Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da zobon Kai ma zaka ci a kudin Dan Haka maza wuce ki kiramin shi kafin naci ubanki"


Da mugun gudu Zahira tayi waje.

Naseer kuwa idonsa ya kad'a yayi ja shi kam zuciyarsa na Dab da bugawa sabida tashin hankali da rashin nutsuwa sosai yake Jin gidan na Masa zafi kamar ya hada kayansa ya rik'e hannun yayansa ya gudu barwa Hajara gidan

Ahaka ya rik'e hanunsu Nadeeya suka Shiga karamin Palo ya cirewa Raheema uniform ita da Humaira ya saka musu wani kayan ya zubo musu abinci suka fara ci


Nadeeya kuwa cewa take Umma Bata dawo ba?

Bai kulata ba sabida gani yake magana ma wahala yake masa.

Muryar Zahira dayaji yasa ya mik'e ya fita

"Ance Baya Nan yayi tafiya"

Zahira tace da rawar.murya

"Maganata ta fito Ni nasan dashi ta tafi Dan da safe yake zuwa gidanan nan wanan abun da tayi ya tabbatar min da ita muguwa ce ta karshe wato shima isihun bazamu more shi ba toh ai shikenan kanta ta cuta wlh Dan ke Zaki kai min ruwa da zobon bazan dau asara ba wlh maza jeki cire Kaya kici abinci kizo ki dauka yanzu yanzu ki siyarmin"


"Aaaa Umma Zahira bazata taba talla ba
ba iya ita ba insha Allahu yarana baza suyi talla ba Haba Umma ko wani Kika ji Yana cewa zai Dora wa Zahira tala ai ke Mai hanawa ne Umma karki.manta yaran Nan ba iya Naeema ce ta haifesu ba yayana ne Kuma jikokinki Dan Haka Bai Kamata kiyayar da kikewa mahaifiyarsu ya shafesu ba da Raina bazan iya Bari yarana suyi Tallah ba Umma kiyi hakuri"


Sakin Baki Hajara kawai tayi tana kallon Naseer dake ta kwara bayani

"Yau Ina ganin ikon Allah toh iskanci nace taje tayi kake zabga min wanan Bayanin Naseer daga Kai har Naeema idonku ya rufe da San Yara bakwa so moresu ko ayi musu tarbiyya Naseer Naga idan ta siyar da ruwa da zobon kananun Abubuwan da babu Zan iya d'auke maka a gidanan tunda Kai zuciyarka ta mutu ka kasa fita ka nemo tundazu nake binka akan kaje ka Nemi kudi ka kasa sanann Dan nace Zahira ta Kai Mana tallan ruwa da zobo kace bazata je ba toh wlh sai taje idan dai har ka dage bazata je ba toh wlh sai dai Kai ka dauka ka kaimin da kanka tunda Ni na Haifeka na Kuma Isa dakai"


"Da Zahira ta je tallan Nan Umma gwara na je da kaina Sanan Mai amfamin ita Safiyya da bazata je ba sai Yar karamar yarinya Nan zaa ce taje"

Hajara na k'ok'arin Magana Naseer ya dakawa Safiyya tsawar daya gigita Safiyya ta mik'e batare da ta shirya ba "Dan uwarki d'auki zobo da ruwan kije ki siyar tunda kin k'i fito da miji kiyi aure Maza mik'e dan yarana ba bayi bane da Zaki Mike kafa a nemo.a kawo.miki ki dauka nace kafin na hada.kanki da bango Naseer yace Yana nufar Inda Safiyya take.

"Wlh bazata je ba Naseeru tunda ka Hana Zahira zuwa Kai da kanka zaka je"

"Wlh Nima bazanje ba Umma Dan Babu yanda kanwata tana zaune kina kallonta kice Zahira taje talla ko Ni wlh ko ta Kai tallan Nan ko ta barmin gidana umma Dan Nagaji da Zamanta a gidana ki dauka nace"


"Wlh bazanje ba Haka kawai Zan d'auki kula akaina na fita talla da girmana da komai"

Safiyya tace tana k'ok'arin Shiga d'akinsu.

Naseer kuwa ya fusgota cikin zafin nama zuciyarsa na tafasa kwallo kawai yake da Safiyya tana zunduma ihu duka yake Kai.mata ko ta Ina

Hajara kuwa ta hau rike Naseer tana ihun wlh ya cikata zata tsine Masa kashe Safiyya zaiyi

Naseer da Ransa ya Kai kololuwa wajen b'aci idonsa ya rufe sosai baya ma Jin abinda Hajara ke cewa dan ji yake kamar dukan da yake wa Safiyya ne kawai zai rage Masa radadin zafin dayake ji a zuciyarsa .

Hajara kuwa ganin idan batayi da gaske ba zai kashe Safiyya tana ji tana gani

Muciya ta dauko aguje tayi Kan Naseer.........


Ayi.maneji yau naje Dubiya

*NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*


*Page 36*

Kafin ta Kai wajen Naseer din ta wurga tabaryar Naseer ya kauce da Sauri Safiyya kuwa a garin mik'ewa ta gudu muciya ya sauka akanta ta saki ihu tana dafe keyarta.

Hajara Kuwa tsantsin Inda Suka kulla zobo da ruwa ya deb'eta ta Fadi kafarta ta lankwashe baya ta saki ihu.
Naseer kuwa yayi kanta da Sauri ya dawo Mata da kafarta daidai

Ita kuwa sai girgiza Kai take tana wayo kafata

"Kaga abinda ka jawo ko Sabida Naeema ta tafi shine ka haukace kake neman kashe Safiyya Dan kawai nace Zahira ta Kai min talla shine ka dage bazata Kai ba sai dai Safiyya ta Kai tayaya Zan dorawa Safiya talla tana budurwa Banda bakada hankali Zahira kuwa yarinya ce Amma dayake bakada mutunci kana so ka nunamin ban Isa da Kai ba shine zaka ce bazata je ba gwara Safiyya ta tafi iya Nan Bai isheka ba sai ka hada Mata da duka"



"Kiyi hakuri Safiyya Bata fi Zahira ba yanda kike ganin Bai Dace Safiyya ta je talla ba nima.haka nake ganin Bai Dace na bar Zahira ta tafi talla ba bawai Dan Baki Isa da ita bane kema kinsan duk abinda kike cewa ta Miki ban taba hanata ba Amma talla ne bazan yarda Zahira tayi da Raina ba Umma matsawar kudin kikeso sai dai ta Kai Miki tallan gaskiya amma matsawar bazata Kai ba wlh sai dai mu zauna Haka Umma Banga amfanin da Safiyya take min a gidanan ba Dan Ni nasan wasu Abubuwan wlh ita ke sawa kiyi shegiya Shaidaniya Wlh Nagaji da Zamanta a gidana Ki fada Mata ta fito da mijin Aure ko kunya Bata ji tana ta tsufa agabanki a madadin ta nemi Wanda zai Aureta shine ta zaune min a gida tana hadamin balai Umma keda yarana ne kawai kuka zame min Dole Safiyya ba Dole na bace Dan Haka wlh ko kudin na samo iya ke da yarana Zan ciyar bazan ciyar da ita ba"


"Ai Ni nasan ka samu tabin hankali Naseer K'arfi da yaji ka haukace sabida Naeema ta tafi Safiyya ba akanka take zaune ba yata ce Kuma dolene ce tunda Kai Kace ba Dolenka bace Ni nasan zafin talauci dayake damunka ne yasa kake Neman hucewa akanmu talla Kuma danace Yarka tayi ai sabida Kai din ne Amma tunda kace Haka naji Amma wlh wanan dai bazanyi asararsa ba sai ka Nemo Mai zuwa ya siyr min dan yanda ka rantse ba Inda zahira zataje nima.na rantse ba Inda Safiyya zataje miji Kuma da kake magana idan Ana siyarwa a kasuwa ka siyo ka kawo Mata Naseeru da kake zancen ta fito da miji kana da kudin da zaka Mata kayan d'akine bakada ko sisi kazo kana zancen tayi aure idan Auren yazo yanzu da uban me zaa kaita bamu ajiye ko sisi ba kafita ka Nemo kudi ka k'i ka zauna zuciyarka ta mutu mace na ciyar da Kai Dan ta tafi ka haukace kana neman kashe min 'ya



Naseer hannun Zahira ya rik'e da jkinta ke rawa sabida tsoro Rai a bace Suka Shiga karamin palo yabar Hajara na cigaba da masifar yazo ya biyata kudinta idan ba Haka ba ta huce akan yaransa Bazai iya cigaba da sauraren maganganunta dake barazanar buga Masa zuciya ba

Naseer daki ya shige ya kwanta ringingine sabida ciwon da kansa keyi

Sosai yake jinsa a takure kamar a prison a yau da Naeema ta tafi bazai iya misalta caza Masa Kai da Mahaifiyarsa tayi ba Wanda yakeji Kamar ya kwashi yayansa su bar Mata gidan inaga Naeema da ta kwashi shekaru tana fama da ita sosai yaji tausayin Naeema ya danne haushinta da yakeji wacce zata iya hakurin Zama da Mahaifiyarsa idan ba Naeema ba.

Ya dauka Naeema Mahaifiyarsa ta tsana kila data tafi zai Samu sasauci daga masifarta sai gashi daga shi har yaransa Basu tsira ba ya rasa gane irin halin ta.

Dak'yar ya taushi zuciyarsa ya fito wajensu Zahira da har ta ci abinci itama sun saka kayan islamiyya.


Hannun Raheema da Humaira ya rike sukayi waje Minal da Nadeeya da Zahira suka bishi a baya Basu samu kowa a tsakar gidan ba sai Dan ihun Safiyya da ke tashi a d'akin Sabida daddane Mata jiki da Hajara keyi da ruwan zafi Dan ba karamin dakuwa tayi a wajen Naseer ba keyarta da muciya ya sameta ba karamin kumburewa yayi ba sai Allah ya Isa take zabgawa Naseer tana rantsuwar sai ta Rama Akan Zahira.

A Haka Naseer ya rakasu har makaranta sai da suka Shiga ya juyo ya dawo gida.

Yana Shiga gidan yayi kicibis da Kular ruwa da zobon Hajara na zaune ita kadai sai jijjiga k'afa take tana ganinsa ta mik'e tana "wlh ka dauka ka kaimin tunda ka dage Yarka bazata Kai ba dan bazan dau asara ba wlh kaji na rantse maka Safiyya Kuma da kake magana gata can a kwance bama gani take sosai ba sabida yanda ka kumbure Mata jiki.

Nima ga k'afata Nan a kumbure inajin ma sai naje Naga likita sabida zugin da yake min banida Kuma ko sisi sai ka siyar Zan samu kudin ganin Likitan maza d'auki da ruwa da zobon na dari biyar da talatin ne"


Naseer matsar da kulolin yyi gefe ya wuce ciki Hajara kuwa ta biyo shi tana cigaba da masifa a tsakiyar d'akin ta tsaya ya Shiga bandaki ya d'aura alwala Dan lokacin sallah La'asar ya wuce.

Yana tada sallah tayi waje tana ya iddar tana jiransa

Sai daya iddar da sallah ya daga katifa ya d'auko kudin da Naeema ta ajiye mishi.

Wajen Dubu hamsin ne maida kudin yayi Bayan ya Ciro dari biyu guda uku ya saka a Al jihunsa ya yi waje.

Har Hajara zata taso taga ya d'auki kula yayi waje ya dawo ya d'auki daya ya fita k'ofar gida

Ya rabar wa da Yara ruwa da zobon yayi zamansa a k'ofar gida Yana tunanin Sana'ar da ya Kamata yayi da kudin da Naeema ta bashi batare da yayi nisa da gida ba Dan ko Naeema Bata ce Masa ya sakawa yaran Nan Ido ba halin mahaifiyarsa bazai Bari yayi nisa dasu ba.


Sai da su Zahira suka dawo suka Shiga ciki gabadaya da kulolin Hajara da Safiyya na zaune Akan tabarma.

Minal ya bawa kudin Akan ta kaiwa Hajaran Dan bama yaso ya karasa wajenta ta Kara tare shi da wani masifar .

Minal na mik'a Mata kudin ta karbe da sauri ta hau kirgawa sai data tabbatar ya cika har da doriya ta washe baki tana k'ok'arin cusa kudin a zaninta Safiyya ta wafci dari biyu tana "bazaki janyo min wanan dukan kici kudin ke kadai ba anjima balangu Zan siyo naci"

Hajara hannu ta Kai Dan ta kwace cikin masifa Safiyya ta rik'e kudin gam.

Abincin dare ma Naseer ne ya dafa musu.

Sai daya tabbatar da sunci sun koshi yasa suka fito da home work dinsu sukayi.

Kafin bacci ya d'auki Zahira haka ta ringa Masa maganar Naeema Akan Dan Allah yabi bayanta ko ya Kai su wajenta sai daya daka Mata tsawa ta rufe bakinta da sauri.

A ranar Naseer Bai iya runtsawa ba sabida tunani a karshe ya yanke Kara siyan engine markade guda biyu sauran canjin ya siya musu kayan abinci Yana kyautata zaton markaden ne zai saka su Dan samu kudin da asirinsu xai rufu batare da Kuma yayi nisa da yaransa ba duk da yasan sai n an samu matsala ta b'angaren mahaifiyarsa Amma da dai ta dorawa yarsa talla gwara ya siyi engine tunda abinda yasa takesan Zahira tayi tallan sabida rashin engine ne.

Haka kuwa akayi Washegari da safe Bayan su Zahira sun tafi makaranta.

Ya dauki kudin ya tafi kasuwa ya siyo injina biyu sauran canjin ya siya musu kayan abinci har dasu kayan sawa ya siyowa su Zahira da takalma.

Kasancewar ranar Jumaa ne hakane yasa Bai iya komawa gida da wuri ba.

Bai karasa gida ba sai wajen karfe uku na rana.


Mai taxi na ckin sauke Masa injina yaji ihun zahira hakane yasa ya Shiga gidan aguje.

Safiyya ce akan Zahira tana ta dukanta kamar ta Samu babba Hajara kuwa na zaune Akan kujera Dan tsugunno ta saka tsinken a bakinta tana ta sakace hakori Kamar Bata wajen.

Minal da Nadeeya sai duka suke kaiwa Safiyya suna kuka.

Tsabar rufewar da idon Safiyya yayi Sam Bata San da shigowar Naseer da jikinsa ya kwashi wani irin rawa ba Hajara kanta sai data tsorata da yanda ya shigo da balain sauri ta mik'e tana k'ok'arin yiwa Safiyya magana Naseer ya isa wajensu ya kaiwa Safiyya wani irin wawura ya hadata da bango ya shaketa Ta fara kakarin mutuwa.

Hajara kuwa ihu ta saka Dan dagaske Naseer so yake ya kashe Safiyya fata kawai yake ta mutu a hannunsa a Kai shi gidan yari ya huta da bakin cikin Safiyya da Mahaifiyarsa.


Duk dukan da Hajara take kaiwa Naseer Sam baiji ba har muciya sai daya karye a jikinsa Bai cikata ba

Safiyya kuwa tuni ta sume a hannunsa.

Hajara sai waje tayi da gudu ta Kira aka zo aka bambara Safiyya daga hannun Naseer.

Hajara tayi Kan Safiyya tana ihun Naseer ya kashe Mata ya.

Naseer kuwa d'akin ha Shiga ya hau watso da kayan Safiyya waje Yana ta bar Masa gidansa bazata Kara kwanar Masa a gida ba.

A ranar ba karamin rikici akayi tsakanin Hajara da Naseer ba

Dan da Safiyya ta farfado sai da Naseer ya fitar da ita waje Akan bazata Kara kwanan Masa a gida ba


Hajara kuwa ta dage akan sai dai ya koresu su biyun K'arfi da Yaji Hajara ta Masa fin karfin ita mahaifiyarsa ce ta kulle Safiyya a daki Akan ba Inda zata je ai ba Haka kawai Safiyya ta daki zahiran ba rashin kunya tayi Mata.

A ranar Naseer kwana yyi Yana kuka daga tafiya Naeema da zaa auna jininsa zaa iya ganin ya mugun Hawa sabida tashin hankali shi kam yasan rayuwar Zahira na cikin hatsari Bai tab'a ganin uwar da Bata San danta bata San jikokinta ba sai Mahaifiyarsa ya yarda uwa na iya tsanar matar danta Bai San uwa na tsanar danta ta tsani zaman lafiyarsa ba.


Ya Zama Dole ya d'auki mataki inama Naeema ta tafi da Zahira da Nadeeya ta bar mishi sauran yaran bazai dauwama Yana zaman gida ba Dole wani uzurin ya taso yyi nesa da gida Amma in ya fita yasan yana ckin fargaba da rashin kwanciyar hankali.

A takaice tundaga ranar Safiyya ta fara balain tsoron Naseer indai Yana Nan ko fitowa Bata iya Yi gashi baya fita sai dai idan Massallaci zaije.

Akan engine markaden ma sai da sukayi rikici da Hajara ta dage sai dai ya bar Mata guda daya ya dau daya idan aka kawo.markade ita ta d'au daya shi ya dau daya sai dai me tunda aka siyo engine sau biyu aka kawo markade baa Kara kawowa ba Sabida masifar Hajara har suna Suka saka Mata a unguwar suna kiranta da masifafiyar tsohuwa.

Naseer yanda ya d'auka zai samu kudi idan ya siyi engine markaden lura da yanda Naeema ke samun kudi Bai samu ba Dan bama zuwa ake ba wani zubin yana ma zaune a k'ofar gida zaa wuce gidansa a Kai wajen bakin titi da dai a Zo gidansa tuni damuwa tayi.masa yawa kasa da wata daya komai na gidan ya Kare Wanda sai da ta Kai shi da siyar da engine guda daya Dan Bai shigo Masa da kudin ba.


A cikin kudin ya biya kudin makarantar su Zahira sauran canjin shima Nan da Nan ya Kare.

Kafin kace me dayan ma sai daya siyar.

Hajara kuwa masifa ta hau yi akan ita tasan Naeema ce tayi asiri aka ki kawo musu markade k'arfi da yaji tana ji tana gani Naseer ya siyar da engine data ci burin samun kudi dashi ta siyi filaye.

Kamar ta fashe dan bakin ciki wata uku da tafiyar Naeema sai gashi abinda zasu saka a cikinsu Yana neman gaggararsu.

Safiyya kuwa data ga bazata iya ba aikatau taje ta nema a wani gidan masu kudi zata ringa zuwa tana dawowa daddare.

Idan taje abincin da ake Bata shi take kawowa gida taci Hajara na kallo idan tayi Magana kuwa Sai tace Mata kowa tasa ta fishe shi


Naseer kuwa Dan abinda ya fita ya Dan samo sabida tuni ya nemi aikin lebura na gini ya farayi Dan kudin daya samu yake siyowa su Zahira abinda zasuci ahaka ma sai dai shi ya hakura Dan bazai iya barin Hajara da yunwa ba.


Ahaka Safiyya tayi albashi Hajara tayi ta rokon ta Allah da annabi kafin ta yarda ta Bata wani Abun.

Tana Bata kuwa ta siyo shinkafa da kayan Miya ta girka ta kakasafta a kwanu.

Zahira na dawowa daga makaranta tasa ta cire uniform ta Dora Mata farantin

Ta bawa Nadeeya Yar robar miyan tace musu su dau hanya su tafi su siyar Mata taja musu kunne akan kar su sake su dawo gida batare da sun siyar Mata ba idan Naseer ya Isa idan ya dawo ya mata magana yaga yanda zata Yi dashi

Suna fita ta dakawa Minal tsawa Akan su saka kayan islamiyya su tafi.

Minal sai data Dan gwada Mata taurin Kai ta dan bubuge ta kafin suka bar gidan.

Naseer dake ta Dora bullo a wani gida da ake ginawa kamar ance ya daga kansa ya hango Zahira da Nadeeya na tafe a Gefen titi suna rarrabewa a gefe ga uban faranti akan Zahira ga Nadeeya itama da nata robar miyar.

Naseer Bai San sanda ya duro Yana mirtsika Ido ba Dan ya tabbata da su Zahira yake gani.

Jiki na rawa ya Isa wajensu.

Ya sauke farantin dayake ganin yayi wa Zahira nauyi yace musu waye ya Dora musu talla.
Ce Masa sukayi Hajara ce.

Yayi shiru Ransa na balain baci.

Dak'yar ya hadiye b'acin Ransa yace su zauna a wani dakali su jira shi Yana zuwa.

Ba a cikin hankalinsa Suka karasa aikin ba Dan har sai da bulo ya Fado Masa a kafa Sabida tunani.

Ana biyansa kudinsa ya wanke jikinsa ya cire kayan aikinsa ya maida Mai kyau jikinsa.

Ya tsallaka wajen su Zahira ya d'auki farantin abincin.

Ya rarrabawa almajirai

Ya Kama hannunsu ya tare musu bus Suka hau suka nufi gwammaja.

Bashida tabbacin Gane gidan Tijjani Amma ahaka yaje sai da kyar ya Gane gidan da kwantance.


Suna zuwa k'ofar Gidan Tijjani na isowa a vespa.

Ko parking baiyi sosai ba ya duro daga vespan Dan murna ya rungume Naseer cikin murna


Naeema


Kwana biyu kawai nayi a garinmu danaje da Ashe sun Dade suna nemana sosai naji mutuwar Mai unguwa da nake Jinsa tamkar mahaifina ashe shekara daya kenan da rasuwarsa

Kafin rasuwarsa ya siyar da gidanmu ya boyemin kudin Dan lokacin sosai ake San siyan gidan hayan daya saka kuwa sai yaga ma.kamar mutanen ciki Bata gidan suke hakane yasa ya siyar da gidan Akan duk lokacin da Nazo zai bani ya kuma San bazanji Haushin siyarmin da gidan mu da yayi ba

Dubu dari uku da sabain ya siyar da gidan namu.


Kafin rasuwarsa Haka yayi ta rokan yayansa da matansa akan Dan Allah Kar su tabamin kudina duk lokacin Dana Zo a damka min kudina.


Sosai naci kuka na Godewa Allah da rashin Mai unguwa a Haka na kwana biyu cikin zuciyata ba dadi uwa uba ga tunanin yarana daya dameni ko baccin kirki bana iya yi sabida Ina tunanin kamar suna can suna Shan duka a wajen Safiyya abinda zai taimakeni kawai shine Kila Naseer bazai yarda a tab'a min su ba da Wanan tunanin hankalina ke Dan kwanciya.

Sosai iyalin Mai unguwa suka nunamin soyaya Dana tashi dawowa Dan Kaya Suka bani sosai na amfani Dan ban Gaya musu abinda ke faruwa Dani ba.

Karfe uku na rana na iso gidan kanwar Aunty Ina zuwa kuwa na tada Aunty a gidan.

Bazan manta Aunty a rayuwata ba tamin abunda har na mutu bazan manta alherinta a gareni ba.

Ina sallahr La'asar muka nufi dorayi da ita.

Ta kaini gidan data kama min ta hau min bayanin da kyar Mai gidan ya yarda ya bada haya Dan yace siyarwa zaiyi Amma ko yanzu ya samu Mai siya zai maidamin kudina ne na siyar.

Gidan Mai kyau ne dakuna biyu da bandaki biyu da Palo sai dan karamin shago a k'ofar gida

Gwada tambayarta nayi nawa ne gidan.

Tacemin Dubu dari uku da ashirin

Take nace Mata Zan siyi gidan Kamar Wasa ta rakani wajen Mai gidan na nemi ya siyarmin Dubu dari biyu da hamsin dak'yar ya siyar min a Dubu dari biyu da casain

Washegari muka Kai Masa kudin gidan ya d'auko takarda gidan ya bani

Aunty sai murna takemin ni kuwa sai tambayarta nake tana ganin yarana cemin tayi tana ganinsu kar na damu Naseer na kula dasu Dan ta saka Ido a kansu

Take naji hankalina ya Dan kwanta.

A. Cikin kwana uku naja wutan.nepa gidan

Aunty ta Nemo min Katifa second hand na biya da Dan ledar tsakar daki da Dan kayan amfanin gida da bazaa rasa ba.

Wata Hassana da take bazawara da ta kasance Yar uwarsu ta kawomin Akan mu ringa kwana tare Dan Ina tsoron kwana Ni kadai.


Hassana kuwa zata iya girme min Amma tana da kirki

Makotana na zaga na Dan duba abinda baa samu unguwar Naga har da dai markaden sai sunyi tafiya Mai nisa suke samu.

Ana Kuma neman ruwan Sanyi kayan provision ma sai sun Yi tafiya Mai nisa.

Take kuwa na nemi engine second hand na siya Dan gaskiya Ina San sanaar markaden dan ya shigomin da kudi

Cikin Ikon Allah kuwa sati daya da siya aka faramin layi.

Dan har Hassana Tayani takeyi idan na gaji.

Kamar Wasa sauran kudin hannuna na Nemo kafinta ya bubbuga min canter na Dan zuba provision din kad'an su Maggi biscuit bredi da alewa da littattafai makaranta Dan Naga Ana yawan nema


Shima sati da fara siyar da provision din Rabbi ya Sanya min albarka a hankali sai gashi shagon k'ofar gida ya cika da kaya.

Sai gashi a cikin wata biyu har freezer na siya shima na saka a shagon Ina siyar da ruwa.

Nikam a wanan gabar sai dai nace Alhamdulillah Dan kudi ko ta Ina shigomin suke abinda yake damuna Bai wuce kewan yarana danake kwana Ina mafarkinsu ba wani zubin a mumunan yanayi wanan Abu shi yake hanani sukuni ko abinci bana iya ci.gashi dai komai na samu cikin rufin asiri Amma tunanin yarana ya Sakani balain Rama Nafi tunanin Zahira Dan jikina na gayamin tana Shan wahala a hannun Umma da Safiyya Koda kuwa Naseer na nan.

Sau uku Ina zuwa unguwar da likkaf na tsaya a k'ofar gida Naga ko Zan ga wani ya fito daga gidan a cikinsu sai dai bana ganinsu sai dai Naga Naseer daya balain Rama ya fita hayyacinsa sosai yake karyamin zuciya idan na ganshi ahaka zan karaci tsayuwata idan na gaji na karasa gidan Aunty tacemin Kar na damu dazu ma tagansu lafiya Lau suke ba Abunda ya samesu har tambayar Zahira tana yi dake da balain zurfin ciki tace mata ba komai.

Ahaka Zan dawo da tunaninsu a Raina Nima rashinsu kusa Dani ne ya saka Ni mugun Rama Dan Sana'ar tawa Dan hassana na rik'ewa ne da bazan iya tab'uka komai ba a yanzu da aka tafi wata uku rabona da yayana naji bazan iya jurewa ba Ina bukatar ganinsu ko ta halin Kaka hakane Yasa na yanke zuwa gidan aunty idan sun zo islamiyya nagansu Koda daga nesa ne.


Naseer..........

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka

5 Comments On NAGA TAKAINA
avatar
huda

1 year ago

Reply

Chapter 21

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment