Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nauyi.


Karfe Hud'u ciwon Mara da baya ya tasheni haihuwa na shidda take nasan Nakuda ne gashi kasana naji kamar Ana danno ni.

Saukowa nayi daga Kan katifar tare da tashin Naseer.

Ai Yana bud'e Ido naji kamar ya tasomin da Nakuda gadan gadan sallati kawai nake shi kuwa ya zura doguar Riga yayi waje kafa ba takalmi.

A mak'ota ya samo Aron mota Yana zuwa ya taimaka min na mik'e cikin tashin hankali ya hau cemin bashida kudi.

Kasan katifata nasa ya daga ya d'auko jakar kudina.

Jiki na rawa ya d'auki kudin ya dau jakar Dana hada kayan haihuwa Dan Ina shiga watan haihuwa na hada komai na bukata.

Asibitin dake kusa mukaje.

Zuwa lokacin sosai naji kamar Ana dannoni da k'arfi.
Ko tafiyar ma ban iya yi ba sai da gadon marasa lafiya aka zo aka daukeni aka Shiga Dani dakin.


Muna Shiga d'akin kafin nurse ta saka Safar hannu naji faya ta fashe nayi Nishi da k'arfi.

Sai kuka baby mukaji.

Take naji kamar an d'aukemin duk ciwon da nakeji.

Na hau numfarfashi
Ban damu da kallon abinda na Haifa ba Dan nasan macece.

Inaji suka yanke cibi tare da zaro mahaifa daya nurse din ta hau goge BBY dayar Kuma na kaina.

"Juyo kiga Mai Kika Haifa naji nurse din tace"

Ban juyo ba nace "Macece Rabbi ya Albarkaci rayuwarta"

"Sai dai ya albarkaci rayuwarsa Dan namiji ne"


Wani irin juyowa nayi da balain sauri a daidai lokacin data doramin jaririn a kirjin........

*NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*


Hannuna har karkarwa yake wajen d'ago da jaririn Dan na tabbatar da Namijin ne.

Take na hau hawayen farinciki na Kara kwantar dashi a kirjina inata Godewa Allah da Wanan kyautar da yamin a cikin jaririn Nan ne kawai ban saka Rai da samun namiji ba Amma sauran duk saka Rai nake da maza ne sai gashi a lokacin da ban kawo ba na cire Rai da haihuwa Namiji Allah ya bani.


Kasa d'auke idona nayi daga kansa har Nurse din ta saka Mai Kaya bayan ta goge Mai jiki da man zaitun

Yanda taga Ina binsa da Ido Ina murmushi yasa tace halan ban taba haihuwa d'a namiji ba gyada Mata Kai nayi a lokacin da take sake mikomin shi na karbe shi da Sauri na tashi zaune na zuba Masa Ido ba Inda ya baro Naseer kamar an tsaga Kara Haskena kawai ya d'auko.

Sosai na ringa Jin kaunar jaririn a Raina inajin nurse din na Bari tayiwa Naseer albishir tayi waje da Sauri Dan tasan indai ta Gaya masa kila ya mata kyauta


A bakin kofa ta tada Naseer din kamar zai fado d'akin Ana bud'e kofa yyi Kan nurse din da Sauri.


Ita kuwa ta mik'a Masa hannu tana ya Bata goron albishir

Washe baki yayi daya ga alamar Naeema ta sauka lafiya addua ya hau yi Yana "Na Riga da nasan Mai ta Haifa Allah yayiwa rayuwarta albarka"

Murmushi nurse din tayi tana mamakin yanda daga Naeema har Naseer din suka cire Rai da haihuwar da namiji

"Sai dai Allah ya Masa albarka Dan namiji ta Haifa katoto"

Naseer Ido ya gwallo Yana me kikace.
Kafin ma ta bashi amsa ya fada d'akin da Sauri har Yana tuntub'e.

Daga yanda yaga Naeema na murmushi yasa ya Isa wajenta da Sauri tare da saka hannu ya karbi jaririn Bakinsa har kunne sai hamdala yake Yana kamkame jaririn a kirjinsa.

Sai albarka yake shiwa Naeema ji yake kamar baa Tab'a Masa haihuwa bama inama lokacin da yake da kudi Naeema ta haifi namiji da yaron ya Sha Gata.


Bakinsa ya kafa a kunnen jaririn ya Masa huduba ya d'ago ya kalli Naeema Yana "Allah ya raya Naseer sunana na saka mishi"

Murmushi na saki Ina Jin dadin sunan daya saka mishi nace "Allah yasa ya gaji halin Mai sunan ya bashi ilimin addini irin na Mai sunan insha Allahu addua kawai ce tsakanina da yarana Allah Kar ya jarrabceni da fushi dasu"

Na tsinci kaina da fad'a duk da kallon da Naseer kemin yasa na hadiye sauran maganar.

Karfe takwas na safe aka Sallame mu daga asibitin bayan Naseer ya biya kudin komai.

Hamdala kawai yake a Ransa da Allah yasa Naeema nada kudi da yau asirinsa ya tonu ta Ina zai samu wanan kudin da suka kashe a asibitin.

Naeema sai data saka ya siyi kayan shayi da sauran Abubuwan a zata bukata kamar yanda yake siya idan ta haihu shi kuwa sai dari dari yake baya San kashe kudin Wai Dan Kar ya kare.

Lokacin da muka Isa gida Naseer ne ya rungume jaririn a kirjinsa daya hannunsa d'auke da kayayakin mu Ni Kuma Ina biye dashi a baya Ina takawa a hankali kamar iska zai d'aukeni nakeji sabida rashin kwarin jiki banida burin daya wuce na kwanta sabida ciwon baya danake yi

Bakin Naseer a washe ya Shiga palon

Da Sallama Umma da Safiyya kawai muka samu a palon Umma ta hade Rai tana ta jijjiga k'afa Ina ganin Haka nasan wani rashin mutunci Umma zatayi.

Naseer kuwa tuni Naga ya nutsu duk da gabansa sai daya Fadi da ganin Umma Amma Haka ya nufi wajenta ya tsugunna Ya hau gaisheta.

Wani irin kallo ta Masa ta d'auke kanta batare da ta amsa ba

Shi kuwa ya Kara gyara Jaririn a hannunsa Yana "Umma Naeema fa ta haihu Kinga"


"Sai me dan ta haihu yau ta fara haihuwan?Mai abin murna a haihuwa Naeema da take cike.maka gida da tarin Mata"

"Umma wanan Namiji ne wanan Karin Allah ya azurtamu da Samun namiji"

Ina dab da Isa k'ofar karamin Palo Amma sabida Naga ya Umma zatayi idan taji Namiji na Haifa yasa na tsaya.

Mik'ewa tayi da Sauri ta lek'a fuskar jaririn da Naseer ya juyo dashi Sabida Umma ta ganshi sosai ta gaskata maganar da yake.

Ja da baya tayi tana "Kuma sai ka yarda wanan danka ne.

Sai ka yarda wanan Jininka ne?

Watanmu kusan hudu a gidanan tunda muka zo Maza suke sintiri a gidanan wayanda zasu Zo da safe daban wayanda zasu Zo da Rana daban Sabida Kai dakiki ne an asirceka idonka ya rufe shine zaka ringa murnar ta haifo maka namiji.

Kar idonka ya rufe ka kasa gane gaskiya har Ina Naeema zata samu kudin da zata gyara gidanan Bata tsaya iya Nan ba ta siyi engine biyu Kai Kaga irin kudin datake rik'ewa kuwa Amma dayake zuciyarka ta mace idonka ya rufe duk baka gani ba ka hau rawar kafar ta haifo ma namiji indai Jininka ne ai mace zata haifo iya wanann ma ya Isa yasa ka Gane Dan Nan ba naka bane"


Yanda nakejin zuciyata da jirin dake d'ibana sabida tsananin bakinciiki sheganta min da da Umma keyi da kazafin da take neman yimin yasa.na shige palon Dan Ina cigaba da tsayuwa zuciyata zata iya bugawa Ni Kam wane irin nauyin kiyaya Umma zata gwadamin Wanda Bata gwadamin ba ya isa Haka ai batare aka halliceni da Naseer ba tafiyar Naseer ban fasa numfashi da rayuwa ba Dan Haka barin rayuwar Naseer na huta bazai Hana shi rayuwa ba Haka Nima idan akwai abinda ke damuna Bai wuce yarana ba Dan Ni nasan matsawar na tafi dasu kamar inasan Naseer ya dawo rayuwata ne.

D'akina na Shiga na kwanta ganin Banga kayan makarantarsu Zahira da jakunnan makarantarsu ba yasa nasan sun tafi makaranta.

Hawaye kawai nake Ina tunanin hanyar da Zan bi wajen barin rayuwar Naseer na har abada.

Allah yasan Ina kaunarsa Amma ya zama Dole mu rabu idan kuwa ya zargeni sabida bashida kudi na rabu dashi baimin adalci ba Dan ko kanwarsa ake matsawa Haka ya Bata shawarar ta hakura da auren.

Ina jiyo Naseer na Mata kana Nan rantsuwa Akan yasan Halina ko shekara goma zaiyi Zan rik'e Masa amanar aurensa wlh Dan Nan NASA ne Dan Allah ta karbi jaririn taga yanda Suke kama.

Ita kuwa Umma dagewa kawai take Tana rantsuwar ba dansa bane Wai Ni Mata nake Haifowa inaji tana balai Yana Bata hakuri.

Inaga Safiyya ce ta saka Baki naji ya daka Mata wani uban tsawa daya saka jaririna razana ya saka kuka.


Naseer kuwa kukansa Bai sa ya bar wanke Safiyya.kamar zai ajiye jaririn ya rufeta da duka ba yayi ta cewa ta Kai shi bango wlh xai koreta daga gidansa Dan bazata Zo tana hura Masa wuta a gida ba shiyasan wani zubin ita ke zuga Umma.

Ita kuwa Umma cewa take "Kar ka wani wayance Ni zaka yiwa fada ba ita ba tunda Ni nake Maka magana"

Kukan Jaririn yasa Naseer bai ce wa Umma komai ba ya nufo d'akina Ransa a balain b'ace Yana shigowa d'akin.

Ya mikomin shi na karbe shi take kuwa yayi shiru na Ciro abincinsa na saka Masa a baki tare da bismillahi ya kuwa cafe da Sauri a fili nace "Allah ya rayaka Walid ya shiryaka bisa tafarkin musulunci"

Ameen Naseer yace can kasar murya idonsa ya kad'a yayi jawur ban nuna Masa naji Haushin abinda umma tamin a fuska ba Amma ya juyo ya hau bani hakuri Yana na taimaka masa mahaifiyarsa ce babu yanda zaiyi da ita Yana Nan Yana gayawa Allah.

Murmushi kawai nayi Dan daya bani hakuri da Kar ya bani hakuri na Riga da na yanke hukunci a raina.

Ce Masa nayi ba komai kar ya damu.

Sai a lokacin ya saki ajiyar zuciya masu markade da suka zo yasa ya mik'e Yana Bari ya markada musu.

Amma kafin Nan Bari ya saka Safiyya ta dafamin ruwan tea da Sauri na ce ba sai ya sakata ba ya Bari na Gama bashi Zan fito na Dora ruwan da kaina tunda Dama Ina bukatar ruwa Mai yawa sabida ma nayi wanka na wanke Walid.

Har zai Musa min Kuma ya fasa Yana bari ya fara doramin ruwan inyaso sai ya fara markaden.

Nima.fada kawai nayi bazan iya tashi ba sabida jirin danake ji.

A kitchen ya tarar da Safiyya itama ta juye musu ruwan zafi a jug ga kwai ta soya a faranti duk a kudin Naeema da suke Mata fin k'arfi su kwace.

Yanda Naseer ya hade Rai yasa ta fice daga kitchen din da Sauri.

Tana fita ya Dora ruwa a babban tukunya ya fito ya kunna engine ya fara markaden.

Yana cikin yi ma Isihu ya shigo ya fara markaden.

Shi kuwa Naseer ya koma.dakin ya d'auko ledar zanin da Naeema ta Bata ya zuba a katon baho dayake akwai Omo da dettol a bandaki ya zuba ya koma kitchen

Ganin ruwan yayi zafi sosai yasa ya cika flask ya Kai daki ya juya sauran a katon Bokiti.

Duk abinda yake Umma da Safiyya binsa kawai suke da kallo.

Umma kuwa kamar ta fashe Dan bakin cikin yanda Naseer yake neman Zama bawan Naeema

Shayi Mai kauri ya hadamin ni kuwa na fara sha

Ganin Yana k'ok'arin fita yasa nace Masa Dan Allah ya bawa Isihu kudi idan ya gama markaden ya siyo.min nama bakina ba dadi.

Zama yayi a gefena Yana "Naeema ba asan Raina Kika haihu banida ko sisi ba wlh bana Jin dadi Amma ba yanda zanyi Haka Allah ya hukunta Naeema na baki labarin ban zo gidanan da ko biyar ba Kar muzo muyita kashe kudin ya Kare kiyi maneji da Abunda Kika samu gaba idan Allah ya hore duk Zan Miki Abunda ban miki ba a haihuwar Nan"

Murmushi nayi na ajiye kofin hannuna Dana Gama shanye shayin na kalli Naseer Ina "Naseer karka damu Ni Mai fadawa wani ne halinka idan kana dashi ma baya b'uya amma karka damu Ina da kudi ba iya na hannunka ne damu ba a d'akin Nan ma akwai kudi Banda dashin danake har ajiya nake badawa ka Bari idan na samu Kaina sosai zamuyi shawara ko zaka fitar da shago ka Dan zuba provision ka ringa siyarwa da zaman hakan.

Tun kafin na karasa Naga Naseer ya washe baki ya hau murna Yana shimin albarka.

Yana "Kice idan su Zahira sun dawo na fita kasuwa da kaina na siyo Dana Kaya Dan Naga kayan mata Kika siyo Masa yanzu na kashe duk kudin wajena"?


"Gyad'a Masa Kai nayi Ina murmushi"

Ya fice waje da Sauri Yana murmushi Ni kuwa Jin na Dan ji kwarin jikina yasa na mik'e na hada ruwan zafi a na wanke Walid na shirya shi na rufo kofata Nima na Shiga wankan.

Naseer kuwa Yana fitowa daga d'akina kayan Naeema daya jika ya sunkuya Dan ya wanke.

Hajara ta mik'e a fusace Tare da daka Masa wani uban tsawa "Kai yanzu Dan asara da mutuwar zuciya Mai aiki Naeema ta maidaka kenan sabida baka da kudi shine ta hadoka da wankinta kayi Mata kana matsayin mijinta?


Da lokacin da kake da kudi Kai kake mata wankin dayake Bata da mutunci sabida taga bakada ko sisi shine zata ce ka wanke mata kayan jini toh wlh bazaka wanke ba indai nice na Haifeka bazaka yi wankin Nan ba"

"Umma wlh Ni nake Mata wanki idan ta haihu bawai ita ta Sakani ba Dan gani nake Bata da Mai matan idan bani ba"

"Toh wlh bazaka wanke ba idan Kuma ban Isa dakai ba zaka iya wanke Mata"


Umma tace tana jijjiga k'afa.

Duk Inda Naseer yaso shawo Kan Umma tub'urewa tayi.

Ni kuwa Ina Jin duk abinda ke faruwa hakane yasa Ina saka Kaya na fito

Ban ko kalli Inda Umma da Naseer suke tsaye cirko cirko ba na jawo bahon na hau wanke kayana.

Umma kuwa ta hau zagina tana ita tasan asirce mata da nayi ban Isa na bautar Mata da D'a ba.

Bance Mata komai ba Naseer kuwa kamar yayi kuka sai neman kwayar idona yake Dan ya bani hakuri nak'i kallonsa.

Sai Dana Gama wankina na shanya na Shiga kitchen Dan Ni Dama tunda na auri Naseer bansan Zama Wai na huta idan na haihu ba Ni nake komai nawa.

Girki na Dora naje na dauki robar custard da gwangwanin da ya cika da kudin markade

Na zuba a ledar dana gani na ajiye gwangwanin custard din na koma d'akina.

Ina cikin had'a kudin Naseer ya shigo yana k'ok'arin Magana nayi sauri na dakatar dashi.

Ina Kar yace komai indai Umma ce na Riga da na Saba da kome zatamin ba wani Abu sabo.

Bai iya cemin komai ba yayi shiru Ina Gama hada Kan kudin na cusa a akwatina ganin waleed na bacci yasa na Kara barin d'akin na koma kitchen na zauna Dan girkina yayi na sauke.

Ina cikin juye abincin su Zahira suka dawo.

Ina ganin ta dawo na bar kitchen din dan nasan zata karasa min girkin.

Su Minal kuwa d'akina sukayi aguje suna murna sunyi Kani irin murnar da suke ne Yasa na manta da damuwar da nake ciki.

A takaice da kudina na wajen Naseer Naseer ya siyowa Waleed Kaya har dasu Zahira ya taho da Naman danace Masa.

Duk abinda Muke ciki Umma idonta na Kai.


Kudin dashina kwana uku da haihuwa nasa aka karbomin na bawa Isihu Dubu goma akan ya kaiwa Matar Ala.ramma Dan a gidansu na siyi katon ragon da zaa yanka duk da ba haihuwar fari nayi ba Amma kasancewar namiji ne hakane yasa na saki bakin Aljihu nayi dinkuna nayi komai na taron Sunan Waleed Naseer sosai.nake ganin farinciki kwance a fuskarsa Dan shima burinsa yayi taron Amma bashida kudi

Shima dinki na Masa kala biyu.

Umma kuwa ta Kira shi ta hau balai tana masifar sai ya tambayeni Ina na samu kudi Haka sanan ya zaayi nayiwa kowa dinki har da shege Isihu ita da Safiyya ban.musu ba.


Naseer kuwa ce Mata yake ba shi yayi dinki ba Ni na musu komai.na gidan Ni nayi.

Ita kuwa Umma dagewa tayi sai Nima na musu dinki.

Ni kuwa Naseer da Yar murya ya zo wajena Yana na bashi Rance Ni kuwa na murzawa idona toka nace Masa bazan bayar ba Dan kudin karuwanci ne Ashe Umma na labe tana jinmu ita kuwa ta hau tsinemin tana gwara Kar na Bata mantawa.ma tayi kudin karuwanci ne.


Sosai sunan Waleed ya cika da mutane har k'ofar gida.

Abinci kuwa sai da aka rabawa mak'ota mmn Mannir ma sai data zomin itama da abun arzkiki har da.makotana da mukayi zaman mutunci dasu.


Na yarda idan kana da abin hannun ka mutane har rububin muamalla suke Yi dakai.

Bazan iya lissafa Abubuwan Dana samu a sunan Walid ba Dan har na kusa maida kudin Dana kashe masu kawomin markade da customers Dina masu siyan zobo da ruwa duk baa barsu a baya ba Haka suka ringa zuwarmin barka da abin arziki.

Daga Ni har yarana da Naseer Shar mukayi bazaka yarda muna cikin wani matsala ba.

Umma kuwa da Safiyya tsabar bakin ciki barin gidan sukayi Basu dawo ba sai da aka Gama taron

Makotan arziki suka Tayani wanke komai da gidan.

Ai fa Bayan suna Umma kamar ta jefani a wuta matsamin tayi ta sakoni a gaba a gaban Naseer zata Zo har d'akina tayi ya zagina tana tsinemin Wai nayi asiri na kwace dukiyar Naseer.

Naseer ya zama kamar Dan aiki a gidan Dan Haka na fada Mata Inda naje nayiwa Naseer asiri.

Idan Ina San nayi magana sai ta saki ihu ta hau cewa na Mata rashin kunya Naseer na kallo.

Naseer masifar.umma yasa Dan kwanciya hankalin daya samu ya fara Rama.

Ni kuwa a hankali na fara kwashe.kayana Ina bawa Isihu Yana kaimin gidan matar Ala ramma Dan Bayan mmn Mannir itace mace ta biyu Dana bud'ewa cikina duk da shawarar data bani na sakani zubar da hawaye naji kamar bazan iya ba Amma babu yanda zanyi Haka Allah ya kaddaramin.


Kwana hudu kenan Ina rashin lafiya da kuka a b'oye da Naga lokacin Dana saka wa.kaina barin gidan Naseer nata matsowa.

A cikin yarana ba wacce nake balain tausayi kamar Zahira da Raheema ba Naseer ne a gabana ba yanzu yarana kawai nake tunani.

Idan Naseer yaga Ina kuka hakuri yake bani Dan ya d'auka takurar da Umma takemin ne Nan kuwa bai San tunanin da nake daban ba.

Ahaka dai ranar Dana sakawa kaina Bayan da Naseer ya tafi massallaci nayi sauri na goya Waleed a bayana.

Na Shiga d'akin yarana a zaune na tada Zahira kamar ma batayi bacci ba Haka kawai naji hawaye na neman zubomin nayi sauri na mayar Ina ta tashi kanennta suyi sallah.

Yanda na hade Rai yasa ta Shiga band'akin tana waiwayena kamar tasan tafiya zanyi.

Dak'yar ta Shiga band'akin.
Ni kuwa na toshe bakina sabida kukan dake neman k'wacemin na karewa yarana kallo na fito daga d'akin na ajiye zungureren wasikar Dana rubutawa Naseer a bakin kofar dakina na na fice daga gidan nabi ta Bayan gidanmu ta hanyar da ba fiye bi ta hanyar ba inayin Nisa da gidan Waleed ya fara tsalla kuka.......

*NAGA TA KAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸


®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*

*Page din jiya duk haushin Naeema akeji akan ta gudu inaso ku ringa saka kanku a matsayinta she is a human being itama mutum ce Kamar kowa ita tasan azabar da take Sha a hannun uwar mijinta karku manta mutuwa ma na raba uwa da Yaya har uba ma Yara su tashi ba uwa ba uba Kuma yaran bazasu fasa rayuwar da Allah ya tsara musu ba yanda Allah ya tsallakar da ita da ga duk wani sharrinsu take rayye har yanzu Allah Nan zai Kare Mata yaranta Wanann shine guduwa da tayi na biyu na farko da yaran Naseer yabi bayansu ta dawo abubuwa suka Kara cakudewa har ya Kai su ga Zama a cikin wanan halin ta bar Yara Dan Naseer Kar ya biyota kila ta gaji yau da gobe a Kuma Yi hakuri dai a cigaba da bibiyar labarin Ana Kai zuciya Nesa Kar a daki Naseer ko Naeema*🤣🤣🤣🤣🤣🤣

*This page is yours Surayyams Marubuciyar Ajalin so Ina San yanda kike bin novel din kike Kuma fito da lessons din ciki kina fahimtar da mutane*


*Page 34*
Kuka nake kawai Ina jijjiga Waleed da naji kukansa ya karade ko'ina kamar ya saka lasifaka Sauri nake ta zabgawa Ina ganin Kamar Kukan waleed na iya sawa Naseer ya biyomu

tunanina rabuwa gida biyu yayi Ina tuno yanda Zahira ta Shiga band'aki tana waiwayena.

Irin dukan da Safiyya da Umma ke Mata Agaban idona sabida kawai a yarana tafi Kama dani komai nawa ta d'auko kiyayyar da sukemin ya shafeta

Anya matakin Dana dauka shi ya dace kuwa na bar Wa Umma yarana Ni nasan sai ta kashe su.

"Idan Kika biyewa Makomar yaranki Uwar mijinki watarana zata ci Galaba akanki wajen rabaki da Numfashinki ganganci ne cigaba da zama da ita tunda kiyayyar da take Miki a bayyane yake Naeema rayuwa da kike gani kowa da yanda Allah ya tsara Masa yau da mutuwa kikayi fa Kika bar yaran?ko kinsan akwai yaran da tun suna kananu Suka taso ba uwa ba uba kin taba zuwa gidan marayu Kinga yaran da basu da kowa suke rayuwa su kadai Zahira shekararta Sha hud'u ta tafi na Sha biyar Nadeeya tana da Sha uku har ta iya girki ta kula da kanenta Kinga kuwa da wayonta.

Kina ganin Naseer zai Bari Mahaifiyarsa ta cutar da yaransa idan ke ya bar mahaifiyarsa ta gana Miki azaba bana Jin zai Bari a tab'a Masa yaransa Dan Haka tafiyarki shi yafi alheri Neeema inyaso kiringa zuwa kina duba yaranki a Kai akai"

Maganar matar Ala ramma da nake cewa Aunty ya fad'omin yanzu Haka ma gidan kanwar ta zanje na jirata idan gari ya waye zata kawomin kayana daga Nan su rakani Tasha Dan isihu ya dage sai yaje ya ga garinmu yaga Inda nake zaune kafin ya dawo


Duk da hankalina ya rabu gida biyu ahaka nayita zabga Sauri har na iso bakin titi na tsallaka na cigaba da tafiya har lokacin kuka Waleed yake Ina jijjiga shi Nima kaina kukan nake a Haka na iso gidan kanwar Aunty na bubbuga ba dadewa kuwa ta bud'e dayake mun tab'a haduwa a gidan Ala ramma ta sani ta kuma San da zuwana

Ciki na shiga ta rufe k'ofar Haka kawai na fashe da kuka da yake mijinta baya gari Palonta muka Shiga na kunto Waleed na rungume shi a kirjina Waleed Kamar yasan Mai ke faruwa bashida kuka amma sai gashi yana ta kuka.

Hakuri kawai take bani tana rarrashina.

Nidai gani nake kamar bazan iya tafiya na bar yarana ba ada na dauka zan iya Amma yanzu Kuma da na fito daga gidan Ina tuno yanda Suke wa yarana sai naji bazan iya ba.


Dayake itama kanwar matar Ala ramma yayarta ta Bata labarin komai a kaina cikin tausayawa ta fara min magana tana "Ni sai nake ganin kamar guduwa ki bar yaranki bashine mafita ba Naeema kikayi hakuri duk tsawon lokacin Nan ballantana yanzu Agaban idonki ma Ana cin zalin yaranki Ina ga bakya Nan nidai Dan aunty ta dage ki tafi ne wlh da kinyi zamanki ai wuya Bata kissa Kuma komai Mai wucewa ne idan kayi hakuri idan. Allah ya raya Miki yaranki wlh da kansu zasu iya kwato Miki yanci a wajensu tunda ance Minal karama ma na musu rashin kunya Amma har ga Allah Nima ban goyi bayan tafiyarki ba"

Cikin tsananin kuka na fara magana Ina "Ya zanyi Nagaji ne mmn Abdul nayi hakurin nayi biyayyar nayi rokon duk a banza shekara Sha biyar Ina k'unsar bakin ciki mmn Abdul ba Dan Ina da tsawon rayuwa ba da sun Dade da kasheni wlh gajiya nayi da abinda sukemin tacemin Ni Mayya ce naki rabuwa da danta Ina neman na kaina tace karuwanci nake yaron Nan sai data sheganta shi Naseer baya iya komai sai dai ya bani hakuri nace Miki da cikin yaron Nan guba suka zubamin a abinci Dan kawai naci na mutu yau da gobe watarana zata iya cin Nassara akaina shiyasa na yanke tafiya na bar Mata gidan indai na tafi da yarana wlh Naseer sai ya biyoni Ni Kuma shiyasa na bar yaran Dan tasan dgsk nake zan iya rayuwa babu Naseer Amma yanzu Dana bar gidan wlh sai naji kamar bazan iya tafiya ba Ina tausayin yarana da basu ji ba Basu gani ba bana San a cutarmin dasu gwara Ni na cigaba da Shan wahalar da su Sha wahalar.

Kuka itama mmn Abdul ta hau yi tana "Allah ya tsinewa

5 Comments On NAGA TAKAINA
avatar
huda

1 year ago

Reply

Chapter 21

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

11 months ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment