeyi yau ga Ramlat ta dawo aiki gidan citta,nan fa Boss da sauran mutane ake ta faman tambayar Ramlat inda taje,kawai tace gidan yan uwansu taje a Abuja.zo kuga ihu da murna wajen Habiba da Firdausi,nan suka ja Ramlat gefe wai sai ta basu labarin Abuja,

To dama Ramlat ai sunyi zaman Abuja tasan harkar yan gayu,Zama tayi ta fara sharara musu karyar labarin haduwa,Habiba tace wlh watarana sai na tanaji kudin mota na biki can nasha kallo,
Firdausi tace ke a yan Uwan naku wacce za ayiwa biki mu je muma mu bawa idonmu hakkinsa, Ramlat ta tuno da dan Uwansu da Ummanta take bata labarinsa dan Iyayi dan gayu wanda ya tafi London karatu Mohd Sardauna,

Tace kai yayanmu za ayiwa aure kwanan nan baku ganshi ba kamar Bature,kyakyawan gaske dan gayu me kudi,a London yayi karatu,Habiba tace har naji sonsa ya kamani don Allah ki hadani dashi inama zai aureni,
Firdausi tace ai na fiki kyau banza ni zaki bawa shi,dan Allah kawata kimin hanyarsa,
Habiba tace to sai dai ko wacce ta hakura ko kuma Ramlat ta fada masa ya hademu ya aura,
Firdausi ce tayi magana ya sunansa? Mohd amma Sardauna ake ce masa Ramlat ta basu amsa, wow......wayyo.....Allah ya tafi da Imanina cewar Firdausi,Ramlat sai kallon shirmensu takeyi tana dariya suma kamar ba yan Birni ba akan namijin da basu taba gani ba ko ita me fadan bata sanshi ba amma sun rude haka,

Ramlat tace kun San me?sukace sai kin fada tace Duk sati biyu yake zuwa Makkah,Hangame baki sukayi Habiba tace amma Rijiyar kudi ce dasu ko? Ramlat tace a'a Maminsa tace engine buga kudi ne dasu,
Yana nan a cikin wani daki a gidan kasa anan suka boye ake ta bugo kudi,Suka kara gigicewa sosai,Habiba ta kara washe baki tace har gidan kasa ne dasu? Underground building sosai harda gado kamar jirgin sama a ciki in kika ga Bed Din sai kin kusa suma ni kaina Ramlat me babbar kwakwalwa na kusa shidewa bare Ku da ko secondary baku je ba you can't even spell ur name, kullum da naman kaza suke karyawa gashi nan cikin katon baho baho an soya kullum Kaci ka bari,tunda naje nake faman ci bana cin komai sai shi.

Tab dole kice baza ki dawo ba kawas gashi nan kinyi wani haske,na zata Mai kika samu me kyau,Ramlat tace hmm tare da tabe baki tana basarwa tace ina ai zaki da maikone kawai ko ruwa ban fiye Sha ba sai Madara.
Kullum sai kayi wanka sau bakwai a gidan,Habiba tace me yasa baki samo miji ba a gidan ai wlh da nice saina auri wani ta karfi da mai da yaji,
Ramlat tace kun San Mohd din da nake fada muku to babansa yayan Umman mu ne kuma ni yace yana so wai dan Allah na aureshi,shine ni kuma nace bana sonsa,in fada muku har kuka ya dinga yi wai mutuwa zaiyi idan ba ni,Habiba takaici ya kamata tace aikin banza dalla Firdausi zo mu koma aikinmu,Firdausi tace Ramlat tunda mu Allah baiyi zai aure mu ba mun hakura mun rungumi kaddara amma ina baki shawara ki koma ki aureshi, Ramlat tace na gama da babinsa ko kukan jini zaiyi,harfa a asibiti aka kwantar dashi a kaina,Allah sarki cewar Firdausi ba komai kinwa kanki wlh baza ki samu kamar sa ba kuma sai Allah ya saka masa,Ramlat kara langabewa tayi tana yanga tace nan da 2wks zan koma can fa,maybe idan yaci sa'a I wl go back to him
Nan suka ci gaba da aikinsu suna hararaar Ramlat kishi ya kamasu,hassada da zallar bakin ciki ya gama kama su Habiba,har tayi sati biyu tana zuwa aiki su Habiba basu kara Kula Ramlat ba,kunji kuruciya.
Ramlat dama in baza Ku manta ba na fada muku watarana muguwar shu'uma ce sai kayi mamakin abinda zata aikata,watarana kuma ba ruwanta da duniya.

Bayan Ramlat tayi sati biyu a gidan Talatu sai suka fara zaginta da ci mata mutunci tare da yaranta yan mata,ganin Ramlat tana samun yan kudi su basa samu,
Ba arziki Talatu tace Ramlat ta bar mata gida ta koma wajen dan iskan ubanta,
Ramlat tana shiryawa ta koma zangon Katab sabo da bata son auren da Babanta zai mata,daga Hafsat Umma har Idrisa Kawu babu wanda ya dawo gidan suna can,

Yaran maza sun lalace Almajiri ya fisu daraja a kauyen,makwaftan ma da suke zuwa sun koresu,haka suka koma gidansu ba kowa sai su kadai,haka suke kwana da safe suje barar abinci makwafta,haka za ayi ta tsuga ruwa su kadai a daki kwal,yan yara kana na abin tausayi,yanzu sun koma yo itace da ciyawa a kauyen suna siyarwa masu kiwo ciyawar,itace kuma masu abincin siyarwa,Fahat shi ke musu wanki da dan sauran Abubuwa,

Ramlat sati daya tayi tal a Zangon Katab nan ma ta samo kudi wajen abokan arziki wanda suka riketa da Amana wato Alhaji Salisu da matarsa Umaima,sai yaranta sa'anin Ramlat guda uku,sune ma suke bawa Ramlat kwancen kayansu,shi yasa har da sutura ta samo sannan cike da tausayin yan Uwanta tace gwara ta dawo gida ta Kula dasu kar rayuwarsu ta tagayyara,

Suna zaune a gidan sunyi takugumi dan acaba ya sauke Anty Ramlat da kaya Niki Niki sai gulmarta akeyi a kauyen ta Zama sarkin gantali irin uwarta,ganin ta kara kiba da kyau suka dinga bazawa cewar karuwanci takeyi yanzu a birni,duk farin jinin Ramlat samari daina zuwa zance sukayi wajenta,
Ko mutum yazo sai a zuga shi bazai kara zuwa ba.

Su kuwa yan kannenta Fahat,Daddy da Shaheed da gudu suka fito suna Oyoyo Anty....sai murna sukeyi,Ramlat tana ajiye kayanta gidan ta hau gyarawa ko iyayenta bata tambaya ba don tasan halinsu, saida ta gama gyara ko ina fes sannan ta tattara kayan wankin yaran ta wanke musu tsab ta shanya,sannan tayi musu wanka sosai ta shafesu da Mai da sa musu sababbin kayan gwanjon da ta siyo musu,sai ga yara sunfito fes dasu dama gasu kyawawa farare wahala ce ta dafar musu da fata sukayi duhu,

Doya da kwai me uban yawa tare da Awara da kwai harda tsire a gefe a bakin kasuwa ta tsaya ta siya musu,
Harda yogourt kowa roba daya, tsakar gida suka zauna a tabarma suka baje suka ci suka koshi sannan suka cika gidan da ruwa,tayi wanka ta shirya, suka koma daki saman tabarma ta kwanta ta jawo kannenta jikinta Fahat ta sashi a bayanta,Daddy kansa ta dora a saman cikinta,Shaheed kuma ta sashi a gabanta haka sukayi baccinsu me dadi,

Bayan dawowarta da kwana Uku yan iskan kauyen suka fara haura musu gida suna son su lalata Ramlat,
Wani dan tsoho me mutunci Ramlat taje ta fadawa ai kuwa tsohon yace taje Allah zai kiyaye ba abinda zai samesu,

Saida Ramlat ta kwashe sati Uku da dawowa kauyen kudin da ta samo sun fara karewa,sai ga Idrisa ya dawo daga Abuja Niki Niki ana ta shigo da buhun huna,
Sannu da zuwa kawai sukayi masa amma a fili sai sukayi magana kasa kasa mun shiga uku Anty Kawu ya dawo,
Kwantar musu da hankali tayi tace karku damu babu abinda zai faru kar Ku kara barin gidan nan kunji? To sukace tace kwanan nan zanyi aure,me kudi zan aura a birni na zo na kwasheku,murna suka fara yi Fahat yace Anty ya sunansa? Ramlat ta rasa wanne suna zata ce tace Mohd ana ce Masa Sardauna,shine mijina fa,Fahat yace amma Kawu fa a kauyen nan zai ba dake,Ramlat ta rasa me zata ce sai Hawaye shauuuuuu suna ta sintiri a fuskarta,dama tasan indai Kawunsu ya dawo zai mata auren.

Kawu dai an kawo kayan abinci da tarkacen amfani,abin mamaki sai ga kawu ya jawo buhu buhun kaya tare da budewa Ramlat sai ga set din glass cups da juck kala biyu da gani ba sababbi bane second hand ne,aka bude wasu plates ne shima na zamani sunfi set goma na yan gayu amma second hand,
Sai ga cocula me yatsu da Sauran kalolin kayan kitchen harda tukwane,da abubuwa da yawa na amfani amma babu sabo ko daya,yana murmushi yace Ramlatu kayan dakinki ne,ai sai kinfi kowa gata a garin nan,

Takaici ya gama kashe Ramlat amma tace na gode Kawu ta kaisu daki ta ajiye cike da bakin ciki,Ranar dai sunci kayan dadi da Idrisa ya kawo tsaraba.

Idrisa ya gama sanarwa danginsa cewar aure nan da sati biyu,Abu tace yanzu Idrisa wa ka taba ganin ya aurar da yarsa ba gado ba katifa sai kayan faranti da cokula suma na wasu ne suka cire zasu zubar su canja sabo amma ka karbo,maimakon kuyi amfani dasu a gida sai kace shi zaka sawa ya a dakinta.

A wanne garin mahaukatan kaga anayin haka? Dama wannan ne shirin naka da shine har ka bada yarka karama da ita Ramlat har nawa take,har yanzu Ramlat bata fara Al'ada ba fa bare kace ta gama girma,Idrisa yace yarki ce Abu ko tawa? Baki bude Abu tace takace,yace to ki kyaleni ba ruwanki aure ba fashi dama dan kar kuce ban fada muku bane shi yasa.

Abu dai tafiyarta tayi ta kyalesu,Hafsatu dai har yau tana kano ita da Ilham,Da kyar Idrisa ya samu Number inda take,tace baza ta dawo ba sai ya aiko mata da kudin mota,da kyar ya aika mata da kudi,amma maimakon ta dawo sai ta kara hawa motar Zamfara sai da ta kara sati daya a Zamfara tayo Maula sosai sannan ta dawo gida,

Yaran sunyi murna sabo da sunyi kewar Uwarsu,
Zakari kwaya ya kawo akwati daya ta lefe yar karama komai guda biyu duk kayan babu na arziki amma Idrisa sai murna,
Ramlat kullum kuka takeyi da addua a boye sabo da idan Kawunsu ya kamata tana kuka akan bata San Zakari kwaya to tasan sai taci dukan gaske.

Mohd kuwa bayan siyan motarsa yanzu kuma ya rushe gidansu ya hade da wanda ya siya kusa dasu tare da Gina musu sabon gida na gani na fada a unguwar da suke,Mami ce tace kawai ya Gina musu a inda suke.komai ya lafa Sardauna ya samu nutsuwa sai kara girma da kyau yakeyi kullum,
Ga gida me kyau ga sabuwar mota ya karo wulakanci yanzu kullum tsirfa da felekensa karuwa sukeyi basa raguwa,
Daukan wanka kuwa abin ba magana sai abinda ya Karu,domin sajensa da dan gemu ya kara yawa sosai..yanzu iyayensa ne ke gabansa kawai yanda zai gasu.

Biki ya kankama ana ta shirye shirye,Yau Saturday Saura kwana Uku biki,Ramlat da Hafsatu suka shirya suka tafi neman danginsu ko za su samu tallafi amma ina Alhaji Kabiru Fakas da iyalansa ance wai sun koma kasar waje karatu,Mami kuma bakin cikin yayanta yasa ta canja state,haka suka dawo gida suna sauka a mota suka ci karo da wanda za a bawa Ramlat Zakari kwaya sai tsamin dauda yakeyi Wal hamhamatu da Hamami,yamurmurin tsoho dashi ba kyan gani ragowar Wiwi.

Ramlat ya kalla fuska ba Rahma yace ke dan Ubanki baki daina gantali ba kin gaji uwarki ko to kije na fasa aurenki zan turo a karbi kaya,bazan hada jini daku ba,
Wani farin ciki ne ya lullube Ramlat har bata San sanda ta saki murmushi ba,nan take ta tsuguna kasa tayi sujjadar godiya ga Allah a titi kowa na kallonta,Hafsatu ma dadi da farin ciki taji,rai fes suka koma gida,

Washe gari da sassafe Idrisa ya shugo a fusace yana kwalawa Ramlat kira tana fitowa jiki na Mazari kafin tace komai ya kwasheta da mari nan yafara dukanta baji ba gani yana zaginta ya fara ball da ita sai da ta kusa daina Numfashi sannan ya kyaleta ya bi Hafsatu itama da nata dukan kafin ya mata da yawa ta dauki itace ta kwala masa a ka,nan ya fadi ya Sume a wajen, Ilham dake Kuka ta goya ta dauki akwati tana kuka tare da barin gidan ta kara Hawa mota ta tafi..

Su Fahat ne suka ruga suka Nemo mutane aka zo tare da watsawa Idrisa ruwa ya farfado,Abu tana kuka suka kinkimi Ramlat suka kaita asibiti,bayan sun dawo suka mata wanka tare da gasata,taci abinci sannan aka kira me dori ya duba Ramlat kashinta ya tsage a hannu da kaf targade ko ina an daureta da tsumma da kara,ga su bandage da plaster ba kyan gani,ana haka aka nemi Fahat kaf garin aka rasa,nan zance ya watsu Fahat ya bata,wasa wasa har an shafe sati ba Fahat ba dalilinsa.

Bayan kwana goma Ramlat ta danji sauki Sannan dangi suka hadu aka Nemo Idrisa aji dalilinsa na wannan dukan kaf garin tsinewa Idrisa akeyi ana Allah Wadai da halinsa,




AsmaBaffa
🏀🏀🏀🏀🏀🏀
🏀🏀🏀🏀🏀🏀



DUK INDA TA FADI



21-25




Official



By
AsmaBaffa





Bazan daina gode muku ba masoyana kuna sani nishadi.






Dangi kaf an Taru har Talatu dake cikin Kano,da liman tare da mai unguwa Idrisa yana tsakiyarsu kamar mutumin kirki.
Liman yace Bismilla Idrisa muna jinka mene dalilinka nayiwa yarka wannan mummunan hukunci? Idrisa ya fara magana ta mai Dani mutumin banza Saura kwana Uku bikinta ta fadawa Zakari bata sonsa tare da ci masa mutunci,na rageku cikin halayen Idrisa harda karya domin Idrisa mugun makaryaci ne,haka kawai zai zauna ya tsara zance ya fada,har yaransa da dangi kowa baya yarda da maganarsa,sabo da rabinta karyace kawai,

Ramlat suka kira itama,Liman yace Ramlat ya akayi zakaninki da Zakari? Ramlat ta kwashe yanda akayi ta fada,nan aka taru suka rufe Idrisa kowa da nasa sai da sukayi masa tatas Sannan sukace zasu kaishi kara kotu nan gaba a yada shi a gidan radio Allah ya bashi Amana yayi watsi da ita.mai unguwa yace Idrisa yanzu kai dadinka ne yaranka duk sun tarwatse badan Allah ya baka shiryayyu ba ya kake zato,wannan Bai isheka ba,duk abinda kake musu Allah fa zai tambayeka ka daina tunanin basu da hakki, shi yasa Allah yayi su shiryayyu har sunfi wanda ke da gata shiryuwa da Hali mai kyau,wlh ka kiyayi duniya,matarka ta tafi ba a San inda take ba,ba dole halinka yasa ta Zama kamar mahaukaciya ba,ka kyalesu da talauci da halayenka na banza ma kadai ya ishesu ba sai ka kara musu da wannan bakin muguntar taka ba,

Talatu tace kai kullum baka kaunar Zama lafiya kullum kamar a gindinka Bala'i ya kare,ga shaye shaye mutumin banza makaryaci barawo.
Haka kowa da abinda zai ce sannan sukayi masa nasiha,aka jawo Aya da hadisi sannan Idrisa yace shike nan komai ya wuce zai gyara,
Kamar gaske Ramlat ta murmure da yaransa Amma ba Fahat ba labarinsa,
Kuma Idrisa Bai damu da batan yaronsa ba,shuru shuru tun ana sa ran dawowar Hafsatu itama abin yaci tura,

Ramlat duk sun shiga damuwa,babu inda ba a nemeta ba amma an rasata,tafiya tayi nisa har an kwashe wajen wata biyar babu Labarin Hafsatu har ma sun hakura,Fahat ma ya shiga duniya babu labari,
Halayen Idrisa kuwa sai abinda ya Karu kullum abin gaba yakeyi,game da Ramlat zancenta take fita,sannan kuma bata cika Zama a kauyen ba kullum tana kano tana aikinta a Company dinsu na Citta,babu abinda ke damunta face tunanin Ummansu da ta bace da Fahat.
Komai duk ya gama fita a kanta,zagi da hantara kuwa bata fasa Sha ba a wajen su Talatu da yaranta aikin gidan ma duk Ramlat keyin sa,abin mamaki Ramlat idan taje birni bata Kula ko wanne saurayi ko da wasa dalilinta samarin birni baza ta iya musu wayo ba,idonsu a bude yake,ga mafi yawancin samari soyayyarsu yanzu daga mutum yazo zance sai ya fara taba mace da ta tsaya shike nan ya samu wajen rage Zafi.
Gani sukeyi wannan itace soyayya,ko wannan shi zaisa mutum ya soka ko ya aureka,wasu sabo da kwadayin kudi,yan mata Ku kwantar da hankalinku Ku daina bari samari suna zuwa suna tabe muku jiki me tsada me daraja ba tare da sadaki ba,wacce keyi dan kudi to ki daina domin ko ba ta hanun namiji ba,ko baki bari ya tabaki ba rabonki shi zaki samu,Allah sai ya baki abin indai zaki rokeshi zai kawo miki hanya ki samu ko mene kike nema,ko nawa kike nema baki da hanya koma ki roki Allah,yi sallah,karatun Qurani etc ki roki Allah kullum zai baki,ki kai kukanki idan waya kike so,ko Computer ke mota ce wlh ki dage iya yinki ba wasa ki roki Allah ki gani idan Allah Bai kawo miki silar samun abun ba,
Ba kya son talauci ki daina saida jikinki kina zina ko Maza su danyi tabe tabe koma kullum da dare ki dinga karanta suratul waqi'a ba ke ba rasa kudi kina rasawa wasu zasu zo,zakiga ko Saurayin ne ba sai ya taba ki ba zai baki kudin.
Dan Allah Ku kiyaye mata yanzu wannan ya gama duniya kaf aikin kenan,ya kamata muyiwa kanmu fada.

Sardauna zaune cikin Office dinsa yana rubuce rubuce ga kwalin juice nan a gabansa da glass cup me matukar kyau,yana korawa wayarsa ce ta fara ruri,Murmushi ya saki ganin Naufal rubuce kan screen,yana dagawa Sardauna yace am still waiting for u here in my Office,i wanna go home Man,dariya Naufal yayi so sorry am on way just give me 5mnt yanda suke tsara turanci kai

Please Login or Register in order to submit comment