Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*NAGA TAKAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸🌸🌸🌸


®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_


*Free Novel*


*Tun kafin nayi nisa a rubutu nake da burin rubuta wanan labari Allah bai nufa ba sai yanzu labarin Nan ya faru a gaske tun 19's wahalar rubuta shi nake gani Sabida yanda xan na had'a present da past Amma a yanzu Allah ya nufa zanyi insha Allah zai na zuwar muku sau uku a sati idan na samu sarari ma zaku iya samun pages fiye da haka labarin Nan ya bambanta da sauran novels Dina na baya za'a ga abubuwa da za'a ga Anya dagaske zai faru kuwa ya faru dagaske zaka iya aikata Abu da baka d'aukeshi a bakin komai ba sai bayan shekara da shekaru sai abun ya dawo maka Allah ya tsare mu da tsarewarsa ya tsaremu da imanninsa Ameen*


*Page 1*

*1992*

Da Sauri na shige d'akina na rufo k'ofa a lokacin da Umma ta hangoni ta biyoni a guje ko nauyin cikin dake jikina banji ba sabida tsabar tsoronta da nakeji.

Jingina nayi da k'ofar d'akin Ina sauke numfashi Umma kuwa sai tura k'ofar take Tana auna min zagi iyayena da kasa ta Dade da rufe musu Ido da take ta Kiran sunansu Tana zaga yasa naji wani irin hawaye na zubomin Sanin na riga da na kulle k'ofar yasa naja k'afana na nufi Kan gadona Sabida kaina danaji Yana neman fad'owa sabida tsananin ciwo rabona da abinci har na manta lemon kwalba da bredi su kawai suka zama abincina a matsayina na Mai tsohon ciki nida gidana ban Isa na fita ba sai uwar mijina ta nada min duka bredin ma da lemo sai na fakaici Bata palon nake fita na siya kamar yanda yanzu na faki idonta na fita Ina dawowa ta gani ta biyoni a guje sabida kawai na fita siyan abinda zan sawa cikina.



Dan cikina dake ta mutsu mutsu yasa na tuna da yunwar da nakeji na tashi na mik'e dak'yar na jawo ledar bredi da lemo Dana siyo na fara tusa bredin Ina hawaye Dan ko kad'an ba dadinsa nakeji ba ci kawai nake.

Abban Zahira daya fad'omin a Raina yasa naji na k'asa ma had'iyar bredin bansan lokacin da kuka ya k'wacemin ba na fara magana a fili cikin tsananin kuka

"Nasiru Mai nayi maka haka Dana cancanci haka daga wajen Kai da mahaifiyarka?laifine Dan na zab'eka a cikin dumbin masoyana na aureka ka raboni da dangina da kowa nawa ka kawoni wani garin kana wulakantani Mai nayi Dana cancanci haka daga wajenka"?

Kukan dayaci k'arfina yasa na kasa cigaba da maganar da nake a fili na koma na kwanta sabida rawar da jikina keyi na cigaba da kukan da ya zame min jiki ko da ba'a min komai ba fuskata Bata rabo da hawaye sosai nake k'ewan yarana Amma uwar mijina ta hanani ganinsu Mahaifinsu kansa sai dai na jiyo muryarsa rabon Dana saka shi a idona wata hud'u kenan da sunan muna gida daya.

Mahaifiyarsa ta zama tamkar itace matarsa Dan komai ita ke masa kwana ne kawai Bata yi a d'akinsa.


"Mommy Mommy"

Naji siririn muryar Zahira Tana tab'a k'ofata

Zumbur na mik'e nayi hanyar k'ofa har Ina cin tuntub'e rabon dana ga ita da Nadiya har na manta Dan k'arfi da yaji Umma ta hanani ganinsu a d'akinta suke kwana ko d'akinsa da ta ga sun nufo d'akina zata daka musu tsawa tasa kanwar Nasiru Safiyya ta d'aukesu ta maidasu daki ta kulle tun yaran Ina jin suna kukan hanasu da akayi su zo wajena har suka zo suka Saba

Idona ya rufe sosai da San ganin yarana hakane yasa ko kad'an ban tuna da wata Umma na palon ba Dan inajin tashin muryar ita da Safiyya da kanwar Safiyya Lami a palon suna Hira.

Da Sauri na bud'e k'ofar banyi wata wata ba na d'aga ta Sama na rungume ta a jikina inajin wani irin Sanyi a zuciyata Wai ace Kai da danka karfi da yaji a nemi rabaku itama zahiran lamo tayi a jikina Tana sauke ajiyar zuciya ko damuwa banyi da yanda naji cikina ya dunkulle ba sabida yanda na Dora Zahira a jikina wuwurga Ido na fara yi ko zan hango Nadiya Amma Banga alamarta ba da Sauri na sauke Zahira na ruk'o hannayenta nace Mata "Ina Nadiya"?

Cikin maganar Yara tace min "dazu Yaya ya rik'e hannunta suka fita Ni Kuma inasan ganinki Dana ga Umma Bata kallona shine na taho wajenki mommy Dan Allah zan kwana a dakinki Aunty Safiyya Tana yawan dukana ta mitsini na har da tsintsiyar kwakwa take Zane Ni"

Zahira ta karasa fada tana Kara fad'awa jikina


Rungumeta nayi kukan da nake d'annewa ya k'wacemin Wanda hakan ne ya jawo hankalin su Umma da kallo ya d'aukewa hankali kaina

Wani irin Ashar Umma ta lailayo tayo wajenmu har zaninta na neman fad'uwa

Kara rungume Zahira nayi a jikina ko kad'an banji tsoron yanda ta taho wajena gadan gadan ba Dan gani nake kamar Zahira na iya taremin dukan da zata kawo jikina Tana isowa ta fusge Zahira da k'arfi daga jikina ta wancakalar da ita daga Ni har Zahira ihu muka saka lokaci guda Dan Zahira ta Bugu Ina k'ok'arin mik'ewa Umma ta jawo hannuna ta murd'a Tana "Bana hanaki tab'a yaran Nan ba kin Raina Ni ko toh wlh Kika Kara tab'a yaran Nan sai na saka waya na zaneki babu ruwana da cikin jikinki shegiya Yar mayyu jikar mayyu gidan uban wa ma Kikaje dazu"?

Duk maganar da take sheshek'a kawai nake Ina kallon hannun Zahira daya kumbura sabida bugawar da tayi ko kadan banji zafin yanda take murd'amin hannu ba

Kamar numfashina zai d'auke na fara magana Ina "Umma idan Wani Abu nayi Miki Dan Allah Dan annabi kiyi hakuri ki yafemin Dan Allah ki daina azabtar Dani banida kowa sai Allah sai ku Dan Allah kiyi hakuri kibarni Naga yarana"


"Kinci ubanki Naeema ba dai kin dage sai kin zauna da Nasiru ba azaba yanzu na fara gana miki nace miki bana sanki bana kaunarki tunda Kika Haifi wanan faratun Yar Taki nace ki tafi Kika k'i sabida maita kafin ma tayi shekara Kika Kara k'unsar wani cikin ke gaki kin Samu gidan arzkiki Zaki baje ki cike Mana gidan da Yaya itama Nadiyar ko shekara biyu batayi ba Kika Kara d'aukar wani cikin Zakici ubanki Dani kike magana wlh azabar da zan gana Miki a gidanan sai kin roki mutuwa da kanki Nasiru kuwa sai dai ki hangoshi daga nesa ya Miki nisa wanan tsinanan cikin jikin naki Kuma ki haifeshi nagani"


Ta karasa Tana wancakalar da hannuna tare da juyawa ta fusgi hannun Zahira dake ta tsunduma ihu har lokacin tayi hanyar dakinsu da ita ta wurgata Kan katifa ta jawo k'ofar ta rufe.

Ni kuwa kukan ma kasawa nayi na koma na zuci

Ina kallonta ta dawo zauna ta cigaba da kallo ita da yaranta da duka suka girme min Dan banfi Sha takwas ba lokacin Dan inada shekara Sha hud'u Mukayi aure da Nasir shekara hud'u kenan da auren mu.


"Ke Naeema zo ki wuce kiyi wanke wanke zan Dora Mana girkin dare kafin Yaya ya dawo"


Safiyya tace Tana jefomin harara.

Ban tashi ba sai da Umma ta juyo ta Kara zabga min wani mugun harara na mik'e jikina na rawa cikin dafa bango na Isa kitchen din na fara tattara lodin kayan wanke wanke Wanda wasu Dan keta ba amfani akayi dasu ba aka jibgashi wajen wanke wanke Dan kawai a bani wahala.

A hankali na fara wanke wanken hawaye nata zubarmin har da majina ban damu duk na hanasu zubowar ba Dan gani nake zan samu sa'ida idan suka zubo zuciyata datamin nauyi zata ragemin nauyi

Guntattakin abincin da suka rage na hada naci Dan banida abinda xan sawa cikina anjima bredin Kuma na gaji da ci Yanzu wajen sati kenan bana iya ba haya sabida Basir daya sakoni gaba.

Bani na fito daga kitchen din ba sai da na musu jajjagen kayan Miya na Dora musu farar Shinkafa sanan Umma ta umarceni da na fito na koma d'akina Dan danta ya kusa dawowa Bata San yayi arba Dani zuciyarsa ta tashi.

Ahaka na koma d'akina inajin duk gabobin jikina na min ciwo sallah ma kasawa nayi sai kwanciya kawai da nayi Ina tunanin shekara biyu da.suka wuce da nake rayuwa da mijina Naseer dake balain Sona kamar ya goyani da irin soyayyar daya shayar Dani daga Kan haihuwar Nadiya zuwa Kan cikin jikina Naga ya fara sauyamin tunda mahaifiyarsa ta dawo gidan da kannensa Akan tunda babansu Tijjani ya saketa Bata da gidan zama sai gidansa tunda shine babban danta d'akin daya Kamata ya zama mallakin su Zahira ta gaje d'akin da yayanta.

Da tunanin da iyayena suna raye da kila duk Banga irin wanan rayuwar ba mahaifina da kowa ke shakka da Yana Raye da kila ya kwatomin yancina da kila ban Sha wanan wahalar ba sai dai Kash Allah baya barin wani Dan wani yaji dadi bansan lokacin da baccin wahala yayi awon gaba dani ba


*Mafarki*

Karar bud'e k'ofar d'akina ne yasa na bud'e idona da Sauri na mik'e na zauna Ina tunanin kila Umma ce na mata ba daidai ba tazo jibgata

Ganin babu wanda ya shigo d'akin yasa na mik'e daga kwancen da nake Ina mamakin wanda ya turo k'ofar Ina k'ok'arin nufar kofar na rufe kawai Naga mahaifiyata ta shigo da farin lullubi har saman kanta fuskarta kawai ne a waje.

Gwallo Ido nayi nace "Ummaaaa"

Kallona kawai take batayi magana ba Ni kuwa na durk'ushe akan gwiwata na fashe da kuka Ina "Haba Umma meyesa Kika tafi Kika barni a lokacin da nake tsaka da bukatarki? Umma kinsan wahalar Dana ke Sha kuwa a gidanan Dan Allah karki Kara tafiya ki barni ki tafi Dani Dan Allah"

Nace Ina Kara fashewa da kuka

Har lokacin Bata ce da Ni komai ba in Banda kallona da takeyi Ni kuwa Ina ganin haka na mik'e da sauri Dan na d'auko mayafina Dan bazan Kara yarda ta tafi ta barni ba nagaji da zaman gidan Naseer da bashida bambanci da kurkuku gwara nabi mahaifiyata zanina dake Kan gado kawai na rarumo na juyo da Sauri Dan ko batamin magana ba wlh sai na bita sai dai Ina nufar kofar Naga Ina ta tafiya na kasa isa wajen da take a tsaye sai kallona take idonta itama kamar da hawaye har da Dan guduna Ina mik'a Mata hannu Amma sai Naga kamar nisa takemim Ina hangota daga nesa kuka na fashe dashi Ina "Umma Dan Allah karkimin haka ki tafi Dani wlh azaba nake Sha a gidanan Dan Allah Umma ki tafi Dani ko ki Kaine wajen yan uwanki ko na Abba

Ihu nake sosai ina Kiran Sunan Umma da take tamin nisa Ina ta k'ok'arin tadota a haka naga ta zauna a dakalin dake tsakar gidan ta jawo buta naga ta fara alwala cak na tsayar da kukan da nake da naji muryarta Tana "Naeema bazan iya taimaka Miki ba Shawarar da zan baki shine ki daina Wasa da Sallah ki Kara kusanta kanki ga Allah ki Kai masa kukanki Yana sane dake Yana Kuma ganin duk abinda ke faruwa dake addu'a na iya canza komai ki dage da addu'a Naeema daga ni har mahaifinki ba zamu iya taimaka Miki da komai ba ki dage da addu'a Naeema ki tashi daga baccin nan kije kiyi sallah Naeema ki gayawa Allah komai Yana jinki Kuma zai kawo miki mafita ki tashi Naeema Umma ta fad'a da k'arfi tana cigaba da alwalar da take"


A firgice na tashi daga baccin da nake duk nabi na had'a Gumi k'ofar na kalla Ina Umma tare da wuwurga idona a tsakiyar d'akin Dan gani nake kamar ba mafarki nayi ba kamar dagaske Naga Umma maganarta sai dawomin yake ni ba wani ilimi ba ballantana inyi addua iya fatiha kawai na iya shim wajen Naseer na koya dan Naseer nada ilimi sosai yayi sauka har sau biyu sai da mukayi aure yasan banida ilimin Arabi na bokon ma iya Aji biyu nayi aka cireni daga makaranta Ana ta zuga mahaifina idan nayi karatu zan zama 'yar iska hakane yasa daga na bokon har na islamiyyar banyi ba Sallar ma ba sosai nake maida Hankali nayi ba Kuma hakan bai wani dameni ba sabida bani kadai bace duk yan garinmu da saoi na kusan haka muke rayuwarmu.

Mafarkin danayi da Umma ba karamin tsayamin yayi a Rai ba hakane yasa na mik'e da sauri na shiga bandaki nayi alwala na fito na fara Rama Salolin da banyi ba Dan sallar asuba kawai nayi a rashin ilimina gani nake shi ne ya zama Dole ayi sai Dana auri Naseer yake Dan nusar Dani nasan duk salolli biyar din wajibine sai Naseer na nan ma nakeyi cikakkiyar sallah Idan baya Nan kuwa ba kasafai nakeyin biyar d'in ba Naseer Yana Dab da kawo haske rayuwata mahaifiyarsa ta shigo rayuwarmu ya juyamin baya inasan ganin Mijina inasan muyi magana naji idan Wani Abu nayi masa na nemi yafiyarsa Amma mahaifiyarsa ta kafa ta tsare ta hanani ganinsa


Ina daga Kan sallaya na cigaba da zubar da hawaye
mafarkin da nayi da Umma ya tsayamin a Rai sosai Allah datace na kaiwa kukana na tuna na d'aga hannayena na fara gayawa Allah matsalolina Ina rokonsa ya kawomin agaji ta window labule d'akina nagane dare yayi duk da bansan ko karfe nawa ba a lokacin

Haka kawai naji inasan ganin Naseer a yau d'inan ko ta halin k'ak'a abinda Umma kemin bai min ciwo kamar yanda Naseer ya shareni ya watsar Dani a kwandon shara ko da ba auren soyayya mukayi ba bai Kamata ya watsar Dani haka ba ballantana auren soyayya mukayi Yana Sona Ina Sansa mukayi aure hasali ma duk Wanda yasan mu yasan yafi Sona Amma bansan Mai ya canzamin shi haka ba har yasan akwai cikinsa a jikina ya manta Dani haka bayan duk alkawarin dayamin na zame min uwa da uba tunda iyayena suka mutu yayi alkawarin rik'eni da Amana sanin banida kowa sai Allah Yaya na daya tal danake bi ya tafi makaranta Sojoji har yau bamu Kara Jin labarinsa ba ballantana na saka Rai Yana Raye tun Kan iyayenmu su rasu ake nemansa banida kowa sai Allah sai Naseer Dan haka na taso iya iyayena kawai nasani ba wani wajen muke zuwa ba ballantana nasan danginmu haka ma ba Mai zuwar Mana lokacin banida wayo balle nayi tambayi mahaifina ko mahaifiyata danginsu.

A hankali na mik'e daga Kan sallayar na nufi k'ofa na tsugunna Ina lek'a palon ta Ramin mukullin k'ofata ganin ba kowa a palon fitilun gidan ma a kashe yake yasa nasan dare yayi sosai Dan su Umma basa kwanciya da wuri sai wajen Sha biyu ko dayan dare suna kallo.

Bud'e k'ofar nayi a hankali gabana na fad'uwa addua kawai nake Allah yasa Kar Umma ta kamani cikin sand'a na nufi d'akin Naseer dake can karshen palon gabana Banda fad'uwa babu abinda yake yi Ina zuwa Tsakiyar palon haske ya gauraye palon gabana yayi wani irin tsinkewa na tsaya cak jikina na rawa ko kad'an bansamu k'arfin gwiwar juyawa ba.

"Shegiya tsinananiya Mayya wato ke Mai wayo ko? kina tunanin nayi bacci shine Zaki tafi d'akin Naseer sabida tsabar kwartuwa ce ke Ana dole ne Naeema wlh bazan Kara yarda ki rab'i Naseer ba asirin da iyayenki suka miki kike neman juyar min da Kan d'a na karya asirin lokaci nake jira kawai nayi maganinki

Umma tace Tana juyo Dani a fusace.

Da Sauri na runtse idona a lokacin da muka had'a ido da ita sabida yanda na tsorata da ganin ta Jan doguwar Riga ta saka har kasa ta rambada kwalli gata da manyan idanu hakan yasa na balain tsorata da ita kunnena data Kama da k'arfin tsiya yasa nayi saurin Kai hannuna na dafe hannayenta Dan kamar zata ciremin kunnen ko damuwa batayi da cikin jikina ba ta fara jana da karfi tayi hanyar d'akina sai da muka shiga d'akin ta sakarmin kunnen tare da rankwashina Tana

"Wlh duk ranar da Kika Kara gingin zuwa d'akin Naseer sai na kusa kasheki a gidanan kinyi kad'an ki b'atamin aikina D'ana Yana da arzkiki bana San ya zauna da macen da zata Haifa masa ya ko d'a Sama da daya tunda Kika Haifi Zahira nace ki tafi Kika k'i tafiya ke alailai sai an zauna dake toh wlh tunda Kika min taurin Kai zakigane shayi ruwana idan ma tunaninki idan Kika Haifa masa Yaya Zaki samu lasisin zama dashine toh karyarki taci karya Dan ko na jikin Nan naki wlh baki Isa ki haifeshi ba sai kin tafi D'ana ya auro wata tsalelliyar itama taci rabonta ta tafi banasan in Kara ganin kafarki a waje kiyi zamanki a d'akin Nan duk ranar danaga kafarki a waje wlh sai na b'allaki banza shashasha"

Umma tace Tana Kara dunguremin Kai tayi waje a fusace Tare da bugomin k'ofa


Kuka na fashe dashi Ina Kiran ummana akan tazo ta taimakeni ta tafi Dani nagaji a daren ranar ko kadan bacci bai ga idona ba tunanin rayuwata kawai nake da ace nasan hanyar garinmu wlh da na gudu na koma garinmu gashi ba 'yan uwa ne Dani ba banida kawaye ba Wanda na sani ballantana na Gaya masa halin da nake ciki ya kawomin agaji.



Naseer kuwa a lokacin daya dawo daga wajen aiki a Palo ya tarar da Umma dasu Safiyya sai Mai bi masa Tijjani da shima yayi rashe rashe a palo Yana Kai lomar abinci bakinsa sannu da zuwa suka masa ya amsa
Ya tsugunna gaban mahaifiyarsa ya gaisheta tare da jawo hannun Zahira dayake Jin Santa daban a zuciyarsa wanda hakan nada Nasaba da balain kamar da take da mahaifiyarta rungumeta yayi a jikinsa Yana "Mamana kinci abinci"?

"To da zamu barta da yunwa ne kake wani tambayarta taci abinci nifa bana San irin haka"


Umma tace Tana banka masa harara sauke Zahira yayi ya sunkuyar da Kai Yana "Allah ya baki hakuri"

Ya mik'e Yana satar kallon d'akin Naeema Yana Jin wani iri a zuciyarsa bai San Mai yasa idan zai tuna ta sai yaji kansa kamar ya rab'e gida biyu ba Yana balain kewarta a zuciyarsa Yana balain San ganinta Amma ya rasa Mai ke sa shi Jin wani irin nauyi da d'ad'aurewar jiki

"Ka tafi d'aki kaje ka watsa ruwa kazo kaci abinci"

Umma tace Tana Kara hararsa sabida yanda taga yana satar kallon d'akin Naeema.

Su Safiyya da suka zubawa tv ido yabi da kallo Yana Jin wani irin Mugun Haushin rashin tarbiyya da basu dashi

A tsawace yace musu "Kunyi Sallah kuka zauna Kuna kallo"?

Da Sauri suka mik'e mahaifiyarsu kuaa tace "Ku koma ku zauna ku cigaba da kallonku sabida na tab'a yar gold yake neman hucewa akanku Banda iskanci irin na Naseer har yazo Yana tambayar 'yarsa taci abinci a gabana"


"Umma wlh ba haka bane gani nayi Ana sallar isha suna zaune suna kallo shiyasa nayi musu magana"


"Dalla rufemin baki bazasu tashin ba sai ka bugesu yanda ka Saba bugunsu akan wancan mayyar matar taka"

"Allah ya baki hakuri"

Naseer yace Yana Kara kallon su Safiyya da suka koma suka zauna har da Kara volume din tv shi kuwa ya wuce d'akinsa Yana Jin wani irin d'aci a makogaransa shi Kuma nashi jarrabtar kenan Mahaifiya bai San Mai yasa take masa haka ba har gida ya Kama Mata tak'i yarda ta dage sai ta zauna dashi da kannensa wajen su uku.

Alwala ya daura ya fito ya tafi massallaci bashi ya dawo gidan ba sai wajen takwas da rabi har a lokacin suna zaune suna kallo.

Ko sallamar da yayi ba Wanda ya amsa masa Inda sabo ya Saba hakane yasa ya kinkimi Zahira da ke bacci a kasan carpet ya Kai ta d'aki ya dawo ya d'auki Nadiya itama ya kwantar da ita a gefenta ya dawo palon ya zauna duk da ba yunwa yake ji ba bai isa yace ya koshi ba dan Umma fad'a zata rufeshi dashi kamar zata Kai masa duka.

Yana zama umman ta mik'e ta nufi kitchen da kanta ta d'auko farantin data jera abincinsa a Kai ta ajiye masa yace mata ya gode.

Yana bud'e abincin yaga baki bakin gari a kwance akan farar Shinkafa a hankali ya saka cokali ya fara jujjuyawa Yana mamakin abubuwan da yake yawan gani a abincin da umman ke bashi Amma bai isa ya tambaya Bismillah yayi ya fara cin abincin.

Umma kuwa tayi Tsaki Tana zabga Mai harara taurin Kan Naseer din na balain Bata mamaki.

Yana gama ci ya koma d'aki ya kwanta ya zubawa Zahira Ido Yana kallon ta tamkar itace Naeema sosai yake so ya tuno ta wani Abu na danne shi har karfe goma sha biyu na dare bacci yak'i zuwar masa hakane yasa ya d'aura alwala ya hau Kan sallaya ya tadda sallah Dan tun Yana shekara goma sha biyu ya sauke al qurani Mai girma Naseer nada ilimin addini sosai Wanda duk mahaifinsa Mallam Ibrahim ya gado Dan shahararren mallami ne
Sosai har almajirai ne dashi da yawa har sai daya rasu.


Har karfe biyu Yana Kan Sallaya a zaune Yana Jan carbi maganar da yake juyowa kasa kasa yasa ya mik'e a Hankali ya bud'e k'ofar d'akinsa ya

5 Comments On NAGA TAKAINA
avatar
huda

1 year ago

Reply

Chapter 21

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment