Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawo Mana iskanci shi kuwa Yaya Naseer sai yanda kikayi dashi Kuma wlh ko Dan wanan matar Umma ya Kamata muje mu roki Shugaba muna bukatar mudubin mu ko Dan gudun Kara faruwar Haka yau da ace da Karfin mu a tare damu ai sai dai wata a yau ba ita ba"


Wani irin girgiza Kai Hajara tayi zuciyarta fal cike da mugunta da San d'aukar fansar abinda Murja ta musu

"Sabida abinda yarinya Nan tamin Zan nemi kudin mota naje wajen shugaba ko da Bata maidamin karfina ba inaso a hukunta min ita inaso a makantar min da ita na dawo na zaneta na saka Tijjani ya saketa bayan nayi aiki a kansa Dan Ni nasan bata barshi Haka ba asiri tayi Masa.


Idan zaman Nan din bai yiwu ba sanan muyi tunanin zuwa gidan Naseer.

"Toh Ina zamu samu kudin motar tafiya"?


"Idan Tijjani yazo sai ya Nemo min kudin motar duk Inda ya shiga kuwa wlh idan yak'i bani sai na tsine Masa Dan bashida amfani a wajena tunda har ya iya fifita matarsa akaina ya ringa toshe kunnensa idan na masa maganar matarsa tashi ki lek'a min kiga ko ya dawo Dan bazan Kara kwana a gidan Nan ba"


Safiyya fitowa tayi daga d'akin da kumburarren baki

A Palo ta tarar da Murja tayi hadin kauri ga kwai ta shimfida tana ci tana gyad'a kai sai murmushi take.

Safiyya da kumburarren idonta ta hau hararar Murja.

Murja kuwa ta saki murmushi tana "Wanda ya ja Dani wlh zai Sha wuya dama idan kun samu kudin motar kun taimaka wa kanku Kun siyi abinci Dan duk Inda zakuje ma wahalar da kanku zakuyi ba Abunda zaku iyamin"


Tsaki Safiyya tayi Dan ta d'auka lab'ewa tayi taji abinda suke cewa


A k'ofar gida ta tarar da Tijjani ashe ya dawo Yana zaune Akan benci kusa da kantarsa.

Safiyya tana Isa wajensa ta fashe da kuka Tijjani ya d'ago ya kalleta ganin jikinta duk a kumbure yasa ya mik'e Yana "Ke lafiya Mai ya Sameki Haka"?


Cikin kuka Safiyya ta bashi labarin abinda Murja ta musu.

Ta Kara da cewa "Yanzu Yaya tsakani da Allah Haka zamu cigaba da rayuwa a gidanka matarka na Mana horar yunwa tana dukanmu da anyi magana sai kace Umma ce ta jawo komai Kai baka San tashin hankali har matarka ta saka hannu ta daki Umma toh kaje tana kiranka Dan ta rantse bazata kwana a gidanan ba tafiya zatayi"


"Murjan ce ta daki Umma Akan abinci"?

Tijjani yace cikin mamaki

Bai tsaya ma jiran Mai Safiyya zata ce ba ya shiga gidan

Sai dai me suna Shiga palon Suka ga Murja a kwance a kasa tana ta numfarfashi kayan jikinta duk a yayyage jikinta ya wani kumbure Yana ta kyalli Kamar wacce akayiwa shegen duka

Shigowar Tijjani yasa ta fashe da kuka ta hau mik'a Masa hannu tana "Zo ka taimakeni zasu kasheni"?

Dak'yar.tayi.maganar tana numfarfashi.

Tijjani kuwa ya saki sallati ya karasa wajenta a guje ya d'ago ta cikin tashin hankali Yana duba yanda jikinta ya kumbure.

Safiyya kuwa mamakine ya kasheta a tsaye ta saki baki tana kallon Safiyya

Hajara ma fitowa tayi daga d'akin dataji muryar Murja kamar wacce aka daka.kafin ma ta fito ta hau addua Allah yasa ruwan zafi ne ya kwarowa Murjan.

Amma abinda ta gani ne ya sa ta kasa motsi daga ita har Safiyya kallon Murjan kawai suke suna Jin Mai ke fitowa a bakinta


"Na shiga uku Tijjani mahaifiyarka da kanwarka zasu kasheni kaga yanda suka dakeni suka had'u akaina sukayita jibgata akan sunce na kara musu abin karyawar bazai isa ba

Shine nace musu bredin guda daya ka kawo babu wani shine Ina ajiye musu kayan shayin suka yi ball da shayi da bredin suka tashi Suka rufeni da duka"

Ta karashe tana matsar kwalla"

Tsabar mamakin makircin Murja Safiyya zub'ewa tayi a kasa.

Tana "Yaushe muka dakeki? A yaushe Kika bamu shayi da bredin" kiji tsoron Allah ke Kika dakemu ko mu muka dakeki"?


Tijjani kuwa tuni idonsa ya kad'a yayi ja halin dayaga Murjan ya balain b'ata Masa rai.

Mik'ewa yayi a fusace Yana "A gaskiya na gaji wlh Nagaji Umma Akan me zaa ringa dukan matata akan abinci kuka had'u kuka Mata irin wanan dukan Umma wlh bazan d'auka ba Dan Ni ba Naseer bane ku barni Mana inji da masifar da nake ciki akan me zaa zo a Kara min wani a ringa dagawa iyalina hankali ahaka kuka sako matar Naseer agaba yanzu Kun bar kanta Kun dawo Kan matata toh a gaskiya bazan yarda ba na gaji Umma ki koma gidan Naseer kawai kasheta kuke so kuyi akan abinci?kunsan da yanda nake Samun ma abinci"?

"Ke Kuma Dan uwarki har wuyanki yayi kaurin da Zaki kawo hannu jikin matata Sa'oinki suna can daga Mai yaya bakwai sai takwas ke kinzo Nan Zaki daga min hankali maza ki shiga daki ki kwaso kayanki Kar na sake ganin kafarki a gidan Nan"


Kuka Safiyya ta fashe dashi tana "Wlh Tallahi yaya karya take Mana Ita ta dakemu fa daga Umma ta Shiga kitchen dinta ta d'auko bredi zata ci shine ta hau Umma da duka na fito Zan ceceta ta had'a Dani haba Yaya Kar San matarka ya rufe maka Ido ka kasa Gane sharri take Mana ka kalli fuskata ka kalli fuskar Umma mu zamu daketa mu Kuma daki kanmu"

"Wayyo Allah kaina wayyo Allah bayana"


Kawai Murja ke cewa tana matsa kwalla Tijjani kuwa hakan ba karamin Kara Masa Haushin Hajara da Safiyya take ba.

Bakin cikin sharrin da ta musu yasa Safiyya ta fara kuka

Hajara da wani irin Abu ya tokare Mata wuya Tama kasa magana sabida sharri da.makircin da Murja ta had'a musu Tijjani ko bincike Bai tsaya Yi ba ya hau Kai ya zauna Yana fadar duk maganar data fito daga bakinsa.


"bani kudin mota na bar maka gidanka a yau Tijjani yau Akan mace ka rufe Ido kake gayamin bakaken maganganu matarka ta daki nida kanwarka ta Kara hada Mana sharri ka goyi bayanta ka k'i bincike kaji daga bakinmu.

Tun aurenku da ita ban saka albarka ba nace maka Bata min ba sabida ba matuniyar arziki bace kak'i ji a karshe ta ringa Mana horon yunwa sabida na Shiga kitchen na dau bredi ta rufeni da duka kazo ta Mana sharri ka yarda da maganarta.

Tijjani a yau Ina umartarka da ka saketa saki uku ko na maka baki"

Tijjani kallon Hajara kawai yake cikin mamaki Yana "Da tamin me Zan saketa Umma kawai Dan matata ba ta kwanta Miki ba sai ki dage na saketa yanzu idan na saketa ke Zaki Nemo min wacce Zan aura wai.mai yasa bakida burin daya wuce ku watsa rayuwarmu ne ki hanamu sukuni da zaman lafiya Umma karki manta fa akwai hakkinmu akanki Haka zalika hakkinki akanmu Umma bakida burin daya wuce ki cutar damu muna yayanki Haka kika Sako Naseer a gaba sai da Kika Hana shi sukuni Umma yanzu Nima din baki kyalleni ba sai kin rabani da matata toh a gaskiya bazan iya rabuwa da ita ba Dan babu abinda tamin matsayinki daban matsayinta daban"


"Au Haka kace ko toh shikenan gata Nan na sallama Mata Kai Tijjani daga Yau Murja ta zame.maka uwa karka Kara doso.inda nake tunda ka k'i bin umarnina sai ka tagayyara ka wulakanta Sai wanan tsinaniyar matar ta zama ajalinka"

"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Allahuma ajirni fi musibati wa aklifnin khairin minha Umma yanzu akan naki rabuwa da matata kikemin baki Haka"?

Hajara Bata kulashi ba ta koma daki ta d'auko buhun Kayanta Ta fito tayi waje.

Safiyya itama ta mik'e ta shiga d'akin ta d'auko Kayanta tabi bayanta.

Tijjani kuwa tsananin mamakin kalmomin Umma ya hanata motsawa.


Murja kuwa cikin makirci tabi bayansu tana "Umma Dan Allah kiyi hakuri ki dawo ya sakeni.

Tana Isa Dab dasu ta Sha gabansu ta saki murmushi tana "Kar na sake na Kara ganin kafarku a gidana duk Wanda ya ja Dani wuya zai Sha Dan Baku San wacece ni ba Kuma danki auren zobe mukayi mutuwa ce zata rabamu karki wahalar da kanku wajen yimin wani Abu Dan Babu abinda zai sameni.

Daga Haka ta matsa daga gabansu ta sakar musu murmushi fitowar Tijjani yasa ta zub'e a kasa da Sauri ta rik'e kafar Hajaran tana "Umma Dan Allah kiyi hakuri ki koma Zan saka ya sakeni."


Tsabar bakin ciki Hajara kasa magana tayi har Tijjani ya karaso wajensu.

Ya mik'awa Safiyya kudi
Safiyya ta d'auke kanta ya daka Mata tsawa kamar zai Kai Mata duka tayi saurin juyowa ta karbi kudin

Shi kuwa Tijjani yace "Allah ya kiyaye hanya Umma idan kin huce zamuzo"


Daga Haka ya juya ya koma ciki.

Murja kuwa ta musu gwallo ta bi bayansa.

Daga Hajara har Safiyya ba Wanda ya iya magana har Suka Isa Tasha suka hau mota.

Sai da motarsu ta d'au hanya Hajara ta rufe fuskarta ta fara kukan bakin cikin abinda Murja ta musu yanda take Jin zuciyarta da zata samu wuka daga Murja har Tijjani zata iya kashe su.

Sai a yanzu ta Gane Naseer Dan halak ne Yana kuma Mata biyayya Naeema ce dai data tsana yak'asa bin Umarninta Karo na farko da tayi Nadamar abinda tayiwa Naseer.

Naeema ta tsana ba Naseer ba da ta sani tun farko Naeema tasan yanda akayi ta kau da ita duk da Naeema duk abinda take tayi dan ta cimma burinta ta kasa samun Galaba a kanta Bata San Mai yasa yaran nata maza suke k'in Mata biyayya Akan matansu ba.

Tuna Naseer da Naeema ya Kara taso Mata da tsanar Naeema da take ganin ita ce silar dayasa idonta ya rufe tayiwa Naseer abinda tayi Masa.

A yanzu Kuma ba wacce take San ganin ta aikata barzahu sama da Murja da take Jin kowacce fitar numfashinta da tsanarta take fita.

Bata da burin daya wuce ta Isa Calabar.


Tsabar b'acin Rai ma neman yunwar tayi ta Rasa.

A lokacin da suka Isa Calabar sanin babu Inda zasu sauka yasa Suka nufi gidan Lami.


Lami Bata ma iya musu magana ba sabida yanda suka had'e rai.

Bata San da zuwansu ba Amma abincin data girka Haka ta juye ta kawo musu

Daga Safiyya har Hajaran Loma kawai suke kaiwa bakinsu har suna neman fada akan abincin.

Sai da suka nutsu Lami ta hau tambayarsu abinda ya faru tagansu Haka.

Cikin bakincki Hajara ta hau Bata labari tana cin alwashin irin Abubuwan da zatayi wa Murja Naeema da Tijjani.


Safiyya kuwa cewa take Banda dai Tijjani tunda nasu ne Kuma ita tasan bayin kansa bane.

Lami girgiza kanta tayi tana "Umma a gaskiya shawarar da Zan baki shine ki hakura ki koma ga Allah Ni yanzu nasan asiri da tsafi duk karyace Umma a sanadin tsafi Umma bayana ya koma haka Umma shekara nawa muna had'awa Naeema abubuwa tana tsallakewa kin taba tunanin da wa Naeema ta dogara take neman fin karfinmu nidai Umma Dan Allah ki hakura ki dawo hanya"


"Kimin shiru Lami zan sauke fushina akanki idan bazaki tayani ba karki soma hanani"

Ta Inda Hajara take Shiga Bata nan take fita ba.

Lami kuwa d'akin ta baro musu tana musu adduar Shiriya

Karfe Sha biyu Hajara da Safiyya suka nausa daji.

Duk yaren tsafin da suka ringayi Shugaba bata bayyana gabansu ba .

Sai da suka Sha bak'ar tafiya ko tsoro basaji suka iso wani wawaken waje Mai dauke da wani gini a tsakiya shi kadai wanda na shugabarsun ce.

Suna Isa wajen suka ganta a zaune ta daura Jan zani Ido ta zuba musu har suka zube a gabanta.

Hajara kuwa cikin kuka ta hau rokonta ta yafe Mata ta maido Mata mudubinta ta tuba bazata Kara ba tana San daukar fansar abinda Murja ta Mata.

Sai data Gama tsaf

Shugabarsu ta jawo wani katon mudubi Mai dauke da wani irin zanne ja

Tayi surutai ta ajiye a gaban Hajaran da Safiyya.

Sai ga wata Mata ta Bayyana sanye da bakakken Kaya Fuskarta gwanin ban tsoro.


"Wannan itace mahaifiyar Murja ko ni ban Isa Naja da ita ba Dan Haka ki bar zancenta Dan idan ta gano daga ke har Ni sai ta kashemu idan kina da wani Abun ki fada kawai Banda wanan"


"Yanzu Bazan iya d'aukar fansar abinda Murja tamin ba kenan mahaifiyarta sabida babba ce itama a kungiya Mai zaman kanta"?

"Abinda nake nufi kenan"

Hajara tsabar bakin ciki kuka ta fashe dashi sai data gaji dan kanta tace


"Dan Allah ku maidamin karfina Shugaba Ina bukatarsa"

"Bazai yiwu ba Abu daya Zan Miki karbi Nan.

Duk Inda kike idan Kika turara Zan bayyana ki fadamin abinda kikeso"

Sai a lokacin Hajara ta Dan ji sanyi a ranta

"Dan Allah inaso a dubamin Inda Naseer yake yanzu shida matarsa Naeema"

Wani Abu ta watsa Akan mudubin sai ga Naseer ya bayyana a cikin mudubin Yana zaune a benci a k'ofar wani katon gida ya zurawa waje daya Ido ya rame sosai Kamar bashi ba rigar jikinsa har ta Masa yawa"

"Ga danki nan ya zama driver a garin Abuja Yana neman kudin da zai dawo wajen iyalinsa.

Matarsa ita Kuma tana Nan a gidansa na gadon Kaya tana d'auke da ciki har ya tsufa"


Shugabarsu ta hau kwararawa Hajara bayanin komai

"Wanan yarinya anyi shegiya tana so ta kashemin d'a da Ransa in Banda balai suna cikin wanan matsin zata Kara k'unsar wani cikin ba Dole ya gudu ba Amma ba komai nasan abinda zanyi ngd Shugaba idan Ina bukatar taimakon Zan turara"


Suna k'ok'arin mik'ewa Safiyya tayi caraf tace "Shugaba inasan nayi aure sai dai babu mijin aure ba Wanda ya tab'a cewa Yana Sona ga Lami har tayi aure cikine da ita"

"Karbi kwallin Nan duk wanda Kika gani kikaji ya kwanta Miki a Rai ki saka kwallin wuyanta ku hada Ido.

Da tsananin farinciki suka dawo

Duk da kasan ran Hajara ba Haka taso ba taso ko Yaya ne taci Galaba Akan Murja.


A takaice kwanansu Uku suka shirya tsaf suka karbi kudi a wajen Lami suka dau hanyar kano.


Naeema

Sosai Nake samun bud'i ta sanadin siyar da Zobo da ruwa.

Zuwa yanzu Zan iya cewa idan akwai abinda yake damuna Bai wuce rashin Naseer ba har adashe na Shiga Ina tara kudi sabida cikin da nake d'auke dashi sosai nake adduar Allah yasa Kafin na haihu Naseer ya dawo inaso na ya dawo kafin ya haihu.

Cincin din danake Yi da Dankali da yamma shima ba karamin cinikinsa nake ba ahaka na Kara Tara kudi na siyi engine markade danaga layin namu babu masu engine markaden sai an fita titi.

Ba karamin ciniki nake ba da Wanan engine Dan Nadeeya da Zahira indai suna Nan ba islamiya haka zasuyi ta markaden ganin Ina samun kudi ko ta Ina yasa na fara gyara gidan namu Dan dakuna biyu ne kawai gyararru siminti nada araha a lokacin hakane yasa na siya wajen goma aka fara Mana plaster banida burin daya wuce na gyara gidan idan Naseer ya dawo yaji dadi a Ransa.

Kamar Wasa sai gashi nice har da pentin gidan gabadaya daga engine markade daya sai gashi na Kara ya zama guda biyu

Kayan abinci kuwa sai dai Nima na bawa wani Mai bukatar.


Yanzu da muka samu kwanciyar hankali banida burin daya wuce ganin mijina ko nasan halin da yake ciki har makarantar islamiyya su Zahira nake zuwa da waina na roki mallamin ya rabawa almajirai ya Tayani da Addu'a Akan Allah ya dawo min da mijina lafiya.


A Haka watarana daddare wajen karfe Takwas na iddar da sallah ishai Zahira tana tsakar gida tana markade.

Su Nadeeya Kuma suna tsakiyar palon Dana sakawa Leda suna home work dinsu


Ni Kuma Ina daga d'akina.

Haka kawai naji gabana ya yanke ya Fadi na ba gaira ba dalili hakane yasa carbina rik'e a hannuna na turo cikina na fito na tsaya a bakin kofa Ina kallon su Nadeeya jefi jefi Kuma Ina kallo tsakar gidan Sabida k'ofar Palon a bud'e yake Zahira na tsaye tana ta markaden

Banko k'ofar Gidan da akayi da k'arfi ne yasa na kalli k'ofar da Sauri gabana yayi wani irin fad'uwa dana hango Umma ta shigo Safiyya na biye da ita abaya.

Zahira kuwa Tana ganin ta ta saki robar hannunta ta kwaso aguje ta shigo palon ta buya abayana jikinta na rawa.

Umma da Safiyya kuwa a tsakiyar gidan Suka tsaya suna karewa koina kallo.

Ni kuwa sallati kawai nake jikina na rawa.........


*Nagode da kauna Allah ya saka da alheri ya bar zumunci Ina mutukar Kaunar Mai kaunata Fatima salis da Umma misbah Allah ya biya muku bukatanku na alheri Allah ya bar zumunci ga masu neman lambata ido rufe ga lambata Nan Mata kawai pls 08033719070*
[6/26, 6:13 PM] +234 706 571 7620: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*


*Page 28*

Ban kawo Zan siyar da duka kosan ba sai gashi kafin Tara na siyar gabadaya har Ana Kara tsayawa a tambaya ko da akwai.

Zahira sai washe baki take tana murna cinikin da mukayi.

zazzabin daya rufeni da k'arfi yasa na dauki gwangwnanin kudin na bawa Zahira umarnin ta kashe itacen ta shigo da komai.

Daki na shige na kwanta na rufe kaina.

Dan Sosai Nake Jin wani irin Sanyi

Bansan Mai yasa wanan cikin yazomin a Haka ba Dan ban fiye laulayi ba iyakacina zazzabin dare Ina tashi Kuma shikenan Amma wanan kuwa amai da zazzabi nake wuni har dan yawu nake yi Wanda duk cikin da nayi ban taba yinsu ba.

Zahira kosan Dana zuba musu a flask ta juye musu a faranti ta had'a musu da ruwan Lipton suka Sha sai da suka Gama gyara gidan ta shigo d'akina tana min Sannu.

Dan ta San banida lafiya
Kosan da ta rage ta zubomin har da tea tana "Umma ki daure kici abinci sai ki Sha magani"

Ganin duk ta damu yasa na mik'e da kyar na Kai kosai bakina sai dai ko uku banci ba na fara kwara amai.

Sai Dana Gama nasa ta d'auko min pcm na Sha da ruwan shayin na koma na kwanta Nan da Nan bacci ya d'aukeni

Zahira kuwa Bata tsaya jirana ba dayake ta Dan iya girkin ta kirba musu jollof din shinkafa a kula jifa jifa Kuma tana lek'o Ni taga ko na tashi.

Bani na tashi ba sai wajen karfe daya na Shiga bandaki nayi wanka Dan na d'an ji kwarin jikina nayi Sallah na fito na tarar da Zahira da kannenta da tsofaffin littafinsu Wai Nan gwaji take basu itace mallamarsu


Sai tausayinsu ya rufeni nasan suna San komawa makaranta Babu yanda zasuyi ne.

Suna ganina Suka hau min Sannu na musu murmushi na zauna Ina ganin rubutun da suke.

Wa zai ce yarana sunyi makaranta.mafi tsada a gadon Kaya da sharada Amma ji yanda duniya ta juya damu ko makaranta gwamnatin ma sun kasa zuwa sabida babu

ko wane Gari Naseer yaje ko ya yake rayuwa yanzu dan nasan ko a Ina yake Yana can ne zuciyarsa na Nan.

Gwangwanin kudin nasa zahira ta d'auko min na fito da kudin ciki na kirga kudin abinda na kashe na ware na kirga ribar da shima ba laifi mun samu.

Kudin na Kara Bata ta siyomin komai na kosan gobe na saka ribar a gwangwani Dan inaso ko yayane na nema musu makaranta yaran nawa girma suke Kara yi

Sai dai Mai washegari kasa tashi nayi Sabida azabar zazzabi jikina kamar garwashin wuta amai kawai nake Ina Jin jiri

Kosan da ban iya fita na soya ba kenan har cikin gidan aka ringa kwada Sallama Ana nema.

Kafin ma Rana tayi jikina yayi wani irin laushi ko kaina bana iya dagawa na bud'e baki ma na yiwa Zahira magana na kasa.

Ina dai kallonta ta Dan gyara gidan tayi musu abinci suka ci.

Ta dawo gefena tana min Sannu hannun data kawo jikina taji da zafi yasa ta mik'e ta fita.

Bata fi minti ashirin da fita ba ta dawo tana "Umma ki tashi muje asibiti jikinki yyi zafi da yawa na Kira Mai taxi"

Gwallo Ido nayi Ina kallonta Taya zanje asibiti banida kudi canjin wajena da ribar Bai fi Dubu da dari biyu ba Kuma shima banaso na tab'a.

Bansan ya akayi tasan yawu ne a bakina ba ta nemi gwangwanin Madara ta kawomin tare da dago kaina na zuba yawun a ciki Ina "Zahira sabida mai yasa Zaki Kira Mai mota banida kudin zuwa asibtii fa ki barni na Sha magani Zan warke"

"Aaa Umma gwara muje asibitin bakida lafiya sosai gwara likita ya dubaki Dan Allah ki tashi muje"

Ba yanda zanyi Haka na mike tana rik'e Dani na zura hijabi muka fito ta d'auko kudi a cikin gwangwanin muka fito waje ta cewa Nadeeya ta rufe gidan Kar ta bud'ewa kowa har sai mun dawo

Muna zuwa asibitin daga su dubani suka bani gado sabida jikina ba kwari Ina Kuma bukatar Karin ruwa.

Abu kamar Wasa sai gashi kamar zuwa na asibitine yasa jikina ya Kara rikicewa.


Duk kudin da ke ajiye a gida sai gashi duk ya kare.

Zahira ke Tayani kwana ta roki makotana akan su Nadeeya zasu ringa kwana a wajensu.

Kwana na hudu a asibiti na Dan ji sauki.

Ahaka aka sallameni muka dawo gida.

Kayan hadin kosan kuwa tuni Zahira ta girke Dan abincin da mmn Mannir ta bamu ba wani yawa ne dashi can can ba tsitsinta Mana tayi.


Ganin babu kudi Kuma bbu kayan abinci yasa na fara neman yin wani rashin lafiya abinda muke dashi Bai wuce Kofi hudu na shinkafa ba sai dari da ashirin ni nasan badan rashin lafiyar Nan da nayi ba da Kila na Dan samu kudin ta silar siyar da kosai

Inaji Ina gani duk burin Dana ci na juya kudin Nan ya Kare a hannuna.

A ranar na kasa bacci Ina tunanin Kuma abin yi dan da kunya na Kara komawa gidan mmn Mannir to daga Ina Zan fara.


Washegari sauran abincin Zahira ta dafe musu.

Ni kuwa na rik'e dari da ashirin a hannuna Ina juyawa.

Har d'akin Zahira ta shigo ta zauna a gefena tana "Umma ya baki Fito ba ko jikin naki ne"?

"Zahira ba jikina bane Ina tunanin Inda Zan samu kudi na Kara siyo kayan yin kosai Zahira bamuda komai a gidanan abincin daya yi saura Kika dafa muku yanzu anjima daddare Mai Zakuci babu abinda ya rage mana sai dari da ashirin din hannuna shiyasa ranan nace Miki bazanje asibiti ba Yanzu Ina zanje na samo Mana abinci daga Ina Zan fara mutane sun gaji ma da taimaka min"


Kamar wata babba na hau yiwa Zahira maganganu Ina kuka

Itama kuwa ta hau kukan ta kawo hannunta ta karbi kudin hannuna tana "Umma wannan ma zai isa muyi wani Abun ki kawo kigani"

Bata Bari nayi magana ba ta fita da hamsin tare da ajiyemin sabain.


Ina zaune a daki Naga ta shigo da farin Leda irin na kulla kankara.

Ta Shiga kitchen ta d'auko Kular ruwan Sanyi mu ta wanke sosai.

Sai a lokacin nace "Wai Mai zakiyi ne Zahira"?

Murmushi tamin ta dauki bokiti Mai kyau ta taro ruwa Dan muna da pampo a gidanmu Mai dadi kuma.

Ina kallonta Naga ta dauki farin ledar ta fara diban ruwan Tana zubawa a Leda tare da kulawa.

Nidai kallonta kawai nake Ina mamaki Dan Ni nasan bamuda freezer ballantana nace so take mu fara siyar da kankara.

Tana gamawa ta rufe ta Kara fita Bata Jima da fita ba sai gashi ta dawo da kankara manya guda biyu ta faffasa ta zuba tana "Umma naira biyar biyar ake siyar da ruwan Sanyi a bakin titi Ana ciniki sosai anjima zanje na siyar zamu samu kudin da zamu ci abinci"


"Aaa Zahira bazan Bari kiyi talla ba Ni da kaina zanje indai kinsan Ana siya"

"Umma bakida lafiya fa ki Bari naje Zan iya wlh"

Kare Mata kallo nayi Zahira duk doguwa ce sosai fara gashi ta ma Dan fara kirgan dangi bazan iya Bari ta tafi talla ba mutane basu da Amana Kar su yaudare min ita.

"Na warke Zahira Bari ayi sallah naje ganin tana San sake Musa min yasa na hade Rai baa San ranta ba ta fice daga d'akin

Cikin Dana samu na yawan Sakani Jin bacci ko Yaya naji iska ya kadani bansan sanda bacci ya d'aukeni ba.


Sai wajen biyar na mike a firgice tare da yin palo da Sauri.

Nadeeya da kanenta ke wasan Yar baby


Da Sauri nacewa Nadeeya Ina Zahira

Sai tacemin ai tundazu ta fita da kula a kanta.

Banji dadi ba Dan har ga Allah Ni naso zuwa.

Daki na fad'a da Sauri
Na daura

5 Comments On NAGA TAKAINA
avatar
huda

1 year ago

Reply

Chapter 21

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment