Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hannunta tare da kyalkyalewa da Dariya,
Sardauna ko a jikinsa bai san ma ana kallonsa ba gaban Ramlat yake sha yana chashe mata a hankali,
Key din motar Sa ya Mika mata wai tunda taki hakura ya bata motarsa,kin karba tayi,ya Ciro kudi nan ma ta makale kafada,dukawa yayi ta hau baya taki hawa,Dariya take Sosai ya juya cikin mota bata ma san tun kafin su taho tana wanka yayo musu take away na chicken da chips da wasu abubuwan,

ledar ya Mika mata ta karbe tare da budewa ta leka sai taga Kaza da chips tana dagowa wukil ta daga masa Babban yatsa.komawa yayi suka jera suna tafiya,Ramlat tace baka da kunya Allah ya Sardauna duk mutanen nan kaga abinda ka dinga yi hmm kuma fa ka iya rawar,muje kici time yana wucewa kar kiyi late
Dalibai kuwa wasu dariya suke ta yi Maza da mata,wasu suna ai da ganin yaron nan dan Iska ne sosai,wasu suce ai da gani bashi da kunya ko kadan,wasu sukace ai kudine ya ratsashi,wasu na ai da kanwar tasa dashi duk zamu ce ta tadda mujemu irinsu daya iskancinsu daya.wasu kuwa ba karamin birgesu sukeyi ba har so suke suzo schl dan susha kallo.manyam mutane suka ce ai yaro ne bashi da aikin yi,indai Yara matasa ne ka sake wlh sai sun kashe maka aure ko su raba ka da budurwarka Sabo da basu da aikin da zai hanasu soyayya,

tsayawa sukeyi bilhakki su nunawa yarinya caring da love sosai,kafin kayi aune sun kwace ma budurwa,idan yaro ya yaudari Mace tafi shan wahala Sabo da yanda ta shaku dashi zai zauna ya bata lokacinsa har suyi muguwar shakuwa,
Wani yace af ai yan Tecno ne shegu,a siyi waya Tecno a kwana ana chat ko waya da budurwa to me ya damesu babu aikin yi komai yi musu akeyi fa me zasuyi,

Wani dattijo yace matar da zan aura an Sa mana rana da ita saura 2mnths bikinmu irin yaran nan yazo suka hadu gani da kudina ina can busy ina neman kudi ashe ya zo ya rushe Gomnatina gaba daya,ya baje min aiki,ya gama mallake zuciyarta,shi kuma ko sisi bai da shi ba aurenta zaiyi ba,amma ina ji ina gani wlh tace ta fasa gaba daya yaro ya tafi da imaninta yanda yake nuna mata love da caring,

Wani cikin
dattijan yace ai Allah raba mu da sharrin yan
Tecno bala'i ne idan suka hadu da yarka ko budurwarka harda matan aure kashe musu aure sukeyi.

Haka kowa da abinda zaice akan Sardauna da Ramlat.
Har ya janyeta cikin mota suka ci abincinsu tunda ta fara cin naman bata kara magana ba saida ta gama,
Toothpick ya dauka guda yace bude hakoran na gani ko wani abu ya makale,ta kuwa bude kyakyawan hokaranta farare kar kanana dasu ya fara dan cire mata duk abinda ya gani yana inye ashe dai yarinyar me tsafta ce muga can ciki?ta kara wangalewa saida yayi dariya yace inye yar Kawunta ko kin canja uban ne,Ramlat tayi murmushi a'a dama bacin rai ne dole ina son Ubana,Good girl haka ake so,saida ya gyara mata komai tas,sannan ya kara shafa mata powder da lipglow,tace jambaki red nake so ka samin kaji. A'a banda shi kina da aure fa ki dinga tunawa ke me aure ce idan bakya tunawa duk sanda na dawo naga ba dai dai ba sai na mayar da ke cikakkiyar macen Aure,
Taya zaka maidani?zaki gani idan naazo mayar dake ai.
Tabe baki tayi tare da gyara mayafinta tayi kyau,
Gashinsa ya kara tajewa ya gyarashi ya ajiye comb din a mota tare da cewa muje,
Har class din da zasuyi lecture ya rakata tare da mika mata handbag dinta,ta shiga tare da zama a saitin window yanda zata dinga hango Sardauna tana dago masa hannu.

Lecturer bai shigoba,
Sardauna yana ta waje jikin window da take zaune tare zura hannunsa ta window yana nuna mata wani topic da aka koya musu a cikin waya yana mata bayaninsa,

Ramlat kuwa kallonsa kawai takeyi yana birgeta,
Yan ajin ana kallonsu sai kus kus akeyi,
Wayarta ya karba ya bude mata a ciki yana nuna mata a tata yanda zata dinga yi,domin Ramlat tunda ya siya mata wayar bata cika wani amfani da ita ba kullum tana Jakarta.
Wata budurwa ce cikin yan ajin ta dawo kusa da Ramlat tare da zama tace sannu Ramlat ko? Ramlat bata ji ba,sai Sardauna ne yace ana miki magana,sannan Ramlat ta juyo tace oh sannu kece ta rannan ko Fadeela?yeah nice ya kk?lfy sannan Fadeela ta gaishe da Sardauna ya amsa da fara'a.sai ga malamin ya shugo sannan Sardauna yace ayi karatu sosai kinji,i wl be waiting for u,Ramlat yanda yayi maganar cike da iyayi sai taji ya birgeta itama ta kwaikwayeshi Ok Na Mami tana basarwa, murmushi ya saki,Fadeela ma tayi dariya suka fara sauraron lecture.

Sardauna yana can zaune a sit din dake jikin bishiyoyi na students yana latsa waya,Ramlat tana hangoshi ta window da take,da ta dan bushi iska sai ta kalloshi idan Allah yasa ya dago sun hada Ido su sakarwa juna Murmushi wani sa'in ma har hannu take dago masa ta ajin shi kuma yace ta saurari lecture,

Tana ji tana jotting important words sosai take maida hankali har aka tashi 5pm dai dai,
Ta fito a gajiye wai tasha wahala ita da sabuwar Kawarta Fadeela,
Suna kara sowa ita da Fadeela mutuniyar kirki Sardauna ya mika mata ruwa Faro da juice,da murmushi ta karba tare da mikawa Fadeela daya suka Sha abinsu,Fadeela ta musu Sallama ta shiga motarta ta wuce gida, Sardauna ma suka shiga tasu suka bar schl din Ramlat na bashi Labarin Fadeela me kirki da hankali.

Ammi da yaranta suna Palo duk sun dawo daga schl suna tsara yanda Zasu bullowa Sardauna ya auri daya cikinsu dole.
Sallamar Sardauna suka ji cikin muryarsa can kasa,shuru sukayi tare da amsawa,
Tare da Ramlat suka shigo palon,Ammi suka gaisar kawai suka zauna kadan sannan suka Mike bari muyi wanka cewar Ramlat,
Ammi baki bude bayan sun shige Room tace lallai yarinyar nan Karuwa ce ta gaske,mu fa take fadawa wai zasuyi wanka mu San mijinta ne cewar Chuchu.
Bar shegiya zai tafi ne ai cewar Baby Juicy.

Sardauna kuwa da takalminsa ya kwanta kafarsa na lilo kasan bed,kafin Ramlat ta fito daga wanka har yayi bacci,tana fitowa ta tsuguna tare da cire masa takalman sannan ta gyara masa kwanciya da kyar,
Gown tasa har kasa me karamin hannu bata da nauyi Sam,Nesa can Da Sardauna ta kwanta itama amma sai ta tuna ba kyau baccin kusa da magrib,kuma lokacin Sallama ya kusa,
Haka ta daure ta tashi Sardauna dole ba kyau bacci bayan La'asar.Wanka ya shiga sannan ya fito tare da shirin masallaci,yana fita Merry ta fado dakin Ramlat ta zagi Ubanta son Ranta Ramlat na bata hakuri sai ga Ichichy ma ta dan dungureta tare da lakace mata hanci,
Kafin ta fita Juicy da Lilla sunzo suka zuba mata rankwashi lafiyayyu Chuchu ta kara da kinababbiya kamar Saliha Sumi Sumi zaki ci ubanki zai tafi ne,
Ammi tace Ku kyaleta ko ba komai taci darajar Mami amma ki dinga adana Karuwancinki ba a gidan nan ba munafuka ta gaji ubanta,ubanki zaki ci wlh.

Ramlat ba baki sai bada hakuri ana hawaye,Juicy tace kuma idan yazo kika fada masa sai na yankaki in ya tafi nan gidan ubanmu ne ba na wasu ba,cin arziki kika zo ki taka a sannu.
Ramlat tace Allah baku hakuri nima ina da gidan uba,Chuchu ta make bakinta dan uwarki kauyen?gidan kasar? Ubanki barawon banza mashayi mijin Hafsatu ai mun San komai,gantalallu.
Ramlat a hankali kamar tana kunkuni tace Kawu da Umma Ku kuka jawo wa kanku wlh bazan ji haushi ba gaskiya aka fada,ku gyara halinku gashi kun jawo mana amma ba ruwana ayi ta fada tunda ba ni bace ina ruwana ni nace kuyi😀😀 kunji Ramlat badai shirme ba,su Chuchu sun dauka kunkuni take musu tana zaginsu sai suka fara masgarta, a fili tace ni dai kuyi hakuri dan Allah Ramlat ta gansu jibga jibga. ficewa sukayi tare da cewa kinci darajar Mami.

Sardauna da ya dawo bata fada masa ba sabo da ta wani fannin Ramlat tana da hankali da wayo tare da hakuri,
Waya ta dauka tare da kiran Mami suna ta hira karshe ta mikawa Sardauna shima yace sai Next wk zai dawo sai yayi 2wks cif,
Haka Sardauna ya kwashe kwana 12 a Zaria Bai tafi ba,makarantar su Ramlat duk babu wanda Bai San shi ba sabo da yanda yake kula da Ramlat baya Jin kunyar uban kowa,
a ciki har frnds yayi jefi jefi yan wanka masu irin halinsa,
Ramlat sun shaku da Fadeela sosai,Har Sardauna yasan Fadeela sosai,
Islamiyya Saturday Sunday duk tana zuwa,Sosai Sardauna da Ramlat suka shaku sabo da zaman da sukayi komai tare sukeyi,
Ramlat Ya gama shagwabata da yanda yake kula da ita komai shi ke mata gashi jibi zai tafi ya barta.
Suma yaran Ammi sun dage sosai ganin Sardauna ya zabi daya Amma abu yaci tura kwata kwata da shi da Ramlat basa yini a gidan,
Ramlat duk aikin da zasu Sa ta tana yi musu ba musu ba raini,amma kullum basa gani sai hantara da zagi duk Sabo da Sardauna suna so aci dukiyar Ubansa wanda shi kanshi bai ma san uban nasa ba sai a photo.

Yau ana gobe Sardauna zai tafi sunyi shirin tafiya schl,yau kam bai Sa manyan kaya ba kanana ya sa,wando Jean baki pencil duk jikin wandon sarkoki ne baya da gaba,gashi duk a yanyanke crazy Jean, rigarsa silver color me hoton Michael Jackson a jiki,takalmi Silver shima harda Sa siririyar sarkarsa ta azurfa ta Maza tana masa kyau,Wandon ya zazzagoshi yana tafiya yana gyara shi domin Silver boxers dinsa rabi a waje yake,Sardauna yau kamar mawakin London haka ya fito yayi kyau sosai ga uwar Suma tasha shegen aski,duk inda Sardauna ya shiga sai ya haske wajen saboda daukan wanka da kyawunsa.
Ramlat cikin Lace ta fito Maroon and Milk doguwar riga mayafinta da takalmi hand bag duk Milk color ne,
Ba karamin kyau tayi ba,Sardauna saida ya kalleta ya kara Sannan suka tafi,yau wanda ke shakkun Sardauna tantiri ne to yau kam ya daina kokonto ya tabbatar,sabo da shigarsa kamar dan England ba kunya wandonsa ya gama zazzagewa duk da cewa ba karamin kyau yayi ba suna ganin Manyan kaya suna masa kyau sai suka ga ashe yama fi haduwa a Kanana.
Ga uwar Isa da takama yana yi kamar dan Sarki wasu sunce ma dan Sarki ne maybe,yayinda wasu basa ma so su kulashi domin da gani dan rainin hankali ne na gaske.










AsmaBaffa
🏀🏀🏀🏀🏀🏀
🏀🏀🏀🏀🏀🏀


DUK INDA TA FADI





116-120




Official





By
AsmaBaffa






FLOWER ga naki page.





Yau Sardauna sunsha gulma da kallo har suka dawo gida,su kansu su Chuchu wankan ya tafi da Imaninsu ba karya.
Da yamma Sardauna fita sukayi ya siyawa Ramlat abinda zata nema tare da koya mata wasu abubuwan sai da ya tabbatar ya gama mata komai da ya dace,
Suna dawowa a palo suka tarar da Professor Papa ya sha farin Medical glass,hannunsa dauke da magazine yana dubawa,gefensa kuma Wani dundumemen littafine na yan boko,su Chuchu sun ware kida palon suna jin wakar Falz wasu a ciki har rawa sukeyi Amma Professor ba abinda ya dameshi wai shi boko ta ratsashi Bature ne,
Su Ramlat suna shigowa suka gaida Professor bai amsa gaisuwar ba sai cewa yayi bismilla ga rawa nan idan zakuyi harkar ta yarace gasu nan ko wacce kure bajinta takeyi ba Sa gajiya ya kara Sa yana dariya tare da mikewa Ya shige ciki,
Ramlat tabe baki tayi tare da cewa Sardauna yi musu taka su gani tamu ba irin tasu bace, ka gani basu iya bama,

Na gaji Bazan iya Rawa ba,Dan Allah to kayi min na gani kaga gobe zaka tafi,Ramlat so take Su Chuchu su tabbatar sai abinda tace Sardauna keyi,shi yasa ta dameshi sai yayi rawar da ake yayi
Duk yanda taso Yayi rawa kin yi yayi shi ba a sashi ba a canja masa ra'ayi,
Su Ichichy da suke Saurarar Hirar dariya suka Yiwa Ramlat tare da cewa cusa kai ba kwarjini.
Maganar da sukayi itace ta fusata Sardauna ya mike tare da jan hannunta zasu wuce kenan sai ga professor ya fito.

Prof yace ku zauna mana yarana,ina son magana da ku,Sardauna suka zauna suna sauraron Prof,
Gyara Medical glass dinsa yayi tare da kallonsu ta kasan glass kuriiiii dama a saman hanci ya sashi,
Kai kace kana da aure ko?Sardauna ya furta yea,
Ina matar taka take da zama? dama Ammi bata Fada ma ba?gata nan ya nuna masa Ramlat.

Oh.....thats really? wannan yarinyar ai an kashe mata rayuwa,ina tabbatar maka idan tazo haihuwa Zai wahala bata hadu da yoyon fitsari ba, kamar wannan meke damun Mami da Baban wannan yarinya? Gaba daya an kashe muku rayuwa banji dadi ba sam,
Sardauna murmushi ya saki kana yace da na nemi matan banza fa? Ga Matata bani da matsala,
Prof kamar zaiyi kuka Sabo da Tausayin Ramlat an mata aure ko 20yrs bata kai ba yace ai gwara ka nemi manya a waje baka da matsala idan kana da Ilmi ga su Condom ne ko kunya babu.
Ramlat tayi tsagal tace ba kororon roba ba ko na kororon karfe ne Bazai bi mata ba,na yi yoyon fitsarin yafiye min, hhhhh I realise that u r very funny yarinya kina da abin dariya cewar Prof baiji haushi ba sai ma ganinsu yake rashin Ilmi ne

Kai gobe zaka wuce ko? Prof ya tambaya,Insha Allah Prof yace sai goben, babu Allah ya kaimu ba komai kawai sai goben yace.dama Prof shi akwai tattalin rayuwa baya zakka bare sadaka ko kyauta daga shi sai yaransa da matarsa,ko danginsa basa cin sisinsa.

Yace Ramlat da fatan Zaki dage kiyi Karatu sosai?duk abinda baki gane ba u r free to ask kizo dakina ki tambaya,
Ramlat tace tab yaushe zanzo dakinka Allah Bazan zo ba da aurena fa haka kawai ka Ja min.duk Prof kallon Ramlat bagidajiya yake.

Prof yace wannan yarinya da abin dariya kike,kamar jaririya haka nake kallonki Sabo da kankanta baki da wayo na gama ganeki Sabo da psychologically bakya abu in a moral way, I...I mean Morally,ki dake ki kara Ilmi Sabo da definetely kina rashin wayo eventually zaki tashi Zero a rayuwa,amma idan kin zama wise akwai possibility din cewar nan gaba zaki zama wata a kasar nan,amma kina haka Baza ki zama kowa ba.

Sardauna yace bari muci abinci suka bar masa wajen, tsohon baida kunya kaji dan Iska wai naje karatu wajensa cewar Ramlat,
Kyaleshi dakikin tsoho ne ai ki daina Saurarar zancensa da Alama asarar kudin karatu yayi bai ma san komai ba the way he use to talk hmm.

Sardauna gobe zai tafi sam baya son tafiya Sabo da shakuwa da sukayi da Ramlat,itama Ramlat haka abin yana ranta,
Da dare suna zaune cikin Room dinsu Ramlat tana kasa zaune tare da jingina jikinta a jikin gadon nasu Sardauna yana Saman Bed yana amfani da System dinsa.

Ramlat ta fara magana Tsoro nake ji.....na me?Sardauna ya furta ba tare da ya kalleta,
Tsoron gobe nake ji,dan Allah gobe kar kizo da wuri tsoronki nakeyi,Sardauna baice komai ba yana jin Ramlat tana ta Addua Allah kasa kar gobe tazo da wuri.

Kwana Ramlat tayi tana masifar Kuka akan Sardauna zai tafi,dole sai dai su zauna tare suyi karatun,in dai ba haka ba ta fasa yin kokari,tun Sardauna na lallashinta har ya gaji yace kada Allah yasa kiyi kanki zaki Yiwa ina ruwana.
Kuka ta kara fashewa dashi wai Sardauna yaci mata mutunci ya wulakantata shine taki kwanciya a saman Bed ta kwana kasan tiles tare da cewa Allah sa Mura ta kamani nayi ta tari muryata ta dashe ma.

Sardauna Dariya abin yake bashi ko yar 4yrs ai Baza tayi shirmen da Ramlat take zubawa ba,ko dai rashin iyaye ne tsayayyu?yace no kawai haka Allah yayita bata da wayo.
Ashe maganar da yayi Ramlat taji shi ba a zuciyarsa ya fada ba,ai kuwa tace ba sai ka bude kwakwalwata ka samin naka ba,wanne wayo ka fini?mutumin da aka masa tsallaken aji kayi tsayin kafa duk gemun nan da gani cream ka shafa ya fito, idan ba haka ba da nawa ka girmeni harda za a ganka da gemu haka?
Sardauna yace Amma dai kin san na fiki kuma ni namijine ke mace ki daina hada kanki dani ko Rabina baki kai ba.

Wa ya sani ko a London din Asibiti kaje aka maka Allurar girma ka dawo kato haka,kuma yaushe zaka fini fari, ai bazai yuwu ba kaje an kwashe ma fatarka an canja ma ta larabawa,
Na dai fiki yarinya ba yanda zakiyi kuma gobe ma zan tafi idan kika bata min rai sai na shekara guda ban zo na ganki ba,
Ramlat ta kara kukanta tare da cewa ai dai Bazan yi karatun ba,Insha'allah sai na nafi kowa jahilci a department dinmu.
Bacci ne ya kwashe Sardauna ya kyale Ramlat, Ramlat har ta gaji itama tayi bacci a kasan Tiles,cikin dare daya farka daukanta yayi tare da maidata Saman bed,
Light ya kunna ya shiga karewa halittarta kallo,daga nan ya fara Jin yanayinsa na canjawa,
A hankali ya janye mata rigarta me hannun bra boobs dinta suka bayyana gwanin birgewa,sai da ya dade yana kare musu kallo,sai kuma ya girgiza kansa yace no...no....ban girma ba da sauri ya jawo mata rigarta tare da rufewa harda cewa kusha zamanku cikin aminci sai nan da 5-6yrs
Kash 5-6yrs fa yayi yawa Allah kasa nayi sauri kawai naji na kai 27 ko 26 ne ma,tunani ya fada yanda zai girma da wuri ya fara lagude Ramlat .
Ramlat ce ta farka cike da rigimarta taci gaba da Kukanta kadan harda mikewa ta koma kasa ta kara kwanciyarta,

Washe gari da ciwon jiki ta tashi har Mura ta fara kamata kadan,
Sardauna yace maganinki kenan kinga adduarki ta karbu,nan ma subhanallah Ramlat ta dinga jaraba wai ya jawo mata cuta yana mata fatan cuta.
Da wuri Sardauna ya kira Mami gashi nan zai taho fa,Ramlat ta kara tsurewa yanzu tafiya zakayi?
Baki da hankali Ramlat yanzu ko ce miki nayi zan zauna ai kya min fada na tafi, a kan me zan maka fada ka tafi?Ina Jin dadina sai na ma fada ka tafi wlh bazan ma fada ba ai kara birgeni zakayi,
Bazan ma fada ba kayi zamanka kaji dan Allah,

Dariya ta kama Sardauna Sam Ramlat bata ganewa yanzu maganar da yayi ma Sam bata gane ba yace Ai kya min fada ita nufinta tsoro yakeji kar ta masa fada shine tace ai baza tayi ba.
Sardauna ya gama shirinsa tsab kayansa duk dama a boot din mota suke Bai fito dasu ba,i dan zai dauki wani abu sai yaje motarsa.
Yana gamawa Ammi ta kawo masa Abinci lafiyayye sabo da tasan bazai taba zuwa dining dinsu ba,idan ma yaje da Ramlat yake zuwa tana nuna musu karuwancinta cewar Ammi.

Zama sukayi suka ci abinci sosai,ana gamawa ta fara kukanta,yau kuma Sunday ba schl, bakya gajiya da kuka? Sardauna ya tambaya yana kallonta,
Tace Bazan gaji ba ni sai in ka fasa tafiya haka kawai suje su kasheni.harda shesheka takeyi.

Sardauna yace idan sun miki abu ki fada min a waya zanzo na daukeki,kiyi karatu sai na dawo na Canja miki gida,Ramlat tace ni bazanyi ba na fasa,ko naje Ajin bazan kalli jikin Board din ba,kuma toshe kunnena zanyi da tissue,
Sardauna yace kanki yarinya ya furta tare da mikewa tsaye ya kwashi wayoyinsa tunda kinki bari muyi sallamar arziki bari ma na tafi da wuri,
Shuru tayi,yaci gaba ke da ba masifaffiya ba Ramlat amma kike ta jaraba tun jiya,ke da ake shedarki me hakuri ce yau meke damunki,bakya hayaniya ana yabon halayenki yanzu jibi abinda kikeyi,ke da na sanki nutsatsiya me hankali yar shuru shuru dake ba ruwanki da duniya,.

Ramlat dadi taji an yabeta a ranta tace Ashe mutane sun San ina da Hali me kyau gashi yanzu abinda nakeyi kai bata kamata ba,a fili kuwa murmushi ta saki tare da cewa ni dama me hankalice ban san me yasa ba nake Kuka da masifa yau ne kadai fa,Na daina to. wai dan ta birge,Yace ko kefa ke da kike me hankali kuma sai ki dinga yin haka dan Allah?ya furta da shagwaba yana mata wayo, ai kuwa ta kyalkyale da dariya tare da cewa na daina ai,
Waka ya kunna mata ya dan mata rawa kadan, kafin kace me Ramlat ta koma dariya sosai,ya fara mata wakar Raps ta Lilwayne Wizzy kamar shi ya rera wakar yana rike hantsar wando yana yi da hannu daya abin dariya,
Ramlat tana dariya ta cire masa hannun daga rike hantsar wando da yayi tare da cewa abin kunya ba sai ka nuna min ba nasan kana da ita kaima,
Murmushi ya saki sannan ya kashe kidan wayar tasa zan wuce muje ki rakani, Kudi ya bata da yawa yace kudin napep,cin abinci da wani abu da ya dace dai gashi nan,idan wani abu ya taso Just give me a Ring call me,
Atm card na koya miki yadda ake komai zan dinga turo miki kudi kina cirewa,

Ramlat hawaye suka Sulalo mata tace to..na...na...gode Allah kara budi amma dan Allah ka dawo da wuri kaji?yace ba sai kin fada ba da wuri zan dawo kuma kullum za muyi waya,
Harda manna mata Kiss a goshi tare da hugging dinta tight sannan tace Allah kar kaji da wai in dai wata tayi min wani abu sai na balla

Please Login or Register in order to submit comment