Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Allah ya kawo maka mafita kayi hakuri da tambayar da zan maka kana Sallah kuwa"


"Ada inayi kafin na aurota sai Dana aurota ta ce Kar na sake Mata sallah a gida.

Wani irin nauyi yaji a kirjinsa ya zubawa baba Tijjani Ido da duk ya firgice

"Ka ringa sallah a boye kana gayawa Allah Yana jinka Yana Kuma sane dakai zai kawo maka mafita"

Sosai.Naseer ya bashi shawarwarin da take baba Tijjani ya fara aiki dashi yayi alwala ya shiga wani Massallacin daya gani a bud'e.


Naseer kuwa Yana Isa gida yajasu sallah shi kadai ya Sha lemonsa da Ayaba Dan mutanen da akwai azabar kunya Tama k'i bari su had'a ido balle ta saki jiki ta Sha lemon.

Shi kuwa ko a jikinsa Dan yasan kunya ke dawainiya da ita.

Daren farko yakan zama Daren tarihi ga maurata karfe goma.sha daya Naseer yayi Shirin kwanciya Yana cikin yiwa Naeema magana yaji an fara buga k'ofar gidan a haukace.


Mamakine ya rufeshi ya zura jallabiyarsa ya fito Yana "waye"?

Tara da bud'e k'ofar sakin baki yayi a lokacin dayaga Safiyya da Lami da uban Kaya

"Lafiya kuwa"?

"Eee Umma ce tace muzo mu Taya Naeema kwana idan an kwana biyu sai mu koma.

Daga haka suka shige gidan suka bar Naseer da sakaken baki a bud'e.


A takaice amarcin da Naseer baiyi cikin dadin Rai ba kenan dan Safiyya da Lami sosai suka sa musu Ido duk abinda akayi idonsu na Kai sai Kuma sun kaiwa Hajara rahota.

Naeema kuwa ko kad'an Bata tab'a damuwa ba Dan tana da balain hakuri idan kuwa Naseer ya fita ya d'an siyowa Naeema Abu tofa an shiga uku Dan sai sun gayawa Hajara ita Kuma sai ta Masa tas kamar ta dakeshi.......
[6/26, 6:15 PM] Buhari Yusuf IBr: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*


*Page 5*


Naeema sosai take tsoron Safiyya da Lami Dan sun girme Mata indai Naseer baya Nan sai dai tayi ta zaman d'aki.

Ahaka ma bata tsira ba haka zasuyi daidai a Palo suna zuba mulki tunda suka lura Bata da wayyo ga Kuma yarinta ga balain tsoro da take dashi.

Da tsoron da take dashi suke tak'ata yanda sukeso Bata tab'a d'aga Kai ta kallesu ba ballantana ta Kai kararsu wajen Naseer da zamansu Safiyya a gidansa yafi k'ona Masa Rai irin rayuwar daya so Shimfid'awa da Naeema idan ya Aureta ba irinshi yakeyi ba Dan Su Saffiya ma ba wani shak'arsa suke ba idan yaso tsawatar musu ma yasan Ransa sai ya b'aci.

Hajara kuwa ko tari Naeema tayi a gidan sai su Saffiya sun bata labari


Naseer ma in zaiyi kwanciyar Aure da Naeema a b'oye shima hankali ba a kwance ba Sabida fargabar su Saffiya na iya fad'o musu d'aki sosai Naseer ya takura da irin zaman da su Safiyya ke Masa a gida hakane yasa wani dabara ya fad'o Masa ranar da Naeema tayi wata biyu a gidansa daddare ya shirya ya nufi gidan Hajara.

Da isarsa kuwa ya sameta a zaune a Palo da wata doguwar mata sun saka ja doguwar Riga iri daya har yanayin Saka kwallin ga wani bak'in tukunyar kasa a gabansu an sosoka allurai haka a saman tukunyar.

Ko d'ar Hajara batayi ba ta matsar da tukunyar gefe ta kalli Naseer tana yamutsa fuska Dan ko kad'an Bata so zuwansa a yanzu ba taso sun Gama abinda sukeyi da wata kawarta Yar kungiya da hatsabibancinsu ya zo daya da rashin Imani da Suke ganin gidan Duniya gidan zamane dazasu ringa tsulla tsiyarsu San ransu.

Naseer kuwa wani Yam yaji a jikinsa ya d'auke idonsa daga Kan tukunyar ya Kara Sallama Ya durk'usa a kasa ya hau gaishe su.

"Lafiya naganka.yanzu"?


Naseer kasa magana yayi Sakamakon yanda kawar Hajara ta zubo Masa na Mujiya Kamar idonta ya fad'o kasa sau biyu suka had'a ido yaji kansa ya Sara masa take ya karanta addua a hankali.

Hajara kuwa ta kalli Kawarta ta tana "Kibi a hankali wanan D'ana ne nasan kinfi kowa sani Naseer ne Kar naji Kar nagani ki d'auke idonki a kansa"


Wani irin murmushi kawar tata tayi tana "Ai Sanin danki ne shiyasa kawai na tsaya iya kallo"


"Auzibikallimatillahi tammat Naseer ya hau Dan karantawa a fili.

Hajara kuwa ta daka Masa tsawa tana "Dalla gayamin abinda ke tafe da Kai ka tashi ka bani guri inada abin Yi"


"Umma Dama wani islamiyya Na samowa Safiyya da Lami shine nace Bari Nazo na fara fad'a Miki Dan Naga alamar basuda ilimi a cikin duhu suke rayuwa har yanzu Banga alamar suna maida hankali wajen Sallah ba"

Kamar wacce aka cakawa wuka haka Hajara ta mik'e Tana "Ban yarda ka samin Yara a makaranta ba nice Banga Daman saka su yanzu ba idan lokacin saka sun yayi zan saka su da kaina idan ma ka tsiro da hakane Dan su bar maka gida zasu bar maka gida a yau d'inan ba sai gobe.

A takaice da Wannan damar Naseer ya samu suka bar Masa gidansa kafin ya samu Sa'eeda sai dai kasan zuciyarsa Yana balain bakin ciki da halin mahaifiyarsa gashi yak'i yarda maganar da ake fada akanta Amma hakan Bai saka yayi Sake da Addu'a ba Dan bazai yaudari kansa ba Dole mahaifiyarsa tana cikin wani kungiyar daga irin shigar da takeyi duk dare.


Sai da Su Saffiya suka bar gidan Naeema ta samu Sa'ida take Kuma Jin a yanzu ne zatayi amarcin ta sosai Naseer ke tattalinta kamar kwai duk wani Abu na Jin dadi yagani sai ya siyo mata.

Ba abinda Naeema ta nema ta rasa tunda su Safiyya suka bar gidan babu Wanda ya Kara zuwa Sosai Naseer Yaji dadin yanda suka d'auke kafa daga gidan

Hajara ma tunda Naseer ya mata zancen Saka su Safiyya a islamiyya ta d'auke Masa wuta Gaisuwa kawai ke had'asu Dan ko yaje.haka zai karaci zamansa idan ya gaji sai ya tashi ya tafi bayan ya Ajiye Mata kayayaki da kudi.


Nan kuwa Hajara kallon Naseer kawai take Tana tarashi Dan sun gano a kungiyarsu Naseer na taimakon Baba Tijjani da Addu'a har Baba Tijjani na iya adduoi da kansa yanzu ya Kai ya kawo Baba Tijjani baya kwanan gidan a Massallacin yake kwana sai yayi kwanaki ma Bai zo gidan ba aikin Kuma da tayi akansa taga idan Bata dage ba warwarewa zaiyi Kuma ba kowa ne ya ja Mata hakan ba sai Naseer hakane yasa take fushi dashi sosai shi Kuma Bai sani ba.

A d'an Zaman da Naeeer yayi da Naeema ya fahimci Bata da ilimin Addini babu Kuma abinda ta sani Dan ko wankan tsarki ma shi ya koya Mata.

Hakane yasa ya Dan fara koya Mata gajerun surori da Addu'oi da kwakwalwarta zai iya d'auka sai dai Naeema tana cikin irin mutane Nan da ake cewa Slow learner hakane yasa ta kasa d'auka da wuri fatihar ma sai da suka kusa Sati.

Sabida Naseer na yawan tafiye tafiye hakane yasa Bai wani Samu lokaci ba ballantana karatun ya zauna a kanta.

Ko kad'an Naseer baiyi Sake da Addu'a ba Dan Dama shi akwai jajircewa Dan Bai fiye kwana bacci ba Rabin Daren yakan raya shi tun lokacin ma dayake yaro hakane yasa ya Riga da ya saba.


Indai ya kwana bacci to bashida cikakken lafiya.

Tunda ya kyalla ido.yaga Naeema ta samu ciki yaji kamar ya taka rawa hakane yasa ya Kara zagewa wajen kyautata Mata duk da ba abinda Naeema ta nema ta rasa kudi kuwa har ta rasa Inda zata ajiyesu Dan kullum in zai fita sai Ya Ajiye Mata naira Ashirin Wanda yake kamar Dubu daya na yanzu.

A cikin akwatinta ta ringa Tara kudin Inda ta ringa cin burin yiwa Iyayenta siyayya idan ta tashi zuwa gida Dan Naseer yace Mata sai ta haihu zata je gida.

Cikinta na da wata bakwai Naseer ya Gama Siyayyar kayan Jarirai cikin akwati haka ma Naeema sosai yake ji da cikin Naeema ya Kuma matsu lokacin haihuwar ta yayi Dan Yana so tana haihuwa ma ya sakata a islamiyya ba iya shi ba har Dana bokon.

Har a lokacin Hajara Bata sake Masa maganar komai ba Inda ya ringa mamakin Canzawarta sai watarana dayaje.ya Mata Sallama zai tafi yazo fita tace Masa

"Kai Yanzu ya dace ace tunda ka auro matarka Bata tak'a k'afarta tazo gidanan gaisheni ba Ni kake so naje na gaisheta kenan ko"?

Hajara tace Tana watsa Masa wani mugun kallo.

Naseer kuwa cikin kunyar rashin kyautawar da baiyi ba ya tsugunna Yana "Dan Allah kiyi hakuri Umma nayi kuskure laifina ne da ban Bata izinin zuwa ba Amma gobe insha Allahu zan kawota"

"Au Bata da k'afa kenan sai ka goyata ka taso ta a gaba zata zo ta gaisheni sai ma na roki gaisuwar ta ko Naseer"?

Naseer hakuri ya Kara Bata

Hajara ta girgiza Kai batare da ta ce komai ba sai da Naseer ya gaji Dan kansa ya mik'e ya Mata sai da safe.


Washegari kuwa kamar yanda ya alkawarta da sassafe yasa Naeema ta shirya har da sata ta soya Kajin da zata Kai mata.

Naeema cikin kunya cikinta daya turo sosai ta nufi gidan a lokacin Naseer Vespa ne dash.

Sai daya Dan rage Mata hanya duk da gidan ba nisa ya Nuno Mata gidan akan ta shiga Dan yasan idan ya rakata cikin gidan Nan ma case ne har Naeema ta doshi gidan ya kirata ta dawo.

"Ki kula da kanki Naeema"

Murmushi ta Masa ta gyada Kai har zata juya Naseer ya tsinci kansa da ce Mata "Ki kula da abincin da Zakici kinji idan an baki abinci kice bismillahi rahamanir Raheem ai kin iya ko"?

Da Sauri Naeema ta gyada Kai tana har Alhamdulillahi rabbil Ala meen na karanta zuwa karshe kafin naci abincin ko"?

Murmushi Naseer yayi Sabida yanda tayi maganar cikin yarinta ya gyada Mata Kai tana "eee a hankali Zaki karanta kar ki Bari kowa yajiki daga Nan sai ki faracin abincin"


Gyada Masa Kai tayi ta nufi gidan shi Kuma ya wuce Tasha karbar wani Sako.

Naeema da Sallama ta shiga gidan.

Ganin babu Wanda ta gani yasa ta cigaba da kwada Sallama

Ta kusa minti goma a tsaye tana Sallama kafin taga an d'aga labulen palon an zubo Mata Ido Ana kallonta.

Da k'arfi Dan cikin Naeema ya motsa gabanta yayi balain fad'uwa cikin tsoro Sabida Bata tab'a ganin Hajara ba sai Yau.


Hajara kuwa sosai ta gwallo idonta dake d'auke da kwallin tsafi tana kallon cikin Naeema da take ji kamar ta fusgo cikin ta bawa shugabarsu.

Naeema kuwa cikin rawar jiki ta zub'e a kasa da Kular hannunta ta hau gaisheta.

Kallonta Hajara ta cigaba yi dayi Tana Jin kamar ta shak'e Naeema ta rabata da numfashin jikinta.

Bata ji tsanar Naeema ba sai Jiya da Shugabarsu ke Gaya mata irin San da Naseer ke yiwa Naeema har tana ce mata Naseer zai iya sadaukar da rayuwarsa sabida ita a yanzu ma haka dukiyar Naseer duk akan Naeema yake tafiya Dan haka ta tashi tsaye ya kwato danta idan Naeema ta Haihu ta saka Naseer ya saketa idan ma Dan Dan dazata Haifa xaa fake sai a rabata da jaririn.

Naeema Bata Kara dagowa ba sabida yanda jikinta ke rawa a Dan karamin shekarunta tana ganin Abubuwan ban tsoro Amma mahaifiyar Naseer ta balain kad'a Mata ciki har lokacin cikin jikinta mutsu mutsu yake.

Hajara sai data gama ayyana mugayen Abubuwa ta saki labulen ta koma ciki babu alheri ko kad'an a zuciyarta Bata da burin daya wuce duk Wanda take muamalla dashi ya zama a kasanta tana mulkarsa haka ma taso Naseer ta ringa mulkarsa sai dai duk abinda takeyi a kansa ta kasa cin Galaba a kansa Amma ta silar matarsa zata ci Galaba akansa.


Sai da Naeema ta kusa awaya daya a tsakar gida kafin ta ce Mata "Jira kike na shigo dake ko kuwa"?


Da Sauri Naeema da baganta ya kage ta shiga palon har lokacin ta kasa daga Ido ta Kara kallon Hajara.

Hajara sai data Gama kare Mata kallo taga tsadadden zanin data daura a jikinta ga fatarta datayi fresh ta girgiza Kai tana

"Ke dago ki kalleni"

Naeema da Sauri ta daga kanta ta kalleta Sabida Allah ya zuba Mata tsoro

Tana Shirin maida kanta kasa da Sauri sabida yanda idon Hajaran ke tsorata ta

Hajara ta daka mata tsawa tana "Karki Sake ki sunkuyar da kanki ki kalli idona kiji Mai zan ce miki
Naseer Dana ne Ni nake da alhakin na zab'a Masa matar da nakeso ya aura na barshi ya aureki ne sabida wani dalili nawa Izuwa yanzu ai kinci rabonki yanda ya Kamata ko to kina haifar abinda ke cikinki ki gaggauta had'a kayanki kice ya sakeki Dan banida burin daya wuce Naga idan ya auri mace Tana haihu ya saketa Dana Yana da arzkiki bazan Bari mace daya ta nanike Masa tayi ta morarsa ba kinci rabonki haka Nan ki Bari wata itama ta zo taci nata Rabon dafatan kinji Mai nace"

Da Sauri Naeema ta gyada mata Kai tana hawaye Dan Abu kad'an ke sakata kuka.

Hajara Bata Kara ce Mata komai ba ta tashi ta shige daki bayan Yan mintina ta dawo da langa hannunta dake d'auke da tuwo da miya da yaji barbaden maganin da zai kashe abin cikinta Dan bama taso abin cikinta yazo da Rai.


Naeema duk da Bata Jin yunwa da Sauri ta karbi abincin cikin ikon Allah Bata manta da yin Bismillah ba har da fatiha har karshe ta fara cin tuwon.

Hajara kuwa kul ta Kure ta da Ido har ta Gama ci.

Daga Nan ta hau saka Naeema aiki sai data Gama gyare gidan tas sanan ta bar Naeema ta tafi bayan ta Bata manja Mai d'auke da maganin da zata samu Galaba akan Naseer tace ta ringa musu girki dashi.

Inaso mu tsunduma cikin labarin Dan Yana da Dan tsawo sai na danyi briefing.


A takaice lafiya Lau Naeema ta Haihu da taimakon Allah da na Naseer daya dage da Addu'a ba dare ba Rana duk da irin harin da Hajara tayi ta kawo musu Dan ganin jaririya Bata so da Rai ba hakane ya Kara dasa tsanar Naeema a zuciyar Hajara.

Sosai ta bud'ewa Naseer wuta akan ya saketa Amma yak'i ya saketan har ya gwammace yayi tafiya Mai nisa kafin ya dawo duk sabida ya kaucewa maganar Hajaran arzikinsa sai bunkasa yake har da San Naeema.

Yarta da aka sawa Zahira nada wata uku Allah yayi wa Aminat Rasuwa Inda sai da akayi Sadakan bakwai kafin Naeema taji labari sosai Hankalin Naeema ya tashi tayi ta kuka Haka Naseer ya d'auketa da kansa ya kaita garinsu.

Sosai Naeema tayi kukan rashin mahaifiyarta data ci burin Kara haduwa da ita.

Mahaifinta da shima yake dauriya Sabida ya Dade a kwance ba lafiya har ma yafi Aminat Jin jiki amma abin Allah ita tazo ta Riga shi tafiya.

Sosai ya roki Naseer rike Naeema da Amana ya had'asu ya musu naseeha.

Naseer anan ya tafi ya bar Naeema akan shima zaije Jos wani aiki idan ya dawo ya biyo ya d'auke ta.

Kwana ashirin da rasuwar Aminat Lawan shima ya amsa Kiran Mahallacinsa.

A shekarar Nan anyiwa Naeema mutuwar da sai da Naseer yayi da gaske ta dawo daidai Dan har kwanciya tayi itama a asibitin.



Bayan wata hud'u da rasuwarsu Hajara ta cigaba da matsawa Naseer akan ya saki Naeema da Allah ke ta kareta daga sharrinsu Wanda hakane ya ruru Mata wutar tsanar Naeema har tana tunanin itama Naeema ilimi ne da ita har take adduoi da take Kare kanta.

A irin wanan yanayin Naeema ta sake samun ciki Zahira nada wata takwas.

A daidai lokacin da Naseer ya Gina gidan dayafi gidan da suke ciki kyau suka koma.

Hajara kuwa ganin idan batayi dagaske ba bazata iya raba Naeema da Naseer ba yasa ta biyo ta bayan gida ta fara Jan Naeema jikinta sai data tabbatar ta saki jikinta da ita taje gidan tayi musu girki da kanta daya Sha barbaden maganin lokacin Cikin Naeema nada wata shidda.

Tsautsayi baya wuce ranarsa a ranar Naseer ya dawo a gajiye da yunwa Naeema na bashi abincin ya cinye tundaga lokacin ya fara Dan canjawa Naeema ahaka ma Wai dan Yana addua Dan so akayi ya mata saki uku har da duka Amma Allah baiyi ba.

Ahaka ta Kara haihuwa cikin ikon Allah ta Kara samun mace aka saka Mata Nadeeya zuwa Lokacin an Kai Hajara bango hakane yasa ta fusata suka dage ita da kungiya har sai da suka Yi wani irin aiki akan Naseer a lokacin suka ci Galaba akansa Sabida babu tsarki a jikinsa tun daga lokacin Naseer ya Dan fara wulakanta Naeema har Allah ya Kara kawo rabon wani cikin Inda Hajara kuwa tasha alwashin bazata haife cikin ba indai tana rayye take ta tattara ta dawo gidan ita dasu Safiyya da Tijjani gabadaya Dan Baba Tijjani ya Dade da guduwa daga Nan suka hau matsawa Naeema suka juyarwa da Naseer hankali ya fara manta Naeema a kansa ahaka Naeema ta kasance a mawuyacin Hali har dukanta Hajara keyi ta gaje gidan ta ringa laftawa Naseer abinci Mai barbade barbaden magani a yanzu haka cikin Naeema ya shiga watan haihuwa.

Cigaban Labarin


Nayi mantuwa sabida Ina Sauri mu cigaba da labarin

A shekarar da aka haifi nadeeya 1991 a shekarar Allah yayiwa Mahaifin Naseer rasuwa


Wanan kenan*NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*


*Page 6*


Cigaban Labarin


"Tunda Umma tazo min cikin Mafarki ban Kara Wasa da sallah ba Sosai Nake kaiwa Allah kukana cikin Sujjada Dan Nagaji da irin Rayuwar da nake a gidan Aurena k'arfi da yaji zaman d'aka ya aureni nida gidana horar yunwa kawai Umma kemin Bata da burin daya wuce taga yunwa ya zama ajalina tunda nayi yunk'urin zuwa wajen Naseer daddare ta Kara matsa min lamba wajen gana min azaba Dan bredi da lemon da nake samu na siya a b'oye yanzu duk ta hanani Dan kullum Tana zaune a Palo Dana bud'e kofa zata min kallon da zai kusa sakani fitsari a wando hakane yasa nake komawa d'akina aguje.

Dan wanke wanken da suke Sakani ma na samu naci ko da kanzo ne sun daina Sakani ruwan bandakina kawai nake Sha na rasa Mai taimakamin a rayuwata na Gaji da zaman takunkumin da nake a gidan Nan na Riga da na gwammace Dana gudu na shiga duniya da irin wahalaliyar rayuwar. Da nake a gidan Naseer kila a duniya na samu Mai taimakamin.


Kwana biyu kenan dana ji cikina ya daina motsamin nasan Kuma ya daina motsine Sabida abincin da bana ci duk da banyi karatu ba na iya lissafi nasan cikina ya shiga watan haihuwa har ya kusa shiga wata na goma Amma shiru har yanzu ban haihu ba wanan shine haihuwar da zanyi batare da na tanadi komai ba na samu ma Mai zanci a cikina tukunna kafin nayi tunanin tanadar wani Abu Dan Ma Allah ya rufa asiri ina da alkinta Abu akwai kayayakin Zahira da Nadeeya da suke ajiye Kamar ban tab'a amfani dasu ba.

Sosai na fara Jin tsanar Naseer a Raina gani nake da gangan ya shareni da gangan ya watsar Dani Mai nayi Masa haka Dana cancanci haka daga wajensa Mai nayi Masa da muna gida daya baifi taku biyar zaiyi zuwa dakina ba yak'asa lekoni.

Kuka nake sosai jikina na rawa sabida yunwar danakeji.

Mutuwa kawai nake fata ya daukeni da irin Rayuwar da nakeyi a gidanan.

Har gobe nakan yi mamaki wane irin zuciya ne a kirjin Umma da Bata tausayamin take burin na tagayyara da farko bana damuwa idan tace na haifi cikin jikina tagani yanzu kuwa Dana wuce watan haihuwa na fara tsorata da kalaman Koda mutuwar zanyi Ina fatan na ga abinda zan Haifa Ina addua ya zamto Namiji Mai Kama da Naseer.


Cikina daya harb'amin da k'arfi yasa na cije lebb'ena Ina Dan Jin dadi a raina hakan na nunawa Yana Nan lafiya yunwa yasa ya bar motsi Kamar wacce aka mitsina haka na mik'e duk da babu kwari jikina

Haka na nufi kofar dakina Ina gayawa kaina na rage tsoro haka na Nemo abinda zan sakawa cikina karshenta dai Umma ta jibgeni kamar yanda ta Saba Amma ya zama Dole na nemi abinda zan sawa cikina ko Dan jaririn cikina har zan murd'e kofar na fita na dawo Baya na dauki Hijabina na saka na bud'e akwatina na Ciro Naira Ashirin a cikin iirn kudin da Naseer ke bani a lokacin da yake kaunata Ashe dai kudin zasu min amfani.

Duk da gabana dake balain fad'uwa ahaka na bud'e k'ofar na fita na tsinci kaina da karanta Fatiha Dana balain haddacewa Dan shi kadai na iya sai suratul iklas da shima sai Dana Dage na iya.

Wani irin ajiyar zuciya na saki a lokacin danaga ba kowa a palon.

Sai kamshin abinci danake jiyowa daga kitchen daya saka cikina fara motsawa sosai naji wani irin bakar yunwa Ni danayi niyyar yin waje sai gani nayi na nufi kitchen.

Ba Wanda nagani a kitchen illa Dan madaidacin tukunya da aka Dan bude Mai dauke da farar Shinkafa daya saka yawuna tsinkewa gefe Kuma Miya ne dayaji namomi.


Bansan ya akayi na dauki tukunyar Shinkafar na Dora na miyan akai nayi hanyar dakina dashi ba zubawa nayi niyyar Yi a plate Amma sai na tsinci kaina da daukewa gabadaya na kai d'aki lokacin idona ya rufe da yunwa ballantana nayi tunanin idan aka kamani fa


Ruwan da suka dura a Robobi dake cikin fridge na koma na dauki guda biyu Dan karfinn hali irin nawa har da d'aukar bredi guda biyu dake ajiye a kitchen din.


Ina shiga dakina na kulle d'akin tun kafin na zauna na fara dibar Shinkafar Ina kaiwa bakina ko zafin abincin banaji tsabar yunwar danakeji.


Ina cikin ci naji an fara buga min kofa Muryar Lami Dana Safiyya naji suna ta auna min zagi suna cemin Barauniya wlh idan na Bari suka shigo d'akin sai na lahira yafini Jin dadi ya zaayi su Gama Shan wahalar girki na sace abincin.

Ko kulasu banyi ba na cigaba da cin abincina nasan ban Isa na guje musu ba Dole sai sun dakeni ko naci ko banci ba gwara ma naci abincin.

Koda sun dakeni zasu dakeni da kwarina.

Da hannu bibiyu nake tusa abincin duk uban yajin dake cikin miyar dayasa nayita kwarewa yanda suke jijjiga k'ofar.kamar zasu b'alla ne yasa na dage na cigaba da auna abincin bakina da iya karfina ko taunawar kirki banayi.

Cak na tsayar da cin abincin danaji kukan Zahira muryar Saffiya na tashi cikin balai

"Wlh idan baki bud'e k'ofar Nan ba yau kwana zanyi Ina dukan Zahira da Nadiya sai sunyi kwana uku basu ci abinci ba.

Wani irin mik'ewa nayi cikin tashin hankali Jin Safiyya zata dakarmin yaran da nake tunanin su suka ragemin a rayuwata.

Aguje na nufi kofar na bud'e.

Ban karasa bud'ewa suka banko d'akin suka shiga Safiyya da Lami kuwa suka rufeni da mugun duka suna kaimin naushi ko ta ina nidai durkushewa kawai nayi inata Kare cikin jikina Sabida Kar su kawo min duka sai hakuri nake basu.

Lami da nake tunanin sai ma tafi Umma mugunta idan ta samu waje naji ta harba min kafarta cikina.

Take na saki wani irin ihun azaba na wargaje a kasa.

Nadeeya da Zahira kuwa ihu kawai suke suna kuka suna rike Lami da Safiyya Nadeeya da k'ok'ari har da kankame Lami ta Kai Mata cizo a kafa.

Take Lami ta bar kaimin dukan ta dau Nadeeya tayi cili da ita.

Ihun da Nadeeya ta saki yasani mik'ewa tare da manta azabar danake ciki.

Safiyya dake ta kaimin duka na wawuro na damfara ta da kasa a zuciye

Ko a mafarki akace min xan iya karfin dagata sama karyatawa zanyi


Lami ma dake neman Kara kamoni na wawuro tukunyar Shinkafar da har lokacin da Saura na hau kwada mata akanta Ina ihun kuka.

Sosai idona ya rufe sabida tab'a min 'ya da sukayi.

Sai da Safiyya ta fusge tukunyar nayi wajen Nadeeya aguje da jini ke ta zubar Mata Sabida kanta daya fashe.

Bansan tashin hankali Hawa Hawa bane sai ranar duk dukan da sukamin nemansa nayi na rasa sabida tashin hankali ganin jinin dake zuba a Kan Nadeeya.


Ihu kawai nake Ina sun kashemin 'ya da hannu bibiyu na d'aga Nadeeya nayi waje Ina ihun a taimakamin.

Ina

5 Comments On NAGA TAKAINA
avatar
huda

1 year ago

Reply

Chapter 21

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment