Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da rike hannunta,yace ana ga yaki kina ga Kura Ramlat Mami bata Fada miki komai ba? ni da kayana zan tsaya har sai kin kawo kanki,ai kyaleki nayi ki warke sosai Sabo da naga kin wahala na farko,

Abinda baki sani ba Mall dina fa Gomnati wai tasa Masa x zata rushe wai diyya zasu biyani Amma na gano ba Gomnati bane ba wata diyya da za a bani,kuma abin mamaki ace ko tsinke Baza ka dauka ciki ba,ina tunanin fa Daddy ne yasa amin haka dan na karbi nasa kyautar,kuma wlh ko wanne Hali zan shiga Bazan ko kula su ba,domin da nayi niyyar kyalewa kawai na musu biyayya tunda dole su suka haifeni Amma naga ma abun nasu ba Imani na fasa wlh,

Wai Taxi ta ma an nemeta an rasa a gidan driver,abin haushi fili dukka wai an kwace su Gomnati tun daga nan na gano Mama ce suka shirya,
Ina tabbatar miki gidan nan ma ba tsira zaiyi ba nan gaba,
Kuma kinga ni banda kudin da koti zata bi min hakkina abin kunyane ma aji iyaye ne sukayi wannan abu,na tozarta kaina,yanzu Mami ma lallabawa nakeyi kar hawan jini ya shigeta

Ban san ya zanyi ba ya furta tare da zamewa ya kwanta a cinyar Ramlat tana shafa masa gashi tare da dan bubbuga kirjinsa a hankali kadan na lallashi.
Zuwa gobe ki zama Ready Mami tasan komai canja state zamuyi gaba daya inda Baza su ganmu ba ma sai na tabbatar da sunyi nadamar halinsu .

Ramlat ta fara kuka Suna lallashin kansu tace ai ni bani da matsala na saba da rayuwa ko wacce iri ce yanzu zan samu damar baje fasahata,dariya Sardauna yayi yace to karatu fa? Ramlat tace ai Allah ya rigada ya amshi mugun fatan da nayiwa kaina,daina zancen karatu sai munyi kudi,in ma bamuyi ba ai ba dole bane bokon sai nayi arabic,

Yanzu ka daina damun kanka Allah baya hana bawansa haushina daya kana yaro haka nauyinmu ya hau kanka da wuri,kafin kace me annurin Sardauna ya dauke yace na hanaki ce min yaro wlh zanyi maganinki ,

Ramlat murmushi tayi tare da rungumo mijinta tana kissing dinsa dan ya manta da damuwarsa,nan wasansu ya canja Salo Mohd ya zauce,ya susuce itama Ramlat haka,Dukiyar fulaninta ya cafka tare da fara baje kolinsa, yau ma Ramlat ta dandana azaba ba laifi,sai da ya kusa kwana suna abu daya Sabo da ta sashi farin ciki bata nuna taji Zafi da yawa ba.
Sardauna yau ma wasai yaji shi zam zam,sunsha baccinsu da adduoi sosai,

Washe gari da sassafe sai ga Babar Bilkisu da wasu danginta su biyu sunzo daga kauyen tudun wada,
Daddyn Mohd yazo tare da kannen Sardauna kaf su ukun mace da Maza biyu,sai iyayi sukeyi suna ji da kansu tun daga kallonsu kasan inda mutunci yake basu dosa bama,basu da tarbiyya ko daya kasancewar a turai suke rayuwa.

Gaba daya an hadu a palo Harda Sardauna,Mami,da iyayen Bilkisu,Ramlat na kusa da kafar Daddyn Mohd,Mohd yazo ya jawota kiiiiii ta dawo kusa dashi,kannensa sai kallonsa sukeyi yanda suka taso cikin kudi da gata Amma ya fisu komai da komai kyau,ga daukan wanka kamar a turai,gashi duk iyayinsu sunga ko kama kafarsa basuyi ba,magana ma da yayiwa Ramlat da turanci suka ji kamar dan America mamaki ya kamasu har iyayensa,
Kuma ko kallo kannan nasa basu isheshi ba,shima ganin yanda suke yanga yasa yaki kulasu ya nuna ya fisu iya shege,kuma ai shine babba.

Da addua aka bude taro,dangin Bilkisu Babarta ta fara magana Bilkisu naji komai kuma banyi mamaki ba,kin bani kunya dama nasan zaki aikata,tunda muma kaf danginki mun san halinki na son kai,rowa,da wulakanci akan tsafta da rashin kawaici,ni nan uwarki a gabana kika fadawa kawarki a Abuja cewar yar aikinkice ni,sannan mijinki yasha yi mana kyauta ki rage kudin ki bamu kadan duk mun sani kyaleki mukeyi,akwai sanda yar uwarki taje da yarta jaririya kika ce indai da sabuwar haihuwa ne Baza ta kwanar miki gida ba,kina kyankyaminta
Sannan kanwata Uwa daya Uba daya taje gidanki tana zawo kikace mun shiga Uku Amma ba kwana zakiyi ba?zaku dauki cholera ke da yaranki da Mijinki,Mami duk idan nace fadar halin Bilkisu zanyi na rashin kyautawa bazai fadu ba suna nan jingim.

Sanadin idan na tsine miki kaina nayiwa shi yasa na kyaleki ba kyau tsinewa yaro,abinda kukayi kun kyauta?Kai Kabiru baka ji kunya ba uwarka fa,
Nifa ba cewa nayi ta bani ba no su dawo gaba dayansu mu zauna na bashi kwakwaran aiki kawai cewar Daddy

Nan Mami da Babar Bilkisu sukayi musu tas,Sardauna yayi magana tare da cewa ku kwantar da hankalinku ai dai dan ni ake wannan ko?to Bazan je ba kuma bana son abin hanunnunsu,ko zan mutu da talauci tunda suka bullo min ta haka wlh Bazan karba ba,
Kome za ayi min sai daí ayi Mami shirya ki bisu Allah yasa bakin iya jarabawarki kenan,ni da Matata zamu tafi in Allah ya yarda sai kun sha mamaki,Allah yana tare damu,karbe min Mall da wasu kaya nawa bazai Sa ni komi ba,dama karshensa ne yazo Allah ne ya tsara haka,ku kuka haifeni dole da yayiwa iyayensa biyayya indai yana so ya gama da duniya lfy,

Duk da cewa baku cancanci iyaye ba,bai dace a kiraku da iyaye ba,kun haifeni Bazan iya biyanku abinda kukayi ba Musamman ke Mama Uwa,nayi laifi kuyi hakuri ku yafe min Amma wlh Bazan biku ba kuma kwandalarku bana so,

Ramlat Hawaye ta fara Sardauna ya mintsineta wai tayi shuru,Mami kece tawa Bazan iya rayuwa ba ke ba while kina fadin duniya,kije ku tafi na gode zamu dinga waya zanzo mu dinga dubaki,Mami tace wa?ai wlh kafata kafarku wa nake dashi kamarka a duniya ai ko mutawace Mohd fata nake Allah ya karbi raina a hannunka ku tashi mu tafi ga gidan nan an bar musu,

Daddy yace Mami tunda shashasha ne ki kyaleshi kizo mu tafi tunanin Daddy dole Sardauna zaizo ganin Mami gidansu,
Mami tace Allah kiyasheni Kabiru,Sardauna yace Mami karki sha wahalar rayuwa ta biyu ko ki koma gidan su Naufal,Zanzo na daukeki,Ramlat tace tab wannan ba shawara bace kafarmu kafar abarmu.

Bilkisu takaici ya cika ta tace Mohd idan kabar nan Allah ya.....Babar Bilkisu ta karasa da ya Isa ban yafe miki ba,

Wlh kika kuskura kika masa baki kema na miki irinsa Allah ya Isa ban yafe miki ba Allah tsineki miki indai har kika masa baki,Bilkisu tace na yafe wlh karki min baki,Babar tace a zauna lfy.

Mami tace nima Kabiru indai na Isa dakai Sardauna ko a mafarki wlh ka masa baki ko Kalma marar dadi Ban yafe ba bani ba kai na cireka a Yara na,

Dadi ya lullube Sardauna sannan yace Da kun Barsu Mami suyi ta tsinuwarsu ba binsu zanyi ba kuma kwandalarku Bazan karba ba,naji da kunnena za ayi min aure ko da an daura tun yanzu ma nace na saketa saki iku wlh ko an daura a take zan saketa a filin ba sai anje ko ina ba,
Ga wannan yaron nan sune yayanku ku daura masa mana sai lallai dani ina da aurena an riga da an siyar dani aure mafi daraja a duniya.haka kawai ku tsinceni sama ta kai a takura min tashi muje Mami,
Daga Bilkisu har Daddy kallon Sardauna sukeyi da birgewa dadi na ratsasu yanda Sardauna ya nuna shi Namiji ne ba irin yaransu da suka rainasu ba.

Daddy yace zaka dawo da kanka yaro jeka muna jiranku,Sardauna yace Allah bamu lfy da nisan kwana me amfani.ga kannenka nan Nabeel shine me binka ga Nabeela ta tsakiya sai Auta Ammar cewar Bilkisu

Sardauna ya kallesu shekeke suna wani epizy yayan me kudi abinka da rashin shakuwa ba wanda ya damu da wani,Sardauna ne ma ya basu hannu suka gaisa Nabeela sai chewgum takeci,kas Kas, Sardauna ya mika mata hannu ta wani yatsina tana Kebe baki maimakon ya tafi sai karar Mari akaji Sardauna ya gallawa Nabeela shegen mari,Mama tace kaji yaro zaka dakar min yarinya haka kawaai? Nan Mama ta nuna Lallai da Su Nabeela suka shaku basu damu da Mohd ba tunda babu wannnan shakuwar ta jini ba a taso tare ba,

Mami tace Mohd kyalesu kazo,Nabeela ta jawa Mami tsaki Sardauna ya kara kafe shegiya da Mari,Mama kawai sai ta saka kuka za a kashe mata Yarta,anyi wa danta asiri zai kashe kanwarsa,Daddy Jin za a Zagar masa Uwa ya fara bala'i da masifa wa Bilkisu ahir dinta da gayawa mahaifiyarsa magana.

Nabeel kuwa Murmushi yayi tare da kara dagawa Sardauna babban yatsa ya birgeshi dama Nabeela bata da kunya ta rainashi a gida.
Ammar kuwa auta cewa yayi mama ki mari waccen kawai zai daki mana Anty Nabeela,Sardauna wani zagi da turanci ya aunawa Ammar tare da banko kofar bedroom ya shige ciki,Ramlat ta Mike tare da gallawa Nabeela da Ammar Harara tabi bayan mijinta fuuuuuuu tana kunkuni da zaginsu an tabo mata miji hhhh kuji Ramlatu da shishigi.

Daddy lallabasu yayi suka tafi da tunanin Nan da kwanaki talauci zai ishi Sardauna ya koma ya bisu har inda suke,Mama kuka takeyi a flight banzan yaro Sardauna ya daki Yarta.danma tana Jin sa a ranta ne sosai,da sai ta ramawa Nabeela.

Suma Iyayen Bilkisu Mami sukayi ta bawa hakuri suka tafi garinsu,
Washe gari da wuri ma Sardauna ya saida gidan da suke ciki suka tattara komai nasu kaf Ramlat ta kawo shawara a koma Adamawa ko kauye ne,Sardauna yace baki da hankali kauye ina zamu samu sana'ar yi har na dauki nauyinku?ko so kike mu lalace na haifi yara a kauye ba Ilmi,

Mami tace zancenka dutse namijin duniya mu tafi birni da kudin siyen gidanmu dana abinci kafin ka samu aikin yi,Baba me aiki harda kuka an sallameta,Sardauna yace karki damu Baba zanyi kudi insha'allah lokacin ba ke ba aiki ma du tare zamu zauna,Baba harda guda ayyiriri,tana masa Kirari.

Ramlat tace har motar ka siyar ne?tana nan da ita zamu tafi ai baza ayi gaggawar saida mota ba sai abinda Hali yayi,
Hannunta ya riko yana rada mata kiyi hakuri Ramlat haka rayuwa take Allah zai hore kinji zuciyar Ramlat tayi rauni kwalla ta cika mata Ido,ta dan waske tana murmushi tare da cewa af karka ji komai My King ai ni wannan ba bako na bane,Allah ya taimakemu dai,Mami tace yan nema kuzo mana mu wuce motar kayanfa tuni tayi gaba,

Motar Oga Sardauna suka shige Mami na baya,Ramlat a gaba Sardauna driver, Ramlat tace to Bismillahi mun tafi da kafar dama,DUN INDA TA FADI SHANE komai ta fanjama fanjam.

Yanzu zan fito da basiru na da dabaruna dana sani na gwagwarmarya da fuskantar rayuwa da nayi a baya.
Nice Chairman kaine sectiary mami kuma treasurer,rada masa tayi a kunne dan ciki na kuma p.r.o na wannan Tafiya.Dariya yayi Tare da cewa banyi ajiya ba ai sai nan gaba,Mami tace bafa nason gulma a fada mana a fili ya za a dinga wareni. Dariya sukayi sosai.
Saida suka je suka Yiwa Su Hafsatu Sallama,Idrisa harda sharbar kuka,yaron kirki surukinsa ya dinga musu addua da Sa Albarka.







Yanzu fa za a fara Novel din nan readers ayi hakuri a jure karatu.



AsmaBaffa
🏀🏀🏀🏀🏀🏀
🏀🏀🏀🏀🏀🏀


DUK INDA TA FADI





2PAGES





201-205 206-210




Official





By
AsmaBaffa







Wannan page na kara bawa kaina shi 🤣🤣🤣🤣







Tafiya sukayi Mami na bayan mota Ramlat da Mohd a gaba yana driving,tafiya suke uban shararawa,motar kayansu katuwa tana gabansu.
Shuru kakejin motar kowa da tunanin da yakeyi cikin ransa,Sardauna hankalinsa baya ma jikinsa Sam,Ramlat ta fuskanci hakan,bayan motar ta leka taga Mami bacci takeyi ma,

Hannunta ta daura saman nasa da yake driving tare da kallonsa,kadan ya kalleta tare da sakin murmushin karfin Hali,Ramlat tace tunani ko? Hmm ai kin san ma dole nayi tunani Queen,
Ramlat matsawa tayi tare da Dora masa kiss a lips tana murza yatsansa cike da shagwaba ta kwantar da kanta a kafadarsa, tace haba dan Allah King ka daina damuwa pls kaji zamu iya rayuwarmu ba matsala,
Murmushi ya sakar mata na farin ciki Ramlat fa hankali takeyi yanzu.

Sunyi nisa da Tafiya suka tsaya a resturant suka ci abinci yayi musu take away na wani abincin harda me kaya dayar motar,
Suka kara take hanya,sunyi nisa da Tafiya Ramlat ta rada masa a kunne Nice Chairman ta wannan tafiya Sabo da na saba ni da irin wannan rayuwar,kaine sectiary,Mami kuma P.r.o ta wannan tafiya, a hankali yake dariya tare da tambayarta shi kuma dan cikinki fa?Ramlat tace Trasurer kenan ai.


Suna Tafiya sosai magriba tayi kusa da wani kauye motar Sardauna ta tsaya sai gangarewa sukayi gefen titi,
Ya duba motar ba abinda basuyi ba taki tashi,Mami tace ga dare yayi,Wani me machine yazo wucewa Suka tsaidashi tare da tambayarsa ko akwai bakanike kusa? Mutumin yace ai kunyi sake sai dai ku kwana a kauyen can da Safe can gaba kanikawa suna fitowa da sassafe karfe 5 na yamma suke tashi,sai ka kira su gyara ma kuci gaba da Tafiya,

Mami kinji me yace?Mami tace ya zamuyi muje dama mun gaji kafata ta kumbura,tsayar da motar kayan mu kwana dashi dole a kauyen.

Tare da Driver me kaya suka tura motar zuwa kauyen Ramlat wai zata taya su Sardauna ya zabga mata harara tayi shuru.
Bayan magrib suka karasa Mami da Ramlat suka shiga wani gida a kauyen,ba kowa sai wata dattijuwa me matukar shafta kuma gidanta kaf kauyen shine ginin bulon siminti ko ina sumul sumul,
Sallah sukayi Suka fito wajen Driver da Sardauna suna saman wani bench a zaune,
Ramlat ta dauko abinci take away dinsu ta kai Mami cikin mota suka ci suka koshi suka sha ruwansu,Mami tace ni bacci nakeji bari na koma gidan tsohuwar nan ta bani makwanci na huta nayi bacci,ke Ramlat Mohd yana cikin matsala ki zauna wajensa tukunna kin san dai abinda ya dace,
Ramlat tace sai da Safe Mami jeki kawai,Mami ta wuce cikin gidan tsohuwar dake bakin kusa da Titi,suna hirarsu kamar sun san juna.

Ramlat wajen Sardauna taje tare da jawo hannunsa zo kaji,Driver me kaya ma ya shige gaban motarsa ya kwanta ciki abinsa,
Ramlat ta bude bayan mota tasa Sardauna ciki tare da jawo abinci take away ta dinga bashi a baki yana ci tana kwantar masa da hankali da kalamai masu sanyi na nutsuwa da nuna tsantsan kauna.

Bayan ya koshi ta mika masa brush dinsa yayi a wajen motar, itama haka suka kwanta a bayan motar Sardauna kasa kan kujerar baya,Ramlat tana samansa ya zama katifa,Mohd ba yanda baiyi ba tabi Mami amma ta ki sam sai ma hade bakinsu da tayi waje daya,tana masa shagwaba iri iri.

Har bacci ya kwashesu Sardauna yasa Karamin wani blanket me kyau ya rufesu basu farka ba sai da rana ta fito suna bude ido Ramlat ta kara kissing dinsa sannan suka fito daga blanket,yara suka gani cincirundo sun zagaye motar suna kallo,Ramlat tace bamuyi sallah ba dear,bari naje wajen Mami kafin na dawo kayi sallah,
Hannunta ya riko yana mata kallon so da kauna sannan yace Ok.

Tana zuwa gidan taga Mami har tayi wanka ta canja kaya tayi shar da ita suna karyawa ita da tsohuwar nan me tsafta.

Gaishesu Ramlat tayi matar tace ga ruwan wanka can kice da jikan namu ya shugo kuyi wanka ku karya sai ku tafi ai an zama daya.
Farin ciki ya kama Ramlat dama Mohd takeji shugaban yan Tsabta ace har ya tashi baiyi wanka ba ai ba lfy,
Da Sauri ta dawo wajensa lokacin yayi sallah saman Sallaya yana ta Addua tace taso muje inji Mami,da kyar ya yarda yabi Ramlat suka je gidan suka gaisa tsohuwar har tsokanarsa takeyi wannan askin fa dan boko?,
Murmushi kawai yayi,Ramlat tuni ta hada masa ruwan wanka ta kara wanke toilet din dama kuma ba ta bukatar wankewar Sabo da tsab take har kamshi takeyi,
Sardauna ya shiga wanka Ramlat ta bashi soap dinsa,kayan jikinsa yace ta shigo ta karba,mota ta koma ta bude boot ta gyara kayan ta ebo wanda zasu Sa ta dawo, Sardauna har ya gama wanka yana jiranta,
Na shigo?Ramlat ta tambaya,tana shiga da towel ta goge masa jiki tare da Sa masa riga t-shirt me dogon hannu,yasa boxers ta daura masa towel a kugu suka fito. A kusa da toilet din ta kara wanke masa kafafu ya daura alwala Sabo da baya zama ba alwala a jikinsa,

Kujera ta bashi a tsakar gidan suka zauna tare da shafa masa mai hannu da kafafu,sai man gashinsa ta shafa masa tare da taje masa gashinsa wanda yasha askin guyu,naga ana zafi yau kuma idan munje ma da Sauran aiki a gidan da zamu zauna sai an gyara gidan,ko wannan 3qutr zaka Sa? Sardauna yace ae mana in kina so sai na Sa,nan yasa wandon ya bata towel Amma duk da haka Ass down yayi da 3qtr rabin Boxers a waje abinka da dan wanka.

Abincinsu ta kawo kunun gyada me zafi da kosai,sai waina da miya ta Dage sai da ta tabbatar yaci ya koshi da yawan gaske,Mami suna kallonsu ta cikin daki tace kuyi Sauri mana Ramlat,
Ke ko wankan bakiyi ba,haka Sardauna yace bari na kira me gyaran jeki shirya,ya fice Ramlat tayi wanka fes itama ta shirya ta maida komai nasu cikin mota,sannan ta zauna a kusa da Mami dakin Tsohuwa ta shafa Powder da red jambaki sai kwalli ta zizara,
Sanye take cikin Atamfa red and blue tayi kyau Dinkin riga da skert daf daf a jikinta komai charas,bata daura dankwali ba acuci tayi tare da yafa gyale , takalmi irin kayanta,

Sannan ta fesa Bodyspray cikin jikinta,Mami na kallonta tana jin dadi yanda take kula da jikanta.
Me gyara na zuwa ya duba yace ai ba gyara bane kaga abinda ya zare daga jikin can,nan ya maida yace bazai karbi kudi ba, ba wani gyara bane.

Nan suka Yiwa matar Sallama da godiya suka tafi,mota me kaya tuni tayi gaba,Sardauna ya juyo ya kalli Ramlat yace kinyi kyau Queen,tace ai ka fini King.Mami tace na gaji da wareni da akeyi,sai dai kuyi ta kus kus ko yaushe ana maidani bare,
Dariya sukayi gaba daya har suka kusa karasawa cikin Adamawa state.

Mami a waya ta kira wani Babban mutum da ta sani a Adamawa dama shi ta fadawa ya nemo musu gida zasu siya me dan kyau a unguwa cikin birni me kyan rayuwa.

Mutumin Ya dade da sanin Mami tun suna Kwara state makwafta ne sunyi zaman mutunci da matansa,Kuma Mami ba karamin taimakonsa tayi ba lokacin yana talauci,
Mami tana fada masa jiki na rawa ya nemo musu gida karami me kyau a unguwa me kyau ta yan gayu.
Sardauna ba karamin Murna yayi ba gani gidan da unguwar nan take aka biya komai ayi takaddu da shedu me gida ya tafi,
Mutumin da ya nemo gidan shi ya taimaka da wasu mutane suka share gidan suka wanke komai neat tun kafin su Mami suzo,

Kaya aka shigar da Furniture suka shirya komai tsab Ramlat ta kara gyara gidan me dan gate karami mota daya ce zata iya shiga filin gidan,
Inda Allah ya taimakesu sabone gidan gal 3bedroom flat da palo kato yasha tiles ko ina me gidan aure zaiyi aka fasa yace gidan ya masa kadan wani zai Gina.

Me motar kaya suka masa sallama me kyau yaji dadi ya tafi,
Abinci Sardauna ya siyo musu,Ramlat sun gaji likis Sabo da aikin da sukayi,tun Safe suke shirya gida har Kusa da magrib sannan suka gama tare da yin wanka,Ramlat ta tattara kayansu da suka cire ta wankesu gaba daya ta shanya ta koma bedroom nata sai bacci,Mami ma tana nata dakin tayi sallah bacci takeyi Sardauna ya dawo dauke da take away bai ko zauna ba ya kwanta jikin Ramlat suka dinga bacci har 11 na dare sannan Ramlat suka farka cike da yunwa,abinci suka ci bayan ta kaiwa Mami nata.

Sardauna ne yayi magana gobe kuma kasuwa zamuje a siyo kayan girki duk da mun taho da na wancan gidan bai kamata a kashe kudin ba gwara asiyi Important abu,hakane cewar Ramlat.

Dafta Jibrila gaban Babynsa Hajara ya kalleta yana shanye idanu yace a'a duk wannan bathing din nawa ne? Zis clothe is Good,Sai ya tuno da karatun Coper yace Amazing and nice,u are special u are white and u are a quality and expert Baby,
My Blood is Moving slowly Wiz ur Love,U are living me in critical condition Wiz ur Love, wai dan a harkar lafiya ana cewa mutum ya shiga Critical condition shine ya rike words din, ,my heart is Bombing every day,My love Hajara you are dangerious to me,hhhhhh Hajara ta saki dariya,shi kuwa tunaninsa ya gama Tafiya da imaninta ita kuwa Hajara ma recording takeyi tana ji a wayarta tana dariya,
Amma sai taji Muryar Dafta na sheka dariyar murna yace Allah kuwa Hajara na making dinki Laugh ko cewararsa, Iam Kill Hajara(na mutu) wiz out u,Hajara ta masa fari tace ya ka gani sweetheart ai Dafta langabe kai yayi kamar ya suma,
Da zai tafi ya zaro 5k ya ba Hajara,a kauye Highest kyautarsa 1k ce Amma Hajara ta birni ce sai 5k zuwa sama.
Hajara tayi godiya Jibrila yace af wannan ba komai bane a wajena is Nosing(nothing) sai ko Ya hau mota suka yi sallama ya tafi, Hajara batace komai ba shi yayi ta zuba turanci ya mata sallama zai tafi Hajara tace ka bari mana nima kaji ta bakina?

Dafta yace no.. noo ai na gama fadar abinda ke raina a kanki ba sai kince komai ba,haka shine wayewa,irinmu bama doguwar hira mun mallaki hankalinmu kuma muna da aikin yi,, ai zance rata rata sai marar Sana'a ba irinmu busy ba,yana fada ya tada motarsa tare da warewa gida.

Lantan ta kwashe sati daya a Cikin garin Jigawa,ta kara gogewa,sabi da Lantan akwai basira da saurin gane abu,Allah ya zuba mata wayo, tayi yawo tayi yawon har yau bata samu ko Almajiri yace yana so ba,
Saloon ta shirya

Please Login or Register in order to submit comment