Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Naseer ya dauki hanyar gida kuka kawai yake Yana tuno maganganun Mallam Musbahu.


Ki yafemin Naeema wlh bana cikin hankalina shine kalmar da yayi ta fada har ya Isa k'ofar gidansa.

Bai tsaya ma kwankwasa k'ofar ba yayi wa k'ofar wani irin Bugu ya fada palon hajara dake zaune a Palo da tukunyar kasarta tana ta murmushin cikar burinta ta mik'e da Sauri tana kallon Naseer daya fad'o palon kamar an jefoshi.

Naseer ko kallonta baiyi ba ya nufi d'akin Naeema aguje Yana kwalla mata Kira.

Ihu Hajara ta saka ta Sha gabansa hankalin ta a balain tashe adaidai lokacin da tukunyar kasr ta fado kasa ta tarwatse shi kuwa Naseer da idonsa ya rufe ya ture Hajara data Sha gabansa ya banka k'ofar d'akin Naeema ya tsaya a bakin kofa yana kallon Naeema data kumbure kamar ba ita ba zubewa yayi akan gwiwarsa jikinsa na kwasar wani irin rawa.

Kamar a mafarki Naga Naseer ya banko k'ofata ya tsaya a bakin kofa yana kallona.............


Duka page dinan wlh babu fiction
[6/26, 3:25 PM] +234 803 635 0240: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*



*Page 8*


Da kumburarren Fuskata nayi murmushin tare da Kara rufe idona ganin Fuskar Naseer da nake tunanin a mafarki yazo min Dan Ni nasan babu yanda za'ayi Naseer ya zo Inda nake naso ace na ganshi na bashi amanar 'ya'yana.

Zuwa yanzu farinciki barin wanan azababen rayuwa dana tsinci kaina nake Ina Kuma bakin cikin rabuwa da Nadeeya da Zahira ko ya rayuwarsu zata kasance bayan Raina.

Gunjin kukan Naseer ne ya saka na Kara bud'e idona na kalli Naseer dake durk'ushe a bakin kofa jikinsa na rawa ko ta Ina hawaye na zubo masa.

Umma kuwa Tana daga bayansa hankalinta a balain tashe sai rawa jikinta yake tana Kiran sunan Naseer da k'arfi Dan Had'uwar Naeema da Naseer na nufin duk aikin da tayi akansa ya wargaje ita kanta Naeema duk Shirin da tayi akanta wargajewa zaiyi Dan tasan Naseer sai yayi tsayuwar daka akanta.

Gashi tukunyar da ta tsaface mutane da Dama ya fashe Wanda hakan ke nuni duk a yau zasu dawo hayyacinsu waye ya Mata wanan danyen aikin Naseer ya dawo hayyacinsa Bata da burin daya wuce janye Naseer Kar ya Kai ga isa wajen Naeema dan ita tasan wahalar da ta Sha kafin ta iya shiga tsakaninsu da iya karfinta ta cigaba da Kiran sunan Naseer.


Ni kuwa ganin Naseer na ta kuka Yana kallona tare da Kiran sunana yasa na d'an runtse hannuna sabida Naga kodai ba mafarkin nake ba.

Ganin tabbas ba mafarkin nake ba yasa naji wani irin hawayen farinciki ya zubomin da Allah ya amsamin addua ta da zan Kara ganin Naseer na bashi amanar yayana kafin na mutu.



Ganin Naseer bashida niyyar tasowa sai sharbar kuka yake Yana Kiran sunana yasa na gwada magana

"Naseer karaso gareni Dan Allah na baka amanar Zahira da Nadeeya kafin na mutu"

Naseer mik'ewa yayi Yana Jin kafafunsa kamar bazasu d'aukeshi ba halin da yaga Naeema a ciki ya balain daga Masa Hankali yanzu Naeemarsa ce ta dawo haka.


Duk tsawon lokacin Nan tayaya take rayuwa a Haka ita kadai anya ya rik'e amanar da Iyayenta suka bashi kuwa Ina hankalinsa yake duk lokacin Nan ya iya manta matarsa uwar yayansa.


Kuka yake sosai jikinsa na rawa yanda ta kumbura yasa hankalinsa ya balain tashi a Haka ya Isa wajenta.

Tun kafin Naseer ya karaso wajena wani irin kuka ya k'wacemin sai da mutuwa tazo min Naseer zai zo wajena Mai nayi Masa Haka ya watsar Dani.

Hannuna daya ruk'o cikin nasa hawaye na ta zubar Masa yasa na fara magana Ina
"Haba Naseer Mai nayi maka Haka Dana cancanci Haka daga wajenka? Mai nayi maka da zafi Haka Naseer da zaka watsar Dani bayan kasan banida kowa sai Allah sai Kai idan wani Abu ma nayi maka Naseer Mai yasa bazaka gaya min na nemi yafiyarka ba Naseer kasan rayuwar da na ringa Yi kuwa a cikin gidanan sai daka ga mutuwa tazomin zaka zo Naseer"


"Bazaki mutu ba Naeema insha Allahu bazaki mutu ba yanzu na dawo gareki Naeema wlh duk abinda ya faru ba a cikin hayyacina nake ba Naeema ke Mai bawa wani labarine wlh ko dabba bazan iya cutar dashi ba ballantana ke da Kika kasance rabin rayuwata wlh Naeema sai a yau na dawo hayaccina wlh duk tsawon lokacin nan kaina a juye yake Dan Allah ki yafemin Naeema"

Mai ya kumburaki Haka Naeema Mai ya Sameki Haka? Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun"?

Kawai Naseer ke iya maimaitawa Yana tattab'a jikin Naeema dake kumbure.

Cikinta ma yayi wani irin tsini da kumburi kamar zai fashe

"Naseer ga amanar Zahira da Nadeeya Nan Dan Allah ka Kular min dasu karka Bari a cutarmin dasu Naseer mutuwa zanyi"


"Insha Allahu bazaki mutu ba Naeema Zaki samu lafiya insha Allahu yanzu ba abinda zai Kara samunki Ina Nan tare dake Zaki haihu lafiya kinji Naeemata"


Girgiza Kai kawai nayi Dan ni nasan Mai nakeji a jikina.

Naseer da Sauri ya shiga band'aki ya d'aura alwala ya fito ya shimfida Sallaya dama da akwai Qurani a d'akin ya bud'e ya tadda sallah ya fara adduar da Mallam Musbahu yace yayi sai da ya kusa awa a tsaye baiyi rukuu ko Sujadda ba Haka ake yin adduar sai da ya fara Jin Kiran Sallahr asuba yayi ruku'u da Sujjada yayi ta kaiwa Allah kukansa Yana nemawa mahaifiyarsa Shiriya da yafiyar Allah.


Ni kuwa kasancewar Naseer a d'akin da Karatun Qurani da ya fara Yi ya Sanya min wani irin nutsuwa bansan lokacin da bacci ya d'aukeni ba.


Naseer kuwa kasa ma fita massallacin yayi a d'akin yayi Sallahr Asuba daya iddar kuwa ya cigaba da Addu'a da Mallam Musbahu ya bashi.

Sai daya Gama wajen karfe bakwai ya bar Kan Dadumar ya kalli b'arin da Naeema take Yana Jin wani irin tausayinta Zahira da Nadeeya daya ga sun tashi yasa ya karasa Kan gadon ya sauko dasu.

Ya zauna a Gefen Naeema da har a lokacin a kumbure take ya fara totofa Mata adduoi Yana shafe Mata jikinta shi kansa yasan wanan kumburin ba na lafiya bane.

Ya dade Yana tofa mata adduoi kafin ya rik'e hanunsu Zahira yayi waje sai a lokacin Hajara ta fado Masa ko Ina tayi oho.

Bai kalli ma Inda d'akinta yake ba ya shiga dakinsa yyi wanka a gurguje yayiwa su Zahira brush ya fito ya shiga kitchen ya had'a musu breakfast dayake ba abinda Naseer bai iya ba


Har a lokacin baiji motsin kowa ba Yana gamawa ya fito daga kitchen din tare da breakfast din daya had'a ya nufi d'akin Naeema ya Ajiye ya had'awa Su Zahira tea har a lokacin Naeema bacci take hakan kuwa ya Dan kwantar Masa da hankali ya Ajiye abin karyawar ta a Gefen gadon ya fito waje.

Duk abinda Hajara zatayi Masa bazai tab'a iya canzata ba itace dai Mahaifiyarsa Bai Isa yayi fushi da ita ba.

D'akinta ya nufa ya tura k'ofar yaga ba kowa har su Safiyya ma Bai gansu ba hakane yasa ya fara mamakin Inda suka kwana ba Inda Bai duba ba Bai gansu ba.

D'akinsa ya koma ya dauko radionsa da cassette din dake d'auke da Karatun Qurani izzu Sittin ya jona radion ya saka cassette din aciki tare da kunnawa.

Take Suratul yunus ya fara tashi ya karasa wajen Naeema ya fara tashinta.

Kamar a mafarki naji Ana tashina daga d'add'an baccin daya d'aukeni wanda rabona danayi irin shi zan iya cewa tun farkon Aurena.

A hankali na bud'e idona Naga Naseer a tsaye akaina.

Na rufe idona na sake bud'ewa Ashe dai a gaske Naseer yazo dakina ba mafarki bane yanda gari yayi haske yasa nasan gari ya waye kuma ban mutu ba kamar yanda nake tunanin a jiya zan koma ga Mahallicina.

A fili na fara Hamdala Ina nanatawa jikina dayamin nauyi da nakejinsa a d'ad'aure yanzu duk babu sai kumburin dai da nayi da ban sace ba har a lokacin


Shima Naseer Tayani Godewa Allah yake

Na mik'e zaune Ina "Naseer ban mutu ba Alhamdulillah"

"Karki damu Naeema bazaki mutu yanzu ba insha Allahu.

Mik'ewa nayi da Sauri Naseer yayi saurin taroni Yana cemin nayi hankali nace Masa Kar ya damu Sallah kawai nakeso nayi.

Sai Dana yi wanka na wanke Bakina na daura alwala na fito na saka doguwar Riga na tadda sallah duk Sallar da banyi ba jiya na Rama na zo nayi Sallah Asuba Ni nasan ikon Allah yasa har yanzu nake rayye.

Naseer yana Gefen gado a zaune Yana kallona Yana ganin na iddar ya kawo flask din kayan karyawar gabana ya had'a.min shayi Mai balain kauri ga kwai shima da kaurinsa daya soya.

Tankwashe kafarsa yayi ya fara k'ok'arin bani.

Ni kuwa hawaye suka hau zubomin Ina ganin Kamar dai mafarkin nakeyi yaushe rabona Dana Sha shayi Haka yaushe rabona Dana ga mijina a d'akina ko Ina Umma take data min adduar Allah ya jikaina

Kofin shayin ya Kara dosar bakina dashi.

Ni kuwa na kau da Kai Ina "Ina Umma ka shigo d'akina har ka kawomin abincin karyawa"?


Wani irin kallo Naseer yayi min Yana "da ba'a baki abincin karyawar ne, "?

Ganin yanda idonsa ya kad'a yayi Ja da alamar Kuma dagaske Bai San Ana min horar yunwa ba yasa na karbi kofin shayin daga hannunsa na fara kurba batare da na sake cewa komai ba cikin kankanin lokaci na Gama shanyewa ya Kara hadamin wani na Kara shanyewa.

Dauriya kawai yake agabana Amma so yake ya kebb'e yayi ta kukan tausayina.

Bakin kofar da Umma ta binne Abu jiya na zurawa Ido inaso nayiwa Naseer maganar binne Abu da Umma tayi Ina tunanin yanda zan Gaya masa da yanda zaiji.

Naseer kuwa ganin ta ci abinci ya mik'e Yana Bari yaje ya dawo akwai abinda zaije yayi baxai Dade ba.

A tsorace na gwallo Ido Ina mik'ewa tare da waige waige Ina "Dan Allah Naseer karka Kara tafiya ka barni ka tafi Dani duk Inda zakaje ko ka kaini wani wajen.


Ido ya zubamin Yana kallona dayaga yanda jikina ke rawa cikin tsoro.

Hannuna ya rik'e ya ruk'o hanun Nadeeya da daya hannun yayi hanyar fita daga d'akin damu.

Kafin mu Isa bakin k'ofar nayi saurin tsayawa Dana tuna abinda Umma ta binne Ina tsoron na tsallaka Dan abinda ta binnen kamar Mai ciki.

Lafiya "?

Naseer yace ya juyo Yana kallona.

Inda ta binne abin na nuna Masa Ina "akwai Abunda Umma ta binne anan Ina tsoron tsallakawa"?


Wajen ya zubawa Ido batare da yace komai ba ya saki hannuna ya dauko wani abin labule ya tsugunna tare da Addu'a a bakinsa ya fara tone ramin.

Da addua a bakinsa ya zaro farin abin Yana Jin wani irin nauyi a kirjinsa Wai duk wannan tsafin mahaifiyarsa ce takeyi Bai San lokacin da hawaye ya hau zubo masa ba.

Shi kunyar ma Naeema yakeji data San wacece mahaifiyarsa waje yayi da abun ya k'ona ya dawo.

Ya rik'e hannuna mukayi waje dasu Nadeeya ya kaimu d'akinsa ya koma ya d'auko radionsa da har lokaci yake karatun Qurani ya Kure volume din radio ya kwantar Dani akan gadon

Yana "yanzu Nan zan dawo insha Allah akwai adduoin danakeso na karbo nayi Miki Dan wanan kumburin naki bana lafiya bane kiyi kwanciyarki anan Babu Wanda zai shigo zan kulle ku ta waje idan na dawo zan bud'e ku.


Sosai naji na rage tsoron danake Ina kallonsa ya fice daga d'akin tare da kullemu.


Yana fita Bai zame koina ba sai wajen Mallam Musbahu Inda ya bashi labarin yanda na kumbura.

Shi kuwa ya d'auko Masa ganyen magarya da ruwan zamzam da adduoin da zaiyi a cikin ruwan zam zam din da zai shafe jikin Naeema dashi.

Naseer Bai dawo gidan ba sai daya biya ta wajen da ake siyar da tumakai ya siyi wani katon tunkiya Mai dauke da ciki haihuwa yau ko gobe Kamar yanda Mallam Musbahu yace.

A hanyar komawarsa gida ya siya musu abincin da zasu ci.

Naseer na fita wani baccin ya Kara awon gaba dani Mai dadin gaske.


Sai danaji karar bud'e k'ofar na bud'e idona.

Tunda Naseer ya dawo Bai Kara fita Waje ba.

Adduoi kawai yake Yi da Karatun Qurani



Sosai na shiga tausayin mijina Sabida tsayuwar dayake Sha tun dayan dare Haka yake tsayawa da Qurani a hannunsa Yana karantawa duk kafafunsa sun kumbura Kuma nasan duk sabida Ni yake wanan adduar abincin da zamu ci kawai ke fita dashi idan ya kawo Mana sai ya Dora daga inda ya tsaya Nima baa barni a baya ba sosai Nima na dage da Addu'a Akan Allah ya saukeni lafiya duk da na rage kumburin sosai tunda Naseer ya shafamin ruwan zamzam da ganyen magarya.

Sosai nake mamakin Inda su Umma suka shiga Dan Ni nasan basa cikin gidan sau biyu Ina tambayar Naseer sai yacemin shima bai San Inda suka tafi ba.


Hajara da 'yan kungiyarta sosai ransu ya b'aci da wargaewar da aikinsu yayi tunda suke a kungiyar baa Taba samun wacce ta basu ciwon Kai kamar Naeema ba Hajara kuwa har da kukanta wiwi tana cewa shugabarta tayi mata mumumman aikin da zata kawo karshen Naeema data zame Mata karfen kafa har take neman rabata da Naseer akan ta Naseer ya rufe ido ya tureta.

Dayake mugaye ne tuni suka hada k'arfi Dan su kawo karshen Naeema ko ta k'ak'a su kasheta Amma Ina duk aikin da sukayi wargajewa yake sabida karfin adduar da Naseer yake yi.

Babu wacce Bata zama miciji da mage dan su kashe Naeema ba Amma suna zuwa gidan suke bacewa Sabida Karatun daya karade gidan.

Sosai suka cigaba da gwada saarsu akan Naeema amma duk a banza hakane yasa Hajara fara kukan bakin ciki Dan gani take Yar karamar yarinya Naeema Wai har ta gagareta Sam Bata yarda Allah ne ya shiga lamarin Naeema ba gani take akwai abinda Naeema ta taka shiyasa ta kasa cimma burinta akanta.


Sosai tsanar Naeema ya ninku a ranta ta ringa Shan manyan alwashin Halaka Naeema.

Naseer kuwa ita kadai tasan Mai zata Masa daya fifita Naeema akanta.

K'arfi da yaji suka kasa komawa gidan Sabida adduoi da karatun da Naseer ya dage da Yi daidai da su Safiyya suma ta saka su kungiya Wai duk Dan su ringa taka duk Wanda ransu ke so karsuyi tausayi Kar suyi yafiya.


Ranar da ya rage kwana biyu Naseer ya Gama adduar da yake yi da Rana Hajara tazo gidan da su Safiyya data daidai ci Naseer na girki Dan tana ganin komai ta mudubi ta shiga gidan.

Fuskarta a balain had'e Naseer na ganinta ya tsugunna ya gaisheta Bata amsa ba ta samu waje ta zauna dasu Safiyya ta kalli Naseer tana "daga yau ban yarda ka Kara kunna wanan radion ba idan ka Kara wlh xan maka baki.

Naseer Bai ce komai ba Dan duk yagane matsalar mahaifiyarsa abinda Bata sani ba ko Bai kunna radio ba zai iya karatunsa da kansa.

Hajara zaginsa kawai take Tana neman Yi Masa baki Bata da burin daya wuce Naseer yaje Massallaci ta fada d'akin da Naeema take ta caka Mata wukar Tsafi sai dai Kash ba Inda Naseer yaje a ranar Yana d'akin tare da Naeema da yayansa.

Sosai Hajara ta ringa neman hanyar da zata cimma burinta akan Naeema amma Naseer bai Bata wanan damar ba.


A ranar daya Gama adduar ya faki idon Hajaran ya fita Dan yaje ya yanka Tinkiyar ya binne.


Daji ya Kai Tinkiyar ya yanka ya binne.

Inda take Naeema ta fara Nakuda gadan gadan ta fara Sallati tana Kiran sunan Allah Dana Naseer da yayanta.

Hajara kuwa shigowarta kenan gidan taji muryarta .

Dan Bata kwana a gidan indai Naseer zai ware murya yayi karatun Qurani.

D'akin Naseer ta lek'a taga Naeema ita kadai.

Wani irin farinciki ya lullubeta ta fito da Sauri ta shiga d'akinta Dan ta dauko wukar tsafin ta.


Ni kuwa ganin Umma yasa naji duk azbaar danakeji ya d'auke diff daga yanda ta fita nasan zata dawo Kuma nasan zata iya kasheni.

Da hanzarin da bansan inadashi ba na bud'e window d'akin da babu bugla a wanan lokacin duk da window yamin kad'an kuma ya danyi sama ahaka na hau danne window na dura kamar ba Mai Nakuda ba Ina dura na gurje a kafata ban tsaya ba na fara gudu.

A daidai lokacin da Umma ta shigo d'akin ganin Bata gani ba ta lek'a ta window ta hangoni Ina gudu cikin tsananin bakinciiki tace da k'arfi "Allah ya tsine Miki albarka Naeema....[6/26, 3:25 PM] +234 803 635 0240: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*





*Da farko idan baku manta ba sau uku nace zan ringa posting a sati sabida tight schedules Dina but yanda kuka karbi labarin da Kuma comment dinku akan labarin yasa nakeso na ringa faranta muku yau muka fara page nine Amma I received alot of call akan Anya Haka na faruwa kuwa Anya ba Nigeria film na kwafa ba Kai anya zaa samu mace mara Imani Haka kuwa sai duk dariya ya kamani ai Mai Imani da tsoron Allah zai na ganin kamar mutum bazai yiwu ya aikata Haka ba kamar abin yayi yawa sabida wata data kirani daddare jiya zanyi bayanin nan acikin lavarin Nan na rage halin Hajara kashi hamsin Dan wasu bazasu yarda ba nasani a ranar da Nima Naeema ta fara bani labari wlh Tallahi tana kuka inayi na kusa sati ban dawo daidai ba sunan Hajara ban sakaya ba Amma sunansu Naeema na Dan Sakaya yanda na fara labarin Nan Allah ya bani ikon gamawa shine fatana ku pacigaba da bibiyar labarin kawai*😃😃😃


*Page 9*


Ba gabana nake kallo ba Sabida waigen Umma da nake hakane yasa naji nayi Karo da mutum a daidai lokacin da marata tayi wani irin murd'amin k'afata ta rik'e

Take na fara zubar da jini guda guda.

Na durk'ushe awajen Ina neman taimako.

Nasan dai mutane sun kewaye ni Ina Kuma kallonsu dishi dishi

Kafin idona ya Kai ga rufewa naji muryar Naseer akaina Yana kwalla min kira cikin tashin hankali.


Naseer kuwa Yana binne Tinkiyar yayo hanyar gida da saurinsa Dan Haka kawai yaji zuciyarsa Bata kwanta da barin Naeema ita kadai da Hajara ba.

Sauri yake ta zubawa sosai Dan Bai fita da mota da kafa ya fita.

Tunda ga bakin kofa gidan ya farajin fad'uwar gaba.

Inda ya fada gidan da Sauri tare da nufar d'akinsa daya hango a bud'e.

A daidai lokacin da ya shiga d'akin yaji Hajara na tsinewa Naeema albarka da wani irin kaifafen wuk'a a hannunta tana hucci.


Cikin wani irin tashin hankali ya je jikin window tare da matsar da Hajara adaidai lokacin da yaga ta bangaji wani ta Fadi kasa.
Kwalla Mata Kira yayi ya bar bakin window da sauri

Hajara kuwa ta Sha gabansa tana neman hanashi wucewa k'arfi da yaji takesan Naeema ta mutu jinin data hango a kafar Naeema ya balain faranta Mata Rai Bata San wani ya taimaketa.

Naseer cikin rufewar Ido ya kwace hannunsa tare da hankada Hajara yayi waje da balain Sauri ya zagaya ta bayan gidan

Da gudun balai ya Isa wajen Naeema har wani Mai mota ya tsaya wasu na neman d'aukarta.
Da saurinsu ya turesu yana Kiran sunan Naeema cikin tashin hankali ya rungume Naeema Yana "Dan Allah karki tafi ki barni Naeema na shiga uku Umma Mai nayi Miki Haka kike san kashe min farinciki na"


Dak'yar mutane suka bambare Naseer daga jikinta suka hau Masa fadar ba mutuwa tayi ba Suma tayi asibiti ya Kamata a kaita Sabida irin jinin da ke ta zuba a jikinta.


Naseer Bai iya d'aukar Naeema ba sabida rawar da jkinsa keyi cikin tashin hankali Sam bai yarda Naeema zata rayu ba ganin irin jinin da take zubarwa gani yake kamar Hajara ma ta Samu nassarar caka Mata wuk'ar.

Bai ma San lokacin da suka iso asibitin ba sai dayaji mota ta tsaya ya fita da Sauri kafa ba takalmi Allah daya taimaka ma asibitin da suke zuwa ne.


Da Sauri aka zo da gadon marasa lafiya aka Dora Naeema akai sukayi ciki da ita.

Naseer kuwa kamar ya bisu ciki sai da Wanda ya Kai Su yace ya kwantar da hankalinsa babu abinda zai faru insha Allahu.

Kafin Naseer ya hau Masa godiya Dan mutumin ya Masa mutunci ba kadan ba duk motarsa ta b'aci da jini.


Tuni Nurses suka rufu akan Naeema tana farfadowa ta cigaba da Nakuda tana Kiran Sunan Allah cikin minti goma ta haifo katuwar 'yarta da kana ganinta zaka San ta kusa shekara a ciki Sabida girmanta.


Naeema na Jin kukan jaririyar hawaye ya fara zubo Mata ta daga hannunta sama tana Godewa Allah Bata tab'a tunanin tana rayye zata haihu ba.

Tun basu goge jaririyar ba ta mik'a musu hannu ta karbeta.

Ta Kura Mata Ido tana Jin kaunar jaririyar na ratsa ta ko ta Ina har hawayen da take na diga a jikin jaririyar Sabida tuna wahalar da ta Sha da cikinta da itama jaririyar ta Sha duk ukubar Nan da aka gana musu Bai sa Yar ta mutu ba Allah yayi sai ta Rayu.

Bakinta ta kafa a kunnen jaririyar ta karanta Mata fatiha a kunnenta Dan gani take duk da ba zurfi tayi a ilimi ba fatiha data karanta Mata zai Kare Mata ita daga duk wani sharri ita kanta tasan ba ikonta ko dabararta bane yake kareta daga sharrin Hajara Allahu Arhaman Arahim Al malikul qudusu Sallam shi yake kareta.

Mik'a musu Jaririyar tayi ta kwanta tana cigaba da hawaye.

Tana Jin nurses din na Kara Mata jini sabida jinin data zubar

Suna ta hirar girman jaririyar da kyaunta.

Shigowar Naseer Kamar Wanda aka hankado d'akin yasa Naeema bud'e Ido tana kallonsa hawaye na cigaba da zuba a idon ta.

Naseer kuwa ajiyar zuciya ya sauke daya ga Naeema ta Haihu lafiya ga jaririyar an kwantar da ita a gefenta.


Hamdala kawai yake a zuciyarsa ya karasa Kan gadon a madadin ya d'auki jaririyar ya ruk'o hannun Naeema cikin nasa ya Dora hannunta a saman fuskarsa Dan bayaso taga hawayen dake neman zubo Masa daya kasa rik'ewa.

Ya kasa yarda mahaifiyarsa ke San kashe Masa mata har rashin Imani da kiyayyar da Mahaifiyarsa ke yiwa Naeema ya Kai ta nemi d'aukar ranta da tsohon ciki batare da tausayi ba shi kam iya saninsa mata da tausayi aka Sansu tayaya Mahaifiyarsa zata kashe mace Yar uwata da ciki har rashin Imaninta ya Kai Haka har yanzu yana cikin shock din ganinta da wuka Wai to Dama hake take ta yunk'urin kashe Naeema kafin ya dawo hayyacinsa.

Wai laifin Mai Naeema tayi Mata haka da zafi da har ya Kai data nemi d'aukar ranta.





Naeema kuwa Tana Jin danshin hawayensa a hannunta ta fashe da kuka daga ita har shi babu Wanda yayi magana sai da Naeema ga Gama Dan kanta

Ta Kira sunansa tana "

"Naseer na rasa Mai nayiwa Umma ta tsaneni bansan Mai nayi Mata ba take San kasheni Cikin Ikon Allah na Rayu har na haihu da kaina Wanda ba Haka Umma taso ba bansan Mai yasa take San rabuwar mu ba Amma Naseer tunda har Umma ta iya d'auko wuka Dan kawai ta kasheni zamana da ita wlh Tallahi hatsarine Naseer inasan na Rayu sabida yayana bazan Rufe idona sabida Kaunar San zama dakai na saka rayuwata a Halaka ba har yaushe zamu cigaba da irin wanan rayuwar Dan Haka Naseer Dan Allah Dan annabi ka sauwake min zan je na nemi Inda zan ringa Koda wanke wanke ne na rik'e kaina tunda banida kowa sai Allah Ni nasan Allah Yana sane Dani na gwammace nayi rayuwa da kowa akan nayi da Umma Naseer Dan Allah ka sauwakemin na samu kwanciyar hankali tunda Umma ta sakoni gaba da Ido daya nake bacci Ina tsoron Mai zatamin yanzu idan tayi nassarar kasheni rayuwarka zaka cigaba dashi Naseer Dan duk San da kake min bazaka bini ba ka hakura ka mata biyayya Sabida na tsira da Raina"

Rufe idonta tayi a lokacin da Naseer ya dago jajjayen idonsa Yana kallonta Wanda Hakan ya balain karya Mata zuciya itama duk maganar da take ba kaiwa zuci yake ba itama tasan bazata iya rabuwa da shi ba ta dai gaji ne kawai tana ganin kamar rabuwar tasu shine mafita a garesu.


Cikin karyayar murya daya Kara saka Naeema zubar da

5 Comments On NAGA TAKAINA
avatar
huda

1 year ago

Reply

Chapter 21

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment