Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ina "Naseer ya zama Dole mu bar gidanan wlh tsoro nakeji sau uku kenan muna neman yn gobara Ina yawan mafarki Ina tsoron muna ciki da tsakar dare wuta ta tashi Dan Allah Naseer mu bar gidanan ko haya ka Kama Mana"


"Naeema ki daina Mana baki insha Allahu babu abinda zai Samu gidana idan bazaki Fadi alheri ba kiyi shiru Kuma Ni nasan duk sakacinki ne kila Abu Kika dora Kika manta dashi har gobara ya tashi ta Inda Naseer ke shiga ba ta Nan yake shiga ba


Nidai shiru na Masa har ya Gama fadansa
Tunda nake da Naseer bamu tab'a samun Sab'ani Mai tsayin wannan ba ahaka mukayi ta zama cike da fargaba yanzu kuwa ba karamin taka tsantsan nakeyi ba idan na Dora Abu akan wuta Zan iya cewa da Ido daya nake bacci
Sabida fargaba

Dak'yar na samu Naseer ya sauko daga fushin da ya hau.ahaka har muka samu wata biyu da gobarar da mukayi na shagonsa da gidansa.


Hajaraa ke zaune a palonta Safiyya da Tijjani suna ta Bata baki akan ta yafewa Naseer

Bata kulasu ba ta bawa banza ajiyarsu

Tijjani kuwa ganin Haka ya mik'e Yana zai tafi sai da safe

Umma.kuwa ta mik'a Masa hannu tana ya Bata Dubu ukun da ta tambayeshi.bata San iskanci ahaka tun baiyi aure ba yake neman ya ringa hanata kudi.

Tijjani kuwa hannu ya zura a Aljihu ya kirga Dubu daya Yana "Sai dai kiyi hakuri da wanan wlh hidima ce a gabana badan kin dage kinyi fushi da Naseer ba da ko Dubu goma Kika tambayeshi zai baki"


Tsaki tayi.ta fusge kudin daga hannunsa tana ya fice Mata daga gida

Shi kuwa yayi waje Yana dariya ya rasa Gane wane irin haline da Mahaifiyarsu.

Suna Nan a zaune har Sha biyun dare
Safiyya ta sako Jan doguwar rigarta

Hajara ma ta saka nata.

Safiyya na k'ok'arin yiwa Hajara magana kawai suka ga kitchen din gidan na ci da wuta kafin su ankara har wuta ta fara cin Ceiling din kitchen din .

Ihu Safiyya ga saka tayi waje.

Umma.kuwa da taso tsayawa yanda wutan ya Kama ko'ina gadan gadan yasa itama tayi waje tana mamakin Mai ya haddasa Mata gobarar Nan toh Mai hakan ke nufi.

Tana ji tana gani wutan ta cinye duka.gidan har da mudubinta a ciki sosai hankalinta ya tashi da konewar gidan nasu.

Tsirarun mutane ne suka ringa fitowa suna Mata jaje.


Safiyya kuwa cewa take "Umma Kinga abinda nake Gaya miki ko idonki ya rufe kina San ganin bayan Yaya Naseer kina so kiga ya Shiga ifitilai alhalinn kin manta da kudinsa Kika siyi gidan toh idan ma.arzkinsa konasu kikayi toh gashi Nan har gidan da Kika siya da kudinsa ya kone


Umma Bata iya cewa komai ba ahaka har gari ya Dan fara wayewa makotansu sai ce musu suke su shigo daga ciki gidansu Amma fir Umma Taki kallon gidan kawai take daya ruguje katakwaye naci.

Wajen karfe shidda na safe Tijjani ya taho wajensu a guje kafa ba takalmi duk ya hargitse hajara kuwa ta d'auka labarin konewar gidanta ne.ya je.masa sai dai kalmar daya fito daga bakinsa ne ya kusa sata suman wucen gadi

Agabnta Tijjani ya zub'e Yana "Umma shaguna na duk sun kone haka kawai wuta ta tashi da tsakar dare na Shiga uku Umma komai nawa Yana cikin shagon.


Ko biyar ban tsira dashi ba Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Tijjani yace Yana hawaye.


Safiyya kuwa ta daka tsalle cikin tashin hankali tana asirinmu ya tonu Umma kin jawo Mana.........[6/26, 3:37 PM] +234 803 635 0240: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*


*Page 25*

Wani irin fusga Hajara tayiwa Tijjani cikin tashin hankali tana "Kana da hankali kuwa ko mafarki kake tayaya shagonka zasu Kama da wuta abinda ya rage mana kenan fa da Kai na dogara fa na Shiga uku Ni Hajara Mai ke Shirin faruwa Dani Banda Tijjani fa nace"


"Kikace me Umma zargina ya tabbata Umma wlh kina da hannu a konewar shagon Yaya Naseer da gidansa da
motarsa Umma
,Umma sai danace Miki karkiyi Haka Naeema ce ta Miki laifi ba Yaya Naseer ba Umma karki ce min duk dukiyar Yaya Kika k'ona Ni nasan tunda Kika fara min boye boye nasan akwai abinda kike kulawa toh ga irinta Nan idan ma.da Yaya Tijjani kika dogara toh shima shagunansa ya kone tunda Yaya Naseer ne ya basa kudin"


Hannu Hajara ta D'ora akanta tayi zaman dirshan akasa.

Tijjani kuwa cikin rashin fahimta ya kalli Safiyya Yana "Bangane ba Wai Mai kike nufi ne Umma ce tayi wani Abu Dan arzkiin Yaya Naseer ya k'one ko me"?


Hajara ido ta hau kiftawa Safiyya.

Safiyya dake cike da balain haushin Hajara kau da.kanta tayi ta hau bawa Tijjani labarin duk abinda ya faru ta Kara da "tun Akan hanya nake Bata hakuri tana rantsemin sai Naseer ya talauce ya tsiyace yyi bara Naga dai idan ya talauce ya tsiyace muma sai ya shafemu data ga alamar bana goyon bayanta shine ta daina min maganar Ni dai daga abinda ya faru wlh nasan Umma ce silar komai.ta Kona arzkin Yaya Naseer a kungiya"


"Wane kungiya.kuma Mai nake ji Haka Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Ashe dai maganganun da ake Yi akanku gaske ne kenan Safiyya?

Safiyya sai a lokacin ta tuna Tijjani baisan duk suna cikin kungiya ba

"Umma Ashe dagaske ne labarin da nake ji a Calabar kina cikin kungiya Umma yanzu Sabida rufewar ido da Baki samu yanda kikeso ba Kika k'ona dukiyar Yaya Naseer?Umma.ina tunaninki ya tafi Umma karki manta fa duk abinda kike takama dashi daga ke har mu wlh shine toh shikenan ai kin huta kin zama silar da na rasa komai nawa yanzu kowa sai yayi ta kansa dan wlh banida shi bazaki Sakani sata ba ko me Naseer yayi miki Bai Kamata kiyi Masa Haka ba Dan kawai yak'i rabuwa da matarsa"


"Marina fa yayi Tijjani Marina yayi Akan Matarsa har Ni Ina mahaifiyarsa ya daga hannu ya mareni"?

"Haka kawai ya mareki ba shake Masa Mata kikayi ba kina neman kasheta Kuma Naga Yana ta baki hakuri akan Bai San ya mareki ba Amma duk da Haka shine Kika k'ona dukiyarsa toh sai ku nemi gidan Zama ai tunda kunsan nima a shago nake zaune Allah Kuma ya shiryeku ya sa ku Gane gaskiya "


Daga Haka ya fara k'ok'arin juyawa Safiyya ta tsayar dashi da Sauri tana "Yaya ka taimaka.mana da kudin mota komai namu ya kone fa"

Wani irin kallo ya wurga Mata yaja Tsaki ya tafi

Safiyya ta juyo a fusace ta kalli Hajara tana "Sai kisan yanda Zaki damu ai"

Safiyya Shugaba bata min adalci ba wlh ba Haka mukayi da ita ba"


"Ahap kenan kece Kika k'ona dukiyar Yaya Naseer Umma"


"Aaa na dai fada Mata inaso ya Sha wahala rayuwa idan kudi ne ma yasa Naeema taki rabuwa dashi ya rasa kudin Tijjani shi Kuma yayi kudin tace na bar Mata komai a hannunta bansan Haka abubuwa zai kasance ba"


"Duk wannan balai ke Kika sakamu a ciki Umma Naeema ya Kamata ta Sha wahala ba Naseer ba Naeema ce take ja dake Kuma duk tsawon lokacin Nan kin kasa komai a kanta Haka kawai muna zaune kin janyo Mana balai rufin asirinmu daya shine gidanmu na Calabar da asirinmu ya tonu.


Mik'ewa Hajara tayi tana yanzu Bari na nemo Mana kudin mota a mak'ota mu samu mu tafi daga baya ma san abinyi"


Daga haka Hajara ta nufi gidan mak'ota sai data shiga gida.hudu Bata samu ba sai a gida na biyar ta samu kudin.

Ahaka suka.nufi tasha daga su sai rigar.jikinsu Safiyya kuwa sai Masifa take Hajara kuwa Bata ce komai ba Dan tayi nisa a tunani.

Da yamma Likis Suka Isa Calabar sai dai da isarsu Suka sake tarar da wani sabon tashin hankali gidan da Naseer ya bar musu katoto naci da wuta mutane sun zagaye gidan suna ta watsa ruwa.

Hajara jiki na rawa suka fito daga motar aikuwa ganin yanda wuta keci yasa ta cire zaninta ta fara kurma ihu tana a taimaka Mata Dan karamin gidan Naseer ma ta siyar dashi tuntuni.

Ihu take sosai Safiyya kuwa ta Dora hannu aka itama tana zunduma ihun


Mutane sai basu baki suke suna Haka kawai suka ga gidan ya Kama da wuta Hajara Kamar tayi karamin hauka.har wani rukota ake tana fusgewa Bata tab'a tunanin Abubuwa zasu juye Mata Haka ba

Bata kawo Abinda tayiwa Naseer zai shafeta Haka ba ta d'auka shi da Naeema ne kawai zai shafa Tijjani shi Kuma ya cigaba da kula dasu sai gashi tun ba'aje koina ba komai ya juye.

Allah Allah kawai take dare yayi ta nausa daji wajen shugabarsu.

Safiyya kuwa ce wa take ta cucesu.

Dayake An Dan San Hajaran acan hakane yasa ta samu wayanda suka dan taimaka Mata da wajen zama na Dan lokaci kafin su san abin Yi.

Sosai Hajara taci kukan yanda abubuwa Suka juye tsanar Naeema na Kara sab'untuwa a ranta Dan gani take duk ita taja Mata wanan masifar


Karfe Sha biyun dare ta fito daga gidan mutane Safiyya kuwa Taki binta sabida takaici.

Tana Shiga daji ta fara yarensu na tsafi.

Sai data Dade tanayi kafin shugabarsu ta bayyana a gabanta da fitilar kwai ranta balain b'ace

Bata Bari ma Hajara tayi Magana ba ta hau magana tana "mun cireki daga kungiya mun karbe karfinmu sabida kinyi sakacin da mudubinmu ya kone Dan Haka Abu daya kawai zan iya Miki shine idan wani Abu ya taso miki.ki zo ki fada min Zan Yi iya k'ok'arina ki samu cikar burinki ita Kuma matar danki yak'i ne tsakanina da ita Ina dab da samun cikar burina akanta ki juya ki tafi Hajara abinda kikeso na Miki ba Abunda Kuma Zan iya Yi akai"

Daga Haka ta b'ace Bata Bari ma Hajara tayi Magana ba.

Haka Hajara ta Kara dawowa tana rizgar kuka.

Sosai zuciyarta ta Kara taurara da mugayen alwashi duk akan Naeema da Bata ji ba Bata gani ba


Safiyya Kamar ta rufe Hajara da duka Dan gani take duk ita taja musu wanan masifar.


Hajara kuwa Bata ita take ba abinyi kawai take tunani

"Nidai Umma Ina Samu kudin mota wlh gidan Yaya Naseer Zan koma can Kano Dan shine dai gatanmu a yaushe zamu cigaba da zama a gidan mutane nasan ai Yana da Dan sauran Canji

"Bashida wani sauran Canji Safiyya lokaci kalilan ne shima zai dawo Kamar mu gwara mu Kara sanin abinyi

Umma wlh kin cucemu yanzu har yaushe zamu cigaba da zama a gidan mutane wlh komawa Kano ya Kama mu Dole Yaya Naseer da yaya Tijjani su San yanda zasuyi damu"


Naeema

Daga Ni har Naseer sosai muka dage da Addu'a Dan har lokacin ban fasa mafarkai ba Haka Kuma karamin Abu sai Naga kamar gidanmu zaiyi gobara yawan damun Naseer da nake da maganar yasa muke samun Sab'ani hakane yasa na daina Gaya masa.mfarkin da nake idan nayi kawai na tashi washegari Zan danyi sadaka.

A haka watarana da bazan tab'a mantawa ba bayan an iddar da sallah asuba Naseer ya dawo da wuri yacemin bacci yake ji ya kwanta Nan da Nan bacci yayi awon gaba dashi Nima Haka kawai naji bacci na cin idona Akan Sallaya baccin ya kwasheni.


Kamar a mafarki naji mutane a waje suna ihun wuta wuta wuta.

Amma abin mamaki na kasa bud'e idona sabida nauyi.

Sallatin Naseer kawai naji da k'arfi Yana Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun.

Dak'yar na bud'e idona Naga hayaki ya cika Mana daki na mike da balain sauri Ina sallati jikina na rawa Dan dakinmu ma ya fara ci da.wuta.

Naseer kuwa window ya bud'e ya fita aguje ya Shiga d'akin yarana da Suma bacci Mai nauyi ya daukesu.

Duk su ukun Haka ya rungumosu a kirjinsa Zahira na kamkame da hannunsa sai sallati take Zahira na ihu Ni kuwa numfashina ne ya ringa k'ok'arin daukewa sabida tashin hankali Kamar an Dasani na kasa motsi

Ahaka Naseer ya zura yarana ta window Yana ta min magana Dan ba Inda Bai Kama ba har k'ofar dakin Inda nake tsaye kawai da gadon ne Bai Kama da wuta ba.

Yana zura Raheema ceiling ya fado Kan katifar d'akin

Cikin zafin nama ya duro daga Kan gadon ya kama.hannuna Dan bbu ta Inda xamu fita sai ta window ahaka ya kamani ya zurani ta window Dan lokacin window ba Mai burgular bane wani ne Mai guda biyu haka Ana bud'ewa mutanen d'a zasu iya gane window.


Har lokacin ban dawo cikin hankalina ba


Yana durowa shima.kwanu da ceiling din suka ruguzo mutane kuwa da suka kewaye gidan Suka zo suka ja hannun Naseer da ya ji ciwo a hannu.

Suna barin wajen Gidan ya fara wani irin rugujewa wuta na tashi kamar an watsa fetur.

Motocin Naseer guda uku da komai.namu.muna ji muna gani Suka kone har lokacin bansan Inda hankalina yake ba Naseer kuwa sai Sallati yake hawaye na zubo Masa zuwa yanzu yasan mahaifiyarsa ce silar komai dake faruwa dashi.


A gidan makotanmu aka Kai mu dasu Zahira.

Inda aka ringa tausaya Mana da Wanan mumunan gobara daya tashi a gidanmu da aka rasa Mai ya haddasa shi.

Haka matan mak'otana suka zagayeni suka hau yayyafa min ruwa wasu na min tofi

Ina dawowa cikin hankalina na mike zumbur na fara Kiran sunan yayana ganin suna kewaye Dani yasa na saki ajiyar zuciya na mik'e da Sauri nayi waje kafa ba takalmi nesa da gidan na hango Naseer ya tsugunna mutane na kewaye dashi ya zubawa konannan gidanmu ido da babu ma abin mora a ciki.

Wani irin tausayinsa ne ya rufeni Mai ya rage mana yanzu Babu sai shaguna uku da gidansa na goron dutse da Bai karasa ba.

Ban damu da yawan mazan dake wajensa ba Haka na nufi wajensu Ina zuwa na fashe da kuka suka kuwa baje suna bamu hakuri akan mu yarda da kaddara.

Naseer Bai Dago ya kalleni ba na tsugguna agabansa Ina "Naseer Kayi hakuri Dan Allah ka yarda da kaddara Allah Yana sane damu Dan Allah karka saka damuwa a ranka"

Wani irin murmushi Mai ciwo yayi ya dago da jajjayen idonsa ya kalleni "Naeema komai Kika ga ya samu bawa daga Allah ne duk abinda ya faru Dani Allah ne ya hukunta zai sameni bansan Zan samu dukiyar Nan ba Allah ya bani Dan Kuma ya jarrabceni bazan yi fushi ba Zan Kara gode Masa da har mukayi irin wanan gobarar daga Ni har iyalina babu abinda ya samesu Alhamdulillah iya Rai da lafiya da ya bamu Naeema arzkine shika shikan musulunci akwai yarda da kaddara Mai kyau ko mara kyau Allah ya Mana zabin dayafi alheri nidai roko na a gareki shine kiyi hakuri da yanda rayuwa yake juyawa Dani mu rungume abinda kaddararmu yazo Mana dashi insha Allahu watarana sai Labari ku kwana a gidan Mallam hafizu ni.kuma Zan kwana a shagon k'ofar gidan gobe da safe zanje na na saka a Dan gyara Mana gidan mu na goron dutse danaso Umma ta koma ko iya katifa ce sai na saka Mana muna daga ciki sai mu karasa wasu Abubuwan tashi ki koma ciki"


Tausayin Naseer yasa na kasa mik'ewa idonsa kawai ya nuna dauriya yake kawai amma.yana cikin tashin hankali ahaka na mike na koma gidan a ranar naci kuka kamar Raina zai fita nayi nadamar dawowa rayuwar Naseer da zuwana yazo ya zame Masa masifa Taya Zan manta Naseer a rayuwata.


Naseer kuwa kamar yanda ya alkawarta washegari ya nufi goron dutse tsohuwar unguwar mu da mukayi gobara gidan dayake ginawa a kasan layin da rufi kawai akayi yaje shagonsa na Sabon gari ya d'auko kudi Nan da Nan aka fara saka Mana cieling aka Yi plaster ko penti baayi ba muka tare a Haka.


Tijjani kuwa Dan kudin da yake tarawa a banki ya Ciro ganin da Dan yawa yasa ya Kama karamin gida

Sabida bikinsa da akeyi

Ya Dan Yi hidimar biki da canjin hannunsa sauran Kuma ya kafa kanta anan k'ofar gidansa ya zuba Dan abinda bazaa rasa ba.

Yan unguwar da yake zaman mutunci dasu ne Suka Masa komai da dangi ya Kamata su Masa

Sati biyu da aurensa yana Kan benci zaune ya ga an sauke Hajara da Safiyya a taxi sun nufo wajensa Hajara kuwa na washe Masa baki......



Ayi maneji kaina yau Dan ciwo yake wlh kamar bazanyi bama na daure nayi
[6/26, 3:38 PM] +234 803 635 0240: *NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*


*Page 26*


*JIYA NAYI MISTAKE WAJEN DA NASEER YAKE CEWA YANA CIKIN SHARUDAN MUSULUNCI YARDA DA KADDARA MAI KYAU KO MARA KYAU INSTEAD CIKAR IMANIN.MUTUM SHINE YA YARDA DA KADDARA MAI KYAU KO MARA KYAU THOUGH NASAN ZAKU SAN MISTAKE NAYI DAN BAN BI BA JIYA LABARIN NAEEMA AKWAI TAUSAYI ALAJABI MAMAKI KU DAINA KOKWANTO AHAKA WLH NA CIRE WASU ABUBUWAN BAN SAKA BA KUNJI NACE WLH ALLAH YA BAMU IKON CINYE NAMU JARRABAWAR AMEEN*


Tijjani sakin baki yayi Yana kallonsu har Suka karaso cikin mamakin Mai ya kawo su wajensa Yama akayi suka San gidan daya koma Nan kuwa bai san tsohuwar unguwar daya baro Nan suka je aka kwatanta musu ba.

Daga yanayin fuskar Tijjani yasa itama Hajara ta had'e Rai tana San amfanin da karfinta na uwa sabida Tijjani ya Shiga hankalinsa

"Baka ganemu bane ka saki baki kana kallonmu"?


"Ba Dole na saki baki na kalleku ba umma ai Naga bansan da zuwanku ba Kuma kema kinsan halin da.muke ciki Kuka kwaso Kuka taho.

Umma Kinga kayan Dana kasafta nake siyarwa duk a dalilin tsanar da kikayi wa Naeema Kika jawo mana

"Dan ubanka zaka wuce muje ciki ko tareni zakayi da surutu mu Sha wanan uban tafiya ka tsaya kana min zancen banza"

Hajara tace tana harararsa

Mik'ewa yayi Yana cigaba da Magana ciki ciki.

Yayi gaba suka bishi a baya.

A madaidacin palon suka yada zango

Tijjani ya hau kwallawa matarsa kira Murja

Hajara kuwa cikin mamaki ta kalleshi tana "wacce Haka naji kana Kira"?

"Matata Mana Umma"?

"Matarka Tijjani yaushe kayi auren yanzu Ina mahaifiyarka Tijjani kayi aure batare da nasani ba"


"Ai fa Umma nayi aure sati biyu kenan ki saka albarka kawai"

Hajara na k'ok'arin Magana Murja ta fito daga d'akin tana Hamma ganin Hajara da Safiyya yasa ta katse Hamma


Cikin dan murmushi tace "Ashe bak'i mukayi sannunku da zuwa"

Ta karaso tsakiyar palon

Hajara kuwa ta tab'e baki tana binta da kallo tundaga sama har kasa.

Safiyya itama.kallon Sama da kasa take Mata ganin yanda take ta tsatsare su da Ido tana kad'a k'afa.


"Ba bak'i bane Mahaifiyata ce da kanwata suka zo bansan da zuwansu ba kwatsam na gansu"


"Aaa lalle sannunku da zuwa Umma dafatan.kun iso lafiya"

Murja.tace tana Dan rusunawa

"Yauwa"

Kawai Hajara.tace Murja ta mik'e tayi.waje Dan ta kawo.musu ruwa

Ko Gama fita batayi ba Hajara ta rufe Tijjani da fad'a

"Bacemin Kai bakada kudi ba ina ka samu kudin da kayi aure?ka Kuma rasa wacce zaka aura sai wanan mummunan da gani ma Bata da tarbiyya

Ji yanda take tsatsarmu da ido

"Aaa umma Dan Allah kiyi hakuri bana San tashin hankali daga aurena bazaki zo ki dagamin hankali ba gaskiya ki barni naji ma da talaucin danake ciki"


"Tijjani Ni kake gayawa magana Haka gatse gatse daga aurenka Tijjani"?

"Umm Bari na tashi na Baku guri a huta lafiya"

Daga Haka Tijjani ya mik'e ya fito Hajara ta bishi da kallon mamaki.

A daidai lokacin da Murja ta dawo palon hannunta d'auke da ruwa.

Ganin Tijjani baya Nan ta dungurar da ruwan a gabansu ta koma Kan kujera ta zauna tana kad'a k'afa Dan duk abinda Hajara tace tana jinta

"Mai wanan ya zamu kwaso yunwa da gajiya ki wani kawo Mana ruwa"?

Safiyya tace tana hararar Murjan

"Toh ba abinci a gidan Sata zanyi na kawo Miki"?

Itama tace tana hararar Safiyyar.

Hajara kuwa mik'ewa tayi tana "Nida gidan Dana ai baki dai Isa ki Mana iyaka ba ko Naga alamar bakida kunya idonki Kuma Bai ga kunya ba daga take takenki nasan ke ba matuniyar arziki bace"

Wani irin Dariya Murja ta kwashe dashi tana "Hakane Umma gidan danki ne fa Amma kayan ciki nawa ne ki tab'a iya gidan karki tab'a min Kaya ehe"

"Tab Umman kike gayawa magana Haka dan ubanki"


"Kul Kika zageni gwaggo dan har gidan mijina Kika zo Kika sameni kema ki zuciya kije naki gidan mijin kiyi mulkinki a can Idan Kuma kina da aure Zaki iya komawa naki gidan mijin.



Tsabar mamaki Hajara kasa magana tayi Tana kallon Murja tare da jinjina K'arfin Hali irin nata.

Zage zage Suka hau Yi da Safiyya Hajara kuwa tacewa Safiyya ta rabu da ita ta Kira Mata Tijjani a waje.

Waje tayi fuuu kamar zata tashi Sama bayan Yan mintuna sai gasu sun dawo tare.

"Tijjani Ina ka samo yarinya Mara tarbiyya Haka zagina tayi fa daga Safiyya ta tambayeta ya zata bamu ruwa ba abinci"?

"Haba Umma yaushe na zageki ce min kukayi ya zan kawo muku ruwa ba abinci alhalin Kun d'ebo yunwa shine nace Miki wlh ba komai a gidan sai ka kawo Zan girka Amma yaushe na zageki haba Umma ya da girmanki kike karya"?


"Umma nifa bana San hayaniya da tashin hankali maganar Allah wlh banida komai a gidanan Rabonmu da abinci tun Karin safe yanzu ma so nake nayi ciniki na samu kudin cefanen dare idan zaku ci bredi ko biscuit Safiyya tazo ta karba muku kuci kafin ayi girki idan kuma Kuna ganin bazaku iya ba wajen Naseer dai da bakiso kije Nan zakije ki samu yanda kikeso Kinga bazai yiwu nayi sata ba"


"Ke Zaki karbo muku bredi"


Tijjani yacewa Safiyya Yana ficewa daga palon Safiyya kuwa da take ji Kamar taci babu tabi bayansa ta karbo bredin Yana ta masifa Yana gwara ma su koma gidan Naseer shi bazai iya ba

Hajara kasa ma cin bredin tayi Sai Safiyya ce take ta tusa bredin Kamar tayi kuka sai zabgawa bredin harara take

Suna Jin Murja nata kananan wakoki a daki

Makircin Murja ya bawa Hajara mamaki tsananin bakin ciki da takaicin Tijjani duk ya tsaya Mata a rai.

Matarsa kuwa da yau akwai karfin tsafinta a tare da ita da yau sai dai wani ba ita ba amma a hakan ma zata san abinyi .

Safiyya kuwa Tana cin bredin ta fara magana tana "Gaskiya Umma gobe mu tafi gidan Yaya Naseer Zaman mu anan bazai yiwu ba Dan wlh zuciya na iya sawa na kashe wanan matar da duka.
Gashi Yaya Tijjani shima sai wani wulakantamu yake yi.abinda yaya Naseer bazai Tab'a Mana kenan ba bama Zan iya jure yunwa ba gwara.mu koma can banza banza zamu ci abinda ranmu yakeso ko bashida kudi wlh zai Nemo ya kawo Mana duk wanan masifar Umma wlh ke Kika jawo Mana Kika cucemu yanzu rabon Dana ci nama har na manta"


"Hmmm bazanje gidan Naseer ba Safiyya Amma idan kina San zuwa Zaki iya zuwa ke kadai"


Extra d'akin da babu katifa sai Leda anan su Hajara suka.kwana Inda ta ringa cin alwashin cin uban Murja ta tsani mutane biyun Nan Naeema da murja.


Naseer.


Wani irin rama yayi Sabida tunanin halin daya fara tsintar kansa a ciki.

Tunda wanan ifitilai ya Fad'o Masa shagonsa ma ya fara ramewa kamar.ana yashe kayan ciki ya rasa ma Ina kudin shagon yake zuwa balle azo Kan riba.

Tsabar ma San ya Dan tattala kudin nasa kasa sakin kudi yayi ya gyara gidan da suka koma dakuna hudu ne a gidan manya sai paluka biyu ba Wanda yayi wa fenti dakuna biyu kawai ya gyara sai kitchen da band'aki biyu.

Dak'yar ya sakewa su zahira makaranta Mai Dan saukin kudi.

A Haka rayuwa ta ringa tafiyar musu Naseer Duk kudin daya juya baya Masa albarka yaran shagonsa kuwa Suna ganin ba wani Samu suke ba Suka ware.

Halinn da Naseer ya tsinci kansa a ciki na iya sawa Mai raunin imani zuciyarsa ta buga Naseer da ya saba kama kudi sai gashi kudin suna neman Yi Masa wahala tunda ya Shiga halin Nan Bai tab'a hawaye ba sai daya wayi gari yaga duka yaran shagonsa dayake taimakawa duk sun gudu tun shagonsa na da kyaun gani har yazo ya zamana babu Kayan ma sai daidaiku.

Ahaka ya Kara siyar da filayensa da gidajensa suka kone na Sharada da gadon kayan har Dana Gefen gidansa na gadon kayan ya Kara zuba Kaya a shagon nasa.

Sai dai me Dan kananan

5 Comments On NAGA TAKAINA
avatar
huda

1 year ago

Reply

Chapter 21

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment