Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sabida tsabar maita toh gashi dai kin janyowa Yaya Naseer tsinuwa agurin Umma Akanki Yaya Naseer ya wankawa Umma Mari na tsaneki Naeema na balain tsanarki shegiya tsinaniya"

Daga Haka ta wancakalar da ni ta kalli Umma tana "Umma kalamanki sunyi tsauri Akan yaya Naseer ki janye Sabida muma sai ya shafemu karki manta Yaya Naseer shine cinmu shine shanmu komai namu shine yaya Tijjani ma arzikinsa yake ci tayaya sabida wata jakar Naeema zaki zuciya ki Masa baki Haka Umma"?


Wani irin kallo Umma ta yiwa Safiyya cikin wani irin murya tace "na gwammace nayi yawo tsirara nayi bara naci na Sha da na janye kalamai na Badai kudi Naseer ke takama dashi ba Badai Dan kudi Naeema ta makale Masa Taki rabuwa dashi ba har Ni yau Dan Dana Haifa ya daga hannunsa ya mareni ya Kuma k'i bin umarnina Wlh Naseer Bai ga komai ba ke kuma"

Umma tace tana Nuno da hannu "Badai ke Naseer ya zaba akaina ba zaki gani Badai kina da Yaya ba Zaki gani"


Daga Haka ta wuceni fuuu Safiyya tabi bayanta Ni kuwa na fashe da wani irin kuka Ina sallati.

Ina kallo Suka tari abin Hawa Suka tafi kukan danake a zaune dirshan a kasa yasa aka fara Dan taruwa Ana kallona hakane yasa na mik'e dak'yar na nufi gida Ina Jin jiri.

A yanda na fito Na bar Naseer ahaka na taddashi

Kuka yake kawai Yana "Umma ki.yafeni wlh bada niyya na mareki ba bansan ya akayi na d'aga hannu na Mari Mahaifiyata ba Wanan wane irin kaddara da mumunnan Rana ne Umma Mai na Miki da zafi da Zaki min irin wanan kalaman Umma nifa danki ne Dan Allah ki yafemin.

Yarana kuwa curewa kawai sukayi waje daya suna kuka.

Tashin hankalin danake ciki Bai saka nabi ta kansu ba ba abinda ke yawo a kunnena sama da kalmomin Umma masu nauyin gaske ga Naseer.

Haushin Naseer ne ya danne tausayinsa a Zuciyata

Cikin kuka na fara magana Ina "Haba Naseer idan rai ya bace ai hankali ke Nemo shi Naseer kasan girman uwa kuwa tayaya zaka Mari Umma?tayaya zata baka umarni ka k'i bi kana Jin irin kalmomin da take jifanka dasu fa haba Naseer Ina iliminka da tunaninka suka tafi Taya zaka dage sai ka zauna Dani yanzu idan na mutu zaka iya Bina ne?kana da damar da zaka sake aure bakada damar da zaka sake uwa Naseer ka mike yanzu tun lokaci Bai Kure ba kabi bayan Umma kaje ka nemi yafiyarta ka rubuta takarda sakina agabanta sabida taji dadi kamin saki daya ko biyu sai mu cigaba da Addu'a kila a gaba sai mu maida aurenmu.


"Naeema Umma tayi fushi Dani sosai bazata saurareni ba zuwana yanzu na iya sawa ta hau ta cigaba da min kalamai marasa dadi naso bin Umarninta Amma bakina yak'i bani hadin Kai jinayi bakina yamin nauyi na kasa bud'e na furta Miki kalmar saki Wlh da hankalina da tunanina Naeema bazan daga hannu na Mari Umma ba bansan.mai ya hau kaina ba burina kawai lokacin na Hana Umma ta kasheki burina kawai lokacin na tseratar da ita daga Halaka kar ta d'au nauyin kissan Kai a yanda na taho so kawai nake na ceceki ba wai na Mareta ba bansan Mai ya sameni ba da ilimina na aikata irin wanan danyen aikin ya Allah ka yafemin ka sauko da zuciyar Mahaifiyata innalillahi wa Inna ilaihi rajiun"


Yanzu ma Bai b'aci ba Naseer kaje ka Bata hakuri burinta kawai ka sakeni ka Kai mata takarda sakina ni nasan zata yafe maka"


"Bazan iya hada Ido da Umma ba tunda na Mata ba daidai ba na kasa hada Ido da ita Naeema ki kyalleni naji da ciwon dana keji a kirjina da asuba zanje zuwa lokacin nasan kila ta sauko Kuma Zan bi umarninta tunda Haka take so"


A Ranar daga Ni har Naseer bamu runtsa ba sosai Naga tashin hankali a tare da Naseer Duk jarumtarsa ranar haka ya zama kamar mace Haka nayita bashi baki.


Haka nayita bashi magani sabida zazzabin dake ta rufeshi.

Washegari da asuba Naseer ya nufi goron dutse duk a hargitse Dan sallar ma ba a nutse yayi ba.


Turus yayi a lokacin da yaga gidan a kulle da kwado sosai yaji hankalinsa ya tashi yayi zaman dirshan a k'ofar Gidan lailai ba karamin fushi Umma tayi dashi ba yanzu ya zaiyi"


Yana zaune a wajen su Lukman suka fito suka hau gaishe shi suna tambayarsa dafatan lafiya Dan kana ganinsa kasan baa hayyacinsa yake ba


"Bai iya musu magana ba Dan ji yayi idan zaiyi magana zai iya fashewa da kuka hannu Lukman din ya saka a Aljihu ya dauko mukullin gidan ya mik'awa Naseer Yana gashi Hajiya ce ta bani jiya Akan na baka idan ka dawo sun koma garinsu jiya daddare inata ma hanasu tafiyar Taki saurarata.


A zuciya Naseer ke nanata innalillahi wa Inna ilaihi rajiun.

Bai ma ji Mai Lukman ke cewa ba ahaka ya mik'e ya hau taxi ya dawo gida.

Ni kuwa tunda Naseer ya fita massallaci Ina iddar da sallah na dawo Palo na zauna na buga tagumi Ina ta tunanin abinyi hankalina gabadaya na wajen Naseer ko ya zasu Kare da Umma tunanin hada kayana Dana yarana ne ya fad'omin Dan Naseer na dawowa Zan tafi garinmu bazan Kara Sakan daya ba
su Zahira ma a ranar da suka gani a zaune basu min zancen na shiryasu su tafi makaranta ba suma duk jikinsu ba kwari Haka suka tashi daidai da Humaira karamar yarinya ma kamar tasan Mai ke faruwa Haka tayi lamo da ita.

Wajen bakwai da rabbi Naseer ya dawo duk a firgice mik'ewa nayi da Sauri na tare shi Amma sai ya matsar Dani gefe ya shige daki.

Ahaka na bi bayansa Inda Yana shiga daki kwanciya yayi ya fara hawaye nayita tambayarsa Mai ya faru yak'i kulani.


Hasali ma da yaga na dameshi da tambaya sai ya daka min tsawa akan na fita na bashi waje yaji da Abunda ke damunsa

Haka na fito daga d'akin Nima Ina hawayen Inna zuwaira Bata Nan balle nace ta dafawa su Zahira abinci jiya bansan ya akayi ma ta bar gidan ba ahaka na daure na Shiga kitchen na Dora musu ruwan tea Yana tafasa na juye a flask na hada musu tea na ajiye musu bredi na koma Kan kujera na zauna sosai naji Haushin abinda Naseer yamin Naga dai duk shi ya jawo Mana wannan tashin hankalin da yabi umarnin Umma da duk Haka Bai kasance ba ina Jin ciwon tsanar da umma tamin na ba gaira ba dalili na rasa Mai nayiwa Umma a rayuwata k'arfi da yaji take so ta tasheni daga Kan yayana.

Haka nayita zubar hawaye sama da awa biyu sai dana gaji Dan kaina kafin na mik'e na Kara komawa d'akin Dan so nake Naseer ya gayamin yanda sukayi da Umma ya bani takarda ta na tafi Dan indai ya sakeni bazan zauna ba tafiya zanyi tsinuwar da Umma tayiwa Naseer sosai ya tsayamin a zuciya tsinuwar kawai idan na tuna sai gabana ya tsinke ya fadi sosai duk kalmomin suka tsayamin a Rai suke razanani"


Rawar Darin da Naseer keyi yasa nashiga d'akin da gudu Ina tab'a shi naji jikinsa zafi zau.


Ahaka na kwasa nayi waje na Nemo Mai taxi ya shigo ya Tayani kinkiman Naseer mukayi asibiti bayan na Kai su Zahira gidan mak'ota a takaice sai da Naseer yayi sati a asibiti Inda aka ce jininsa ne yayi balain Hawa sabida damuwar daya saka a ransa.


Sai da aka sallamo mu da kwana biyu yake bani labari su Umma sun koma Calabar Wanda hakan na nuni da Umma ba karamin fushi yayi ba shi Marin daya matane inya tuna yake daga Masa Hankali.

Shawara na bashi akan yabi bayanta zuwa Calabar ya nemi Mallam Musbahu ya raka shi su bawa Umma baki ya Kuma tabbata da ya sakeni sabida Taji dadi idan na furta kalmar saki Ina ganin wani irin tashin hankali a idon Naseer Amma ahaka yake daurewa.

Sai da jikinsa ya Kara kwari kafin ya shirya tafiya Calabar tunda abinan ya faru bana iya cikakken bacci idan bacci ya d'aukeni haka nake mafarkai marasa Kan gado masu firgitarwa nayita ganin Naseer a mumunan yanayi idan na farka sai na danganta Haka da tsinuwar da Umma tayiwa Naseer na saka a Raina dayawa hakane yasa nake mafarki da Naseer.

Sosai na sake zage damtse wajen kaiwa Allah kukana Ina Addua Allah yasa Kar bakin umma yayi tasiri akan sa Dan nasan duk a dalilin yak'i sakina tayi Masa wanan bakin uwa Kan sadaukar da farincikinta sabida yaranta Akan Umma na fara ganin uwa Mai San danta ya wulakanta ya tozarta har da su kudi sai ya Masa wahalar samu sai dai ya gani a hannun wasu Mai yayi zafi haka.

A ranar da Naseer ya tafi a Haka nayi jigum Kamar Mara lafiya ba lokacin da ake da yawaitar waya bane ballantana na kirashi naji ya sukayi.


Naseer kuwa addua d'auke a bakinsa Akan Allah ya sauko da zuciyarta ta yafe masa ya Isa gidan Hajara a lokacin da ya sauka a Calabar

Sai dai me Yana zuwa gidan yagan shi a kulle Wanda hakan ya haddasa Masa fad'uwar gaba sai daya tambayi mak'ota akace Masa ai sunce sunyi tafiya sai an kwana biyu zasu dawo.

Sosai hankalin Naseer ya tashi Dan yaga alamar Umma ta d'au zafi gashi Bai San ta Ina zai soma nemota ba har tsohon gidanta yaje shima a kulle jiki ba kwari a Haka ya nufi gidan Mallam Musbahu shima sai ce Masa akayi sun bar Calabar sun koma garinsu Dan Dama kasuwanci ne ya kawo Mallam Musbahu sosai Naseer Yaji baiji dadin abinda ya faru ba duk Inda yake tunanin zai ga mahaifiyarsa ya nemi yafiyarta ya samu nutsuwar zuciya ya nema Bai sameta ba yasan Umma tasan zai zo neman yafiyarta shine ta nisanceshi ahaka yayi kwana biyu a Calabar kafin ya juyo ya dawo.


A takaice zuwan Calabar biyar Yana dawowa Bai samu ganin Umma ba Akan dole ya hakura da nemanta muka dage da Addu'a Akan Allah ya sauko da zuciyarta daga fushin data hau.

Addua Naseer keyi sosai ba dare ba Rana Akan Allah yasa Kar bakin data Masa ya bishi.

Duk Wanda yasan Naseer a baya idan ya ganshi tunani zaiyi shekara yayi Yana jinya sabida damuwar daya saka a ransa sai nice ma nake Dan kwantar Masa da hankali sosai yake nadamar k'in bin umarni Umma Dan tunda ta tafi ya rasa nutsuwar zuciya.

Ni kuwa kullum cikin addua nake da sadaka Dan sadaka maganin masifa ce idan wani abune ma zai Same mu Allah ya kawo Mana da sauki.

Mafarkan danake na d'aga min hankali Amma bantaba gayawa Naseer ba.

Naseer kuwa har tausayinsa nakeji nayita kuka a boye.

A cikin wanan yanayin Allah ya saukeni lafiya na Kara haifar mace sosai naso ace namiji na Haifa amma Ina ganinta naji kaunarta ya rufeni.

Addua na Mata Naseer shima kadaran kadahan Bai nuna komai ba ya saka Mata Raheema yamin komai kamar yanda ya saba na kyautata wa.

A Haka rayuwa ta cigaba da tafiyar Mana tun muna dari dari daga Ni har Naseer har muka zo muka saki jiki.

Naseer kuwa sai Kara samun budi yake duk da Yana Dan samun sarari Yana zuwa Calabar Amma har lokacin baya ganin Hajara.

Ahaka akayi shekara biyu babu abinda ya faru sai a lokacin Hankalina ya fara kwanciya sai na danganta yawan mafarkin danake da kila dan na Saka abinda ya faru tsakanin Naseer da umman ne a Raina.

Shima Naseer zuwa Lokacin ya Dan saki jikinsa duk da abin na Fado Masa a Rai Kuma Yana addua sosai

Sai watarana ran Monday bazan tab'a mantawa ba Na shirya su Minal Dan lokacin Zahira na iya yiwa kanta komai ita da Nadeeya tana da shekara goma lokacin Nadeeya nada takwas da watani Zahira na primary 3 a lokacin Nadeeya na primary one Minal da Humaira Kuma suma nursery section Raheema ce kawai Bata fara makaranta ba


Naseer ne ya shirya Kai su makarantar Dan Dama shi ne yake kaisu


Har k'ofar gida na rakasu sai danaga tafiyarsu na dawo Ina kwanciya bacci yayi awon gaba dani na hau mafarki Wai gidan danake ciki ya Kama da wuta.

Da sallati na tashi a firgice ai kuwa na jiyo kauri da Sauri na mik'e na nufi kitchen Ashe Wai heater na kunna ruwan ya kone shine heater tayi jawur shap na manta cikin zafin nama na zare socket din na koma Palo na zauna Ina Dan Jin fad'uwar gaba ahaka nayi jigum na zauna na rasa Mai kemin dadi.


Naseer kuwa yana sauke su Zahira ya bisu har cikin makarantar sai daya ga shigarsu Aji ya juyo ya hau motarsa ya fara k'ok'arin tayarwa

Kamar ance ya juya yaga wata Mata ta tsaya a bakin gate din makaranta ta yafito shi Akan yazo.

Fasa tada motar yayi yana mamakin Kiran da matar ke masa anan ya fara tunanin kila a cikin mallaman makarantar ne shine take so ta fada Masa wani Abu game dasu Zahira hakane yasa ya fasa tada motar ya fito.

Yana barin jikin motar da taku biyu.

Motar ta Kama da wuta. .......

*Wlh Haka Naseer ya tsallaka rijiya da baya da ya Bata lokaci wajen fitowa daga motar da yanzu sai dai wani bashi ba*
[6/26, 3:37 PM] +234 803 635 0240: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*


*Page 23*

Cikin fad'uwar gaba Naseer ya juya da Sauri Yana sallati daya ga yanda Motar ke ci da wuta mutane masu wucewa kuwa sai Sallati suke Dan wasu sun ma dauka da mutane a ciki.

Naseer kamar Wanda aka dasa shi Haka ya daskare a wajen sabida shock jikinsa sai rawa yake.

Da yanzu fa Yana cikin motar dake ci da wuta Kamar an watsa fetur.

Sai a lokacin ya tuna wata ce ta yafito shi daga bakin makaranta tana sanye da fararen Kaya

Da Sauri ya juya ya kalli bakin makaranta yaga ba ga matar data kirashi ba sai Mallamai maza biyu dake nufo Inda suke cikin turanci suna ihun konewar da motarsa keyi


Tuni mutane suka zagayeshi suka fara Masa barka da arziki wasu kuwa cewa suke Mai ya haddasa hakan motar ita kadai ta Kama da wuta.
Naseer Da har a lokacin jikinsa Bai daina rawa ba most especially dayaga yanda Motar ke taci da wuta.

Makaranta ya nufa Dan yaga matar data taimaka masa ta kirashi Wanda ba Dan ta kirashi ba da yanzu Yana cikin motar.

Sai dai ga mamakinsa har office din headmistress din yaje Yana tambayar ko akwai mallamar data Yi Shigar fararen Kaya tazo yau

Take aka Kira duka Mallamai matan babu wacce ta saka fararen Kaya hakan kuwa ya Kara d'aurewa Naseer Kai Dan fa yaga.mace da fararen Kaya ta yafito shi Akan yazo hakane yasa ya fito daga motar.

Sallati kawai yake a zuciyarsa har lokacin jikinsa na balain rawa sai shigowa ake makaranta ana kallonsa Ana Masa barka da arziki idan aka ga yanda Motar tasa ke ci.


Sai daya Dan samu nutsuwa tsoron dayake ji ya Dan ragu kafin ya mik'e ya fito waje ya tari taxi ya nufi gida har lokacin jikinsa rawa yake akwai kudaden dake cikin motar da zasu Kai Dubu dari da hamsin da a lokacin kudine Mai yawa Yana so Yana sauke su Zahira ya wuce kasuwa ya Saro Kaya shi konewar motar da kudi duk Bai dameshi ba Kuma yasan ba mafarki yake ba ballantana yace idonsa Bai Gane Masa matar data Kira shi ba da fitowarsa daga motar da taku biyu motarsa ta Kama da wuta iya saninsa motarsa lafiya Lau take balle yyi tunanin
Ko wani abune yasamu motar shiyasa ta Kama da wuta.

Wacece matar da ta kirashi daga mota idonsa ba karya yayi Masa ba a bakin gate ya ganta ko wani Abu tagani a cikin motar shiyasa take kiransa abinan ya daure Masa kai.


Ina Nan zaune jikina duk a mace na rasa Mai kemin dadi bansan ma tunanin daya Kamata nayi ba

Ahaka naga Naseer ya fad'o palon a hargitse da Sauri na mik'e Ina sallati tare da tambayarsa lafiya Ina su Zahira duk na dauka ko wani abun ne ya same su.

Bai cemin komai ba in Banda Zama da yayi

Ya kurawa waje daya Ido ni kuwa tuni hawaye ya cikemin ido a rude na cigaba da tambayarsa lafiya na gansa Haka.

A hankali ya fara bani labarin abinda ya faru dashi ya Kara da "har yanzu abinda ya daurmin Kai Bai wuce matar data kirani na fito daga motar da banganta ba da Bata kirani ba Naeema da wlh yanzu sai dai kiji labarin mutuwa ta bansan wacce Mata ce wanan ba bansani ba ko alama tagani motar zata Kama da.wuta ta kirani"


Tunda Naseer ya fara bani labari jikina ke balain rawa Ina zabga Sallati hararowa kawai nake da ace Yarana hudu suna ciki da mahaifinsu fa da yanzu haka zaa kawomin labarin mutuwarsu Allah ya kiyaye.

Sosai na ringa tsoron darsa wani tunanin a Raina ba Kuma nasan na danganta konewar motarsa da wani Abu duk da idan Ina tuna irin mafarkan danake yi hankalina Kan tashi wani zubin har sai ya kaini ga yin sadaka.

Boye tashin hankalina nayi na fara kwantarwa da Naseer hankali akan kila dai ba wacce ya gani idonsa ne anan Kuma yayi ta min musu Akan shi mace Mai sanye da fararen Kaya ce ta kirashi ya fito daga motarsa shi damuwarsa Bai wuce yasan wacece matar ba shi konewar motar ba damuwarsa bace tunda Alhamdulillah lokacin Motocin hawansa sun Kai hudu duk da asara ko Yaya take Bata da dadi.

Nidai dak'yar na samu ya Dan nutsu take kuma Naga ya ware sai da ya sake wanka abincin Dana samu na girka.na Rana da duk ba a nutse ba sabida tashin hankali da nake ciki da fargaba tsinuwar da Umma tayiwa Naseer ne ya hau dawomin ya tsayamin a rai bandai Bari Naseer yasan halin danake ciki ba har yaci abinci ya sake ficewa akan zai d'auko su Zahira tunda lokacin sun tashi yacemin Yana saukesu a k'ofar gida zai wuce Kasuwa kwana biyu Bai ma lek'a su Lukman ba har yake cemin gwara ma ya saka gidan Haya tunda ba kowa a gidan ko da Allah yasa Umma ta yafe Masa ta dawo sai ya Bata gidansa na kasan layin mu daya Gama ginawa karshen kad'an ne.


Addua na Masa ya fice Ni kuwa na zauna cikin damuwa da fargaba Anya shirun Nan da Umma tayi na lafiya ne tun sanin Dana yiwa Umma daga aurena da Naseer zuwa yanzu bata taba share mu Haka har tsawon shekara biyu ba duk da nasan fushi tayi naso ta dawo ko ta Bari Naseer ya ganta ayi wacce zaayi na samu nutsuwa zuciya amma shariyar nan data Mana na damuna Ina fargabar abinda zaije ya dawo ya kawai motar Naseer zata Kama da wuta batare da wani dalili ba wacce Mata ce ta Kira Naseer sabida Kar ya kone Allah ubangiji ya tsaremu daga duk wani masifar da zata tunkaromu idan Yana cikin kaddararmu Allah ya bamu ikon cinyewa.

Sallah ma kasa tashi nayi nayi sai da naji sallamarsu Zahira naji hankalina ya Dan kwanta a Raina kuwa na Kara yiwa Naseer addua kariya daga sharrin karfe da komai ma Dan a wani motar ya Kara fita.


Naseer kuwa tuni ya ware ya danganta konewar motar da kila wani abune ya samu engine din yayi zafi shi yasa ya Kama da wuta abinda kawai ya tsaya.masa a Rai Bai wuce matar data kirashi da yake tunanin Anya kuwa ma mutum ce.


Isarsa kasuwa da yawan mutanen dake San siyayya yasa ya manta da abinda ya same shi a ranar yayi cinikin da zai iya cewa ya Dade baiyi ba Dan Haka akayita tururuwa a shagonsa ahaka ma akwai yaransa biyu.

Dake Taya shi Sallama sauran shaguna biyun ma akwai wayanda ke rik'e dasu.

Irin cinikin da yayi da ribar daya samu yasa yayi ta Godewa Allah Dan a ribar ma ya kusa hada kudin motar daya yi a asararsa.

Duk yanda yaso zuwa gadon kayar Bai samu zuwa ba sabida yanda kansa ya dau zafi sai karfe Tara ya koma gida agajiye.

Yana komawa gida abinci kawai ci yayi wanka ya shige daki.

Ya bar Naeema dasu Zahira a Palo tana duba home work dinsu.


Sai da Naseer ya dawo gidan hankalina ya kwanta duk da kasan zuciyata cike take da fargabar Mai zai Kara faruwa.


Sosai naji inaso na Kara yiwa Naseer maganar zuwa Calabar wajen Umma ko Allah zai saka ya ganta ya nemi yafiyarta.

Sai da su Zahira suka gama home work na raka su daki suka kwanta na tofesu da Addu'a na kashe duk wani electric fanka kawai na bar musu a kunne na ja musu k'ofar na koma d'akina.

A kan Sallaya na tadda Naseer a zaune da Qurani a hannunsa Yana Dan gyangyadi shigowata yasa ya bud'e ido tare da Hamma ya rufe Quranin ya mik'e Yana cemin bacci ne a idonsa kwanciya zaiyi wajen karfe daya ko biyu na tashe shi akwai Addu'a dayake so yayi.

Toh kawai nace Masa ya Kwanta na shige bandaki na daura alwala nayi shafai na dau carbina nayita istigifari Ina yiwa Annabi Sallati bansan adadin danayi ba sai da naji idona ya fara yaji na ajiye carbin na maida kaina nayi Sujadda nayita rokon Allah Ina adduar Kariyarsa a garemu bansan Mai yasa nake Jin tsoro ba bansan Mai yasa kalmomin Umma Mai nauyi ga Naseer ke dawomin ba tamkar a lokacin take fada Masa Haka nakejinsa a kaina.


Wajen Sha daya da rabbi na shafa na hau Kan gado Dan Nima tuni naji idona ya cika da bacci.


Daga kwanciya ta na hau mafarkai marasa Kan gado Ina ta mafarki da Naseer sai Dana farka ya Kai sau uku Ina komawa

Wajen biyu da rabbi na fara mafarkin d'akinsu Zahira naci da wuta yarana nata ihun Kiran sunana.

A firgice na tashi Ina sallati aikuwa sai na jiyo kauri bansan lokacin Dana duro daga Kan gado.ina kwalawa Naseer kira da ya.tashi a firgice Sabida Kiran Dana Masa ba.


Ihu na saka a.lokacin Dana fita Naga hayaki ya cike palon wuta nacin labulen palon Wanda da ace ya Kai ceiling gidan gabadaya xai Kama da wuta.


Tashin hankali yasa nayita zunduma ihu tare da daskarewa waje daya nama Shiga d'akin yarana na duba na kasa.

Ina kallon Naseer da shima jikinsa ke rawa Yana sintiri daga kitchen zuwa palo Yana d'ebo ruwa Yana watsawa labulen bakinsa d'auke da sallati cikin Ikon Allah kuwa wutar ta mutu.

Ya saki wani irin ajiyar zuciya ya juyo Yana kallona Ni kuwa tuni nayi zurfi a tunanin Mai ke faruwa damune Mai wutan Nan danake ta gani a.mafarki ke nufi Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun.

"Naeema Mai kuka Bari a kunne ne da baki kashe ba"?

Maganar Naseer ya dawo Dani hankalina bance masa komai ba na nufi d'akin yarana Dan na duba lafiyarsu.

Dukansu baccinsu suke cikin kwanciyar hankali Ni kuwa na Shiga d'akin na zauna a kasa tare da zabga tagumi Ina tunanin dazu yanda muka so yin gobara Allah ya Kare gashi yanzu ma labule naci da.wuta bansan daga Ina wutan yazo ba Dan Ni na tabbata ban bar komai a kunne ba ga motar Naseer shima da Haka kawai ya Kama ci da.wuta Anya kuwa.

Naseer naso yiwa magana Amma bansan na daga Masa Hankali inaso ya Gane da kansa Akwai matsala Dan Ni nasan akwai matsala.

Naseer kuwa ganin naki kulashi nayi zurfi a tunani yasa hau min fadan nayi sakaci na bar fitilu a kunne an kawo wuta Mai k'arfi hakane yasa bulb fashewa Dan gashi can bulb wajen biyune suka fashe.

Bance masa komai ba ya gama fadansa ya fita Ni kuwa Yana fita na fara kuka a boye bansan.mai yasa nakejin tsoro ba bansan Mai yasa nakeji kamar gidan Nan na iya kamawa da wuta ba tunda har nayi mafarkin wutan har sau biyu.

Ban iya komawa bacci ba sai danaji Ana Kiran Sallah asuba na fito daga d'akin na koma.dakina na daura alwala Naseer ya tafi massallaci.


Duk jikina ba kwari Haka nayi ayyukana yanda na Saba gabana na

5 Comments On NAGA TAKAINA
avatar
huda

1 year ago

Reply

Chapter 21

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment