Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hayaki ya fara gauraye d'akin Shugaba ta bayyana da fitila a hannunta

Safiyya da Umma Suka zub'e a kasa Umma ta hau magana "Naeema yau dukan Safiyya tayi Nima ta zubar Dani a kasa a sanadinta nayiwa Dan cikina mugunta ya rasa komai nasa na tsani yarinya Nan Shugaba banida burin daya wuce na Gama da ita na huta inaso kimin aikin da jini zai balle Mata tayi ta zubar jini har ta mutu yau yarinya Nan har gadara take ta gyara gidan Dana so take ma ta nunamin gidan nata ne"


Hannu kawai ta mik'a mudubi ya bayyana ta ajiye agabansu tayi surutai sai ga Naeema ta bayyana ita da Zahira akan Sallaya suna sallah tana k'ok'arin magana Hoton Naeema da Zahira ya d'auke mudubin ya fara tsagewa .

Shugaba kuwa ta duka ta d'auke mudubin tana "Ina zaune zaki janyomin balai wannan yarinya fa aiki akanta zaiyi wahala matsawar zatayi sallah dak'yar duk abinda zaa Mata ya sameta ki duba kiga daka ganin ta mudubi ya tsage Amma karbi wanan ki jarraba zuba Mata a abinci indai ta Kai bakinta sai dai ku hadu a lahira"


Ta jefawa Hajara wani Leda Mai dauke da garin magani.

Daga Haka ta b'ace Hajara taja Tsaki Tana "Ni matar Nan ma.bana Gane Mata wlh yanzu kamar itama Bata da wani k'arfi kame kame kawai take"


"Mu jarraba zuba Mata mugani dai"

Haka Suka zauna suna kulla sharri da yanda zasu kawo karshen Naeema


"Ni kuwa mafarkai nayita Yi a hargitse Wai Umma sun shigo d'akina da wuka zasu kasheni Cikin Ikon Allah na samu na kwace wuk'ar suka fita a guje na bisu.

Bayan nayi wanan nayi mafarki da mahaifiyata yanda na Saba ganinta ta daura alwala ta hau kan Sallaya ta daga hannu tana ta rokon Allah na Dade ban ganta a mafarki na ba bansan fassarar mafarki ba Amma zuwa yanzu nagane indai Ina cikin matsala ko Zan Shiga matsala sai nayi mafarki da Ummata tayi alwala tana adduar Wanda Ni na fassara Haka da tana nuna min na dage da Addu'a in ta gayawa Allah.

Wajen hudu na farka baccin da ban koma ba kenan.


Har sai da akayi sallah asuba yarana ma har sun Saba tare duk mu kayi Sallah zuciyata fes ba tsoron komai muka fita kitchen nida Nadeeya.

Zahira Kuma ta hau yiwa su Naeema wanka.

Cikin awa daya na Gama soya musu Dankali da tea har da jollof din shinkafa na juye a babban coleer na samu cooler madaidaiciya na zuba wa su Umma duk abinda na dafa.
Na bar musu a kitchen din na dauki namu na Kai d'akina.

Haka kawai na tsinci kaina da kwashe kayan abincinmu har Mai na Kai d'akinsu Zahira da kayansu yake ba katifa iya ashana kawai na Bari da kwandan kwanuka.

Kafin takwas tayi har Zahira ta Tayani tace zobo ta had'a sun hada hannu ita da Nadeeya sun kulla zobon cikin kular biyu Dan Haka suke Tayani kafin su tafi makaranta.

Ni Kuma idan na tashi sai na kula ruwan Isihu idan yazo sai ya amso kankara na watsa sai na bashi abinci safe karfe Sha biyu yake zuwa ya d'auka wajen biyu ya sake dawowa na basa abinci na bashi na biyu wajen hudu ya dawo.ya kawomin kudin sai Kuma gobe.

Karfe bakwai da minti hamsin na raka yarana makaranta bayan na kulle k'ofar daya Shiga babban palon da zai sadaka da b'angaren Dana koma.

Masu markade kuwa sun fi goma suna jirana sai Dana ga sun Shiga makaranta na dawo.

Na cire hijabina na kunna engine markaden daya kasance na wuta lokacin Wanda ake sawa fetur Bai fito ba inaga.

Ina markaden Ana Kara tururuwa zuwa a irin wanna lokacin idan Isihu yazo daya engine yake kunnawa ya hau Tayani ahaka har mu Gama idan nagaji Haka zai cigaba sosai nake Jin Isihu a Raina kamar Ni na haifeshi Ina Kara Jin shaawar inama na haifo namiji Mai irin kokarinsa har gobe Isihu tamkar Dan cikina nake Jinsa.

Ahaka na zauna a gefe Ina satar kallon su Umma da suka fito babban Palo suka.zubomin Ido suna ta kallona.

Har layi ya fara raguwa robar custard din da nake saka kudin markade har ya cika.

Sai da isihu ya Gama markaden ya kashe engine ya kawo robar custard din gabana Ni kuwa na bud'e na dauki ashirin na bashi nace ya siyo koko da.kosai ya Sha Dan tea da Dankalin ya Kare.

Da sauri yayi waje Ni kuwa na bud'e robar na hau hada kudina Ina jerawa sai Dana gama tsaf na hau kirgawa

Kudin a wajena yake Amma Umma da Safiyya dasu na kirga kudin suna gwallo Ido Kamar basu tab'a ganin kudi ba sosai suka ringa mamakin yawan kudin hannuna.
Ni kuwa Ina gamawa na mike da kudina a hannu

Na shiga babban palon na dauke kaina kamar ban gansu ba

"Ke Na fa ga alamar kin Raina Ni Dan uwarki wucewa zakiyi batare da kin gaisheni ba Wai dame kike takama ne Naeema karki ga kinyi amfani da tsafi kin daki Safiyya jiya wlh kikamin da kaina Zan dakeki"

"Ina kwana Umma"

Nace Ina cigaba da tafiya

"Zaki bamu abinci ko sai mun roka"?

Ta Kara cewa tana jifana da harara

"Abincinku na Kitchen Umma"

"Kinfi karfin ki dauko Mana kenan"

Ban tsaya ma Kara Bata amsa ba na zura hannu a zanina na dauko mukulli na bud'e k'ofar karamin palon na shige.
Inaji suna ta Auna min zagi.

Ina Shirin Zama naji masu kawo markade suna ta Sallama kudin hannuna na ajiye a cikin akwatina

Na fara k'ok'arin fitowa naji Safiyya na "Wlh umma kin cucemu ji lodin kudin hannun Yar iskar matar Nan Ni na tabbata kudin Yaya Naseer ne ya koma wajenta yanzu ita ta zama.mai kudin"

Dalla tashi kije ki faki Ido ki zuba Mata maganin kafin ta fito.

Girgiza Kai nayi na bud'e kofa Safiyya tayi sauri ta koma ta zauna tana boye maganin a bayanta

Ban kalli.inda suke ba na fita na Kara kunna engine na fara markade

Ahaka har Isihu ya dawo ya cigaba da Tayani Ni kuwa nace Masa idan ya gama ya kawomin kudin d'akina.

Ban kalli Inda suke ba na Kara komawa d'akin Ina mamakin halinsu wato har yanzu nemana suke da sharri Allah ya taimakeni na kwashe komai daga kitchen din

Ina Shiga d'akin Safiyya ta mik'e da Sauri ta Shiga kitchen kulolin data gani Bata tsaya dubawa ba ta bud'e shinkafa ta watsa maganin Haka ma Dankalin ta fito ta dawo ta zauna.

Suna kallon yanda ake ta kawo markade

Isihu kuwa sabida kwarewa injina biyun ya kunna Yana tayi hakane yasa Nan da Nan ya Gama kudi ya Kara cika rubber custard har da gwangwani

Sai daya wanke wajen ya dauki rubber custard din da gwangwani ya nufo b'angarena ganin bakin fuska yasa ya hau gaishe su ya hau raba Ido yaga ko Zan fito daga d'akina

Safiyya kuwa mik'ewa tayi ta nufi wajensa tana "kawo a Kai Mata"

Isihu da wayonsa ya kamkame rubber custard da gwangwani yana "hajiya nake nema"

Ita kuwa a hasale ta kai hannu ta kwace gwangwani a daidai lokacin Dana fito danaji muryar isihun

Ina fitowa Umma ta mik'e tayi daki Safiyya har da gudunta Dan su shige daki.

Cikin zafin nama na saka gudu tana dab da Shiga d'akin na damke kafadarta na juyo da ita tare da kwace gwangwani da k'arfi "Ina akan me Zaki daukemin kudi"?

"Wlh idan baki danne ta kin kwace kudin Nan ba sai na tsine Miki"........


*Huuuh Ashe Haka nake da masoya har gajiya nayi da amsa waya toh ngd da soyyaya da Kauna Ameenat abdlouye ngd Allah ya biya miki bukatunki na alheri*


*Wnan Shafin sadaukarwa ne ga duk masoyan Naga ta kaina da masu Kaunar Naeema da ita kanta Sadnaf din mungode sosai*


*DAGA PAGE ONE ZUWA 30 WANE DARASI KUKA DAUKA A LABARIN NAEEMA MAI YAFI BAKU MAMAKI DA ALAJABI MAI YAFI BAKU TAUSAYI TSAKANIN NASEER DA NAEEM WAYAFI SHAN WAHALA DISCUSS KO BAMA GRP DAYA IDAN KAYI ZAAYI FORWARDING YA ISA WAJENA DA NAEEMA NGD*
[6/26, 6:13 PM] +234 706 571 7620: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*

*Page 31*

"Kiji ki da wani magana ke ki matso ki danneta ki kwace kudin kina kallon yanda muka kwashe da ita jiya ta Taki wani Abu ba tsoronmu takeji ba yanzu tsinaniyar ban shirya ta danne Ni ba da sasafen Nan

"Ke dai anyi matsoraciya asarariya bani guri"

Ni kuwa juyawa nayi na nufi wajen Isihu na karbi robar custard din hannun Isihu Ina juyowa Naga Umma a gabana ta balain had'e Rai cikin mugun kallo ta mik'o min hanun tana "Tafi da kudin robar ki bani na gwangwanin Nan dan Ni nasan da kudin Naseer kika siyi engine dinan"


Ja da Baya nayi na kamkame kudina Ina "Umma bada kudin Naseer na siyi engine Dina ba na Sha wahala kafin na iya siyan engine Nan da shi asirina yake rufe Dana yarana da Naseer ya gudu ya barni Dan Haka bazan iya Baki kudin Nan ba Naseer watansa bakwai da sati biyu kenan da tafiya Bai barni da ko sisi ba Umma a Haka na ringa bin gida gida Ina neman abincin da xamu ci kafin Allah ya dubeni ya kawomin hanyar Dana samu kudi har na siyi engine dinan Umma kudina ne bana Naseer ba"

Nace na juya da Sauri Ina k'ok'arin nufar karamin palon ta jawoni da Karfin tsiya ta kawomin duka cikina na kauce cikin zafin nama

"Dan uwarki rashin kunya zakimin yaushe Kika zama Haka?mai Kika taka da har Zaki iya tsayawa agabana ki ringa fadar duk abinda ya fito daga bakinki indai ba karuwanci kikayi da Naseer baya Nan ba babu yanda Zaki iya siyan injina har biyu nama ji dadi da kikace ba kudin Naseer bane duk lokacin da ya dawo wlh sai.ya sakeki shegiya fitsarariya wlh zanyi maganinki a gidanan ba dai Dani kike ja"


To karashe tana Kara kawo hannunta jikina na kauce tare da nufar karamin Palo ina cewa Isihu ya zo ya sameni


Ina Shiga d'akina kuka na fashe dashi Dan har ga Allah Umma da Safiyya sun isheni na gaji da halinsu shekara goma Sha biyar Ana Abu guda sun ki rage kiyayyar da sukemin a yanzu ma da Naseer ya gudu ya barni bazasu sarara min ba Karo na farko da naji Haushin guduwar da Naseer yayi ya barni sosai na ringa Shan alwashin matsawar zasu cigaba da takuramin wlh siyar da gidan zanyi batare da saninsu ba na gudu da yarana Dan bazan tafi na bar musu gidan ba gwara na koma.garinmu na zauna da yarana a gidan mahaifina tunda Shi kansa Wanda nake zaman aurensa talauci yasa.ya gudu ya barni

Hawayena na share na fito na samu Isihu dake ta rafka Sallama na dauko wani Dan jaka da nake Tara kudina tare da rubber custard da gwangwanin cinikin da mukayi yanzu na zauna Akan tabarmar dake shimfide a kasan palon na hade kudin na kirga Naga ba laifi kudin da yawa.

D'agowa nayi nacewa Isihu

"Kasan Inda ake siyar da katifa babba irin wannan da muke kwana akai"?


Nace Masa ina Nuno Masa d'akin da muka kwana

Gyad'a min Kai yayi.

Ni kuwa nace yaje ya tambayomin ya dawo cemin yayi Bari ya fara min wanke wanke kafin ya tambayomin


Sai a lokacin na tuna baiyi wanke wanke ba Dan har wanke wanke Isihu kemin
Sanin kwanukan da muka Bata na dakina yasa na tashi na dauko kwanuka da kofuna da su Zahira suka ci abinci na kawo Masa shi kuwa ya kwashe ya fita wajen kitchen din ya hada wanke wanke ya fara Yi.

Su Umma kuwa sai harararsa suke jira kawai suke Naeema ta fito ta dauki abincin da suka zubawa magani suci tsabar mugunta ma yunwar suke ji amma sunfi San ta fara d'aukar abinci taci kafin su d'auko abincinsu.


Suna kallon Isihu ya Gama wanke wanke ya Kai kwanukan kitchen ya had'a kulolina masu kyau da yawanci ba a kitchen nake barinsu ba daki nake kaiwa har Wanda na zubawa su Umma abinci a ciki shi kuwa ganin akwai abinci a flask din Dana zubawa su Umma yasa ya bar abinci ya taho min da Wanda ya wanke

Bangarena Yana shigewa su Umma suka hau murna ya kawomin abincin da suka zuba magani.

Ina karbar kulolin na Kai d'akina shi Kuma ya wuce wajen Dana aikesa.

Yana fita Safiyya ta nufi kitchen cikin farinciki har.da.wake wakenta ta dauko flask din Dankali da tea d'in Wanda ba Dan rufewar ido ba da yaci ta Gane shine Wanda ta zubawa maganin Dan iya abincinsu ne a kitchen shayi ta zuba musu tana "Umma ai yau sai dai wata Naeemar Kuma su Naeema sai dai Kuma a lahira nidai tana tafiya kudaden Nan Zan debo shegiya Mayya a karshe dai zamu huta da naci"

Ta Kai Dankalin bakinta Umma kuwa tsabar murnar cikar burinta a koshe ma take jinta kunnuwa kawai ta baza tana jiran ta fara jiyo ihun Naeema.

Safiyya kuwa sai Loma Dankali take tana Shan Shayin dan murna ma tayi da Hajaran Tak'i cin abincin Dan ita Tana da balain ci hakane yasa ta cigaba da Jan Umma da Hira mutuwar Naeema



Cikin kankanin lokaci ta Gama cinye duk yawan Dankalin Umma kuwa sai data Kai hannu Dan ta dauko taga wayam ta hau surfawa Safiyya Zagin cinye Dankalin da tayi


Safiyya na k'ok'arin Magana taji wani irin azababen ciwon Mara daya kusa d'auke Mata numfashi


Hannu biyu ta Kai ta dafe cikinta tare da kurma ihu

Jkinta ya hau wani irin rawa da jijjiga Hajara kuwa hankali a balain tashe tayi kanta tana ke me Haka"?

Birgima kawai Safiyya ta ringa yi kafar ta na jijjiga kafin kace me wani irin mahaukacin jini ya balle Mata

Wani mugun ihu Hajara ta kwalla.

Ni kuwa da bacci ya fara fusgata ihun Umma yasa ni mik'ewa hankali a tashe nayi waje da Sauri.

Umma kuwa ihu take Tana "Abincin Naeema Kika dauko Kika ci Safiyya na Shiga uku na lalace"

Ni kuwa jikina ne ya hau rawa Dana ga irin jinin dake zuba a jikin Safiyya da cikin ta ke wani irin zillo shi kadai.

Cak na daskare waje da naji maganganun da Umma keyi cikin fitar hayyaci Ashe Ni suka so naci abincin Nan bansan sanda na durk'ushe wajen kuka na kwace min ba Wai Mai nayiwa mutanen Nan suke Neman rayuwata.


Da yanzu Ni Zan ringa zubar da irin wanan jinin da Safiyya ke zubarwa toh garin ya ma.suka dauko abincin da da kansu suka zuba maganin

Ina kallo Umma ta shige daki aguje tana Shiga d'akin cikin rawar hannu ta d'auko Abunda suke turarawa ta zuba a bakin tukunya jikinta sai rawa yake tana Shugaba ta rufa Mata asiri yarta zata mutu

Sai da hayaki ya gauraye d'akin ta bayyana cikin ihun kuka Tana ta taimaka Mata Safiyya ce taci abincin da suka barbadawa magani

Jini sai zuba yake a jikinta.

Shugaba b'acewa tayi Hajara ta Kara kwashe da ihu da kuka bayan Yan mintina sai ta Kara bayyana ta mik'a Mata wani ruwa a kwarya tana "Kiyi Sauri ki zuba Mata a jikinta"


Wani irin fusga tayiwa Kwaryar Bata tsaya jiran sauran zancen ba tayi palon tana zuwa ta watsawa Safiya da jikinta ya Dan fara saki jini kuwa Kamar an yanka Dan Saa sabida yawa.

Take kuwa jinin ya tsaya.

Safiyya tayi wani irin fari fat Kamar matacciya idan ba Kura ido kayi ba zaka dauka mutuwa tayi.

Wani irin Ajiyar zuciya Umma ta sauke ta dago da rinannun idonta ta kalleni da Nima ita nake kallo


Idan a da ne kallon Nan da takemin na iya sawa na fara nakudar da ban shirya ba

Tana k'ok'arin Magana na Riga ta fara magana kasan zuciyata Ina Jin dadin tsorona daya ragu

"Umma Raina a hannun Allah yake ba a hannunku ba duk yanda Ku so ku kasheni idan lokacin tafiyata baiyi ba babu yanda zakuyi Koda kuwa zaku Haka ramine ku binne ne duk tsawon lokacin nan Umma da kukemin abubuwa Allah na tsallakar Dani yaci ku hakura ku kyalleni Umma kin min horar yunwa ban mutu ba Umma kin kumburani ban mutu ba kin zuba min guba a abinci ban Sha ba kuka rufeni da duka Umma kin hayo yan d'abba har gida Dan su kasheni Allah ya tsallakar Dani kinyi abubuwa da yawa sabida kiga bayana Allah Bai nufa ba Mai na Miki da zafi Haka ?Mai laifina laifine Dan Ina Auren Naseer Umma tun lokacin Dana haifi zaheera Kika so rabamu Allah baiyi ba Taya Zaki raba auren da Allah ya raya bayan Zahira.na haifi Nadeeya Minal Humaira da Raheema ga cikin na shidda a jikina duk wanan Bai Isa ki Gane auren nida Naseer Bai Kare ba Sabida rabon dake tsakaninmu ya zakiji yau idan aunty Safiyya tayi aure mahaifiyar mijinta na gana ma ta azaba Tana neman rayuwarta yanda kike San Aunty safiyya har Kika rude da Kika ganta a cikin wannan halin Haka iyayena suke Sona Umma mutuwa ta rabamu Inda iyayena suka je kowa ma sai yaje Koda banida kowa Umma ai inada Allah daya halliceni Umma tunda na auri Naseer ba dadi nakeji ba ba wani dukiya na Tara ba shekara goma Sha biyar Ina cikin wahalar rayuwa Ina cikin tashin hankali da fargaba Mai zai sameni idan Allah ya tsallakar Dani daga wani mugun abin da Kika so ya sameni Umma iya sanina ban miki komai ba laifina daya Dana auri Naseer na Haifa masa Yaya Ni ba bakin haline Dani Ni ba wani abu nake ba da zakice shine dalilin daya sa bakya Sona Kika tsaneni Umma Akan tsanar da kikamin Kika yiwa Naseer Baki komai nashi ya Kare har sai data Kai shi da guduwa ya barni Umma yau idan kikayi nassarar kasheni menene ribarki Umma. A yau abinda ya faru yasa na Kara gasgata irin tsanar da kikamin a Kuma yau zan miki alkawarin rabuwa da Naseer har abada Umma kimin hakuri na haihu tukunna a yau Ina haihuwa naji kwarin jikina zan d'auki yarana na bar miki gidanan na bar rayuwar Naseer har abada"

Na karashe kuka nacin karfina.

Na dauka kalamai na zasu saka Umma jkinta yayi sanyi ko taji tausayina sai dai maganar daya fito daga bakinta yasa na tsayar da kukana Ina kallonta

"Ai ko kin tafi yanzu ban samu cikar burina akanki ba a sanadinki ba wahalar Da ban Sha akanki ba Dana ya daga hannu ya mareni ya nunamin ya gwammace ya rabu Dani mahaifiyarsa daya rabu dake fitarkin shine ki kwashe yaran naki ki bar gidanan kqmar yanda Kika fada idan ba Haka ba sai na samu cikar burina akanki Zan samu kwanciyar hankali bana kaunarki bana jin akwai ranar da Zan kaunaceki na gwammace ya auro koma wacece da dai ya cigaba da zama dake Ban taba ganin yarinya mai taurin Kai irinki ba gashi sai cika gidan Naseer kike da mata marasa tarbiyya masu irin halinki kiyi addua Kar wani Abu ya Samu Safiyya idan ba Haka ba zakiyi mamakin abinda Zan Miki

"Wane dare ne jemage Bai gani ba Umma mai zakimin da zai zame min sabo magani kuka zuba abinci Dan naci Allah ya tsareni ya Dubi zuciyata Ita data zuba garin magani da kanta Kuma ta d'auko abincin taci iya wanan ya Isa kigane Umma Allah ba azzallmin sarki bane Koda wani Abu ya Samu Safiyya ita ta jawowa kanta Dan ta Haka Ramin da Zan fada da zurfi sai ya zama itace ta fada"


Fuuu ta taso tayo wajena abinka da Mai ciki kafin na mik'e har ta iso ta rufeni da duka tana zagin uwata da ubana wai.maganar da nake Mata rashin kunya ce


Nidai fuskata da cikina kawai nake ta karewa Ina cigaba da Magana cikin kuka da a ce Safiyya ce zanyi k'ok'arin Rama dukan da tamin Amma wanan mahaifiyar Naseer ce bazan iya ramawa ba ko maganar da nake ta fada Mata baa San Raina nake fada ba Dan gani nake dgske rashin kunya nake Mata Amma Naga sai nayi maganar Zan jin sanyi a Zuciyata sai data gaji Dan kanta ta kyalleni na mik'e dak'yar na Shiga d'akina jikina namin ciwon dukan da Umma tamin.

Kuka nayita yi Ina tunanin Abunda ya dace nayi Sosai nake ji Kamar na hada kayanmu a goben Nan mu bar musu gidan.

Sai dai karatun yarana da suke tsaka da yinsa suna Kuma Jin dadinsa na hau tunani yanzu suna zango na karshe da zaayi canjen aji Zahira ta tafi primary 4 badan rayuwa data juya ba yaci ace tana jss 2 Nadeeya Kuma tana primary 3.

Shigowar Umma a fusace yasa na mik'e zaune Dan a kwance nake

dube dube da hau yi bance Mata komai ba ta hau daddaga kayana tana watsi dasu.

Nidai Ido na zuba Ina kallon ikon Allah sai data hargitsa d'akin ta juyo a fusace ta mik'amin hannu tana "Bani Kudi Zan Kai Safiyya asibiti Dan ta zubar da jini da yawa Ina binki cikin Salama Naeema kulleki a d'akin Nan na banka Miki wuta ba wahala zaimin ba Maza bani kudi karki batamin lokaci.

Sauka nayi daga Kan katifar na d'aga na Ciro kudin da na kakkasa a.karkashin katifar na zaro dayake ware biyar biyar goma goma.har zuwa hamsin nayi cikin Ikon Allah kuwa biyar biyar din na zaro.ina k'ok'arin duba kudin ta fusge daga hannuna tayi waje.

Inajin motsin fitarsu a daidai lokacin da Isihu ya dawo Ni kuwa na mike na fita jinin palon Naga Yana bi da kallo Ni kuwa na bashi umarnin ya wanke palon gabadaya Ina tsaye a bakin kofar karamin palon ya wanke palon sai karni ke tashi hakane yasa na saka ya amso min garwashi muka saka turare wuta Nasa ya Shiga karamin Palo na zubo Masa abincin da lokacin tafiya da ruwa.da.zobon yayi.

Sai daya fara ci ya ke gayamin kudin katifar dana saka ya tambayomin.

Ban ce Masa komai ba Dan yanzu Bata katifa nake ba wani abune Kuma a Raina.

Sai daya gama cin abinci ya fita da ruwa da zobon da sukayi sanyi sosai akwai wani shima dake tayashi dauka Suka tafi


Ina nan a zaune su Zahira suka dawo.

Sukaci abinci suka Kara gyara gidan har lokacin su Umma Basu dawo ba.

Har Isihu ya dawo ya Kara fita da wani ruwa da zobon.

Zahira da Nadeeya kafin su tafi islamiyya.suna ta Tayani markade sai da lokaci yayi suka.shirya.suka tafi.

Na cigaba da markaden wajen hudu da rabbi Isihu ya dawo lokacin na Gama markaden na hade Kan kudadena na zuba su a Leda Dana kasan gadon na canza musu wajen ajiya.

Na saka hijabina na kulle gidan na nufi makarantarsu su Zahira.

Mallam ala ramma shine babba a makaranta Yana da balain mutunci Isihu na saka ya kiramin shi

Yana zuwa na tsugunna na gaishe.shi shima sabida sanin darajar mutum Haka shima ya zub'e yasan komai a Kan gidana yasan babbnsu Zahira baya Nan Ni na fada Masa sabida shima sananne ne a unguwar Kar Yan unguwar suga ba namiji a gidan su Raina min hankali.

Koda yanzu shawara na yanke Na Masa magana Ina bukatar ayimin sauka a gidana ko na kwana bakwai ne sabida Allah ya Kara tsareni daga sharrinsu Umma da lokacin da Naseer ke Nan ne da sauki yanzu daga Ni sai yarana Ina bukatar tsari daga sharrin masu sharri.

Banma Gama iddawa ba yace min Kar nadamu zai turo yaransa su ringa zuwa karfe Tara suna karatun Qurani a gidan karfe goma sai su dawo zasuyi Haka har tsawon kwana bakwai zai Kuma ringa min addua daga nan Akan Allah ya saukeni lafiya ya dawo da mijina lafiya.

Godiya na ringa Masa na dauko kudin sadaka na bashi ya dage bazai karba ba ahaka na dawo gida Ina Dan Jin nutsuwa insha Allahu albarkacin Quranin da zaa sauke a gidan ba abinda su umma zasu min.

Tundaga nesa na hango masu markade da Umma da.safiyya a zaune a k'ofar Gidan.umma Nata magana tana yarfa hannu alamar masifa take sun dawo na fita na kulle gidan

Safiyya kuwa ta Yi wani sanyi kalau Dan kwance ma.take jikin Umma


Ina karasawa Umma.ta hau zagina wai.na tafi.karuwanci na kulle gidan bazata laminta ba daga Yau idan Zan tafi gantalina Kar na

5 Comments On NAGA TAKAINA
avatar
huda

1 year ago

Reply

Chapter 21

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment