Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kara kulle mata gida Agaban wayanda Suka kawo markade tayi ta zagina har na bude na Shiga suka shigo ni kuwa na kunna engine na fara markaden


Ahaka na bawa banza ajiyarsu Safiyya Bata iya magana sai Umma

Sai wajen Shidda na Gama markaden a daidai lokacin dasu Zahira suka dawo

Muka Shiga babban palon gabadaya Zahira na hada Ido da Umma ta zub'e ta hau gaisheta.

Kannenta take suma Suka zub'e suna gaida Umma.Minal ce ta tsaya cak Bata zub'e ba hasali ma cunno bakinta tayi ta kau da Kai.

"Shegu Yan iska marasa tarbiyya uwarku duk ta koya muku munafinci da gulma ke Dan uban uwarki wa.kike cunnowa Baki"?

Umma tace tare da mik'ewa su Zahira kuwa kafin ta karaso suka baje Suka shige Palona a guje.

Amma Minal ko gezau batayi ba Ina tsaye Nima a bakin kofar mamakin abinda Minal din tayi nake.

Umma kuwa Tana Isa wajenta ta rufeta da duka Ni kuwa na runtse idona inaji kamar Ni take bugu sai cewa Minal take tsinaniya Minal ko tari batayi ba ballantana tayi kuka kafa ta daga zatayi ball da Minal sai gashi kamar Jiya zaninta ya tadeta ta tafi gabadaya akan fusktarta ta Fadi.

Minal dariya ta kyalkyale dashi ta nufo palona a guje tare da tureni danake bakin kofa

Umma.kuwa ta dago tana rik'e da bakinta data Bugu sosai ta hau zagin Minal "Tana tsinaniya yarinya Mara albarka Zan kamaki idan uwarki ce ma ta zugaki kikamin Haka akanta Zan Rama ke Kuma zaki.bamu abinci muci ko sai mun roka"


Bance komai ba na juya na Shiga palona Ina zuwa na rik'e hannun Minal Tare da Jan kunnenta na hau Mata fadan rashin.kunyar da tayi wa Umma a yarana Ni nasan Minal nada zuciya bansan ta had'a har da rashin kunya ba

Hakuri tayi ta bani akan bazata sake ba

Ni kuwa na zuba abinci a flask.

Da Zan aiki Zahira ta Kai na tuna halin Umma na Kai abinci na ajiye musu a Palo Dan sun shige daki sai Masifa take ita kadai.

Daki na dawo nayi Sallah na juye Mana abincinmu a faranti muka ci gabadaya.

Ahaka mukayi sallar Isha ban Kara Jin motsin su Umma ba Ido na rufe Ina Jin gajiya da ciwon jiki Naseer na fad'omin a Rai inasan naji haushinsa a Zuciyata na kasa inaji kamar Inda yake wuya yake Sha.

Ahaka nayi zurfi a tunanin halin da Naseer yake da Kuma dalilinsa nak'i waiwayarmu motsin da naji cikina yayi ya Sakani sakin murmushi tare da bud'e idona Dan wani ikon Allah indai Zan Yi tunanin Naseer sai cikina ya motsa Ni nasan macece a cikina Dan na riga da na cire Rai da haihuwar maza inama cikin jikina namiji ne na haifo Mai Kama da Naseer.

Su Zahira Ina kallonsu Suka Gama home work dinsu Humaira da Raheema da Minal tuni bacci yayi awon gaba dasu.

Akan katifa ta kwantar dasu ta shimfida bargo ita da Minal suka kwanta a kasa.

Sallama Isihu danaji a Palo yasa na fita Inda yake sanarmin masu karatun sun zo


Iso nace ya musu na Kara shimfida musu tabarma a babban Palo

Suna shigowa Umma ta fito da Daurin kirji tana binsu da kallo ban kalleta ba nace su zauna su fara karatun

Kafin ma tayi Magana na koma ciki abuna

Ina Jin muryar ta tana Ashe maza nake kawowa gidan karuwanci ma Agaban idonta zanyi na shigo da Tika tikan maza hudu su kuwa Suna ganin alamar rigimamiya ce Basu saurareta ba Suka hau bud'e Quraninsu suka hau karatunsu.

Sai goma Suka gama suka tafi.


Na fito na kulle gidan
Hankalina a kwance a ranar ma ban wani Yi bacci ba sai Dana rayya daren.

Kafin bacci yayi awon gaba dani da asuba Ina iddar da sallah na Dora Mana abinci kamar dai jiya na Mana tazarce na Kai komai d'akina na ajiyewa su Umma nasu a kitchen.

Sosai nake taka tsantsan da duk abinda zanci.

Indai zanyi girki bana barin kitchen sai na Gama ko cokali na daina Bari a kitchen din sai risho


Tsakanina da Umma kuwa zagi ne da tsinuwa idan tsautsayi yasa yarana suka Dan tsaya wajen da take sai ta Kai hannu jikinsu

Safiyya kuwa Bata samu kwarin jikinta ba sai da aka yi sati biyu itama ta cigaba da Taya Umma wajen musgunamin Amma ban taba tanka musu ba indai Safiyya tamin sai na rama.

Alaramma har cassete ya aikomin Mai dauke da izzu sittin na siyo karamin radio na ringa kunnawa duk dare.


Ni kuwa ganin na samu kudi dayawa yasa na siyi katifar na saka a daya dakin har da sip Mai saukin kudi na sakawa su Zahira.

Cikina na da wata takwas da sati biyu na siyo kayan jaririrai na mata mai saukin kudi shima.

Sosai nake adduar Allah ya saukeni lafiya Dan insha Allahu indai na haihu na samu kaina sai na bar gidan Amma bazan tafi ba sai na siyar da gidan tunda takardun gidan. Na wajena.

Hakane yasa na cigaba da Tara kudina Banda dashin da nake.

Yanzu wani Abu da su Umma suka tsiromin idan nayi girki sai suce bashi zasu ci ba sai su zabi wani abincin suce shi zasu ci

Idan nace babu bazasu cemin komai ba sai sun ga Isihu ya dawo daga tallan Yana shigowa sai su kwace kudin

Sau uku suna min Haka Ni kuwa nace ya daina kawomin kudin ya ringa kaiwa matar Ala ramma Dan muna mutunci da ita Nan ma ban tsira ba idan nayi markade na Gama hada kudin sai Umma tazo da k'arfi ta rabani da wani abun.

Sosai zamana dasu waje daya ya gundureni na matsu na haihu na bar gidan.

Wanan ma Bai musu ba da suka ga Ina d'auke Kai sai Suka koma Kan zahira

Tana dawowa daga makaranta Umma da Safiyya zasu tsiri sakata aiki tayi.musu wanki ta wanke.musu bandaki sunayi suna zaginta wani zubin har duka suke Kai.mata tun Ina kawaici Naga abin ya fara yawa Dan ta Kai ma sai ta shirya zasu tafi islamiyya Haka Safiyya zata kirata ta hau sakata aiki karshenta makaranta da bazata je ba kenan tana Shan aiki.

Ni kuwa ganin abin yayi yawa yasa na fara takawa Safiyya birki idan ga saka ta aiki zance ta Bari sai ta dawo


Anan Umma zata hau zagina bana ce musu komai


Amma Zan rik'e hannun Zahira tabi Yan uwanta.

Idan Kuma ba ranakun makaranta bane a daki nake cewa tayi Zamanta karshenta sai Umma ta biyoni har d'akin ta min tas daga Ni har Zahira Tana Shan mugayen alwashi akanmu .

Ahaka Watarana lokacin daya kasance alhamis ba makaranta Ina kitchen Ina girki Zahira namin markade Nadeeya Kuma na wanke uniform din bokonsu.
Minal Kuma tana Taya su Humaira home work

Umma da Safiyya suka fito daga d'aki hannayensu d'auke da lodin wanki

Kansu tsaye suka.nufi wajen da Zahira take suke zuba kayan wankin a kasa Safiyya ta Kai hannu ta kashe engine tana "ke maza hada Mana kayan Nan ki wanke Mana yanzu yanzu"


Na gaji sun kaini bango


Ludayin hannuna na ajiye na nufi wajensu Ina "Nagaji aunty Safiyya Kun takura wa yata Kun hanata sukuni koni kuka bawa wankin Nan bazan iya ba sabida yawansu ku Bari na nemi almajiri yazo ya muku Zahira bazata iya wankin Nan ba"


"Wlh ita zata Mana wankin Dan uwarki ke Nan kin dauka tarbiyya kike musu yaranki ma baa Isa a saka su aiki ba"

Umma tace tana k'ok'arin jawo Zahira da har ta fara kuka jikinta na rawa.

Ni kuwa na shiga tsakiyarsu Ina "Wlh bazata yi wankin Nan ba"

A zuciye umma.ta saka hannu biyu ta hankadani

Yarana Suka saki ihu gabadaya nima na Gama sadakarwa fad'uwar Nan da zanyi na iya haddasa min komai amma a madadin najini a kasa sai ji nayi na an tareni ban Kai kasa ba.

Bud'e idona nayi na kalli Wanda ya tareni numfashina naji Yana neman daukewa da mukayi Ido biyu.......


🙆🏻‍♀️NAGA TA KAINA🙆🏻‍♀️
Page 1 to 30

Assalamu alaikum barka da warhaka🙋🏻‍♀️

Ta bangarena abinda na samu acikin wannan buk din shine

1-duk wani dabara da wayo naka da wani inda-inda bazai taba sawa ka gujewa kaddarar da Allah ya rubuto makabah ako'ina kake sai dai addu'ah tana ragemata kaifi sosai fiye da tinani mai tonani dan idan ba karfin addu'ah ba babu wanda zai taba tinanin naema zata rayu kafin ta haifi nadeeya kinga kuwa addu'ah ce taragewa wannan kaddar tata kaifi ta dawo mata da hankalin mijinta a ranar da aka yanke mutuwa zatayi

2- akwai riko da addini, sallah akan lokaci da yawaita addu'o'i da kuma rage yawan bacci da daddare, sallah shine jogsran
cewa kai cikakken musulmi ne sannan sallah akan lokaci yana tunkude masibu kala-kala. Addu'o'i suna rage kaifin kaddara wani lokacin ma yakan chanja maka ita daga mummuna zuwa kyakykyawa sannan takan shiga tsakanin nagari da mugu misali a page 30 din nan karfin addu'ah ne ya ceci naeema akan hajara da ta fadi kunkuru ya rike mudage da addu'a koda lokacin bamuda tsarki a jikinmu.

3- Hakuri wanda yaxama jagora akan rayuwar zaman duniya wanda shine yake zaune da naeema agidan naseer har wannan lokacin Allah yakara mana hakuri da imani

4- Biyayya koda kuwa wanda kake yiwa baya gani indai akwai hakkin biyayyarshi akanka to kayi iya bakin kokarin ka matukar batakaika ga shirka ba biyayya ma wani babban jagora ne arayuwa misali, koda babu auren naseer akan naemah a yanxu tinda har 'ya'ya suka shiga tsakani to akwai hakkin biyayya atsakanin umma da naeema Allah yasa mudace👏🏻

5- neman nakai rashin zaman banza da ace naema ta cigaba da zaman banza babu sana'a da ayanxu sun tagayyara arayuwa Amma dayake ita sana'a maganin takaici kuma idan ka dace da Allah ya sa maka albarka akai to wllh zaka samu rufin asiri acikinta. Ina bama 'yan'uwanmu mata akan mutashi munemi sana'a dan zaman banza na abune mai amfani bah.

Allah yakara rufamana asiri duniya da lahira yasa muyi kyakykyawan karshe yamana katangar karfe da makiyanmu aduk inda suke

Ina mika jinjinata ga sadnaf daya tamkar dubu Allah ya kara baseera ya biyaki albarkacin wannan fadakarwar da kike

Ina mika gaisuwata ga naeema jarumar mata Allah yayi ma rayuwar 'ya'yanki albarka ya karamana hakurin zaman duniya

Mrs naseer ceh👉🏻

*NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*


*Page 32*


*ZAFIN NEMA*
*baya kawo samu*

Lokacin da Naseer ya bar gida Bai zame ko'ina ba sai Tasha baiji tsoron duhun dare ko karnuka ba Haka ya rungume kayansa kala biyu ya rungume a kirjinsa ya samu waje ya zauna dan lokacin ba wani motoci Haka ya zabga tagumi Yana tunanin Naeema daya bari da Yara Yana tunanin Anya shawarar daya yanke Na guduwa ya nemi kudi shi ya dace yayi ko kuwa ya koma su cigaba da zama a haka.

Ko shi daya fito daga gida Bai San garin daya nufa ba.

Ahaka ya zauna zuciya fal da tunani har akayi Kiran a sallah asuba

Ya nufi Massallaci dake kusa da tashar yayi Sallah Asuba sosai yayi ta addua Akan iyalinsa Ji yake kamar Bai kyautawa Naeema ba kamar tafiyar tashi ba mafita bace a garesu Amma tunanin barin garin ya danne tunanin Haka a Ransa.

Karfe Bakwai yaga wani karamin mota na loda fasinja Abuja

Haka ya shige motar Yana tunanin zuwansa Abuja zai saka ya samu kudi.


Duk tafiyar da suka Sha zaune kawai yake a cikin motar Yana tunanin Naeema zuwa yanzu yasan ta tashi taga wasikar da ya bar Mata ko ya zataji a ranta.

Sai da wani a gefensa ya taba shi ya dawo daga duniyar tunanin Daya tafi

Nan fa Kuma daya Bai San Ina zai nufa ba Bai Kuma San ta Inda zai fara ba

Hakane yasa ya sauka daga motar ya samu wani benci ya zauna.


Yana kalle kallen mutane pure water kawai yayi ta durawa cikinsa.

A takaice Haka yayi ta zama a cikin tashar har tsawon sati guda Dan ya lura Abuja ba kamar Kano ba kowa shaanin gabansa yake.

Wani Abdullahi Mai lodin mota daga Kano zuwa Abuja ne ya fara Gane halin da Naseer yake ciki.

Dan ya Dan Saba da Naseer a Haka Naseer ya Dan bashi labarin halin da yake ciki shi kuwa ya Masa alkawarin taimaka masa ta hanyar nemo Masa motar haya ya ringa ja.

Cikin Sati daya da maganar Abdullahi ya had'ashi da wani Alhaji Idris wani Mai kudi dake da motoci da taxi na haya.

Take ya bawa Naseer mota da zai na Lodi daga garin kogi zuwa Abuja ya Kuma yanke masa kudin da zai ringa biyan shi.

Sosai Naseer ya hau murna kwana biyu da bashi motar ya fara aikin sai dai duk yanda Naseer yayi tunanin aikin tukin nada sauki sai yaga ba karamin wahala ne da tukin ba gashi bashida cikakken nutsuwar zuciya Dan zuciyarsa na kano gangan jikinsa ne kawai a Abuja.

Ko abinci baya iya ci Dan idan yazo ci ya tuna iyalinsa sai yaji cikinsa ya cushe ya kasa cin abinci Daddare kuwa tunani baya iya Bari ya samu cikakken bacci idan ma ya rayya daren Yana sallah ba nutse yake yin sallah ba sabida tsabar tunanin su Naeema.


Halin tunanin dayake ciki sai daya kusa saka shi hatsari sau da Dama Inda tuni fasinjoji suka fara Gane shi indai motarsa ce bazasu hau ba sai su ce Yana tafe yana tunani.

Ahaka Watarana garin tunanin ya bugi motar wani Mai kudi Wanda ya Masa asarar glass din gaba sai gashi case din sai daya kaisu ga tafiya police station Alhaji Idris na zuwa motarsa kawai ya karba ya Kara gaba.

Karshe dai sai Dan kudin da Naseer ke tarawa ya biya mutumin kudin glass din motarsa.


Wata biyar da yayi a Abuja a wahalce yyi shi cikin tsananin wuya duk inda ya Kai ga fara wani Abun sai wani sanadin yazo kudin ya tafi.

Yayi garuwa,ya siyar da bonse ya siyar da ruwan Sanyi ba irin Sana'ar da baiyi ba Amma abinda yazo nema a Abujan Bai samu ba ahaka a garin siyar da bonse ya hadu da wani shima dake yawan wucewa ta danger da yake tsayawa ya siyar da bonse yayi parking ya fara tambayarsa ya iya tuk'i

Gyad'a Masa Kai yayi da Sauri.

Kamar Wasa ya zama driver mutumin ya Kuma barshi yake kwana a boy's quaters din gidan

Sai dai rashin nutsuwar zuciya da tunani iyalinsa yasa ya kasa maida hankali a Haka ya Kara cin wata uku da sati biyu a gidan.


Mai gidan kuwa tuni ya Gane Naseer Yana cikin matsanacin damuwa Dan duk Wanda ya San Naseer idan.ya ganshi bazai Gane shi ba sabida yanda ya rame ya lalace ga kasumba ya rufe masa.fuska har wani Dan tsufa yayi.

Cikin tausayawa ya kira Naseer ya hau tambayarsa Mai ke damunsa Haka cikin karayar zuciya Naseer ya fara bashi labarin yanda ya baro iyalinsa sabida talauci.

Yana bashi labari Yana kuka

Shima sosai ya tausaya Masa Inda ya Shiga d'aki ya d'auko kudi Yan dari bibiyu na Dubu dari biyu da a lokacin kudi ne Mai yawa da zai Isa Naseer yaja jari ya cika shagonsa.

Ya Ajiye a gaban Naseer Yana ya d'auka ya koma ga iyalinsa.

Naseer zubewa yayi Yana ta Masa Addu'a Yana ji kamar an tsoma shi a Aljanna.

Sosai ya ringa zumudi Yana murna komawa da zaiyi ga iyalinsa Yana kyautata zaton kudin da ya samu zai Isa yaja jari.

Yaso tafiya a washegarin daya samu kudi sai dai Alhaji Ismail ya dakatar dashi akan ya Bari sai wani satin sabida akwai kudin da yake sa Rai idan ya samu zai Kara Masa baa San Ransa ba ya hakura ya Kara cin sati daya duk a takure Wanda yayi daidai da cikarsa wata takwas da sati uku


Gabadaya hankalinsa yayi gida Ido biyu Ido rufe Naeema yake gani da yayansa a cikin mawuyacin Hali hakane yasa Bai tsaya jiran Alhaji ismail ba ballantana ya Masa Sallama ya kwashi kayansa da kudi ya nufi Tasha da asusuba.

Karfe Takwas suka dau hanyar kano sai dai gani yake kamar ba Sauri driver yake ba.

Suna dab da shigowa Kaduna yaji motarsu taci wani irin birki kafin su ankara mutane masu sanye da bakakken Kaya sun zagaye su
Da manyan bindigogi.

Tuni suka bud'e motarsu suka hau fito dasu Naseer kuwa sallati kawai yake.

Duk kansu a sunkuye Barayin Nan suka caje kayansu suka kwashe komai nasu.

Basu iya dagowa ba sabida bindigar da aka Dora musu akai ahaka suna ji suna gani suka rabasu da komai suka haye motarsu suka tafi


Sallati da ihu kawai Naseer ke yi kamar ya haukace.

A takaice a Haka suka hau motar suka nufo garin Kano wajen uku da rabi ya iso.

Sam hankalinsa ba ajikinsa ba a tashar ma.wani ne ya taimakawa.Naseer da kudin motar da ya iso gida kafarsa ma ba takalmi.

Sai dai Yana isowa unguwarsu tundaga nesa yaga yanda gidan nasa ya canja ya Sha gyara tuni gabansa ya yanke ya Fadi Yana tunanin kila Ma talauci yasa Naeema ta siyar da gidan.

Ba dai ta gudu itama da yaran ba hakane yasa ya taka da sauri ya Isa k'ofar Gidan ya tura da k'arfi a daidai lokacin da Hajara ta hankado Naeema ta fado jikinsa.ya cafeta

"ABBAAAA"


Su Zahira sukace da ihu a lokacin da idonsu ya sauka Akan Naseer da ya zuba min Ido kamar yanda na zuba Masa Ido Ina ganin kamar a mafarki nake ganin Naseer ba gaske ba

Fusge jikina nayi daga nasa nayi hanyar cikin gidan da Sauri na shige adaidai lokacin dasu Zahira suka rungumeshi suna ihun murna Raheema ce kawai Bata karasa wajenshi ba.

Hajara itama daskarewa tayi a tsaye a lokacin da Naseer ya shigo suna had'a Ido ta juya da Sauri ta nufi daki Dan Haka kawai taji Kuma tana Jin nauyin ganin da Naseer yayi Mata a gidansa bayan cika bakin da tayi akan bazata Kara tak'a kafarta gidansa ba.

Itama Safiyya bayanta tabi da Sauri.

Naseer kuwa wani irin Sanyi da nutsuwa ya ji Yana shigarsa a lokacin.

Da ya rungume yayansa a jikinsa.

Kasan zuciyarsa kuwa Allah Allah yake yaga Naeema da idonsa ya Gane masa ta na dauke da tsohon ciki Ashe Dama da ciki ya tafi ya bar Naeema.

Da Sauri ya cire su Zahira daga jikinsa ya nufi d'akin da yake kyautata zaton na Naeema ne da su Umma suka gaje.

Yasan yaga Umma Amma San ganin Naeema yasa yak'i Bari ma tunaninsa ya rabu gida biyu.

"Wai me Kika shigo daki a guje ne tsoron Yaya Naseer din kikeji ne ko me?


"Aaa Safiyya kunyar ganin dayamin a gidansa nake bayan na Gama Shan alwashin ba abinda zai saka na Kara tak'a k'afata a gidansa Kar ganina da yayi a gidansa ya d'auka banida wajen da Zan zauna ne kinsan na cicika Masa baki"

"Tab kiji ki Umma ai borin kunya zakiyi ki hade ranki idan ya gaisheki ma ki amsa da kyar yanzu Yana ganin kina Jin nauyi wlh Raina ki zaiyi kamar yanda Yaya Tijjani ya rainaki"


Tana rufe Baki Naseer ya turo kofa tayi Sauri ta Samu waje ta zauna tare da had'e Rai.

Sai Safiyya ce ta amsa sallamar tana kallon yanda Naseer ke mamakin ganinsu d'akin Naeema Amma ya hadiye mamakin da yake ya zub'e a kasa ya hau gaida Hajara data k'i kallon Inda ma yake sama sama ta amsa gaisuwar sa.

Safiyya tayi caraf ta fara magana tana "sati daya kenan da muka zo dak'yar na samu Umma ta biyoni da mukaji labarin Naeema Bata da lafiya sai da nayita rokon Umma Allah da annabi kafin ta yarda ta biyoni.

"Dama Naeema Bata da lafiya"?


Naseer yace hankali a tashe tare da mik'ewa da Sauri yayi waje batare da ya tsaya sauraron sauran maganar da Safiyya take ba.

Inda yakejin muryarsu Zahira yayi da Sauri sosai yaji dadin yanda aka gyara gidan b'angaren ma da Bai gyara ba ya gansa fes.

Amma Bata gyaran gidan yake ba ta Naeema yake.

Dakuna biyu dake jere ya shiga na farkon daya kasance nasu Zahira Yana daga labulen ya ga Naeema a zaune Akan katifa tana ta share hawaye daga labulen da yayi yasa ta dago ta zuba Masa Ido.

Shima idon ya zuba Mata Yana Jin wani irin tausayinta na nukurkusar koina na jikinsa.

Dak'yar ya iya daga kafa ya Shiga d'akin Naeema kuwa kukan da takeyi kasa kasa ta kasa dannewa ta fara yinsa a fili.

Da rarrafe ya karasa kusa da katifar ya ruk'o hannun Naeema cikin rawar murya ya fara Bata hakuri daya hannun nasa Kuma ya Kai cikin ta Yana shafawa.

A durk'ushen ya hau Bata labarin duk wahalar daya Sha daya tafi da yanda barayi suka tare su a hanya suka kwace Dan kudin daya samo musu.

Sosai Tausayin Naseer ya rufeni Dan ko Bai bani labari ba daga yanayinsa kawai nasan ya Sha bak'ar wahala Dan ba karamin Rama yayi ba.

Nidai ban iya bashi labari ba ya hau min tambayoyi game da rayuwar da mukayi ya akayi yaga na baro wancan d'akin na dawo Nan waye ya gyara gidan Ina muka samu kudi.

Ce Masa nayi ya Bari Anjima Zan bashi labari daga Haka na mike na nufi kitchen Dan na karasa girkina Inda Naga har Zahira ta karasa ta juye a kula har nasu Umma ta zuba musu.

Nadeeya Kuma nata markade.

Namu abincin na dauko na ajiye a karamin Palo Inda na tarar da Naseer a tsaye Yana ta kalle kallen gidan kamar bakonsa.

Su Minal kuwa sai danne shi suke suna Masa surutai.

Kiran Sallah Magriba ne yasa ya d'aura alwala ya nufi Massallaci cikin farincikin dawowarsa cikin iyalinsa dayaga alamar suna cikin rufin asiri sosai ya matsu yaji a Ina suka samu kudi Haka har da engine markade guda biyu.

Naseer na fita kuwa Umma ta mik'e da Sauri ta kalli Safiyya cikin b'acin Rai tana "Kinga Bai ma damu da ya bani hakuri ba ya nufi wajen Naeema Sabida yaji ance Bata da lafiya k'arfi da yaji yake nuna Kaunar yarinya Nan a fili Kinga fa yanda ya rud'e dayaji munce ba ta da lafiya.

"Hmm Umma Naeema fa ba Haka ta barshi ba tun lokacin da ya gwammace ki Masa baki Akan ya rabu da ita nasan ta asirce shi Dan Haka ki daina ganin laifinsa ba a hayyacinsa yake ba asiri aka masa"


Sosai ran Hajara ya b'aci da abinda Naseer yayi na nuna damuwarsa Akan Naeema sai alwashi take ci Akan Naeema Safiyya na zugata.

A faranti daya mukaci abinci da Naseer da ke ta washe baki kamar gonar auduga idan muka hada Ido sai ya sakarmin murmushi.

Nasan ba yanda zaiyi ne Agaban Yara da ya rik'eni a jikinsa.

Duk cika bakin da na ringayi na zanyi fushi dashi sai gashi Nima Ina cikin tsananin farinciki zuwan Naseer at least I felt Safe da dawowarsa (bansan yanda zan saka da hausa ba shiyasa na saka da turanci ayi hakuri)

Karfe Tara su Zahira sukayi bacci.

Sai Dana tofesu da Addu'a na fito daga d'akin tun tafiyar Naseer sai a yau zasu kwana su kadai.

A Gefen katifa na samu Naseer a zaune Ina shigowa ya mik'e ya ruk'o hannuna ya zaunar Dani a gefensa sai wani rawar kafa yake kamar Wanda yayi amarya Ni kuwa dariya yake bani ma Dan ni cikin jikina ma ya isheni.

Tambayoyin da yayi ta jera min Akan Inda na samu kudi.

Yasa na fara bashi labarin duk abinda ya faru bayan tafiyarsa irin wuyan Dana Sha da yanda na Sha laulayi Zahira ta kawo Mana shawarar siyar da ruwa da har gobe shi ya zame silar rufuwar asirinmu da yanda na Tara kudi na siyi engine daya har na Kara samun kudi na Kara siyan wani da yanda na gyara gidan.

Da zuwansu Umma da irin abinda suka ringa mun ba abinda na boye Masa.

Da har zuwan da yayi rigimar da mukeyi da su har ya kai Umma ga tureni ya cafeni.

Naseer sosai ya matse hannunsa cikin nawa idonsa ya kad'a yayi jawur sai sallati yake Yana jijjiga Kai Bai tab'a tunanin har yanzu su Umma Basu daddara ba.

Ni kuwa halin Dana ganshi ciki na b'acin Rai yasa na hau basa Baki duk da kasan Raina Ni nasan na Gama yanke hukunci rabuwar mu idan na haihu Amma bazan Gaya masa ba.

Daga rarrashi Kuma muka farantawa juna Rai duk da cikin jikina.

Sai da muka yi wanka bacci yayi awon gaba damu Mai

5 Comments On NAGA TAKAINA
avatar
huda

1 year ago

Reply

Chapter 21

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment